Hausa Novels

Komai nisan dare Hausa Novel

Komai nisan dare Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KOMAI NISAN DARE…..!

 

 

 

 

 

_By_

_Zeey Kumurya_

 

 

 

 

 

 

 

*ELEGANT ONLINE WRITER’S*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*0️1️*

 

 

 

 

 

 

 

 

*ALHAMDULILLAH I’M BACK*

 

 

 

 

 

 

I’m selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!

BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE

I’m

selling MTN data with this cheap price

MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500

Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month

Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Whatsapp OR

Call 08066268951

 

 

 

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
_Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu ‘batawa kai lokaci🙏🏻_

 

_*infection*_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu’amula mussaman ga ma’aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za’a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

_07084653262_

 

 

 

 

 

 

 

 

………Unguwar *Ƙofar fada* dake cikin garin *Kumurya*. Yarinya ce wadda baza ta wuce shekaru goma sha ɗaya zuwa sha biyu ba a duniya take tafiya cikin ƙwaleliyar ranar da ta ƙwalle. Sanye take cikin uniform na makarantar government primary school dake cikin garin. Cikin sauri take tafiyar amma kana ganin yanayinta zaka gane a galabaice take. Ƙafafuwanta duk sun yi fututu cikin ɗan Madina slippers. Wani Babban gida ta shiga mai ɗauke da ɓangarori da dama kamar yadda duk yawancin gidajen garin suke. Bayan ta wuce dogon zauren gidan ta shiga ɓangare na biyu daga b’arin dama da ɗan gudunta tana ƙwala kiran sunan “Inna! Inna.” Inna dake duƙe a cikin madafi gaban murhun duwatsu ci tana hura wutar kara wadda ta mutu, gaba-d’aya ta haɗa uban gumi hayak’i duk ya turnik’e ta. Sauri take wutar ta ruru dan ta dafa dankalin Hausa kafin *A’isha* ta dawo daga makaranta, dan ta san da yunwa zata dawo tunda ba wani karin kumallon kirki ta yi ba da safe. Sai dai haƙan ta bai cimma ruwa ba har A’ishan ta dawo, sakamakon wutar data rura ta mutu gashi kuma bata da ashana, guntuwar ta kenan ta yi amfani da ita. *Inna* ta ɗago idanuwanta wanda suka fara rinewa zuwa launin ja saboda hayak’i ta dubi A’isha wadda ta shigo kamar an cillo ta. Cikin ɗan faɗa Inna tana goge idonta da ya fara tara ruwa ta ce. “A’isha ban hana ki gudu da shigowa gida babu sallama sai dai aikin ƙwala mun kira kamar wata sabuwar makauniya ba?” A’isha ta turo ɗan ƙaramin bakinta bata ce komai ba ta koma ta fice daga ɓangaren ta sake shigowa bakinta ɗauke da sallama. Girgiza kai kawai Inna ta yi tare da amsa mata ta cigaba da abun da take yi. Jakar buhun hannunta ta ajiye akan tagar ɗakinsu ƙwaya ɗaya tal dake cikin zagayen nasu sannan ta cire takalminta ta matsa kusa da Inna tana kare fuskarta da hannunta saboda hayak’i ta ce. “Inna sannu da aiki.” Inna ta gyaɗa mata kai kawai. A hankali ta ce. “Inna ki kunna masa ashana mana.” Inna ta ce. “Ta ƙare ne A’isha, daa da ita ai da tuni na kunna.” A’isha da yunwa ke ƙwaƙular hanjin cikinta ta ce. “Bari na aro miki a gurin innarsu Ma’u.” Bata jira cewar Innan ba ta yi waje da gudu ko takalmi bata saka ba. Inna tana kiran ta tare da faɗa mata Innar Ma’un bata nan amma bata ma ji ta ba balle ta tsaya. Ɓangaren Innar Ma’u a jikin nasu yake, tana shiga ta tarar da ɗakinta a kulle da ƙaramin ɗan mukulli alamun bata nan. Juyawa ta yi ta shiga ɓangaren dake kallon nasu dan arowa Inna ashanar, duk da ta san zai yi wahala su bata saboda tsanar da suka yi musu ita da innarta, kaf faɗin gidan Innar Ma’u ce kawai take k’aunarsu idan ka cire Marigayi Malam Mijin Inna. A tsakar gidan ta tarar da matan gidan guda biyu, ɗaya tana daka a turmi ɗayar kuma suna zaune akan tabarma ita da wata mata, da alama bak’uwa ta yi dan matar bata yi kala da mutanen garin ba, duba yanayin shigar jikinta gami da buɗewar idonta da uban bleaching ɗin da ta ci. A’isha ta yi sallama tare da gaishe su, babu wanda ya amsa mata sai ma wani matsiyacin kallo data samu daga matan gidan. Matar nan kuma wani irin kallo take bin ta da shi mai kama dana mamaki. A’isha bata damu ba ta dubi wadda ke zaunen ta ce. “Baaba Ramatu dan Allah ki arawa Innata ashana zata kunna wuta.” A harzuk’e Ramatu ta ce. “Idan Ubanki ne ko na Asaben ya siya mun ashanar sai ki zo ki ƙwata, shegiyar yarinya kawai.” A’isha ta ɓata fuska tare da kallon wadda take daka zata yi magana, sai dai bata ba ta damar hakan ba ta hanyar daka mata tsawa da faɗin. “Fice daga gidan nan dan malafar Ubanki, ita Uwar taki uban wani ya hanata siyan ashanar, zaki kwaso jiki ki taho wai a baki aron ashana, Uwar ashanar za’a baki ba ashana ba.” A’isha ta marairaice ta ce. “Dan Allah Baaba Hansai yunwa nake ji kuma wutar ta ƙi……” Zaburowar da Hansai ta yi yasa ta juyawa da gudu ta bar ɓangaren. K’wafa Hansai ta yi ta ce. “Da kin cigaba da tsaiwa ai dana yi ƙasa_ƙasa dake a gurin nan, Mayyar yarinya kawai ta tsare mutane da shegun idanuwanta kamar zata lashe mu.” Matar nan data kasa ɗauke idonta daga kan A’isha har sai da ta fice, ta sauke numfashi tare da kallon Ramatu wadda ta bi bayan A’isha da muguwar harara kamar idonta zai faɗo ƙasa, cikin mamaki ta ce. “Ramatu wannan kyakkyawar yarinya fa a ina take?” Ramatu ta tab’e baki cikin baƙin ciki da hassadar an cewa A’isha kyakkyawa ta ce. “Gaskiya Hajiya kin dad’e baki zo garin nan ba, yanzu baki san Mayyar matar da Malam ya auro mana ba shekara fiye da goma?” Hajiya ta ce. “Kin manta Ramatu na yi zaman Saudiyya na shekaru, ai rabona da garin nan na kusa shekara goma sha biyar sai gaisuwar Malam dana zo.” Ramatu ta ce. “To kin gan ta nan dai Malam ne ya auro mana jaraba dan Mayya ce.” Cikin mamaki Hajiya ta ce. “Mayya kuma?” Ramatu ta ce. “Mayya mana, ban da haka daga ya tsince ta a hanya da shegiyar jaririya a hannu bai san asalinsu ba bai san daga inda suke ba kawai ya saka aka d’aura masa aure da ita ya kawo mana ita cikin gida ya gurɓata mana zuri’a, Ubangiji ma ya so mu da arzik’i bata haihu da shi ba. Ta shanye masa kurwa sai abin da ta ce Malam ya yi yake yi kafin ya rasu, ke in tak’aice miki zance cewa ya yi ko bayan ransa kar ta bar gidan nan, ya bar mata inda take ciki a zaune halak malak tunda shi ya gina abunsa, kin ga kuwa wannan abun ai ba na dan Allah ba ne, ko mu da muke iyayen ƴaƴansa bai yi mana irin wannan kyautar ba sai ita.” Hajiya ta jinjina kai tare da sakin wani ɗan murmushi, wani tunani ya ɗarsu a ranta game da A’isha. Ta dubi Ramatu ta ce. “Allah ya kyauta.”

 

 

 

 

 

 

 

A’isha kuwa bayan barin ta ɓangaren su Ramatu cikin gida ta nufa tana bi ɓangare_ɓangare tana a ba su aran ashana, duk inda ta je da bak’ar magana da cin zarafi ake koro ta, amma hakan ba ya hana ta ƙara shiga wani gurin ta tambaya, dan ita burinta kawai ta samo ashana ta kaiwa Innarta ta yi ta hura wuta abun da ta ɗora ya dahu ta ci. Jiki a sanyaye ta dawo ɓangaren nasu, ta tarar wutar ma ta ruru Inna tana aikin azawa. Zama ta yi a ƙasa ta fara hawaye. Inna ta dube ta bata ce komai ba ta cigaba da abun da take yi. Tana hawayen ta ce. “Inna a ina kika samu ashanar?” Inna ta ce. “Ban sani ba, ina kiran ki dan iskanci shine kika yi gaba ko?” A’isha ta ce. “Ban ji ba fa Inna, kuma na je Innar Ma’un bata nan, na manta da safe dana biyawa ma’u makaranta ta ce baza ta je ba za su je unguwa.” Inna ta ce. “Da kika ga bata nan sai kika je inda ban aike ki ba ko?” Shiru A’isha ta yi bata ce komai ba. Tana nan zaune har dankalin ya dahu Inna ta juye mata duka a roba ta bata, sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko wani guntun k’uli_k’uli ta kawo mata dan ta haɗa ta ci da shi. Cikin sauri_sauri A’isha take cusa dankalin a bakinta tana ci, Inna tana zaune akan langa ta yi tagumi tana kallon ta, tunanin abun da zata yi na sana’a take yi dan zaman nan haka ba zai musu ba, Tunda Malam ya rasu suka shiga taskun rayuwa, abun da za su ci ma wataran gagarar su yake yi. Ta yi sana’oi da dama domin ta samu abun da za su rufawa kansu asiri amma kamar wadda aka sakawa hannu abun ba ya ci, sai ta fara an fara ciniki rumi_rumi Masha Allah sai abun ya lalace, wataran idan ta yi abun sai dai su cinye ta rabar da guntun dan ko na biyar babu wanda zai zo ya ce a ba shi. Ta rasa ma ina zata saka ranta…… “Inna gashi na ƙoshi ke ma ki ci.” A’isha data ajiye mata guntun dankalin a gabanta ta katse mata tunani da faɗin haka. Inna ta sauke numfashi tana kallon kwanon dankalin ta ce. “Har ya ishe ki?” A’isha ta ce. “Eh na ƙoshi Inna.” Inna ta sauke numfashi ta ce “Ɗauko murfi ki rufe kya ci anjima.” A’isha data nufi gurin randa dan ɗiban ruwa ta sha ta ce. “Inna ki ci mana.” Inna ta girgiza mata kai kawai bata ce komai ba. A’isha ta ɗibi ruwan ta sha ta yi hamdala sannan ta shiga ɗaki ta cire uniform ɗin jikinta ta zira kayan gida ta fito tsakar gida. Inna ta dube ta ta ce. “Ga ruwa nan akan wuta na ɗora miki, idan ya yi d’umi sai ki juye ki yi wanka kafin ki tafi karatun, ki je ɗaki zaki ga Naira goma a kan window, ki ɗauko ta sai ki ɗauki botikan can ki kai ki saka mana a layin fanfo, zan zo in ɗauka idan an zuba ruwan.” A’isha ta turo baki gaba ta ce. “Inna da safe fa kafin na tafi boko na yi wanka, kuma yanzu in ƙara sakewa?” Inna ta ce. “Zaki yi abun da na ce ne ko kuwa?” Kamar zata yi kuka ta koma ɗaki ta ɗauko kuɗin ta fito ta sungumi bokatan guda biyu ta fice. Miƙewa Inna ta yi ta shiga ɗaki ta kwaso uniform ɗin da A’isha ta cire ta fito da su dan ta ɗauraye mata su bayan rufe guntun dankalin da A’ishan ta rage.

 

 

 

 

 

 

 

Gurin ɗiban ruwan a cike yake da mutane ƴan ɗiban ruwa yara da manya, mata da maza. Tunda A’isha ta ga haka ta ɓata fuska, dan ta tsani duk abun da zai haɗa ta da taron mutane a cikin garin, domin ta san baza su taɓa gwanyewa lafiya ba, tunda babu mai k’aunar su a cikin garin sai waɗanda baza a rasa ba, dan ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba, shi yasa bata k’aunar Inna ta turo ta gurin fanfon nan. Kasancewar garin suna da wahalar ruwa yasa aka yi tanki a wajen gidan mai gari, to duk mutanen dake kusa a nan suke ɗiban ruwa, shi yasa kusan kodayaushe gurin a cike yake da mutane. Kanta a ƙasa ta ƙarasa ta je gurin wanda ake bawa kuɗin ruwan ta gaishe shi tare da ba shi kuɗin. Ya amsa mata tare da karɓar kuɗin sannan ya nuna mata ƙarshen layi ya ce ta je ta saka buckets ɗinta. Bata yarda ta kalli kowa ba a gurin ta ƙarasa ta ajiye bokitan a hankali, duk da yanda kusan kowa na gurin yake kallon ta. Ta koma gefe ta tsaya kafin layi ya zo kanta. Mintuna biyu da tsayiwarta ta ji tsayuwar mutum a gaban ta, ko da ba’a faɗa mata ta san waye, Ɗan_juma ne ɗan gidan Mai gari, matashin Saurayi mai tashe a cikin garin, wanda bai da kirki da mutunci ko kaɗan, tun A’isha tana ƴar ƙaramarta ya takurawa rayuwarta, shi a dole son ta yake yi. Ɓata fuska sosai A’isha ta yi tare da kawar da kanta gefe. Ɗan_Juma ya riƙe k’ugu ya ce. “Ke! Dan na zo gurinki shine zaki wani kawar mun da kai kina wani ciccin magani, eye? A’isha ta watsa masa harara ta ce. “To Ni ina ruwana da kai, ba Innata ta ce karka ƙara kulani ba?” Ɗan_juma ya yi wata ƴar dariya ya ce. “Babu wanda ya isa ya hana ni kula ki A’isha duk garin nan wallahi, na gani kuma na yaba dole na samu, lokaci kawai nake jira ki ƙara girma a sha bikinmu.” Turo baki A’isha ta yi ta ce. “To ni bana son ka, Allah ya sauwak’e na aure ka, kuma kar ka ƙara kula ni.” Ɗan_juma ya haɗe rai sosai ya ce. “Ke! dan ma kin samu zan taimaka in aure ki shine kike faɗa mun magana? Wace ce ke?” A’isha ta murgud’a masa baki ta ce. “Mutum ce ni ƴar mutuwa jikar rasuwa kakar jana’ida.” Kasancewar da ƙarfi Ɗan_juma yake magana yasa hankalin mutanen gurin gaba-d’aya ya dawo kansu. Wata budurwa ce wadda baza ta wuce 16 years ba ta ƙaraso inda suke tana faɗin. “Ni wallahi Ɗan_Juma na rasa me ka gani a jikiy wannan ƙwailar *MAYYAR* Yarinyar ka na ce mata haka, yarinyar da *SHEGIYA* ce *MARA ASALI*, ga mu nan ƴanmata birjik a cikin garin nan sai ka zaɓa ka darje amma ka bi ka lik’e mata.” Ta ƙarasa zancen tana karkad’a ƙirji tare da jifan A’isha da wani mugun kallo. A kufule A’isha ta dube ta, ta ce. “Ke Hindu kar ki ƙara ce mun Mayya ko shegiya, ni ba Mayya ba ce kuma ba Shegiya ba ce.” Kamar Hindu zata kai mata duka ta ce. “An faɗa ɗin Shegiya Mayya me zaki yi mun? da mece ce ke idan ba mayyar ba, kuma idan ke ba Shegiya ba ce waye Ubanki a cikin garin nan?” A’isha ta fashe da kuka ta ce. “Wallahi ni ba Mayya ba ce, kuma Baba Malam shine Babana.”………✍️

 

 

 

 

 

 

_*Tafiyar fa mai nisan zango ce, Allah ya bani ikon yin posting kullum🥹*._

 

 

 

 

 

 

 

*By*

*Zeey Kumurya*

Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!