Labarina Hausa Novel Complete
LABARINA
Tsaye suke jikin su sanye da uniform na makarantar secondary din kantitin cikin makarfi road dake Rigasa kaduna.
cikin layin dake kusa da makarantar suke a tsaye akofar wani gida, ‘yan matane guda biyu dogaye kansu daya, daya daga cikinsu sunanta ARWA black beauty ce, round face, kyawawan kwayar ido, yalwataccen gashin gira Dana ido take dashi.
Sannan dayar itakuma farace siririya me kyangaske, doguwar fuska gareta dauke da manyan idanuwa da kwayar ido masu launin Brown, tsararren gashin gira Dana ido kamar wacce akaimata kari Dana kanti, karamin baki gareta dauke da jerarrun hakora fararetas hade da siririyar wushirya a tsakani agefen kumatunta Kuma dimples ke bayyana aduk sanda tai dariya,
sannan gashinta hargadon bayanta yake sauka baki me laushi ga sheki KHALEESAT kenan.
Murmushi tayi tace Hummmm kawata kinki barina intafi gida tundazu, gashi yanzu har karfe nawa?
Arwace takalli agogon dake wayar hannunta tace karfe 3:30pm ne fa kawai,
Karanta Littafin Muradin Rai Hausa Novel Complete
Take yanayin fuskarta ta canja, cikin damuwa tace yauna shiga uku agurin ALAJA, wallahi danasan ruwan baze tsagaita da wuriba Dana tafi acikin shi.
Harara Arwa ta watsa Mata tace keda kikasan matsalarki sannan saboda fadan da za’a Miki seki tafi ruwa yamiki dukanda se yajamiki zazzabi ko? cab! Tabe baki tayi sannan tacigaba da cewa yakamta yanzu ace kinsaba da fada, kidena cutar da kanki tinda kinsan kina da gaskiya. Murmushin kafi kuka ciwo Khaleesat tayi tace bazaki taba ganewaba nidai yanzu zoki rakani bakin titi ko achabane inhau inwuce gida Dan wallahi yanzu innace zantafi akafa zankara bata wani lokacinne da setasa andakeni.
To muje har sun Fara tafiya Arwa tace tsaya! tsaya! Kinama da kudin mota kuwa?
Tace inafa kezaki bani kinsan jiya banyi mata cinikin shago yakai 2k ba balle tabani kudin mota yauma akafa nazo,
Arwa tace to jirani inje indakko Miki kokuma kizo mukoma gidan tare inba hakaba Kisha jira danni senama cire wannan uniforms din Dan bazan iya karasawa titi dasu ajikina ba
Wata muguwar harara Khaleesat ta watsama Arwa tareda faÉ—in da wani munafuncinne yahanaki cirewa tuntuni?
Hada hannuwa Arwa tayi guri guda tace ba munafurci bane Ranki ya Dade mantawa nayi Kuma in Gimbiya ta Amince Ina neman Alfarmar damar shiga cikin gida, dariya sukayi suduka alokaci daya,
sannan Khaleesat tace Dan Allah jeki fito karki Dade Ina nan Ina jiraki.
Shigar Arwa cikin gida keda wuya sega wata katuwar motar kirar Range Rover melaunin ruwan toka ta taho da gudu………… batayi auneba sejin ruwan tabo tayi ya wanke mata fuska tare da uniform din dake jikinta gashi kiris yarage ma yabigeta tai saurin matsawa tana tafiya da baya da baya harseda takai da tafadi kasa,
Kafin kace meye wannan mutane harsunfara taruwa,.
Shiko Mai motar wucewa yayi kamar bazai tsaya ba Amma da yadan Kara gaba kadan da motar sai yayi parking. Ya futowa da gudu ya nufi inda take matsar da mutane ya shiga yi cikin sauri, Kai jama’a abunkallo ba ya kadan gun mutane yafada acikin ransa.
A zaune yaganta, sai shima ya tsuguna Yana fuskantar ta cikin natsuwa yace sannu baiwar Allah, yauwa ta amsa dashi dai dai lokacin da take dago kanta sukayi ido biyu da juna,. Mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta tare da shiga wani bakon yanayin da tunda tazo duniya Bata taba shiga irin shiba sakamakon mayatattun idanuwan shi da sukayi Mata dirarmikiya a nata idanuwan. shima a bangarenshi irin yanayi daya suka shiga ko ince ma nashi yanayin daya shiga nafi nata ninkin ba ninkin, anan kowannensu kasa kauda Kai yayi Sunkai gurin minti daya ahaka suna kallon junansu.
Muryar Arwace tadawo dasu daga Duniyar kallan kallon da suka shiga! Cikin rudewa take faÉ—in “Subhallahi Khaleesat meyasameki?”
Da sauri Khaleesat ta kawar da kanta daga fuskar matashin, sai dai Kafin Khaleesat din ta amsama Arwa tanbayar ta shi yayi sauri ya amsa mata da “no bawani abu bane in Sha Allah ba’abunda zesameta tashi kinji sannu” mikewa tayi tareda fadin ba komai Arwa.
Hannu yasa acikin aljihun shi yafito da wani kyalle fari tas yamika mata yace gashi kigoge danttin fuskarki,
sannan yakara da tanbayar Allah yasa dai bakiji ciwoba? Kai kawai ta daga mishi alamar eh.
Dadai yaga lafiya_lafiya kuma jama’ar dasuka taru sunwatse seyacemata sannu Allah yatsare nagaba,.
Se anjimanku nagode, tunda ya wuce bekara ko wai gowaba yaja motarshi yayi gaba.
Abangaren su kuwa Khaleesat ce kemagana tana fadin nikam yau nashiga uku yazanyi? Sannan tawaiga ta kalli Arwa tace ni bani kudin motar inkindakko min inwuce gida
Cikin mamaki Arwa tace Mene? tareda bude baki dazare ido, aiko kinsan dai bawanda zedaukeki akan mashin dinshi da wadannan kayan masu dattiko.
Dan Allah yakikeso inyinewai?,
Arwa ta amsamata da aiko zuwa za kiyi mukoma cikin gida kiyi wanka inbaki kayana kisa sannan kiwuce gida,
Wai ke ba kya ganin irin sabon hadarin dake sake haduwane, Kuma kinsani sarai indai bada wannan dattin najema da Alaja ba bazata taba yadda daniba kome zance mata ko?
Ganin irin damuwar da Khaleesat din ta shigane yasa Arwa ta dafa kafadarta tace karki damu muje Dan gaskiya bazan iya barinki dawannan dattin duk inda kikabi adinga kallonkiba please muje nasan in Sha Allah kafin kigama shiryawa YAYA AAHIL yadwo seyakaiki har gida tafada dai dai lokacin datakalli agogon dake daure a hannunta tace nasan yana hanya yanzu. Amma kina……….? Arwa ta dakatar da Khaleesat ga abunda takeson fada tace please banason Jin Amma dinnan zomuje kawai
Rikemata hannunta tayi tare da bude gate din gidan suka shige.
Direct Fallon kasa suka nufa HAJIYA ASMA’U suka tarar zaune kan kujera tana latsa remote, Jin motsin shigowarsu ne yasa ta waiga takallesu fuskarta dauke da farin glashi tace,
“A’a Khaleesat dama baki wuceba?”
Kunfifa mintuna Arba’in dafita daga gidannan tafada yayin da takalli kayan jikin khaleesat sannan takuma tanbaya, mekuma yafaru naga duk ta jike ga datti kota Ina lafiya daiko? Arwa tabata labarin dukkan abubuwan dasuka faru awaje, Allah ya kyauta ai saikije kiyi wanka kicire kayan, Momy Nima dama Haka nace Mata tunda Kinga Yaya Aahil yakusa dawowa ba saiya kaita ba? Haj Asma’u ta amsa Mata da eh Hakan ma yayi, sukuma suka wuce daki.
Mikewa hajiya asma’u tayi tareda shigewa daki domin dauro alwala sakamakon kiraye kirayen sallar la’asar din dake tashi Kota ina.
Bayan shigarsu dakine khaleesat tashiga toilet tasakarma kanta ruwan dumi, tana wanka ruwan dumin na ratsata rufe ido kawai tayi, Sosai takejin dadin ruwan sakamakon Sanyin garin saboda wuni da akayi Ana ruwan sama a garin na kaduna. Ahankali dukkanin abubuwan da suka faru Bayan fitarsu suka Fara dawomata kwakwalwa kamar Mai kallon TV take ganin komai hakan yasa gabadaya Tama manta da batun fadan da Alaja zata Mata intakoma gida, mummunan faduwar gaba ta tsinci kanta aciki sakamakon tuna kyakkyawar fuskar saurayin nan daya kusa bigeta dazu da mota, da sauri tabude ido tareda hanzartawa daga wankan bayantagama dauro alwala tayi tafito, Arwa tagani zaune abakin gado dauke da waya tana buga game din ZUMA motsin futowar khaleesat ne yasa Arwa ajiye wayar tareda fadin Kai kawata shine kikaje kikai zaman ki abayi kamar wacce zata……….Karan saukan ruwan datajine yahanata karasa maganar datai niyya, tareda zare ido tana fadin ikon Allah yaudai marka marka mukesha a kaduna, itako Khaleesat babu abunda take fadi se Alhamdulillahi Alaakulli halin cikin damuwa taketa Mai maitawa, sannan takara da fadin nidai yau babu abunda zanma Allah se godiya domin shikadai yasan dalilin yin hakan,
Arwa ta amshe zancen dafadi gaskiya kam Allah ne mafi sani akan komai.
Kaya Khaleesat tasa sannan tagabatarda sallah itama Arwa haka, sannan suka zauna suna hira agabansu ga kayan ciye ciye da abubuwan Sha Wanda Arwa ta debo musu daga fridge din kitchen.
Mikewa Khaleesat tayi tana fadin ummmm nidai bari inje intaya momi aiki a kitchen inzaki taso muje mikewa itama tayi tareda fadin dama kuwa yau abincin ku yarbawa tace zatayi AMALA da miyar AYAYO Shikenan ma Kinga tazo gidan sauki se intuke mata ita tas Khaleesat tafada tareda fara tafiya, takai dede kofar fita daga dakin takusa faduwa dasauri Arwa ta rukota tana fadin Inna nillahi wa Inna ilaihirraji’un, sekuma tafashe da dariya , haushinta ne yakama Khaleesat daure fuska tayi tana ballamata harara tace meye haka kosannu babu Amma kinamin dariya ko wato dadi ma kikeji zan fadi?
A’a wallahi badan Zaki fadi ne nake dariya ba cikin dariyartake cigaba da magana tana fadin skirt dinnan dakikasane yabani dariya duk yamiki yawa to kece kinki kiyi kiba kullum jiya iyau kamar bafulatana ba beyerabiyaba.
Hummmm wayasani to wai tayama za ayi inyi kiba Bayan agidanmu kullum Ni Mai laifice a idon Alaja bantaba yin wani abun burgewa agurin ta ba , Ni zomu tafi jan hannun arwa tayi suka nufi kitchen.
Hajiya asma’u suka gani tagama tsabtace ganyen ayayon ta zata zubashi a turmi, jin muryar Khaleesat ne yasa ta dakata da zuba ganyen ! Momi sannu da aiki, ta amsa da yauwa sannu yayin da ta kalli inda suke.
Arwa Kuma budar bakin sai tace Momi memakon kisa UWALE me aiki tadaka Miki shine zakiyi da kanki?, murmushi kawai momi tayi tace ai sanin kankine bansan uwale ta tabamin komai na abinci, nafison inyi komai da kaina ko?.
Khaleesat ce ta karbe zancen da rabuda ita momi ai tasan komai gulmace kawai, momi ta amsa da eh Mana ai dama ita dince, Harara Arwa ta aikama da Khaleesat tana fadin to kanwa anji. taya momi aikin abincin sukayi suka gama gab da magariba, har a wannan lokacin ruwan sama akeyi kamar da bakin kwarya be tsagaitaba se bayan sallar magariba.
Fitowa Khaleesat tayi Arwa nabinta abaya tana kiransunanta, tareda fadin haba Khaleesat yazakiyi kice Zaki tafi acikin wannan sanyin kibari yaya Aahil yadawo mana, shima yau ko ina yatsaya haryanzu be dawoba , haka dazuma kikacemin gashi har yanzu shiru nikam tafiya zanyi, dandai bakisan mezanje intararbane shiyasa kiketa hanani tafiya.
Wallahi bahaka bane jin muryar momi sukayi a falon tana magana bakinta cike da abinci , “Khaleesat lafiya ina zakije haka awannan sanyin? wai kinma ci abincin kuwa? Eh naci momi yanzu kuma gida zanje amma Arwa takeso ta hanani tafiya tana magana tana kokarin kwace hannunta daga cikin na Arwa cikin yanayi damuwa da santafiya gida take magana.
Momi tace to ainima bazan barki kifita ki hau mashin a sanyinnan ba kijira Aahil yadawo yakaiki inkuma bedawo da wuribama to gaskiya sedai ki kwana gobe kya koma gida, cikin damuwa khaleesat tace to amma momi………… dakatar da ita momin tayi tana fadin Kinga nidakaina zanje gidan naku insamu alaja inmata bayani.
Amsawa tayi da toh momi Arwa kuma taja hannunta suka koma daki, suka cigaba da kallon TV dake makale a bangon opposite din gadon dakin Arwa suna dan taba hirar makaranta suna haka har aka kira sallar isha’i sukayi sallah suka dora da wata sabuwar hirar.
Suna tsakiyar hirar tasune har misalin karfe 10:00pm Wanda yayi dai dai da jin karar shigowar motar Aahil.
Khaleesat ta daga hannu sama tana fadin ALHAMDULILLAH ga yaya Aahil dinnan ma ya dawo yanzu sai tafiya gida shiyasa dama naki bari bacci ya daukeni, cab yanzu kam ai dare yayi bayadda za’ayi kije gida nasan ita kanta Alaja tayi bacci yanzu Arwa fadi tana kallonta, murmushin kafi kuka ciwo Khaleesat tayi tareda fadin Hummm yaudai yatabbata sena kwana agidanku kenan, banza Arwa tayi da ita ko kallon inda take ma batayiba aranta Kuma tana fadin ai seki tashi kitafi.
Bayan gabatar da shafa’i da wutirine ko waccensu tasa kayan bacci sukayi addu’on bacci suka kwanta domin yin bacci.
Bayan idar da sallar asubahine Khaleesat taduba uniform dinta taga ko sun bushe?, Dan tunbayan data cire Arwa tasa uwale me aiki ta wanke Kuma ta busar dasu Amma basu bushe sosaiba sakamakon garin ansha marka marka, akwai sanyi ajikin su gogesu tayi sannan suka gama yin duk wasu abubuwan dazasuyi .
Sunyima momi sallama zasu fitane setakira sunan Khaleesat, amsawa tayi tare da dawowa momi tacigaba da cewa…. In antashi karki tafi kidawo nan zansa Aahil yakaimu nidake a motarshi jiyama wai yabiya gidan abokin shine daga makaranta shiyasa bedawo dawuriba sannan yau bashi da lecture shiyasa ma ba inda zeje, amsa mata tayi da to momi.
Suka wuce makaranta suna tafiya suna hira. Bayan shigarsu school kai tsaye class dinsu suka nufa SS3 science 1, kasancewar duk ranar talata basayin assembly ne yasa shigarsu aji suka tarar da ajin akwai Dan surutun dalibai natashi wasukuma karatu sukeyi, har wurin karfe 8:30am babu malamin daya shiga ajin suna cikin wannan yanayinne suka hango principal dinsu tareda wani mutum suna tahowa izuwa ajin, “kowa yayi shiru” inji daya daga cikin yan mazan ajin mesuna AL-AMIN YUSUF ga principal nan, take ajin yayi tsit kamar babu kowa aciki, dama Khaleesat da Arwa su hankalinsu nakan takardunsu suna dubawa, jin muryar principal yana fadin good morning class ne yasa suka dago kawunan su tareda mikewa tsaye gabadaya daliban domin gaida shi, bayan ya amsane kowa yazauna, sannan yacigaba da magana, wannan da kuke gani agefena sunanshi MALAM KHALID, sabon malmine amma Wanda yazo domin yin bautar kasa anan na tsawan shekara daya zakuji cikakken bayani daga bakinshi NAGODE nabarku lafiya, da turanci principal yagama magana sannan ya fice abunshi.
Gaban Khaleesat ne yayi mummunan faduwa data daga kanta wazata gani?………. Wannan kyakkyawan saurayinne daya kusa bigeta da mota Kuma ya wankemata jiki da tabo, kokari tayi ta tattaro dukkan natsuwarta Dan kar mamakinta ya bayyana.
Good morning class khalid yafada tareda daga musu hannayen shi biyu sama yana murmushi da seda hakoranshi suka bayyana sannan yakara da cewa kamar yadda kukaji daga bakin principal nazone domin bautar kasa awannan makarantane natsawon shekara daya, Kuma sunana KHALID ISMA’IL SULAIMAN Kuma zandinga koyar daku biology ne Amma kafinnan yakamata kowa inji cikakken sunanshi kamar yadda kukaji nawa ko?, Aji ya rude da hayaniyar dalibai suna fadin yes Sir, takan mazan akafara kowa na mikewa yana fadin sunanshi daya bayan daya har akazo kan mata takan Arwa akafara tafada ta zauna, itako Khaleesat kanta na kasa bama tasan me akeyiba Dan hankalinta na kan daya daga cikin abunda ke hannuta ko littafinta dai kokuma wannan farin kyallen da Khalid yabata jiya.
Khaleesat ke muke jira yafada fuskar shi dauke da wani irin murmushi medaukar hankalin duk Wanda hankalinshi yakai kanshi, kuma yayi dai dai da san ya Dora kyawawan idanuwanshi akanta , mutuwa dukkan jikin ta yayi dajin zazzakar muryar shi uwa uba data dago kanta taga ita yake kallo, ya Salam Kara afkawa tayi cikin wani yanayi da ita kanta batasan yaya haka kefaruwa da itaba, jarumta tayi tamike asanyaye tace sunana Khaleesat Abdul-Hakeem, sannan ta zauna tana mamakin taya akayi yasan sunanta sedaga baya ta tuna Ashe jiya Arwa ta Kira sunanta agabanshi.
Bayan suntashi makarantane tayi kamar yadda momi ta umarceta da tazo sutafi gidansu tare Wanda yake cikin LOKOJA ROAD, dake RIGASA
Kai tsaye kofar gidan suka nufa tun kafin motar tagama tsayawane ta hangi Alaja abakin shagon provision dinta tana ta masifa ita da wani mefaskare da ze faskara mata lodin itacen data sauke, tana fadin Haba wannan Dan itasenne sakise fasaki feskeresi a deri biyer ba se dubu deya geskiya inba hakaba sede ki Kara gaba mana basen iyaba.
sallamar da momi tayine yasa ta tsagaita da fadan tare da amsa sallamar ….. A’a Hajiya kese? toh senufa desuwa tafada tana washe baki , sannan tashiga shago tana faÉ—in kisigo mana momi tashiga sannan tanemi wurin da Alaja tai mata umarni tazauna, bayan sungaisane tabata labarin komai sannab ta dakko naira dubu biyar tabata.
Alaja taji dadi sosai ta Kuma yi godiya sannan momi ta fito tana dagamin hannu nima hannun na daga mata.
Shigewa shagonnayi domin shiga cikin gida ta kofar dake cikin shagon, Alaja batacemin komai ba tanata kirga kudinta tare da yin wakarta ta yarbawa abunta.
Kasancewar Yan 20-20 ne yasa tajima tana ƙirgawa.
WACECE ALAJA ATAƘAICE?
ALAJA bakace me matsakaicin tsawo, bayerabiyace fuskarta dauke take da tsage irinna ƙabilarsu YARBAWA,
Tana da yara guda biyu mace da namiji sunan namijin ABDUL’WASI’U Amma anakiranshi da wasiwu Dan shekara 21 ne ayanzu.
Macen Kuma sunanta Raliyat Yar shekara 12.
Namijin shine babba tahaifeshine awani gidan ma’ana shi ÆŠan mijinta nafarko ne Alhaji Abdul-Fatah kasancewar ya aureta lokacin bashi da komai ta matsa mishi seyarabu da ita bayan Allah ya azurtasu da wasiwu yana sonta ahaka ya hakura yarabu da ita domin bazata taba bari yasamu kwanciyar hankaliba saboda ita macece me kwaÉ—ayi shikuma bashi da komai,
Bayan rabuwarsu da wasu Æ´an lokutane Kuma se Allah ya azurtashi, taita kokari takoma shikuma yaki tunda yariga yasan baza a taba zaman lafiya da itaba domin bashi takesoba Dukiyarshi takeso.
Ana hakane tasamu ta auri wani me kuÉ—i Alhaji Abdul-Hakeem mekudine sosai domin É—an kasuwane yana saro atamfofi a Æ™asashen Africa harma dana waje, ya aureta lokacin wasiwu yana da shekaru uku dan haka sai tazo dashi gidan har lokacin da yakai shekaru shida ko É“atan wata bata tabayiba shikuma Alhaji yakasance mutumne me son yara, yanata addu’ar Allah yabashi haihuwa Amma shiru dayake lokacin beyiba, kwatsam Ranar wata jumma’a yadawo daga masallaci yana tafiya akafa yaga wata jaramar yarinya acikin layin lokoja road tanata kuka Wanda a shekarunta bazata wuce uku ba dauke da wata jaka karama ahannunta yadauketa yatafi daita gidanshi yakaima Alaja ita, bayan isarshi da ita gidane suka tanbayeta sunanta tace Khaleesat tundaga wannan amsar databasu duk tanbayar da akamata bata saniba, inkuma aka tanbayi sunan iyayen ta setace dady da momy, bude jakar Alhaji Abdul-Hakeem yayi seyaga ribbons ne da bit masu kyau se mankitso da Kuma wani hoto guda daya medauke da mutum biyu ajiki namijine da baze wuce goma sha É—aya ba rike da hannun Khaleesat dukkansu sunyi dariya se sukayi kyau sosai a hoton, daya tanbayeta setace yaya, nantake Alhaji Abdul-Hakeem yai ma Allah godiya yacigaba da riketa tareda Dan Alaja wasiwu domin yanata kasa kunne ko zaiji cigiya a gidan Radio ko acikin unguwa amma babu ko É—aya, shike musu komai nakaratu da dukkan buÆ™atun yau da kullum.
Ikon Allah! Bayan samun Khaleesat da shekara É—aya Allah ya azurtasu da samun ya mace wato Raliyat, Ranar zokaga murna agurin Alhaji Abdul-Hakeem abun ba’a magana.
INNAA NILLAHI WA INNAA ILAIHIRRAJI’UN,Ranar wata litininne daya ga cikin abokan kasuwancin Alhaji Abdul-Hakeem yakira lambar telfon din gidan Alaja yana sanar mata sakon mijinta yayi hatsari yana nan a *Yusuf Dan tsoho hospital (Asibitin dutse)* atake tafadi kasa a sume, wasiwu ne yaje yadebo ruwa ya yayyafa mata, bayan ta farfadone taga wasiwu da Khaleesat a kanta sunata kallon ta alokacin Raliyat tana bacci bamatasan abundake faruwaba Dan bazata wuce 2years ba.
Bayan kwantar da Alhaji da kwanaki 8ne Allah yadauki rayuwar sa , Allahu Akhubar, Allah kaimana kyakkyawan karshe.
Haka Aka gama zaman makoki aka tashi, shikenan yanzu babu Alhaji, me daukan nauyin gidan shi dama Wanda banashiba, harma da jama’ar unguwa Dan asanda yake raye hatta makota suna shaidawa da kyauta da kyautatawa irin tashi.
Bayan 40 darasuwarshi sega masu binshi bashi kama daga kan bankuna, abokan sana’arshi dama wadanda ba’asandasuba duk sun yunkuro, kilama wasu karya sukeyi, ahaka duk aka kwashe kaso masu yawa daga Dukiyarshi sekadan aka barma, Yan uwanshi, matarshi, da yarshi, suka raba gado, Alaja da yarta Raliyat sunsamu gadon babban gidan saman dasuke ciki Wanda daga baya bukatun yau da gobe yajawo suka saida mafi kyau daga bangaren gidan.
Wanda ayanzu a bq suke tai mishi gyara, ta ja jari da ragowar kudin tabude shagon provision da Kuma saida itace akofar shagon, domin cigabada daukar nauyin karatun yara.
Daga sanda aka tsinci Khaleesat zuwa yanzu shekara 15 kenan Dan ayanzu tana da shekara 18.
afiyar Laraba, Khaleesat ce kecin uban aiki tun karfe 5:40am tafara bayan idar da sallar asubahi se karfe 7:40am ta kammala, tai wanka takarya kumallo sannan tasa uniform zata wuce makaranta.
Biyowa tayi ta kofar shago Alaja ta tarar a zaune tana ta cinikin safe, gaisheta tayi cikin harshen yarbanci, itakuma ta amsa mata cikin fara’a Amma cikin wannan hausar tata dabata fita sosai, Wanda amsawar da Alaja keyima Khaleesat da hausa aduk sanda tai mata magana yana daure mata Kai bata taba yimata magana da yarensu Wanda haryanzu batasan meye daliliba.
Itako Alaja abunda take nufi dayin haka shine ita tunda tasan Khaleesat ba bayerabiya bace bataga dalilin dazesa ace dole seta mata magana da yarenda banataba duk da cewa ita bama tasan meke faruwa, sannan Alaja bayadda zatayine da tuni ta kadata dandai tariga tayi ma marigayi Alhaji Abdul-Hakeem Alkairi ne domin kafin kalmar shahada itace maganarshi ta karshe da Alaja, Dan Allah duk runtsi duk wuya karki sake Khaleesat tasan bamune muka haifetaba,
*Lafiya lau kheleesah* , Alaja tafada Dede lokacin da takeba wani yaro sugar tare da karbar kudin hannunshi kafin tamaida kallonta ga Khaleesat, tace *saka tafi tefi school ne*? Tace eh , taja ta tsaya da zata balbaleta da masifa sekuma ta tuna irin Alkairin datasamu jiya saboda ita har 5k, atake ta dakko 200 tabata tana fadin *gasi seki hau moto Kuma kisiya abinsi ko? Sekin dawo* amsawa tayi da yauwa.
Tafiya take cikin natsuwa harta isa bakin titi inda zata hau mota, tana tsaye har kusan mintuna 15 tana jira batasamu abin hawaba Dan duk motar dazata wuce acike takezuwa hakama mashina duk da goyo suke zuwa, bayan wasu mintuna 5 dinne taji ana Horne abayanta waiga warta keda wuya setaga wannan motarcedai data kusan bigeta akofar gidansu Arwa shekaranjiya da yamma medauke da bakin glass , matsawa tayi taba motar wuri tawuce, sannan tatsaya tana kallon ikon Allah.
Khalid ne yafito daga ciki fuskarshi dauke da murmushi jikin shi sanye da farar Riga me dauke da rubutu da tanbarin bautar kasa N.Y.S.C wandan shikuma jeans ne meruwan dark blue amemakon launin na masu bautar kasa, kafarshi sanye da bakin takalmi merufi, sekuma fuskarshi sanye da bakin glass Amma bame duhu sosaiba ta yadda zaka iya hango wadannan kyawawan idanuwannashi masu daukar hankalin Wanda ya kallesu, sekuma gashin kanshi dana gemu da kasinbarshi bakake masu laushi se sheki sukeyi sunsha gyara, se kamshin yakeyi Wanda kan iya jefa duk Wanda yashaka cikin wani irin yanayi mara misaltuwa.
Tunkaro inda take yakeyi bayan ya kulle kafar motar , Assalamu Alaikum, yafada cikin natsuwa, amsawa tayi tare da yimishi kallo daya sannan ta sunkuyar da kanta kasa Dan bata iya jure kallonshi natsawon lokaci, sakamakon afkawa cikin wani irin bakon yanayi datake tsintar kan aduk sanda idanuwansu suka hadu.
Khaleesat Abdull_Hakeem ko? Yafada yayin da acikin ranshi Kuma fadi yake gaskiya Allah me girmane wannan irin kyakkyawar halitta haka, Kuma bayerabiya?.
Amsawa da eh datayine yasa yadawo daga zancen zucin dayake yi, yace nasan makaranta Zaki shiga muje inrage Miki hanya nima chan zani, shiru tayi nadan dakiku kafin tace toh, nuni yayi mata da alamar tashiga haka tabi umarninshi asanyaye tashiga, suka fara tafiya shiru bawanda yayi magana dayaji shirun yayi yawane seya kunna radio tashar *liberty fm, 103.1* yakamo Wanda adai dai lokacin da *khumsat Muhammad Hassan* *ke gabatar da shirin gamzaki mefita da subahi* dukkan su saurara kawai sukeyi.
Ahaka har suka iso cikin harabar makaranta yasamu guri yayi parking, dukkansu suka fito godiya taimishi yaji dadin sautin muryata, Amma sai ya boye alamar hakan ya amsa mata da bakomai.
Ya wuce office, itakuma tawuce ajinsu.
Bayan fitarsu break ne suna zaune akan dakalin kofar ajinsune, jingine Arwa take jikin karfen dake dashe a cikin dakalin tana facing din office din khalid itakuma Khaleesat tana jingine ajikin bango tana facing din Arwa, sannan dukkansu suna zaune ne akan daddumar dasuka shinfida wacce Arwa kezuwa musu da ita daga gida kullun.
Kayan ciye ciye da abubuwan Sha ne zube a tsakaninsu asaman daddumar Wanda suka siya.
Sunaci suna Sha Kuma suna hirarsu irinta Aminan juna, daga idon da Arwa zatayi ne seta hangi mlm khalid a tsaye akofar office dinshi yanata kallon inda Khaleesat take tanacin snacks dinta anatse tanama Arwa hira, itako Arwa bamatasan abundatakeba tanacan tana kallon inda Khalid yake tana ganin ikon Allah, tana mamakin shin komeyasa yake kallon ta oho, jinshiru da Khaleesat tayine yasa ta waiga takalli kawartata setaga Ashe wani guri take kallo, kallon da Khaleesat tayi mata nadan dakiku har ta hango matukar mamaki akan fuskar kawartata Arwa, saboda tsananin shakuwar dake tsakaninsu yasa tagane haka cikin sauri.
Tabata Khaleesat tayi tana fadin ke lafiya?……………….
Na’am Arazane arwa ta waigo sakamakon tabata da Khaleesat tayi, sannan tace mekike cewa?,
Cewa nayi lafiya kike kuwa inata magana kinyi shiru kina kallon wani guri, ba komai Arwa tafada.
Haba kedai kinsan bayadda za ayi kimin karya inyadda kinsandai dadewarmu tare shekara ta 5 kenan tunlokacin da kuke zuwa keda momi yin saloon kusa da shagonmu a sanda muka gama primary, ke private kika yi nikuma ta gwamnati sabodani kika fara karatu a j.s ta gwamnati to ko daga lokacin zuwa yanzu yaci ace nagama sanin dukwata alama ta karya da gaskiya tattare dake, kawai malama kifadamin gaskiya Khaleesat tafada tana kallon Arwa tareda zuba kunnuwa tana saurarenta,
shiru Arwa tayi natace komai ba da Khaleesat taga bata da niyyar yin magana yasa tafara kokarin tashi tabar gurin, rike mata hannu tayi tare da fadin dawo mana ni dadina dake wani lokacin saurin fushi bafa wani abu bane mutumin kine nagani yanata aikin kallon ki gashican abakin office dinshi tafada batare da takalli wurinba Dan karya gane, A sanyaye Khaleesat takalli inda kawartata tafada Amma ga mamakinta setaga ba kowa awurin , Ina yake nidai Banga kowa ba tafada tare da bude hannan yenta alamar ba kowa,
wallahi Ni naganshi da idona , naji meye Kuma na rantsuwa na yarda nasan bazakimin karyaba, To kimace karyane mana Arwa tafada tana kallon Khaleesat tana dariya itama dai dariyar tayi,
Wanda yayi Dede da lokacin da aka buga kararrawar komawa aji, tsam suka Mike suka wuce aji.
Bayan kamar mintuna 5 ne mlm khalid ya shigo ajin Dan alokacin shine kada period din, bayan yagaisa da dalibaine yayi rubuce rubuce akan allo na darasi da kwanan wata sannan ya yima dalibai tanbaya, students dayawa sunata daga hanna yensu da zummar amsawa,
sedai shi fa batasu yakeyiba hankalinshi na kan Khaleesat ne kawai ko Arwa dake gefenshi tanata famar daga nata hannun ko ganintama beyiba.
Itakuwa hajiyar bama tasan yanayiba kanta na kasa Dan ita kwata kwata bama tasan tana kallon inda yake sakamakon bakwan yanayin datake shiga inta kalleshi.
Jitayi kamar anyi wata irin tsawa a tsakiyar damuna an ruwa me karfi,
dajin muryar shi yana fadin Khaleesat Abdul_Hakeem stand up and answer my question yafada yana nunata , yayi hakane Dan ya fuskaci yarinyar tana da kwakwalwa sosai to Amma tana da tsananin kunya Kuma ma yanaganin alamar kamarma jin tsoranshi takeyi ne ko kunya yasa take yawan sunkuyar da kanta inyana class din ? oho ♀.
Jitayi rass gabanta yayi mummunan faduwa,
take tafara fadin *innanillahi wa inna ilaihirraji’un* *Allahumma ajurni fii musiibati wa Aklifli khairan minha*
da duk wata addu’ar datazo bakinta, sannan ta tashi a natse sakamakon addu’a bata faduwa kasa, ta amsa mishi tanbayar tare da yin bayanai masu gamsarwa,
haba base aji ya rude da tafin dalibai da ihunnuna jinjina ga Khaleesat ba, Amma dayane daga cikin mazan ajinne yafara tafawa zeyi sa’a da yayanta *wasiwu*
mesuna *Yusuf Al_Amin* bakine siriri dogo kyakkyawa, tun Ranar daya fara ganin Khaleesat yaketa binta wai yana sonta ,
Amma ita Sam takima ta saurareshi gani take yayi yaro dayawa, sannan ita ba shirme yakawota makarantaba karatu tazoyi, amsar databa mlm khalid ne yasa yaji takara burgeshi ,
sanann yana lura da dukkan movement din mlm khalid din Dan dazuma a break yana lura dashi ba wacce yake kallo se Khaleesat dinshi jiyayi kamar yaje ya shake shi saboda tsabar kishi .
Itakuwa tana kulashine kawai in anbada Assignment akan darasin da bata ganeba sesu hadu dashi Al_Amin din da Arwa da ita tana sakin jiki dashi sosai indai akan harkar karatune ,
Amma daya fara nuna mata kulawa irin ta soyayya take zata daure fuska Dan bata San shirme irin nashi.
Akwana atashi kullum haka Khaleesat da mlm khalid da Al_Amin keta yin drama su irin ta masoya Amma har yanzu ba Wanda yataba fadama Dan uwanshi wata kalma data danganci soyayya sedai harkar karatu amma daka kallesu zakasan akwai magan sedai da zaka tunkari daya daga cikin su biyun, wato Khaleesat da khalid cewa zasuyi karyane.
Gashi lokaci nata tafiya har sun fara jarabawar kammala secondary wato WAEC,
basu da matsalar komai daga ita har Arwa da Al_Amin domin suna karatu sosai, kullum insukayi bacci da farkon dare saisu tashi suyita karatu da salloli da addu’oi har asuba , Kuma Alhamdulillah da ankawo question paper suke bugeta da amsoshi,
kullum suke fara gamawa , duk da ba aji daya suke jarabawar ba Amma kusan lokaci daya suke fitowa Dan da wannan yafito sewannan.
Aranar da suka gama jarabawar sunsha kukan rabuwa da juna sosai, haka suka karasa wunin ranar jiki duk ba kwari saboda shakuwa,. *School life is the best*
********************
Khalid Ismail sulaiman yayi Horn da katuwar motar me kirar Range Rover, launin ruwan toka “Ash”.
Buzu megadi ne ya taso da gudu ya bude wani irin nannauyan kato gate baki Wanda yasha ado da launin ruwan zinari , kaya taccen gidane ko ince gidaje Dan agefen gidan da khalid yashiga akwai wani irinshi sak bako banbanci domin magina dayane sukayi aikin shi,
Ana Kiran gidajen da suna *Tagwayen gida* kayatattun manyan gidajen samane nagani nafada, Wanda suke acan cikin layukan dake farko farkon sabon kawo, cikin wani madaidaicin street .
mesuna *Abuja street* gidajen basu da wani nisa da bakin titi sosai.
Bayan shigar khalid farfajiyar gidanne, buzu megadi ya gaisheshi da *sannu namiji* yawwa kawai ya amsa mishi tareda Dan murmush.
Kai tsaye ya shige kafaren babban falon dake kasa, shiru yaji falon yayi se sautin T.V ne kaw ai ketashi babu kowa a falon,
se wani irin daddadan kamshin turare dana girki me dadi Wanda daji ba’a jima da kammala shibane suka hade suke bada wani irin launi mekara tsokano yunwa gawankejinta.
Yawwa mom kamar kinsan kuwa yunwa nakeji wallahi, Kuma naji da alama ma kinyi my favorite ne
*tuwan shinkafa da miyar agusi*
to Amma ya kike aiki kekadai , Ina lantana me aiki da sister *Amrat* suka shigane? Yana maganarne adaidai lokacin daya ja ya tsaya abakin kofar kitchen yana kallon wata mata fara kyakkyawa me madaidaiciyar kiba, acikin kitchen din take tsaye dauke da serving spoon ahannunta tana kokarin dorawa akan babban farantin dake dauke da kulolin abinci nagani na fada guda uku,.
Harara ta watsa mishi sannan ta kauda kai.
Haba mom kamar bakya murna da dawowa ta daga yaufa nadawo gida gaba dayane fa,
Haba Dan Allah? Tafada tareda ajiye komai tana fuskantar inda khalid dinyake sannan tacigaba da fadin to kaine ai kashigo daki ko sallama babu Kuma daga zuwanka kafara maganar abinci,
wallahi mom nayi sallama tunda nashigo Amma kila karar TV dake kunne a falo yahana kijini, kuma kingafa dole in fara maganar Abinci shekara 1 fa kenan bana tare daku sedai indanzo inkoma, to yau ina murna nadawo gabadaya zanci girkime dadi koda yaushe Kinga ko ai Ina da gaskiya ko? Hakane kam kana da gaskiya nima ai da nadauka kalekomune kamar yadda kasaba, ace kana bautar kasa a garinku Amma kiri kiri kaki zama a gida, nidai Banga amfanin barinka a kd dinbama da Alhaji ya nemamaka alfarmaba,
haba mom to baga shinan bade Allah yanufa harmun gama ai shikenan ko?………mom……mom wata muryace ke kiranta daga falo, banza Tai da ita tacigaba da hirarta da danta itama kitchen din tanufo tana cigaba da Kiran sunan mom, bayan tazo Dede kofar kitchen dinne tayi wani irin ihu,
tareda yin tsalle tafada jikin Khalid
tana fadin….oyo..oyo Yaya tureta yayi tare da fadin wai ke yaushene zakiyi hankaline wai.
Hummmm fada mata dai nikaina nayi nayi tadena irin wadannan sakarcin Amma taki denawa.
Sanye take da Riga da wando na Pakistan masu launin sararin samaniya kanta ko Dan kwali babu, yarinya ce karama wacce bata wuce shekara 12 ba, wuce kije kisa Dankwali, khalid yafada yayin dayake mata nuni da hannu,
kunkuni tayi tana buga kafa tawuce.
Kwaso kayan abincin Mom din tayi suka koma Fallon zuwa dining area, Ahaka sukaci suka Sha suka cigaba da hira ta yaushe gamo tsakanin da dauwa .
*WANENE KHALID A TAKAICE*
*Alhaji Isma’il Sulaiman* shine mahaifin khalid sekuma *Hajiya Amina* itace mahaifiyarshi , Allah ya azurtasu ne da yara guda 2ne dashi khalid din sekuma kanwar tashi Amrat Wanda akwai tazarar shekaru 11 atsakaninsu.
Alhaji Isma’il Sulaiman babban dankasuwane me sana’ar gwanjo agarin kaduna Wanda sunkafara shida abokin shi mesuna *Alhaji Usman Aliyu* Wanda sunkafara sana’arne a baro tunbayan da suka gama karatu amma dayake Allah ya albarkaci sana’ar tasu yanzu kaf fadin garin kaduna sune suke rabama duk Yan kasuwar bacci data kawo dama dukkanin kasuwannin da ake cin abinci da sana’ar gwanjo agarin kaduna.
Tsananin shakuwar dake tsakaninsu yasa sukayi ginin gidajensu iri daya Kuma kusa da juna dahaka Yan unguwa ke Kiran gidajen nasu da sunan Tagwayen gida.
Alhaji Usman Aliyu Kuma yana da mata dayane mesuna *Hajiya Hauwwa’u* Allah ya azurtasu da haihuwar yara ukune Amma yanzu biyune kawai ke raye a gabanta, babbar mesuna *Maryam* sekuma mebinta *Umar*.
Hajiyoyin biyu matan Alhazan biyu suna rayuwa ne cikin zaman lafiya, zumunci da kuma kaunar junansu, kamar yadda muslumci yayi umarni, sannan suna gudanar da sana’ar gwanjo ne irin ta mazajensu acikin gidajensu.
Haka mazajen kesa asauke musu dilolin gwanjo afarfajiya gidajen biyu, haka gidan ke cika aduk sanda aka sauke musu kaya, wani lokacin asauke agidan Hajiya Amina, wani lokacin Kuma asauke agidan Hajiya Hauwwa’u, aduk lokacin da aka sauke gidan Hajiya Hauwwa’u sunfi saurin karewa saboda tafi saukin Kai dakuma hakuri, itako Hajiya Amina tafi tsawwalawa Kuma gata da masifa, sedai duk masifarta Allah besa tana da hassada ko bakin ciki ba, suna tare kansu ahade yake ita da kawarta, matar abokin mijinta, Kuma makociyarta, abokiyar kasuwancinta, sannan Kuma aminiyarta, da irin wannan dangantakar tasucema yasa Hajiya Amina bata da wani buri daya wuce taga tahada tsatso da Hajiya Hauwwa’u, har rokonta tayi dacewa Dan Allah in yarta Maryam tagama secondary School tayadda tabama danta khalid inyaso seta cigaba da karatu agidanshi.
Babu wata matsala Allah ya tabbatar Mana da Alkairi, Amsar da Hajiya Hauwwa’u kawai tabayar kenan.
Sedai abangaren goganna ku kwata kwata shawarar mom din tashi bata mishiba ko kadan baya so, cemata yayi shifa gaskiya tayi mishi kankanta, tayama za’ayi ya auri Yar 15, duk sanda khalid din yafadi haka se mom din tamaida maganar wasa tana dukan kafadarshi tana fadin karfa nangaba kaga yartawa Maryam takara zama Yan mata kace kanaso Dan bazan bakaba, shikuma se yace Allah ya sawwake mezanyi da kwaila, nifa akalla inasone ace ayanzu budurwata takai 18, se hajiyar tabashi amsa da cewa to ai bayanzune za’ayi aurenba inbanda abunka senanfa da shekaru 4 kaga lokacin bama 18 ba 19 zatakai, tunda kaga yanzu tana j.s.s 2 going to 3, aduk sanda mom din tace haka, ko Abinci yakeci tofa yabarshi kenan, in mom din taga ya matsa baya so sedai tayi dariya sannan ta Kara da yaro yarone, Dan tasan ko kadan bayaso ana mishi maganar Maryam, itakuma yarinyar data ganshi harwani boyewa take wai ita alamar kunya , in yaga haka wani lokacin tabashi dariya wani lokacin Kuma tabashi haushi sedai yayi tsaki ya wuce.
Acan unguwar lokoja road dake Rigasa kaduna kuwa, Khaleesat ce ke zaune acikin shago agefen ta Kuma kanwartace Raliyat ke zaune tana Shan garin rogo tanata mata surutu tareda mata tanbayoyi gameda karatunta , yanzu Anty Khaleesat innagama primary se inshiga inda kika gamako?, Dariya Khaleesat take mata sannan tace A’a malama bahaka akeyiba sekin gama junior tukunna kafin……….. Kasa karasa maganar tayi sakamakon hango motar khalid datayi a bakin kofar shagon askin dake kallon kofar shagonsu , gani tayi ya fito daga motar ya shige cikin shagon ko kallon inda take beyiba, Wanda yayi Dede da lokacin da wani yaro yazo yana cewa abani sabulu, Raliyat ce tamike takarbi kudin sannan tanufi gurin da sabulan suke setaga Ashe tsawonta baze Kaiba yayi sama da yawa taita tsalle har tagaji, dawowa tayi tana ma Khaleesat magana da yarbanci tana fadin Anty Khaleesat za’asiya sabulu nikuma bazan iya dakkowaba , inaaah ita batama San anayiba tana can tana kallon khalid Wanda yama Riga da ya shige shagon, abundai yanata bata mamaki magana kawai take cikin ranta, Toh waima meya kawo wannan bawan Allah nan unguwar? .
*Sege kanasi ana magona saka gyamun asara yaro taso sata siya sabulu kana San kana kallon masu kudi ko ?*
Firgita Khaleesat tayi dajin muryar Alaja na zubaba mata ruwan masifa da hausarnan tata da bata fita sosai, hakuri kawai Khaleesat ta iya bama Alaja, asan yaye tace yi hakuri Alaja banji sanda yazo bane , haba kamar takara tunzurata fada taci gaba dayi tana fadin .
*Ai basa kajisi ba saboda kanasan kana kwabdayi, kaga mekudi kasa kana kallonta to babu abunda satayi dakai, garama kamaida hankalinka kanemi kudi Dan yansun bawanda sebaka kudinsi haka kawai* nima dai ayau na yadda da maganar Alaja fa, wallahi inbaka nemaba bawanda zebaka. Allah yasa mudace inmun dace mu dafe, Ameeeen .
Tundaga hakurin da Khaleesat tabata bata Kuma kulataba, shiru kawai tayi zuciyar ta cike da tunanin wai shin meya kawo khalid unguwar su da tsakiyar Rana haka?. Nimadai bansan amsarba, namika tanbayar ga masu karatu duk Wanda yasan amsa seya fada mana .
Bayan shigar khalid cikin shagon askine ya tarar da Qasimu me aski tareda abokanshi 2 suna hira sannan gawani zaune kan kujerar aski Wanda shi akema aski alokacin, daya daga cikin su biyunne ke magana yana fadin, tofar ga waccar masifaffiyar matar can tasoma bala’innata data saba, se dayan yace aidama haka take, Kuma Ni Ina mamakinta du cikin yaranta tafi yima Khaleesat irin wannan jarabar , sekace ba ita tahaifetaba , seko Qasimu ya karbe zancen da cewa wama yasani ko ba yarta bace Dan natabajin jita_jitancewa kamarfa ba ita tahaifetaba tsintarta sukayi Kuma Amma yarinyar ma haryanzu batasaniba.
Kudai kunji kunya wallahi kuna abokan Wasiwu Amma kurasa gulmar wa zakuyi sena mahaifiyarshi inji Wanda akema askin .
Rabu dasu ai yanzu gulma tabar mata takoma gurin maza khalid ne yafada yana murmushi ajingine ajikin bangon gefen kofar shigowa, waigowa sukayi suna kallon shi kwata_ kwata bama su San da mutum agurin ba, bawanda ya kulashi acikin su dayaga haka seyayi musu sallama, amsawa sukayi suna wani kauda Kai sannan Qasimu yace haba mlm ko Kaifa tunfarko sallama yakamata kafara mana ba tsoma Mana baki a hirarmu da ba ruwanka acikiba.
murmushi kawai yakumayi sannan yace to gani nayi kunyi nisa da hirar takune Kuma ma nayi sallama bawanda ya amsa shiyasa nace to bari intsoma baki watakila zakufi jina sosai.
To dai shikenan ya wuce aski kazoyi? Qasimu ya tanbaya yana wani daure fuska , A’a gyaran fuska kawai nazo ayimin khalid yabada amsa.
To zauna inna gama ma wannan se inyi maka , amsawa kawai yayi da toh tareda neman guri ya zauna hannun shi rike da mukullin mota da clipper yana jira.
Bayan angama ma dayanne khalid yazauna akan kujerar askin za’a fara yimai gyaran fuskar seya fara takalar me aski da hira cikin dabara , farawa yayi dacewa abokina meye ma sunanka? Take Qasimu yadaure fuska sannan yace bakaga anrubuta abakin shagon bane ? Indai kagani to shine sunana, maida abun wasa yayi tareda fadin ohoo yi hakuri Ashe sunankane ajiki tabbas naga ansa *AL_QASIM *BARBING SALOON* shine ko?, Gashinan kafada Qasimu yafada yayin da yake kokarin Dora mishi clipper akai , da sauri khalid yarike hannun Qasimu yana fadin dakata Mana abokina nazo da nawa clipper din Kuma ma kamantane cemaka nayi gyaran fuska nazo ba askiba, amsa mishi da toh kawai Qasimu yayi sannan yakarbi clipper khalid yafara Mai abunda yakawoshi.
Bayan fara yimishi gyaranne khalid be daddarab yakuma yima Qasimu magana yana fadin abokina Al_Qasim, Na’am ya amsa mishi, khalid ya cigaba da cewa Niko yarinyar danaji kuna gulmarta wacece ita ?.
Ina ruwanka yafada adakile , murmushi kawai khalid yakumayi yana kallon Qasimu ta mirror sannan yace babu ruwana kam Amma da nima inasone indan shiga cikin hirartaku , chab ashedai masu gulmar suna da yawa bamu kadaibane, tunda Qasimu yayi wannan maganar be Kara cema khalid komai ba, shima khalid din be Kuma cema Qasimu komai ba.
Shiru shagon yayi kasancewar babu wutar lantarki se dan karamin generator aka kunna Kuma a tsarin Qasimu indai babu wuta to baya kunna kida a shagon wai yana shanye mishi Mai.
Bayan angama mishi komai ne yamike tareda tanbayar nawa ne kudin dazan biya?.
Qasimu yace kabada 200.
Hannu yasa a aljihu yafito da kudi yamika ma Qasimu 2k amemakon 200 din daya nema, Habawa Qasimu naganin dattawan Nigeria biyu masu daraja, kuma gashi har su 2 base ya washe baki ba tareda fadin yanzu duk wadannan nawane nikadai ? Yace Eh nakane Allah ne yabaka, Kai Amma gaskiya nagode sosai, godema Allah khalid yafada yana kokarin fita daga shagon.
Biyoshi Qasimu yayi abaya yana fadin yallabai Dan dakata tsayawa khalid yayi tareda cewa Ina jinka.
Ranka ya dade wallahi dazu dinnan dakayi magana naji haushi dandai dama bansan Kai bane, dariya ce ta kwacema khalid sannan yakalli Qasimu yanata mamaki kamar bashine keta daure fuska dazuba, Amma yanzu yaga kudi duk ya rude.
Dakewa khalid yayi sannan yace Al_Qasim dama kasannine? , A’a amma Dan Allah kayi hakuri, ba komai ai ya wuce.
Har khalid ya juya ze wuce Qasimu yakuma cewa, ranka shi dade , wai gowa yayi yana kallo da sauraron shi kafin yace inajinka.
Wallahi in dai kanaso kasan wacece Khaleesat da komai narayuwarta zan tema kamaka kasani, duk dadai mu bamu wani dade sosai a layinnan ba, kwata_kwata bazamu wuce shekaru 3 da dawowa ba Amma akwai wata mata tsohuwace a mazauna wannan unguwar sunanta *jummai me koko da kosai* tana da wanijika mesuna sani ana cemai *sani na me koko*, abokin yayan Khaleesat dinnema tare suke shaye_shayensu da wasiwu, Dan dai tun safe ma banganshibane Dana hadaka dashi.
Har alokacin dariya kawai khalid keyima Qasimu ganin yadda 2k tasashi yaketa zuba harma da abunda ba’a tanbayeshiba, Toh yanzu yaushene za’a samu ganin sanin me kokon? Khalid ya tanbaya, ai shi ganin sanin me koko habone Amma kabani number ka Ina ganinshi se inkiraka in hadaku koya kace?.
Hakan ma yayi, take khalid yakaranto mishi number, sannan yabashi 1500 yace gashi inka hadu dashi ka bashi 1k 500 kuma kasa kati, habawa base Qasimu yakara wangale baki ba harda wani dunkule hannu yana wani yima khalid jinjinar ban girma, godiya kawai khalid yayi sannan ya juya yana dariya yashiga mota yayi tafiyar shi.
Har awannan tsawon lokutan Khaleesat na zaune a shago gaba daya hankalinta atashe yake ta kasa sukuni, ita ko Alaja dataga abun yaki ci yaki cinyewa sekawai tacigaba da masifa, tana fadin *sege inde basaka nemi kudi a sagoba to saka soma tallar bired, sansaro maka bired katafi talla kawai, seka nemi kudi dakanka kasiga jami’a Dan geskiya basan iyaba , Kuma sima jarin da senbaka ba kyauta bane fah toh, inkayi siniki seka biyani kudina, inkuma hakama basaka yisiba toh seka tafi kasiwa ka sauna a sago nakayan robobi ka sauna tareda iyawo.*
To kundaiji inda Wanda ze kawoma Khaleesat dauki toh, kofa abude take
Itadai Khaleesat duk abun duniya ya isheta shiru kawai tayi kanta akasa idanuwan ta cike fal da hawaye, da gudu tamike tashige cikin gida, tana shiga kukane me karfi ya kwace mata tare da jin wani irin radadi acikin ranta.
Bayan taci kukanta ta koshine duk abubuwanda suka faru suka dinga dawowa cikin gwagwalwarta tare da tunani dayima kanta tanbayoyin da basu da amsa, shin wai meyasa Alaja kemata irin wadannan abubuwan, taga dai ita ba Yar farkoba balle ace anamata hakane domin Kara to Kuma ai irin wannan karar ta hausawa ce, Kuma sukansu hausawan sundena kyarar Yaransu wai Dan kawai suna nafari, acikin ranta taketa wadannan tanbayoyin tareda zubar da zafafan hawaye, hakan yayi Dede da fadowar da khalid yayi aranta, nanma tashiga duniyar tunani me zurfi game da irin rayuwar da sukayi a school, da duk wata irin kulawa daya dinga bata, Amma yau taganshi alayinsu Kuma ta tabbatar da yaganta Amma se yanuna bemasan Allah yayi wata halitta mesuna Khaleesat awurinba, to ko me hakan ke nufi? .
Wunin ranar haka tayi shi cikin rashin sanin meye abunyi gameda abubuwan dasuka faru, hakanan ma ta kwanta cikin wannan yanayin Kuma tawayi gari ahaka, idanuwan ta duk sun kunbura sakamakon kukan data kwana tana sha sannan gashi bawani baccin kirki tayiba.
Bayan kammala duk wasu abubuwan da sabayine kowace safiya, yauma shago tashiga kamar kullum, alokacin Alaja nacikin gida tana wanka, awannan Ranar Khaleesat tasamu Allah ya temaketa tayi ciniki dayawa, don duk bread din da aka sauke musu jiya ya kare, ga suger duk wacce aka kulla ta kare, dadin dadawa itacen suma ansiya sosai, sakamakon duk unguwar su babu mesaida busheshshen ice inba Alaja ba, duk da ana daminane Amma ita bata bari ruwa yadaki icenta cos ta siya irin manyan yadin tenfol dinnan ne tana rufewa dashi, *Hausawa nacewa duk wani Wanda yasha inuwar gemu tofa baya ga makogwaro yake* to haka dukwani Wanda zeyi murna da cinikin Khaleesat to bayaga Alaja yake, Haka ko tafaru, Alaja nashigowa shagon neman guri tayi tazauna tana zare idanuwa tana neman abunda zatayi fada akai, dade taga bata samuba setace *Ina siniki?* Tafada tana mazurai, jakar kudin Khaleesat tamikamata, tana karba ta kirga taga anyi ciniki me tsoka har 5,500 dasafe kawai, haba baseta Mike tafara rawa tana wakokin yarbawa ba tanata juya duwaiwaka, seda tagama cashewa abunta sanann ta zauna tana fadin, *Ah kheleesah ase kafara samame wayo sose, kene kayi wannan siniki, Ah kafadi kome kakeso yau sanyi maka si mano A’a* tafada tareda Dan zungurin Khaleesat da jakar hannunta, murmushi kawai tayi tadanyi shiru tana nazari, take seeabara tafado mata, ta anbaci sunan Alaja sanan tace abu biyu kawai nakeso, *fada Mona ah* tace nafarko de Ina so Dan Allah kibar maganar doramin talla kokuma kaini shagon iyawo, shiru Alaja tayi batace mata komai ba, sena biyu Kuma inaso kibarni inje gidansu Arwa kawata, *Ah jeka mano kagesesu, yausene saka tafi?* Ni ko zuwa gobene, *No sekatefi yansu mano* , mikewa Khaleesat tayi cikin murna dukda dai Alaja bata amsamata rokonta nafarkoba Amma hakan bewani dametaba tunda zataje gun kawarta tasan in Sha Allah inde taje zasu samu mafita zakuma ta bata shawarwarin dazasu amfaneta.
Shiryawa tayi tsab cikin Riga da skirt na atamfa fara me ratsin green da Dan baki kadan se gyale fari data yafa, tasa bakin takalmi sannan ta rataya madaidaiciyar jaka baka wacce Arwa tasemusu iri daya, shigar tamata kyau sosai, sannan afuskarta Kuma tayi make up dinta bana haukaba Dan dedetayi Kuma tayi kyau sosai tsantsar kyanta dakuma tsarin halittarta suka Kara bayyna, ba namijiba hatta mace Yar uwatta dazata ganta seta yaba da irin kyandatayi ta tsaru ta fito tas.
Yanzu kam ta kofar gida tabiyo bata kofar shagoba, fuskarta asake tayima Alaja sallama sannan tace zantafi, amsa mata tayi da *toh kheleesah sekadawo do Allah kase muna gesuwa* sanan ta dakko 200 tabata tahu mota, karba tayi tareda yin godiya.
Tana karasawa bakin titi kuwa taci sa’ar samun acaba ta haye se gidansu Arwa.
Tana Kai wa kofar gidansu Arwa dinne bayan ta sauka tana bashi kudi sega Aahil yafito daga gida da alamade banisa zeyi ba Dan akafa yake, juyowarda zatayine suka fuskanci juna kiris yarage suyi karo *Subhallahi* Khaleesat tafada tana kokarin kaucewa, shima kaucewar yayi tare da zuba mata ido kyar yana kallonta gani yayi tayi wani irin masifaffan kyau jiyake kamar ace gobe za’a daura musu aure, wani irin yanayi yashiga me wahalar fassarawa, be ankaraba tsintar kanshi yayi cikin duniyar kallon kallo tare da shiga duniyar tinanin San kasancewa da ita arayuwar shi ta har abada, kasa kauda kanshi yayi, gashi tana magana yana kallon pink lips dinta Amma besan metakecewa burgeshi komai nata yakeyi yakasa controlling kanshi, Yaya Aahil yi hakuri wallahi banganka bane!!! Tafadi haka yafi 5× kafin yadawo daga cikin duniyar tunani, na’am Khaleesat yakike, Eh Arwa naciki momi ma tana nan, yana gama fadin haka cikin jin nauyi yayi sauri yajuya yatafi batare da ya Kara ko kallonta ba, binshi tayi da kallo sannan mamakin shine yayi matukar kama Khaleesat ganin yadda yayi behaving yanzu bahaka yakeba, ummmm Allah dai yasa lafiya, tafada tareda bude gate din tashiga ciki.
Zaune ta tarar da Arwa a tsakar gida kan farar kujera hannunta dauke da waya,
Sallamar da Khaleesat tayi ne yasa taisaurin dago da kanta tareda amsa sallamar, tana ganin itace ta taso da gudu tana fadin oyoyo sister rungumeta tai niyyar yi, tureta Khaleesat tayi tana fadin ni dalla matsa karki yaddani inda kindamu da kiganni da baki biyoniba.
Allah sarki wallahi Kinga nan da kika ganni azaune pics dinda muka dauka a school nake kallo Ina hirarki araina, Kuma wallahi kitanbayi yaya Aahil makiji dazunnan da sasassafe yazo yake tanbayata wai shiko tunda muka gama exam be kuma ganinki agidannanba wai inbashi number ki yakira kugaisa nace mishi bakida waya, kuma kinzo last week lokacin baya gida.
Ke atakaice dai har mun yanke shawarar gobe ko jibi zamuje gidanku, yanzunnan ma ya fita wai ze tsallaka bakin titi wancan shagon seda wayoyin ya semiki waya inkuma be samu irinwacce tadace ba to gobe zeje kasuwa, Dan yau yace ba inda zeje da mota wai hutawa zeyi.
Ke haba naji Ni duk kin isheni da surutu, ya isa hakanan karki karar da maganganunki tunkafin kitsufa zasu Miki amfani nan gaba, dariya suka kwashe dashi dukkan su alokaci guda, tareda rike hannun junansu suka nufi Fallon kasa babu kowa a Fallon, Ina momi? Ina tunanin kamar tana wanka Dan yanzu suka dawo daga dakin motsa jiki ita da dadi, A’a dama dadi yadawo shine kokifadamin, hara rarta Arwa tayi sannan tace ta Ina zan fada miki bayan baki da waya? Itama Khaleesat din hara rar Arwa tayi tana fadin aikin San dayake Alaja bata da wayane.
Yanzu daj kiyi hakuri naji nayi lefi Arwa tafada tareda hade tafukan hannayenta guri guda sannan takara da Afuwan .
Naji na hakura Khaleesat tafada tareda rike hannun Arwa tana janta tareda cewa, zoni kirakani ingaida dadi da momi, kwace hannunta tayi tana fadin ke kamarfa kowannensu yashiga wankane , nizomuje insun fito kwa gaisa.
Bayan sun shiga dakinne sunnemi guri sun zauna, shiru ya ratsa na tsawon dakiku 40 ne, Sannan Arwa tace ya gajiyar ranannan , babu gajiya, sannan tace ke bayan tafiyar ki da kwana 3 base ga Al_Amin Yusuf yakirani yana tanbayata ba, wai Ina gida? Nace mishi eh bayan mintunan dabasufi 15ba segashi cike da abokananshi a mota mundade muna hira dashi key dinshi yaba abokannashi suka tafi yawo da motarshi, nikuma har tsakiyar gidannan nace yashigo, ke yafara tanbaya na wai kina lafiya, nace mishi kina nan lafiya kalau, sai Kuma yake cemin wai Dan Allah inkina dawaya inbashi number ki Ni Kuma nace baki da ita, secewa yayi wai inkaishi gidanku watarana Mana.
To kekuma mekikace mishi? Cemishi nayi to zannemeki muyi magana inkin amince se inkawo Miki shi,. Cab karkifara wallahi ko hanyar gidanmu ke bama hanyaba ko sunan layinmu bance kifada mishiba balle ma kiwani kwaso minshi haka kawai kijamin masifa gurin Alaja ko kuma kija tadaga waya ta kirawo kaninta *uncle Alfa* mijin *Anty iyawo* me robobi yadakeni, inkuma bansamu dukaba kisa tace zata bama Al_Amin din aurena Kuma gashi dan yaro……
Khaleesat ce ke cigaba da magana tana fadin, Kuma kinsan dai natabbata koshi Al_Amin din iyayenshi babu yadda za’ayi sumishi aure yana Dan 21 tunda naga iyayennashi suna sanshi da karatu kina dai ganin irin yadda baban shi keyawan zuwa school Dan ya dubashi ko yana karatu yadda yakamata ko beyi.
Kuma karkimanta shidakanshi Al_Amin din yafada mana ba yadda babanshi beyi dashi yayi karatunshi a private secondary School ba Amma yaki, Kuma a unguwar su *Askulaye* akwai schools na kudi sosai Amma yaki yayi kome yasa Oho?.
Ajiyar zuciya Arwa tayi dajin zancen Khaleesat me tsawo , domin kallonta kawai takeyi tunda tafara maganar batacemata kalaba, sedatagama sannan tace kinsan nima namishi tanbayar wai meyasa yanace seyayi makarantar gwamnati duk da mahaifinshi yana Dan siyasa.
To meyacemiki? Khaleesat ta tanbaya, cewa yayi wai shima besan takamaimain dalilinba Amma dai shi yana ganin kaddarar haduwa dakene yasa.
Hummmm Dan Allah rabu dashi kinji nime zanyi da karamin yaro, Ni yarinya shi yaro haka kawai in aure shi muje muyita hauka Kuma sanda zan tsufa lokacinne shikuma zefara tashe , nikuma nagama zubomishi “ya “ya yawulakantani ya auro karamar yarinya, gaskiya nidai nafison Wanda ya girmeni akalla ace yakai kamar shekaru 8 atsakaninmu ko zuwa goma.
Kamarsu malam khalid kenan ko? Arwa tafada tare da dariya da kanne ma Khaleesat ido daya.
Banza tayi da ita sannan daga baya tace Hummmm kenifa wallahi matsaloline Dani sunema suka sa nazo neman shawara agunki in akwai mafita kifadamin inji.
Zare idanuwa Arwa tayi tareda fadin, toh fah keko wadannan wasu irin matsaloline haka harkike neman shawara?.
Anan Khaleesat takwashe labarin dukkan abubuwan dasuka faru jiya kama daga bangaren khalid haryazuwa kan maganganun Alaja, tafadama Arwa.
Adai dai lokacin ne Aahil yashigo dakin tare dayimusu sallama, bayan yagama sauraron dukkan labarin da Khaleesat taba kanwarshi.
Amsa sallamar sukayi a tare, sannan Arwa tace Yaya kadawo? Allah dai yasa kasamu wacce tadace, tafada tareda kallon ledar dake hannun shi.
Dan daure fuska yayi sannan yace ke Arwa momi nakiranki , toh.
Atare suka Mike Khaleesat tana fadin muje dama ban gaisa dasu momi ba.
Juyawa Aahil yayi batare da yace komai ba Amma aranshi bahaka yaso ba Dan yanason ganin Arwa ne kawai ba wata momi datake kiranta toh Kuma ga Khaleesat tabiyosu.
Tafe yake suna binshi abaya suna cigaba da hirarsu, suna isa Fallon kuwa sukayi sa’ar samun momi da dadi azaune.
Sannu momi sannu dadi Khaleesat tafada tare da Dan russunawa kafin tanemi guri akasa ta zauna , Ina kwana dadi, dariya dadin yayi tareda fadin *Ekaro* , dariya itama Khaleesat din tayi tana fadin dadi andawo lafiya? Ya amsa da lafiya kalau Khaleesat yanzudai angama secondary koh? Toh sora Kuma jami’a, wai mema kikeson zama ne ?.
Murmushi Khaleesat tayi sannan tace dadi inaso inzama lecturer ne kuma inason yazamana ta bangaren *Health* ne, Ah lallai Allah ya taimaka, Ameen dadi.
Dai dai lokacin ne momi tace wato Khaleesat kinata hira da dadinki kinma manta Dani ko?, Hhhhhhhhh dariya tayi mefidda Dan sauti sannan tace momy yi hakuri wallahi banmanta dakeba kingafa mundade rabanmu da dady kekuma muna tare dake, toh naji inakwana Khaleesat? Dariya takumayi tana fadin momy afuwan niyakamata infara gaisheki, to dai gani nayi kinmanta shiyasa natina Miki, to you hakuri Ina kwana, lafiyalau Khaleesat ya mamanku Alaja dasu Raliyat,? Lafiya kalau tacema ingaisheku, toh muna amsawa.
Mikewa tayi danufin yima Arwa magana setaga batanan , batasan cewa sanda taketa hira da su momi Aahil ya janye hannun ta zuwa dakinshiba, wucewa daki kawai Khaleesat tayi a tunanin ta Arwa nacan, toh acan dinma de dataje gani tayi babu kowa se T.V yanata magana shi kadai, wuri kawai tasamu ta zauna tana jiran tsammani.
Acan dakin Aahil dinkuwa bayan ya janye Arwa, kunnenta yaja yarike yana fadin kinfada mata cewa zamuje gobe ko? Yar Kara tasaki kafin tace bance mata komaiba Yaya, seda yasaketane sannan tace wallahi nafada mata Amma Dan Allah karka Kara kamamin kunne tunda dai kaga tun farko kaine bakace min kar infadaba, to wai ma Yaya meye ne aciki Danna fada ta Kaifa ba saurayinta bane , rankwashinta yayi tareda fadin zauna, zaunawa tayi tareda fadin Kai yaya yaude se cin zalina kakeyi, be kulataba.
Naji duk labarin da Khaleesat tabaki gaba daya wanene wannan mlm Khalid din danaji Kuna magana akanshi Aahil yatanbaya?.
Eh wani malamin mune Amma danbautar kasane daya koyar damu natsawon shekara 1, naji to Amma meke tsakaninsu da Khaleesat?.
Tabe baki tayi sannan tace soyayya Mana Amma fa mara amfani tafada tana kallon Aahil tareda ware tafukan hannayenta , keh ! Dan Allah inaso kinatsu kimin bayani sosai gameda abunda kike nufi da soyayya mara amfani.
Gyaran murya tayi sannan tace kasan meye? A’a sekin fada.
Atake tabashi labarin komai da komai tunga farkon haduwar su harya zuwa irin wulakancin daya mata jiya dayazo layinsu.
Dadi yaji aranshi duk da dai alamu sunnuna suna San junansu toh Amma abunda ya faranta mishi rai basu sanar da junansu ba, in Sha Allah senasan duk yadda zanyi dannaga na mallaki Khaleesat, Dan gaskiya Inasonta Ina kaunarta bazan iya Rayuwa babu Khaleesat ba, sannan bazan iya daukar lokuta masu tsawo banganta ko naji muryartaba, to Amma tayaya hakan zata faru?.
Yaya mecece zata faru?, Arwa tafada tareda zare idanuwa tana kallon Aahil, iye ? Babu komai kinji nace wani abune? A’a kawai naji kanacewa ne to Amma tayaya hakan zata faru, se alokacin ya fahimci Ashe maganar dayakeyi azuciya harta fito fili kenan.
Sharewa yayi sannan yace gashi yamika mata ledar dake hannunshi karba tayi tabude tace kasamu kenan , yace eh zakiga sim guda 2 na zain Dana Mtn nariga nayimata register da sunana kawai chargy zatayima wayar tafara amfani dashi Dan har kudi nasa akowani layi sannan Kuma akwai social media kala kala seta zabi Wanda zatayi setai register kawai, sannan ga wannan kibata, kudine yamiko mata acin envelope fari tas 10k ne aciki, Yan 200 ne sabbi fil abunka da gidan ma’aikacin bank C.B.N Kuma a Abuja.
Amma dayake mahaifinnasu *Alhaji Salisu Inuwa* bashi da girman kai, abokan aikinsu dayawa acan Abuja suka gina gidaje manya manya suna zaune acan, kasancewar matar shi dashi mutanene masu San zama tareda talakawa dakuma masu matsakaicin karfi yasa ta Amince yaje aikin shi duk sanda yasamu lokacin seyazo yadinga dubasu, dukda tarin Dukiyarshi inde yana gari shike Jan sallah a masallacin unguwar su, mutumne me ruko da addini gashi da San jama’a, yaranshi kenan biyu Arwa da Aahil, dukkan su seda suka sauke Qur’ani bayan kammala primary din kowannensu. Ma dallah da gida irin wannan.
Sakin baki Arwa tayi tana kallon yayannata, har seda yagaji da kallon yace ke meye haka Kuma?, Yaya wannan irin hidimarfah, ta lafiya ce kuwa? Meyasa kikamin wannan tanbayar ? , Toh gani nayi daga jiya zuwa yau kadage ne da nuna damuwarka akan Khaleesat shine nake tunanin anya ba sonta kake ba kuwa?
Ke bansan shirme so Kuma wani irin Inasonta Kuma kema ba kinason taba, tace Eh Mana Ina sonta Yaya amatsayin ta na musulma yar’uwata , toh kingani tunda kanwata tana sonta itama Kuma tanason kanwar tawa aikinga nima dole insota koh?.
Cewa tayi hakane Yaya to Allah yasaka da Alkairi…..
Ameen kawai Aahil yace yamike yana kokarin fita, sannan yace inkin fito ki kulle min dakina bejira amsartaba ya fice abunsa. Seda Arwa takai kusan 10 mins tana zaune tana mamakin chanji irinna Aahil da yayi lokaci guda .
Fitowa tayi jikin ta babu kwari tareda addu’ar Allah dai yasa ba son Khaleesat yakeyi ba domin inde sonta yake tana hango rikici ya al’amarin Kuma batason a Mai maita abunda yafaru 11years back, koda tafito fallo gani tayi Babu kowa a fallon sedai tashin kamshin girki me dadi ne kawai ya gauraye ko ina.
Daki tashiga, tana shiga ta tarar da kawarta ta ta hada zufa tana ta bacci me nauyi, kare mata kallo tayi sannan tace Allah sarki Khaleesat Allah yakawo Miki karshen wadannan matsalolin kozaki samu sukuni, ajiye ledar tayi, ta gyara mata hannunta da da yasakko kasa ta gefen gado sannan tace Sha baccin ki lafiya dannasan jiya bawani baccin kirki kikayiba tafada tare da kunna mata Ac.
Fita tayi daga dakin ta nufi kitchen gurin momi domin ta tayata girki, tarar da momin tayi tana ta famar soya shinkafa, sannu momi, wai gowa Hajiya Asma’u tayi tace yauwa sannu, Ina kika baro Khaleesat din, tana daki tana bacci, ok dakko waccar abarbar ki fere min , sannan inkin gama ki kankaremin waccar cittar sekuma farar shinkafar dake cikin ruwan nan nariga na wanketa na gyara tsamemin ita kawai zakiyi kihada da sauran abubuwan da kika gyara kisa awaccar babbar blender kinika min su sosai, kitace kizuba a abu me tsafta kisa a fridge, kafin in gama girki, to momi, insa sugar da flavor? A’a karki samun komai kinsan Ni da dadin ku bama son ahada natural and artificial ko, in anzo Sha duk Wanda keson yasa koma menene sekusa, amsawa tayi da toh.
Se wuraren 12:45pm Arwa da momi suka kammala hada abincin su, fride rice, da juice din danyar shinkafa, citta dakuma abarba, sannan ga farfesun manyan kifin ruwa dayasha kayan kamshi da tarugu ta yadda zeyi maganin duk wani tsohuwar mura da Dan sanyi sanyi, kamshi kawai gidan yakeyi dagaji za’a kwashi gara, .
Jere kayan abincin sukayi akan dining table, sannan kowannensu yashiga daki domin yin alwalar sallar azhar Dan har anfara kira.
Koda Arwa tashiga daki har alokacin Khaleesat baccinta kawai takeyi, murmushi kawai Arwa tayi sannan tashige toilet ta doro alwala, bayan ta idar da sallah ne ta tashi Khaleesat domin itama tayi sallah, Ina kikajene kika barni nikadai Khaleesat tafada tare da yin Mika da hamma, Ina dakin yaya Aahil Kuma nashigo naga kinata bacci shiyasa ma na kyaleki Dan kihuta , toh nagode tafada tana kokarin tashi, bayan ta idar da sallah ne tana zaune kan dadduma Arwa Kuma na kishin gide akan gado dawaya ahannunta , motsin shigowar Aahil cikin gidanne dataji yasa ta tuna da sakonshi takalli ledar sannan ta dakko ledar tana fadin kawata Albishirinki , galala kawai Khaleesat ke kallonta sannan tace mene ne abun albishir Kuma? Bansaniba inde bazakice goro ba sedai kibarshi , to goro tafada yayin da take kokarin zama akan gadon, ga sako akace inkawo miki tafada tana Mika mata ledar, karba tayi tana cewa waye yabaki, shiru Arwa tayi tana jiran Khaleesat tabude taga ko meye aciki, please kifadamin waye yace kikawomin? Wanene Wanda yawuce Yaya Aahil, shiru tayi tana Dan nazari tana magana a ranta, toh fah wannan kuma me yake nufi da hakan?, Kibude Mana kigani Mana nabaki abu kinki shiru, dawowa tayi daga tanbayoyin datake azuciyarta sannan ta bude ledar, taga duk abubuwan dake cikin.
Yanzu Ni Ina zankai wadannan abubuwan, tayi tanbayar tare da kallon Arwa, inda ake kaiwa mana . Please ba bakar magana nace kifadamin ba bansan tayadda zanfara bane because kinsan halin Alaja Sarai yanzu tana ganin wadannan abubuwan cewa zatayi Yaya Aahil saurayinane Kuma muddin tafadi haka toh gaskiya bani da bakin da zan mata bayani tafahimceni, Hummm ai ba Alaja kadai ba hatta Ni kaina nagama fahimtar Yaya Aahil sanki yakeyi tafada tareda kanne mata ido daya , Harara Khaleesat ta balla mata sannan tace ke dadina dake se ana serious talk seki kama kisako was aciki.
Daure fuska Arwa tayi sannan ta Kara matsowa kusa da kawar tata takama hannayenta biyu tarike tana kallonta tana fadin wallahi Khaleesat dagaske nake Miki wannan maganar Kuma in dai hasashena yazama gaskiya tofah akwai babbar matsala.
Dan Allah Khaleesat inde har Yaya Aahil nasonki please kidaure kisoshi tafada cikin murya me bantausayi tareda kwalla cike a idonta, hankalin Khaleesat ne yayi matukar tashi daganin abunda bata taba gani a idanuwan kawar tataba, rike mata nata hannuwan tayi tana fadin haba Arwa meye Kuma nakuka , please ki daure kimin bayani meyake faruwane? Kankame hannayen junansu sukayi, sannan tace nasan bantaba baki labarin rayuwar mu kafin muhadu dakeba, nasani kinason khalid Kuma shima yanasonki sosai duk da dai dagake harshi bawanda yataba furtama daya abundake ran Dan uwansa, sannan nikaina bansan meye soba ban tabayi ba but I can recall what was happen to my brother 11 years ago, sannan kuma zan iya fahimta Sarai dacewa irin soyayyar ce me karfi ke tsakaninki da khalid.
Amma duk da haka zan rokeki alfarma da please don’t leave my brother alone, fashewa tayi da kuka me karfi tana fadin, i don’t want to loose my one and only bro, Dan Allah kitaimaka nasan nafi karfin innemi wani abu agareki inkasa samu, tausayine me tsanani yakama Khaleesat rungume Arwa tayi tana Dan bubbuga bayanta ahankali alamar rarrashi seda suka dauki tsawon mintuna 10 ahaka, sannan Khaleesat ta dago kan Arwa taje ta dakko tissue paper akan TV stand tabata tace share hawayenki, sannan ta cigaba damata magana, Arwa!, Na’am, kidaure kimin bayanin dazan fahimta, mene ne yafaru 11years din?,Daurewa tayi take magana, zuciyarta tana wani irin tafasa, Amma afili tayi iya kokarinta wajen shanye damuwarta Dan karta karama Arwa wata damuwar.
Kallonta Arwa tayi da idanuwanta jajaye, tace Khaleesat Yaya Aahil shine irinnamijin dakike so, Dan ayanzu yana da kimanin shekaru 30 kenan mutum ne me hankali da natsuwa, yana da sanin yakamata, yanada hangen nesa , Kuma tunda nataso bantaba ganinshi da wata mace da sunan masoyiyarshiba , ko abokin shi mustapha dasuke karatun likita tare inyazo gidannan bantaba ji yace yana da budurwa ba hasalima tsiya nakeji yana mishi yana fadin wai Kai yaushe zakayi budurwa ne kodai bazakayi aure bane ,sedai Yaya Aahil yayi dariya yace toh kaima inataka budurwar seya nunani yace mishi gatanan Arwa.
Abunda baki saniba shine bahakanan bane yasa su momi da dady basa San zaman mu a Abuja kusa da dady ba, akwai dalilin haka, kuma baya rasa nasaba da abunda yafaru da Yaya Aahil, kafin mudawo kd, domin kuwa da a Abuja muke.
*11 years ago*
Bayan rasuwar kakanninmu ta bangaren uba dama ita mahaifiyarmu marainiyace mahaifinmu ya aure ta, gab da bikin su mahaifinshi yarasu , itakuma mahaifiyarshi bayan haihuwar Aahil tarasu, bayan rasuwar ta da 2years akayima dady transfer daga kd zuwa Abuja, acan akahaifeni, muna tareda wani makocinmu mesuna *Alhaji Sunusi Mu’azu* ana mishi lakabi da *Mesaka* sakamakon taba aiki dayayi a masakar kd da aka kulle shekaru da dama dasuka wuce, yana da yara guda 2, mace da namiji, awancan lokacin I was 7 yrs old, babban yaron nashi sa’an Aahil ne mesuna *Nurudden* alokacin shida Aahil suna da shekaru 19, sungama secondary School sunyi shekara 1 agida kafin suka fara shirye shiryen shiga jami’a, itakuma kanwar Nurudden she was 14 yrs old, mesuna *Rabi’atu, jininsu yahadu da Yaya Aahil sosai.
Da mamanta talura da haka setasa bbnsu Rabi’a yayima dady maganar cewa anya bazasu hada aurensu ba kuwa Dan sunlura suna San junansu sosai, da akayima yaya Aahil maganar se cewa yayi shifa Babu wani soyayya atsakaninsu, kawai shakuwa ce.
Da dady yaji Aahil yafadi haka seya samu momi yace mata, tayima Aahil magana saboda yalura tafishi fahimtar rayuwar Aahil sosai, Dan haka ya umarceta da tasameshi tamishi magana.
Haka kuwa akayi, Wata Rana da safe Aahil yana daki yanata shiri domin yaje yakai Rabi’a makaranta kamar yadda muka Saba kullum dasafe nida ita yake daukar mu, tana j.ss 2, nikuma Ina primary 2, makarantarsu Rabi’a tana gaba da tamu to Amma seya fara kaita kafin yake dawowa ya ajiyeni, wai in ya tsaya saukeni zansa tayi late acewarshi.
Da momi tashiga dakin tarar dashi tayi harya gama shiryawa, yana zaune kan kujerar bedroom dinshi yanasa safa da takalmi, bayan tayi sallama ya amsa tashiga, wuri tasamu tazauna sannan tace, Aahi!!!, Na’am momi, sonawa nakiraka? Momi so 3, inason magana dakaine, momi sauri nakeyi kibari inje inkaisu Rabi’atu da Arwa makaranta indawo Dan karsuyi late, yafada yana kokarin tashi dafe kafadarshi tayi tana fadin kwantar da hankalinka su sunma dade da tafiya nasa *Tanimu driver* yakaisu. Komawa yayi yazauna yana sauraron momi duk da dai bahaka yaso ba.
Aahil inaso intabbatar da gaskiyar meke tsakaninku da Rabi’atu, ba aure mukace zamuyi muku ayanzu ba Amma kaga mahaifiyarta tace inde kanasonta , to tabaka ita Kuna kammala karatu koda secondary ne lokacin kunkara girma , kuma kaima kana gabda gama karatunka na medical doctor,.
Arwa takalli Khaleesat tace kinsan amsar daya ba momi?..
Tsuru tsuru Khaleesat tayi tana kallon Arwa tareda gyada Kai alamar A’a……….
Toh kwatan kwacin irin amsar daya banice yau Dana mishi tanbaya akanki, cemata yayi momi shakuwa ce kawai irin wacce ke tsakaninki da mahaifiyarta Wanda business din laceses da atamfofi yahadaku, irintace ke tsakanin dadi da Alhaji mahaifinta, Wanda kasancewar suna aiki wuri daya yasa, sannan irin sabonne dayake tsakanin Arwa da Nuruddeen, toh waima momi meyasa bakuce akwai wani abu tsakaninsu Arwa ba seni?.
Murmushi kawai momi tayi sannan tace kafin inbaka amsarka zan fara fada maka cewa irin shakuwar ce ke tsakaninku amma ku sakamakon soyayya da Kuma haduwar jini, sannan amsarka Kuma itace su Arwa da Nuruddeen akwai kuruciya sosai in akayi la’akari da cewa Arwa ko 10 yrs batakaiba , Amma kaga kaida Rabi’atu you are all above 10.
Daka tsalle yayi waishi Sam babu wani abu tsakaninsu.
Dadai sukaga abun yaki yiwuwa se suka kyalesu.
Bayan yin maganar da watanni ne wataranar Monday da safe Yaya Aahil da Rabi’atu sukayi fada kome yahadasu oho banmantawa ranar Ina bayan mota da uniform dina ajikina mukaje kofar gidansu Rabi’a yayi tayin horn sannan megadin gidansu yafito bayan sungaisane Aahil yatanbayeshi Ina Rabi’atu yamata magana tafito sutafi aikuwa nan megadi yasheda mishi ai Rabi’a yanzunnan tafita, take yaya Aahil yajuya kan motarshi muka bi hanyar makaranta tunkafin muyi nisa da gidane muna kan titin unguwar mu irin titinnan ne da zakaji shiru se karar motoci Abunka da Abuja kowa gudu yake zubabawa da tafka tafkan motoci.
Akai sa’a kuwa muka fara hangota tana tafiya akafa Wanda yayi dai dai da zuwan wata katuwar mota feeeewwww tawuce mu da karfi.
Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
Innah nillahi wa innah ilaihirraji’un Rabi’aaaaaaaah!!!!!…..
Haka Yaya Aahil yadinga Mai maitawa cikin yanayin tsananin tashin hankali da rudewa me, gaggawar tsaida motar yayi waje yafita da gudu.
Nima bude kofar nayi nafito domin ganin meke faruwa?.
Ina karasawa inda naga mutane suntaru ne, na kutsa , muryar Yaya Aahil nafara ji yana fadin, kitashi Dan Allah Rabi’a karki tafi kibarni please, kiyi hakuri kitashi , kitaimaka min kucemata Rabi’a ta tashi bazan iya Rayuwa babu itaba , kitashi nafahimci komai yanzu, kece Rayuwata zuciyata tana bugawane tare da taki inkika bari taki ta tsaya nima tawa tsayawa zatayi, karkimin haka please help me you are my everything, don’t leave me hanging out in the field, all alone, my life is just a field without you, yana kuka me karfi, jijiyoyin kanshi Dana wuyanshi sun fito sunyi baro baro, ga hawaye masu kama da wutar Kira suna zuba daga idanuwan shi.
​
Name: | [Labarina Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Leave a Comment