KO BA SO…
Page 01
10th November, 2024
Whitestone Suite, Katsina.
Gate din a bude yake dukkan shi, mai gadin kuma yana gefe tsaye don baiwa manyan motacin da ke kutso kai damar shiga, a duk bayan yan mintuna. Kallo daya za a shaida taro ake, taro na manya manya ba yuyuyu ba. Harabar wajan haggu da dama zagaye take da decorations tare da manya manyan poster mai dauke da hoton kyakkyawan mutum da a hasashen shekarunsa za su yi 50-57 a kasa an rubuta sunansa Hon. Jamil Usama. Da wasu poster din an rubuta Free Medical Outreach Opening
Sai kuma matasa sanye da T shirt, a gaba hoton Hon. Jamil ne, a baya kuma an rubuter Free Medical Outreach, a hulunan kansu ma haka. kowannen su dauke da poster din sun yi kamar an jera su a gaban kofar da zata shigar da mutum cikin hall din alamun sannu da zuwa su ke yi.
Daga ciki kuma tangamemen hall ne da ya gaji da haduwa, komai na ciki sheki yake yana daukar ido. An kawata kujerun zaman tare da tables dinsu sannan a gefe guda in da aka shirya ganimar nau’in abinci ne da abin sha a killace. A kwai kuma waje na musamman da aka ware mai nuna alamun wurin zaman masu ruwa da tsakin taron ne.
A saman steps din ma hotunan Hon. Jamil ne ke haskawa suna wucewa a slideshow tare da hotunan kauyuka da mutanen cikinsu, wasu kwance a asibiti wasu a jeme alamun rashin lafiya wasu kuma bakin mono da alamun suna son dibar ruwa kuma babu, sai hotunan magunguna da allurai da su ma suke giftawa.
Yawancin mutanen duk a zaune suke in da aka tanadar masu don zaman, sai tsirara da ke dan tasowa in an ga idon sani a gaisa, ko kuma an hango wanda ake sa ran za a samu wata alfarma a yanzu ko a gaba sai a taso a gaishe shi, har zuwa lokacin da Hon. Jamil da Family dinsa suka shigo hall din. Maroka na biye da su suna ta zabga kirari tare da kambama shi. Daga haka securities suka yi masu katanga. Mutanen wajan duk a ka mike alamar girmamawa shi ma ya russuna masu kafin ya je ya zauna in da aka tanadar masa. Su hudu ne suka shigo, shi Matar da ke gefensa wanda ko ba a tambaya ba an san matarsa ce sai saurayi daya da budurwa daya dukkan su sunci ado sai walkiya suke. Wajansu na musamman suka zauna.
Mc ya zo ya yi kirarinsa, ya gaida baki na zaune wadanda ya gane da wadan da ke ida shigowa hall din. Daga nan sai ya mikawa wanda zai bude taro da addu’a mic yayi. Ya kuma mikawa wanda aka wakilta don yiwa manyan baki barka da zuwa , ya zo ya yi. Sai kuma wanda aka wakilta don gabatar da taro shi ma ya zo yayi, bayani akan manufar taron. Ya yi bayanin manufar Hon. Jamil akan son ci gaban arewa akan lafiya, kare kai daga cututtuka tare da magance cututtukan da suka zama ruwan dare ga al’umma musamman mutanen kauye da yake ganin sun fi bukatar hakan. Yana yi tare da bayanan da aka tsara a slideshow din da kowa ke kallo su na gyada kai cike da gamsuwa. Daga nan wasu kungiyar health organization suka fito suka sake bada haske akan *Infection disease* kamar pneumonia, Tuberculosis (TB), Cholera sai kuma *Martenal and child health issues* Birth defect, malnutrition da sauran wasu cututtukan.
Bayan haka ne aka tsagaita MC ya kuma surutan shi sannan ya sanar za a bada damar cin abinci a jika makoshi sannan idaan an dawo aji sauran karin bayani daga uban taron, tarihinsa da na itayalansa, abin da ya ke son cimmawa da sauransu. Sai kuma bayanan su ma iyalan daga nan sai tambayoyin da yan jarida zasu ci gaba da watsa masu ita lokacin da aka yanka. MC ya sanar ne don su sake shiryawa da kyau.
Dukkan abin da ake yi ana daukar shi live ne kai tsaye ake watsa shi gidajen television mabambanta da kuma channels na social media.
Nan fa aka ci gaba da hada-hada kamar dai kowanne taro idan lokacin cin abinci yayi, sai dai wannan cikin nutsuwa duba da duk manyan mutane ne masu ruwa da tsaki a gwamnati. A nutse suke tashi suna isa in da aka jere ganimar kowa na daukar plate sai ya bi daki-daki ya zuba duk abin da ya yi mashi ya zabi kalar lemon da ya ke so ya tafi. Akwai nau’in da masu diabetes zasu iya ci, akwai na masu ulcer da sauransu don haka abin ya birge kowa ganin kowa zai ci abu ba daidai da lafiyar shi.
A table din Hon. Jameel. Fuskarsa ba annuri ya kalli matar da ke gefensa da fuskarta ke cike da annuri, ya ce
“Yaron nan ya san yau ake taron nan kuwa ko kuma dai ya na sane zabar tozarta ni yayi a idon jama’a?”
Cikin fuskar damuwa ta ce “Zai zo Dadyn su, zai zo In shaa Allah. Ka san Fahad da rashin lokaci”
Ya tsuke fuska, “Har akwai lokacin da ban ci darajar da za a bani shi ba Hajara? Minti nawa ne yazo ya tafi? Ko ce masa akai ina son zaman shi a inuwa ta ne?”
“Dady mana…Yayaa Fahad zai zo, ya fada min zai zo, bamu san uzurin da ya tsaida shi ba”
Kyakkyawar budurwar ta fada fuskarta da damuwa. Saurayin da ke gefenta kuwa kamar bai san me suke fada ba abincisa kawai ya ke ci. Hon. Yayi shiru kawai amman ranshi ba karamin tafasa ya ke ba, yana tunanin kalar hukuncin da zai mashi idan har bai halarta ba har aka gabatar da introduction na Family, don wannan ai abin kunya ne, in da ma ba shi bane babba can matsalar sa ce amman shi ne babba a yaransa, dole ana bukatar sa a wajan ya nuna support dinsa. In ban da bakin ciki babu abin da Fahad ke haddasa mas a rayuwarsa. Ya kalla agogo da zullumin kar a dasa program din. Kamar kuwa MC ya sani ya yi gyaran murya a mic din sa
“To Alhamdulillahi an ci an sha an godewa Allah….” Kafin ya gama jawabin sa tuni ma’aikatan wajen sun fara tattare plates suna kwashe kwalaben ruwa da na lemo, zuwa sadda ya gama ya bukaci family’n Hon. Komai yayi fes.
Dariya kawai ya ke a lokacin da yake hawa steps din stage, ana masa tafi amman tsinewa Fahad ne kawai bai yi ba a cikin zuciyarsa, bakin ciki da kaicon kasancewar shi da na farko a wajansa ya ke yi.
Bayan ya karbi Mic yayi sallama, yayi godiya ga mahalarta taron, da magoya bayan taron, ya kuma mika cikakkar godia ga mai girma gwamna da shugaban kasa da suka yarje masa suka bashi wannan dawainiyar don ci gaban al’umma. A jawabinsa tare da taimakon slideshow ya bayyana duk manufofinsa, cigaban da hakan zai kawo a yanzu da kuma gaba,
Ya kuma jaddada da samuwar aikin matasa a dalilin project din don taimakawa a gudanar da aikin yadda ya kamata, ta haka za a rage zaman banza da baragurbin matasa, sace-sace da shaye-shaye. Sai dai kamar yadda aka shirya slideshow din ya ke wucewa tare da hotunan bayanan duk da yayi, haka hoton ya bayyana baro-baro a bainar jama’a a daidai sadda ya ambaci shaye-shayen. Wajan yayi wani kalar shiru na wucin gadi, Hon. Ya cire glasses din idonsa ya murza, ya sake murzawa ya tabbatar da Fahad ne ke layi a duhun dare ga ‘yan sanda nan gaban motar sa da wata leda da ke nuna alamun daga motar aka fiddota suna kokarin wucewa da shi. Gashin kansa ya sha dying ta yadda ya zama an ratsa brown color a cikin bakin gashin har kai tsaye ba za ace baki bane ko kuma brown din. Rigar jikinsa armless ce ta yadda har za a iya hango tattoo din da ke damtsen hannunsa duk da bashi da yawa. Video din yayi buji-buji, da ya dawo clear kuma wata mace aka hango ta tare shi yana shirin faduwa sannan ta daura hannunsa a kafatarta daga haka sai video din ya dauke.
Mic din hannunsa ta fadi kasa. Fahad da kadan ya rage masa karasowa inda suke cikin sauri saboda makarar da yayi, ya ja tunga ya tsaya idanunsa kan screen din sun kada sun yi jawur lokaci guda. Duk wani annurin fuskarsa da ya shigo da shi sun bace bat! A lokacin kuma ya fara jin idanun mutane na yawo a kansa, camera yan jarida na dallo shi, duk da idanuwa da camera wasu abubuwa ne da yayi sabo dasu, ko ma ya ce abokanan rayuwarsa ne, amman wadannan daban suke. Wadan nan na tuhuma ne, tuhuma kuma ba kalar wadda Daddy ya saba yi masa bace, haka camera ba wacce aka saba haska masa bace.
5 weeks ago
*******
“Kai ne ka koya mini son ka, kai ka ce in yarda da kai, ka ce in dogara da kai..Daga karshe sai ka tafi ka barni ba tare da ka sake waiwayata ba.”
Ta dauki Apple din gabanta ta gutsira tana tauna shi a hankali tare da lumshe manyan idanuwanta. Kamar wacce aka tsikara ta kuma ware su a kan makeken hotonsa
“Kar ka neme ni, ba sai ka neme ni ba, ni ce zan neme ka Fahad. A lokacin da kai ba kai tsammani ba, kuma zaka rayu dani har karshen rayuwarka ko ba so! Ba ka ganin lokaci yayi da ya kamata na waiwayi rayuwarka? Haka ne?”
Ta kece da dariya,irin dariyar nan ta mugunta ta cigaba da dariya har tana durkushewa ƙasa, sai kuma ta fashe da kuka kamar wacce aka aikowa saƙon mutuwa. Hawaye share-share tana shessheka. Sai da tayi kuka mai isarta, zuciyarta tayi baƙi kirin da ɓacin rai. Ƙarar wayarta ya saka ta goge hawayenta ta miƙe ta dauko wayar.
*
Mijinah Ta gani a fuskar wayar, ba tare da É“ata lokaci ba ta É—aga.
“My”
Ta faɗa cikin ƙasa da murya.
“Ki na ina ne haka na kira ki baki É—auka ba É—azun, are you okay?”
“Yeah, kar ka damu na É—an yi bacci ne yanzun na tashi. Yaushe zaka dawo? Na yi kewar ka sosai”
“Da gaske? Ko in taho kawai?”
“Nah, ka gama aikin ka My zan jira ka..”
“To shikenan na gode, ‘yar aljanna. Zamu shiga meeting yanzu zan kira ki idan na fito okay?”
“Okay. Sai na jika muah”
Ya katse kiran daga can. Guntun tsaki tayi bata ƙara bi ta hotunan gaban ta ba kuma ta dauki plate din Apple dinta ta kulle dakin da makulli.
Ta cikin wani corridor ta biyo ya sada ta da tsakar makeken parlour’n ta, sai da ta zo tsakiyar dakin ta tsaya ta kalli sama da Æ™asa ta kalli manyan kujerun da ke zagaye da É—akin ta É—aga kanta ga stairs din da za su sada ta da manyan bedrooms É—inta wanda ta tabbatar ko É—iyar sarki ba za ta gwada mata komai ba ta nan É“angaren, Ta saki dariya, a gefe É—aya kuma tana hango rayuwarta ta baya.
“Oo!”
Ta É—an daki saman kanta kaÉ—an.
“Ki daina tuna wannan kin ji?”
Tayi murmushi sannan ta samu É—aya daga cikin kujerun ta zauna ta na É—aura kafarta É—aya bisa É—aya.
Shafin Instagram ta bude bayan ta dauki wayarta. Kai tsaye account dinsa ta dosa yanzun ne lokacin da ya faɗa zai yi live video.
Hi everyone, I’m here again.
**
Hi
You’re handsome
Can’t wait to see you
I’m a big fan
Ta saki murmushin takaici yadda ake ta tura masa saƙonni ta ko ina yawancin duk mata ne ma.
“I’ll ruine your life Fahad Jamil”
Ta faÉ—a tana sake maida hankalinta kan wayar. Ba ta bada duk wata dama ta abin da yake ciki ta wuce ta, hakan ne kawai take ganin zai zamo matakin nasarar ta. Kuma kwankwasa kofar da akai shi yai sanadin rasa live din da ta shirya kalla. Ta ja wani mugun tsaki da ya zamo mata jiki.
“Mamma…! Na dawo”
Muryar yar yarinyar da a shekaru basu wuce huÉ—u da wani abu ba ta faÉ—a”
“Na gani ai, waye ya ce yanzu za a maido ki?”
“Wai gobe a kwai school in ji Naani..”
Ta É—auke kallon ta daga kan Noor ta maida ga Amira da ke shigowa hannunta dauke da katuwar leda mai dauke da tambarin SAAN Store na Company’n mijinta.
“Aunty Bie sauri na ke ga Noor nan, sai na dawo Friday”
Ta aje ledar hannunta ta juya da sauri ta fita. Tsakin dai ya raka ta ita ma duk da bata san anyi ba. Ledar ta jawo ta zazzage duk tarkacen chocolates ne da teddy’s kamar ko yaushe idan Noor ta je gidan kakanninta.
“Sophie!”
Da sauri ta iso tana sunkuya kanta ƙasa, kamar yadda ta sani ba ta isa haɗa ido da mai gidan tasu ba.
“Ki kwashe kayan nan, ki kai mata É—aki. Ki yi mata wanka kuyi wasa”
“Ni a wajan ki zan zauna..”
Noor ta faɗi tana dire ƙafa. Wani kallon da tayi mata ya saka yarinyar juyawa ta bi Sophie mai kula da ita.
Agogo ta kalla ta ja tsaki, ta san tayi missing live din. Ta koma kan wayar
“Bye lovelies,see ya”
Ya yi wink.
Ta wullar da wayar.
•••••••••••✓•••••••••••
“OMG! Bye bye Fj”
Ta faÉ—i tana mirgina bisa gado.
“Farha ba ki da hankali Allah, mutumen da bai ma san da zaman ku ba ku yi ta hauka a kan shi”
Ta karkata wayar gefe ta É—ago ta na kallon ta da mamaki.
“Hauka? Mene abin hauka a nan to? Ni bana son kalar abin da ki ke min wallahi, ni ban hana ki abin da kike so ba kema kar ki hana ni nawu haba!”
Ta maida hankalin ta akan wayarta. Gallery ta shiga folder da ta tanada musamman don hotunansa ta shiga tana kallo duk hoton da ta shiga sai ta yi zooming din shi ta kalle shi da kyau cike da wani kalar so na ban mamaki. Kiran da ya shigo mata da sunan Qawata ya saka ta É—auka da sauri.
“Qawa kin kalla?Ta fadi cikin zumuÉ—i bayan ta daga kiran.
“Na kalla Qawa dole na ai shiyasa ma na kira ki ai. Kin ji zai fans eve?”
“Hmm ki bar tuna min, wata Æ™ila wannan ce dama ta…ke dole ma ita ce Wallahi muyi ta addu’a dai”
“Ga Mamana cen na kira na zan kira ki”
“Okay” ta kashe kiran.
Laylah ta sake kallon ta
“Wai ke ki kaddara ma kun hadu, duk dandazon fans dinsa sai kawai ku haÉ—a ido shikenan sai ya ce yana son ki sai kace a novel ko shirin film?”
“Wai don girman Allah Ya Layla ina ruwanki ne ni kam? Ko kina so ko baki so sai na auri Fahad, wallahi sai ya aure ni Ko ba so! Zan zauna dashi”
Laylah ta yi dariyar takaici.
“Ni gaskiya na ke nuna miki Farha, duk ma su zuga kin nan bawai hanyar kirki suke saka ki ba…”
Da sauri Farha ta mike ta diro daga bisa gadon.
“Na bar miki É—akin sai in ga wanda za ki addaba haba!”
Ta fadi ta na jan kofar É—akin garam! Ta rufo.
“Ke lafiya?”
Cewar dattijuwar mata fara tas dake zaune tana cin abinci bisa tabarma a tsakar gida.
“Umma..”
Kawai ta fadi tana turo baki.
“Ke da ‘yar uwarki halan?”
“Ai ita ce ke shiga harka na”
“Mtsw! Ban san sai yaushe za kiyi hankali ba Farha, ita ‘yaruwarki ce idan bata shiga harkanki ba nawa zata shiga.. kina da wata ‘yaruwar da ta fita ne? Ki daina kalar haka kin ji na fada miki”
Shiru dai tayi kawai tana nadamar fitowa wajen. Haka Umma tayi ta fadan ta kamar ta rusa kuka ta dinga ji, ita bata son fadan nan na Umma marar karewa. Kuma duk Laylah ke ja mata shi ba kowa ba. Ta rasa dalilin da yasa ita ba za tayi harkar gabanta kawai ta kyale ta tayi nata ba.
“Ki aje wayar nan kin san kina da wanke wanke ko? Kuma ke zaki girka abincin dare”
Umma ta katse tunaninta. Wayar ta aje kawai ta miƙe in ba haka ba ba zata bari ta danna wayarta cikin dadin rai ba sam.
“Wallahi kika jijjika kayan ba su fita ba sai kin sake wanke su”
Muryar Umma ta raka ta. Ta san halin Farha sarai da shegen kuiya. Kuma duk da kashedin da umma tayi mata haka bai hana ta yin aikin shaf-shaf din ba, burin ta kawai ta dawo taga sabbin hotunan da Fj zai daura a yau. Leƙowa tayi taga Umman na zaune t sai kawai ta koma kitchen din ta na ƙunƙuni ta ɗaura girkin dare.
Umma na sane ta Æ™i barin wajan, don ta sani zata fito ne ta cigaba da latsa wayarta,har girkin ya Æ™one tsaf in ba ayi Sa’a ba.
*
Lokacin da ta gama girkin magriba ta yi, bata ma iske Umma wajen ba, ta wuce dakin su ta zagaye Laylah da ke sallah ta shige toilet yin alwala.
Bayan ta idar da sallar ne ta dubi Laylah da har lokacin tana in da ta barta bata tashi ba.
“Ta sallah” Ta fadi ciki-ciki tana hayewa gado. Layla na jinta ta yi banza da ita dai, Farha bata jin magana sam. Ita dukkan tunaninta yana ga yadda zata fara zuwa Skye Royale aiki gobe ta ke. Ita ko Æ™ofar hotel bata taÉ“a tsayawa ba bare shiga ciki.
Gadonsu Farha ta haye ta ja bargo ta rufe kafafuwanta, sannan ta kunna data ta fara posting hotunan FJ da ta dakko a page din ta na Ig mai taken Road to FJ.
****.      ****
Misalin karfe takwas da rabi na dare bakar mota ta tsaya dai-dai katon gini, wanda tun daga saman benen da ake iya hangowa har kasa gilassaine masu daukar ido, da ga can sama dambareren sign board din an rubuta FJ RECORD dara-dara a sama mai kawo hasken kalolin wuta da dare, in da rana ne kuma ruwan gold ne mai kyawu a idanun duk wanda ya kalla. Hasken wajan ya maida area din tamkar rana. Matukin motar ne ya fara fitowa kafin da sauri ya zuge kofar baya ya matsa don bawa mai fitowar damar fita. Sai da ya russuna wajan fitowa saboda tsawo. Yana sanye da jeans da riga hoodie duka baƙaƙe, har sneaker din da ke kafarshi ma. Duk da dare ne ana iya ganin kyallin siririyar chain din da ke rataye a wuyansa da kuma stud da ke like a kunnensa na hagu.
Hannunsa ya saka ya zame hular ta kwanta bisa bayanshi, ya cusa hannunshi cikin sumar kanshi kamar yana so ya sosa wani waje da ya ke mashi kaikai. A zahiri kuma yana yin hakan ne a duk lokacin da yake jin abubuwa sun cakude masa, ko yana son subucewa wani abun wanda hakan ya zamo sararsa a kodayaushe. Ajiyar zuciya ya sauke ya na ci gaba da takawa zuwa in da yake hangen Khalid tsaye da alama ya dade yana jiran sa wurin.
“Na san nan za ka yo, tun da ka fahimci zan iske ka gida ai”
Ya fadi a dai-dai sadda FJ ya iso. Kansa ya sosa
“Kana da damuwa”
Ya fadi yana zagaye shi ya shige. Kai Khalid ya girgiza ya na bin sa a baya. Fridge Khalid ya bude ya fito da coke guda biyu ya mika masa daya, bayan sun shiga. Ya zauna.
“Fadi mani kayi signing din ko ba ka yi ba?”
FJ ya tambaya yana tsare shi da idanu.
“Ban yi ba…”
“To kar ka yi”
Ya katse shi ya na balle marfin coke din ya kai baki. Sai da ya sha sosai kafin ya sauke yana kallon Khalid da ke kallon shi cike da magiya.
“Kai ma ka sani mafarki ne kawai ka ke yi, duk da ba wai muna shiri da Abba ba amman ba zan yi harÆ™alla da abokan hamayyar sa ba, wannan yana daya daga cikin alkawarin da na yi masa. So mu bar maganar nan kawai”
Jijjiga kai yayi, ya san zai sha matukar wahala kafin FJ ya yarda su siya tsohuwar ma’aikatar nan, ba sune kawai ke so ba Elaas entertainment ma suna son daura hannun su a lamarin. Ba zai taba bari su riga su samu ba duk da babbar matsalar na ga FJ.
“Mu bar maganar a yanzun”
Ya fadi yana jijjiga kai.
“Ko a gaba ma ba za mu yi ta ba.”
Ya fadi sanin Khalid da naci ga abinda ya ke so.
“Miye schedule din wannan satin?”
Tab din da ke hannunsa ya kunna ya dan dudduba kafin ya kashe ya dubi FJ
“Kana da tattaunawa da Company L&L Luxurious..”
“Ka ce min kun kammala duk wata magana kuma?”
Ya katse shi, yana zuba masa idanu.
“Yes, amman a da. Abin da ni ke Æ™okarin gaya maka kenan jiya sai baka tsaya ba. Ka san ba Æ™aramin Company bane gaskiya suna da tsare-tsarensu musamman akan harkar talla, bayanan dai da Khamis ya yi min da yawa, a takaice manager din ya bukaci ganawarku kafin a tabbatar da contract din.”
Yadda Khalid ya ɗauki maganar nan da muhimmanci, ba zai bar maganar nan ta tashi a banza ba. Kuma dai shi kansa ya sani L&L Luxurious ne da zai ƙara ɗaga su sama ba ma kaɗan ba. Sai kawai ya amince kai tsaye.
“…kwana É—aya ne washe gari za mu bar Kano mu wuce Abuja za a ida video din Booj Arewa(WaÆ™ar da ya ke shirin saki) Kwana uku za mu yi acen mu dawo Katsina”
“Okay” ya fadi ya na miÆ™ewa
“Zaka iya tafiya gida”
Kai ya girgiza mashi.
“Ka gama rehearsal din sai mu fita tare”
Hakan kuwa a kayi sai da ya jira ya gama kafin suka fito, sai da Fahad ya shiga mota suka tafi kafin Khalid ya shiga motar shi ya tafi gida shi ma.
Yana kallon round about din da idan sun bi zai kai su har kofar gidansu. Ya janye idonsa tare da tusa hannunshi cikin sumar kansa. Bai shirya haÉ—uwa da Abba a tsohon daren nan ba duk da ya sani cewar abu ne mai wahala Abban ya yarda ya ganshi É—in. Mami ce ya ke son gani kuma zai yi kokarin shiga da safe kafin su bar garin.
*KO BA SO…*
Page 02
_”Nabeelah”_
_Ta É—ago idanunta da suke cike tabb da hawaye ta dube shi._
_”Ki yarda da ni uhmm?” Kin san zan yi ko miye don ganin mun rayu a inuwa guda ko?”_
_Ta gyaÉ—a kanta kurum._
_”Ki yi mini magana don Allah kin ji?”_
_”Na yarda da kai mana”_
_”Good”_
_”Yaushe za ka dawo to?”_
_”Ba zan É—auki wani lokaci ba, zan dawo da wurwurin da baki zata ba. Ina zuwa za mu tafi.”_
_”Kana ganin Baffa zai yarda ka tafi da ni ba muyi aure ba? Kuma yaya mutanen garin nan za su dubi abun…”_
_”Nabeelah”_
_Ya katse ta, ya na gyara tsayuwar shi._
_”Ban sha nanata miki babu ruwanki da tunanin mutane a kanki ba? Kawai ki yi duk abin da kike so kina ji?”_
_Ta gyaÉ—a kai._
_”Shin ba kina son ki yi karatu mai zurfi ba? Kina son ki tallafi Baffa da jajircewarki ba? To duk hakan za su faru ne kawai in kin toshe kunnuwanki, kuma kin rufe idanuwanki ga mutane. Auren zai zo daga baya.”_
_”To uhm…”_
_Ta dade fuskarta da hannayenta._
_”Ai kaine mijin uhm uhm”_
_Ya shafi kansa da hakan kusan ya zame masa jiki._
_”Nabeelah ko ni ne mijin ko ba ni bane babu abin da zai canja. Aure aure ne kuma ya na yin katanga da duk wasu abubuwa masu muhimmanci, a ciki har da burika!”_
_Ya jinkirta ya na kallon ta, kafin ya ce_
_”Ki yarda dani kawai”_
_Ta jijjiga kanta._
_”Na yarda da kai” Ta faÉ—i ta na jin yadda wutar son shi ke ruruwa a kirjinta…_
**
“Mamma..Mamma!”
Ta yi saurin maida ruwan hawayen da ke barazanar zubo mata. Har yaushe ta fara dogon tunanin Fahad haka? Ta girgiza kanta. Idan a kwai wani tunanin shi da ya rage mata to na É—aukar fansa ne.
“Mamma”
Ta kalli Noor da ke faman jijjiga ta.
“Noor mene wai?”
“Abbu ne ya kira ki”
Ta mika mata waya. Lumshe idon ta tayi ta bude cikin kasala kafin ta karɓi wayar.
“Hello..hello?”
Ta ciro wayar ta kalla. Kiran ya katse ashe bata ko kula ba. Ta ajiye wayar kan gadon da ta ke kai.
“Abbu yana aiki yanzun, idan ya gama zai kira kin ji?”
Ta gyaÉ—a kai.
“Oya je kiyi wasan ki”
Ta faɗi tana maida hankalinta akan saƙon da ya shigo a wayar.
Dukkan takardun sun haɗu, sa hannunki kawai ya rage. Za ki iya zuwa ƙarfe goma na safiyar gobe? Don a goben za su juya suka ce
Ta ciji leben ta na ƙasa, ƙarfe goma ai ko juyin farko ba tayi ba, to amman ya za tayi?
‘Okay’
Kawai ta rubuta ta tura. Kafin ta ajiye wayar kuma ta dau rurin neman agaji. Ta kuma cije leben tana kauda kanta gefe, ta kuma maido dubanta akan wayar kafin ta É—aga.
“Mijinah”
Ta faÉ—i a cike da É—oki. Tana jiyo sautin dariyarsa.
“Kun tashi lafiya?”
“Alhmdulillah, ya kake ya aikin? Kana dai cin abinci ko?”
“Ina ci dear kar ki damu, duk da dai kewarki ta hana ni sakewa..”
“Ni ma ina kewarka sosai, yaushe zaka dawo?”
Tayi saurin katse shi tun kafin ya fara yi mata magiyar ta biyo shi ko kuma in zai falla wani garin ya ce zai tafi da ita. Abin da ba zata taɓa yarda ba kuwa domin tafiyar nan tashi hutu ce a wajanta da kuma sakewa yadda ta ke buƙata.
“Gobe!”
Kamar daga sama ta jiyo goben. Idanuwanta ta bude tana girgiza kai kamar ta ce kar kai min haka.
“Goma na safe ina cikin garin ma In Allah ya so.”
“Da gaske kake?”
“Za ki sha mamaki”
Ya karashe maganar da dariyar jin dadi. Ba zata ce ga yadda sauran yanayin ya yi mata ba har suka ƙarashe wayar. Ta yi wurgi da wayar tana cije labba tare da ɗamƙe zanen gadon da karfi, zuciyarta na wani kalar zugi. Me yasa ya ke son bata mata duk wani tsarinta ne, me yasa yake shiga tsakanin ta duk wata nasarar da take son cimmawa. Ta girgiza kanta da sauri. Ba za ta bari ba, ba za ta taɓa barin wannan damar ta wuce ta ba idan har ta bari waɗannan mutanen suka tafi ba tare da sun kare yarjejeniyar su ba, tabbas tana ruwa. Domin takardu ne da idan har ta mallake su ne kawai zata iya hulɗa da mutanen da take ganin sune tsaunin da zata taka zuwa ga nasarar ta.
_Ki tabbar sun siyar miki da building din nan ki zo min da takardun masu É—auke da sa hannun da kika yi da nasu!”_
Yadda maganar ta faÉ—o mata, jin ta tayi tamkar yanzun ne ta ke faÉ—a mata hakan. Da sauri ta jawo wayarta ta shiga wajan sakon É—azun, babu suna sai number kawai. Ta rubuta,
‘Zan so Æ™arfe takwas!’
*****.       *****.    ******
Ta fi ƙarfin mintuna talatin ta na juye-juye, sai ta kunna waya ta dudduba google sai ta rufe.
Farha da ke latsa wayarta ta kallo ta da wutsiyar ido
“To wai ke da ba wani interview zaki kuma yi ba, ki kwanta mana kawai.’
Ta ida maganar ciki-ciki tana maida hankalinta a wayarta. Ajiyar zuciya Layla ta sauke tana kife wayar tare da kallon inda Farhan ta ke
“Hankalina gaba É—aya ya na ga hotel din can wallahi, ya zan tarar da su? Yaya zan yi aiki da su? Duk ban sani ba fa..”
“Ji beki da wata magana don Allah. To ina ruwanki da duka wannan? Ke dai ba aiki za ki yi masu su biya ki ba? Akwai mai dafa ki ya cinye ne?”
Fara ta katseta. Girgiza kai Layla ta yi da murmushin a fuskarta, Farha bata cika fahimtar rayuwa ba ita sam. Ita kawai ta na kallon rayuwa ne kayi abinda kake so shikenan, duk wani kalubale da zai biyo baya baya cikin lissafinta.
Skye Royale babban Hotel ne mai rassa a garuruwa kusan biyar, a ciki har da Katsina. A cikin rayuwarta bai fi sau uku ta taÉ“a gitta shi ba daga nesa kuma tana daga cinin Keke Napep. Ko a mafarki aka ce za tayi aiki da su zata karyata hakan, sai dai an ce rabon kwado baya hawa sama. Dalilin dalili da tsananin rabo ya saka sunan ta ya ratsa cikin jerin ma’aikatan Hotel din.
Ba zata taÉ“a manta alkairin Zainab ba gaskiya, don ita ce sanadin samun aikin nan nata. Zainab Æ™awarta ce da suka taÉ“a catering tare na wata shidda, a nan suka shaku da juna, bayan sun gama kuma da taimakon Zainab din ta dinga shiga classes kala-kala na zahiri dana online akan duk wani kalar abun da basu iya ba har da wanda suka iya din ma, wasu abubuwan duk na Æ™asashen waje ne. Ta sha cewa Zainab bata ga fa’idar koyan abinciccikan waje ba tun da wasu ingredients din ma babu su a nan. Sai tayi dariya ta ce
“Sai kin samu aiki a wani jigunannen Hotel zaki gane abin da wadannan abin da muke koyon suke da rana. Don ni burina in ganni kawai a Skye Royale”
Sai suyi dariya su duka, don ita ma Zainab ba wasu masu hali bane don dai yayanta dan siyasa ne kuma yana da kuɗi da kuma hanyoyin alfarma. Kuma shi din ya samo mata aikin a cen lokacin da suke neman kwararrun chefs. Abun sai in kana da hanya mai ƙwari. Ta taya Zainab murna sosai, duk da ita ta nuna rashin jin dadin yadda ba a samo da Layla din ba saboda ita ma dakyar aka samu nata. To da ya ke tana da rabo sai kwatsam maganar Auren Zainab ta taso aka sa biki nan da wata 2 kuma Lagos za ta zauna tun da acen mijin ya ke aiki. Shi ne Zainab ɗin ta roƙi yayanta ya shiga ya fita akai replacing din ta wajan Zainab, don har Interview sun riga sun yi.
Farha da Layla su biyu ne wajan Iyayensu Mal Mansur da suke kira da Baba da kuma Maryama (Umma). Baba malamin makarantar Secondary ne ta maza, suna da wadatar zuci sosai don kuwa Baba tsayayyen uba ne mai tsare dukkan hakkokinsa ga iyalansa, duk wani abu da bai fi karfin shi ba ya na masu iya kar kokarinshi haka Umma ma bata zama ragguwar mace ba mai bani-bani tana sana’o’in cikin gida, markade, ruwan sanyi da kunun aya almajirai na fitar mata da su, ko babu nepa Baba ya siya katon gen ya aje masu a tada a fridge yayi sanyi kuma su sha iska. Sannan tana saro takalma fashion na mata tana siyarwa a lokuta da dama har ta samu masu sarin shidda har goma suma su aza riba su siyar. Sannan ta na da injin markade da take yi a cikin gida.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da yanke shawarar ta kwanta din kawai.
**
Duk yadda ta saba tashi da wuri na yau ya bambanta, kuma hakan na da alaƙa da aikin da zata fara zuwa ne. Agogon dakin ta kalla 4:30 ,ta kalli gefen da Farha ta ke tayi dai-daya tana sharba bacci abinta. Ko bata tambaya ba ta san night subscription ta yi, ta raba dare ba tayi bacci ba. Ta girgiza kanta tana saukowa daga gadonsu, kwarai ta ke ganin kokarin Farha ta yadda mutum zai hana idonsa bacci saboda wata data cen duk da in da sabo ma ta saba gani in dai Farha ce. Kuma ba komai take ba sai bibiyar FJ da sauran celebrities. Tana ƙwakwar celebrities a rayuwarta duk wani labari sabo da tsoho yana bakin Farha, yadda ta ke bibiyar rayuwarsu a Social media ba zata yi karya ba idan ta ce bata bibiyar lahirar ta haka.
Sai da aka kira sallar asuba kafin ta tsaida karatun Qur’ani da ta ke yi ta tada Farha, tana mata mita da gunguni ta yi tsaye har sai da ta sauko ta fita don yo alwala kafin ta bar wajan ta dawo ta tada sallah.
6:30 ta gama shiryawa, ta fito. A waje ta ci karo da Umma ta gaishe ta.
“Ba dai har kin fito ba?
Umman ta fada bayan ta amsa gaisuwan. Ta yi dariya
“Ai na fada miki fitar malamai muke yi”
Ta fadi ta na dariya, umman ma dariyar tayi don ta fahimci da Baba ta ke. A lokacin shi ma ya fito, ta gaishe shi.
“Ki ci abinci yanzun nan in shirya kafin ki gama sai na aje ki”
Da sauri ta girgiza kai.
“A’a Baba da ni sa gaskiya, ko kafin mu isa har ka dawo ka wuce aiki ka makara, zan wuce kawai”
Dubu daya ya fiddo ya bata.
“Kin hau abin hawa to, ki kuma ci abinci kafin ki fita”
Ta karba ta yi godiya.
“Da sauri Umma ta koma kitchen ta sheka kokkon da take ta sauri ta yo daman saboda Layla din, tun da ta saba tashin wuri ko don Baba da ke fita kullum da safen.
“Yo sauri ki sha, barin duba in tuwon can yayi zafi sai na kawo miki ki hada”
Ko da tayi gardama ma ba zasu bar ta ta tafi haka ba don haka ta karbi kofin, ta zauna visa kujera nan tsakar gida ta fara sha. A gaggauce ta ci har dinamen tuwon da Umma ta bata sannan ta leka labulen dakinsu ta cewa Farha
“Ni na wuce, Sai na dawo”
Ta na ganin yadda Farhar ta dago mata hannu dakyar alamun bata son baccin ta ya tafi. Da addu’a su Baba ta fita.
****
Beelah
Dakyar ta bude idonta ta jawo wayarta karfe bakwai ya nuna har da yan mintuna. Ta yi hanzarin mikewa kai tsaye ta fada toilet ta yi wanka. Shaf shaf ta shafa face cream ta bi jikinta ta shafe da butter cream kafin ta dakko Black abaya mai adon purple daga baya, ta nada veil din abayawar ta dauki makullan mota ta fita. A gaban motar ta tsaya ta sake duba kwatancen da aka turo mata kafin ta shiga, mai gadi ya bude mata gate ta fita da sauri. Ta yi tafiya mai nisa kafin ta gangara bayan Muhamman dikki stadium din da aka fada mata. Ta dakko waya ta kuna kira tare da shaida in da ta ke, bayan an kuma yi mata ta sake nutsawa ciki kafin ta isa har lambar da ta gani da kalar gate din da aka fada. Aka bude ta shiga da mamaki take kallon wajan don bata zaki haka zata gan shi ba, don kamar ma gida mai part biyu ta tabe baki koma dai meye bai dame ta ba. Ta na tsaye wani saurayi ya fito a daya daga cikin part din yai mata jagora ciki. Dan siririn corridor suka wuce suka isa gaban wata kofamai nuna alamun office din da suke ne. Ta murda kofar da sallama ta shiga.
mutumen da ke zaune bisa kujerar da ke kallonta wacce da alama shi ne mamallakinta,wani mamaki ya sake kama ta. Ba kama ba alama.
‘wannan har wani kudi ne da shi?’ ta fadi cikin ranta tana kare masa kallo. Fari ne dan tsamurarre da shi, kamar ma baya samun abincin kirki duba da yadda tayani muninshi suka lotsa, sannan ga kasusuwan wuya kiri-kiri.
Busashen murmushin da ya yi mata ya saka ta janye idonta daga garesa tana murmushin yake ita ma. Bayan guntuwar gaisuwar da ta shiga tsakaninsu ya miko mata paper mai dauke da account details, ta karba ta tura msa kudin, jim kadan ya duba wayarsa ya sake murmusawa kafin ya miko mata wasu takardu ya ce
“Yi sign”
Ta karɓa, ta dinga bude kowanne page ta yi sign din da tasha wahalar koyonsa ba dare ba rana, don kawai wannan ranar. Murmushi ta yi idanunta na bisa sign din har zuwa lokacin da ta ji muryar Dan busasshe (Sunan da ta raɗa masa a ranta)
“Za ki iya tafiya da su”
Ta gyaÉ—a kai, tare da kwashe su ta tusa jikka. Ta yi masa bankwana ta tafi. A cikin mota ta dauki hotunan takardun ta tura hotunansu ta whatsapp tare da cewa ‘An gama’
*
Da sauri ta ida isa gida, ganin cewar lokacin da Abbun Noor ya fadi zai dawo ya kusa, kuma ta san shi sarai bi cika saba lokaci ba. Kitchen ta leƙa kai tsaye ta iske Sopie na wanke kayan da ta ɓata na kayan karin da ta yi masu. Ba ta damu da abin da aka girka ba, balle ta tambaya duk kuwa da cewar ba ita kadai za ta ci ba. Daki ta wuce ta tsala wanka abinta ta tsala kwalliya ta saka kananun kaya riga da dan guntun wandonta fari da ja ta tufke kitson brazil din da aka yi ma ta , a tsakiyar kai ta zubo shi ya na reto a tsakar bayanta. Idan akwai abin da bata da shi a duniyar nan a fannin kyau to gashi ne, mutane da yawa da suka san ta ba karamin mamakin yadda bata da gashi su ke ba. Kallo daya da an mata za a tsammaki tulin gashi a tattare da ita, musamman da gaban kanta ya ke kwance luf sai a zaci duka kenen sai ta cire kallabi za ka sha mamaki. Hakan ne ya saka ta saba da karin gashi kala-kala.
Ta na tsakar shafa turare ta ji shigowar motarsa. Ba tare da tunanin kayan jikinta ba tayi hanzarin fitowa har a harabar gidan bakinta a washe.
Dogo ne ba cen ba, don dai yayi wa gajeru fintinkau. Sannan fari ne duk sai dai ko kafar farinta bai kamo ba tun da ita irin farin nan ne da ita da ko ciwo ta yi bata duhu sai dai ta sake yin fayau, sabanin shi idan yayi ciwo ko ayyuka suka sha kansa ya kasa zama, sai ya yi duhu don ma dai kudi na boye kaso tamanin na wahalar idan ya sha.
Da sauri ya iso yayi mata rumfa da jikinsa ta hanyar rungume ta, kafin a cikin kunnenta ya fadi
“Mene ya sa ki fito a haka? Ko so kike na kori mai gadi da sauran ma’aikatan gidan?”
“Uhm uhm” Kawai ta yi ta na sake shigewa jikinsa.
“Oya mu je ciki”
Ya kama hannunta suka shiga daki. Sai bayan yayi wanka kafin ya fita ya kwaso kayansa da ya bari a mota ya dawo.
“Motarki kamar an hawo ba jinawa kin fita ne?”
Ta juyo da sauri ta kalle sa, sai kuna ta saki murmushi
“Na kai Noor makaranta ne da kaina”
Ya dan bude baki cike da mamakin wai ita ta kai Noor makaranta. Mafi yawan lokaci ma bata san sadda Noor din ke tafiya ba, ko shi sai yayi sa’a ta ke sanin fitarsa tana cen ta na bacci balle kuma har ta kai Noor makaranta?
“Mene?”
Ta tambaya a ƙagauce, don ita ma ta san amsar ba mai saurin kamawa ba ce
“No, na yi mamaki ne”
Ya faÉ—a ya na zama a dining table.
“Na kwanta da wuri ne, kwanciyar ta ishe ni shiyasa kawai na tashi”
Ta faÉ—a ba tare da ta kalle sa ba. Ya gyaÉ—a kai kurum. Abincin ta buÉ—e za ta zuma masa ta ga soyayyar doya da kwai, dan turus ta yi sai kuma ta kalle sa.
“Ya ya dai?” Ya ajiyewayar hannunsa yana duban ta da murmushi.
“Doya Sophie ta soya” Ta fadi a hankali har idonta na kan doyar. Ta sani ba ya son soyayyar doya da kwai ko kadan gara ki dafa masa ita da miyar ganye da manja.
“I’m sorry Dear, ban san abin da ta yi ba kenan”
Ta sake fadi jin yayi shiru.
“Ke da gidanki har ayi abin da baki sani ba?”
Ta narke fuska
“Ka yi hakuri, in dafa maka noodles?”
“Zan sha tea kawai”
Ya fadi ya na jawo flakes din ruwan zafin ya zuba. Shi din ma fari ƙal ruwan babu wasu kayan kamshi ko daya, a haka dai ya haɗa tea ya sha da zallar biredin da ya sa wa butter. Ita kuma ta ci doyarta ta yi naƙ! Abinta, ta kora da ruwan lipton din strawberry.
Ya na gamawa ya miƙe, ya shige bedroom dinsa ya kwanta don huce gajiyar da ya kwaso da nufin idan ya tashi zai je gaida Hajja. Wayoyinsa ya saka a silent mood ya na ajiye su a bedside ta shigo.
“Mijinah”
Ta fada ta na zama gefen gadon.
“Ka na fushi da ni?”
“Meyasa?”
Ya tambaya.
“Na sani ai, ka yi hakuri kaji? Allah ban san za ta yi shi ba. Kuma yau da kai na zan yi maka girki kafin ka tashi.”
“It’s okay, kar ki damu bana fushi da ke”
Ya faÉ—a ya na dan bubbuga bayanta.
Da gaske kuma baya iya dogon fushin da ita, ya na mata wani kalar so da shi kansa bai san iyakarsa ba, wannan ne dalilin da ya saka bai cika ganin laifinta ba sam.
Tare su ka kwanta baccin, sai dai ta riga shi tashi. Ta na zuwa dakinta ta iske wayarta na ƙara.
Ba su yi doguwar magana ba kamar yadda su ka saba kiran ya katse. Takardun dazun ta dakko ta harhada. Ba a fi minti shabiyar ba wani kiran ya shigo. Hijab ta zura ta fita daga cen dan nesa da gidanta ta hango dan aiken tsaye gaban machine dinsa. Ya sha facemask da katom tabarau da su ka taimaki boyewar fuskarsa. Sai da ta kira number dazun ta tabbatar shi ne kafin ta ba da takardun ta koma gida.