Kyawuna Jarabta ta Complete Hausa Novel

Kyawuna Jarabta ta Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Kyawuna Jarabta ta Complete Hausa Novel

Free page

EPISODE 1️

 

Tudun Yola, Kano!

Baban Anguwace kuma sabuwa dan babu mutane haka sosai a anguwan, saidai irinsu uncompleted building da ake kan ginawa dakuma sababbin gidaje da ba’a dade da tarewa cikiba.

 

Baban gidane dayasha fenti milk color, kana ganin ginin gidan kaga ginin irin family house dinan, tsakar gidan mai bala’in fadi, ga katuwar bishiyan mangwaro a tsakar gidan datai y’ay’a sosai dudda basu nunaba, flat biyune agidan wani babban dankareren flat saikuma wani karamin flat mai kamada boys quarters agefenshi, gidan kana ganinshi kasan bawani gidan mai bala’in kudi bane gidan rufin asiri ne dai namai karfi daidai, motoci biyune parke atsakar gidan wata bus mai kyan gaske milk color saikuma mota sienna ash da mai gadi ke wankewa ga dukkan alamu motar maigida ne sabida yanda ya kuke yana wanketa yanabin wakan sangaya dake tashi a karamin radio daya ijiye kan plastic chair.

 

 

 

 

 

Bude kofar karamin flat din dake kusada babban flat din akayi, wani Matashi ne baki dogo baida jiki sosai yana sanye da jallabiya brown hannunshi rikeda makullin mota yafito, takalmi yasaka sanan yasauko daga matattakalan bakin kofarsu yadumfaro babban flat din, da sallama yabude kofa ya shiga ciki.

Babban falo dakeda girman gaske, wani Babban Magidanci ne zaune akan kujera akalla zaiyi 60years kokuma 59, kana ganinshi kaga mai gidan, bakine yanada jiki, hannunshi rikeda jarida dayake budewa yana karantawa.

 

 

 

gefenshi kuma wata Mata ce mai kiba Hajiya Balaraba akalla zatai 40yrs tasaka wani hadadden lace tana kurban shayi a cup, saiga yara dasuke zazzaune akasan carpet suna breakfast kowanne nashan tea da bread da soyayyan egg dinshi, Mata uku ne a tsakar falon da maza biyu wanda duk kasansu daya, Amal that is 14, sai Asiya 13yrs, sai Aneela dakenan 11, Mazan kuma Muhammad dakenan 11 sai Mudasir wanda shine autan gidan 6yrs, gabaki dayan yaran kana ganinsu kaga mahaifinsu tundaga bakin fatar da jikin dan dukansu tuluka tuluka dasu very fat gwanin ban sha’awa kana ganinsu kasan sunacin lafiyayyen abinci, dukansu suna sanyeda uniform din makaranta da alamu hadda zasu danyau sunday.

 

 

Kitchen aka bude, wata black beauty Matace dan itama ba yarinya bace akalla zatai 38yrs tafito tana sanyeda doguwan rigan atampa mai kyau da akama stonework tana rikeda tray dawasu hadaddun kwanuka ke kai, hada ido tayi da wanda ya shigo dakin dukbasu luradashi ba yasa tace “this children zasusa kayi latti for your program Ya Hamad” kiran sunan shi datayi yasa duka yaran dakowama na falo yadagokai ya kallai, atare duka yaran suka gaidashi “Ya Hamad good morning” batare daya amsasu ba yakarasa shiga falon har gaban Abba yakarasa sanan yazauna agefenshi yace “ina kwana Abba” sanan yakalli matar dake gefenshi yace “Ina kwana Mum” daidai lokacin dayan matar taja coffee table zuwa gaban mijin nasu ta dauramai tray akai tace “your food is ready Daddy Hamad” jaridan ya linke tareda mikamata, karba tayi dayan matan tadauke kai Abba kuma yatura hannu a aljihun sanan yaciro wasu kudi yamikama Hamad yace “inka kaisu kabiya musu kudin makaranta” sanan yajuya yakalli matar dake gefenshi yace “me yaran nan sukeyi asama har yanzu basusan zasu makaranta bane”? dasauri tace “kumafa su tuntuni sukai break, Nanaa, Hawwa” daga chan sama aka amsa, wasu yan mata manya masu jiki guda biyune suka sauko daga stairs, yaran zaka dauka yan biyu ne dan suna kama, irin kama na jini dinnan, Nana itace Babba 26yrs take tana final year a BUK tana karanta Mass Com, sai Hawwa 24yrs tana 300level tana karanta international relation itama a Ado Bayero, Hawwa na kama da Hamad sosai, dukansu suna sanyeda lemon green hijabi na haddan, dukansu ransu abace yake dan sun tsani zuwa hadda suna uni amman suna wani zuwa hadda shikuma Babansu yanuna babu wacce ta isa tabar hadda cikinsu kodako PHD sukeyi, tashi duka yaran sukayi sukama iyayensu bye suka fice, sanan Ya Hamad din yatashi yace “bari nakaisu Abba” gyadamai kai kawai yayi dan haka Babansu yake baifiye son magana ba, sanan yawuce yafice.

Kaman ance tadaga kanta sama taga gittawan mutum dasauri an bude kofa anshige daki batare da an bari sun hada ido da Mami ba. Ahankali Mami tasauke ijiyan zuciya dudda bataga fuskanba but ko amafarki aka tadata tasan waye.

 

 

 

 

 

Duk suna zaune afalon harya gamacin dumamen tuwon yadauki ruwa yasha, Dan gyaran murya matan dake zaune kusada shi tayi Mum tace “Alhaji nace bari namaka tuni, kaga duka duka bikin Nana bayan Babban salla da sati uku ne, gashi lokaci nata matsowa yanzu baifi wata daya bikin ba, nasan dama kariga kabada kudin kayan daki, cha kayi daman wanan satin zakaban kudin kayan kitchen, kaga idan kabani nida Zainab saimu shiga kasuwa yau muyo siyayyan koya kika gani Zainab”? Mum tama Mami dake zaune tana sauraransu magana, gyadamata kai tayi sanan tace “eh hakane Abban Hamad” ruwa yadauka a cup yakara kaiwa baki yasha sanan ya ijiye cup din, hannu yasa a aljihu yaciro bandir din yan dubu daya guda biyu yabata yace “kinemi wata kijeda ita kasuwa, Zainab bazata iya zuwa ba itakeda girki, kuma yau lahadi ina gida” yana fadin haka yatashi yawuce sama duk suka bishi da kallo, saida taga yashiga dakinshi sanan tabata rai tace “Alhaji Alhaji bantaba ganin kafaffen mutum irin shiba wlh” tashi tayi batare data kalli Mami ba tai stairs tabude bangaren ta tashige dan saman bangare biyune nata dana Zainab saikuma dakunan yaransu guda uku, na maza kanana dana mata kanana saikuma na yan matan suma dakinsu daban.

 

 

 

Ahankali Mami ta tashi ta tattare duka kwanukan takai kitchen sanan tasa Mai aikinsu Uwani tazo tashare falon ta kunna turare sanan tai sama itama bude dakin mijin nata tayi tashiga bata wani dade aciki ba sanan tafito, direct dakin yan matan tayi ahankali tabude kofar, dakin nada dan fadi gashi a gyare Kal Kal, gadaje ne guda uku irin nayan boarding jere adakin kowanne da bangaren nashi saiga wardrobe na bango da kayan kowa keciki, bin kan gadajen tayi da kallo ganin babu kowa kai yasa takarasa shigowa dakin tareda maida kofan tarufo sanan tashigo ciki takaraso tsakiyan dakin saikuma ta tsaya turus tai shiru tana kallon gaban gadon dake tsakiyan dakin, wata faran budurwan yarinyace azaune akasa tabama dakin baya tana kallon bango tadaura kanta kan kafafuwanta ta, nimai rubutu M Shakur banmasan mutum bane awurin ba saida naga Mami ta tsaya turus tana kallon wajen, wani irin silk black gashin kaman na yar India ne zube awajen yana taba tiles din kasan daki sabida yanayin zaman datayi tsabagen tsayin gashin, sai farin kafanta sol mai bala’in kyau da dogayen fararen farcenta dababu komi akai sai uban haske kaman ana wankesu da madara. “Du’a” jin ankira sunanta yasa tadago kanta daga kifen dasuke akan kafafunta dasauri batare data waigoba jin muryan Mamin ta, dan Jim Mami tayi tana binta da kallo sanan asanyaye tace “inkin gama kukan ki tashi ki tattare gashin nan naki ki kulle kisa a hijabi kije Abban ki nakiranki yana dakin shi” tana maganan tawuce tafice daga dakin tarufo musu kofan.

See also  Ummu Waheeda Hausa Novel Complete

 

 

 

Ahankali takai fararen hannuwanta tashare fuskanta sanan tamike tsaye ahankali, wani iri mahaukacin cokacola shape Allah yamata gawani irin pointed curvy ass gareta daya fito sosai cikin doguwan rigan material din dake jikinta, itama kaman sauran yaran gidan tanada dan jiki danbazaka taba kiranta da mara kiba ba amman batakai su Nana kibaba, saidai tafisu diri, ga gashin kanta dabaida banbanci dana yan India har waist dinta, juyowa tayi ahankali TSARKI YA TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA’ALA WANDA YA HALLICI SAMAI DA KASSAI DAKUMA HALITTUN DAKE CIKINTA!!!! yarinyar nan koda ace itace tayi kanta banjin zatai kanta tai kyan datake dashi yanzu hakaba dan My Lord!!! dan itace definition of tacika goma cip cip tamakai sha uku, farace Kal fuskanta babu pimple ko daya idanunta sun kumbura sunyi ja sabida kukan datayi wanda haryau takasa sabawa dan by now yakamata ace tasaba duk sanda yan uwan ta zasu makaranta boko ko islamiyya saitai kuka, tanada wani irin long pointed hanci ga pink lips, gashin idanunta dogaye kuma acike sun jikeda ruwa, ga kirjinta awani irin cike kaman wacce taje tai surgery ga flat tummy kaman bata tabacin abinci ba, Allah yamata ass amman waist dinta kona jariri albarka her waist is so tiny, ahankali take tafiya har zuwa gaban madubin dakinsu ribbon dinta dake wajen tadauka sanan ta kulle kanta da kyar sanan tashiga bayinsu wanko fuskanta tayi tafito tadauki dogon hijabin ta maroon tasaka tafito daga dakin ahankali.

 

Karanta Littafin Kuruciya  Hausa Novel

Cikin wata irin siririyan cool melodious voice tai sallama gaban dakin Abban su, daga ciki taji yace “shigo” ahankali tabude kofa tashiga kanta akasa, yana zaune kan couch din dake dakin yabita da kallo tazo gabanshi tazauna tareda saukar da kanta kasa ahankali tace “Abba gani” zama ya gyara tareda bude Al Qur’ani dake kan cinyanshi sanan yace “biyomin haddanki” gyara zama tayi sanan tafara rairomai suratul Yusuf shafa’i ukun dayabiya mata last week, shi karan kanshi idan tana biyamai hadda baiso tadena dan muryanta Allah yay mata dadi saida tagama tsaf sanan yakara mata wasu shafa’i ukun kafin yamata tajweed sanan yace “tashi kitafi” tashi tayi ahankali tai hanyar kofa yasake binta da kallo harta daura hannunta kan handle din kofa taji yakirata anatse. “Du’a” dasauri tajuyoda kanta ta kalleshi saikuma tasauke idanunta kasa tace “na’am Abba” ahankali yace “nariga nasaman miki wata sabuwar malama, daga gobe zata fara zuwa In sha Allah, ki shirya” gyadamai kai tayi sanan tajuya zata bude kofan saikuma tajuyo ahankali batare data budeba ta kalleshi hada ido sukayi hakan yasa takasa magana tajuya zata bude kofan tafice cikin muryan nan nashi nabawasa yace “mekikeso ki fada”? Dan juyowa tayi ta kalleshi saikuma tasauke kanta kasa kirjinta na bugawa fat fat tashiga wasa da yatsunta tsabagen how nervous she was tama kasa magana, dan idan Abban su yakureka da ido zamaka iya fitsari ajiki baka saniba, shifa kokadan baida wasa kuma yanada zafi sosai, gashi kaifi daya saisa duka yaranshi ke tsoron shi. Ganin takasa magana yasa yace “I’m listening” rawa sosai muryanta yafara tanama bude baki maganan yakasa fitowa saikuma tasaki hannunta ta shiga chakuda hijabinta da hannu duk yana binta da kallo hijabin tarike gamgam sanan da kyar tasamu maganan yafito ahankali tace “Ab…..ba ni……maisa ake barina agida kahanani fita kowaje, Abba ni nafison naje school kaman su Ya Nana……” saikuma tasake hadiye wani irin dry miyau hawaye yawani zubo daga idanunta suka sauka akan hijabinta cikin wata irin murya na wacce ke gabda fashewa da kuka kuma take a bala’in tsorace tace “Ab….ba ni maisa baka sona kaman yanda kake son su Ya Nana da Hawwa da….d…..” Du’a!! taji anwani irin kirata da kakkausar murya dayasa tadaga kanta da sauri ta kalli inda taji muryan, Mami ce tafito daga bedroom din Abba da alamu tuntuni take ciki maybe gyaramai dakin take dan taga karamin rag na goge goge a hannunta, cikin wani irin tsananin bacin rai tace “Du’a are you questioning your father? eh? mahaifin ki kika tasa agaba kina tuhuma haka?” girgixa mata kai tayi dasauri saikuma tasaki kuka dasauri tajuya tabude kofa tafita daga dakin dagudunta.

 

 

 

 

KYAWUNA JARABTA TA

 

 

 

 

M SHAKUR

 

UMMI COLLECTION is a whole world of turaruka, both na wuta dana feshi, exquisite burners na electric dana charcoal, and oils, turarukan wanka da sauran su. kunkosan kwanan nan UMMI COLLECTION na promo free delivery, hehehe banso kuyi missing this mad offer just click on this link danyin magana da ita directly.

wa.me/+2348186968736

 

 

 

free page

EPISODE 2️

Azuciye Mami ta jefar da rag din dake hannunta tace “nikema yarinyar nan magana tafice tabarni sabida batada kunya Dadyn Hamad” tataho cikeda bacin rai zatai wajen kofa tabita Abba dake kallonta tunda tafara masifan yace “ina zaki”? Turus ta tsaya tana kallonshi takasa koda motsi, anatse yanuna mata bedroom dinshi yace “koma kicigaba da abinda kikeyi” dasauri tace “but……” “no buts ki koma kicigaba da abinda kikeyi nace” yay maganan babu alamun wasa akan fuskanshi hakan yasa bata karacewa komiba tawuce takoma ciki ranta abace, jaridanshi yabude ahankali yacigaba da karantawa bazaka gane takamaimen wani yanayi yake cikiba dan fuskanshi bata nunawa.

 

 

Dakinsu tabude dagudu tashiga tafada kan gado tana kuka sosai, tayi kuka nakusan awa daya sanan bacci yay awon gabada ita akan gadon.

Hayaniya yatadata daga baccin datakeyi, bude idanunta tayi ahankali saikuma ta yunkura ta tashi zaune tana kallon dakin nasu, Nana da Hawwa ne kecire kayan jikinsu sundawo daga hadda duk sunyi zufa, ahankali tace “Ya Nana kundawo daga makaranta” danjuyowa Nana tayi takalleta tana kokarin daukan zanin dazata daura tashiga wanka tace “eh yanzu muka shigo””sannu da zuwa” tafadi ahankali sanan tajuyo da kanta Hawwa ta kalla taga Hawwa tadauke kai dasauri tana batarai, daidai lokacin aka bude kofan dakinsu, Aneela ce tashigo wacce take kanwarta, dan Du’a ce yar Mami tafarko, sai Aneela, sai Muhammad da Mudasir su Hudu Mami ta haifa, itakuma Mum itace mahaifiyar su Hammad, Nana, Hawwa, Amal, da Asiya yaranta biyar.

See also  Amfanin shan kunun aya ga jiin dan Adam

 

 

Ko kadan Aneel bata kama da Du’a inba ma angayamaka ba bazaka zaci uwarsu dayaba dan tafi kamadasu Nana black beauty ce itama, kyakkyawan yarinya bakutu da ita, zama tayi kan gadon takalli yayartata tace “yauma saida kika kara kuka sabida muntafi makaranta banda keko” Hawwa data zauna kan gadonta tana ciro wayanta daga jaka tana kunnawa tace “asheko xakita kuka har karshen rayuwanki dan Abba yace konan da gate bazaki taba fitaba” turo baki Aneela tayi cikeda rashin kunya ta kalli yayartata saikuma takai hannunta tadaura kan kumatunta tace “karki kara kuka kinji Duudo, kinga ko yau Malam yafassara mana wata aya yace duk wanda yadogara ga Allah to hakika Allah ya isar masa, ki dogara ga Allah and I promise you Allah will be there for you, kiyita addu’a zakiga Abba zai chanza zaice kema kifara zuwa school kaman mu kinji” gyadama kanwar tata kai tayi ahankali, Aneela tawani washe baki tai murmushi hakan yasa itama tai murmushi, Subhanallah idan tai murmushi numfashinka zai iya tsayawa sabida kyan datake karayi.

 

“In dauko mana abinci muci tare?” Aneela ta tambaye ta, Gyadamata kai tayi hakan yasa tasauka daga gadon tawuce tafita, itakuma ta sauka daga gadon ahankali sanan tawuce bathroom dinsu dan dauro alwala Hawwa tabita da harara wanda inda sabo tasaba tun suna yara basa shiri sabida sako da sako nesu dan daga Hawwa sai ita aka haifa agidan, itakuma Nana babu ruwanta bata shiga harkanta as per babban yaya in the house.

 

 

Fitowa tayi ta shimfida dadduma tadau hijabi tasaka ta kabbarta salla daidai lokacin Aneela tashigo ajiye musu rice da stew din tayi akan gado itama tazauna tana jiranta ta idar, itakuma Hawwa ta tashi tafita duk ranta abace yake sabida yanda tadawo Mum dinsu batanan.

 

Saida ta idar da sallan sanan tazauna sukaci abincin tareda Aneela batare dasunyi surutu ba sabida Nana dake waya da wanda zata aura, sosai taci abincin suka gama tass Aneela tafita da plate din takai kitchen sanan tasake dawowa dakin.

 

Wuraren 4 Mum tadawo daga kasuwa da mota guda na kayan kitchen yaran sai murnan ganinta suke barinma yaranta dakin da ake tarin kayanta akakai komi bayan Abba yagani sanan daga ita har Mami suka shiga kitchen sukahau girke girke sabida bakin da Abba zaiyi yan wajen aikinshi da iyalansu, yaranma duk aka kirasu kitchen banda Du’a dakenan ita kadai adaki.

 

 

 

 

 

Tana zaune adakinsu har magrib ita kadai, dan tun dazu aka kira Aneela da Nana da Hawwa duka batasan me akayiba but tadaiji kamshin girke girke kuma yawanci tasan ana irin girkunan nan ne idan zasuyi baki, tashi tayi ahankali ta shiga bayi wanka tayo tareda dauro alwala tafito daidai lokacin da Nana da Hawwa sun shigo dakin duksunyi zufa, dasauri tace “Ya Nana mekukeyi?” “Girki” tabata amsa atakaice tawuce tashiga bayi dan wanka itakuma Hawwa tazauna akan gado tana daukan wayanta tana dubawa ko ankirata, gaban wardrobe dinsu taje tabude bangaren kayanta, wani doguwan rigan atampa black taciro tawarware sanan tasaka dayamata kyau sosai sanan tadauki hijabi tajuyo hada ido tayida Hawwa dake kallonta suna hada ido tadauke kai tacigaba da danne dannen wayanta, saka hijabin tayi tahaukan dadduma tafara salla daidai lokacin Nana tafito daga bayin ta kalli Hawwa tace “tashi kije kiyi wanka Hawwa kinga Abba yace mu shirya dawuri suna hanya fa” tashi Hawwan tayi tashiga bayi itakuma Nana tashiga shiryawa cikin wata atampa.

 

Idar da sallan tayi ta tashi tazauna akan gadonta tareda cire hijabin ta ijiye agefenta tana kallon yanda duk suke shiryawa agurguje, suna makeup abin na bata sha’awa dan ita mai kadai na shafawa gareta sai body spray, batada sauran kayan kwalliyan dasuke dashi kuma bata isa ta taba abinsu ba barinma masifaffiyan Hawwa nan. Daga Hawwan har Nana saka atampopi sukayi iri daya suka shirya tsaf gwanin ban sha’awa sanan kowacce ta zauna kan gado tana danna waya, sosai take kallon wayan dasuke dannawa, duk idan taga suna tabawa saita bata shaawa kaman taje ta karba amman tasan bazama su bataba, duk suna zaune ahaka kowa nawasa da wayanshi banda ita dake kallonsu kaman tasamu film aka bude kofa dasauri duk suka daga kansu suka kalli kofan, Abba ne yasaka lafiyayyan shadda mai ruwan toka da hula akanshi yana tsaye daga bakin kofa batare daya shigoba yakalli su Nana yace “kufito kugaida Abokan aikina da matansu” yana maganan yasaki kofan yay gaba duk tashi sukayi harda ita cikeda wani irin murna koba komi yau zataga wayanda bayan gidansu ba, hijabinta tadauka tasaka sanan tabi bayansu Nana dasukai gaba batareda sun cemata komiba suka fito Abba na tsaye kan stairs yana jiransu su fito yagansu, hada ido yayi da Du’a dake nonnoke kai, ahankali yace “ke banda ke koma daki ki zauna” wani irin murmushi Hawwa tayi ranta fess jin ankorata, Gyadama Abba kai tayi ahankali cikeda mugun sanyin jiki tajuya ahankali tashiga daki tareda maida kofan tarufo daidai lokacin Hamad yafito daga dakin Mum dinshi, hada ido Abba yayi dashi yace “let’s go tunda kafito” shida Abba suka jera yaran kuma abayanshi har zuwa kasa.

 

Abokanen aikinshi ne su uku da matayensu da yaransu kanana suna ganinshi Babban cikinsu yace “what a nice family kakedashi HOD” dan murmushi Abba yayi yakaraso wajen yabasu hannu sukuma yaran suka shiga gaida kowa, Mami da Mum da Uwani suka shiga kawo abinci da kayan kwalama, ahankali Mami kebin kowa na falon da kallo saikuma tasauke ijiyan zuciya ahankali, daya daga cikinsu yace “wayan nanne kadai yaranka HOD”? Gyadamai kai yayi yace “eh” ahankali Mami dake kokarin bama matar abokinshi plate na snack tadan saci kallonshi saikuma tai murmushi tacigaba da serving while Abba yacigaba da magana yanuna Hamad yace “wanan shine first son dina Hamad he’s 30, yakaranta engineering” dasauri bakin sukace “like father like son” danshima engineering yayi yanzu shine HOD engineering department a BUK, murmushi yayi yace “yayi joining NDA yanzuma wani program yakeyi anan kano saisa yakenan, sai Aisha” yanuna Nana yace “muna kiranta da Nana dan tanada sunan Mamana, ankusa bikinta nan da bayan salla, sai Hawwa sai Du….” Shiru yayi dasauri saiya nuna Amal yace “sai Amal, Aneela, Asiya da Muhammad da Mudasir, yarana takwas” “wow masha Allah, nice family wlh, Allah ya rayamaka su kaga aurensu” murmushi Abba yayi yace “Bismillan ku mufaracin abinci” nan aka shiga cin abinci akai shiru, ahankali Hamad yatashi yay excusing kanshi yay sama binshi da kallo mahaifiyarshi tayi babu daman kiranshi sabida bakin dake wajen.

See also  Download Ali Dan Tsoho Hausa Novel

 

 

 

Dakinsu Du’a yabude yashiga tareda maida kofan yarufe sanan yajuyo ya kalli gadonta, a kwance yaganta tarufa da hijabinta, ajiyan zuciya yasauke aboye sanan yashigo dakin yace “Hey Duudo look what i got for you” shiru tayi kaman tana bacci taki motsi, ahankali yasa hannunshi yakama kafafunta yadagasu sama sanan yazauna abakin gadon sanan yasaukar da kafafunta kasan gadon tareda saka hannu yaja hijabin data rufe fuskanta dashi, dasauri ta yunkura zata juya fuskanta kawai yadagota yace “come here Du’a” sata yayi ajikinshi kaman jira take ta kankameshi sosai sai kuka, ko kadan baiyi attempting hanata kukan ba, duk kanninshi babu wanda yakejin tausayinta yake kuma so kaman Du’a sabida tafi kowa rauni, he don’t care about kalaman da family su suke fadi akanta ana cewa itaba yar Abba bace, mayya ce, yar aljanu ce bla bla bla, all he knows is Mami da Abba suka haifeta and she’s his little sister kuma yanason kanwarshi sama da tunanin kowama.

 

 

Cikin kuka tace “Ya Hamad ni wlh inaso namutu” dasauri yacirota daga jikinshi yace “ke are you crazy? Karki kara fadin haka” bayan hannunta takai tana share fuskanta tace “Abba bayasona, Mami bata sona, Mum ma batasona, Kaka ma batasona, kaga ni kadai Abba ya tsana ayaranshi, yakorani nakoma daki dazu, kuma kaga yace yaranshi 8 yacireni daga cikin yaranshi, kullum ina kulle adakin nan kaman mayya, dama Kaka tace ni mayya ce ni aljana ce, sabida ni kadai aka haifa daban bana kama daku does that means am a witch ko aljana eh Ya Hamad? Ya Hamad bakacemin kananan ranan da aka haifeni ba kuma kace Mami ta haifeni maisa su Aneela dasu Muhammad da Mudasir kadai takeso eh? Ya Hamad babu asibitin dake chanza kalan fatan mutum ka kaini naje nakoma kalan yan gidan mu sabida Mami na da Abba su soni nima eh Ya……..” hannunshi yadaura akan lips dinta yace “ya isa haka listen to me all abubuwan nan dakikaga Abba da Mami nayi bawaidan basa sonki bane sunayine to protect you, Du’a tun kina primary school ansha ayi attempting ayi raping naki nasan lokacin kina yarinya ba lallai kituna ba, but kin tuna lokacin dakike JSS 2 abinda teacher ki da Abba ya kulle yamiki ko” runtse idanunta tayi dakarfi alamun ta tuna, hakan yasa ahankali yakai hannunshi yakama hannuwanta guda biyu yace “listen to me, Abba is only trying to protect you, Abba bai tsaneki ba” ahankali cikeda raunin murya tace “amman yana kunyan ya nunani amatsayin Babana” tai maganan tana kallon Ya Hamad kurii da manyan idanuwanta dayasa yakasama mata karya dan to some extend all abinda take fadi gaskiyane, ahankali kawai yajawota jikinshi ya rungumeta yakai hannunshi yashafa gashinta murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita sukeji yace “kin tuna abinda nake yawan fadamiki” gyadamai kai tayi ahankali ajikinshi hakan yasa yace “fada inji” murya chan kasa hawaye nabin kuncinta tace “Du’a kome kikaga yana faruwa arayuwanki Allah yasan dake, jarabawanki ne, karki kaucema Allah karki butulcemai, bake kikai kanki ba Allah ya yoki, love yourself, kiyi imani da Allah kikuma dage da addu’a watarana sai labari my beautiful little Duuudo” suka karashe maganan atare hakan yasa takara kankameshi, murmushi yayi sanan yacirota daga jikinshi, handkerchief yaciro daga aljihunshi yace “now let’s wipe those tears no more kuka okay” gyadamai kai tayi tareda murmushi yan kananun white teeth dinta suka bayyana, sharemata fuskan yayi tass sanan shima yamata murmushi yace “idan bakin nan suka tafi zan dauko miki sababbin novels din dana sayomiki kinji” gyadamai kai tasakeyi, kumatunta yaja yace “idan kika sake kuka saimun bata” dasauri tace “bazan sakeba” “kinci abincin dare?” Girgizamal kai tayi, tashi yayi yace “bari naje nakawo miki saiki bani labarin wayan nan novel din” gyadamai kai tayi yawuce yafita yana murmushi, Allah yamata brain, english novels yake sayomata dasukakai 1000+ pages cikin 2days tagama kuma tsaf zata bashi labarin novel din, abinda yataimaka mata da english ma kenan.

 

Karanta Littafin Kuruciya Hausa Novel

Bai wani dadeba yadawo dakin da bowl na hadadden pepper soup da cow head, kafinma ya iso ta tashi tsaye dasauri tace “Ya Hanad kaman pepper soup ko” bata plate din yayi yace “mayyan nama kawai” dan tana balain son nama tun tana yarinya, murmushi tayi takarba dasauri tazauna tashiga ci ya tsaya shikuma yana kallonta, she looks so happy hakan made him so happy, dan yarinya ce da dawuya kaga she’s happy saisa anytime she looks happy happiness dinta is infectious sai kawai kaji kaima ka kamu da farin ciki. Juyowa tayi takallai tana tana naman kaman wata yar baby looking so adorable ganin ita yake kallo yasa tamikamai last piece na meat din tace “zakaci” hararanta yayi yace “marowaciya sai yanzu zaki bani to banci” dan dariya tayi tace “yakuri bari naci wanan gobe saimuci tare, Ya wai yaya ake dafa nama ne”? “Har yanzu ba’a barinki ki shiga kitchen?” Gyadamai kai tayi tace “ba Kaka tahana ba” gudun karta tunakomi dan yanzun nan kuma tahau kuka tasa yace “zan sayo nama saina koyamiki a kitchen din side dina” sosai tashiga jin dadi tana tauna namanta bude kofa akayi dasauri dukansu suka waiga, Mum ce fuskarta amurtuke, wani mugun kallo tama Hamad tace “mena gayamaka? Zokabar dakin nan” tai maganan tareda nunamai kofa, tashi yayi ahankali batare dayamata gaddama ba yazo yabita gefenta yafice, shigowa dakin tayi tazo har gaban gadon Du’a data sauke kanta kasa tana rikeda bowl din pepper soup din data cinye tace “ke bazakiji da bakin jinin ki kinemi yanda zakiyi ubanki yama yarda cewa ke yarshi ce ko yadinga lissafawa dake cikin yaranshi kina nan kina nema kisama dana bakin jininki ne, sabida kinga yanda ubanku keji dashi first son dinshi ga ilimi ga kyau shine zaki biyo tanan, to ta Allah batakiba bakar mayya kawai, kijechan kiji da kanki, na tsani uwarki amman naga matsalan da haihuwanki kesata ciki wlh har tausayamata nake, wayama sani ko wani aljaninne yadura mata cikinki dan naji ance tayi aljanu datana gida da kyar namijin dare yamabarta tai aure” ahankali tashare hawayen daya zubomata sharr babu abinda ta tsana irin adinga kiranta da yar aljanu ko mayu, Mum tasake wurgamata mugun kallo tace “wawiya dakikiya kawai babu abinda tasani sai zaman daki, kannenta ma sunfita iya karatu sunfiki iya komi Babanki yamaidake gidahuma yaryar aljanu kawai” wanan karan fashewa da kuka tayi sosai takai hannunta tadaura kan fuskanta tana kuka, murya chan kasa ta yanda Baza ajiba tace “niba yar aljanu bace” da sauri Mum dake tsaye kanta tace “me kikace Du’a? Mayarmin da magana kikayi? Did you just talk back at me eh?”.

 

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


2 thoughts on “Kyawuna Jarabta ta Complete Hausa Novel”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top