Ko Kun San Abin Tashin Hankali Akan Kisan Gillan Hanifah

Ko Kun San Abin Tashin Hankali Akan Kisan Gillan Hanifah?

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: hanifah

Ku Karanta Da Kanku Kuji; Allahu Akbar!

 

Wato babban abin tashin hankalin shine. Wadanda ake cewa iyayen ta ne, ba sune suka haife ta ba, an basu ita ne saboda basu taba haihuwa ba.

 

Sun dauke ta kamar yar’su, marikin yarinyar nan ya amince zai biya kudi naira miliya shida, ya nemo miliyan uku, yaci gaba da fafutukar neman wata miliyan ukun dan su tsirar da rayuwar ta.

 

Iyayen ta na riko, sunyi mata riko fiye da wadanda suka haife ta a cikin su. Sunyi kokarin wadata ta da farin ciki, sun samar mata kyakykyawar rayuwa, ance yarinya ce ma farin jini ga kowa, cikin sauki take shiga ran mutane saboda fara’arta.

 

Jiki na yake so

An samu mugu ya datse mata rayuwa, maimakon ya kyautata mata gangar jikin ta, sai ya wulakanta halittun ta ya saka a buhu ya binne a wajen da ko kare ba lallai mai shi ya binne shi a wajen.

 

Ya dasawa masu rike da ita mugun ciwon da har duniya ta kare ba zai fita daga zuciyar su ba, kafin su samu yarinyar data shiga ransu Kamar Hanifa sai sun sha fama.

Hanifah

Tin daga kan mai unguwa, dagancin yanki, kansila, chairman har gwamnan jihar kano damu al’umma. Dole mu nemi yafiya daga wajen Hanifa, mun gaza samar mata da tsaron da zata samu nutsuwar zuwa makaranta cikin salama.

See also  Yadda Yan Nigeria Suke Matukar Son Fim Din Squid Game

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top