Hausa Novels

Labarin Dare dubu daya Dare na 2

 DARE NA 2

Da dare yayi, sarki ( shar ya’r) ya shiga gida, sai ya shigo daki ya samu (shahar za’d) da (dunya za’d) suna zaune, Bayan sarkin ya zauna sai (dunya za’d) tacewa yar uwarta ( shahar za’d) yawwa yayata ! ki karasar mana da labarin da kike bamu a daren jiya, ( wato labarin ATTAJIRI da IFRITU ), sai (shahar za’d) tace : yadda kike so haka za’a yi kanwata, zan karasar da labarin amma sai sarki mai alarma ya bani izini .. sarki kuma da yaji haka sai yayi murmushi yace : na baki izini ya ( shaharza’d )bismillah.. To sai ( shahar za’d) tace : ya sarki mai martaba mai wada’ta .. labari ya iso mini cewa : wannan mutumi ya cigaba da bawa IFRITU labari yace masa : ya IFRITU : bayan na dauki wuka sai nanufi inda BUJUMIN yake, na matso kusa da shi saboda in aiwatar da abunda matata takeso.. sai mukayi kokarin kwantardashi, sai shi kuma ya soma kuka yana I’hu, saboda ya fihimci cewar zan yankashi, nikuma danaga haka sai jikina yayi sanyi tausayi ya kamani, kawai sai na jefarda wukar tawa, nafice waje kayana, nakira ‘dan gidana mai kiyo nace masa : ka dauki wannan BUJUMI ka hada shi da sauran DABBOBI ‘yan uwan sa To a nan sai IFRITU ya girgiza kai saboda mamaki da al-ajabi na wannan labari sannan sai mutumi : ya cigaba dabada labari yace : ya mai girma IFRITU bayan na umurci mai kiyo ya tafida wannan BUJUMI.. to sai washegari rana ta 2 (washegarin sallar layya) ina zaune nikadai, ina jimami da bakin cikin irin rayuwa da tsinci kaian ciki.. sai ga wannan dangidan nawa mai kiwo yazo ya sameni ina zaune a karkashin bishiya, sai ya gaisheni yace mini : ya maigidana ! idan ka amince inaso in gaya maka wata magana, kuma zaka yi farinciki da ita, harma zaka yi mini al bishir da kyauta, sai nace masa : ina sauraron ka kafidi abunda ya kawo ka .. sai yace mini : ya maigidana : inada (‘ya – mace ) a gida wanda ta koyi ilimin SIHIRI tun tana ‘yar karama a wajan wata tsohuwa da take tare da mu agida .. 

jiya lokacin da ka bani wannan BUJUMI wanda ka kasa yankawa, kuma kace mini intafi dashi gida in hadashi da sauran dabbobi ‘yan uwansa .. ni kuma da nashiga cikin gidana da wannan BUJUMI, sai ( ‘yar tawa) taga wannan BUJUMI kotsam acikin gida, kawai atake sai tarufe fuskarta da mayafi, sannan sai tayi i’hu tayi kuka .. bayan haka kuma sai tayi dariya tace mini : haba ya BABANA yanzu darajata da qimata tazube a idanka har zaka shigo mini da samari bare cikin gida? .. sai nayi mamaki da jin wannan maganar da ‘yar tawa ta fada mini, kuma na juya bayana banga kowaba .. to sai nace mata : haba ‘yata ! ina kiga samari bare a nan wurin kuma ? .. kuma me yasa kika yi kuka sannan kuma kika yi dariya ?? .. sai tace mini : wannan BUJUMI da ka shigo da shi ba dabba bane mutum ne .( DAN ADAM ) ‘DAN maigidan ka ne .. amma kuma saidai an sihirce sa .. kuma matar mahaifinsa ne ta ta yi masa asiri da shi da mahaifiyarsa (baiwa) ..wannan shine dalilinda yasa nake dariya ..

amma abunda ya sani kuka shine : saboda mahaifinsa yasa an yanka mahaifiyarsa shi ya sa nayi kuka .. Sai mai kiwon ya ci gaba da cewa mai gidan nasa : ni kuma da jin wannan magana daga wurin (‘yata) sai nayi mamaki matuka .. kuma ban jira rana ta gama bullowa ba har saida nazo wurinka saboda in sanar da kai .. Sai mutumin yacewa IFRITU : wallahi ya IFRITU lokacin da naji wannan labari daga wajen wannan dangidan nawa (maikiwo), atake na tashi dani dashi muka kama hanya zuwa gidansa .. ni kuma a wannan lokaci na zama bugegge (ina cikin maye) batare da na sha giyaba, saboda tsananin murna da farin cikin abunda naji, ha rsaida muka iso gidan wannan mutumi .. da shigarmu cikin gidan sai ‘(yar tasa) ta tashi ta yi mini sannu da zuwa ta girmama ni saboda ni maigidan mahaifinta ne .. sannan sai wannan BUJUMI ya matso kusa dani ya jingina jikinsa dajikina, sai nacewa (‘yar maikiwon) : shin abunda kika fada gameda wannan BUJUMI gaskiya ne ? .. sai tace mini : ranka ya dade hakane, wannan danka ne kuma farin cikin ranka, to sai nace mata : (‘yan mata) idan har kika warware wannan sihiri to zan baki dukkan dabbobina da dukiyata da take hannun mahaifinki, sai tayi murmushi tacemini : ranka yadade : ni bana bukatar dukiya sai da sharuda guda 2 ..

na farko : zaka aura mini wannan yaro naka.. abu na biyu kuma : zan sihirtar da wanda tayi masa wannan sihiri, kuma in tsareta a wurina idan ba hakaba ba zan taba kubuta daga makircinta ba .. sai mutumin ya cigaba dacewa IFRITU : a lokacin da naji haka daga (‘yar) wannan maikiwon ya IFRITU sai nace mata : zan baki dukiyar da tafi wanda take hannun mahaifin ki .. amma gameda matata kuma ‘yar bappana (uncle) wanda tayi masa wannan sihiri dashi da uwarsa, jininta ya halatta a greki, zaki iya yin abunda kika ga dama da ita .. To sai ta dauko kwano ta zuba ruwa a ciki tayi tofi a cikin wannan ruwa .. bayan haka sai tayayyafawa wannan BUJUMI tace masa : ya kai wannan BUJUMI idan ubangijin ALLAH ya halicceka BUJUMINE to kadawwama cikin wannan halitta, karka chanza .. idan kuma sihirine aka yi maka to ka koma cikin halittarka ta farko da ikon ALLAH .. jim kadan, sai wannan BUJUMI ya kumbura ya canza halitta ya zama mutum ,,, kawai sai na ga dana ne wanda aka ce mini ya gudu .. atake na rungume shi nace masa : dan ALLAH ka bani labarin abunda matata tayi maka da kai da mahaifiyarka ? .. sai ya bani labarin dukkan abunda ya faurdashi da mahaifiyarsa lokacin da nayi tafiya dagafarko zuwa karshe .. sai nace masa : ya dana : ALLAH ya kawo maka wanda ya cece ka daga wannan kangi ya warware maka wannan sihiri sannan sai mutumin ya cigaba da gayawa IFRITU yace : sannan bayan haka ya IFRITU ! sai na aurawa dana (‘yar) maikiwo .. sai ‘(yar ) ita kuma – maikiwon kuma matar dana – ta sihirce matata (‘yar bappana) ta zamar da ita BAREWA.. kamar yadda kake gani, itace a gabana..to sai ALLAH ya gaddra ya kawo ni wannan wuri na samu wannan attajirin yana zune yana kuka, sai na tambayeshi abunda ya faru dashi, sai ya bani labarin abunda ya faru stakaninka dashi .. 

to ni kuma nace bazan bar wannan wuri ba, har sai naga abunda zai gudana tsakaninka dashi, idan kazo daukar fansa kamar yadda kafada, a karshe yace : ya IFRITU wannan shine labarina .. to a nan sai IFRITU ya girgiza kansa soboda dadi da mamakin wannan labari na wannan mutumi .. sannan sai IFRITUN yacewa mutumin : labarinka abun al-ajabine saboda haka na yafe maka daya daga cikin uku na jinin wannan attajiri.. Bayan mutumi (tsoho) na farko ya gama bada labari, sai mutum na biyu daga cikin matane uku – wanda ya iso wurin a karo na biyu – (mai KARNUKA) ya gabato ya matso kusa da IFRITU ya buga tambarin gaisuwa tareda girmamawa ya yabi IFRITU sannan sai yace masa : ranka ya dade IFRITU idan na baka labarina mai ban al-ajabi tareda wadannan KARNUKA guda 2 da kake gani yanzu a gabana shin zaka yafemini daya daga cikin uku na jinin wannan attajiri ? .. IFRITU yace :eh idan kabani labarinka kuma naga cewa labarin yana da ban al-ajabi, to zan yafemaka daya daga cikin 3 na jinin wannan attajiri da ya da hallaka mini dana .. sai mutumin yace : ya IFRITU ! ya shugaban aljanu : kasani cewa wadannan KARNUKA da kake gani a gabana, ba dabbobiba ne,, ‘Yan Uwana ne (yayu na) nine na ukun su .. wato abunda ya faru shine : mahaifinmu ya rasu ya barmana gaadon dukiya mai yawa, kimanin DINARI (3000),, to sai muka raba wannan dukiyar a tsakanin mu,, bayan mun raba wannan dukiya, ni na sai yanke shawara na bude shago ina saye da sayarwa,, sai daya daga cikin ‘Yan Uwan nawa ya dauki dukiyarsa – ta gado – ya sari kaya dashi,, ya dauki kayan kasuwancin nasa yayi tafiya saboda ya yi kasuwanci a wani garin daban,, To bayan ‘dan uwan nawa ya tafi, tareda a’yarinsa (matafiya) har kemanin tsawon shekara daya,, kawai watarana sai gashinan ya dawo a tsiyace bashida komai ahannusa ya talauce,, kamanninsa ya chanza, ya zama kamar mahaukaci,, sai nace masa : ya ‘dan Uwana : shin ban baka shawara akan kar kayi wanna tafiyar ? sai ‘dan Uwan nawa yayi kuka harsai da yazubar da hawaye sabodaa taqaici,, sannan sai yace mini : ya dan Uwana hakane,, to amma ubangijin ALLAH ya gaddara haka zai faru dani, wannan maganar da kake mini yanzu batada anfani, yanzu banida komai na tsiyace..

to sai na daukesa muka tafi shagona, sannan sai na kaishi gidan wanka ( AWANCHAN ZAMANI BABU BANDAKI KOKUMA WURIN BIYAN BUQATA AGIDAJE SAI A KASUWA AKEZUWA ABIYA KUDI) bayan ya gama wanka.. sai na sayamasa tufafi mai tsada na daukeshi muka tafi wurin cin abinci,, to bayan haka, sai nace masa : ya ‘Dan Uwana : na yanke shawara zan hada ribar da nake samu daga shekara zuwa shekara, sannan sai in rabana a tsakaninmu,, To sai na irga ribar da nasamu a shekara,, naga ya kai kimanin DINARI (2000),, na yi farin ciki matuka, na godewa ALLAH madaukakin sarki,, 

sannan na raba mana wannan kudi a tsakaninmu,, sai muka cigaba da saye da sayarwa shekara da shekaru mana cikin garin mu batare da munyi tafiya zuwa wani gariba. ana nan, watarana sai ‘yan Uwan nawa guda 2 suka yi niyyar yin tafiya (bulaguro) da nufin kasuwanci zuwa wani garin, kuma sukabuqaci in tafi tare dasu, amma ni kuma naki amincewa kuma nace musu : wace riba kuka samu a tafiya ku ta farko, da har zan biku wannan karon dan in samu,? sai suka sa naci suka matsamini sai muntafi tare, amma duk da haka nikuma naki amincewa,, to sai muka cigaba da zama muna saye da sayarwa har tsawon shekara 1, basu gushe ba, kullum suna yi mini maganar tafiya, suna kodaita mini, ni kuma ina kawarda kaina, naki amincewa,.. anacikin haka kullum suna mini maganar yin tafiya hartsawon shekara 6, ana nan har saida watarana na Amincemu su da muyi tafiyar,, kuma nace musu : ya yan Uwana yakamata kafin mutafi mu irga kudaden da suke hannunmu kafin muyi tafiyar,, sai muka irgasu muka ga sunkai kimanin DINARI (6000),, sai nace musu : yakamata muraba kudinnan kashi 2 mu bar rabi a gida saboda idan bamu yi sa’ar fita ba jarinmu ya karye ko bala’in talauci ya samemu muka tsiyace sai muyi anfanida kudinda muka bari a gida,, sai sukace : hakane madalla da wannan ra’ayi naka,, 

sannan sai na dauki kudin na raba shi kashi 2 na binne rabi a rami, sannan rabin kuma sai na bawa kowannen su DINARI ( 1000 ) nima na dauki nawa,, bayan haka sai muka shirya kayanmu muka dauki hayan jirgin ruwa ( kole kole ) muka zuba kayanmu gabadaya a ciki, muka kama hanya muna ta tafiya har tsawon wata 1, sannan watarana muka isa wani gari, kuma muka sayar da kayakin mu na kasuwanci, sai muka samu ribar DINARI 10 a cikin kowane DINARI 1.. sannan sai muka yi shawarar yin wata tafiyar daban, dan cigaba da harkar kasuwanci.. sai muka kama hanya muka nufi tashar jirgin ruwa.. bayan mun isa bakin kogi inda tashar jirgin ruwa yake,, kawai sai muka hadu da wata yar buduruwa tana lullube da dankwali, kuma almunta yanuna cewa ita ba ‘yar gata bane.. sai wannan buduruwa ta gaisheni tace mini : ranka ya dade….Shin zaka iya mini( ihsani) kyautatawa nikuma insaka maka da alheri ?? . sai nace mata : zan yi miki (ihsani) kyautatawa da alfarma koda ko baki yi mini sakayyaba.. sai tace mini : ranka ya dade.. inso ka Aureni kuma ka daukeni zuwa garinku, Ni nabaka kaina, kai kuma idan ka aureni to ka kyautatamini, saboda nima watarana zan yi maka sakayya.. Da naji wannan magana daga gareta ya IFRITU sai zuciyata ta karkata zuwa gareta, kuma na amince na Aureta, sannan sai na sayamata tufafi na dauketa muka shiga jirgin ruwa (kole kole) muka samu wuri a gefe muka zauna muka yi rayuwarmu ta ma’Aurata.. kuma hakika zuciyata taso wannan budurawa, sai na zamanto ina tareda ita dare da rana, na shagala da ita, har ya zamanto bana kula ‘yan uwana guda 2 – damuka tare -, to a dalilin haka sai ‘yan uwan nawa guda 2 suka soma kishi dani, kuma suka yi mini (hasada) saboda yawan dukiyata.. suka sa koday) a cikin dukiyata gabadayanta, hudubar shaidan tayi tasiri a zukatansu, suka yi shawarar halakani su mamaye dukiyata… To bayan ‘yan uwana sun gama shawara cewar zasu kashini su wawure dukiya… ana nan, cikin dare, sai ‘yan uwan nawa suka zo suka sameni ina bacci dani da matata, suka dauke mu suka jefamu cikin kogi….

a nan sai safiya ta riski (shahar za’d) ta dakata da bawa sarki ( shahar yar) labari… shi kuma sarki sai ya tashi ya tafi fadarsa saboda ya gudanarda al’amura kamar yadda ya saba… kuma yau ma waziri yazo da likafanisa, amma sarki baice masa komai ba, sai ya koma gida kayansa cikin rudani……

Leave a Comment

error: Content is protected !!