Hausa Novels

Kungiyar Matsafa Tashiga Hausa Novel

Kungiyar Matsafa Tashiga Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: KUNGIYAR MATSAFA TASHIGA

(Mahaifiyata)

 

 

( _True life story_)

 

 

 

By

*UMMU SAFWAN*

( _fareeda basheer_)

 

 

 

 

 

 

 

P1️⃣

 

 

 

 

 

 

“Meyasa Talauci yazab’i ya zauna a tare damu,? Musamman a wurinka tare da wurga Masa harara, ta tsuno Baki tana fadin

“Wallahi Tallahi Maigida nagaji da wannan bak’in talaucin naka,

tayaya za’ace mutum takwas yana kwana a cikin daki d’aya, duka numfashin mu Yana hadewa wuri daya, idan ma wata cutar ce dukanmu zamu mutu a banza a Wufi to na gaji wallahi,

 

yaran Nan su shidda dukansu Mata ne tayaya zamu dinga cudanyar aure a daki daya dasu wata kila duk abunda mukeyi suna jinmu ko idonsu akanmu.”

 

Shuru Bello yayi Wanda Yana sauraren matar sa Wanda Sam Bata da godiyar Allah duk abunda yakeyi akansu Bata gani kullum cikin rainawa takeyi da hangen gidan k’awaye masu kudi.”

 

Gyaran murya yayi ya kalli matar tasa

Yace “suwaiba Ni bana tare da Talauci domin Ina da wadatar zuci, a

Kullum Ina godiya ga Allah akan yanda ya barni domin bangaza da kuba, daga ke har yarana dukanku Baku taba kwana da yunwa ko k’ishi ba,

Bakuda rashin sutura sai dai kice wurin kwanciya ne yayi Mana kadan.”

 

Nafikijin zafi da radadin cudanyarmu da mukeyi da yaranmu, a wuri daya, duk da hakan muna kiyaye tarbiyarsu saboda suna falo muna uwar dak’a,

Insha Allah Babu wani abinda zai sami yarana Allah ya masu albarka,

 

Kinfi kowa sanin Ba Dan da aka rage mana albashiba insha Allah da yanzun na iyar da rufe gidana mun tattara munkoma,

Nima na huta da biyan kudin hayar da nakeyi a duk shekara.”

Amma nasan komai lokaci ne dashi Allah Yana sane damu.”

 

Tsawa ta daka Masa Wanda hakan daya daga cikin dalibi”un tane tace “ya isheni bello shekara nawa kana ginin gidan da kake fad’a,

Idan ban manta ba Tun Ina goyon yarmu ta farko Ramla gashi yanzun shekarar ramla goma Sha biyar me kake jira baka karasa ba,

Ni wlh wnn bakin talaucin ya isheni kadubeni da kyau mace ce ni kyakkyawa Mai jikin hutu, Amma duk na jeme na tsofa saboda ta lauci.”

 

Idan na kalli kawayena wadanda muka tashi a tare duk sunfini kyawon gani,

Snn dukansu Babu Wanda yake aurin talata sai Ni, har kunya shiga cikinsu nakeji

Snn ko wanne da motarsa yake yawo Yana saka sutura Mai kyau da tsada,

Ni Kuma idan kaga nasa sutura Mai tsada to atamfar dubu biyar ce kasaya mun,

Ni Kam wlh nagaji bazan iya ba.”

 

“Kallonta yayi cike da takaici da bakin cikin kalaman ta yace “to yakikeso ayi yanzun tunda kince kingaji?

 

Dogon tsaki taja tabar wurin tana fadin ” canza sana’a zakayi kabar aiki a karkashen gwamnatin jaha ka samu wani aikin Mai tsoka Wanda yake kawo kudi ba dole sai kadogara ga albashi ba,

 

Karin wasu littafai da zaku so

Alhaji sanusi mijin hajiya Amina kawata sai da ya taba yimaka magana akan kazo ya baka aiki Wanda yake kawo kudi Nan take,

Kayi biris dashi kaki zuwa,

Hakan Bai Bai Sa ya hakura ba duk natafi gidansu sai yace nai maka magana, ka yarda ya baka aikin Amma kaki yarda kafison mu tabbata cikin wnn bakin talaucin na tsiya so kakeyi mu Kare rayuwarmu a gidan haya to Ni Kam bazan iyaba wlh.”

 

“Ido yabita dashi inda take a tsaye a kofar dakin , ta rike labulen dakin,

Yace “bana son aikin nasa nawa ya isheni ainima ba hakan Zan tabbata ba,

A kullum muna duban ci gaba, Kuma insha Allah muna fatan musamu canji a Nan gaba,

Snn a Koda yaushe nasan Alheri zai zo in Allah ya yarda,

Yana kaiwa Nan yaja tsaki ya fita daga dakin yanufi wurin aikin nasa.”

 

Kasancewar safiya ce duka yaran nasu suntafi makarantar boko ta gomnati Wanda babansu yake kokari akansu,

Yaransu shida ramla itace ta farko snn siddiga sai rufaida snn habiba da subai’a sai Kuma Hassana itace auta husainarta ta rasu.”

Dukansu Yara Mata ne Allah ya basu kyawawa.”

 

Tana ganin fitarsa taja dogon tsaki tashiga Shirin fita zuwa gidan kawarta hajiya Amina ko zata samo abin arziki a hannunta Wanda Bata gajiya Bata kudi da kayan Dadi a duk lokacin da taje wurinta,

 

Atamfar tasaka samuwa dal Wanda anko ce maigidan nata ya dinka Mata tare da yaranshi, ta dauko hijab dinta tasaka ta feshi jikinta da turare ta rufo daki tare da yiwa matan gida sallama cewar zata fita Amma ba jimawa zatayi ba,

 

Adawo lafiya sukayi Mata Sukaci gaba da aikin gabansu domin idan da sabo sun Saba da bakin yawon nata mijinta yana fita tana bin bayansa,

Wanda a kullum mtan gidan suna jinjinawa kokarin da mijin nata yakeyi akanta da yaranta Amma ita Sam idonta a rufe suke Bata gani, kullum cikin cin zarfinsa takeyi.”

[29/07, 9:07 am] +234 816 238 5196: *KUNGIYAR MATSAFA TASHIGA*

( _Mahaifiyata_ )

 

 

( _True life story_)

 

 

 

 

By

*UMMU SAFWAN*

( _fareeda basheer_)

 

 

 

 

 

 

 

2️⃣

 

 

 

 

 

 

‘yar Tafiya tayi ba Mai nisaba

Ta isa gidan hajiya Amina,

Babban gidane maigirman gaske, kwankwasawa tayi maigadi ya fito yaga itace ya koma ya bude Mata Yana murmushi Suka gaisa ya Bata hanya ta wuce,

 

Yar tafiya tayi ta Isa get na biyu, a Nan ma ta kwankwasa maigadi ya bude Mata tashiga,

Hakan tayi ta Tafiya har zuwa get na uku Wanda yafi ko wanne tsayi da girma ga Kuma nisan tafiya domin kafin ka Kai a get na uku din zaka iya gajiya,

Gidane babban gida mai girma da fadi marar misaltuwa,

Da kyar tasamu ta Isa a get na uku a Nan ma maigadi ya bude Mata tashiga

Tana sauke ajiyar zuciya akan tafiyar da tayi,

Kai tsaye babban falon kawar tata tanufa ta tura kofa tare da yin sallama tashiga”

 

Hajiya Amina tana zaune Akan kujerarta ta alfarma tana sanye da wani lafiyayyen lesi d’inkin doguwar riga yasha adon duwatsu,sai kyalli takeyi,

hannunta sanye da gwal hakan ma sarkar wuyanta gwalce sai wani sheki takeyi taci ado da gwalagwalai a hannunta da wuyanta, sai waya takeyi tana dariya,

 

Tana ganin shigowar Suwaiba ta kashe wayar tare da sakin dariya tana kallonta tace “tinda Kika biyo hanya nasamu labarin zuwanki k’awata ta fad’a tana dariya,

 

Suwaiba tasaki dariya taje kusa da hajiya Amina ta zauna tare da sauke ajiyar zuciya tace “kema ai kinsan zanzo din,

Kibari kawai k’awata yanzun muka gama yinta nida Baban ramla keko ayi mutum da taurin Kan tsiya,

nayi nayi naxo wurin alhaji yabashi aikin da yace zai bashi Wanda zai dinga samun kudi Amma yaki,

fad’a Masa ya canza aiki yakiji, gaddamar masifa ce dashi ga bakin talaucin tsiya.”

 

Ta kalli hajiya Amina ta kalli d’akin da take ciki tace “Yanzun Dan Allah kiduba kigani gidan da kike cikinsa k’awata ke kadai kike rayuwarki a ciki ba kishiya ba wata takura,

Hankalinki a kwance gashi Allah Bai Baki haihuwaba bare hayaniyar Yara ta addabeki sai more rayuwarki kawai kikeyi,

ta dafe Kai tace “Ni Kam rayuwata tana cikin matsala ga Talauci ga fitinar namiji kullum Yana kaina Yana raraka ga fitinar Yara idan nayi da wnn nayi da wnn nice bana samu na huta sai idan suntafi makaranta, ga bakin talauci da yai mana katoto, ta dafe Kai tace “nidai suwaiba Ina cikin masifa wlh.”🤦‍♀️

 

Dariya ta bawa hajiya Amina tace “kawata kenan karki damu komai zai Zama tarihi idan kina tare Dani,

TaKira Mai aikinta ta shiga kawo Mata kayan motsa Baki,

Anan take aka cika Mata gabanta da Naman kaxa Naman rago farfesun kayan ciki fruit duk gasunan a gabansa.”

 

Wata irin dariya tasaki tace “nagode k’awata, anan

Taja ta faraci suna Hira,

Sai da taci ta koshi snn ta daga Kai ta kalli hajiya Amina tace, nafa gode Allah ya Kara arziki”

 

Ameen hajiya Amina tace tare da mikewa tsaye tace “Kinga yanzun fita zanyi”

 

Fita Kuma zakiyi Ina Zaki tafi ?

 

Unguwa zantafi idan Kuma Zaki rakani to zamu iya tafiya a tare.”

 

Me zai hana, mutafi mana ai sai na rakaki ko k’amshin motarki na Shaka narage wani radadin a Raina.”

 

Dariya hajiya Amina tayi tace to mutafi Suka mike suka fita bayan ta yafa mayafinta,”

 

Tafiya kawai sukeyi Mai nisan gaske Wanda tin suwaiba Tana magana har ya Kai tayi shuru ta rasa abinda zatace sai Kuma hankalinta ya koma akan yaranta domin lokacin tashinsu a makaranta yayi gashi Bata girka masu abinci ba,

Gashi lokaci d’aya suke dawowa da babansu”

 

Ta juya ta kalli hajiya Amina tace “kawata nikam Wai Ina zamu tafi ne, da har yanzun bamu kaiba gashi har lokacin tashin su ramla yayi a makaranta,

 

Murmushi hajiya Amina tayi tace kecefa kikace kina zuwa ba Dole nai makiba kijira mun kusan zuwa inda zamu tafi,

 

Ta karkata Kan motar ixuwa cikin wani daji inda Babu kowa a cikinsa, sai falla gudu kawai hajiya Amina takeyi da mota,

 

Acan gindin wani k’aton dutsi tayi parking anan suwaiba ta hango jini yana malala a Kan dutsin Kamar ruwa.”

 

Anan Sukaji an daka masu wani irin tsawa kamar saukar aradu Wanda anan take suwaiba ta Suma a wurin.”

 

 

*****************

 

Ramlat tare da k’annenta ta sanyasu a gaba suna gaba tana bayansu sun taso dag makaranta, kasancewar makarantar su d’aya,

sai dai ita tana secondary school tana aji biyar,

sai Mai bi Mata SIDDIK’A tana aji uku sai Rufaida dake aji biyu,

 

Habiba da hassana sune a primary habiba aji biyar hassana tana aji uku,

Duka makarantar daya ce sai dai bangaren secondary daban na primary daban,

 

‘yan primary ake Fara tayarwa

Su habiba kenan, Bazasu iya tafiya gida su kadai ba sai sun tsaya sun jira sauran Yan uwansu idan aka tashi gaba daya snn RAMLAT ta sanyosu a gaba su k’araso gida.”

 

Yau tun a hanya habiba da subai’a suke kukan yunwa sukeji,

Hakan Ramla take lallashinsu akan suyi hakuri da zarar suntaho gida zasu tarar da abinci mama ta kammala masu,

Kasancewar Babu wani tafiya sosai tsakanin makarantar da gidansu Dan hakan da k’afa suke tafiya su dawo da k’afa.”

 

A gajiye suka dawo ko wanne Da sallama dauke a bakinsa tun a zaure habiba ta cire hijab din jikinta domin hakan al’adarta ce Suka shigo cikin gidan,

Matan gidan Suka amsa masu sallamar ko Wance sai faman hidimar kammala abincinta takeyi Dan kada yaranta sudawo su tarar bata kammala ba,

 

Turus sukaja suka tsaya ganin dakin mahaifiyar nasu a rufe da kwad’o.”

To Ina mama ta tafi?”

Ramlat ta tambayi kanta.”

 

Zaune hassana ta kai ta Fara birgima tana Kuka itafa yunwa takeji.”

Dama hassana gwanace wurin cin abinci musamman idan aka dawo daga makaranta Babu inda take Fara zuwa sai wurin da tasan Ana ajiye masu abincin su a wurin”

 

Kallonta Ramlat tayi ta Bata tausayi,

Taje wurin randar ruwan ta debo Mata ta Mika Mata tace “ungo Kisha ruwa kafin mama ta dawo.”

 

Ture kofin ruwan tayi ya Fadi kasa tana fadin “yunwa nakeji ba kishirwa ba,

 

Sauran Yan uwanta Suka nemi wuri suka zauna a kofar dakin mahaifiyar tasu, Suka rafka tagumi,

 

Ramlat ta Kalli d’aya daga cikin matan gidan tace “Dan Allah maman Aminu ko” Mama ta fada maku inda tatafi?”

 

Mere Baki maman Aminu tayi tace “ba Wanda ta fadawa inda ta tafi domin kullum sai ta fita, yau ne kadai akayi rashin sa’a Bata dawo da wuriba,

Shuru Ramlat tayi ta nemi wuri ta zauna tare da janyo hassana a jikinta tana lallashinta.”

 

Suna hakan sukaji tsayuwar mashin a kofar gida da alamar mahaifinsu ne ya dawo.”

Ai kuwa shine ya shigo da sallama a bakinsa hannunsa dauke da ledodin tsarabarsu domin hakan al’adarsa take duk yafita yadawo sai ya shigowa Yara da tsaraba Koda kuwa yalo ne ko Kara’s,

Wani lokacin nama gasanshe wani lokacin Kuma fura da nono domin yasan yaran nasa suna son Shan fura da nono.”

 

Mamaki ya Shigayi ganin yaransa a zaune a kofar daki,

dakin Kuma a rufe da kwad’o.

 

Bai Nuna masu damuwar sa ba,

Saboda mutanen da ya gani a tsakiyar gidan sun tsaresu da Ido suna jiran suji abinda zaice,

 

Murmushi ya sakarwa yaran nasa Yana fadin “mamanku tafita kenan to ai da akwai makulli a hannuna,

Ya Ciro key din a cikin aljihunsa ya mik’awa Ramlat yace “ungo ki bud’e dakin kushiga, ya mik’awa Siddiga ledodin fura da nono tare da kifi da yasawo yace ungo kishiga dashi kujirani Ina zuwa.”

 

Ya kalli hassana yace hassana sarkin Jin yunwa kukan yunwar ne akeyi ko?

Ya Mika Mata hannu yace taso mutafi kirakani.’

 

Ta dauki hijab dinta tasaka ya Rika hannunta suka fita,

 

Shagon kusa da gidan ya tsaya,

Ya saya masu taliya domin yasan itace abincin da za’a dafa tayi saurin dafuwa cikin sauri,

Ya sayi garin kwaki da suga da Madara, ya janyo hannun Hassana suka taho gida,

 

Fura Suka Fara Sha, snn ya jika masu garin rogo hannunsa hannun yaransa suna Sha suna Hira, domin akwai shakuwa sosai a tsakaninsu Zan iya cewa yanda Suka shak’u da mahaifinsu Basu shaku da mahaifiyarsu hakan ba, Dan tsakanin ta dasu fada ne da hantara,

Suna kammala Shan garin rogon Hassana tayi bacci hakan habiba tabi Bayanta,

Ya kalli Ramlat yace “ga taliya Nan na sawo ki tashi ki dafa,

Idan Kika kammala dafawa kizuba kuci ku koshi idan Kuma bakwaci saiki zuba a kula ki ajiye idan kuka dawo daga islamiya sai kici tare da k’annenki, Allah ya maku albarka yayiwa rayuwarku albarka kada kudamu da halinda muke ciki wata Rana sai labari.”

 

Share hawayen fuskarta Ramlat tayi tace “Baba Wai Ina mama tatafi ne?”

 

Kallonta yayi yace “wlh bansaniba, hakan shi taga ya fiye mata,

 

Siddiga ta mere Baki tace “can ta matse Mata Allah yasa kada ta dawo.”

 

Babanta ya d’aga Kai ya kalleta yace “kull kada na Kuma jin irin wnn maganar ta fito a bakinki…..

 

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!