Kundin Ma’aurata Sirrin Rike Miji

Kundin Ma’aurata Sirrin Rike Miji

 

 

 

 

 

 

 

.

 

KUNDIN MA’AURATA //40

.

_*KI KIYAYE WADANNAN*_

_1) Ki yi qoqarin tafiya daidai da zamani, ‘yan abubuwan da aka samu sabo ke ma ki dan sabonta, yadda ake sanya abinci a kula (cooler) don kar ya yi sanyi ke ma ki sanya a sayo miki, yanzu an samo sinadaran qara wa abinci qamshi da dadi (wato seasonings and spicies), ki koyi yadda ake amfani da su ki fara gwadawa, kar ki ce ke haka kike abinki, ki tuna cewa maigidanki fa zai riqa cin abinci a wasu wuraren, kuma zai riqa jin bambanci tsakanin naki da wancan, hatta tsarin gyara gida da sauransu duk an zamananta abubuwa ke ma ki dauka daganan, ga matsukiya a islamic chemists wace ba ta kawo infection samsam ki nemo._

.

_2) In kina ganin maigidanki yana miki komai kike so, hatta ‘yan uwanki suna fa’idanta da shi to ki kiyayi uwayensa, tabbas mace ta fi samun matsala da uwar miji, wata tsamar za ki taras ke ce ba ki da ladabi ba ki san yadda za ki tafiyar da ita ba, wani lokacin kuma za ki ga ita ce, kar ki damu ki yi mata uzuri, duk alkhairinnan da kike ciki da samun kula da komai ita ce sanadi, gashi kin zo kin qwace komai, ba abin da kika bar mata sai suna._

.

_Wannan maigidan naki ya zauna wata 9 a cikinta kamar yadda danki ya yi, haka ta haife shi ta yi ta goyo da raino har ta yaye, tare suke kwana, da ya shiga makaranta ta yi ta wanke kaya, ga wahalar wanki ga kudin sabulu, ko tana jin yunwa za ta nemo masa abinci, da ya girma ita ce abokiyar shawararsa, komai ya kawo gida ita zai kai mawa, yanzu kin qwace komai, a dalilinki ya canja gida, in ma yananan a gabanta za ki saka shi a daki ki kulle qofa, ya dena cin abincinta sai naki, ya kike ji in ya dena cin abincinki?_

See also  Abinda uwar gida ya kamata ta rika yiwa kishiyarta

.

_Hatta ‘yan shawarwarinnan na yau da kullum ya daina yi da ita, har cewa ake yi ke ce mahadin rayuwarsa, in ma wani abu ne nasa ba a tambayarsa sai dai ke, wai ke ce iyalinsa, in ma ba a gida daya kuke ba sai a kwashe wuni bai je wurinta ba, wani ma yakan kwana bai je ya gaishe ta ba, in tana son ganinsa sai dai ta zo wurinku ko in tana son wani abu ta gaya miki ke ce za ki gaya masa, abin da yawa, don haka ki yi mata hanzarin wasu abubuwan, a littafan tarihi mun ga cewa rainon Annabi SAW kawai Halimatus Sadiya ta yi, amma Khadijah RA sai da ta ba ta dabbobi 40 don aikin da ta yi wa mata na rainon mijinta._

.

_3) Ki yi duk qoqarin da za ki iya na ganin kin tsallake abubuwan da za su baqanta miki rai, ko su jefa wasu shakku a zuciyarki game da wanda kike girmawa sama da kowa a rayuwarki, irin wadannan abubuwan sun hada da binciken rayuwar maigida, kina son ki ji ko yana zuwa wani wuri bayan inda ya ce miki zai tafi, kamar ki ce “An ce an gan ka a wuri kaza, me ka je yi?” Ko ki ce “Ni ban san ka da irin wannan turaren ba, a ina ka samo shi” ko “Hala dai kana zuwa wurin wata ne kana cin abinci shi ya sa ba ka iya cin nawa sosai?”._

.

_Irin wadannan sukan fara ne da ba’a gami da zaulaya a hankali har su juya su zama gaskiya, lamarin ya koma tuhuma, yadda za ta sa ‘yan leqen asiri su fara binciken komai nasa, ita kuma ta fara duba wayarsa don ta gano wanda yake hira da ita a waya, in ya ajiye wayar ta fara duba sunayen wadanda ya kira ko wanda ya kira shi, wata in ta ga sunan mace sai ta kwafe lambar ta kira ta ta yi mata kashedi, in abu ya yi nisa takan yi qoqarin sanin gidansu yadda za ta bi ta can, ta zazzage ta._

See also  Yanda zaki gane kina da aljani da addu'o'in da ya kamata ki yi

.

_In ma hakan bai yi mata ba shi kansa maigidan ne zai shiga matsala, duk in ya dauki waya sai ta fara ‘yan zirga-zirga tana neman yadda za ta gano wanda yake magana da shi, in ta ga mace ce to dole soyayya ce a tsakaninsu, to bare mu maza tunda aure daga 1 zuwa 4 sun halatta zai yuwu mutum ya dan fara latsawa don ya samu a gama lafiya, nan wata masifar za ta fara, qila ta iya kaiwa ga rasa rai, kamar dai yadda muka riqa gani, wasu sun kashe mazan a dalilin haka, wasu kuwa sun nemi kisar da wuqa ko da wani abu Allah ya qwace su, wasu kuma sun rabu da mazan duk da tsabar qaunar da suke musu, bincike bai yi rana ba kenan._

.

_Na ji rigimar da ta faru a kwanakin baya yadda wata ta kashe maigidan a dalilin irin wannan binciken, ta ja kunnensa amma bai ji ba, a wajen shari’ar alqali ya tambaye ta “Me ya sa kika kashe shi?” sai ta ce “Wallahi qaunarsa nake yi, ba zan iya raba kwanaki da wata mace a kansa ba” alqali ya ce “To da kika ga ba za ki iya ba, me ya sa ba ki kashe kanki ba sai kika kashe shi?”_

.

_Ta yi shuru ba ta iya magana ba, sai ya ce “In dai qaunar ce za ta sa ki yi kisa ai kin fi kowa son kanki to ga ki a raye, wace kike qin raba kwanakin a raye, shi kuma kin kai shi lahira, kenan in za mu taimake ki dole sai dai mu tura ki can inda yake don ku zauna tare” ma’ana za a kashe ta kenan, nan ta samo lauyoyi don su hana ta riskar mijin, maganar gaskiya ba qauna ce ta sa ta yi kisar ba, qiyayya ce da mugun bincike kan abin da bai dace ba ya kai ta ga wannan matsayin._

See also  Hotunan Soyayya da Kalaman Soyayya

 

_Anan Zan Dakata Sai Mun HaÉ—u A Rubutu Na Gaba Insha Allah_

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top