Kowa Ya Ci Bashin Kura Hausa Novel
Tag: Kowa Ya Ci Bashin Kura Hausa Novel
KOWA YA CI BASHIN KURA
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
SADAUKARWA GA:Â ANTY BILLY GALADANCHI (OUM NUEYM)
MONDAY (Litanin)
Tushen aiki akace ko Bature na tsoronta, tun da na wayi garin yau Litanin nake jin kasala ta tattare dukkan sassan jikina duk wani kuzari ya dasƙare a gaɓaina, a daddafe kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, na samu kammala shiri na, don ina mugun tsoron Yah Arham musamman da na tuna da jan kunnen da yay min na ƙarshe, akan kar na ƙara tsayar da ƴan uwana, waɗanda a kullum suke zaman jirana a mota, sanyin jiki halitta ce amma nawa ko ni kaina yana bani haushi, saboda duk cikin ƴan matan gidan, nafi kowa sanyin jiki da rashin kazakazar ɗin aiki, shiyasa kullum nice makara sai an tsaya jirana idan zamu tafi makaranta.
Abaya fara nasa mai folawowi jajaye sai mayafin ta da na yafa, jikata dana zuba kayana aciki na rataya itama fara mai kyau da tsada, babban falo na fito, sai dai tsit ba kowa, akan na san Daddy baya gari, shiyasa na wuce sashen Mommy, da sallama na shiga, amsa min tayi fuskarta É—auke da murmushi, har Æ™asa na kai ina gaishe ta, cike da so da Æ™auna ta shafa fuskata tana amsa min, tace”Zaitun ashe dama kin iya shiri cikin lokaci, ki ka bari Yayanki ya dinga miki ranÆ™washi yana takura ki duk akan makara?” yaÆ™e nayi nace”Mommy ai ba zan Æ™ara bari in makara ba, don na lura Yah Arham zai fasa min kai da hannun shi mai kama da Æ™arfe…Dariya tayi ta ce”To kiyi haÆ™uri da yayan ku, sannan Zaitun ana son mace da kama jiki, na lura ba don Arham ya dawo ba, to ALLAH kaÉ—ai ya san irin lalacin da zakiyi, wataÆ™il karatun ma ba zaki iya ba, yanzu kije ki karya, an gama haÉ—a komai sai ki wuce.” Tashi nayi ina turo É—an Æ™aramin bakina mai kama da sharp É—in zuciya, ina daddaga Æ™afufuna cike da sangarta na langwaÉ“e kai ina dubinta, sannan na ya mutsa fuska nace”Mommy yau kasala nikeji abincin ma ba zan iya ci ba…” Ƙofar da naji an murÉ—a yasa na juya don ganin wa zaya shigo, caraf idona ya sarÆ™e a cikin nashi nan take numfashi na, ya É—auke na wucin gadi, ganin shi ya haifar min da mugun faÉ—uwar gaba, zare idona nayi cikin nashi a lokacin bugun zuciyata yana kai kawo tare da min barazana a Æ™irjina, dafe gefen da nake jin bugun zuciyata nayi, tare da gyara zaman mayafi na, muryata na sarÆ™ewa Momy sallama, Addu’a tayi min tana adawo lafiya sannan kafin na fita na tabbata na karya, wani harara ya yi min akaro na biyu da idaniyan mu suka sulke da juna sai da naji wani tsam daga Æ™asan Æ™afafu na har kaina, saboda na tsani Yayana na tsani halin sa na cin amana, da sanyin murya nace”Yah ina Æ™wana, banza ya yi min, sai da na zo daf da shi, ina jiran ya shigo É—akin, ni kuma in fita, kamar saukar mashi hakan naji saukar ranÆ™washin a tsakiyar kaina, ban san lokacin da nace”Wayyo Mommy!”
https://mynovels.com.ng/littafan-hausa-novel/
Ina dafe kaina, wanda ya sha sabon kitso, murtuÆ™e fuska ya yi ya ce”zaki wuce ko sai na Æ™ara miki?” ashe kin iya shiri da wuri? Amma ke kullum kece ta baya a fitowa, wato iskanci ne da rainin wayo, ke sa kike makara har ki zo kina wani zuba sangarta da surutu kamar suda dallah ban wuri ko in ball dake…” ta gefen shi na lallaÉ“a na wuce da sauri, Æ™wallah mai É—umi ya É—igo min a hannu, gogewa nayi ban tsaya ma ya Æ™arasa faÉ—an shi ba nayi tafiyata ina *ALLAH* ya isa cikin zuciyata.
Kowa Ya Ci Bashin Kura Hausa Novel
Mommy É“ata fuska tayi tare da zuba masa kallon zo in kashe ka, tace “Haba Arham bana so fa! Haka kawai kasa min yarinya gaba, ko so kake ka gine mata maÉ—iga ne?” Murmushin sa irin na miskilai ya yi, ya ce “Mommy kin san yarinyar nan taki ba jin magana take ba, ni ne ke aikin gyara miki ita ina saita mata notikan da suka Æ™wance a kanta ne”
“To ni dai ka sake mata mara dallah, ai kurciya ce, kowa da irin tasa, duk wannan lalacin da sakaci da take, watarana sai labari.”Momy ta ce tana ninke kayanta dake saman gadon, zama ya yi gefen gadon shi ma yana tayata ninkewa, ita kuma sai mita ta dinga yi masa akan ya fita harkar Zaitun bata so, ganin hakan yasa Arham yace”ALLAH ya huci zuciyarki, daman zan wuce ofis ne, sai na dawo daga nan fita yay yana mamakin wannan Æ™aunar da ke tsakanin Mommy da Zaitun.
Da sauri na isa dining place na zauna zaman karyawa kamar yadda Mommyna ta umurce ni, sai dai me wani turniƙi ya turniƙeni a lokacin da tururin abincin yay arba da hanci na, da sauri na rufe ina dafe ƙirjina, don wani hamami nakeji yana taso yana damfare shi, ga kuma wani zafin kai na ya ƙara taso min inda Yah yay min ranƙwashi, hawayen da suka zubo min a fuska na share, sai jin abubuwa na taso min a zuciyata nakeyi ba tare da nasan dalili ba, tashi nayu ina toshe hancina inda muke haɗuwa a filin estate ɗin don shiga mota na isa, na ja na tsaya, don yau nice ta farkon zuwa, buɗe marfin mota nayi na zauna, littafina na buɗe ina dubawa sai ga Afifah nan muka dinga zuba, don daman ita ɗin ta hannun dama na ce, Anty Aidah da ƙanwarta Arisha su ma ba aji ma suka fito can sai ga Mima uwar tsiwar gida kuma ƙarshen masifa ta zo, haka kawai jinin mu bai haɗu da ita ba, tana shigowa direban ya ta da mota zuwa makarantar mu *ALQALAM UNIVERSITY*
Makarantar mu jami’a ce ta musulmai haka tun kan shigar mu, mun fita dabam da ta sauran É—aliban jami’a, domin daga Hijabs sai Abaya muke shiga dasu makaranta, haka harkokin addini sun fi yawaita a cikin makarantar, kasancewar bayan Anty Aidah duk mun taso kan mu É—aya shiyasa dukan mu acan muke karatu sai dai kowa da abinda yake karatu acikin mu amma ita Anty Aidah tana shekarar Æ™arshe. Tun da muka shiga mota Mima ke hararana tana kallona tana wani hurar hanci, ni dai ban kulata ba, don ni dariya ma take bani, taje hararana caraf idon ta suka sarÆ™e dana Afifa, tsaki Afifa tayi ta ce”Lallai iska na wahalar sa mai kayan kara.” kamar jira Mima take ta ce”Ke kuma as wa? A cikin kayan girki ke awa?” Ni a gishiri, magi, kuma ruwa.” inji Afifa tana murmushi.”
Anty Aidah ta ce”Afifa, Mima kar in Æ™ara jin bakin kowa a cikin ku kun ji kaji, ina ganin fa idan baku daina faÉ—a ba, sai na haÉ—aku da Yah Arham ya zane ku, da naso na faÉ—awa Nanna amma nasan matakinta ba mai sauÆ™i bane, shiyasa zan tsaya inda Yah…”
“Kiyiwa ALLAH Anty Aidah karki haÉ—a mu da wannan azzalumi” inji Mima tana murguÉ—awa Afifa baki.”
Afifa ta ce”Antynmu ni dai na daina kiyi haÆ™uri kin san daga Yaya har Nanna jan wuya ne…”
Dariya suka sa dukan su, ban da ni dake karatun littafi, don ban cika shiga sabgar kowa ba, fira sukeyi sosai wanda rabi na Nanna da Yah Arham ne, sai can idan Afifa ko Anty Aidah sun sako ni zan É—an ce wani abu, daman Arisha miskila ce bata fiye magana ba, amma kam Mima sai faÉ—i take ana dariya har muka kawo makaranta, a hankali muka fara fitowa daga mota sai dai me….
Wani tururin warin man fetur wanda a hasashena na motar mu ne, ya bugi Æ™ofofin hanci na, ba zato bare tsammani amai ya kawo min hari, wurin na durÆ™ushe ina fesa amai kamar an buÉ—e famfo, wanda duk ruwa ne nake amayewa, saboda ban ma yi karin safe ba, dafe cikina nayi saboda ni kaÉ—ai nasan irin azabar da nakeji aciki, Anty Aidah da Afifa ne suka kamani, inda Arisha da Mima ke ta faman jera min sannu, Sale Direba wanda ya rikice ya ce”Hajiya Aidah ko mu wuce da ita asibitin da ke kusa da nan?”
Anty Aidah da ke Æ™oÆ™ari ta da ni, Ta ce”Bari mu gani” taÉ“a jikina tayi wanda nan take ya rikice, Subhanallah!Kun ga Afifa ku shiga School bari mu koma gida adubata ina ga maleria ce, don jikin kamar wuta, ya yi zafi sosai.
“To shi kenan Anty” inji Afifa muryarta a sanyaye tuni wanda idonta yay ja, saboda ganin yadda jikin Æ´ar uwarta ya yi tsanani. Arisha dafani tayi da tausayi ta ce”Anty Zaitun Allah ya baki lafiya.” ni dai bance masu komai ba sai toshe hanci na, da nayi don har yanzu ina ji warin fetur É—in a hancina, da taimakon Anty Aidah na miÆ™e tsaye ina tangaÉ—i, Afifa da Arisha ne suka kakkaÉ“e min jikina, Anty Aidah jikata da takalmi ta É—auka tare da riÆ™o hannuna, ta ce”muje asibitin gida a duba ki.”hawaye naji suna gangaro min a idona saboda na san Æ™arshen ciwon nan, ya kai ni ga maganar allura abokiyar gabata, muryar Mima naji tana faÉ—in “Amma dai ke Æ™atuwar banza ce Zaitun, a makarantar ma sai ke nuna halin ki na sakaci da raki, uhummmn ALLAH ya baki lafiya, Afifa, Arisha muje…” Meyasa baki san ciwo ba Mima? inji Afifa, Mima ta buÉ—e baki ta ba Afifa amsa, Anty Aidah ta ce “Kar kice komai ku tafi.” daga hakan suka wuce, mu kuma mota muka koma, mayafina nasa na É—aure hancina, Sale direba da Anty Aidah sai sannu suke jera min har muka É—auki hanya har muka iso Estate É—in mu.
Clinic É—in da aka tanada domin ahlin mu, can Anty Aidah ta wuce dani, sai sannan ta samu kunin kiran Mommy ta sanarda ita, cikin tsananin firgici Mommy ta ce”Tana zuwa” daga nan ma’aikatan suka duÆ™ufa wurin duba ni, a lokacin duk wani kuzarina ya Æ™are hatta hannuna bana jin zan iya É—agawa da kaina, babu abin da nake ji ga fatar bakina sai É—aci, tuni miyau bakina suka daina kai kawo a maÆ™ogwarona, laÉ“É“ana sun bushe sunyi fari, kukan zucin da nake ya bayyana don naga suna Æ™oÆ™arin É“alle allura a gidanta, sai dai yau Æ™aryata ta Æ™are kuma tusa ta Æ™arewa budari, don ban da Æ™arfin guduwa kamar yadda na sa ba idan za’ayi min allura, Dr. Bilal murmushi ya yi sannan ya ce Anty Aidah ta riÆ™eni. don ya san mai hali baya bari, abin mamaki har ya gama min allurar banyi wani motsin kirki ba, sai idanuwa na dake malalo ruwan hawaye, jinina Dr.Bilal ya É—iba ya wuce Lab don ya san irin matakin da zai É—auka akan ciwona na kullum wato maleria da typoid.
Mommy a suƙwane ta ƙaraso inda nake ƙwance, kamar gawa, sai tambayar Aidah take ya jikin?
Aidah ta ce”Da sauÆ™i Momy yanzu ma Dr. ya yi mata allura, ya dai É—ebi jininta za’ayi test.” Okay, Allah ya sauwaÆ™a Zaitun ciwon nan ya dameta, yaÆ™i ya barta ta sarara, lafiya law fa ta fito…inji Momy tana danna wayarta
Aidah ta ce”Lafiya law muka tashi daga gida, daga mun isa School ta fita daga mota sai amai, nan take jikinta yay zafi, amma yanzu kinji jikin nata ya sauka.” Momy taÉ“a jikin tayi tana kallona sai sannu take jera min tana tattaÉ“a ni, ido na zuba musu don yanzu ba abinda nake sai zufa duk da sanyin Ac da ke ratsa jikina, amma gumi nake haÉ—awa, Momy hannunta tasa cikin nawa tana waya, wanda ga dukkan alama da Yah Arham take waya, Aidah ta ce”Momy bari inje in faÉ—awa Maman Arisha daga nan in ajiye kayan nan…Haba!Aidah ai kin koma makaranta tunda kinga Zaitun taji sauÆ™i” inji Momy
“Ko na koma Momy É—, ba zan gane komai ba, don abin nan yana raina sai dai gobe idan ALLAH ya kai mu.”
“Shi kenan sannunki da Æ™oÆ™ari ALLAH yabar zumunci, amma karki shiga sashen Nanna yanzu sai hankalinta ya tashi idan taji ZAITUN ba lafiya.”
“Karki damu Mommy ba zan biya ta sashenta ba, yanzu zamu dawo ni da Maman Arisha.”Inji Aidah tana Æ™washi kayanta da na Zaitun, sannan ta wuce.
Shi kan shi yasan ALLAH ne ya ƙaddari ya kawo Estate ɗin lafiya, don gudun da ya dinga shartawa saman ƙwalta ya wuce tsammanin mai tunani, da sauri ya shigo clinic ɗin, inda nake ƙwance nayi lamo duk na takure a jikin Momy hannuna dafe da ƙasan cikina dake mini wani murɗawa!
Arham ya ce”Mommy meke damunta? Ko typoid É—in ne? ya tambaya
“Ban sani ba Arham” amma Aidah ta ce”Dr yana lab zaiyi test don aga meye matsalarta.”
” Bari na duba shi a lab É—in.” inji Arham da sauri ya fita daga É—akin.
KiciÉ“is sukayi shi da Dr.Bilal wanda ke ta faman kaiwa da komowa yana duba takardar da ke hannun shi, Dr “ya ake ciki?” Hankalin shi a tashe ya dubi Arham sannan ya maida kallon shi kan takardar fuskar shi É—auke da damuwa.
“Don ALLAH ka faÉ—a min abinda ke damun Zaitun, ko typoid É—in nata ya fars taÉ“a hanjin ne?” Girgiza kan shi Dr.Bilal ya yi ba tare da ya ce komi ba, ya miÆ™a ma Arham takardar result É—in.
Amsa ya yi ya fara karantawa amma bai fahimta ba, har sai da ya duba fiye da sau goma, sannan ya karkaÉ—a, ya runtse idon shi ya buÉ—e, ya dubi Dr. Bilal a firgice ya damÆ™o shi da zafin nama, ya manna shi ga bango yana fidda idonsa da suka sauya daga fari zuwa ja da Æ™araji ya ce”Ka faÉ—a min kuskure ne ko gaske? Ka faÉ—a min kasan aikin ka ko baka sani ba? Ka faÉ—a min kayan aikin ku lafiyan su Æ™alaw, ko sun samu matsala? Dr.Bilal shin gaske ne ko mafarki nake? Idan mafarki ne kace in tashi.