Hausa Novels

Labarin Dare dubu daya Page 1

 KASHI NA 1

( kafin ka soma karanta DARE NA 1 wannan labari yana da matuqar muhimmanci ka karanta shi, idan baka karanta ba baza ka gane ba ) 

LABARIN FARKO DAGA LITTAFIN (DARE DUBU DA DAYA) 

kafin daren farko An rawaito wani labari cewa : akoi wani sarki a qasashen (india da chaina) wanda allah ya bashi (‘ya’ya) maza jarumai guda 2, sunan babban (shaharya’r) karamin kuma (shahi zama’n) kuma masarautar tasa tana da girman gaske. . To ananan.. watarana sai wadannan jarumai guda 2 suka gaji masarautar mahaifinsu, kowanne daga cikinsu yana mulkar wani bangare daga cikin masarutar, To ananan komai yanatafiya daidai – kamar yadda yakamata -har taswon shekaru 20 sai wata rana babban sarkin maisuna (shaharya’r) ya buqaci ganin dan uwansa maisuna (shahizaman) – wanda shima sarkine awani bangare na qasar – . to sai sarki (shahar ya’r) ya aika wazirinsa zuwa garin dan uwanasa sarki (shahi zaman) ya sanardashi cewa dan uwansa sarki ( shaharyar) yanabuqatar ganinsa… 

To sai waziri yakama hanya ya nufi inda aka’aikeshi, kuma ya sanarda sarki (shahi zaman) cewa dan uwansa (sharyar) na buqatar ganinsa, to sai sarki (shahizaman) ya amasa kiran dan uwansa, washe gari ya shirya ya kama hanya zuwa garin dan uwansa (shaharya’r), bai gusheba yana ta tafiya harsaida ya iso bayangari, sai ya tuna wani abu da yamanta agida (wato tsarabar dayakeso yabawa dan uwansa)..To kawai. sai ya juya ya koma gida saboda ya dauko abunda yamanta… to bayan ya iso gida sai ya shiga daga ciki, kuma ya isa dakinsa.. to Me zaigani acikin dakinsa.. ? kawai da yashiga daki sai ya iske matarsa tareda baqin bawa akan gado suna rungume dajuna.. sai yace : (a zuciyarsa) yanzu gashi ban bar garinba, amma ga abunda ya faru, to idan nabar garin kuma menene zaifaru kenan ? 

kawai atake yacire takobinsa yapille musu kayi.. . daganan sai yafita abunsa, ransa abace, yakama hanya zuwa inda yanufa dafarko.. baigusheba yana ta tafiya harsaida ya isa masarautar dan uwansa (shaharyar),, sai sarki (shar yar) yayi farincikin isowar kaninsa sarki (shahi zaman ). kuma yatara (muqarrabansa) da manyan gari saboda tarbar (shahi zaman).. bayan haka, sai suka zauna tare suna hira cikin annashawa da jindadi, jim kadan sai sarki (shahi zaman) ya tuna abinda ya faru a gidansa kafin iso garin dan uwansa ( wato abinda matarsa tayimasa), atake sai yashiga wani yanayi na bakinciki.. launin fuskarsa ta chanza.. 

idanunsa suka nuna alama.. To da (shahar yar) yaga haka sai yazaci cewar wataqila saboda barin gida da yayi shi yasa ya shiga wannan yanayi nadamuwa. sai yabar sha’aninsa bayyi masa maganaba.. To dama dagacikin al a’dun AL UMMAR wannan zamani.. idan mutum ya samu kansa cikin damuwa da bakinciki, to zai fita zuwa daji yayi farauta, kokuma yayi tabin namun daji soboda ya kawarda damuwar dake taredashi to Ananan, bayan wasu yan kwanaki, sai sarki (shaharyar ) ya cewa (shahi zaman) ya (dan uwana) naga jikinka yayi rauni.. launinka ya sauya kamar kanacikin damuwa ?

sai (shahi zaman) yacemasa : Akoi qurji a cikin zuciyata (damuwa).. amma yaqi gayamasa abunda yafaru, to sai (shaharya‘r) yacemasa : inaso dani dakai mutafi farauta… wataqila ko damuwarka zatagushe.. ka samu sanyi acikin zuciyarka.? amma sai sarki (shahi zaman) yaqi amincewa dazuwa farautar.. to sai (shaharya’r ) ya kama hanya yayi tafiyarsa, yabar dan uwansa agida… To dama gidan sarki (shahar ya’r) yakasance mai hawa 2 ne.. kuma (shahi zaman) yana zaune Ahawa na 2.. kuma wurin da yake zaune yana fuskantar wani wuri da Ake shaqatawa (lambu),, to bayan (shahar yar ) ya tafi farauta yabar dan uwansa agida, (shahi zama’n) kuma shahi zaman din ya kasance yana zaune shikadai, yana tunani, jim kadan sai yaga anbude kofar fadar (dan uwansa), kuma sai yaga matar (dan uwannasa) ta fito tareda (‘yan mata) guda 20 (kuyangun gidan sarki) da kuma samari (bayi) suma su 20 sun shiga wurin shaqatawar, matar (dan uwannasa) tana tsakiyarsu.. bayan sun shiga wannan wuri.. sai suka shiga wurinda ake wanka (semen full – ko – tapki).. sai kowa ya tube kayansa, sai matar sarki tacewa daya daga cikin samarin :(ya mas’udu) Sai ga wani baqin bawa matso, sai ta rungumeshi, kuma haka sauran (yan matan) da samari suma sukayi, (ataqaice) an shaqata, an chashe, a cikin wannan lambu harzuwa faduwar rana, Kuma wannan duka yafarune a idon sarki (shahi zaman) yana zaune yanakallo.. da sarki (shahi zaman) yaga haka ya faru a idansa sai yayi mamaki, yace : (a cikin zuciyarsa) : wallahi wannan bala’in yafi wanda akayi agidana, (wato abinda yake nufi : fasadi da akayi a Idansa a fadar (dan uwansa) kuma da matar dan uwannasa.

yafi wanda akayi masa a gidansa) wanda shine dalilin kasancewarsa cikin damuwa, To da sarki (shahi zaman) yaga wannan sai hankalinsa ya kwanta, kuncin zuciyarsa tagushe.. soboda yaga cin amana wanda yafi nasa, kuma an yiwa wanda ya fisa mulki da sarauta, Saboda haka yake farinciki, kuma daama tun lokacinda (shahi zama’n) yazo wajan (dan uwansa) yaqi yaci komai saboda halinda ya samu kansa aciki.. amma bayan yaga abunda yafaru a idansa sai ya koma hayyacinsa yasoma cin abinci kamar yadda yakamata… To. Ananan sai ga sarki (shahar ya’r) ya dawo daga farauta, sai ya shigo wurin (dan uwansa) suka gaisa, sai (shahar ya’r) ya luura da (dan uwansa) yaf ahimci cewar yanayinsa yacanza, wato yana cikin farinciki da annashwa bakamar yadda yatafi ya barsaba, kuma yaga yanacin abinci kamar yadda yakamata, bayan dafarko yaqi yaci komai.. to sai (shahsr yar) yayi mamaki, kuma sai yacewa dan uwan nasa : kafin intafi farauta naga kamar kanacikin wani hali nadamuwa,To amma yanzu kuma na dawo na ganka cikin fara’a da annashwa ? dan ALLAH ka bani labari menene yake furuwa ?? sai (shahi zaman) yacemasa : zanbaka labarin abinda ya sani cikin farinciki da annashwa.. amma zakayimini afuwa saboda abida zanfada ba zai maka dadiba…. sai (shahar yar) yacemasa : dafarko kabani labarin dalilin kasancewarka cikin damuwa da bacinrai inji tukuna… to sai (shahi zama’n) yacemasa : kasani cewa A lokacin da ka aiko wazirinka zuwa wurina, na shirya na kama hanya har na iso bayangari.. sai nayi mantuwa, atake sai na juya na koma gida saboda indauko abinda namanta, iso wata gida sai nashiga dakina nasamu matata dawani bawa akan gado, suna lalata, Atake sai nacire takobi na kashesu.. to daga wannan lokaci sai na kasance cikin bakinciki da tunani harzuwa lokacinda na iso wurinka,

to wannan shine dalilin kasancewata cikin wannan hali na taqaici.. amma abunada ya sani farinciki da annashawa kuma : sai ya bashi labarin dukkan abunda yaga matarshi tayi tareda (yan mata) da (bayi) a cikin lambu a lokacin da ya tafi farauta sai (shahi zama’n) yacemasa : wannan shine abunda yasani farinciki, saboda anci amanar wanda ya fini mulki da sarauta, shiyasa yanzu kaga ban damu ba.. Dasarki (shahar ya’r) yaji wannan labari sai yayi mamaki, amma kuma sai ya nuna rashin yarda da abunda dan uwansa ya fada masa, To sai ( shahi zaman) ya fahimci cewa dan uwannsa bai yarda dashiba, sai yacemasa : Idan kanaso ka tabbatar dahaka.. to kabada Umurni asanar cewa zakatafi farauta kamar yadda ka saba, Idan aka fitar da dawakai kuma ‘yan rakiyaka suka fito zuwa bayan gari, to kai kuma sai ka lullube jikinka kabatar da kamanni, ka sulale ka juyo ka dawo gida abunka, saboda ka ganewa Idonka abunda zai faru a gidanka, kuma kagayawa wadanda suka rakaka kar kowa ya biyoka a lokacinda zaka juyo ka dawo fadarka To sai sarki (shahar ya’r) yayi kamar yadda dan uwansa ya gayamasa. ya bada umurni a sanar cewa zaiyyi tafiya, aka fitar da dawakai .. yan rakiya sun shirya sun fito zuwa bayan gari.. kuma sarki yana taredasu.. da Isarsu bayan gari sai sarki ya sulale yajuyo ya dawo gida bayan ya badda kamanni, kuma ya bada umurnin kada kowa yabiyo shi.. To sarki (shahar ya’r) ya shigo fadarsa a boye, kuma ya labe saboda yaga abunda zaifaru, jim kadan sai ga matarsa tafito tareda yan mata da (bayi) an shiga lambu an shaqata an chashe har zuwa faduwar rana, kamar yadda dan uwansa ya bashi labari, Da (shahar ya’r) yaga abunda ya faru sai yarude yarikide ya dimauce..

kuma ya yarda da abunda dan uwansa ya gaya masa To anan sai (shahar ya’r) ya tuna wasu baitoci ( acikin harshen larabci) kamar haka

(( ﻻ ﺗــﺄﻣـــﻨــﻦّ ﺇﻟـــﻰ ﺍﻟﻨﺴـــــــﺎﺀ ﻭﺗـــــﺜــــﻖ ﺑﻌـــﻬــــﻮﺩﻫــ ـــﻦّ(( )) ﻳـﺒـﺪﻳــــﻦ ﻭﺩّﺍ ﻛــﺎﺫﺑــــﺎ ﻭﺍﻟـﻐـــﺪﺭ ﺣــــﺸـــﻮ ﺛﻴـــﺎﺑــﻬـــــﻥّ(( )) ﺑﺤـﺪﻳــــﺚ ﻳــﻮﺳــﻒ ﻓﺎﻋﺘـﺒــﺮ ﺳﺘــﺮﺍﻩ ﺑﻌـــﺾ ﺧـــﺪﺍﻋـﻬـــﻦّ (( )) ﺃﻭ ﻣــــﺎ ﺭﺃﻳـــﺖ ﺃﺑـــﺎﻙ ﺁﺩﻡ ﺧــﺎﺭﺟـــﺎ ﻣـــــﻦ ﺃﺟـﻠــــﻬـــــﻦ ّ)) 

FASSARAN BAITOCI : (Kada ka amincewa mata, kuma kada ka yarda da alqawarinsu) (zasu nuna soyayyar karya, al halikuwa yaudarace acikedasu)) (Kayi la’akari da labarin annabi yusufa zaka fahimci makircinsu)) (ko bakaga an fitarda Babanka Adama daga aljanna sabodasuba) Bayan (shahar ya’r) ya ga abunda matarshi tayi sai yacewa (shahi zama’n) yanzu nayarda dakai.

To sai yacemasa :

inaso ka tashi dani da kai mubar masarautarmu mushiga yayon duniya ko zamu hadu da wani wanda ya fimu mulki da iko, wanda shima aka yimasa irin wannan cin amana da ha’inci… Idan muka samu wanda aka yimasa haka, to hankalinmu zai kwanta, amma kuma idan bamu samu wani wanda akyi masa hakaba to fa mutuwarmu tafi rayuwarmu anfani, sai (shahi zama’n) ya amincemasa. To daga nan sai suka fita aboye babu wanda ya sani, basu gusheba suna ta tafiya a cikin dajin allah – dare da rana kwana da kwanaki – Har sai da suka iso kusada wani babban kogi – mai dandanon gishiri – wanda a gefensa akoi wani bishiya da kuma wani dan tapki (qaramin kogi) wanda matafiya suke sha ruwa daga ciki, To sai suka zauna aqar qashin wannan bishiya saboda suhuta bayan sunsha ruwan wannan tapkin. bayan wani danlokaci – suna zaune sunahutawa – sai suka ga ruwan wannan babban kogi yana tashi sama yana qara (kamar tafasa ), yana kumfa, bayan haka sai ga wani abu baqi kamar hayaqi mai tsayi (kamar polwaya) ya fito daga cikin wannan kogi, kuma ya nufi inda suke zaune, .da suka ga haka sai suka razana suka tsorata suka hau saman wannan bishiyar dan subuya suga ikon allah menene zaifaru ?? jim kadan sai wannan abu da ya fito daga cikin kogi ya canza ya zama wani jibgegen IFRITU (Aljaini), mai tsawo, mai jiki..mai fadin qirj, yana dauke da akwati akansa, To sai IFRITUN ya iso wurin wannan bishiya, ya zauna yabude wannan akwati ya ciro wani kwalba a ciki..

sannan sai ya bude wannan kwalba, sai ga wata buduruwa kekkyawa ta fito daga cikin wannan kwwalba, sai IFRITU ya kalli wannan buduruwa yace : ya gimbiyata, ya sarauniyar mata, wanda na satota ranar bikinta. inaso inyi bacci kadan ya gimbiyata, sai IFRITUN ya daura kansa akan cinyoyinta yayi bacci abunsa, to bayan IFRITU yayi bacci, kansa akan cinyoyin buduruwar, ita kuma tanazaune aqarqashin wannan bishiya, Bayan wani dan lokaci sai tadaga Idanunta sama takalli wannan bishiya sai taga (shaharya’r) da (shahi zaman) akan bishiyar, sai ta sauqarda kayin IFRITU daga kan cinyoyinta tamike tseye, tayi musu nuni dahannu tacemusu : kusauko qasa kar kuji tsoron wannan aljanin… sai sukacemata : dan allah kiyi mana afuwa bazamu iyaba munatsoro, sai tace : to wallahi idan baku saukoba zan tayarda IFRITU kuma insa yayi muku mummunan kisa, sai sukaji tsoro suka sauko suna karkarwa, bayan sunsauko, sai takallesu tacemusu : Inasokuyi lalata dani, idan kunqi kuma zan tada IFRITU ya kasheku.. sai suka kalli juna suka soma gardama, sai (shahar ya’r) yacewa (shahi zama’n) kai ka somayi, (shahi zama’n) yace : A’A, kai zaka soma, ni ba zan yiba sai kayi…. Suka cigaba da yin gardama agabanta… sai tacemusu : ya naga kuna gardama ? Idan baku matso kunyi abinda Na umurcekuba to wallahi zan tayarda IFRITU ya muku mummunar kisa.. sai suka tsorata sukayi abunda ta Umurcesu dashi (sukai lalata da Ita) . … 

To bayan sun gama sai ta Umurcesu da sumike tseye, sai taciro wani jaka daga cikin aljihunta wanda a ciki Akoi zobe guda (daribiyar da sabain) 570… sai tacemusu : ko kun san menene wannan ? sai sukace : A’A… sai tacemusu : wadannan zobunane kamar yadda kukagani, kuma masu wadannan zobuna dukkansu sunyi lalatadani Alokacinda wannan aljani yake bacci, kamar yadda kukayi, sai ta cigaba dacewa : kuma bayan kowannensu yayi lalatadani sai inkarbi zobensa, sabodahaka kubani zobenku kamar yadda nakarbi zoben sauran mutane.. sai suka bata zobensu… bayanhaka sai tacemusu : kunga wannan Aljani da yake taredani wanda ya kebacci … ya satoni ne Ranar Aurena.. sannan sai ya sakani acikin kwalba.. sannan sai yasaka kwalbar ackin akwati.. sannan sai ya kulle akwatin da kwado (makulli) guda 7.. kuma ya boye akwatin a ckin teku (kogi) inda dan ADAM bazai iya zuwaba saboda kishin kar wani ya ganni. Amma kuma shima baisan cewa su (mata) Idan suka so yin abunda zuciyarsu ta rairaya musu, to babu mahaluqi da zai iya hanasu aikatawa. To wadannan sarakunan biyu sunji abunda wannan buduruwa ta gayamusu, sai sukayi mamaki matuqa ! sannan sai sukace : Idan ya kasance wannan Aljanine wanda ya fimu iko da mulki.. kuma (‘ya mace) tayi masa abunda yafi wanda akayi mana ! To Ai Namu mai sauqine, kuma wannan abune wanda zai daukemana kewa, tunda an ci amanar wanda ya fimu, To daganan sai suka juya suka koma gida… 

ABIYOMU A KASHI NA 2 

zaku ji matakin da zasu dauka idan suka isa gida … kuma zaku ji yadda ta kaya.

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!