DAREN 1
NA LABARUN DARE DUBU DA DAYA
kamar yadda mu kayi bayani a labrin farko cewar : (shahar za’d) da kanwarta (dunya za’d) sun tsara cewa : idan (dunya za’d) ta shigo gidan sarki ta samu sarki ya gama biyan buqatarsa (saduwa) a wurin amaryarsa (shahar za’d) to sai ta zauna taredasu, suyi hira, sannan sai ta bukaci (yar uawarta) shahar za’d ta basu labarai.. To bayan kanwar ta iso an zauna ana hira .. jim kadan sai tacewa yayarta (shahar za’d) : ya (yar uwata) ! ki bamu labari mai dadi mana muji !,, saboda mudebe kewarmu awannan daren ?
sai (shahar za’d) ta kalleta tace : kamar yadda kikeso haka zanyi, Amma sai sarki mai alfarma mai martaba mai a’dalci ya bani izini !!, .. Da sarki yaji wannan magana sai yayi murmushi kuma yayi farin ciki,, atake sai ya umurci (shahar za’d) ta soma bada labari… Daama sarkin ya kasance cikin damuwa bakin nciki, sakamakon abunda ya faru a baya game da (ha’incin) da matarsa tayi masa, da sauransu… kuma ya rantse ya lashi takobi cewa sai ya dau mataki ,a dalilin hakane yayi ta kashe matan gari, bai dena ba harzuwa lokacin da amariya ( shahar’zad) ta shigo gidansa… To sai (shahar za’d) ta matso kusa da sarki, tana murmushi,, tacemasa : ya sarki mai martaba mawadaci !! labari ya iso mini cewa : – Akoi wani attajiri, mai dunbin dukiya, kuma mai yawan hada’hadar kasuwanci a kasashe dadama To ana nan, watarana sai wannan attajiri ya hau dokinsa ya kama hanya da niyyar yin tafiya zuwa wani gari, . bai gushe ba yana ta tafiya ckin duhun daji, har sai da gajiya ta kamashi, ga zafin rana da ishiruwa da yunwa, sai ya hangi wata bishiya mai inuwa yaje ya zauna a qarqashinta, zamarsa keda wuya kenan sai yazura hannunsa A Aljihun sa ya ciro wata KISRE (kamar gurasa ko bredi) da kuma dabino yaci.. bayan ya gama cinye wannan KISIRE da kuma dabinon, sai ya jefar da kollon dabinon…
bayan wani dan lokaci sai wata guguwa mai karfi ta taso a kusa da shi, jim kadan sai ga wani jibgegen IFRITU ( wato al jani kenan ) mai tsawo ya bullo da takobi a hannunsa, sai attajirin yarazana ya soma karkarwa yana salati saboda irin mummunar halittar da yagani, sai wannan al jani IFRITU ya matso kusa dashi, ya masa tsawa yace masa : katashi in kasheka kamar yadda ka kashe mini dana, sai mutumin yace masa : tayaya na kashe maka danka ? Sai al jani IFRITU yace : lokacin da kaci dabino, ka jefo kollon a kan kirjin dana (jinjiri) atake sai ya mutu, sai attajirin yace : INNA LILLAHI WA INNA ILAHI RAJIUUNA, LAHAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHI AL ALIYYIL AZIM, yayi salati, amma inaa.. IFRITU ko kulashi baiyyiba. sai attajirin yace masa : idan har na aikata hakan, to akan kuskurene cikin rashin sani, dan ALLAH ka yi mini afuwa,? sai yayi ta lallabarsa yana bashi hakuri, kuma yanuna masa cewa akan rashin sanine haka ya faru. Amma sai IFRITU yayi kunnen uwar shegu, yaqi hakura, sai IFRITUN yace masa : ka gama surutunka ? saboda kasheka babu makawa sai nayi na dauki fansa…
kawai jim kadan sai IFRITU ya damko attajiri ta wuyarsa, ya kifardashi kamar yadda ake yanka rago, sai ya daga wuqarsa sama zai pille masa kaayi.. kawai sai attajiri ya qwalla I’hu yana kuka, sai yace : nidai na dogara da ALLAH… To a nan sai attajirin yaroqi IFRIRU akan yayi masa jinkiri (yasaurara) yanada maganar da zai gayamasa kafin ya kasheshi, sai IFRITU ya sauqar da takobinsa saboda yaji abunda attajirin zai fadamasa, To sai attajirin yace masa : ranka ya dade IFRITU ! ka sani cewa… ni attajirine,kuma Akoi bashin mutane akaina, kuma inada dukiya maiyawa, gashi inada mata da yara (magada), kayi haquri ka barni in koma gida saboda inbiya bashin dake kaina, kuma in bawa kowa hakkinsa, inyi sallama da iyalaina da yan uwa da abokan arziqi, sannan sai na dawo wurinka ka kasheni ka dauki fansa, ko kuma kayi duk abunda ka keso dani, nayi maka alkawarin zan dawo.. ubangijin ALLAH shine shaida a tsakanimmu.. A nan sai IFRITU ya’amince masa, da yaje ya biya bashin da ke kansa.. ya yi ban kwana da gida ya biya dukkan bukatunsa ya dawo. Attajirin ya koma gida, ya sanarda ‘yan uwansa dukkan abinda ya faru tsakaninsa da aljani IFRITU..
yaransa da matansa da dukkan ‘yan uwansa da mutanen gari aka taru akayi kuka, kuma tundaga wannan ranar aka soma karban ta’aziyar mutuwarsa, akayi masa fatan shiga aljannah, shima yana zaune a wurin makokin, … Bayan wasu yan kwanaki, sai attajirin ya shirya kayansa, yayi bankwaana da matansa da yaransa da dukkan yan uwa, yayi wasiyya, matansa da yaransa sukayi kuka sukayi zaman makoki, sannan daganan sai yayi bankwaana da jama’a.. ya dauki likafaninsa a hammatarsa ya kama hanya.. – yana cikin matuqar baki nciki -…
bai gushe ba yana ta tafiya har saida ya iso wannan wuri da ya hadu da IFRITU, sannan sai ya zauna jiran zuwan IFRITU, kuma ya ciga da kuka yana zubarda hawaye a karkashin wannan bishiya… Bai gushe ba yana cikin wannan yanayi, yana ta zubar da hawaye, chan sai wani mutum tsoho da barewa a ta’redashi ya bullo masa.. sai mutumin ya yi sallama ya yi gaisuwa, sannan sai yacewa attajirin : menene dalilin zamanka a nan wurin kai kadai ?, kuma kafin attajirn ya bashi amsa sai mutumin ya sanarda attajirin cewa wannan wurin fa makwancin (matattra) aljanune…?
To a nan sai attajirin ya bawa mutumin labarin abinda ya fafaru tsakaninsa da IFRITU daga farko zuwa karshe, kuma ya gayamasa dalilin zamansa a wannan wuri, sai wannan mutumi (tsoho) yayi mamaki, kuma yacewa attajirin : wallahi ya (dan uwana) Addininka Addinine mai girma mai amana ( saboda cika alkawari da yayi ) kuma labarinka rabarine mai ban mamaki korai da gaske… sannan sai mutumin ya zauna a gefensa yace : wallahi bazan bar wannan wuri ba sai naga abinda zai gudana tsakanin wannan attajirin da IFRITU, sannan sai ya zauna tare dashi yana lallabarshi yana bashi hakuri yana dede masa kewa.. ana nan, bayan wani dan lokaci, sai attajiri ya suma, saboda tsananin tunani da bakin ciki da fargabar abinda zai faru da shi idan IFRITU yazo, To suna cikin wannan yanayi, jim kadan sai ga wani mutumin daban (tsoho) na biyu ya bullo, kuma a tare dashi akoi KARUNUKA guda 2 (baqaqe).. sai wannan mutumi yayi sallama, kuma ya tambayesu dalilin zamansu a wannan wuri..?
kuma shima ya sanardasu cewar wannan wuri matattarar aljanune, kamar yadda mutumin farko ya fada.. Sai sukabashi labarin a bunda yafaru tsakanin IFRITU da attajiri daga farko zuwa karshe, To sai shima wannan mutumi (na biyu) yayi mamaki matuqa, kuma shima yace ba zai bar wannan wuri ba sai yaga abunda zai faru tsakanin Ifritu da attajiri, sai ya samu wuri ya zauna, yana taya dayan tsoho daukewa attajiri kewa..
To suna cikin wannan yanayi, suna rarrashin attajiri, shikuma sai zabga kuka yake yi, yana suma yana farfadowa… to suna cikin haka sai wani mutumin (tsoho) daban na 3 ya bullo,, kuma a tare dashi akoi ALFADARI, To sai shima wanna mutumin yayi sallama tareda gaisuwa, sannan sai ya tambayesu dalilin zamansu a wannan wuri, kuma shima ya sanardasu cewa wannan wuri makwancin aljanune, shima sai suka bashi labarin abinda ya gudana tsakanin IFRITU da attajiri daga farko zuwa karshe, sai mutumin yayi mamaki da yaji wannan labari..
Suna cikin wannan hali, sai ga wata guuguwa mai qarfin gaske ta tashi a kusa dasu, kuma guuguwar ta nufi inda suke , sai suka tsorata… jim kadan sai wannan guuguwar tayaye, kawai sai ga IFRITU ya bayyana a gabansu, da wata doguwar takobi a hannunsa, idanunsa suna yalqi, sai IFRITU ya matso kusa dasu, ya damqo wannan Attajir, ya fitar da shi daga tsakaninsu, sai yace masa : zonan in kasheka kamar yadda ka kashe mini (DANA) farin cikin raina, sai Attajiri ya tsorata, yana kuka ya naqolla I’hu, haka suma wadannan mutane guda 3 sukayi takuka.. to suna cikin wannan hali, sai daya daga cikin wadannan mutanene (tsoff), – wanda ya iso wannan wuri dafarko – ( mai BAREWA), ya tashi ya miqe tseye ya matso kusada IFRITU yayi gaisuwa irin gaisuwar da ake wa sarki, ya tsunkuyar da kansa ya bada girma, sai yacewa IFRITU : ya mai martaba, ya wanda ADON sarkin aljanu, idan na baka labarina, da abunada ya sameni tareda wannan BAREWA dake tare dani a yanzu kuma kaga cewa labarin ya’maka dadi ya qayatar da kai, shin zaka yafe mini daya daga cikin uku na jinin wannan attajiri ?.. sai IFRITU ya kallesa yace masa : E’h idan ka bani labarin rayuwarka, kuma naga cewa labarin ya qayatar da ni yayi mini dadi, to zan baka (yafemaka) daya daga cikin uku na jinin wannan attajiri kamar yadda kakeso…. To sai wannan mutumi (mai BAREWA) yacewa IFRITU : ya mai girma (aljani IFRITU) kasani cewa wannan BAREWA da kake gani a taredani yanzu, ba dabba bace, wannan mutumne (dan adam) kamarni, (‘ya mace) kuma (yar dan uwan mahaifina), wato (bappana – uncle) kuma ( jininane – dangina),, na Aureta ne tun tana’ buduruwa shekarunta basuda yawa, kuma na zauna da ita tsawon shekaru 30, amma sai dai kuma ALLAH bai bamu haifuwa ba, to adalilin haka sai nasayo wata (BAIWA) na kawota gidana, bayan wani dan lokaci sai BAIWAR ta haifamini (‘DA) namiji kekkyawa kamar farinwata, To muna nan, bayan shekara 15, wannan yaro ya girma, ya soma shiga sahun samari.. a na cikin wannan yanayi, sai watarana (tafiya) ta kamani zuwa wani gari saboda gudanar da al amuran kasuwanci na ..
To daama wannan (yar uwartawa) dake gaba na yanzu ya IFRITU, takoyi ilimin SIHIRI da BOKANCI tun tana ‘yar karama, to sai ta yiwa ‘DAN nawa SIHIRI (dan BAIWAR) ta zamar dashi dan karamin, (BUJUMI),, ita kuma uwar (BAIWAR) ta zamar daita saniya, sai ta daukesu takaisu wurin mai kiyon shanu…. bayan an dauki lokaci mai tsawo, sai na dawo daga tafiya, kuma na tambayi wannan (yar uwartawa) nace mata : ina DANA da matata suka je ? Sai tace mini : matarka ta mutu, DANKA kuma ya gudu, bansan inda ya tafiba, to da naji haka daga gareta sai nayi matuqar bakin ciki, duniyar gabadaya ta zama mini duhu a idanuna, babu abunda yake mini dadi, saboda rashin DANA farin cikin raina da kuma uwarsa, To daga wannan lokaci sai na kasance cikin bakin ciki, kullum sai kuka nakeyi har tsawon shekara 1,, . To ban gushe ba ina cikin wannan hali na baqin ciki, sai da ranaar SALLAR LAYYAr ( EID) ta zagayo, sai na Aika dan gidana zuwa wurin mai kiyon dabbobina nace masa ya kawo mini SANIYA lafiyayya mai qwari wanda zanyi YANKAN LAYYA dashi, jim kadan sai aka zomini da SANIYA irin wanada nake so, Ashe nikuma ban saniba wannan SANIYAR matatace (BAIWA) uawar DA’NA wanda (‘yar uwata) tayiwa asiri, ta zamar da ita SANIYA ..
To daga nan sai muka kwantarda ita saboda in yankata, sai na nade hannayen rigana na dauki wuqa zan yankata .. ita kuma SANIYAR da taga haka sai tayi I’hu, tayi ta yin kuka, nima da naga haka sai tausayi ya kamani nakasa yankata dakaina,… kawai sai nakira dan gidana mai kiyon dabbobina, na Umurceshi da ya yanka ta ya fedeta, shi kuma sai ya yankata, kuma ya fedeta, amma saidai – abun takaici – bai samu komai ajikinta ba, babu nama ajikinta, sai dai qasussuwa da fata, To da naga haka sai nayi nadamar yanka wannan SANIYA, saboda bansamu komai Ajikinta ba, sai nacewa mai kiwon ya kawo mini wata dabbar daban, amma wannan karon namiji nake so (BUJUMI) jim kadan.. sai mai kiwo ya zomini da DAN wannan SANIYA da aka yanka. (wato DANA) wanda aka sihirce sa aka zamar dashi (BUJUMI) bayan mai kiwo ya iso da wannan (bujumi), iso warsu wurin kedawuya sai wannan (bujumi) ya tsinka igiyar da aka daureshi dashi yataho wurina a guje, sai ya yi ta gogar jikin sa da jikina yana kuka, nikuma sai tausayi ya kamani nacewa mai kiwo ya kyalesa ya barsa kar ya yankasa, kuma na Umurceshi da ya kawo mini wani BUJUMIN daban .. To sai wannan mutumi ya cigaba bawa Aljani IFRITU labari, yacemasa : ya IFRITU.. A lokacin da wannan Al-amari yake faruwa a cikin gidana, wannan matartawa dake gabana (BAREWA) kuma (YAR BAFFANA) ta kasance tana zaune a kusa dani tana ganin abunda ke faruwa tsakanina da wannan SANIYA), wanda nasa aka yanka, kuma itace ta tilastamini yanka wannan SANIYA, wanda a karshe ban samu komai ajikinsa ba, kuma nayi nadamar yin hakan.. A lokacinda Aka kawo mini (bujumi) a karo na biyu, kuma naqi yankawa saboda tausayi, sai matartawa ta yi mini I’hu, ta matso kusadani tacemini : wallahi sai na yanka wannan (bujumi) A YAU, kuma a wannan lokaci, saboda wannan ranan ranace mai albarka (layya kenan) kuma babu wani (bujumi) da yafishi Qwari da lafiya, saboda haka dole sai na yankashi, ni kuma sai naqi amincewa, to anan sai tasoma rarrashina saboda in yanka wannan bujimi, kuma bataso in yanka wani daban, nikuma sai nacemata A’A bazan yankaba, saboda wanda nayanka dafarko ma itace ta matsamini na yanka, bansamu Nama ajikinta ba nayi nadama daga baya, saboda haka wannan karon bazan yanka wannan bujumin ba sai tacemini : Narantse da UBANGIJI mai daukaka maigirma sai ka yanka wannan (bujimin) .. idan kuma kaqi to kai ba mijina bane nima ba matarka bane, (bani ba kai).. sai mutumin yacewa aljani IFRITU : ni kuma danaji wannan kakkauasan lafazi daga gareta ya IFRITU sai na rikide.. kuma ban fahimci me take nufiba, atake ban san lokacin da na dauki wuqa na matso kusa wannan BUJUMI da niyar zan yankata…
To A nan sai safiya tariski (Shahar za’d) sai ta dakata, daga bawa sarki labari, ( wato Abun nufi shine : gari ya kusa wa’yewa (shahar za’d) bata gushe ba tana bawa sarki (shahar ya’r) labari, da taga gari yayi haske, sai ta dakata.. sai (dunya za’d) tacewa yar Uwarta (shahar za’d) : kaaai !!! amma yar Uwata, gaskiya wannan labarin naki yanada dadi sosai, ya qayatar damu, sai (shahar za’d) tacemata : to Ai haryanzu bakuji labarin da zanbaku adaren gobeba wanda yafi wannan dadi, amma kuma idan nayi tsawon rai, sarki ba ikasheni ba, shi kuma sarki (shahar ya’r) da yaji haka sai yayi murmushi ya girgiza kansa, kuma – a zuciyarsa – yace : wallahi bazan kasheta ba har sai naji sauran labarun da zata bani, To daganan sai suka kwanta harzuwa fitowar RANA .. Gari ya waye .. RANA ta bullo .. sarki (shahar ya’r) ya shigo fadarsa .. sai ga waziri (mahaifin shahar za’d) ya shigo fadar, da likafini a hammtarsa kamar yadda ya saba a kullum idan sarki ya Auro mace kuma ya sadu da ita, washe gari sai yasa akasheta, to da waziri ya shigo sai ya tseya yana jiran sarki ya bada umurni .. shi kuma sarki ( shahar ya’r) bayan ya shigo fadarsa sai ya zauna .. jama’a kowa da kowa ya bayyana a fada , sai sarki (shahar ya’r) ya gudanar da al ‘amuran masarautarsa kamar yadda ya saba harzuwa faduwar RANA ..
bayan haka, sai Aka watse, kowa ya kama gabansa, .. waziri yana jiran sarki ( shahar ya’r) ya fadamasa wani abu gameda amariyar da ya kawo masa jiya (yarsa shahar za’d) amma sarki baice masa komai ba, .. sai wazrin yayi matuqar mamaki da sarki baice masa komai, .. sai sarki (shahar yar) ya shiga gida abunsa, ya bar waziri shi kadai a fada cikin ruudani…..
Leave a Comment