Kishiyar uwa (true life story)

KISHIYAR UWA

 

 

 

 

; , .

. ..

. , .

. , , .

 

YA ALLAH, YA RAHMAN, YA KAREEM, YA ZULJALALI WAL IKRAM, ALLAH YA SHIGE MANA GABA.

بِسم الله الرحمن الرحيم

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai , mai jin kai .

Salati ya tabbata ga sugabanmu annabi Muhammad da iyalansa da sahabbansa masu girma.

Wannan littafin badan wata ko wani na kirkireshi ba nayi ne domin mutane masu irin halin in sunji su gyara , Allah ya bamu ikon gyarawa amin.

Sadaukarwa ga iyayena , da kuma duk makaranta littafina.

 

Shafi na 1

 

Tafe take akan hanya kana ganinta kasan hankalinta baya tattare da ita , saurin da takeyi ya wuce misali , kai in ka hangota daga nesa tsammani ma zakayi mahaukaciya ce , yarinyace wadda bazata wuce shekaru goma zuwa sha daya ba, a kofar wani gida naga ta tsaya nima kuwa na nemi guri na tsaya dan ganin abinda zai faru , kokari takeyi ta shiga gidan tana kuma ja da baya , ta dauki tsawon mintuna goma kafin daga bisani ta tura kofar gidan da sallama ta shiga , cikin sanda ta shiga a hankali da sallama a bakinta, kitchen naga ta nufa da ajiye abinda ta siya tana kokari fita daga kitchen din juyawar da zatayi sukayi karo da juna, goshinta ta dafe sbd tsabar buguwarda tayi duk wannan abin da akeyi sai yanzu nqga fuskar wannan yarinyar mashaAllahu kawai na ambata saboda tsananin kyau da yarinyar ke da shi , matar da sukaci karo naga ta finciki yarinyar zuwa waje.

 

 

au ke yanzu dan ubanki na aikeki tun dazu amma sai yanzu kika ga damar kawomin aiken , magana take shirin yi amma ta dakatar da ita ta hanyar wanka mata mari sai da bakina ya fashe, kara ta saka saboda azabar da tasha , inna wallahi ba dadewa nayi ba gurin ghalin ne akwai layi in ina bashi kudin baya amsa sai da wani mutum yazo sannan ya mika masa ya bani sakon, rufamin bqki shegiya waya tambayeki , nace miki ki fadamin dalili , labilen dakin aka daga yarinyace da bazata gaza shekarun wannan yarinyar ba itama ta fito tana mika alamun daga bacci ta tashi , inna ina abincina tana magana tana yatsina fuska ni yunwa ma ta fito dani , kallonta tayi tace zo nan yar lelen inna da baba , bara na baki ki sayo alala gidan talatuwa ki ci saboda wannan shegiyar ta sa ke yin halin nata, ta kalleta mai mugun halin tsiya kawai.

 

 

Daga kofar gidan naji anayin sallama alamar zaa shigo , wani dattijo ne naga ya shiga gidan tana tura keke da fartanya akan kafadarshi da alama daga gona ya dawo, haba asabe naji ya ambata yaya tun daga waje nakejin sautin muryarki menene ya faru ya tambaya cike da yunwar ta amsa masa tambayarsa , kaganta nan tun dazu na aiketa amma sai yanzu ta dawo , kallonsa ya juya gurin yarinyar nan ta farko yace Fatima garin yaya kina dade batun kinsan ina gab da dawowa daga gona kuma da yunwa zan dawo , wallah baba akwai layi a gurin sai dana dade sannan ya bani na taho gida, toh a daina tafiya ana dadewa kinji ko toh tace tare da tashi daga wajen saboda tana da aikin da take da shi masu yawa, Alhamdulillah duk da kankantar shekarunta amma aiki ko babba sai haka , ita kuwa wachchan bqta da aiki sai bacci ,girki ta daura sannan ta kama wanke kwanika , cikin kankanin lokaci ta gaba komai tsaf ba tareda wani jan dogon lokaci ba, sallama tayi kofar dakin amsawa babanta yy kamin ya bata izinin shiga ta durkusa kasa sannan tace inna ba gama aiki toh ta amsa mata ba tareda ta kalleta ba kije ki dauko hijjabi zan aikeki toh tace tana kokarin tashi mahaifin nasu ya tsayarda ita ta hanyar fadar kinci abinci aa ta bashi amsa je ki ci sai ki tafi aiken, haba malam tayaya zance zan aiketa amma ka goya mata bayan kar taje don bani na haifeta ba ta fada ta hanyar fashewa da kuka, haba asabe yarinyar nan bataci abinci ba , bazai yiwu yarinyar ta zauna ba abinci ba batun kuma da akwai, ke tashi kinji kije ki ci abinci sai ki tafi toh tace hade da tashi ta fita .

 

 

 

 

Toh bayan ta gama ne aka bata aiken da zatayi , ta tafi , a hanya ta gamu da yar ajinmu rahane , lah Fatima dama kina nan mallam Ahmad yana ta tambayarki kwana biyu bakyason zuwa makaranta , wlh ba haka bane ba yanzu ma inna ta aikeni gidan baraka aminiyarta inayin sauri sai min hadu wajen tallah da dare , toh sukayi sallama ta tafi. Tana zuwa kofar gidan ado ta ci karo da shi a rayuwarta ta tsanin wannan bawan Allah kwata kwata baya burgeta duk kuwa da tururuwar da yam matan garin ke masa, duk da ita yarinya ce amma takan banbance abu mai kyau da zai amfaneta da marar kyau , ah Fatima ya fada yana washe baki naam ta amsa tana kokarin shiga gidan , aa dakata mana , aikena inna tayi kuma ina sauri ne , au wai asabe ya tambayeta gaba tayi bata bashi amsa ba , da sallama a bakinta ta shiga matar ba zaune akan tabarma inna ina wuni lafiya ta amsa , sannan ta bata sakon da aka ce ta kawo batun ta gama dubawa ne sannan ta mai da mata ragowar ki kai mata kice na zaba , zamuyi magana, toh tace sannan ta tafi gida . Tana shiga ta kai mata sakon, toh ki huta ga kayan tallah chan na hada miki, toh tace sannan ta fita.

 

 

 

 

Da magariba bayan an fita a masallaci ta fita da gyadarta zuwa dandali inda samari da yam mata ke haduwa , kawarta ta dazu ta karaso ah Fatima har kin karaso , eh ta bata amsa , wlh kina kokari gaskiya, yanzu abinda zaayi muyi sauri mu sayar mu koma gida saboda kinga garin na damuna ne ,eh haka ne , mashaAllahu sunyi ciniki dan haka kafin a tashi suka tafi gida , kawartace ta fara shiga gida , sannan ta wuce daf da zata shiga yayi saurin shan gabanta tsaya mana tun daga nesa nake kiranki baki juyo ba danAllah Ado ina so na shiga gida inna na jirana , ai da saninta nazo wajenki dan nazo tace bakya nan kina dandali, eh ta amsa masa, amma yanzu zan shiga gida sai da safe saurin janyo mata hannu yayi kara ta saki sannan ta gartsa masa cizo ta shiga gida , kudin tallan ta bata sannan ta ci abinci ta shiga dakin mahaifiyarta wanda ya ratattake saboda asabe ta hana a gyara shi, kwanciya tayi a kan tabarmar kabar dake dakin , tunani ta fada yi shin ina zata ga dangin mahaifiyarta batasan mahaifiyarta ba gashi mahaifinta har yau bai fada maka tayaya akayi mahaifiyarta ta gujeta ba , hawayene ya zubo mata sakamakon tuna irin rayuwar da take ciki shin yaushe zata fita daga rayuwar da take ciki ita dai tun iya tashinta a haka ta taso ta ganta cikin wahala , Allah ya mata magani kawai a haka bacci mai nauyi na gajiya ya kwasheta ta niyyar tashi da wuri saboda tana da niyyar zuwa makaranta kota halin kaka ne , shiyaga take da niyyar yin aikinta da wuri ta gama a haka har asubah tayi ta tashi saboda ta saba tashi ta yi aiki sosai ta kammala kamin ta gama komai tayi sallama da mahaifinta tayi hanyar makaranta.

 

 

*Please*

 

*Share*

*Comments*

 

 

 

 

To be continue

 

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.