Gyaran Jiki

Kayan Make Up da yanda ake amfani da su 

 

Kayan Make Up da yanda ake amfani da su

Kafin mu fara bayani yadda akeyin kwalliya ya kamata mu fara bayanin a kan kayan kwallyar da amfanin kowanne, hakane zai sa afi saurin fahimtar darasin.

Sannan idan ana bukatar cikakkiyar kwalliya ta fuska to dole sai anyi amfani dasu. Gasu kamar haka.

– Concealer

Eye liner/gel liner

– Eye shadow

– Eye Lashes

– Jagora

– Mascara

– Foundation

– Highlighter

– Setting Powder

– Contour

– Lipstick/ Lips Glow

– Finishing Powder

– Beautify blender Sponge

– Shimmer

– Brow Gel

– Brushes Set

– Blush

– Moisturizer/Primer/ Make Up Setting Spray

Wadanan sune jerin kayan kwallyar da muke dasu. Zamu bisu daya bayan daya muyi bayanin yadda ake amfani da kowannensu.

1- CONCEALER;  A na amfani da concealer wajen gyara gira bayan an zana ta da Jagira ko wani nau’in Jagira don daidaita gira ya bada shape.

Sannan ana amfani da concealer don boye tabo ko kurajen fuska. Haka kuma ana gyara karkacewar eye liner ta saman ido da ita.

Me ake nufi da Bitcoin Crypto Currency 

Har ila yau, ana gyaran baki da ita in dan aka sa janbaki ya karkace, ko ya haura saman baki ko kasansa.

Sannan ana highlighting da ita, kasancewar tana zuwa a nau’i kala kala, akwai nau’in da take zuwa kamar pencil, tana kuma zuwa a nau’in tube,  sannan akwai nau’in da take zuwa cikin mazubi mai kamar kwano ko plate.

2- JAGIRA; Wannan wani nau’i ne na kayan kwallya da yake zuwa a nau’in irin na pencil da kaloli iri daban daban.

Sannan tana zuwa a nau’in gari da ake amfani da brush ana zana ta. Ita ake cema Gel liner.

Ana amfani da ita wajen zana gira, wato bin layin sama da na kasa na gira da kuma cike shi. Sannan ana iya sawa a saman ido, a matsayin eye liner, kuma ana sawa a kasan ido a matsayin kwalli.

3- EYE SHADOW; Eye shadow nau’i ne na kayan kwalliya, da ake amfani dashi don a kawata kwalliya.

Ana sanya shine a saman hular ido, wasu ma Suna santa shi a kasan ido. Tana zuwa a nau’i kala kala, akwai mai zuwa a yanayin pencil, akwai mai zuwa a plate ko dam akwati akwati dauke da kaloli daban-daban.

4- EYE LINER/ GEL LINER; Suma Suna taka muhimmiyar rawa wajen kawata kwalliya. Ana sanya su ne a saman ido bayan an shafa eye shadow kuma ana iya shafa su a kasan ido. Suna zuwa a tube, ko kuma gari sai a kwaba.

5- MASCARA; Ana amfani da ita wajen taje gashin ido, ya tashi yayi kyau sosai, sannan ta kara baki saboda mascaran da aka shafa. Tana zuwa a mazubin tube.

6- FOUNDATION; Wannan wata powder ce mai ruwa, ana shafa ta kafin a shafa powder, tana kara ma kwalliya kyau sosai. Tana zuwa a nau’i kala kala, wata mai ruwa wata mai maiko.

7- HIGHLIGHTER; Shima wannan wani nau’in kayan kwalliya ne, da ake shafawa bayan an shafa foundation.

Ana shafa tane a Inda akeso a bayyana kwalliya , misalin saman goshi, kasan ido, kasan gira, gefen kunci, kasan hanci, da kasan baki. Tana zuwa a nau’i kala kala, tana yanayi da concealer.

8- CONTOUR/BRONZER; A na amfani da contour wajen boye inda ba a so ya fito sosai a kwalliya. Itama tana yanayi da highlighter wato tana zuwa a cream ko gari.

9- SETTING POWDER; Wannan itace powder da ake shafawa bayan kin shafa Foundation. Amfanin ta shine yana ss fuska tayi luwai luwai tayi kyau, sannan tana rage duk wani gumi da maiko na foundation.

Wannan powder tana zuwa a daskare, a bushe it’s ake cema cake powder. ko kuma tazo a gari wato Lose Powder. Akwai setting setting powder da ake highlights setting da ita da kuma contour.

10- FINISHING POWDER; Wannan powder ce ake amfani da ita bayan an gama shafa kowace irin powder.

11- LIPSTICK/ LIPS GLOW; A na amfani da su ne wajen shafawa a baki ko ince lebe na sama da na kasa. Ba karamin karawa kwalliya suke ba.

12- MOISTURIZER/PRIMER/ MAKE UP SETTING SPRAY; Wannan ana shafa sune a fuska kafin a shafa komai da ya shafi powder.

Primer kuma ana shafa ta ne bayan an shafa moisturizer, amfaninta tana sa kwalliya ta dade bata goge ko ta baci ba.

Kuma tana hana cabewar kwalliya ta hanyar yin gumi, sannan primer na taimakawa wajen blending din foundation a fuska.

13- BLUSHER; A na shafa blusher a kunci bayan an gama shafa duk wata powder mai ruwa ko busasshiya, ana shafa shi a kunci don kara fito da kwalliya tayi kyau. Shima yana zuwa a launi kala kala.

14- BRUSHES; Wadanan brushes suna zuwa a set,    kuma pieces,  kowane brush a cikin set din amfaninsa daban.

Ana amfani da brushes wajen shafa Concealer, Foundation, Eye shadow, Eye Liner, Blush da sauransu. Sune suke taka muhimmiyar rawa wajen yin kwalliya mai kyau.

15- EYE LASHES; wannan gashi ne da akeyinsa na ido da ake sawa akan ainahin gashin idon mutum yana karawa ido kyau. ( To sai dai sanya shi haramun ne tunda kari ne)

16- BROW GEL; Wannan wani mai ne da yake zuwa a mazubi dan karami da ake shafawa akan gashin gira ta kwanta tayi luf luf, musamman in kina da yawan gashin gira yana da kyau ki ringa amfani dashi.

17- SHIMMER; Wannan wata powder ce mai kyalli da ake shafawa akan karan hanci bayan angama highlighting din kan hancin. Yana kara ma kwalliya kyau kaga hancin mutum ya fito zirrr ko da baya dashi kuwa.

18- BEAUTY BLENDER SPONGE; (BBS); Dashi ne ake amfani wajen shafa Foundation tayi blending sosai ta bi fata.

A takaice wadannan sune kayan kwalliya da mata ke amfani dasu ta zamani wadda ta hada da kwallyar Amare, ta zuwa taro ko ta zaman gida.

Sai mun hadu a darasi na gaba Inda zamu shiga wani sashen na matakan yin kwalliya, har a samu gamsasshiya kuma kyakkyawar kwalliya.

Leave a Comment

error: Content is protected !!