Hausa Novels

Kwaratta Complete Hausa Novel

Kwaratta Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Kwaratta Complete Hausa Novel

^^Shekaruna goma sha bakwai cas a duniya. Babana yana da mata hudu da “ya “ya hamsin da bakwai.^^

 

Mahaifina ya kasance dan auri saki ne, bakin abinda kunne na yaji mahaifina ya auri mata ashirin da takwas.

 

Babana ya kasance talaka ne baya da wata sana’a wadda ta wuce “yan bige bige, ya gwanance wurin iya karya sannan kuma babu abinda kware dashi sai cin bashi………

 

Talaka ne amma baya saka sutura irin tasu, idan kika gansa zaki rantse da Allah yana iya kyautar naira miliyan biyar, yasan dadin kudi sosai amma a sutura baya tausawa naira.

 

^^°Baya da gidan zama haka kuma baya da fili ko taki daya, munyi zama a anguwanni da dama sosai wanda duk anguwar da muka sauka suna mana lakabi da gidan inna ratata, ko kuma suce gidan yawa…

 

Baya da aiki sai shaye shaye sannan kuma duk gidajen cacar dake garin katsina babu inda ba’asan shi ba, ya saka kansa caca wanda ake kira da nigerful, caca ce wacce take cinye tattalin arziki kuma ba kananan talakawa keyinta ba sai masu kudin gaske saboda idan har za’a buga wasan cacar mahaukatan kudine ake zubawa.

Karanta Littafin Kuruciya Hausa Novel

Baya bayar da abinci haka kuma babu abinda ya damesa da rashin lafiyar “ya “yansa ko matansa, idan dai caca tayi masa dadi zai siyo kwanon shinkafa daya da kuma rabin doya,

 

Da safe idan zai fita zai bayar da kudin kalaci ko wane daki naira talatin babu wani abinda ya damesa da yawanku.

 

{}{{{}}} Wata rana can wurin wasan caccarsa aka cisa, amma baya da kudin da zai biya daga cikin abinda aka saka masa, dan haka suka cire masa sutura, tun daga inda ya buga wasan har zuwa gidanmu daga shi sai gajeran wando haka ya ratso mutane saboda tsabar shi tantirine har ya iso gida.

 

Babu ruwansa da tarbiyar dan sa ko yar sa, shi yasa muka mayar da gidanmu kamar gidan karuwai, domin dai kowa abinda takeso shi takeyi dan babanmu yace sana’a itace tafi cancanta ga duk diyar daya haifa, ya daina biyan kudin haya yace mu zamu rika biya tunda kowa ya kawo karfi, dan haka duk yayuna suka tashi dan neman na kansu kowa ya kama sana’a amma banda ni,

 

Abinda yasa kuwa shine, lura da irin kyawun da Allah yayi min, karkuyi tunanin kyawu na wasa ko ku lakaba abin da shirme ni nake gaya muku haka, bawai a gidanmu ba gaba daya zuri’armu babu yarinya mai kyau da daukar hankali kamar nawa….

 

Ina da kyau fiye da tunanin mai tunani, ina da diri daidai irin wanda maza ke so, ina da babban kugu sannan kuma Allah ya bani baiwar iya murzasa.

 

Haka kuma ina da cikar kirji ina da manya idanuwa sannan ina da fari irin na fulanin asali, gaba daya zuri’armu babu mai haske na, idan na shigo taro mata sun gama wali haka kuma babu macen da zata kara tasiri harsai na bar wurin.

 

Ni “yar gayu ce, na iya wanka kuma na iya shafa turare gaba daya bani da tsara idan na ziyarci wuri kamshina zaiyi ta kasancewa a wurin, haka kuma idan na barsa turarena zai dade bai daina tasiri ba, sannan duk gidanmu babu mai ilimin addini na wanda na samesa ta dalilin mahaifiyata saboda nayi sauka kuma bakin gwargwado nasan hadissai amma gaba daya zuri’armu babu mai barna irin tawa, ga sani ga barna dan duk yanda nake dakai a danginmu idan har na kwallafawa raina saina bata ka tou fa lallai saina bata maka rayuwa.

 

Ku kasance dani a cikin littafin *KWARATA* domin jin wannan wane irin ubane ita kuma wace irin diya ce ? Kuma a cikin ita da uban waye yafi tantiranci ? Domin dai ni sana’ar da na zabawa kaina itace *KARUWANCI* danni a gani na itace sana’ar da tafi saurin kawo kudi.

 

Babana mahaifi shine mutum na farko daya fara budemin lasisin karuwanci, domin dai a wurin wasan cacarsa yayi kyauta da budurcina, wannan dalili yasa na zabi sana’ar karuwanci, shine ya fara ni kuma naci gaba da kasancewa da wasan domin dai masu iya magana sunce so da yawa kana koyawa mutum abu amma saiya fika kwarewa.

 

Ni babban kamfani ce kamar yanda ake sakawa a jikin kayan masarufi ace ingrediants to nima ina da nawa ingrediants in, kamar yanda company yake sarrafa abubuwa to nima company ce mai zaman kaina.

 

Wannan labari a kiyayi juyashi ta ko wace siga domin yin hakan babban kuskure ne , ba kagoshi nayi ba a haka ta fadamin shi domin ina so ya zama izina ga matan aure,

 

{{{}}} {{{}}} {{{}}} {{{}}} {{{}}} {{{}}}

 

Baba da Allah ka bamu naira goma zamu cika mu siyo magi,

 

Ba tare daya kalleta ba yace me zakuyi da magi ? Cikin in ina tace dama kanzo ne zamu kwada,

 

Naira biyar ya fiddo daga cikin aljihunsa, ya mika mata tare da cewa anshi idan kin samu kudin magin ki cika ki siyomin sigari……

 

Mahaifiyar ta dake tsaye tana daka kulin da za dasuci kwadon tace haba mai gida idan tana da kudin zata tambaye ka ? Itama bai kalleta ba yace wannan matsalarku ce keda ita, keni yi sauri ki kawomin sigarita jiranki nake ya fada tare da shashantar da maganar matar sa.

 

Fa’iza mahaifiyarta ta kirata tare da cewa ina zaki samo kudin ? Bai bari Fa’izar ta bada amsa ba yace samarinta zasu bata ? Ke kike ganin bata da kudi duk yaran nan da kike kallo sun fiki kudi , ke ki hadomin da lemu mai sanyi kafin mai samomin abincin da zanci ta shigo.

 

Fa’iza na kokarin fita daga gidan sukaci karo da Farida a bakin kofa, da yake gidan baya da zaure wanda ke wucewa ta waje ma zai iya hango na cikin gida, gidan kuma babu kaure sai labulen buhu da aka saka a jikin kofar,

 

Babu sahihiyar katanga sai fasashshin buloluwa da aka jera, wanda ko yaro karami ya wuce zai hango na zaune.

 

Fa’iza ganin Farida yasa ta tsaya tare da cewa, Farida da Allah ko kina da kudi ki rantamin na siyowa Baba sigari da lemu, anjima idan nayi awara zan baki, babu sauran kudi a hannuna duk na kasosu kasuwa canjin daya rage kuma nakai zubin adashe kinga lokacin biyan kudin haya ya kusa.

 

Dan murmusawa Farida tayi tare da cewa ai tunda kika ganshi can ya mimmike kamar gawar sababi yau bashi da ko sisi, dan haka ma wallahi bazan shiga gidan ba komawa zanyi.

 

Tun kafin Farida ta rufe bakinta ya fara kwarara mata kira amma tayi kunnen uwar shaggu dashi ta fice abunta.

 

Rungume na fito da magena sanye cikin kayan islamiyata, nasha nikaf dina kayana sun dauki guga sai zabgaga kamshina nake da turarena dana siya na naira hamsin wurin masu siyar da turaren dure.

 

Da sauri Baba ya tashi zaune tare da cewa Mamana barka da fitowa ? Murmushi nayi tare da cewa yawwa Babana barka da hutawa,

 

Yawwa Mamana za’a tafi neman ilimin ? Eh Baba na fada a takaice, mikewa yayi tare da cewa muje in rakaki, wannan shine dabi’ar mahaifina duk inda zan tafi indai yana gida tou fa lallai shine zaiyi rakiya,

 

A kofar gida muka hadu da Fa’iza sigarin ya ansa tare da cewa ki ajiye min lemun in dawo, shigewa tayi gida tare da cewa tom.

 

A tafiye muke yana zukar sigarinsa hankali kwance, Baba wai har yanzu baka samu kudin da zaka siyamin keken ba ? Na tambayeshi, magen hannuna ya ansa tare da cewa machine zan siya miki uwa ta gari.

 

Murmushin farin ciki nayi sannan nace Allah ya bada sa’a Babana , da amin ya ansa tare damin fatan alkairi dan mun iso bakin islamiya, magena na ansa na shige shi kuma yayi gaba.

 

Yau inacikin farin ciki, domin dai idan har Babana yacemin zaimin abu tou fa ko zai mutu sai yayimin, yana min san da duk duniya bayayi wa kowa irinshi, yana kaunata fiye da yanda yake san kanshi, yana so ya ganni a cikin farin ciki saboda ina da sunan mahaifiyarsa.

 

Yau ban wani yi karatu ba, hankalina ya tafi makarantar boko, na kagara gari ya waye dan injewa kawaye na da labari mai dadi zanyi sabon machine, nidai makarantar bokon haka nan nake zuwa dan ba abinda nake ganewa kaina fanko ne , a islamiya kadai Allah ya dafamin nake ganewa, amma a boko bana gane komai. Haka nan nake zuwa na dawo,

 

Koda na dawo gida na kasa boye farin cikina, amma babu damar na fada, uban da ya kasa biyan kudin haya taya zan fada zai siyamin machine ? Dan haka naja bakina nayi shiru, saboda nasan idan suka ganni da machine in zasuyi tunanin kanin Mamana ne ya siya domin shine yake dauke da hidimata.

 

Ina cire kayan islamiya ta na matsawa Inna sai ta bani kudi na siyowa magena kifi, bazan bayar ba shine amsar data bani , tare da hadamin da cewa itama kanta gari taci , saboda haka bataci kifi ba babu wanda zata siyama kifi.

 

Gaskiya Inna bazan iya ba “yar madara gari taci ba, nice sheda saboda kin hana kanki kin cida magen banza, inna ta bani amsa,

 

Tana fadar haka ta shige daki, na dade zaune a wurin ban samu mafita ba dan duk wanda ke gidanmu haushina yakeji kamar ya sakani wuta wannan dalilin yasa bana shiga sabgar kowa,

 

Saida na gaji da zama na tashi a wurin ganin ban samu mafita ba, daki naje na kwantar da “yar jinjirar mage na nabar gidan dan samo mata abinda zataci, gidane babu kayan dadi daga gari sai kanzo inama amfanin talauci, shi kuma Baba ko tsoron Allah bayayi yazo gaban kowa yaci kaza dan zalinci,

 

Amma duk wannan masifar Maman Fa’iza hada wani ciki ina tausayin dan nan da za’a haifa domin dai zai shigo rayuwar bala’e dama ya sani yayi zamansa baizo ba.

 

Haka nayi ta galbaro a cikin anguwa babu tsiyar dana samo, dole na hakura na dawo gida dan lokacin sallar magrib yayi,

 

Har bayan sallar isha’e Baba bai dawo gida ba, tunda naga ya wuce lokacin dawowarsa na sanyawa zuciyata salama tare da ba “yar madara hakuri, tunda ko mun tsaya jiransa bige zai dawo nasan yana can ya shawu iya shawuwa, mata hudu a gida amma yana neman matan waje. Tirrr da wannan hali.

 

Tunani barkatai a zuciyata, ciki kuwa harda tunanin yanda zamu wayi gari ba tare da bango ya fado mana ba, dan gaba daya gidan nan ya rube ga wani irin hadari sai bakin rai yake, lallai wannan ruwan yau idan ya kwace gaskiya akwai matsala.

 

Allah ka tsaremu da rayuwar talauci, rufe idona nayi domin inyi bacci addu’a nayi a fili cewa ya Allah ka tsare bayinka daga mutuwar katanga, kasa in kasance rayayya, in wayi gari cikin farin ciki, Allah ka shirya Babana ya daina abunda yakeyi,

 

Inna ta ansamin da amin, tare da cewa Allah ya tsare gaba daya gidan, ban mata magana ba dan haushinta nakeji ta hanani kudin da zan siyowa mage na kifi, wani busashshen garinta can ta ajiyemin kuma banci ba, nasan idan naje makaranta gobe Amisty zata kawo mana shayi da biredi daga gidansu, shi yasa kafin kekena ya lalace nake saka “yar madara cikin kwandon gaban keken mu tafi tare itama ta maida miyanta.

 

Da tunanin shayin gidansu Amisty nayi bacci, kuma dashi na tashi, tunda na farka naji yanayin garin da sanyi nasan jiya an kwana kwarara ruwa, dan haka tun kafin na sauko daga saman katifa nace Inna halan kin tara ruwan sama ?

 

Na tara, ai jiya banyi bacci ba saida na tabbatar na cika komai nawa da ruwa, cikin damuwa na kara jan yagaggen zanin da nake rufa dashi tare da cewa wallahi bana san wanka da ruwan sama sai jikinka yayi ta wani sulbi kamar ka kama maciji,

 

Banza tayi dani bata sake cemin komai ba, tsoki nayi tare da tashi ina mai mita cewa saidai kawai inyi sallah amma wallahi banyi wanka da ruwan sama, tsakar gida na fito rike da buta, ina maijin kyankyamin shiga bayinmu,

 

Danni tunin duniya nayi sallama dayin fitsari daga tsugune, ko zanyi bayan gida makota nake shiga, wanka kuma dama tsakar gida nake wanke jikina baya da cikina kawai nake wanke wa a cikin bayin, ina watsa ma jikina ruwa tsikar jikina tana tashi.

 

Dan gajeran tsoki nayi tare da daga labilen bayin na shiga, fitsari nayi na fito, a tsakar gida na wanke cinyoyina, nayi alwallah na dawo daki.

 

Tun ina sallah Babana yake kirana tare da cewa uwar masu gida kiyi sauri mun makara naga har 7:30am, bana so Baba yana bina makarantar boko saboda duk kawata daya gani sai ya bita gidansu ni wannan abun yanamin ciwo.

 

Tsaye na ganshi a kofar dakin mu yana daura agogo sai zuba kamshi yake yasha farar shadda sai daukar ido yake, murmushi nayi a zuciyata nace Baba kenan ko ba’aba ciki ba aba kaya,

 

Katsemin zance zuci yayi da cewa maida hankali Mama mu tafi, mikewa nayi ba tare da nayi magana ba naci gaba da shiri, a gaggauce na shirya, tare da shafa “yar madara nace zan rago miki, Babana ya rikemin jakar makaranta muka fito daga gida…….

 

_Gaba daya kaine sile, dan iska domin ni kai zan kira da kwarto, kaine silar rushewar rayuwata_

 

Cikin farin ciki muka fito daga gida, ina fadawa Babana yabi sannu karya bata jikinsa kasancewar ruwan daya kwanta saman kasa,

 

Cikin jin dadi muke tafe muna fira, har mun kusa fita bakin titi ya sheko da gudu tuki na rainin hankali, tuki na gadara, tuki na wulakanci da rashin arziki, tukun da basa kaucewa mutane saidai mutane su kwauce masa, duk lokacin da zai shigo anguwar nan haka yake shigowa idan ya taka mutum ya taka banza, ko dabbobi gareka saidai ka daure abunka amma badai maganar ka sakesu ba.

 

Tunda na hango motar nake cewa Baba dawo ta nan, amma kafin Baba ya hayo inda nake tuni yabi takan ruwan ya wuce shaddar baba ta koma brown, iya wuya raina ya baci kuma nayi alkawari ko zai kasheni tunda har ya tabomin Babana sai naci uwarshi a safiyar nan.

 

Da gudu nabi motar ina watse hannuwa na yanda ake zagi dakkuwa, ina zaginsa, shima Baba biyoni yayi da gudu cikin tashin hankali, yana Mamana dawo, wanda yayi nisa bayajin kira, a kofar gidanshi da yake kiwon dokunan shi anan Baba ya sameni ya rikeni, shi kuma ya fito daga motar da bulala dorina irin wacce ake dukan dokuna da ita.

 

Zagin dana taho inayi shi ya jawo hankalin mutane yasa duk mutane suka fito daga gidajen su, wanda ke waje suka iso wurin da muke dan ganin kwam,

 

Rikeni sosai Babana yayi tare da rufemin baki saboda yasan ban iya zuciya ba, shima abokansa da sauri suka rikeshi tare da cewa *Dikko* karka daketa dan Allah yi hakuri, Babana kuma cewa yakeyi ranka ya dade kayi hakuri don Allah bata san kaine ba,

 

Raina baci yayi ganin kamar mahaifina yana bawa yaron da haifa hakuri, dan haka na bambare hannun Babana daga bakina nace, nasan kaine kuma na zageka, ban kara maganar ba Babana ya wanka min mari.

 

Tunda nake a duniya magana mai daci ko muni Baba baya fadamin ita, yana tattalin rayuwata yana kaunata amma yau saboda wani sakarai ni Babana ya daka,

 

Ina cikin wannan bakin cikin Baba ya bashi hakuri da taimakon abokansa ya hakura suka ja banza suka shiga gidan da yake kiwon dokuna,

 

A raina na dauka alkawari yanda Baba ya dakeni saboda Dikko saina rama dukana a wurinshi…… Hannuna Baba yaja muka taho yana bani hakurin marin da yayi min, wai yayi haka ne saboda Dikko kar yayimin wani abu, saida ya sakani napep sannan ya koma gida,

 

Cikin bacin rai na tafi sch amma tabbas Dikko sai yaci kaniyarshi………

*KWARATA*

 

&

 

*RABI’ATU AMINU MAMMAN DEE*

 

P—— 2

 

Duk sanyi sanyin da akeyi saboda ruwan da aka kwana kwararawa a daren jiya hade da wani irin iska mai dadi amma Baba zufa yake kamar an tsare mai jegon da a saman gadon kara……

 

Cikin tashin hankali ya fara cire kayanshi yana dorawa a saman katanga, sai bakinshi dake motsawa babu wanda yakejin abinda yake fada saidai lokaci bayan lokaci yakan goge zufar data bulbulo daga jikinsa..

 

Ganinshi cikin wannan yanayi ya dagawa kowa hankali, gashi ya fita da farar shadda amma ya dawo da shadda kamar miyan goro,

 

Idan yana cikin yanayin fushi baya so kowa yayi masa magana haka kuma bayasan ganin kowa kusa dashi, mata da “ya “ya suka gane haka shi yasa babu mai shiga sabgarshi, idan yana cikin yanayin damuwa Sultana kadai ke zuwa wurinshi ta bashi hakuri kuma ya sauka saboda soyayyar dake tsakaninshi da ita,

 

Har na isa makaranta tunanin yi hakurin da Babana ya bawa jakin dana manta sunanshi nakeyi, sunanshi ya bacemin kwata kwata na manta sunan da aka kirashi dashi, nidai Allah yayi min jakar kwalwa, saboda ko “yan gidanmu ba dukansu nasan sunansu ba, amma na alakanta abun da yawan da muke dashi, yayin da wasu suke ganin rainin hankali ne……

 

Ko a aji naso na bawa Amisty labari amma na manta sunan wanda zan fada mata, Amisty itace kadai abokiyata duk a ajinmu, abinda kuwa yasa na zabeta tana da kokari sosai kuma idan ana jarabawa tana bani satar amsa,

 

Amisty irin yaran nan ne da idonsu ya waye tun suna cikin zanin jarintaka, bata da labari sai labarin maza, bata da aiki sai kallon B F, duk hotunan da zaka gani a cikin wayar Amisty hotunan tsiraici ne, walau nata walau na wasu, babu mai tarayya da ita saini kadai domin an dade da canfata cewar tana lesbian, nikam babu abinda ya dameni idan dai zata bani shayi nasha a tashi jarabawa ta bani satar amsa idan anyi rubutu nima tayimin a littafina shikenan banda wata damuwa.

 

Lokacin dana shiga aji har malami ya shiga ya fita, ga rubutu nan a saman allo, bana gane sunan subject haka nan kawai na kalli allon nadan basar tare da cewa ashe malam harya fita.

 

Da Eh kusan rabin ajin suka amsamin dan ina da masoya sosai, wasu saboda kyauna suke sona yayin da wasu kuma gashin kaina yake daukar musu hankali, okey shine abinda na fada kamar wata shegiyar baturiya dan itama okey din na dade ina koyonta a bakin Amisty dakel dai na samu ta zauna ram a cikin kaina, idan na fadi okey zakayi tunanin nasha turanci na koshi, amma babu abinda nake ganewa duk duniya sai sallolina biyar da Allah yasa na iyasu saboda nacin zuwa islamiya.

 

Ina zuwa mazauni Amisty tace yau ina kika baro mana Baban namu ? Wata irin faduwar gaba naji dan nasan Babana shima ba karamin tantirin dan iska bane, kodai itama Amisty Baba ya zagaya ne ?

 

Kinyi shiru, Amisty ta katsemin tunani na, maganata daukewa takeyi duk lokacin da ake tambayata abu, ina da nawar magana akan magana karama sai inja lokaci sosai, inayin in ina kadan wannan dalilin yasa ban cika yawan magana ba.

 

Dan gajeren murmushi tayi tare da matsawa, zauna tacemin tare da maida hankalinta akan allo taci gaba da kwafar note. Zama nayi tare da cewa wane malami ne ya shigo ?

 

Malama dai , wace malama ce ? Malamar English ! Me take koyawa na tambayi Amisty, turanci ta fadamin a takaice, murmushi nayi tare da cewa yarinya ai na gane dama dan inji idan zakiyi min karya.

 

Kedai kika sani, ni ciro littafinki na rubuta miki idan kin gama rainin hankalin naki, Amisty ta fada…….. Bude jakata nayi sawon wani lokaci na kasa gano littafin da Amisty tacemin, tun ina dubawa a cikin jaka har na fito da duka littafan banga littafin turanci ba, dan gajeran tsoki nayi tare da cewa Amisty inajin nabar littafin a gida gaskiya.

 

Daukar littafin tayi domin shine a sama, ajiyar zuciya nayi dan nima ta gane wata jar wuya ce , nace da yake jiya nayi karatu na dauka na barshi a gida ne, tou kawai tacemin bata sake magana ba,

 

Haka malamai mata da maza sukaci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta, a bakin get din makaranta na tsaya ina jiran isowar Babana , tabbas nasan zaizo duk inda yake naji yana kusa dani yana zuwa bada jimawa ba.

 

Banfi minti 2 ba Babana ya iso cikin wata irin kafirar mota yanzu ma yasha wanka ya murza wata irin dakekiyar shadda, sai kasaita yakeyi, murmushin jin dadi nayi domin dai Babana ya kankaro min mutunci na idan yayo wanka saboda dan gayu ne na koyi a idon duniya…..

 

Cikin farin ciki na isa jikin motar na bude gidan gaba na wani kame abuna, zugar kawayena ne sukayo kanshi suna gaishe shi kamar yanda suka saba idan yazo daukata,

 

Dan murmusawa kawai yakeyi tare da karkacewa cikin izza ya jawo wasu irin “yan dubu dubu wanda shi kanshi baisan ko nawa bane , Amisty ya mikamawa tare da cewa ku saka kati.

 

Yana basu bai jira godiyar da suke mishi ba yaja mota muka tafi……, ba’a hana alkairi amma inajin bakin cikin abinda yakeyi, yabar gida da yunwa yazo waje yana alkairi, gida bai koshi ba yakai ma na waje banda gori da zagin iyayenmu babu abinda akeyi a cikin anguwa cewa Babanmu yana tsaye akanmu amma duk mu tsinannin Allah ne mu , haka zaisa ayi ta shiga da buhun na, na shinkafa gero masara katin katin na madara sugar da komai na sarrafawa idon duniya sun gani haka zai biyo dare ya kwashe abinshi yaje ya siyar wannan rayuwar zalinci ce, kuma bai sani ba kanshi kawai yake yaudara,

 

Kasa hakuri nayi nace gaskiya Baba ni kadaina zuwa daukoni makaranta daga yau, ba tare daya kalli inda nake ba yace miyasa Mamana ? Kawai banajin dadin abinda kake ne , me nakeyi wanda bai miki dadi ba ? Wannan kudin da kake bayarwa dama gida kabawa su Inna sukaci abinci gidan kowa yunwa ta kamashi babu mai wani sahihin abinda zaici maganar daya ce kullum daga gari sai kanzo.

 

Dariya yayi sosai tare da cewa Mamana kenan, aisu wannan mutane basa godiyar Allah, kima daina biye musu dan kona basu kudin cefane makalewa sukeyi, duk wanda kika gani a cikinsu daga mai tumaki goma sai mai shanaye babu adadi, idan na basu kudi boyewa sukeyi su hana ku abinci, suna can sun sayi dabbobi sunkai kauyika an boye musu, idan kuma kina magana akan abinda akayi ma wani kuma wannan halin shi ake kiran da hassada idan kikaga anyi ma mutum alkairi koya samu wani abu kikaji bakin ciki a zuciyarki shima hassada ne, kuma ita hassada tana cinye kyawawan ayyuka ne kamar yanda wuta takecin karmami, kuma yawan surutu yana sa mutum ya zama sakarai , ki daina hassada kuma bakinki shiru akan fadar wasu maganganu akaina idan kinki ji kuwa jahannama tsaye ko kina san ki shiga wuta ne uwar masu gida ?

 

A , a Babana, amma zan fadawa su Inna gaskiya su daina irin abinda sukeyi zalinci ne, abun tausayi Baba kaji yaran nan suyi ta kukan yunwa wallahi ni har tausayinsu nakeji, kyalesu Mamana kina iya fada musu gaskiya suji haushinki barsu da halinsu…………….Maganarsa ta kare ne a daidai lokacin da muka tsaya wata majalissa.

 

Fita muje, fitowa mukayi daga cikin motar muka tunkari taron dandazon mazan, kallo daya zakayi musu kasan cikakkin “yan tasha ne ko wannensu ya koshi da iskanci,

 

Gaishe su nayi tare da matsawa daga gefe na zauna, kai bata abincin nan taci mu wuce, Babana yayi maganar a daidai lokacin da yake zama,

 

Mikomin abinci akayi a cikin ci ka yada, { take away } gyara zamana nayi tare da juyawa inda babu mutane naci gaba da aiki, daga nan bansan abinda yaci gaba da faruwa ba, saidai naji hayani tayi yawa sosai anata bawa Babana hakuri ana rirrikeshi.

 

Cikin tsananin bacin rai yake cewa da Allah ku sakeni wallahi saina kwakwale mashi idanuwa tunda nayi rantsuwa saina makantashi duk cikar garin katsina babu wanda ya isa ya hanani aikata abinda nayi niyya, da sauri na tashi nayi wurin Babana ina bashi hakuri,

 

Abokin fadan Babana yake cewa, yo kai “ya “yan wasu nawa ka batawa rayuwa, saini kawai dan na kalli diyarka nace babban lambu zaka nunamin rashin kunya, cewa nayi zan shiga ciki ? Yabawa fa kawai nayi…. Sai kawai hankali ya tashi ?

 

Sanin kanka ne duk kasuwar data burgeni saina ci ta hanyar shiga inyi siyayya a cikinta, duk gidan giyar daya burgeni idan na shiga saina sha kwalba biyar karanci kenan idan banda kudi, haka kuma idan naga gidan karuwai zan shiga ne inyi ta ciyayyar abinda ya sawwaka ba tare dana gajiya ba,

 

Ka sani nima nasan haka, tunda saina gama nake ma gwanjon mata, banyi maka shamaki da matana ba haka diyana, kenan yanzu idan nace ka bani aron Sultana mu bata dare haka zakazo bakin kofa kayi tamin babatu ?

 

Da sauri Babana ya rufe idanuwan shi tare da kauda kanshi gefe guda, tunda ni bansan abinda ya assasa fitinar ba, tou miye b’ata dare ? Kila shaye shayen su suke nufi,

 

Jinjina kai Babana yayi tare da cewa kaci sa’a Mamana tana kusa amma zan maida ita gida na dawo na nuna maka karyar barikanci, yana fadar haka yaja hannuna mukayi gaba, har muka iso gida baiyi min magana ba, saida ya tabbatar na shiga gida sannan ya koma,

 

Da sallama na daga buhun kofar gidanmu na shiga, gaba daya gidan suna tsakar gida uwaye da yara, yaran mazansu da matansu sun gurfana gaban wani dakekin mutum bakikkirin da cikinshi kamar ace Allah saukeshi lafiya, ni a tunani na assembly ake musu saida naga Inna na tuna ba makaranta bace.

 

Saida nazo daidai inda suke nayi musu sallama kamar yanda na saba, ina kokarin wuce yace ke zonan, ban kalleshi ba kuma banzo ba haka kuma ban tsaya ba naci gaba da tafiyata na kusa shiga dakinmu naji yace waccan yarinyar ta raina mutane wallahi da nayi niyar yin hakuri amma na fasa sai kun tashi kunbarmin gidana.

 

Hayani ta kwace bakajin maganar wani duk maganar ta koma iri daya yi hakuri , Allah ya taimake ka Allah ya kara arziki ka taimaka dan Allah karka tashemu, kaji hauka akan wannan rubabben gidan suke wani hadashi da Allah yayi hakuri, Allah ma yasa ya tashemu nayi addu’a ta a bayyane,

 

Zainab ce ta tashi taje wurinshi tana wani irin karye karye, sai kace karyar gidan karuwa taga maza, magana tayi mishi babu wanda yaji abinda tace, saidai suka fita da mutumin, ganin tafiyarshi yasa kowa ya tashi yaci gaba da sabgar gabanshi,

 

Babana da Zainab bansan yanda suka kare da mutanen su ba, haka Dikko bansan inda yake ba, dan an dauki wani lokaci banji labarin yazo anguwanmu ba,

 

Kwanaki da dama sun shude, rayuwa tana tafiya babu abinda yayi gaba sai ci baya ake samu, amma ni na samu ci gaba na rayuwa domin dai Babana ya siyamin sabon machine kamar yanda yayi alkawari, a cikin matanshi kuwa maman fa’iza ta samu karuwa ta aihuwa, yanzu mun zama mu hamsin da takwas cas a gidanmu,

 

Zaune nake a kofar dakinmu ina yanke farce na, “yar kyakkyawar magena tana shan madara, Baba ne ya siyomin madarar da yawa nake bata danni yanzu na daina tausayin “yan gidanmu tunda na gane duk munafikai ne, Kuma Babana ina gani duk safiya yana basu kudi amma bansan ko nawa bane,

 

Kadangare ne ya fado daga saman bango fef, yana ganin mage ya ruga, ita kuma daina shan madarar tayi tabi kadangaren da gudu, nima binta nayi ina kiran “yar madara’ dan bana so tana cin kwarika, kadangare ya rugawa mage, ni kuma nabi magen haka muka fita a guje mu dukanmu muna gudu a tsakar santa….

 

Shima a guje ya shigo kamar yanda ya saba, ganin yanda mutane ke rike yaransu, masu tumaki na kamawa hakan ya tabbatar min dashi dinne ya sake dawowa,

 

Nima kokarin kama “yar madara nakeyi, amma kafin in isa wurinta tuni dan iskan yabi ta kanta da mota ya wuce, jininta yayi tsartuwa a saman fuskata, yana wucewa na ruga na durkusa wurin magen, saida tayi miyau………. Sannan ta daina motsi, wata irin ashariya na babba tare da kurma wani irin ihu dan naji bakin cikin takata da mota da akayi.

 

Cikin kuka na nufi inda yake, dama ina jiran zuwan shi saboda marin da Babana yayimin ta dalilinshi, shima din jirana yakeyi saboda zagin da nayi mashi waccan ranar, kowa yana jiran kowa,

 

Bayan yayi parking ya fito ya zauna saman bayan mota, yauma bulalace a hannunshi yana wasa da ita, sai wani cin cingom yake sai kace karuwa…

 

Abokan da yazo dasu waccan ranar yauma sune ya dawo dasu, mutum biyu tsaye a gefen damarshi biyu a haggunshi daya kuma tsaye ta gabanshi ya dade da bakin glashi,

 

Lafiyayen kato ne mai kirar “yan dambe, singileti ce a jikinshi sai wani maski maski yakeyi kamar anyi mishi wanka da mai, dan nesa dasu na tsaya tare da cewa a cikinku waye yake tuka motar nan ? Na nuna motar da hannuna,

 

Nine nan, mai kirar “yan dambe ya bani amsa, sannan yaci gaba da cewa ko wani abu ya faru ne ? Saida na kalleshi sama da kasa sannan nace da Allah mi yasa ka takamin mage ? Nayi maganar cikin sanyin murya, bashi ne ba nine na taka ta, kema idan kika tsaya a hanya gobe haka zanbi ta kanki in wuce kinji ko an mata, duk shi Dikko yayi maganar.

 

Mai kirar “yan dambe ya anshi maganar cewa, ubangida na yanajin dadi yayi da yaga yana wulakanta talaka irinki, yana farin ciki idan ya zauna daga nan muka fara watso kayanku daga cikin kangon can, da nayi niyar murde miki wuya ki mutu , mutuwa irin ta beraye a ranar da kika wa mai gida rashin kunya, abu daya yasa ban kasheki ba kasancewar ke ba kowa bace,

 

Murmushi yayi tare da cewa ta hanya mafi sauki za’ayi miki hukunci, juya kisha kallo, juyawa nayi a hankali dan inga abinda yake so na gani, babu gidanmu tuni wurin ya koma fili, lokacin da na juyo babu su Dikko babu alamarsu dan tuni sun jima da tafiya daga wurin.

 

Salati nayi tare da tunkarar inda “yan gidanmu suke tsaye cirko cirko domin babu abinda aka bari suka fitar dashi komai an danneshi cikin kasa, sai motaci dake ta kwashe kasar wurin,

 

Ina zuwa kusa da Inna da zumar tambayarta abinda ya faru ta rufeni da duka tare da cewa miya hadaki da Dikko kin dauko mana fitina kin jawo mana masifa Allah kadai yasan karshen wannan masifar.

 

Cacai cacai kowa hayani yakemin a saman kai babu damar a dakeni Babana yaba mace rasid’i, ke kuma diyar gida kimin magana kijawa uwarki masifa, dan haka abinda kawai suke cewa miya hadani da *DIKKO ?* …………….

 

 

 

 

Saida na gama kallesu daya bayan daya sannan nayi murmushin takaici da gefen bakina, kallon inda gawar “yar madara take na kalla wani makoko yazo ya tsamin a makoshi wanda ko yawun zan hadiye sai naji kamar lumfashi na zai dauke.

 

Dikko………………….! Saida na jinjina sunan a zuciyata da kuma bakina, sannan na kalli dandazon taron ahalin gidanmu, nu na su nayi da dan yatsa manuni, sannan na dafa daidai kirjina da hannun haggu na , zanyi magana sai kuma maganar ta kasa fitowa dan bana iya magana a cikin yanayin bacin rai..

 

Wuri na samu na zauna ina ta sauke ajiyar zuciya, tsinuwa da zagi da Allah ya isa bansan iyakar adadin dozinan da suka saukemin ba, zagin ne dai kawai amma nasan bazan daku ba,

 

Har yanzu babu wanda nayi ma magana kuma babu wanda na sake kallo, zama nayi na sauke kaina kasa, yayin da wasu suka gaji da tsayuwa suka durkusa wasu kuma suka bazama neman gida, dan su zasu nemo shi dan ko sun tsaya jiran Baba ko yazo bazaiyi wani abu ba,

 

Bayan sun zauna ne sukaci gaba da tattauna maganar abinda Dikko yayi, ashe tun waccan ranar zagin da nayi masa ranar da zamu tafi makaranta tare da Babana bayan an bashi hakuri ashe baiyi hakuri ba.

 

Da zai jira har na dawo daga makaranta ya takeni da mota ya wuce abinshi, tou bayan ya fito daga gidan da yake kiwon dokuna yaga Babana ya fito daga gidanmu,

 

Shi Dikko mugune na gaskiya da gaskiya, duk duniya babu abinda ya raina yake kyankyami irin talaka, Dikko baya dariya haka kuma baya murmushi kullum fuskar nan tashi a hade take kamar hadarin tsakar dare,

 

Bakya ganin dariyar shi kwata kwata, idan kuwa har Dikko yayi murmushi tou tabbas yaga cuta, idan kuma yayi dariya tou tabbas ku idan kuka ga abun sai kunyi kuka saboda tsabar tausayi. Danshi sai yaga mugunta yake dariya…..

 

Bayan Babana ya wuce, Dikko ya kalli gidan ya sake masa kallo babu abinda baya gani na gidan daga nan waje inda yake tsaye,

 

Kallon rainin hankali yayi ma gidan tare da bata fuska ya juyar da kai ya kalli daya daga cikin wanda suka zo tare sannan ya kalli agogon hannushi yace waye shi…. Ya nuna Babana da gidanmu…

 

Bai tsaya yin magana ba ya bazama cikin anguwa, a cikin kankanin lokaci yaje ya samowa Dikko duk wasu bayanai daya kamata akanmu da rayuwarmu,

 

Jinjina kai Dikko yayi bayan yaji komai tare da cewa karta mutu, amma barsu na jikatasu zata gane Dikko ba sa’ar ubanta bane daga wannan rana tsoron Dikko zai shiga zuciyarta maza a nemo min mai gidan daya basu hayar gidan, dan gajeren tsoki yayi tare da cewa talaka banza a banza, za’a nuna mata su kudi jigo ne masu nuna ishashshen iko. Daga wannan rana zata gane mai kudi ba’ayi masa hawan kasa,

 

Cikin anguwa ya sake komawa dan binciken mai gidan da muke haya, aka fada musu anguwar da yake zama, da kuma wurin da yake zama dan kasuwancin shi,

 

Bayan sun gama daukar duk bayanin da suke bukata, sukayi tafiyarsu, ashe Dikko gidan da muke haya yaje ya siya, kuma mai gidan da muke haya yace wa Dikko Babana baya biyan kudin haya tuni yayi niyar tashinmu sai wata yayata take biyanshi kudin haya daga cikin kaddarar rayuwarta,

 

Tun wannan ranar Dikko ya biya kudin gidanmu, bayan ya biya tafiya ta kamashi, saida yayi wata biyu baya nan, shine fa yana dawowa babu notice kawai yasa aka rushe gidan……

 

Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama jin duk bayanan su, yanzu ita Zainab zuwa takeyi anayin iskanci da ita kenan ? Amma ta bata wayanta,

 

Yawwa an samo gida ku taso mu tafi, gaba daya sowar farin ciki suka dauka tare da mikewa suna cewa a ina gidan yake ? Gidan Alhaji Sabo ne yace mu zauna dan yaji abinda ya faru damu kuma ya tausaya mana sosai, amma duk watan duniya yace zamu rika biyan dubu goma,

 

Eh hakan yayi babu wani damuwa, ku tashi mu tafi, yeay yara da manya sukayi ta shewa muka tafi dukanmu yayin da wasu ke cewa dan uwar Dikko yazo ya anshi wannan idan ya isa.

 

Haka muka koma gidan Alhaji Sabo dake makotan gidanmu da Dikko ya siya, bamu da komai haka muka shiga gidan, kowa daga ita sai kayan jikinta,

 

Nidai har yanzu banyi magana ba, abun duniya duk ya dameni kuma babu wanda yabi ta kaina ko Inna bata sake shiga sabgata ba sunyi ayari wuri daya ana ta shawarar yanda za’ayi a samo kudin Alhaji a bashi dan ya basu daga yau zuwa jibi su kawo mishi kudin shi.

 

Har safiya basu samu mafita ba, haka kuma Babana bai kwana gida ba, bansan yanda akayi ba suka shiga suka fita suka bawa Alhaji kudin hayarshi ba,

 

Kwanan mu hudu a sabon gida Baba yazo gidan, bai tambayi yanda akayi muka dawo ba haka kuma baibi takan kowa ba zance ya akayi aka biya kudin haya ba, haka kuma baiyi ma kowa magana ba saini daya,

 

Uwar masu gida lafiyar ki qalau kuwa ? Lafiya qalau Baba na amsa masa, yace kwana biyu bakije makaranta ba har kawarki ta tambayeni ko lafiya ? Nace mata lafiya qalau gaskiya, kinsan nima bana nan naje Abuja,

 

Allah sarki na fada, tou miya hanaki zuwa makaranta ne ? Ya sake tambaya na, saida na tattara bakina sannan nace Baba ai an rusa gidan, komai namu kuma an tattarashi an kwashe anje an zubar, banda kayan makaranta da littafai,

 

Wayyo Allah Mamana, taso muje waje muyi magana, mikewa nayi nabi bayanshi, yana gaba ina binshi har muka fita kofar gida,

 

Wuri muka samu muka zauna, muna zama Babana yace in fada masa dame dame nake bukata ? Nace masa ko kayan sakawa dukanmu gidan bamu da, kowa kala daya yake dashi, amma makota sun dan tattara mana kaya, murmushi yayi tare da cewa wallahi Uwar masu gida bata saka kwancen kaya, na dawo garin nan jiya da kudi fiye da tunaninki Mamana,

 

Tunda naji abinda ya faru tsakanin shadda da yadi da boyal saida na siya kusan kala arba’in, takalmi da agoguna da hulana duk babu abinda ban siya ba, kayan suna can na kai dinki,

 

Tsare Babana nayi da ido, a zuciyata kuma ina ganin rashin adalci irin na Baba, amma Baba bakada imani iyalinka na nan suna neman abinda zasuci karma ayi maganar wurin zama amma kai har lokacin siyan kaya kake yi Baba……? Duk a zuciyata nake wannan tunanin.

 

Mamana, ya kira suna na, kallonshi nayi ba tare dana ansa ba, tunanin me kikeyi ? Bayan gani a duniya ! Idan har ina nan a raye baki da matsala nayi miki alkawari zan kula dake zan kange miki duk wani bakin ciki da damuwa, idan dan maganar kayan makaranta ne da littafai zan siyo miki komai ma ki daina damuwa, zan miki duk abinda kike so dan kiyi farin ciki Mamana , wallahi da ina da iko ko kuda da sauro da ban barsu sunzo wurinki ba, haka nake alfahari da aihuwarki farar mace lantarkin ciki gida, da nasan zan haifeki wallahi da ban tara wannan yame yamen “ya “yan ba,

 

A ranar da aka aifeki a ranar naci makudan kudade a wurin wasan caca , tun daga ranar na gane ke mai sa’a ce, wannan dalilin yasa nasa miki sunan mahaifiyata ya karasa maganar yana murmushi, sannan yaci gaba da cewa zuwanki yasa talauci ya guji rayuwata, shi yasa na tattara miki buri da yawa domin nasan kedin mai arziki ce.

 

Yana fadar haka yace tashi muje, tashi nayi nabishi, yauma cikin wata zakanyar mota muka shiga, ta gaji da haduwa sai sanyin A C ke tashi ga kamshi mai dadin shaka, Babana fa dan gayu ne gashi da wayewa kuma yana da kalar burgewa amma babu halin kirki.

 

A daren nan saida Babana ya tabbatar duk abinda zan bukata ya siyamin, sannan muka wuce wurin dinki, tela ya aunani Baba ya biya kudi muka dawo gida,

 

Tunda muka dawo matarshi Mariya ta tada hankali ta fara zagina tare da aibatani, bata san Babana yana tare dani ba da batamin ba, yana shigowa cikin gida yace mata ta tafi ya saketa, maimakon Mariya tayi farin cikin sakin kawai sai ta kama kuka, dani Babana ke aure ya sakeni wallahi sai nayi farin ciki sosai na rabu da rayuwar wahala,

 

Amma Mariya saita durkushe tana bashi hakuri, wallahi ko sauraren ta baiyi ba, anyi an gama domin Babana idan ya saki mace ya gama da ita har abadan duniya baya maimaita mace idan har ya riga ya rabu da ita, dan yace ko sitira sawa daya yake mata mace kadai yake ma maimaici a rayuwar shi, shi yasa idan har ya saki yake mantawa da babinta a rayuwarshi.

 

Fita yayi yabar gidan, Mariya kuwa kuka takeyi kamar zata mutu, wallahi ta bani tausayi sosai dandai ba hurumi na bane dana bashi hakuri kuma tabbas nasan zai hakura amma ba ruwana tunda ba hurumi na bane, kuma nasan tsakanin gobe da jibi tabbas saiya karo aure…….

 

Zaune muke lafiya a gidanmu, rayuwar dai tana nan kamar kullum kowa shi yake cida kanshi, gaba gaba dai yayuna sun fara harkar barikancin su har a cikin anguwa, saboda Baba baya tsawa tawa dan yaga dama ma ya kwana biyar ko sati baya gida,

 

Bayan sakin Mariya da sati daya Baba ya auro wata “yar fiririyar yarinya wacce zata tsaya iyakar sa’ata, kankanuwar yarinya itama mai zubin karuwai, wankan tarwada ce kallo daya zakayi mata kasan ta gaji da fekewa da bari…

 

Idan kayi mata magana saita wani yamutsa fuska sannan zata daga idonta dakel tayi maka magana, kai nidai sam tsarinta bai burgeni ba haka kuma bata wani shiga raina ba, dan bata da kunya ko ta misali, caccakakkar “yar iska ce , tasha iskanci ta koshi, amma anyaBaba auro yarinyar nan yayi kuwa ?

 

Rayuwata nakeyi cikin farin ciki, bani da wata damuwa shi yasa bana gane abinda kowa yake ciki a gidanmu, idan na fito daga dakinmu sai dare nake komawa saboda Innata bata san gani na, dan kishiyoyi sun tisota a gaba da habaici saboda ni, Babana yana kula dani sosai baya barina shiga damuwa, ina zuwa makarantar boko da islamiya , amma boko gugar kaya kawai nake inje, islamiya kadai nake da fahimta.

 

Tafiye nake a cikin nikaf ina, sauri kawai nake na isa gida saboda hadarin daya taso, sai wani irin iska akeyi mai hade da kasa, walkiya da cidar hadari duk sun karade sararin samani, tunda na biyo santar nan banci karo da kowa ba har na iso inda nake tunanin nan ne gidanmu,

 

Kamar yanda nayi hasashe haka na yanki hanya domin shiga gida dan bana ganin gabana saboda kasar data shigar min ido, na daga kafata in taka sumintin kofar gidan naji wayam, kara mika kafata nayi dan a tunani na ban tako daidai ba, kamar yanda naji daga farko yanzu ma haka naji,

 

Da sauri na bude idona dan inga lafiya ? Filin wurin kawai na gani kamar ba’a taba gini a wurin ba, salati nayi na sanar da ubangijina to ina “yan gidanmu suka tafi ?

 

Makota na shiga na tambayi inda “yan gidanmu suke, aka cemin Alhaji Sabo ya canza mana gida kafin wata ya kare mu tashi, tambayar dalilin tashin da rusa gidan da akayi nayi amsar da aka bani itace, *Dikko* ne ya siyi gidan amma wannan karon anyi ma kowa uziri ya fita da kayanshi.

 

Bance komai ba saidai na sake tambayarta ina gidan yake ? Kwatanci tamin gida na like da gidan da aka rushe nan muka koma, ban sake cewa uffan ba na nufi gidan.

 

Daki daya ne tak a gidan saboda haka kowa yana zaune cikin barandar dake tsakar gidan, sallama nayi amma babu wanda ya ansa min sallamar har Innarmu, nima ban sake sallamar ba na samu wuri na zauna tare da jan bakina na kameshi,

 

Dukanmu a tsakar gida muka kwana yayin da wasu suka kwana a zaure, babban gida ne sosai amma daki daya ne ya gina shima ajiye ajiye yake a cikinsa, gari na wayewa na shirya na tafi makarantar boko, Baba bayanan sun tafi gasar caca, dan bai fadawa kowa sunan garin daya tafi ba, ni kadai yayiwa bankwana.

 

A makaranta Amisty ta lura ina cikin damuwa, dan haka ta tambayeni abinda ya dameni, ban fada mata ba, saidai nace mata da Allah waye Dikko a garin nan ?

 

Hmm su Amisty idon duniya saida tayi masa wani irin kirari sannan tace miya hadaki dashi ne ? Nace mata kawai dai labarinsa nakeji shi yasa nake san sanin koshi din waye.

 

Abinda Amisty tacemin shine, yanda kike takama Babanki yana masifar sanki da kaunarki dan dole wannan misalin da kanki zanyi shi idan ba haka nayi miki ba tou fa lallai nasan baza ki gane ba,

 

Dikko d’a daya tak a wurin mahaifin shi, yana da yayu mata sosai saboda suna da yawa gidansu suma, amma basu kai gidanku yawa ba, abinda yasa kuwa aka tara yawa a gidansu saboda san haihuwar d’a namiji da basu samu ba,

 

Akan Dikko ya samu namiji daga shi kuma har zuwa yau din nan ba’a sake haihuwar namiji ba, Dikko gaskiya yana da kirki kuma shi ba dan iska bane amma gaskiya baya san raini,

 

Yana da alkairi sosai amma shi baya dariya haka kuma baya murmushi, ni bayan wannan bansan komai ba haka dai kawai naji ana fada a gari,

 

Gyara zama nayi tare da tambayarta shi kuma waye ubanshi ? Murmushi Amisty tayi sannan tace da Allah karki dauki ne wake da shinkafa mana, Dikkon ne a katsina baki san waye ubanshi ba ? Wallahi ban sani ba, na bata amsa, tashi tayi ta barni a wurin dan ita a tunanin na sani jan zance ne.

 

Har muka tashi makaranta Amisty bata fadamin ko waye uban Dikko ba, ni kuma ana tashi makaranta ban tsaya komai ba na nufi gida tunda nasan Babana baya nan,

 

Tunda napep ta ijiyeni, na hango kofar gidanmu daddabe da mutane, Dikko yana zaune a saman gaban mota ya kwantar da bayanshi saman gilas din motar kafarshi daya saman daya, ya tallabo kanshi da hannayen shi, kamar kullum yauma cingom yake ci, kananan kayane jikinshi ya dode da gilashi mai saukin duhu.

 

“Yan gidanmu sun daddabe shi suna bashi hakuri amma ko inda suke bai kalla ba bare su sa a ransu zaiyi magana, sai waso mana kaya akeyi daga cikin gida, yayin da “yan zaginshi ke cewa ai tunda har kuka tabo mai gida a garin nan sai kun rasa gidan zama, wannan dinma ya siyeshi idan kunyi zuciya ku gina naku talakawan banza kuna jayayya da masu katsinar gaba daya,

 

Inda jakar islamiyata take naje na duka na dauka, na koma gefe nayi tsayuwata tunda ko nayi magana babu wanda zaimin magana kowa haushi nake bashi,

 

Wani dattijo ne shima makoci ne , yace ni inje in bawa Dikko hakuri duk saboda abinda nayi masa yake ta wannan saye sayen gidanje, dan gajeren murmushi nayi tare da cewa Baba kenan aini wancan dan iska nafi karfinshi wallahi baikai matsayin da zan kalleshi ba bare har na bawa banza hakuri, idan kuma har ka tilasta naje to lallai ina zuwa zan jawo dan iska ya fado kasa,

 

Lallashi na dattijon nan ya farayi akan lallai sai naje na bawa Dikko hakuri, a lokacin har an gama fito da komai namu an fara rushe gidan.

 

 

Ya uzura min sosai akan naje na bawa Dikko hakuri dan haka na tunkari wurin kai tsaye zuciyana tana min tsake tsaken mugunta iri daban daban.

 

Cike da bacin rai na isa wurin, kamar yanda na fadawa tsohon nan zanyi haka kuwa nayi, dan ina zuwa na kamo kafar Dikko da zumar na fadar dashi kasa ya karya kashin baya,

 

Amma ina, dan ina riko kafar shi daya, ya tattakura yakai min halbi da dayan kafar da ban rike ba, hanci baya raina duka lokaci guda jini ya ballemin kamar an yanka kosashshiyar kaza,

 

Yana halbina ya diro daga saman motar shima ashe yayo dagon muguntar shi yana neman inda zan sauketa ya huta, ganin jini yana bimin baki har yana digowa kasa yasa hankalina ya tashi,

 

Sosai nayo kan Dikko, yaranshi suna kokarin rikeni yace su barni yanzu zai koyamin hankali yanda idan na ganshi da gudu zan canja hanya.

 

Daga nesa mutane suka fara bashi hakuri dan babu wanda ya isa yazo kusa dashi, babu wanda ya kalla bare kayi tunanin ko zai saurare ka, kusa dani ya matso sosai, yasa hannuwan sa biyu ya riko min fuska, sai yanzu nakejin halbin da yayi min yake ratsa duk ilahirin cikin kokon kaina, gaba daya jikina ya saki ya koma kamar ba nawa ba,

 

Sama sama nake ganin Dikko har yanzu bai daina cin cingom in da yakeci ba, saida yayi min kyakkyawan riko sannan ya cire gilashin dake fuskarshi ya kalleni ido cikin ido sannan yayi dan kyakkyawan murmushi, wanda ke nuni da mugunta ta tashi…

 

Sai mun sake had’ewa an mata…yana fadin haka ya k’uma min kanshi da nawa wuri daya wanda haka yayi sanadiyyar daukewar gani na gaba, amma har zuwa wani lokaci goshina da nashi yana hade wuri daya,

 

Bai sakeni ba saida ya tabbatar na tafi suma, dan tabe baki yayi tare da dage girarsa ta dama sannan ya sakeni ya zura hannuwansa cikin aljihu ya nufi motarsa dashi da tawagarsa suka bar anguwarmu.

 

Ni kuma na fadi kasa somammiya, Allah sarki dan uwa mai dadi duk “yan gidanmu basu ji dadin abinda Dikko yayi min ba, sun tausayamin iyakar tausayi gashi babu mai kwandalar da za’a kaini asibiti, saidai aka samo kankara aka rika dandan na min a goshina tunda habo ne nayi,

 

Abokin Babanmu shi yaji labarin abinda ya faru damu, yana da wani gida na Alhaji Sabo da aka saka a caca ya ciwo gidan, shine ya bada makullin gidan aka kawo mana yace mu bude mu shiga,

 

Daukata sukayi suka shiga hadani tare da bani kulawa ta musamman, amma duk abinnan saida nayi sati daya kafin na dawk daidai,

 

Babana har yanzu bai dawo ba kuma bamuji labarinsa ba ko ta waya, kuma har yanzu ban yadda na sake fita ba koda zaure saboda zuwa wannan lokacin bana san ganin Dikko ko inuwarsa,

 

Gaba daya na jingine islamiya da wata bokon banza, daga tsakar gida sai daki, idan ina tsakar gida naji karar mota ma daki nake komawa,

 

Satinmu ukku a gidan abokin Babanmu Baba baizo ba, kuma baiyo aike ba, shima kuma wannan gida da muke ciki Dikko ya siyeshi, ba’a gidan kadai ya tsaya ba duk gidan da yasan na hayane a anguwar saida Dikko ya sayeshi duk sun zama mallakinsa, tashin hankali da damuwa kowa ya shiga,

 

Saida abokin Baba yazo yake fada mana cewa an kama Babanmu yana can an kulleshi saboda ya ranci miliyan biyar din wani abokinsu bai bashi kudin ba, shine ya kaishi wurin hukuma suka tsareshi,

 

Kowa ya jinjina miliyan biyar saboda babu wanda yasan abinda Baba yayi da kudin nan, shiba gida ba, ba mota ba ba fili ba, haka kawai ya saka kanshi rikicin duniya.

 

Inna na kalla data zabga tagumi tana d’igar da hawaye, cikin yanayin tausayi nace Inna wai da zaki auri Babana bakuyi binciken halinsa ba kafin auren ku? Banza Inna tayi dani bata bani amsa ba, tsoki nayi tare daci gaba da cewa muma mata muna da matsala yayin da muka hangi tilin dukiya da babbar mota hankalinmu, ganinmu da kuma tunanin mu sukan b’ace , idan aka samu kwadayayyar zuciya sai kuma takai mutum ta baroshi, kamar dai ku duk zuciyoyi ne da kwadayin duniya suka kawo ku nan suka barku, kiyi ta addu’a kema Allah sa ya sakeki ki huta. Kunga mutum da arziki bakusan taya yai ya samu abinsa ba,

 

Inna dai bata tankamin ba, muka fito domin “yan gidanmu sunce muzo mu tafi wata primary school dake bayan gidanmu mu kwana tunda dare yayi kafin mu samu gidan zama, duk muna tsaye a tsakar gida dan Dikko yace wallahi idan muka kara cikakkun mintina biyar saiya kunna mana wuta,

 

Cikin kyarmar jiki nacewa Maman Fa’iza “yan uwan Babanmu basu da kirki kowa ya zura masa ido dashi da iyalanshi sai wuta mukesha babu mai roka mana sassabci a rayuwarmu, ansa daya ta bani itace, ai babu ubanda yasa shi aure auren kuma basune suka sa duk yayi cikunnan ku aka haifo ku duniyar ba.

 

Haka tayi ta surutai marasa dadi na bad’ala da rashin kamun kai har muka fita gidan muka tafi makarantar, koda muka fito motoci sunkai biyar masu zafi tsadaddu masu burgewa da daukar hankali, an haska fitilinsu duka, amma yau babu Dikko dan naji suna magana cewa mai gidansu yayi tafiya baya k’asa amma ya umurcesu da su tabbatar bamu kwana gidan nan ba, idan mun fita mun huta idan bamu fita ba a kunnawa gidan wuta, wannan shine sakon da Dikko ya aiko dashi,

 

A makarantar mukaci gaba da zama cikin azuzuwa, { Classes } idan dalibai sunzo zamu fita waje idan sun gama suka tafi zamu koma mu zauna, ni na gaji na fadawa matan Babana waisu basu da gidan iyayensu ne ? Wannan wulakanci ai ya isa haka, kowa ta tafi gidan ubanta ta huta mana, ai fa yak’ai yak’ai kamar zamu cinyeni d’anyata saboda tsabar masifa, dole naja d’an bawan Allahna nayi shiru.

 

Satinmu daya kullum sai an koremu kamar karnuka kuma kullum bama tafiya sai mun dawo, da safe kuma su tura yaransu su shiga bara cikin gari, rayuwa dai wulakantattar rayuwa mafi muni da k’ask’anci, Babana baya da adalci kuma baya da imani hakika zai tadda Allah, domin wannan zalincin yayi yawa.

 

Ranar da muka cika kwana takwas aka koremu da karfin bala’e mukabar makarantar malaman suka kara da cewa gwamnati bamu ta ginawa makarantar nan ba muje can musan inda zamu zauna amma ba makaranta ba, suka kara jaddada mana idan suka sake ganin wata wallahi sai sun kaita an kulleta wurin “yan sanda,

 

Nanfa Allah ya bamu sa’a cikin malaman wani ya ji kanmu ya bamu kyautar fili dan mun fada musu matsalar mu, shi kuma ya tausaya mana, saifa suka fara yahani akan fili yayin da kowa ke cewa saidai a siyar da filin a raba kudin aba kowa,

 

Yayin da wasu ke cewa ayi hakuri a zauna, masu cewa ayi hakuri a zauna sun rinjayi wanda keso asiyar, dan haka dole suka hakura, muka dinguma zuwa fili, bayan munje akayi tamalmala ta malmala aka siyo buhunna dasu aka zagaye gidan ,

 

Wannan fili dai bazai ansu a wurin Dikko ba, nima ganin mun samu mazauni hankalina ya komawa tunanin Babana,

 

{{{}}} {{{}}}

 

Bayan wasu kwanaki,

Rayuwata nakeyi cikin jin dadi, nidai Allah ya taimakeni bana bara saboda kanin inna yana kawo mana dauki da abinci, kunsan idan mace ta koshi tou fa lallai bata da aiki sai iskanci da rashin kunya, toni dana koshi nawa iskancin Dikko kadai yake nema ido rufe, kullum ina bisa hanyar zuwa tsohuwar anguwar mu, haka zan hau napep kamar duka kenan saina tabbatar mun kusa zuwa sai in dire abuna, wasu basajin fita ta wasu kuma suna gani idan suka bini basu kamoni ba saidai suyi min Allah ya isa, nima na fara dauko kadan daga cikin dabi’un Babana.

 

Yauma direwa nayi, da gudu nasha lungu na shige wani gida, zaure na tsaya saida na huta sannan na tattaro natsuwa na shiga ciki da sallama,

 

Cikin sakin fuska matar ta ansa min, wuri na samu kasa na zauna ina gaisheta, ta ansa lafiya lau, shiru nayi zuwa wani lokaci nace mata hajiya dan Allah kin iya rubutun wasika ? Murmushi tayi sannan tace niko na iya rubutun wasika, nace tou don Allah kitaima min mijin Yayata ne suka rabu shine yayi mata shegen duka ya raba mata kai da tab’arya tana can asibiti rai hannun Allah, kuma sai rubutun zagi yakeyi yana aikowa gidanmu, shine aka rubutomin ansa na maida mishi kuma takardar ta fadi, ni kuma idan na rubuta sabuwa zai gane rubutu na ne , amma ki taimakamin don Allah, ni na karanta wasikar kuma zan iya fada miki yanda take kiyimin rubutun nakai mishi don Allah……..!

 

Ba tare da tunanin komai ba tace tou, daki ta shiga ta dauko jakar makaranta, da gani ta yara ce , a ciki ta dauko biro da paper tace min bismillah, duk ba tare da tayi wani dogon binkice ba ko yin nazarin yin hakan me zai haifar daga baya.

 

Ni ko dadi naji sosai a zuciyata , tunda ni bazan iya rubuta uwar komai ba, amma nayi farin ciki sosai domin dai yau zanci uwar Dikko kafin in fara kashe dawanki dan iska. Bayani na farayi ta fara rubutawa,

 

_Ka fita daga rayuwarmu yayin da ni kuma yanzun nakejin farin cikin shiga taka rayuwar, salon ka yana da matukar burgewa dan marasa tarbiyya, taya zaka fara rashin tarbiyya kuma ka gaji da sauri haka ? Ko kudin sayen gidajen ya kare ne ? To tunda kudin sayen gidaje ya kare nasan zakayi kokari ka samo kudin sayen dokuna, ina mai farin cikin sanar dakai daga yanzu d’innan har zuwa ranar da zaka bar zaman anguwar nan farin ciki zai bar zuciyarka, kuma zaman anguwar nan zai haramta a gareka kamar yanda ka haramta mana zama a cikinta, zanyi ta kashe dokunan ka harsai ciwon zuciya ya kama ka idan ka fasa kai ba d’an Babanka bane…………_

 

_Sultana ce, Allah ya bawa mai rabo sa’a, idan kaje Islamiya kace amin……_

 

Mikomin tayi bayan ta kammala rubutawa, godiya nayi mata sannan na fita, nayi tafiya mai dan nisa ina kokarin bi hanyar da zata sadani da tsohuwar anguwarmu na hango Dikko ya sauko daga saman doki……,

 

Jar riga ce a jikinshi amma ba irin ja d’innan ba ja mai kyan kallo, sai jar hula akanshi irin wacce matasa ke gayu da ita, fesin cap, bakin wando ya saka wanda suke kira 3quater da rufaffin takalmi, sai bulalar da ake dukan doki a hannunshi, daga gani dai daga kilisa suka dawo,

 

A fili nace shege mai kama da mata, cin cigom kamar tsohuwar karuwa, duk’awa yayi k’asa ya d’auki wani abu wanda ban iya ganewa ba, bayan ya d’auka ya koma saman dokin yayi mishi diddige tare da tsuke bakinshi irin yanda ake kora doki yayi gaba,

 

Da gudu ya wuce ya wani d’an jirge saman dokin yayi kyau sosai bazan mishi haddasa ba gaskiya, ci gaba nayi da tafiya, kafin in ida isa wurin kuma naga ya wuce da gudu cikin mota kura tabi bayan motar sosai kamar guguwa ta taso.

 

Hamdala nayi domin na samu damar farko da zan kashe doki d’aya daga cikin dawakan Dikko, saboda nasan wata mugunta d’aya da ake ma doki, ba’a ba doki ruwa idan aka dawo dashi daga yawo, idan aka bashi ruwa a wannan lokacin tou cikinshi k’ullewa yakeyi ya mutu.

 

Nikaf ina na ciro na saka tare da gyara tafiyata na tun kari gidan kai tsaye, a kofar get in gidan nayi ma mai gadin gidan sallama, ya ansa cikin sakin fuska, nace mishi dama wani mutum ne da jajayen kaya a jikinshi yace in turo mishi kai yana can yana jiranka….. Na nuna mishi hanyar da Dikko ya wuce da hannuna ,

 

Cikin sauri ya wuceni ya tafi, yana wucewa na shiga cikin gidan, doki d’aya ne kad’ai wato shine dokin da Dikko ya dawo dashi, an d’aureshi a gefe kuma an cika bokiti da ruwa an ajiye shi kuma dokin yana ta bubbud’a hanci yana maida numfashi,

 

Da sauri na kinkimi bokitin ruwan nakai gaban dokin na ajiye, aiko ina ajiyewa ya duk’ar da kanshi yaci gaba dashan ruwa, a daidai lokacin da mai gadi ya shigo dan yabi hanya baiga Dikko ba ya dawo,

 

Kay kay kay ba’a bashi ruwa yana k’ok’arin isa dan d’auke ruwan na tareshi tare da cewa anshi yace ka ajiye mishi wannan takardar idan yazo da daddare zai karb’a, bai tsaya ansar takardar ba kuma baimin magana ba ya wuce,

 

Murmushin nasara nayi daga cikin nik’af ina sannan naje na ijiye masa takardar a saman kujerar da yake zama na wuce abuna.

 

Kafin ya isa tuni doki ya shanye ruwan dana ajiye mashi, sai dai abinda ba’a rasa ba, cikin tashin hankali ya ciro wayarshi daga cikin aljihu ya fara kiran wayar Dikko,

 

Mai gida kazo akwai matsala dokin daka dawo dashi yanzu, gashi nan zai mutu, yana fad’in haka ya kashe wayarshi,

 

Cikin k’ank’anin lokaci Dikko ya iso, a k’ofar gidan yayi parking ya fita da sauri ko murfin motar bai tsaya rufewa ba, lokacin daya shiga cikin gidan tuni dokin ya kwantar da kanshi k’asa yana ta zabura irin na fitar rai.

 

Meya faru haka ne ? Dikko ya tambayi mai gadin shi ! Cikin daburcewa ya fad’awa Dikko duk yanda mukayi dashi , sannan ya d’ora da cewa ga takardar can daka bata ta kawo ta ajiye, ajiyar zuciya Dikko yayi tare da furta wace ce ita tayimin k’arya ?

 

‘Daukomin takaddar kila tana da wata manufarta a ciki, d’aukowa yayi yakai mishi, ya warware ya duba, cimimiye takardar Dikko yayi bayan ya gama karantawa ya dink’uleta wuri d’aya sannan ya jinjina kanshi, ya fito da sauri daga cikin gidan,

 

Wurin motarshi ya tsaya, tare da kaima gaban motar duka sannan yace wallahi cikin k’ank’anin lokaci duk inda “yar iskar yarinyar nan take cikin garin nan ku d’auko min ita, yana fadi haka ya shiga mota yaja fa fafa ya tafi kamar zai tashi sama…….

 

Har yayi nisa ya dawo, har yanzu mai gadin bai koma cikin gidan ba yana nan tsaye a wurin, yanzu daya dawo bai fito ba ya sauke glashin motar shi sannan yace, ku kawota wurina zan nuna mata nid’in d’and’an Babana ne wallahi wallahi wallahi sai tayi nadamar zuwanta duniya.

 

Yana fad’in haka ya juya a guje ya tafi, lallai da ganin yanayin shi gaskiya ranshi a b’ace yake, tabbas idan har aka kamoni aka kawai Dikko ni a cikin wannan yanayin lallai Dikko kasheni zaiyi,

 

Lokaci d’aya jikina ya d’auki kyarma naji fitsari ya kamani sosai, “yan hanjina suka juya ai bansan lokacin dana bar wurin ba, cikin tashin hankali na hau napep na nufi filin gidanmu, tun kafin mu isa na dire nayi gida da gudu……..

 

Da sallama na shiga, Babana na gani zaune dashi da abokanshi kuma sune suka amsa min sallama, cikin farin ciki ya kalleni tare da cewa daga ina kike Mamana ?

 

Cikin inda inda na sosa kaina tare da cewa daga gidansu k’awata nake, murmushi Babana yayi tare da mik’ewa yace muje waje muyi magana, naso nayi masa gardama dan gani nakeyi kamar idan na fita zanga Dikko k’ofar gidanmu,

 

Muna fita na fara tambayar shi ya akayi ya dawo ? Yace min su Bello sukayo belin inshi, akwai wani wasan caca da za’ayi an saka naira miliyan hamsin kin san na kware sosai a wasan caca babu wasan cacar da za’ayi a ci ni saidai ni in ciwo shi yasa ake min hassada.

 

Gyara tsayuwar shi yayi tare da d’an jan dogon hancinsa, sannan yace Mamana kinsan ba’ayin wasan caca a bashi sai an saka k’addara, bani da k’addara sai kayan sakawata, na saka amma ance ba’asan sutura, tou Bello ya bani shawara wai in sakaki a matsayin k’addarata,

 

Cikin rashin fahimta nace Baba kamar ya za’a sakani a matsayin k’addara bayn nima banda komai… Murmushi yayi tare da cewa Mamana kenan ai kuwa kece ma mai komai domin keda kanki kece babbar k’addara ta shi yasa na zab’eki a cikin duk “ya “yan hamsin da takwas dana aifa…..

 

Kiyi hak’uri kawai ki yadda duk wanda yazo ya tambayeki kece k’addarata kawai kice Eh, danni na yadda da kaina babu ubanda ya isa ya ciwo uwata a wasan caca saidai ni inciwo uwarshi wallahi, Mamana ki yadda da Babanki nayi alk’awari baza a samu matsala ba, ki yadda dani kinji Uwar masu gida, ya k’arasa maganar yana mai rik’e duka hannaye na duka biyun yayi kalar tausayi.

 

Tou Babana idan aka tambayeni zance Eh kawai ko ? Yawwa Eh zaki ce kawai ya wadatar, insha Allah gobe kamar yanzu muna cikin kud’i kuma ga Uwata a tare dani, ya k’arasa maganar cikin farin ciki, murmushi nayi mishi sannan muka koma cikin gida dan in fad’awa su Bello na yadda……….

 

Allah yasa muyi juma’a lafiya, ubangiji ya sadamu da alkairan dake cikin wannan juma’a mai albarka, mugun ji da mugun gani tsaka mai wuya ubangiji ya tsare daga garesu, Allah ya karemu da jin kunyar duniya da lahira. Am3n,

 

 





Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022



Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!