Sirrin Rike Miji

Kishiya Bayan Mutuwa

KISHIYA BAYAN MUTUWA

 

 

 

 

 

 

 

Wani mutum ne suna zaune suna tadi da matarsa sai kawai ta tambayeshi, yaushe ne zakayi aure idan na mutu? Sai yayi murmushi yace, bazan yi aure ba sai kabarinki ya bushe. Tace kayi mani alkawarin hakan? Sai yace eh.

Akwana a tashi ajali ya cimma matarsa, tayi jinya kadan sai tace ga garinku. Da aka zo jana’izarta sai ya tuna da alkawarin da yayi mata. Don haka bayan sati daya duk sai yaje ya ziyarci kabarinta yayi mata addu’a. Amma abin ban mamaki shine kullum in yazo sai ya tarar da kabarinta danye kamar jiya ne aka binne ta.

Sai da akayi shekarru yana haka, rannan sai yayi kicibis da kanenta yazo makabartar da ruwa a jarka.

Yace, me zakayi ne halan? Yace, ina zartar da wasiyyar yar uwata ne. Yace, me tayimaka wasilci da shi ne? Yace, ai ta rokeni ne bayan Ko wane kwana biyu in kwarara ruwa a kabarinta.

 

*DARASI*

*kishi* kumallon mata ne, ko suna kabari suna jin zafinsa. Mu tausaya masu.

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!