Ke kika Jamin Hausa Novel Complete

Izzarso

Ke kika jamin Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Ke kika jamin Hausa Novel Complete

KE KIKA JAMIN

 

 

 

 

 

# Written by Matar soja#

 

 

 

# Ga mai bukatar karantawa naira 500 ne zaku tura ta wannan Account number din 7304736012 Nafisa sani Hassan fcmb, ko katin waya ta wannan layin 09069200154 #

 

 

*Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah.*

 

 

 

 

Written by Matar soja

 

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jinkai

Alhamdulillah duk kan godiya ta tabbata ga ubangijin kowa da komai, ina godiya agareka da ka bani dukkan Abinda na roka daga gareka kaine maiyi kai ke hanawa idan kaso, dubun salati ga fiyayyen halitta Annabin mu muhammad S. A. W, Allah ya kare mana kasar mu daga dukkan fitintinu ka bamu zaman lafiya mai dorewa, Ina matukar godiya agareku masoya wainda kuka nunamin kauna a zahiri dama wainda ke kaunata a boye wainda nasani da wainda ban sansuba kai harma da makiyan ma duk ina gode muku don kuma muna taka rawa da bazarku, nafa dawo masu jira murubuta suyi Arziki da gumin mu domin suyi mana babban guzuri, bismillah a cigaba da gashi ni bana Allah ya isa domin shi dama isashshene don da isar shi muke rubutawa kuma kusamu naku a karkashin mu, nidai ina cikin farin ciki domin Arziki da yabani ta hanyar Azurtani da ya’ dungurumgun wanda ba Abinda yakai ya’ya Arziki a Rayuwa Alhmdulillah Alhamdulillah masoya wainda suka tayani farinciki dama wainda Alkhairansu bazai faduba godiya tareda Addu’a har karshen rayuwarku,

 

UMMU AMMEER

Ummu kulthum tagode sosai Allah yaraya miki yaranki ya kuma karo Arziki nagode nagode nagode Allah yabar kauna

 

SADIYA SIDI SA’ID SIDIYA

hmm baki bazai iya gode miki ba domin ke ta dabance my journalist naga kauna bazan iya cewa komai ba sai dai ince Allah yakaiki BBC london ko DW

 

SALAHA IBRAHIM

Kawar Arziki kenan mezance miki? Babu wata kalma da zan iya bayyana matsayinki saidai inyi🙊

 

UWAR GIDAN DAN FILLO AISHA

Bazan taba mantawa dakeba kece ta farko akoda yaushe don haka Alkharin Allah ya kaimiki ina kan yimiki Addu’a Alkhairi danko ne

 

Wainda ban kiraba Afuwan muna tare yanzu nafara zakuji naku agaba domin akullum kara haduwa nake da masoya don haka inayinku buhu buhu

 

Free pages

 

 

1⃣&2⃣

 

 

Kaduna state

 

 

 

……. Kyakkyawar yarinyace yar kimanin shekara goma shatakwas, tafe take cikin adonta mai matukar aji da daukar hankali, ba shigar banza bace a jikinta shigace irinta bahaushe riga da sket na stamfa hadaddiya koriya da takalma da gyalenta a rataye a gefe kalar na y’an matan yanzu, daurin dankwalinta kuwa a gaban goshi ta turoshi irin daurin zarah buharin nan, tafiyar kamar batason kasa ta tabata, iya haduwa ta hadu domin kalar hutu ya bayyana karara a tattare da ita ga fatar ta kamar a taba jini ya fito saboda ja da sheki, sumar kanta kuwa kana hango tudunta yanda ta nannadeta tayi a cuci da ita,

Dai dai kofar wani d’an karamin giidan ginin kasa ta nufa tareda sa kai zauren gidan dake rataye da jakun kunan al majirai da robobin su, tasa gefen gyalenta tana toshe hancinta cikeda kyankyami ta shige cikin gidan, tundaga nesa ta turo d’an karamin bakinta tareda murgudashi sakamakon hango wata matashiyar mata na kulla gyada a leda.

Ko sallama batayiba tace “wallahi yau ba zan dauki tallar nan ba ko an kulla ta haba mutum da girman shi ace yafita talla saboda zubarda Aji, duk gayun unguwa na kara raina min class,

Zabura tayi tareda daukar wani zungureren ice a gefenta tace ” koma yar wofi kiyimin sallama duk da tare kika shigomin gida tareda tawagar shedanu, koma ki shigon da mala’ikun rahama kafin intargad’a ki.

Da gudu ta kwasa tareda zubarda takalmin kafarta saida takaai waje kafin ta saita kanta tana kunkuni ta dauki dogon lokaci kafin ta dawo tana yin sallamar,

 

“Wa alaikissalam, da karki dawo ki tsaya har uban naki ya dawo mai daure miki gindi in hada dake dashi duk sai mu kwashe y’an kallon a cikin unguwa ai mun saba nida ke kuma kije ki yi duk tsiyarda zakiyi la’asr nayi zaki fitarmin da gyada waje.

Batada baki domin ganin mahaifiyar tata rikeda zungureriyar sandar da zata maka mata idan tayi kuskuren cewa wani abu, don haka sadaf sadaf ta wuce dakinsu wanda yake falle daya ne dankarami mai dauke da yar katifar kwanciyarta sabuwa wadda baban tane ya siya mata domin yafaranta mata don shine ummul khaba’isin duk Wata tabara” da ta ke yi,kasan cewarta ya’ daya tilo a wurin su don haka ta ke samun duk kan gata, duk da su talakawane futuk masu neman na yau da gobe,

 

Karin wasu littafai da zaku so

Har ta shiga dakinta taji sallamar sanyin idaniyarta wato baban ta don haka a guje tafito tana “baba oyoyo yo.

Ledar hannun shi ta fara karba kafin ta mai sannu da zuwa.

Cikeda farin ciki kamar wanda ya shekara da fita bayan baya our guda bai leko gidan ba don baida nisa da gidan da yakeyin gadi, ihu ta buga ganin kayan kwalliyar da yasiyo mata. “Babana nagode maka Allah ya bani hutu sai ka hau katuwar mota mai Ac. Tafada tana tsallen farin ciki, “ho y’ar nema Allah ya baki hutun nan, ai bakiyi kalar wahalaba Allah ya karba miki wannan Addu’ar.

Murmushi Innar ta tayi kafin ta matso tayi mai sannu da zuwa bayan ta Amsa Addu’ar su cikin zuciyar ta, tace “malam ka daina sa mata babban buri a zuciyarta kubi a hankali idan haka Allah ya tsara mata rayuwar ta ba wanda ya isa ya canja mata. “Laure fata nagari lamiri, Addu’a ce mukeyi ba wanda yake fatar ya kare a wahala a rayuwar shi. “Hakane Allah yasa mudace. “Ameen, dazu malam haladu ya shigo akan zancen kudin hayar nan nafada mai kana wurin aiki ko zai leka can yayita sababi dai ya barmin sallahu”.

 

Tuni jikin dattijon yayi sanyi saboda Allah ya gani baida kudin a halin yanzu, kudin hayar da ake biyan shi a hidimar y’ar shi yake karewa saboda duniya bayason yaga ta rasa komai, wanda hakan hikimace gareku iyaye idan har kuka tsarewa ya’yan ku bukatun su bazasu taba kwadayin na wani ba ko samari su janye musu hankali harsu samu hanyar lalata su.

 

“Malam ba a baka kudin watan bane? “An bani laure saidai ina amsa makarantar su hadiza nafara zuwa na biya mata kudin jarabawar ta ta neco da waec kinga duk ta dora burin son rubutawa tareda kawayen ta. “Ai da ka hakura kabari ansallami malam haladu kafin ya watsa mana kaya waje shine rufin Asirin mu.

“Allah bazai hana yanda za’ayiba laure kitayani Addu’a. “Allah ya kawo mafita.

Tana gefe tana sauraran iyayen nata tareda jin tausayin mahaifin nata domin yanzu ta mallaki hankalin kanta tafara fuskantar al amarin rayuwa wanda abaya ba ruwanta burin ta datace abata kawai abata ne ko akwai ko babu ko ta tashi hankalin kowa.

Jin maganar mahaifiyarta yasa tadawo daga dogon tunanin da tashiga.

“Kitashi kiyi sallah kifitar da gyadar nan nace”. Wani irin tura baki tayi tareda buga kafa, Allah yagani ta tsani yin tallar nan da Inna kebata duk da iyakarta kofar gidan su Abin na kona mata rai saboda yanda gayu ke samun damarta wasuma badon zasuci gyadar suke siyaba sai don su kulata ko suji muryarta don ba karamar baiwa Allah yayi mataba, tanada matukar kyau da kuma murya mai matukar dadin saurare.

 

Wacece ita???

 

Malam mudi dan Asalin garin lere ne dake cikin jahar ta kaduna Asalin mahaifan shi yan niger ni yawon bara yakawosu nigeria kasancewar su bararoji har suka yada zango a lere, shikadai ne duk yan uwanshi sun koma niger, shima saboda yasa kanshi karatun Allo yasa koda ya girma iyayen shi zasu koma kasar su yaki binsu yace shi zaiyi karatu ya kuma nemi kudi.

Saboda tsananin natsuwar shi yasa malamin shi yabashi Auren Yar shi lauratu, wadda suka kwashe shekaru goma shatakwas batareda tayi ko bari ba, sai daga baya har sun cire ran samun haihuwa Allah ya Azurta ta da cikin hadiza wadda mahaifiyarta ke kira uwani saboda sunan maman malam mudi taci suke mata Alkunya, a lokacin malam mudi na sana’ar nika, wanda yakan rufa musu asiri sosai kafin lokacinda hadiza takai shekara goma shabiyu lokacin ya sayar da injin dinshi yadawo cikin gari ya nemi haya a wani tsohon gidan da suke ciki mai saukin kudi, wanda yayi hakan ne domin inganta rayuwar y’ar tashi da ilimin zamani da na addini, yana matukar son ganin taci gaba yakuma yalwata rayuwarta kasan cewarta tilo kuma shi mutum ne mai matukar son yaga yaro ya wadatu da ilimi na Addini dana boko, domin tun tana aji uku a secondry tayi sauka yanzu tana dorawa da hadda.

Da farko rayuwar tayi musu tsauri saboda kowa yasan yanda rayuwa take a cikin babban birni irin kaduna idan har bakada tsayayyar sana’a,

Kafin laure tafara y’an saide saide irin na mata a cikin gida wadda tayi matukar taimaka musu ta hanyar cefanen abinda za abaiwa bakin salati,

Daga baya tafara soya irin su Aya da gyada hadiza na fitarwa kofar gida kasancewar unguwar da suke akwai yara sosai kuma sana’ar sai tasamu karbuwa.

Alhamdulillahi komai ya daidaita a hankali sakamakon aikin gadin da yasamu ta hanyar wani abokin shi malam bala wanda tun zuwansu garin suka hadu kuma yana matukar bashi taimako ta kowane gefe idsn abu ya shigemai duhu wanda shima sana’ar gadin yakeyi a wani gidan,

Suna zumunci sosai kasancewar katangar su daya, haka ma yaransu makaranta daya suke zuwa,

Rayuwar hadiza mai sauki ce duk da ta taso da babban buri ganin duk abinda take bukata mahaifin ta na yimata koda zaiyi yaya kuwa,Sai dai rashin hakuri da kuma bata barin sai ta kwana ko a ina ne har makaranta don haka ko samari shakkar tunkarar ta sukeyi saboda kwarjini da Allah ya hore mata, duk da tana Y’ar talaka da yawa ganin sukeyi tafi karfin su. a hankali yanzu girma yazo mata tafara fuskantar Rayuwa don haka bazaka taba cewa y’ar talaka bace ga kyau data debo gefen uwa da uba kasancewar inna bafulatana, don haka fadin kyanta ma bata bakine don ta hada komai da ya’ mace zatayi Alfahari dashi, samari duk inda tabi ta wuce suna kawo hari saidai sam ita batada ra’ayin kulasu, sai mutum daya wanda tsananin nacin shi yasa dole take kulashi wato Isma’il, matashi ne kyakkyawa shima ba laifi Amma talakane duk da sunada rufin Asiri, yana karatu a Abu zaria, ba koda yaushe yake gariba kusan har su malam sun san tsakanin su duk da iyaye basu shigo cikin zancen ba don duk karatu sukeyi.

Yana matukar hakuri da ita sosai domin yana shan wulakanci, don ko ranar farko da suka hadu saida yasha tsiwa, sundawo daga school tana sanye cikin uniform ya tsayar dasu itada Rabi’a y’ar gidan malam bala don itace babbar kawarta.

Sallama yayi musu Rabi’a ta Amsa cikin mutunci, yace don Allah ya sunan kawarki? Wani irin mugun kallo ta watsa mai tareda jan tsaki kafin ta fara sababi ” malam ina ruwanka da suna na? Bashi ko tara? Murmushi yayi mai kayatarwa domin abun. Ya matukar burgeshi yace ” bsko daya sai soyayya da kauna itace takawo hakan, ayi hakuri afadamin bazan iya hakuraba yau na dade ina ganin wucewar ku, don Allah kifada min sunan ki. “Bazan fada ma ko dolene kko kai ka siyamin ragon sun…. Khadija. Rabi’a tayi surin fada saboda gudun karta barota da yawa.

“Wow nana khadija uwargidan ma’aiki, lallai kinci sunan…. Fuuu tayi gaba bayan ta watsamai kasa da kafafun ta a jikin shi kaf tareda lafta mai harara tayi gaba, rabi’a ta zaro ido tareda bashi hakuri cikin sauri “don Allah kayi hakuri bawan Allah batason sauraren maza ne shiyasa. “Never mind kawar mu muje intaka miki ni ai hakan yasa ta kara burgeni ma bakomai ni ai ta gama tafiya dani ba abinda zatayi yabata min rai kawar taki ta gama sacemin zuciyata baki daya.

Dariya tayi kadan haka kawai gayen yabata tausayi don baida girman kai kuma irin shine dai dai da halin dijen malam din,

Saida ya rakota har kofar gida wanda ita dijen tuni ta shige gidansu kamar walkiya, ita ta nunamai gidan, yayi mata godiya ya juya bayan ya fada mata sunan shi,

Bayan ya wucene ta bita tasameta harta kwabe daga ita sai zani tana shirin yin wanka, tagaida inna tareda cewa “haba dije miye haka in bazaki kulashiba meye na watsawa bawan Allah kasa a jiki?

“Toh ni nakirashi ko nace ya tsayardani ko uban me zanyi mai, ni kalar iya shegen shice ma?

…….. “A’a shiryayya kici gaba zaki hadu da dai dai da halinki ai duniyace, ba takamarki wulakanci ba, kowanne d’an Adam nada irin tashi daraja. Inna dake tankaden garin tuwon ta ta fara fada, harara ta gallawa rabi’a tace “wuce kitafi gida kinjamin fadan Inna hankalinki ya kwanta kuma idan har kin nunamai gidan mune ma kinyi aikin banza don zaiga wulakanci ganin idon shi.

 

“Nidai zanso ganin wanda zai kwashe wannan bakin tsiwar naki dije. “Kinga ki ciremin dijen nan ki kirani khadija ta ko hadiza kamar kowa. Ta murguda d’an mutsilin bakinta ja mai kyau cikeda tsiwa,

Dariya tayi tayi gaba tana cewa Inna ni nashiga gida sai anjima. “Ki gaidamin Innar ku, kice ta aikon gyadar nan da tace Anjima zan soya don ta wurina duk ta kare . “Toh Inna zankarbo inkawo miki in zamuje islamiyya.

 

Tundaga wannan ranar Isma’il yake famar nacin zuwa gidansu, aikuwa yaga rayuwa inzai shekara bazata fitoba sai dai in Inna tasani ta korota inta fito kuwa zaisha masifa haka zaice bakomai, malam kanshi tausayin yaron yakeji don wani lokaci har zama suke suna hira dom Ismail akwai hankali, har tanbayarta yayi ” mamana wannan yaron nada kirki ko dashi za’ayi ne? Kuka tasa a ranar tareda buga kafafu tace ita bazatayi Aureba ma saitayi kudi ta siyamai mota mai Ac ta kuma zama likita,

“Toh Allah ya cika miki burinki mamana.

 

Cigaban lbrn

 

Kwalliyarta taci like always tafito da gyadar Inna kofar gidan kamar y’anda ta saba takan Ajiye tayi zamanta a wurin wani lokaci Rabi’a nafitowa ta tayata zama har takare, Allah yagani tana ganin ta wuce da wannan irin sana’ar da inna kesata yi don tasan sana’ar na taimaka musune da bazata fitar ba don ko malam ma bayason ta,

Kamar koda yaushe unguwar makil takeda matasa wasu nakaida kawo wasu na zaman kashe wando , duk jnta take a takure don haka ta mike tareda tsallakawa can gefe gindin wata bishiya don rage idanun gayun da takejin kamar don ita suke taruwa a kullum suna kasheta da mugayen na mujiyarsu,

Fitowar rabi’a yasa tayi a jiyar zuciya ta tsaya cak agefen hanyar tana jiran karasowar ta,

 

Da tsananin speed motar tashigo unguwar, bakace wuluk baka ko ganin wanda yake cikinta kasancewar ba titi a wurin saidai hanyace da ababen hawa ke yawan bi wurin ya dandale sosai saidai idan lokacin damuna ne wurin yakan kwabe, kowadai yasan irin yanayin kuma in lokacin bushewar yanayine kuma kura kan tashi.

Don haka ko yanzu gudun da motar ta kwaso ya janyo gaba daya jikin su ya bade da kura kasancewar suna gefen hanyar,

“Kutumelesi. Khadija tafada cike da takaici tabi motar da kallo, ganin ko kokarin tsayawa motar batada niyyar yi, saida sukayi gaba sosai suka faka kofar wani gidan dake kulle wanda a nan ne mahaifinta ke gadi wanda tazarar shi da nasu baida wani yawa . sai dai tsawon rayuwarta bata taba zuwa wurin ba koda wasa, duk da mahaifin ta na ciki 24 hours,

Tayi matukar jin haushin mai motar wanda har tayi kudurin da ace nan kusa da ita ya faka sai ya gwammace kida da karatu don sai ta rama Abinda yayi mata.

 

“Gimbiya ta Ayi hakuri ungo wannan ki goge kurar ya riga ya wuce kiyi hakur…… Tsit yayi saboda kasar da ta debo ta watsa mai a jiki, “kaima kayi hakuri tunda hakan ba wulakanci bane a ganin ka mtssssw. Zaro idanu Rabi’a tayi saboda abin na dije ya wuce hankali tayi saurin rikota ” meye haka dije don Allah Isma’il ne fa. “Ai ba malam bane uba na ko? Ko na kirashi shima da shegen nacin shi kunga kubarni kawai kuma wancan mai motar in kere na yawo zabo na yawo watarana zasu gamu.

Dariya suka samata shidai Isma’il yana kakkabe jikinshi yana cewa “Allah ya huci ran gimbiya ai kin ramaa jikina toh ya wuce inkuma bai ishekiba ki kara nidai na rokeki kibar wancan ba laifinshi bane yanayin hanyar ne kema kinsani.

“Kaga malam kama hanyar ka ka wuce sana’ata nafitar ban bukatar surutu.

…. “Ayi hakuri ni ai hajiyata ta aikoni siyan gyadar don haka ta nawace duka zan siya?

“Toh bazan siyarba saboda mugunta yaran unguwar naso zan siyarwa wani can?. H53

“Hhhhh my khadija rigima don Allah Rabi’a kirga mana bari in Anso leda a can shagon ki zubamin. Yayi gaba yana mamakin halin darun ta.

 

“Gaskiya dije bakida hali wai ke lafiyar ki wata rana kina Abu kamar mai tabin kwakwal wa? ” gidan malam niga ce karewar tabin hankali ko dawanau kicema wancan gayen enough nagaji da ganin shi yadaina bina haka. “Ai kinada baki kifadamai ai ba yau farauba da yafara jin mugayen kalamai daga bakin ki.

“Waini ke kam nice kawarki ko shi? ” kece ta….. Shiru tayi ganin wannan motar na dawowa saurin kaucewa Rabi’a tayi tareda janyeta saboda mugun sharo gudun dataga motar nayi saidai tana gotawa tadawo baya kadan taci burki agaban su,

Da mugun mamaki sukebin motar da kallo dukansu kafin suce wani Abu an zuge gilashin motar wanda ke gefen su wato mazaunin driver, wani irin ni’imtaccrn kamshi ne yayi musu welcome, dukan su kallon cikin motar sukayi wanda ya ke gefen suka kalla matashi ne kyakkyawa saidai bashine Abin kallon ba wanda ke gefen shi a kujerar mai zaman banza dako Alamar daga kai bai da niyyar yi.

Saboda yana ganin ya hadu karshen haduwa don ko ita dijen da mutane ke ganin ta hadu wannan gayen ya dame ta Rabi’a ke gani ga kwarjinin shi ya cika motar, katse shirun su dayan gayen yayi ta hanyar tanbaya” don Allah y’an mata wace hanya zata kaimu cikin gari mu bakine bamu gama sanin kan wannan hanyar ba.

Kafin Rabi’a tayi magana tayi carab ta fara zazzagota “nan daji ne ko ba cikin gari mukeba karku raina mana unguwa malamai kamar y’anda kuke shararo gudu cikin unguwa salon ku buge wani kuce kun buge banza, wallahi karya kukeyi duk wanda kuka buge sai hukuma ta hukuntaku mu baruwan mu da wasu kudin ku.

Kallon bakinta yakeyi kafin yayi saurin kallon na gefen shi ko yana ganin abinda yake gani domin yarinyar tayi karshe badon a wannan unguwar yaganota ba da zaice a kankara take rayuwa ba ma a nigeria ba a kuma geto Aria irin wannan ba, ya mugun shagala da kallonta har baisan lokacin da bakinta yayi shiruba, saida Rabi’a tace “wace hanyar kuke tanbaya? “Um wadda zata kaimu central market. Yayi saurin fada yana kallon Khadija wadda tayi kicin kicin da fuskarta tana kallon jikinta dake da kura har yanzu a take taji dole ta fa rama tunda sunkawo kansu dukawa tayi tareda Ajiye bokitin ta fallasa mai daukeda gyadar ta dunbuxo kasa tareda watsa musu unexpected a jikinsu har wanda ke gefen idanun shi a rufe yana sauraren d’an uwanshi har ma da tsiwar datakeyi bai bude idanun shi ba duk da yaso yaga fuskar mai muryar tareda kuma son ganin wacece haka da wannan rashin kunyar? saurin zabura yayi jin ta watso musu kasa cikin mota duk ta bata musu jiki, balle murfin motar yayi ya fito yakalleta cikeda bakin ciki kafin ya kalli jikinshi dayayi budu budu da kasar data watso musu, saurin fitowa mai tukin yayi yanufeshi “am sorry prince please comedwon i will handle the stuation. Da sauri Rabi’a ma ta zagayo wurin su jikinta na rawa don Abin ita ma yazo mata a bazata batayi zaton dijen zatayi hakaba abin yazo musu unexpected dukansu har Isma’il da yadawo yakasa motsi don yana isowa tana d’an bazo kasa tana watsa musu, …………..

 

 

 

“We have just started my fans kubi labarin a hankali da Y’ar dar Allah zai nishadantar daku muje zuwa.

 

 

 

*Matar Soja*

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.