Ke nake gani Hausa Novel

Ke nake gani Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*KE NAKE GANI…!*

Book 1

 

By

_Hafsat A Garkuwa_✨🌹

 

*Sadaukarwa*

_Gaba ɗaya wannan littafin sadaukarwa ce a gareki Adda Ramlat Mai_Dambu ina matuƙar alfahari dake abar ƙauna na gode sosai da karamci Allah ya ƙara girma._😍

 

001

 

2:30am

*…* Dare mahutar bawa a wannan lokaci kowa na kwance a matsugunin da Allah ya hore masa, duk da akwai wasu da basu iya rintsawa sai sun gana da ubangiji, musamman mabuƙata domin su roƙeshi ya biya musu buƙatun su na alkhairi, domin a wannan lokaci ne yafi sauraren kuken bayinsa, hakan yasa da yawa daga cikin bayin sa suke shafe dare wajen bauta masa duk wani bawa musamman mabuƙaci ya kan tashi a wannan daren domin samun dacewa ga abun da yasa gaba, haka shima *ADEEL* yana ɗaya daga cikin waɗan nan bayi masu kai koken su wajen ubangiji domin ya biya masa buƙatar sa, durƙushe yake kan sallaya, idanun sa a rufe hawaye ne suke zuba tamkar famfo, haɗi da ɗaga hannayensa sama alamar roƙo,cikin muryar kuka yake faɗin “Ya Allahu, ya rahamanu, ya rahimu, ya muminu, ya jabbaru ya zuljalali wal’ikram! Allah ka dubeni ka amshi addu’ata ya Allah, a da ni kirista ne! banyi imani da kai ba, ban taɓa yin bauta a gareka ba,hakazalika ban taɓayi maka sujjada ba, ban kuma taɓa haɗa hannaye na a domin na roƙi wani abu daga gareka ba, a yau gashi duk waɗan nan ɗim ina aiwatar wa tsawon shekara uku kenan inayi, a ko da yaushe takan faɗa mini cewar kada na taɓa faɗa wa ubangiji na ƙuncin rayuwar da nake ciki, a kullum na kasance me godewa ni’imarka tare da nuna jin daɗi na a gareka, duk wannan abun ya wadatar, amma a tsawon shekaru ukun nan ita kaɗai tasan azabar da take sha,tana yawan faɗa mini cewa

“ADEEL! a duk lokacin da ka shiga cikin wani ƙunci ko wata musiba, ka tunkari ubangijin ka domin shi a kullum yana saureren kukan bayin sa, yana kuma biya musu buƙatun su, ko da kuwa ba a lokacin da suka bukata ba. “Gani na durkusa a gabanka ina roƙanka da ka ceci rayuwar *AZRAA* tana chan kwance cikin mawuyacin hali, tana numfashi amma kuma bata a raye, *Azraa* wacce ta kasance tana rayuwa a yau gashi mutuwa za tayi nasara a kanta, Likita ya faɗa mana cewar mutuwa Azraa zatayi bayan kuma Azraa tana raye ne a domin ta bauta maka, to amma gashi rayuwar nata tana a hannunka, zuciyata haɗe take data Azraa, ni kuma gani a durƙushe a gabanka a saboda Azraa ya ubangiji ina roƙonka da ka ceci rayuwar Azraa…ya ƙarasa faɗa tare da fashewa da kuka me ban tausayi tamkar ƙaramin yaro, ya jima a haka sai ƙarfe 4:00am bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

 

*AS-SAHL HOSPITAL GOMBE*

 

Wasu dattijai ne Mace da Namiji ke zaune a gaban Docter Asim Macen kuka take kamar ranta zai fita cikin kulawa Docter Asim yace

“Hajiya Khalida a gaskiya haƙuri za kuyi, domin ceton rayuwar Azraa abun ne mawuyaci, a hankali a hankali ƙwayoyin halittar ta sun samu gaggarumin matsala sama da shekara uku kenan bata san inda take ba kuma kunsan manyan likitocin da suka rinƙa dubata amma abun yaci tura.

Cikin kuka da zafin zuciya Hajiya Khalida tace

“Amma zuciyarta ai tana aiki, kuma har yanzu tana numfashi bata mutu ba har yanzu tana raye.

Ta faɗa da ƙarfi tare da nuna Docter Asim da yatsa ta fashe da wani sabon kuka, da sauri Alhaji Arshad ya riƙota tare da sanya ta a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta ya kalli Docter Asim yace

“Ka kalleta fa Dr. Asim ita ka ɗai tasan irin ciwon da take ji, ya faɗa tare da nuna Azraa wacce take kwance bata ko motsi na’urori ne kala-kala a jikinta tun daga hancinta har izuwa singalalin hannunta ya ƙara da cewa

“Gashi baza ta iya faɗa ba,bata motsin da za ta iya bayyanawa.

“Khalida ba iya Azraa ba mu kammu muna yaƙi a domin rayuwarta kukan da kike bashi da wani amfani tun da bazai tada mana da Azraa ba, abu ne mafi ciwo ace iyaye suna tsaye da ƙafafuwansu a gabar ƴar su ace baza su iya sama mata lafiya ba, a haka har ta mutu ba tare da mun iya aikata komai ba.

Ya faɗa wasu hawaye masu zafi suna fitowa daga idanunsa.

Cikin kuka Hajiya Khalida tace

“Abee Azraa baza ta mutu ta barmu ba!

“A’a Khalida kada ki yaudari kan ki Azraa baza ta rayuwa ba, ya faɗa tare da fashewa da wani irin kuka tamkar ƙaramin yaro.

“Wayyo Allah Ƴata kada ki tafi ki barmu baza mu iya rayuwa ba, Hajiya Khalida ta faɗa tare da sake rungume Mijinta gaba ɗaya an rasa me rarrashin wani.

Suna cikin haka Azraa taja wani irin dogon numfashi da ƙarfi ta sauƙe.

Da gudu suka nufeta ganin tana motsi, Dr. Asim ma tashi yayi cike da al’ajabi da mamaki domin babu yadda za ayi ace wanda ya kai wannan matakin zai rayu (Niko nace kum manta ikon Allah kenan?).

A hankali ta fara buɗe idanunta ta sauƙe su tar akan iyayenta mafi soyuwa a gareta, hannunta Hajiya Khalida ta kama tana sake mata murmushi me haɗe da kuka Dr. Asim ne yace

“Azraa!

A hankali ta juyo ta kallesa ta buɗe bakinta da ƙyar tace

“Na’am!

“Alhamdulillah!

Shine abun da suka faɗa gaba ɗayansu, da sauri Alhaji Arshad ya ciro wayarsa ya ƙira number Adeel.

 

*ADEEL POV*.

 

Sai 7:00am ya tashi bathroom ya shiga yayi wanka sannan ya fito ya shafa lotion ya sanya singilet da boxer ya sanya t-shirt ja da wando jeans ya sanya takalmi sau ciki yana cikin feshe jikinsa da turare yaji wayansa na ringing kamar bazai ɗauka ba dai ya ɗauka *Abee* ya gani a jikin screen ɗin gabansa ne ya faɗi da sauri ya ɗaga a zuciyarsa yana faɗin “Allah yasa alheri ne.

Yana ɗagawa yaji Abee na dariya cikin farin ciki yace

“Congratulation Azraaa…

Kafin ya ƙarasa Adeel yayi cilli da wayar ba tare da ya tsaya yaji karshen maganar ba a 360 ya fita daga ɗakin tsallaken step kawai yake har ya sauƙo falon da ba kowa a ciki sai ƙaran AC a guje ya fice ya nufi parking space ya shiga motarsa ya sanya key tun kafin ya iso bakin gate yake danna horn a 100 ya fice ya hau titi, ikon rabbi ne ya kawo shi cikin hospital ɗin ko gama parking bai yi ba ya fito da sassarfa ya ƙaraso bakin I.C.U nurse da ya ci karo da ita ta fito tana kuka ne ya sanya shi tsayawa nan da nan jikinsa yayi sanyi musamman ganin da yayi ta girgiza masa kai tana kuka, a sanyaye ya fara takawa hannunsa na rawa ya buɗe ƙofar turus! yayi ganinta zaune daɓas a kan gado kamar ba itace a kwance rai a hannun Allah ba ajiye zuciya ya sauƙe tare da furzar da iska me zafi a bakinsa ya faɗi ƙasa tare da yiwa Allah sujjada, a hankali ya ƙaraso wajen farin ciki fal zuciyarsa ji yake ina ma da aurensa a kanta da babu abun da zai hana bai rungumeta tsam a gaban iyayenta ba, wasu hawaye ne masu zafi suka sauƙo kan kumatunsa, a hankali ya juya zai bar ɗakin domin yaba Iyayenta su fara ganawa da ita har zai fita Abee ya gansa da sauri yace

“Adeel!

Chak ya tsaya tare da juyowa yana goge ƙwallan idanunsa shigowa yayi ya tsaya kusa da Dr. Asim.

Dr. Asim ne yace

“Adeel a yau dai rayuwar Azraa ta dawo bayan shekaru uku, gashi kuma ta warke gabaki ɗayanta, wannan shine abun al’ajabi na farko da na gani a tarihin aikina, wannan wata mu’ijiza ce daga ubangiji na tabbata

Kallonsa gaba ɗaya suke cike da farin ciki Hajiya Khalida ce tace

“Dr. Asim wannan aikin Adeel ne na tabbata a kullum addu’a yake ba dare ba rana wajen yiwa Azraa addu’ar samun lafiya gashi a yau Allah ya karɓi addu’arsa cikin minti ƙalilan Azraa ta warke kamar ma bata taɓa ciwo ba, a tsawon shekaru ukun nan a duk lokacin da muka fitar da rai akan Azraa Adeel shi yake karfafa mana gwiwan cewar za ta warke.

Azraa kallon Adeel take ba ƙaƙƙautawa a hankali ta fara sauƙe ƙafarta ta kama hannun Sahil dake gefenta da sauri ya riƙe hannunta ganin zata faɗi takawa ta farayi tare da nufi inda Adeel ke tsaye a gabansa ta tana kallonsa take ido cikin ido sun jima a haka kamin ta sulale ƙasa sumammiya.

Kafin ta kai ƙasa cikin zafin nama Adeel ya riƙeta ta faɗa jikinsa cikin haɗin baki suke faɗin

“Azraa lafiya?

Ɗaga ta yayi ya kwantar a gado cike da tashin hankali ruɗu, kiɗama, tsoro, fargaba,gaba ɗaya suka taru suka yiwa zuciyarsu ƙawanya tsoron su ɗaya kada ta koma dogon sumar da ta tashi cike da tashin hankali ya kalli Dr. Asim da ke tsaya yace

“Dr. Kaga halin da take ciki zo ka dubata.

“Kada ku tada hankalin ku ba wata matsala hakan ta faru ne saka makon allurorin da aka mata, ajiyar zuciya ya sauƙe.

Hajiya Khalida ne taja mata blanket ta rufeta sanan Dr. Asim yace su ɗan bata waje ta huta, suna fita ya ɗauki waya ya ƙira Mr. M.D wato mahaifinsa.

Bugu biyu ya ɗauka cike da farin ciki yace

“Daddy!

“Na’am my son ya na jika cikin farin ciki haka?

Dariya Adeel yayi me sauti yace

“Daddy kasan menene…

Dariya Daddy yayi ya tare shi da faɗin

“Azraa ta farka ko?

Cike da mamaki Adeel yace

“Daddy ya akayi ka sani?

Dariya Daddy yayi yace

“Saboda ni ɗin na kasance mahaifinka ne a tsawon shekaru uku baka da walwala ba ka da wata nutsu ba a ganin fara’arka duk saboda Azraa amma yanzu ka ƙirani kana farin ciki nasan bazai wuce samun lafiyar Azraa ba, to yanzu faɗamin na shirya maka shagali dan wannan abun farin ciki ne babba.

Dariya Adeel yayi yace

“Daddy mu jira a sallameta tukunna daga nanne zan haɗa walimar da ba a taɓa yin irin sa ba.

Cike da farin ciki Daddy yace

“Tabbas wannan dakun soyayyar da kayi na tsawon shekara biyu ina ganin Allah ya dube ka ne kuma ya amshi addu’arka.

Cike da jin daɗi Adeel yace

“Na gode Daddy a bisa bani goyon baya da kake tare da ƙarfafa min gwiwa.

“Adeel nifa ba abokin kasuwancin ka ba ne da zaka rinƙa min godiya, kai fa ɗana ne ina son duk wani abun da kake so ina son farin cikin ka a ko da yaushe, ka kasance tare da Azraa ka bata duk wani kulawar da ya dace sannan kai ma ka tabbatar ka kula da kanka kaji ko?

“Tom Daddy in sha Allah.

Daga haka sukayi sallama cike da ƙaunar mahaifinsa.

*DADDY POV.*

 

Yana kashe wayar yaji wani irin ƙara a bayansa yana juyawa yaga Serah matarsa wato mahaifiyar Adeel ce ta sake cup a ƙasa da gangan ya fashe fuskartan nan babu fara’a.

Dariya yayi yace

“Lafiyanki dai ko Serah?

A fusace ta iso inda yake tace

“Ai ka sani Azraa ta dawo rayuwar ɗan mu ne saboda mu sake rasa shi ina jin daɗi ta fece a…

Da sauri Daddy ya ɗaga mata hannu tare da cewar

“Dakata kwantar da hankalin ki Serah a ko wani lokaci kina da yawan ɓaɓatu dan Allah ki jefar da wannan ɗabi’ar,domin ki zamo ɗaya daga cikin wacce za ki taya ɗanki farin ciki, bayan haka ma mu ahalin FARIN CIKI ne ki murmusa mana.

Ya faɗa tare da miƙewa ya bar mata wajen, wani irin ɗaci da zafi take ji a zuciyarta cikin ɗaga murya yadda zai jiyo ta tace

“A saboda farin cikin ɗanka har kana faɗar za ku haɗa shagali ko? ni kuma sai na sanja ƙaddarata.

Ta faɗa cike da ɓacin rai, tsaki yayi tare da bar mata wajen.

 

*ADEEL POV.*

 

Tsaye yake jikin ward ɗin da Azraa ke ciki ta glass ɗin ƙofar yake kallonta

“Bugawar zuciyarki ya samar da sabuwar rayuwa a soyayyan mu Azraa, a lokacin da na sameki ne na tabbatar da cewa idan babu ke… da yanzu ko ni ko soyayyar mu za ta kasance babu ita bata wanxu ba kwata-kwata a doron ƙasa, lokacin da na ɓata ba tare da ke ba a cikin wannan yanayin na kasance kullum cikin tunaninki…Cikin zuciyarshi yake wannan maganar yana cikin haka ne yaji sallama a bayansa juyowa yayi yaga wani ne tsaye wanda bai sanshi ba ya miƙo masa hannu suka gaisa sannan ya miƙa masa kwalin cake yana faɗin

“Adeel ina matuƙar taya ka murna da samun lafiyar Azraa.

Ya karɓa tare da faɗin

“Na gode”

Yana buɗewa yaga wata ƴar farar takarda anyi rubutu kamar haka

_Dukkan wani wanda ya nitse a cikin soyayya to ya tabbatar soyayyar ce ajalinsa_

Cike da ɓacin rai ya ɗago yana faɗin

“Wannan wani irin shashanci ne” ya hango wanda ya kawo masan yana gudu a guje ya bisa yana faɗin

“Kai malam dakata!

Amma ina tuni har mutumin ya fito harabar asibitin ya shige motarsa Adeel na ƙarasowa yaja motar a guje ya fice a asibitin cike da ɓacin rai Adeel ya wurgar da kwalin Cake ɗin yana fitar da iska me zafi daga bakinsa ya so ace ya kamashi da sai ya haɗa masa jini da majina.

 

*AZRAA POV.*

 

A hankali ƙofar ɗakin da take ta buɗe haka ma windon wani irin iska ne yake busowa miƙewa tayi ta tsaya tana wani irin kallo tahowa ta farayi ta fara taka tsaunin matakala tana tafiya kamar wanda ake janta kamar ance Adeel da ke chan ƙasa ya ɗago ya hangeta tana daf da faɗowa cikin wani irin tsoro da tashin hankali yace

“Azraa dakata a nan! ya tafi da gudu ta sanya ƙafa zata faɗa ƙasa ya finciko ta ta faɗo jikinsa ya rungumeta tsam yana maida numfashi yana faɗin

“Azraa meye haka? na samu kin dawo daga rashin lafiyarki shine kike so na rasa ki gaba ɗaya Azraa?

Ƙuri ta masa ba tare da tace komai ba, kamar an tsikareta ta tureshi da ƙarfi tare da faɗin meye haka kai ɗin waye? me yasa zaka taɓani ka sanni ne?…

 

“`My Fan’s ya kukaji wannan tafiyar? shin ya fara kawo light ko kuwa? Sayan wannan littafi shi zai nuna min ƙaunar ku a gareni Hajiyata kar kiji shayin sayan wannan littafi.“`

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
KE NAKE GANI is 100 via… Union bank 0134205910 Hafsat Ayuba ku nuna shaidar biyan ku ta lambar whatsApp ɗina… 08132761212, in kati ne kuma zaki turo MTN na 100 akwai Vip grp posting biyu a rana 300 za ku iya fara biya tun yanzu kafin na gama free page ku karanta cikin farin ciki ba tare da jin wani laifi ba.

 

Comment&share

*ONE LOVE*

08132761212

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.