Kisar Rudu Hausa Novel Complete
TAG: KISAR RUDU
Wa yayi kisar?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al’umma zasu anfana da shi.
SADAUKARWA
Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu’a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta.
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
Littafan Hausa Novels
Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 1
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Wed may 2022
12:00am
Agogo ya buga daidai lokacin da wata yarinya ƴar kimanin shekara Sha huɗu ta fito daga wani ɗaki ta nufi ɗakin da ke kallon na ta, kallo ɗaya zaka ma yarinyar ka fahimci irin sangartattun yaran nan ne da ba’a kwaɓa musu, kofar ɗakin ta tura tana faɗin, “Momy ina jin yun…” maganar ta ne ta maƙale sakamakon ganin Mahaifiyar ta kwance cikin jini, ga kuma Kakar ta riƙe da wuƙa a hannun ta ya na ɗigar jini, nan da nan jikin Hajiya kaka ya fara rawa ta yar da wuƙar tana faɗin, “wallahi bani na kashe ta ba Aneesa ki yarda da ni.!
Hajiaya Kaka ta ƙarishe maganar cikin tsananin tashin hankali, ta nufa in da Aneesa ta ke tsaye tamkar an dasa ta, ganin Kakar ta nufo ta ne ya sa tayi firgigit ta nufi gawar Mahaifiyar na ta tana sakin wani irin marayan kuka mare sauti, shikenan Kaka kin kashe min mahaifiya kin ji daɗi dama kin dade kina ikrarin sai kin kashe Momy,! to kin kashe ta kaka kin huta, na ce kin huta ta bar miki duniyar, ki tattara dukiyar kiyi yadda kike so, kuma wallahi ki sani yau ba sai gobe ba zan kai ƙarar ki saboda duniya ta san me kika aikata.”
Aneeesa na gama faɗin haka ta kama hanya ta fice daga ɗakin, in da take jin zuciyar ta gaba ɗaya ta bushe, kawai ɗaukar fansa ce a ran ta.
Durƙushewa kaka tayi a gurin tana faɗin, “Kaico na ni Hajiya Hindu mai na aikata kenan, yanzu duk duniya ba wanda zai yarda cewa bani na kashe Saudat ba.!
Kuka sosai Hajiya Hindu takeyi tamkar ranta zai fita ga wani irin tsoro da ya dirar mata.
Tafiya take tamkar mahaukaciya kafafun ta ba ko takalmi kanta ba ko ɗankwali burin ta kawai ta isa police station ɗin da ke bayan layin su a zo a kama kaka kafin ita ma ta kashe ta tamkar yadda ta kashe mata mahaifiya, tana isowa kofar get ɗin police station ɗin ta fara bugawa tamkar mahaukaciya, iya ƙarfin ta tana bugawa tana kiran police, da gudu wani ɗan sanda ya futo riƙe da bindiga yana faɗin, “waye yake bugamana get kamar zai karya.?
“Nice nan Aneesa ƴar gidan Commisioner, ƙara na kawo.!
Ta ƙarisa maganar tana ƙara fashewa da kuka, binta da kallo ɗan sandar yayi tamkar yana nazarin wani abu game da ita, sai can ya ce ma ta, “mu shiga ciki ƴan mata, bin shi tayi har zuwa office ɗin ogan su, suna shiga ya sara ma oga ya ce mai, “sir wannan yarinyar ce ta zo mana a ruɗe kuma tana wani magana da ban fahimce ta ba shiyasa na kawota gurin ka domin alamu ya nuna cewa ba a hayyacin ta take ba, ko gama rufe baki bai yi ba Aneesa ta tari numfashin shi tana faɗin, “wallahi ranka ya daɗe ina cikin hayyacina, ƙaran kaka ta na kawo ta kashemun mahaifiya yanzu haka tana can kwance cikin jini, kuma da ido na na gan ta yallaɓai.!
Ta ƙarasa maganar tana mai fashewa da kuka mai tsuma xuciyar mai sauraro.
“What! haba ƴan mata taya za’ayi ki ce kakar ce ta kashe miki mahaifiya, yanzu ina ita kakar ta ki da gawar Mahaifiyar ta ki.?
“Wallahi yallaɓai da gaske nakeyi da idona na ganta, yanzu haka tana gida na kulle gidan don kar ta gudu.
‘Officers ku je da ita ku tabbatar kunyi bincike sosai sannan a kamo ita wacce ake tsargi ɗin.”
“Haba yallaɓai wani irin zargi in ce ma a idona ta kashe mun mahaifiya ka ce tsargi.
“Karki damu ƴan mata binciken mu shi zai tabbatar da haka ai…
SHARE FISABILILLAHI
Zeey yar mutan zazzau ce
Leave a Comment