*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
بسم الله الرحمن الرحيم
*01*
~~~
*Unguwar Madalla, Suleja, Niger state*
*06:00am*
“RABI’A!, nasan cewa bayan na mutu za ki koma gidan mahaifinki…. ADAWIYYA ina da tabbacin bayan kin koma cikin ‘yan uwanki da zama za ki sha wahala, na san cewa za ki shiga taskun rayuwa kala-kala, na san cewa Habiba ba ta sona, bare kuma ‘ya’yana, na san cewa ba za ta taɓa barinki ki huta ba….. Amma ki riƙe addu’a, ki riƙe addu’a a ko wani irin yanayi kika tsinci kanki. Ki yi haƙuri, domin na san cewa ƙaddarorinki yanzu suka fara. Yanzu LABARINKI zai soma………”
Zubar ruwan da ya cika bokitin da ta saka a famfo ne ya jawo hankalinta daga duniyar tunanin da ta faɗa.
Kanta ta ɗan ɗaga sama ta kalli sararin samaniya, har yanzu garin akwai sauran duhun asuba, yanayin gashi kuma yanayin garin akwai zafi, kasancewar ana tsakiyar kwanki goma na ƙarshen watan azumi ne, dan bai fi saura kwana huɗu sallah ba.
Kanta ta sauƙe ƙasa ta kalli bokitin da ya cika har ruwan ciki na zuba, ta tsugunna zata janye bokitin, wata murya ta daka mata tsawa cikin faɗin.
“Ub*n me kike ne wai Rabi?!, Tun ɗazu bokitin ya cika har yana zuba amma ba za ki ɗauke ba?,Saboda baƙin halli da kika gada a wurin uw*r ki ko?, to ki ci gaba da tsayuwa a wurin, idan ƙarar ruwan nan ya tada min yara sai na ci uw*r ki Wallahi!….”.
Rabi ta ɗago da kanta ta kalli inda matar ke tsaye, hasken wutar nepar dake haske tsakar gidan ya haska mata fuskar matar tar, matar babanta ce, Habiba, matar da akodayaushe burinta ta ga ta lalata mata rayuwa.
Kuma bata tsaya iyaka nan ba, har cikin garin Abuja take turata aikatau, yau shekarunta biyar a gidan, tun bayan rasuwar mahaifiyarta, mahaifinta ya je har garinsu mahaifiyarta ya ɗaukota, ya dawo da ita cikin gidansa, gidan da ita zata iya kiransa da kurkuku. Domin ko da da sakan ɗaya bata taɓa jin daɗin zaman gidan ba.
Babu wanda take jin daɗin zama da shi a gidan sai Saratu, ‘yar Habiban ta biyu, a wasu lokutan ma idan Habiban na mata faɗa har baki take sakawa.
Tun a shekararta ta farko a gidan ta fara ganin uƙuba irin ta matar uba, da ta saba jin hakan a labarai, labarin yanda matan uba kan ƙuntatawa ‘ya’yan mazanjensu, ko da wasa bata taɓa hasaso cewa rayuwarta zata fuskanci abu makamancin wannan ba. Sai gata tsundum cikin wannan hali.
Kuma ƙalubalen nata ya fara ne tun daga sanda ta nemi da Babanta ya maida ta makaranta, yace ai ta gama karatu, shi bq zai iya wahalar da kansa wurin sakata a makaranta ba. Ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba a lokacin, dan Allah ya sani tana san karatu, kuma burin mahaifiyarta ne ta yi karatu.
Bayan wannan sai ta koma baiwa kuma jakar aikin gidan, ‘ya’yan Habiba ko tsinke basa ɗaukewa a gidan sai de ita ta yi. Duka wannan bai ishi Habiba ta gama da rayuwarta ba sai da ta fara turata aikatau.
Kullum iƙirari take kan cewar ba zata ciyar da ita a banza ba, tun da ub*nta bashi da aikin yi, ita take riƙe da gidan, kuma kusan hakan ne, dan Mahaifin nasu ba shi da wani aikin yi, kasancewar an koreshi a wurin aikinsa.
Babu abinda yake sai zaman baza, zuciyarsa ta riga ta gama mutuwa, babu abinda yake sai caca da bin matan banza. Haka Habiban za ta saka shi a gaba tana tsigeshi, kamar wani ɗan da ta haifa, amma ko tari ba ya iya mata, saboda yasan ba shi da gaskiya.
Babu yanda Rabin za ta iya, haka ta yarda ta fara zuwa aikatau ɗin, da ko wani ƙalubale dake fuskantar rayuwarta, Kalaman mahaifiyarta na ƙarashe su ne ke yawo a kanta.
A sanda take mata maganganun, gani take kamar zafin ciwo ne ke nuƙurƙusarta, gani take kamar kawai sambatun ciwo mahaifiyar tata take, dan waɗanan kalaman nata sune maganarta da ta ƙarshe, bata sake magana ba har ta koma ga ubangijinta.
Sai a yanzun take ganin duk abunda take faɗa mata, duk abinda ta ce mata zasu faru gareta su take gani. Dan yanzu haka a wata makaranta dake cikin garin abuja take aikin goge-goge da share-share.
Bata da wani buri a yanzu, bata da wani fata, bata da wani abin da take san cimmawa, dan a ganinta kamar rayuwartace ta zo ƙarahe, kamar LABARINTA ne ya ƙare, babu wani abu da ya yi saura.
Ƙwara ma kawai ta zauna ta rungumi ƙaddararta da ta zo mata a haka, tun da Allah yasa a bautawa wasu rayuwarta za ta ƙare to ta amshi hakan……
Ƙarar turowa ƙofar gidan nasu ce tasa ta juyawa takalli ƙofar. Mama ce ta shigo, ‘yar Habiban ta uku. Amma kuma ba wai hakan ne yasa Rabi mamaki ba, mamaki take na san sanin sanda Maman ta fita ta daga gidan.
Ta san cewa jiya daddare tare suka kwanta, tun da ɗakinsu ɗaya, amma ko da asuba bata ganta ba, fitar tata a daren ba wani abun mamaki ba ne, dan ta saba kwana a waje ma, ta saba bin samarinta su tafi yawon banza.
Sunan ‘karuwa’ da Habiba ta saba kiranta da shi ne ya dawo cikin kanta. Sai kawai ta juya ta ɗauki bokitin da ta juye ruwan cikinsa a randa, ta koma bakin famfo ta kunna famfon ta ci gaba da tsaiwa a wurin tana jiran ya cika. Dan Habiba na gama masifar tata ta koma ɗakinta.
A rayuwar gidansu ta tabbatar da karin maganar nan da hausawa ke faɗin ‘Laifi tudu ne, ka take naka ka hangi na wani’, ita zata bada shaidar wannan, domin duk abinda Maman ke yi da sanin Habiba, dan idan ta samo kuɗi ko kayan kwaɗayin da samarinta kan bata Habiban take kawowa. Ita abun haushinta a nan shi ne; ganin cikin watan azumin Allah ta ala ma bata bar abinda ta saba ba. Sai ta girgiza kanta a fili tana kashe famfon da ruwansa ya cika bokitin gabanta.
“Ub*an miye kike wani girgiza kai ?!”
Maman ta tambaya cike da masifa, dan in dai ruwan bala’i ne, to kaf cikin yaran Habiba babu wanda ya gado shi kamar Maman, dan bata da mutunci, Rabi ta kalleta, sannan ta girgiza kanta.
“Babu komai”
Sai da ta ɗan tsaya na wasu sakanni tana aikawa Rabin harara, sannan ta juya kanta ta shige ɗakinsu.
Rabi ta kuma jijjiga kanta a sanda ta juye bokiti na ƙarshe a cikin randar. Share gidan ta shiga, ta share tsakar gidan tas, kana ta shiga ɗakinsu, dan ɗaukan kayan da za ta sa, saboda wankan da za ta yi.
Tana ɗage labulen da harar Mama ta fara cin karo, sannan ta bi ɗakin duka da kallo, Saratu ce zaune tana guga, sai Fatima ƙaramar ƙanwarsu tana kwance a kan katifarta, sai sharar bacci take.
Bata cewa kowa komai ba, ta ƙarasa shiga cikin ɗakin tana nufar inda take aje jakarta ta Ghana must go.
Zip ɗin jakar ta buɗe, idonta ya sauƙa a kan kayan da suke a saman jakar, kayanta ne, kayan da ta zo gidan da su tun shekaru biyar da suka wuce, dan tun bayan zuwanta gidan ba’a ƙara mata sabon ɗinki ba. Kuma a halin yanzu kayan sun mata kaɗan, ba wai dan ta ƙara ƙiba ba, sai dan girma da shekaru suka ƙara mata.
A yanzu ba ma ta saka kayan, kayan yayarta Baby da ta rasu su takesakawa, dan a sanda Babyn ta rasu ba zata wuce shekarunta ba, duk da Babyn na fama da cutar sickler.
Baby?!, sunan ya maimaita kansa a cikin ranta, a sanda ta ɗago wata doguwar riga sama, rigar ta Babyn ce, kuma ba wannan ne yasa ta tsaya ta ci gaba da kallon rigar ba, sai dan tunawa da ta yi da yanda Babyn ke matuƙar san rigar.
_“Umma ki ce ta bani….” _
Muryar Rabi’an ta faɗi a wancan lokacin, mahaifiyarsu dake zaune a kan sofa tana duba wasu takardu ta juyo ta kallesu, sannan ta kalli rigar da suke kokawa a kanta.
_“To wai ke Adawiyya me za ki yi da wannan rigar ?, in ce de ta miki yawa” _
Rab’ia ta turo baki gaba tana wata shagwaɓa irin tata ta autanci.
_“Wallahi Umma ina san rigar” _
Baby ta fisge rigar daga hannun Rab’ia tana hararta.
_“Ai ko ba zan baki ba….” _
“Yayar ummanta Adawiyyan Umma, rabu da ita, zan sai miki sabuwa, wadda ta ma fi tata kyau…..”
Sai kawai ta ninke rigar ta maida ta cikin jakar, Allah ya sani sam bata san tuno LABARINTA na baya, dan hakan sam bai da amfani a ganinta, saboda wannan wata rayuwace da ta shuɗe a baya, sannan rayuwace wadda ta tafi da abubuwa da dama.
Ciki kuwa harda ita kanta, saboda gani take kamar wannan ba waccan Rabi’ar data sani ba ce, wannan wata baiwa ce dake aikatau a gidan mahaifinta, ba kamar waccan Rabi’ar ba, me rayuwa cikin gata da kulawa, autar ummanta, ƙanwar yayarta, jika mafi soyuwa a wurin kakkaninta.
Wata doguwar riga wadda Saratu ta bata kunce ta ɗauko, ta haɗa da hijabin Baby, sannan ta zuge jakar tana miƙewa. Bayan da ta aje hijabin a kan jakar, hannunta kuma tiƙe da rigar da ta ɗauko ɗin.
“Rabi dan Allah yaushe za ki min ƙunshin ?”
Saratu ta tambaya tana aje rigar da ta gama gogewa. Rabi ta ɗan dakata da tafiyar da take, sannan ta juyo ta kalli Saratun dake kallonta ita ma.
“Saura kwana nawa ne sallar ?”
Saratu ta amsa mata da “Ehhh to!, gaskiya ba na ce ba, amma jiya na ji Umma (wato Habiba, dan haka suke kiranta) na faɗin saura kwana huɗu ne ko uku?…”
“Gobe za ayi hutu a makarantar yarana nan, sai na miki goben, nima ina so ki min kalaba”
Ta ƙarashe tana ɗan dukan kanta da ke ɗauke da manyan kalaba guda huɗu, dan bata kitso, kuma ba komai ya ja hakan ba sai santsi da tsayin da gashin nata ke da shi. tun mahaifiyarta na da rai bata kitso, sai dai Ummar tasu ta kaisu wurin gyaran kai.
Amma yanzu fa ?, gashin nata ma ya fara raguwa saboda rashin gyara, kalabar da Saratun ke mata ita kaɗai kan nata ke samu.
Saratu ta gyaɗa kanta sannan ta ce.
“Allah kai mu goben”
Har Rabi zata fita da ga ɗakin sai ta juyo.
“Wani kala zan miki ?”
“Ɗan gama nake so”
Da ga haka bata ƙara cewa komai ba ta gyaɗa kanta, sannan ta fita da ga ɗakin, wanka ta je ta yi, ta fito bayan da ta gama wankan, saboda yanzu ana cikin azumi shi yasa ayyukanta suka ragu a gidan.
Dan idan baki buɗe ne, sai ta kai niƙan alkamar da Habiba ke yin finkason safe, idan kuwa a week end ne ita ce ma da kanta take suyar finkason. Kuma ta hanyar kuɗin da take samu a finkason, da albashi da ake bawa Rabin a wurin aikinta, Habiban ke iya kula da gidan, dan komai na gidan ita ce ke yi.
Bayan ta shiga ɗakin, mai kawai ta shafa, sannan ta ɗauki hijabin da ta fitar ta saka, ta yiwa Saratu sallama, ta fita.
“…..Kin ji matsalata da ke, dan Allah Habiba yanzu idan baki rufa min asiri ba waye zai rufa min?….”
Rabi ta ja ta tsaya a sanda ta ɗora idonta a kan mahaifinsu tsaye yana ƙanƙan da kansa a gaban Habiba,wadda ta wani ɗaga kai sama tana shirin zazzago buhun masifa.
“Wallahi Ɗan Lami baka isa ba, a kan me zan ɗauki kuɗi na baka?, bacin na san caca za ka je ka yi da su……”
Rabi bata tsaya ta gama jin abinda take faɗi ba ta sa kai ta fita. Kuma abinda Habiban ta faɗi gaskiya ne, dan baban nasu babu wani aiki da yake face cacar, duk kuɗin da zai samu a caca suke ƙarewa.
Sai da ta ɗan tsaya a ƙofar gidansu, ta ɗan ɗaga kai saka, da ga nan inda take tana iya hango dutsen zuma rock, dubanta ya kai kan tarin bolar dake tsallaken ƙofar gidansu.
Bolar har tsiri take dan tsabar yawanta, da sauri ta ɗauke kanta da ga barin duban bolar, dan Allah ya sani idan ma takalleta zuciyarta har wani tashi take, dan ta tsani ƙazanta a rayuwarta.
Haka ta ci gaba da tafiya a cikin ƙazamin layin nasu, wanda kwatanni da datti suka masa ƙawa.
Akasarin mazauna unguwar ta Madalla masu magana da harshen gwari da baagi ne, sannan akwai hausawa sai nufawa, da wasu sauran yarukan, sannan a cikinsu akwai musulmai da cristian.
“…..Rabi!”
Ta juyo saboda jin an kiran sunanta, gamin wanda ke kiran nata yasa ta yi murmushi tana juyowa gaba ɗaya, Zara ce, mutum ɗaya da za ta iya ɗagawa ta kira da ƙawarta.
“Aikin za’a je?”
“Eh mana, keda kika sani”
Suka ɗan yi dariya.
“Kunu kika siyo ?”
Rabi ta tambaya yayin da idonta ya sauƙa kan jug ɗin dake hannun Zaran.
“Eh wallahi, bari na wuce, kafin Umma ta soma faɗan na daɗe….”
Kuma daga haka suka yi sallama, bakin titi ta fita, a titin ma sai da ta yi wata doguwar tafiya a ƙafa, kafin ta iso Ɗan kogi motor park.
Inda ta saba hawa mota, ta biya kuɗin da ta saba biya a kullum, wanda Habiba ke bata dan yin kuɗin motar, saboda da ga gidan nasu zuwa makarantar da take aikin akwai nisa. Tafiyar kusan minti 40 ce.
Sun yi doguwar tafiya a motar, kafin suka isa Joy Emodi CI inda za’a sauƙeta, daga nan ta soma tafiya a ƙafa, wadda ta ɗauketa tsawon lokaci, kafin ta iso makarantar da take zuwa aikin shara.
*Brickhall School, Kaura district, Abuja*
A hankali wata farar mota ƙirar Corolla hybrid ta yi parking a harabar makarantar. ko minti ɗaya ba ta yi da parking ba, ƙofar gidan baya na motar ta buɗe.
Wata matashiya ta fito,sanye cikin wata baƙar pleate skirt, da kaɗan skirt ɗin ta sauƙo gwiwarta, sai farar oxford shirt, wadda ta ɗora maroon suit a kai, daga gefenta suit ɗin na dama an manna symbol ɗin makarantar, wuyanta saƙale da tie, kanta babu ko ɗankwali, sai gashin kanta wanda ya ji gyara, an ɗaureshi cikin pony rail, jelar sai reto take a bayanta. Bayanta goye da backpack ɗinta me kyau, ƙafafunta sanye cikin baƙaƙen sneakers.
Kuma ba ita kaɗai ce ke sanye da irin kayan ba, dan gaba ɗaya ɗaliban dake kai kawo a harabar makarantar sanye suke da irin kayan jikin nata, maza ne kaɗai ke saka wando, kuma shi ne abinda ya banbantasu, hakan ke nuna cewa kayan shi ne uniform ɗin makarantar.
Tafiya ta fara cikin takunta na wanda ƙuriciya bata gama saki ba.
“MISHAL!, kin manta abincin ki….”
Muryar drivernta malam Ali ta faɗi da ga cikin motar.Tsayawa ta yi da tafiyar, sannan ta juyo ta kalli motar, kafin ta fara takowa zuwa wurin motar.
Ba tare da ta ce masa komai ba, ta buɗe gidan baya ta ɗauki lunchbox ɗin nata, ta rufe ƙofar motar, kana ta ɗaga masa hannu alamun bye, sannan ta yi gaba.
Malam Ali ya girgiza kai yana murmushi, a cikin ransa ya na wa Mishal ɗin fatan shiryuwa, ita duk gari ana azumi amma banda ita, zai iya cewa tun da aka fara azumin ma bai fi guda goma ta yi ba, da ya mata magana ma sai tace masa wai akwai wahala haɗa azumi da zuwa makaranta.
Duk inda ta wuce sai an bita da kallo, amma ita ko a jikinta, dan bata damu ba, saboda wannan ba shi ne karo na farko da aka saba bintada kallon ba, wasu kallonta suke cikin tsoro saboda sanin halinta, wasu kuma cike da burgewa saboda sanin jarumtarta, wasu kuma suna kallonta ne cikin jin haushi, wata ƙila saboda faɗa ya taɓaa haɗasu.
Bata ko kalli kowa ba, duk da tasan cewa kowa kallonta yake. Har ta kai ƙofar class ɗinsu, ta saka ƙafarta a cikin ajin, sai kuma ta dawo da baya, ta gyara tsaiwarta tana kallon wannan yarinyar.
Yarinyar da ke aikin shara a makarantar tasu, ba yau ne karo na farko da ta fara ganin yarinyar ba, hasalima tafi wata shida tana ganin gilmawarta a makaranta.
Ba wannan ne yasa take kallonta ba, kawai rayuwar yarinyar ce ke bata tausayi, dan da alama yarinyar na cikin halin ƙuncin rayuwa, ita kuma haka Allah ya yi ta, duk da baƙin halinta da rashin jin maganarta da wasu ke gani, Allah ya hallici zuciyarta da tausayin wanda bashi da shi, haka Allah ya saka mata tausayin yarinyar.
Duk da ba za ta iya kiranta da yarinya ba, saboda da alama ta girmeta, saide bata kai sa’ar Akinta(Yayanta) ba.
Da alama ma ita yarinyar bata lura da ita ba, dan moping ɗin floor take bil haƙƙi da gaskiya. Ba tare da ta yi komai ba, ta juya ta shiga ajin nasu.
Malamin geography ne a ciki, kuma tana shiga ajin ya yi tsit!, kallo ya dawo kanta kamar kullum. Ba tare da ta damu ba ta nufi seat ɗinta.
“Ke Hafsat Muhammad Auwal!”
Uncle ɗin geographyn ya daka mata tsawa, ta juyo ta kalle shi da sauri, idonta babu ko da ƙwayar tsoro a ciki, dan bata saba jin tsoron kowa ba, kowa gani take kai kai ɗaya yake da ita.
A hasalle Uncle ɗin ya cillar da littafin da ke hannunsa, ya ɗauki wata cane ya yi kanta, yana ƙarasawa kusa da ita ya ɗaga bulalar sama zai zabga mata ta kai hannunta ta riƙe bulallar.
“Babban kuskuren da za ka yi shi ne duka na da wannan bulalar, dan Wallahil Azim ka kuskura ka dakeni sai na rama”
Ta ƙarashe tana wancakalar da bulalar, Uncle ya haɗiye wani abu a maƙoshinsa, yana ci gaba da kallon yarinyar, Ba ƙaramin jajircewa ya yi ba da har ya iya yunƙurin dukan yarinyar, dan malamai da dama na yawan bada labarin yarinyar a staffroom, wasu da ga cikinsu ma kan ce wata ƙila aljana ce, dan normal ɗan adam ba zai iya abin da yarinyar nan ke yi ba.
Ta addabi kowa a makarantar, watan da ya wuce har wani malami ta mara, ɗalibai kuwa kullum sai an samu wanda zai kawo ƙararta.
Sai da ta aika masa harara, sannan ta aje jakaarta a kan desk, ta zauna tana baza ƙwayoyin idonta a cikin ajin, hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa.
Sai da ta yi ƙwafa sannan ta buɗe jakarta ta ɗauko littafi ta gyara zamata ta shiga kwafar note ɗin da uncle ɗi ya ci gaba da yi.
*
“Wai me yasa ke bakya azumi kamar ‘yan uwanki musulmai”
Muryar Angelica yarinyar Mishal ta faɗi a sanda aka fito break, dan sai dai a kirata da yarinyarta, saboda duk wani aike ko bautar Mishal ɗin ita Angelican ce ke yi. Kuma kaf makarantar Mishal bata da ƙawa ko ɗaya, ita ma Angelican ita ta cuso kanta gareta. Mishal ta ture flask ɗin gabanta tana miƙe ƙafa.
“Saboda bana san wahala, bazan iya haɗa azumi da zuwa makaranta ba”
Ta bata amsa cikin harshen turanci, kamar yanda itama Angelican ta mata maganar cikin harshen turancin, kasancewarta baturiyar Engiland. Aiki ne ya kawo mahaifinta zama a nigeria.
“Amma su Rashida su na yi”
“Baki ji me nace ba ?”
Sai Angelica ta girgiza kai, tana kai loma bakinta.
“Kai ka ga wata balarabiya”
Wani sabon ɗalibi da ya fara zuwa makarantar ya faɗi yana kallon Mishal da ga nesa, abokin nasa da ake nunawa Mishal ɗin ya juyo ya kalli wurin, kuma a lokaci guda idonsa ya zare cike da tsoro da kuma mamaki.
“Kai!!, karfa kace min santa kake!”
Sabon ɗalibin me suna Abdul ya yi murmushi.
“Ka jika da wani zance, waye zai ga wannan kyakyawar ya ce ba ya so, Allah da da na ganta na ɗauka balarabiyace”
Abokin ya haɗiye wani abu.
“Abdul da ka je ka ce kana san wannan, gwara ka samu Madam Joke (Malamarsu ta Math) ka ce kana santa”
Abdul ya ƙyaƙyale da dariya.
“Kai ana gabar kana yamma, me zan yi da wata Joke arniya kuma tsohuwa, ga kyakkyawar baby a nan”
“Idan za ka ka bar jirana, tun da na haneka baka ji ba, idan ka je ita zata maka bayani….”
Kuma yana kaiwa nan ya fita da gudu ya bar wurin zaman cin abincin nasu. Abdul ya bi bayansa da kallo yana dariya, ya gyara tie ɗin wuyansa, sannan ya gyara stocking ɗin wandonsa, ya nufi wurin da kyakkyawarsa take.
“Ke rabu da assignment ɗin nan, wallahi bazan yi ba, in yaso idan mun haɗu da python ya kasheni” Cewar Mishal
Pytho shi ne sunan da suke kiran malamin math ɗinsu da shi, kuma sunan ya samo asaline tun sanda suna jss3, lokacin da ya koyar da su Pythagoras rule.
“Ke idan ki ka ƙi yi ba damuwa, ni fa ?, wata ƙila ya karyani, gwara na je na yi”
Angelica ta ƙarashe tana miƙewa tare da barin wurin.
Mishal ta gyara zamanta tana aika lomar abincinta baki, kafin wata murya ta daki dodon kunnuwansa.
“Salam!”
Kuma kafin ta ɗago da kanta ta amsa sallamar, har wanda ya yi sallamar ya ja kujerar da Angelica ta tashi ya zauna. Mishal ta ɗan kalleshi na wasu sakkani. Bata taɓa ganinsa a makarantar ba, hakan kenuna mata cewar sabon zuwa ne, dan in ba baka ba,babu yaron da ya isa ya yi gigin mata magana kaf brickhall.
“Ba kya azumi ne na ga kina cin abinci?…”
Bata amsa shi ba, sai kallonsa da ta ci gaba da yi da olive green color eyes ɗinta.
“A wani class kike ?”
Yanzu ma bata amsa shi ba, hakan yasa Abdul tunanin ko de bata jin hausa,sai de kuma farin fatarta baya kama da na larabawa, farace, fara kuma sosai, sai dai ba irin farin fatar larabawa da turawa ba.
Kyan fuskarta, idanuwanta da kuma gashin kanta sune suke kama da na larabawan, idan zai iya sakata a jerin mutanen nigeria, sai dai a danganta ta da jinin shuwa arab.
Mishal ta zuƙi taliyar indomien da ke bakinta,sannan ta ci gaba da kallonsa.
“Can’t you speak hausa ?”
“Me kake buƙata ?”
Ta tambaya da hausa tana kallonsa.
“Ashe dai kina ji….”
“Na ce me kake buƙata ?”
Abdul ya ɗan shafa kansa sannan ya ce.
“Idan ba zaki damu ba, shin zamu iya yin soyyaya”
Sai ta yi murmushi, wanda ya bayyana ƙarafunan braces ɗin dake saman haƙwaranta, wanda Abdul ya ɗauke shi a matsayin amasar tambayarsa, sai shi ma ya yi murmushin.
Mishal ta rufe flask ɗinta a karo na biyu, sannan ta miƙe ta zagayo ta ɓarin da Abdul yake.
“Miƙe pls”
Yana murmushi ya miƙe tsaye. Tashi ɗaya Abdul ya ga yanayin fuskarta ya sauya zuwa fushi mabayyani.
Sannan ba ta yi wata-wata ba, ta ɗaga hannunta na dama ta ɗauke shi da maruka uku kyawawa.
*
Tsaye suke a office ɗin principal ita da Abdul ɗin da ta fasawa baki da marin da ta masa, bayan shi Abdul ɗin ya kawo ƙararta office ɗin principal ɗin.
Principal ɗin nasu ya kalleta da kyau, bayan da Abdul ya gana tsara masa aabin da ya faru, kuma ko musu ba ta yi ba, ta amsa lefinta, shi a rayuwarsa bai taɓa ganin yarinya irin wannan Hafsat ɗin ba. Kullum cikin kawo ƙararta ake, ba ga malamai ba, ba ga ɗalibai ba, kuma shi yarasa yanda zai yi da yarinyar. Shi dai ba zai iya korarta daga makarantar ba, saboda tana da ƙoƙari, tana ɗaya daga cikin ɗaliban da suke alfahari da su a makarantar.
“Hafsat, me yasa kika mare shi?”
Mishal ta wani juya idonta a cikin office ɗin, sannan ta ɗan sosa hannunta.
“Zuwa ya yi yace wai yana so na…”
“Kuma da ga cewa yana sanki sai ki mareshi ?”
“Ai dokar makaranta ya karya, shi yasa na mareshi, ya godewa Allah ma da ban karya masa hannu ba”
Principal ya ci gaba da kallon yarinyar, ba wai da wasa take faɗar hakan ba, a bakin gaskiyarta take faɗin zata karya shin, dan ta karya ɗalibai biyu a makarantar, kuma tun daga junior ta fara makarantar, sannan tun da ga lokacin kullum sai an kawo ƙararta.
Wani lokacin ma a ajinsu na koyon kung fu take dukan ‘ya’yan mutane, hakan yasa shi da kansa yace ta fita da ga anjin koyon kung fu ɗin, amma yarinyar fir taƙi, kuma taƙi ɗaukar ko wani sport sai kung fu ɗin.
“Ga wannan takardar, ki kaiwa yayanki”
Hannu ta kai ta karɓi takardar, sannan ta sa kai ta fice, ba wannan ne karo na farko da suka taɓa bata takardar suka ce ta kai masa ba, dan idan da sabo ma yayan nata ya saba zuwa makarantar a kan matsalarta.
A kusa da staffroom ɗin malamai mata ta ga wannan yarinyar….wannan yarinyar da ke tsananin bata tausayi. Sai kawai ta tsaya da tafiyar da take, ta nufi wurin yarinyar, dan tana so tai mata magana.
“Sanu da aiki!”
Yarinyar da ke sharar ta yi saurin ɗagowa ta kalleta, ita ma yarinyar ta gane Mishal ɗin, tana yawan ganinta a makarantar.
“Menene sunan ki”
Mishal ta tambaya fuskarta ɗauke da murmushi. Sai da yarinyar ta haɗiye wani abu, sannan ta amsa mata da.
“Rabi’a”
Mishal ta gyaɗa kanta.
“Me yasa kike aikin shara a nan?…”
Rabi ta gyara ruƙon tsintsiyar dake hannunta, to me yasa take mata waɗanan tambayoyin ?, amma kuma abun yaso ya bata mamaki, dan gaba ɗaya ɗaliban makarantar babu wanda ma yake kallonta da kima ko mutunci, kallon banza suke mata, ga wahalar da suke bata, wasu ma har tsokanarta suke.
“Am….Imm…ummm”
Ta kafa inda-inda, dan bata santa ba, batama san me za ta ce mata ba.
“Is it personal issue?”
Kuma tun kafin Mishal ɗin ta yi tunanin cewa ba lalle ace tana jin turanci ba Rabi ta amsa mata da sauri.
“Yeah, it’s personal”
Mamaki ya kama Mishal, duk da dama yarinyar bata mata kama da irin villegers ɗin nan ba, ta fi kama da waɗanda ke cikin ƙuncin rayuwa, duk da ba a walaƙance take ba, amma kana ganinta zaka ga hakan, sai dai kuma yanayinta na wayyayun ‘yan mata ne.
Sai kawai ta gyaɗa kanta.
“Gobe za ayi hutu, inaso ki min siffa, kin iya ?”
Girar Rabi ta haɗe wuri guda alamun kokwanto.
“Menene siffa ?”
Mishal ta ɗan daki gaban goshinta.
“Lalle nake nufi, kin iya?”
Sai Rabi ta yi murmushi, a shekaru zata iya girmewa yarinyar, amma da alama yarinyar tana da kirki.
“Na iya, kina so na miki ne?”
Da sauri Mishal ta gyaɗa mata kai, kuma da gaske tana buƙatar amata siffar, dan sallar azumin ba a Abuja zasu yi ba, a mahaifarsu zasu yi, wato Maiduguri.
“Wanne kike so, ɗan gam ko ɗan zane ?”
“Ni dai baƙa nake so, kuma a hannu za ki min”
Sai Rabi ta gyaɗa kanta.
“A ina zan miki ?”
Mishal ta juya tana kallon inda suke, to a ina da suka haɗu ?, a makaranta suka haɗu, to a ina zata mata da ya wuce makarantar ?.
“A nan mana”
Rabi ta zaro ido tana jinjina yarintar yarinyar.
“Makaranta ce fa”
“To sai me?, kin ga kawai zan sa a siyo min lallen, gobe zaki min, sunana Mishal”
Rabi ta kuma gyaɗa kanta….kafin wata murya ta yi magan da ga ƙofar staffroom ɗin malamai mata.
“Ke!, da kika tara wannan sharar a nan ub*nki ne zai kwashe!”
Rabi ta zabura za ta koma ta ci gaba da sharar da take.
“Kawai sai ki zagi ub*nta, me ta miki ?”
Muryar Mishal ta katse mata hanzari, da sauri Rabi ta juyo ta kalli Mishal ɗin, wadda ta wani haɗe rai, tana kallon malamar.
“Ke ba na ciki da rashin kunya, ki bar ganin sauran malamai su na ƙyaleki, wallahi ni ub*nki zan ci….”
“Ahir ɗinki Abu, ub*ana ya fi ƙarfinki, wallahi ki fita sabgata, in ba haka ba yanzu zan nuna miki kalar nawa rashin hankalin, kuma ki musa ki gani”
Mishal ta katseta tun kafin ta rufe bakinta, kuma cike da rashin kunya take maganar, tana yi tana nuna malamar da ɗan yatsa.
“Bamu taɓa haɗuwa da ke ba ne, dan kina malamar art ba shi zai hana na bi ta kan mutuncinki da kika zubar na wuce ba, dan haka ki kula, kuma sharar ba zata kwashe ba, ki yi abinda kike ganin zaki iya….”
TALLAH!
Salma’s Graphics:
•Muna haɗa book cover.
•Banner
•poster
•Certificate
Kuma duka a kan ₦ 300 kacal.
Domin neman ƙarin bayani: 08130172702.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters
°°°°°°°°°°°°°°°°
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*02*
~~~
*No.234, Efab Estate, Gwarinfa, Abuja*
*06:00pm*
Me gidan Abubakar Muhammad Auwal, tare da matarsa Hajjara, sai yaransu guda biyu, Hammad wanda ya ci sunan kakansa da kuma fahima, ‘yar jaririyar da bata wuce wata biyar ba. Su ne zaune a kan danning table. Wanda ke shaƙe da kayan buɗe baki kala-kala.Da alama jiran kiran sallah suke, dan ƙiris ya rage a kira sallahr.
Ƙofar ɗaya daga cikin ɗakunan falon ce ta buɗe, farko keken guragu ne ya fara bayyana, zaune a kan keken kuma, wata matashiyar yarinya ce, wadda ba za ta wuce 9yrs ba. Kallo ɗaya zaka mata ka ga nakasarta, dan bata da hannaye gaba ɗaya, sannan kanta a langwaɓe gefe guda, bakinta nazubar da yawu.
Mishal ce ta biyo baya,wadda ita ce ke turo keken, sanye take da wata farar linen tunic dress, da kaɗan rigar ta sauƙo gwiwarta, ga kuma rigar ko hannu bata da shi, kanta babu ɗankwali kamar yanda ta saba zama, gashin kanta tifke cikin braid(kalaba) guda ɗaya, ta saka hair band daga sama.
Gaba ɗayansu suka kalli wurin, kuma daga Hajjara har mijin nata basu ɗauke idonsu a kansu ba har suka ƙaraso danning area ɗin.
Kujera ɗaya Mishal ta kawar ta mayeta da keken Firdaus, wadda take kira da Daala.
Sannan ita ma ta samu kejera kusa da ita ta zauna, sai da ta ɗauki tissue ta gogewa Daalan yawun da ya zubo mata sannan ta juyo tana kallon mutanen dake kan danning ɗin.
Hajjara ta kawar da kanta tana taɓe baki, Allah ya sani, har cikin zuciyarta bata san Mishal, wata ƙila dan igiyar aurenta da ta taɓa zama sanadiyyar tsinkewa ne, ko kuma dan rashin kunyar da take mata.
Mishal ta kalli yayanta,wanda shi ma ita yake kallo, hannunta na dama ta ɗago, wanda ke riƙe da envelop, ta miƙa masa.
Abubakar ya girgiza kansa, ya san duk yanda aka yi wani laifin ta aikata, ba yau ta saba kawo takardu irin wannan ɗin ba, hasalima suna nan tili guda yana ajewa, dan sun ma fi yawan report ɗin ta na makaranta da take kawowa. Abu ɗaya ne yasa ba zai cireta daga makaranta ba kwata-kwata, hazaƙarta ce tasa hakan, dan ba ma shi ba, hatta da makarantar suna tinƙaho da ita, gashi de ba wasu shekaru ne da ita ba, amma girman jikinta ne zaisa ka zaci wata babbace.
“Me kuma kika yi ?”
Ya tambaya yana karɓar envelope ɗin, kanta ta sunkuyar, tana wasa da yatsunta.
Murmushi kawai ya yi a sanda ya buɗe ya karanta, dan bi da bi ya gama haddace kalaman da ke ciki, saboda a kullum abu iri ɗaya suke turo masa tun tana junior. Ya rasa irin abunda ke damun ta.
“Hammad yace min yau baki yi azumi ba, bayan shi ma yau yana yi”
Ta ɗago da kanta ta kalli Hammad ɗin dake gefen uw*rsa, kamar yanda bata san uwa*r yaron shi ma haka ta tsaneshi, dan kaf halayen uw*rsa babu wanda bai ɗauko ba.
“Saboda makarantar da nake zuwa ne…”
“Makaranta sai ta hanaki azumi?”
Sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.
“Bari na je waje…..”
Bayanta ya bi da kallo yana mamakin halin yarinyar, du-du-du ba za ta wuce 17-16 ba, har yau yana tuna yanda ya ɗauketa da hannayensa ranar da aka haifeta, da kuma irin maganar da mahaifiyarsu ta masa a wancan lokacin.
_“Sadiq, ka kula da ita, nasan za ta tashi cikin maraici, bata da kowa sai kai, kada ka danƙa renonta a hannun kowa, ciki kuwa harda Amma (tana nufin mahaifiyarta), ka kula da ita, ka kula da ita……”_
Kuma kalamanta na ƙarshe kenan, a kan idonsa a ka shiga da ita ɗakin tiyata. sai kawai fito masa aka yi da jairiya, aka ce ta haihu, amma ta rasu sai dai babyn da ta haifa.
“Wai haka za’a zuba ido ana kallon yarinyar nan tana abinda take so?…..”
Hajjara ta faɗi a ƙufule, dan Allah ya sani ta gaji da halin yainyar, kuma da ma tun sanda ta ɗora idonta a kan yariyar ta washeta.
“Me ta yi ?”
Ya furta hakan cikin halin ko in kula, yana ninke takardar da Mishal ɗin ta bashi.
“Jiya fa na yi baƙi, baka ga rashin kunyar da ta min a gabansu ba”
“Yarinta ce take damunta, idan ta girma za ta dena”
Haushi kamar ya kashe Hajjara, dan dama abin da ya saba faɗa mata kenan, a duk sanda ta kawo masa ƙarar Mishal ɗin, yau ɗin ma tsautsayi ne yasa ta kawo ƙararta, a ranta ta yi ƙwafa, Allah ya kawo ranar da za ta ga bayan yarinyar nan.
Idonta ya sauƙa a kan Daala dake ta zubar yawu, ita ma yarinyar Hajjaran take kallo. Tawarta ɗaya kenan a duniya, wannan yariyar da Allah yasa ta haifota a nakashe, kuma nakasar yariyar yasa ta gujeta, babu wani abu dake shiga tsakaninta da yariyar irin na uwa da ‘yarta, Mishal da Naani ɗin da Abubakar ya ɗauko su ne ke kula da yarinyar har wa yau.
Mishal na fita daga falon gidan BQ ta wuce, dan bata da wurin zama a gidan da ya wuce BQ ɗin, in baka sameta a BQ ba zaka sameta tare da Daala suna wasa, dan Allah ya ɗora mata ƙauna da tausayin yarinyar.
Ganin yanda Hajjara ke bagarar da lamarin yarinyar saboda nakasar dake tare da ita, ita kuma Allah ya hallici zuciyarta da wani irin tausayi, kuma tausayin ne ke sakawa bata da aminan hira a gidan sai masu aikin gidan.
A bakin ƙofar BQ ɗin ta tsaya, tana ƙare musu kallo. Mutum biyar ne zaune a kan bujukura. Ladi, wadda ita ce ke kula da Daala sai mijinta Malam Audu, wanda ke musu gadi, sannan Khalifa, ɗan Mama Ladin na farko, wanda shi ne yake musu sharar garden da ta compound da ma aike idan ya taso, sai Shatu ‘yar Mama Ladin ta biyu, sai autar Mama Ladin wato Ummul.
A taƙaice de duka ahalin Mama Ladin ne, waɗan da suka kasance ahalinta ita ma, dan bata da wurin zuwa da ya wucenasu, Shatu kuma ita ce wadda zata iya kira da ƙawarta, Mama Ladi ta zame mata uwa.
“Ah-ah, Hafsatu, ƙaraso mana”
Sai ta yi murmushi har ƙarafunan braces dake saman haƙwaranta na bayyana, tana ci gaba da kallonsu, su ma sai hadaniyar haɗa kayan shan ruwansu suke, a hankali ƙafafunta da babu takalmi suka ci gaba da takawa har zuwa kan bujukurar. Guri ta samu kusa da Shatu ta zauna.
“Yau kin yi azumi ?”
Mama Ladi ta tambaya, yayin da take juye tiyara a cikin wata doguwar roba, Mishal ta girgiza kanta.
“Ban yi ba”
“Haba uwata, sau nawa zan faɗa miki cewar kin isa azumi ?, bai kamata ace ki na shan azumu ba gaira ba dalili ba”
Cewar Malam Audu yana aje radion hannunsa.
“Rabu da ita Baba, ai kullum gaya muku nake cewar yarinyar nan raguwace, amma bakwa yarda” Cewar Khalifa.
Mishal ta turo baki gaba tana sosa kanta.
“Allah ni ba raguwa ba ce, a class ɗin Kungu fu ɗinmu fa kullum ni nake zuwa a farko, kuma watan da ya auce ma saida na karya wani malamin mu….”
Hannunta ta kai ta rufe bakinta, sakamakon suɓul da bakan da ta tuna cewar ta yi, dan tasan yanzu Mama Ladi za ta shiga mata faɗa.
“Kema kin san cewa ba dai-dai kika yi ba kenan, shi yasa kika rufe baki” Cewar Mama Ladin tana miƙawa Baba pure water.
Sai kuma ta sauƙe hannun nata.
“To ai shi ne ya min tsawa, kuma ya dake ni….”
“Ai haƙuri ake uwata, idan kika yi haƙuri sai labari, dan wata ƙila ma kina gama makarantar auren ki za ki yi”
Ido waje take duban Baba.
“Aure fa Baba ?, a’a ni ba wani aure da zan yi yanzu, nawa ma nake da har zan wani yi aure?”
Abinda bata sani ba shi ne, waɗanan kalaman nata zasu mai-maita kansa a cikin kanta kwanaki kaɗan masu zuwa, dan bata da masaniyar ƙaddarar da Allah ya hukunta za ta faru a ‘yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura, ta kuma zama silar ɓacin wasu.
A wurinsu ta zauna ta sha ruwa, har sanda su Baba suka fita Sallah, Sai da Mama Ladi ta mata jan ido a kan ta tashi ta je ta yi sallah, dan Allah ya sani, zuciya ɗaya take zaune da yarinyar, ganin ta ɗauketa kamar uwa, shi yasa ita ma ta ɗauketa kamar ‘ya.
Saboda rayuwar yarinyar tana buƙatar kulawar uwa, gashi ita kuma bata taso ta samu hakan ba.
Ko da ta koma cikin gidan ɗakinta ta wuce. Wani haɗɗaɗe kuma ƙawattacen ɗaki wanda aka cika shi da kayan buƙata irin na matasa dai-dai shekarunta. Komai na cikin ɗakin peach color ne, sannan ga tarin teddies a ko wata kusurwa ta ɗakin.
Lokarta ta buɗe, da ƙyar ta samu hijabin da ta saka, dan ba saka hijabai take ba, hatta da kayanta yawancinsu ƙananu ne, bata sakka kayan hausawa sam, a cewarta takura mata suke.
Bayan ta yi sallar ta fita falo, a lokacin Daala ce kaɗai, zaune kan kujrarta tana ta gwalantunta, bakinta sai zubar da yawu yake.
Zama ta yi kusa da ita, ta kunna musu tashar mbc 3, sannan ta shiga bata labarin da ita kanta tasan cewa Daalan ba fahimta take ba.
Hammad ne ya shigo falon ta ƙofar ɗakinsa,byana shigowa ya ɗauki remote control ya sauya tasha. A fusace Mishal ta yi kansa.
“Sh*ge ub*n baƙin hali, dan me zaka sauya mana tasha?, dan ka ga ban maka magana a kan munafurcin da ka min ɗazu ba ko?”
Ta ƙarashe tana ƙwace remote control ɗin tare da maida mbc 3n da suke kalla.
“Bar falon nan kafin na karya maka wuya”
Da gudu ya yi sama. Kuma bai tsaya ko ina ba sai a ɗakin Hajjara, wadda ke kwantar da Fahima a kan gado, sakamakon baccin da ta yi. Ƙarya da ƙarerayi ya sameta ya zayyana mata.
Kafin ita kuma ta bazamo ta sauƙo ƙasan ta samu Mishal ɗin tare da balbaleta da masifa, cikin ƙaraji da ɗaga murya take faɗan.
“Wai ke yarinyar nan me kike nufi ?, so kike mu fice mu bar miki gidan ko me ?, to wallahi baki isa ba, shi har gwara shi, tun da nan gidan ub*nsa ne, ke kuma fa ?, sakabu fa kike, to wallahi ki fita idon yarana!……”
Ba komai Mishal ke fahimta cikin kalaman nata ba, sakamakon ciwonta da ya shiga ƙoƙarin tashi, dishi-dishi take ganin komai, numfashinta ya shiga ƙoƙarin ɗaukewa daga ƙirjinta, waccan ranar ta soma dawowa cikin kanfa.
_“Yau daga ni sai ke, kuma babu me ƙwatarki a hannu na!….”_
Abinda ya biyo bayan kalaman nasa sune ya zama silar shigarta cikin halin da take a yau.
Numfashinta ya ci gaba da yin sama, da ƙyar take iya janyo shi. Zuwa lokacin Hajjara ta tuna da ciwon nata, sai ta tsaya a gefe tana kallonta kawai, a ranta addu’a take, kan Allah yasa idan nunfashin nata ya yi sama kada ya dawo.
Mishal ta kai ƙasa tana dafe da wuyanta, sai neman iskar da za ta shaƙa ta ke, duk da sanyin acn dake falon sai gumi take, tuni idanuwanta sun kaɗa sun yi ja, har hawaye ya fara sulalowa ta gefnsu, sai jan nunfashi take kamar me asthma.
Fatan Hajjara bai karɓu ba, dan a dai-dai lokacin da ta faɗi ƙasa gaba ɗaya, a lokacin ne ƙofar falon ta iyo ciki, alamun wani ne zai shigo, kuma bai fi tazarar sakan ɗaya ba, siffar Abubakar ta bayyana a cikin falon.
RABI POV.
Zaune take daga gefe a kan dakalin ƙofar ɗakinsu, yayin da Habiba da sauran yaranta ke zaune a kan tabarma suna kiciniyar shan ruwa.
Ba yau aka saba haka ba, kusan kullum hakan ake, a duk sanda za su taru irin haka, to ita za ka ganta daga can gefe tana kallonsu.
Amma yau ɗin ba kallonsu take ba, tunanine fal kanta, tunani take kan abinda ya faru ɗazu a makarantar da take aiki, abinda ya faru ɗazu tsakanin Malamar nan da yarinyar da ta kira kanta da Mishal.
Yanda yarinyar ta haƙiƙance kan ba za ta kwashe sharar ba, ita da ta mata magana, sai ta ganta a matsayin me sauƙin kai, ashe ba haka ba ne.
Dan da ƙyar ta samu ta tausheta, sannan ta haƙura ta tafi, kafin ita Rabin ta dawo kan malamar ta bata haƙuri, kana ta ci gaba da sharar da ta fara.
“Ni ban ga Abba ba”
Cewar Saratu, kuma maganar tata ce ta dawo da Rabi zahiri.
Habiba ta yi tsaki tana taɓe baki.
“Yana can yawon gantalinsa mana”
“Gaskiya Umma bakya kyautawa Wallahi, kullum ina faɗa miki cewar abinda kike bai dace ba….”
Cewar Saratu, kuma tun kafin ta ƙarashe Mama ta tari numfashinta.
“Eh, me u*a, an taɓo mata ƙahon zuciyarta, yau ni Allah na tuba har na kalli wannan abun na ce shine ub*na?!….”
“Mama ya isheki haka…. Da kike rena shi a yanda yake, gwara shi sau dubu da iyayen wasu, kuma ub*n mutun ko a bola yake kwana indai har shi ne ya haifi mutum ro ub*nsa ne, ko miji bai isa ya amsa sunan uba ba…. Kuma ki sani cewar; da ub*a ake ado…..”
Kuma Saratun na kaiwa nan ta miƙe daga kan tabarmar ta faɗa ɗakinsu har tana ƙoƙadin bangaje Rabi.
“Aikin banza…. Umma mi ye na faɗa ba dai-dai ba ?”
Mama ta tambaya tana tauna doyar bakinta, dan bisa ga dukkan alamu ma ba ta yi azumin ba yau”
“Wallahi baki da laifi, me ake da Ɗan Lami a rayuwa?!, ita ma in ta gaji da abinda ake masa ne a gidan nan,ta yi zuciya ta nemi mijin aure….”
Ita dai Rabi sai ido, dan bata isa ko tari ta yi ba, bata da wani kataɓus a gidan, yau wanda ya kawota ya aje ma bashi da iko da gidan bare ita karan kaɗa miya.
“Umma babu ruwan sanyi fa…”
Habiba ta kalli Fatima, sannan ta kalli ruwan dake aje a can baranda.
“Yanzu ke dan baƙin hali kinsan babu ruwan sanyi a gidan shi ne kika yi shiru, yanzu da an kira sallah fa?”
Ta kawar da kanta.
Habiba ta yi ƙwafa tana cince ƙullin dake gefen zaninta, ta fito da nera ɗari biyu, sannan ta cillawa Rabi.
“Karfa, uw*r ‘yan baƙin hali, tashi ki je ki siyo mana ruwan sanyi leda ɗaya, kuma idan kin so ki zauna a can kin ji ?”
Rabi ba tace komai ba, ta miƙe tsaye, sannan ta shiga ɗakinsu ta ɗauki hijabinta, ta fita.
Mama ta bi bayanta da harara.
“Wallahi na tsani yarinyar nan, dan Allah Umma ki koreta ta koma inda ta fito”
Habiba ta yi dariya.
“Baki da hankali Mama, ai idan na barta haka ban amsa sunan Habiba ba, so nake sai ta tagayyara tukunna, ba na so ta koma wurin dangin uwarta ta ji daɗi, dan kinsan ai ‘yan uwan uwar tata suna da kuɗi, so nake sai ta gama lalacewa, so samu ma ta haɗa da cikin she*e, sannan zan sa Ɗan Lami ya koreta daga gidanan, tunda dama ni ce na saka shi ya kawota!”
Mama ta tintsire da dariya, Fatima na na tayata.
Rabi na fita kai tsaye bakin titi ta nufa, a hanya ta tsaya tana kallon wasu yara dake buga wasan ƙwallo.
Ba yau ta saba ganinsu suna ƙwallon ba, kusan kullum a lokaci irin wannan suna buga ƙwallo, a wasu lokutan ma ba su ne suke yi ba, manya ne ke yi a filin, kasancewar ana azumi shi yasa manyan basa bugawa.
Tsaiwarta ta gyara tana ci gaba da kallonsu, ƙwallo na ɗaya daga cikin burukanta na duniya, ƙwallo mafarkin rayuwarta ce, a da bata da wani fata sai na ta zama shahararriyar ‘yar ƙwallo.
Sanda Ummanta na raye burin nata ya ɗauko hanyar cika, dan akwai wata football academy da Umman nata ta sakata, kuma kullum tana zuwa yin training, sai dai bayan rasuwar Umman tata komai ya sauya.
Komai ya ruguje, ciki kuwa harda burinta na zama ‘yar wasan ball, dan a nan gidan makaranta ma ba’a barta ta je ba, ta ina za’a barta ta wani samu damar tarining.
A gidan kakaninta kuwa cewa suke ai ƙwallo ba wasan mata ba ce, dan haka ita ƙwallo ba ta dace da ita ba, ko a sanda Umman na raye babu yanda ba’a kai ruwa rana ba a kan wannan ball ɗin.
Ganin tsaiwar ba zata kaita ba hasa ta kwashi ƙafafunta ta yi gaba.
*FHA 2 lugbe, abuja*
*11:00am*
Wasu baƙaƙen motoci ne har guda biyu suka yi parking a gaban wani gida cikin layin. Yanayin gudun motocin ne kaɗai zai tabbatar maka da ba lafiya ba.
Ƙofar gaba ta ɗaya daga cikin motocin ta buɗe, wani matashi ya fito a fusace, yanayin yanda yake fitar da iska daga hancinsa ne kaɗai zai tabbatar maka da cewar a fusace yake.
Sauran ƙofofin suka buɗe, sannan ɗaya bayan ɗaya mutanen ciki suka firfito, yanayin shigarsu ne kaɗai zai shaida maka matsayinsu.
Duka sanye suke da baƙaƙen kaya, sannan a jikin kowannensu akwai bullet proof jacket, wadda a jikinta aka rubuta DSS. Na farkon da ya fito ne kaɗai babu bullet proof jacket ɗin a jikinsa.
Kuma shi ne a kan gaba wajen shiga cikin gidan, a harabar gidan suka tsaya. Matashin sai safa a marwa yake, kamar wanda aka ɗorawa maganar duniya. Ɗaya daga cikin ma’aikatan ne ya taho kusa da shi, hannunsa riƙe da bullet proof jacket, a tsorace yace.
“Sir baka saka wannan ba…”
Wani irin kallo da ya masa ne yasa bai ƙarasa faɗin abinda ke bakinsa ba.
Hakan yasa jami’in ja da baya, ya matsa kusa da mace ɗayan dake cikinsu, dan kaf wurin maza ne, ita kaɗai ce mace.
“Ki masa magana”
Kanta ta gyaɗa, sannan ta sofare bingarta ƙirar pistol a aljihun wandonta na baya. Ta sa hannu ta karɓi rigar, ta matsa kusa da shi.
“KULIYA kana buƙatar wannan……”
Sai da ya fitar da wani huci na takaici, sannan ya miƙo hannunsa ya fisgi rigar ba tare da ya kalleta ba, rigar ya saka yana ta hura hanci. Sannan ya yi alama da kawo masa abun magana.
“Ta ko ina gidanan a kewaye yake da jami’an tsaro, zai fi muku da ku miƙa wuyan ku cikin ruwan sanyi, idan kuma ba haka ba!…….”
Ya kai ƙarshen maganar yana haɗe haƙwaran sama da na ƙasa cikin fusata, sai da ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya ci gaba.
“Idan ba ku miƙa kanku ba, sai na binne kowannenku da ransa, idan kuma kun musa, kada wanda ya fito a cikinku!….”
Wani irin shiru ya ratsa wurin tsawon muntuna biyar, cikin gidan babu wani motsi kamar babu kowa, alhalin akwai mutum har biyar a cikin gidan.
“Wallahi wannan mara mutuncin ne!….”
Wani matashi ya faɗi daga cikin gidan, bayan ya sauƙe labulen ɗakin da suke ciki. A tsorace ya yi maganar, kuma daga yanda jikinsa ke rawa zaka fahimci hakan kalar tsoron da yake ji.
Cikin halin ko in kula wani cikin mazan dake ɗakin yace.
“Wai wa kake nufi?”
“KULIYA!”
Kusan a tare gabansu su duka ya buga, ciki kuwa harda wanda ya furta sunan, KULIYA!, wani suna ɗaya da yake firgita duk wani me laifi a garin abuja da kewatenta.
Sunansa kawai kan sa cikin mai laifi ya ɗuri ruwa, KULIYA wani irin bahagwan mutum ne, wanda ba’a gane gabansa bare bayansa, ga saurin fushi da fusata, bashi da imani ko kaɗan.
A razane suka miƙe tsaye gaba ɗaya, kuma ɗaya bayan ɗaya suka shiga leƙa windown dan tabbatar da abinda ɗayan nasu ya faɗa.
“Yanzu miye abun yi ?”
Ɗaya daga ciki ya tambaya, fuskarsa na nuna tsantsar tashin hankali.
“Kawai mu miƙa wuya”
“Kai baka da hankali, mu miƙa wuya fa?”
“To mu ci gaba da zama har ya shigo ya harbe mu”
Daga harabar gidan, Kuliya ya fiddo da bindigarsa wadda ke saƙale a bayansa, sannan ya nufi hanyar shiga cikin gidan gadan-gadan.
“Kuliya!, what are you trying to do ?”
Wannan macen cikin nasu ta faɗi tana bin baya sa.
“Sharon, kar ki takuramin!”
“Ba’a bamu umarni ba, dole sai mun jira umarni…..”
Sharon bata rufe bakinta ba, Kuliya ya raɓata ya wuce cikin gidan. Cike da takaicinsa ta ɗaga kanta sama tana girgiza shi, har abada Aliyu ba zai taɓa sauyawa ba.
Matasan nan na tsaye a cikin ɗakin, suna ta nemawa kansu mafita. Basu ankara ba suka ji an banko ƙofar ɗakin, kuma a cikin ƙasa da sakan sittin.
Ƙarar harbin bindigar Kuliya ya cika gidan. Kafin aka samu wani harbin da ya fito ba daga bindigar tasa ba!.
*Kano….*
*11:30pm*
Motoci biyu ne parker a wani filin Allah, wurin ba gida gaba da baya.
Duka fitilun motocin a kunne suke, kasancewar babu wani haske a wurin bayan na motocin. Motocin na kallon juna ne, yayin da wasu mutane shida ke tsaye a tsakiyarsu.
“Ku bamu saƙon”
Muryar macen cikinsu ta faɗa, wasu gardayen maza ne guda uku a bayanta, alamun dai tare suke. Yayin da take fuskantar wani matashi, wanda shi kuma mutum ɗaya ne tsaye a bayansa.
Matashin ya yi murmushi.
“Ku bamu kuɗi tukunna….”
Ya faɗi cikin rainin wayo. Sai macen ta yi murmushi, tana kawar da kitson kalabar attachment ɗin da ya sauƙo mata kan fuska.
“Ka…bamu saƙon!”
Ta maimaita masa abinda ta faɗi tun farko, sai ya kuma yin murmushi.
“Ku kira ogan naku ya zo ya karɓa muku….”
Daga cikin motar dake bayan su macen, mutum ɗaya ne zaune a gidan gaba, kansa a sama, yayin da bayansa ke jingine da jikin kujera. Waƙar lonely at the top dake tashi a cikin motar yake biyawa, yayin da idanuwansa ke a lumshe.
“Zuwan RAJA nan ba zai mana daɗi ba, dan haka ka bamu saƙon, mu juya….”
A wannan karon fushi ne kwance a fuskar matashin.
“Waye shi ?, kira mana shi ya zo ya ƙwata da ƙarfinsa”
Bisa ga mamakinsa sai ya ga budurwar tana murmushi. Sannan ta juya kanta kaɗan, ba tare da ta kalli bayanta ba, idonta a kan matashin ta kira sunan na cikin motar.
“RAJA!”
A hankali mutumin cikin motar ya buɗe idonsa dake rufe, kafin ya sauƙe kansa, idonsa ya sauƙa a kan mutanen dake gaban motar tasu, ɗan guntun tsaki ya ja. Sannan ya buɗe ƙofar motar ya fito.
Hannunsa kan ƙofar motar ya ci gaba da kallonsu. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya kai hannu ya sodai tattoo ɗin kan zakin dake bayan wuyansa, ya fara takawa zuwa wajen da suke tsaye.A gaban matashin ya ja ya tsaya.
“Ka bamu kayan za mu juya”
Muryarsa me cike da kamala da kuma nutsuwa ta furta, idan ka ji muryarsa ba tare da ka ganshi ba sai ka rantse da Allah ba daga bakinsa ta futo ba, dan sam yanayinsa baya kama da yanayin muryar tasa.
“Sai kun bamu kuɗi tukkuna“
Raja ya kuma yin guntun tsaki, ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Kana ji ko bana san jayyaya, sannan nakan jima banyi fushi ba, ka bamu kawai mu juya”
Wannan karon muryar tasa cikin wani irin taushi ta fito.
“Ni ma ba na san jayyaya…..”
Bai ko gama rufe bakinsa ba, Raja ya ɗauke shi da mari, sannan ya ci kwalarsa da hannunsa na dama, tare da zaro bindigarsa da hannunsa na hagu, ya ɗorata a kan matashin.
Yaron dake tsaye a bayan matashin ya fiddo da tasa bindigar ya nuna Raja da ita, yayin da mutanen Rajan ma suka fiddo da tasu bingidar. Matashin ya shiga ƙoƙarin motsa bakinsa cike da tsoro.
“Shhhhh!”
Rajan ya faɗi yana ɗauke bindigar daga kan matashin, tare da ɗora bindigar a bakinsa, alamun ya masa shiru.
“Ba na san jayyayya!……”
Ya ƙarshe yana maido da bindigar kan matashin, cike da tsoro matashin ya gyaɗa kansa, sannan ya yi wa mutuminsa alama da ya basu kayan.
Da sauri mutumin ya juya cikin motarsu ya buɗeta, sannan ya ɗuko wani brief case, ya danƙa a hannun macan nan, ita kuma macen ta miƙawa ɗaya daga cikun mazan dake tsaye a bayata.
Kuma har zuwa lokacin Raja na riƙe da kwalar matshin nan, sannan bindigar Rajan sete a gosbinsa.
Sai da mutumin su Rajan ya buɗe brief case ɗin, ya tabbatar musu da sahihancin abin da ke cikin brief case ɗin, sannan Raja ya saki matashin.
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, sannan ya maida bindigar bayansa, yana kallon matashin da shanyyayun idanuwansa, hannunsa ya kai yana gyarawa matshin kwalar rigar jikinsa. Da farko saida matshin ya razana, ya ɗauka cewar wuya zai shaƙe masa. Kuma har lokacin cike da tsoro yake kallonsa.
“You are such a good boy, ka kyauta, da ka yi abinda na ce”
Kuma daga haka ya juya. Da hannu ya yi wa yaransa alama da su shiga mota.
Har motar tasu ta bar wurin matashin na tsaye a wurin yana kallonsu, a ransa yake hasaso irin masifar da ogansa zai masa idan har yasan cewa ya basu kayan ba tare da sun bashi kuɗi ba.
*Unguwar Karkasara….*
*12:30am*
“Da kyau Raja!”
Cewar Garuje, wanda yake shugaba a wurin Rajan, yana faɗin hakan tare da bubbuga kafaɗar Rajan. Bayan da ya duba kayan da ya aikasu su karɓo masa.
Raja ya yi murmushi yana ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Ka ga yanzu nan muka gama waya da me gida, yana ta tambayata akan kayan….”
Garujen ya kuma faɗa. Kuma yanzun ma Rajan bai ce masa komai ba, sai juyawa da ya yi ya kalli yaransa huɗu dake tsaye a bayansa,Rhoda, ta hannun damansa kenan, sai Zuzu, Alandi da kuma Jagwado. Sannan ya juyo ya kalli Garuje, a hankali cikin nutsuwarsa wannan kamillaliyar muryar tasa tace.
“Kai ma ka sanni ai”
“Ai dole ne ma na sa me gida ya maka kyauta, sbd wannan ƙwazon da ka nuna”
Lumsassun idanuwansa na ci gaba da kallon Garuje, yayinda ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
*No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja*
KULIYA POV.
Har zuwa yanzu a idonsa yana ganin abinda ya faru a ɗazu, ɗazun da ya buɗe ƙofar kai tsaye wuta ya buɗe musu. Bai ankara ba ashe wani daga cikinsu yana riƙe da bindiga, kuma shi ne ya yi yunƙurin harbinsa. Sai de cikin ikon Allah sai ya bashi damar kaucewa, bullet ɗin ya samu bango.
Kuma bayan ya juya ta kalli bangon da bullet ɗi ya fasa, juyowa ya yi ya kalli yaron da hannunsa ke karkarwa, kuma bai jira komai ba, ya riƙe gaban rigar yaron, ya shiga dukansa da hannunsa, har saida yaransa suka shigo sannan suka raba shi da shi……
“Yau ma halin aka sake?….”
Muryar Wata dattijuwar mata ta dawo da shi zahiri. Hannunsa na dama ya sauƙe daga kan bakinsa, kafin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
Bai cewa matar komai ba, har ta samu wuri ta zauna kusa da shi, matar ta ci gaba da kallonsa tana nazarinsa.
Kamar kullum, kamar yanda ya taso a wurinta, kamar yadda ta rene shi, sanye yake cikin baƙaƙen kaya, wasu jogger set ne sanye a jikin nasa, ya rufe kansa da hular hoodie ɗin rigar.
Idonta ya sauƙa a kan hannunsa na dama, rauni ta gani, kuma da ma ɗazu tun da taga labarai, ta ji an sanar da cewa hukumar DSS sun yi kame a wani gida, har sun kashe mutum ɗaya, ta tabbatar da shi a cikin aikin.
Dan yanda tasan Kuliya, haka ta san yunwar cikinta, bata jin akwai wani da zai faɗa mafa halayensa. Hannun nasa ya farfashe daga kan yatsunsa, alamun dai ya daki wani abun da shi.
Kanta ta girgiza sannan ta miƙe ta bar falon. Jim kaɗan sai gata ta dawo, hannunta riƙe da plate ɗin abinci, sanna firstaid box. A kan coffe table ta aje masa abincin, sannan ta ɗauki firstaid box ɗin ta ɗora akan cinyarta kafin ta buɗe.
Hannun nasa na dama ta kama sannan ta shiga shafa masa maganin zafi a wurin. Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga yana kallonta. A duk sanda Anna zata nuna masa kulawa, idan ya kalleta sai ya ga fuskarta na rikiɗewa tana koma irin tata.
Mahaifiyarsa, mahaifiyarsa da a duk sanda zai tuna da ita sai ya tuna da mahaɗinsa, ɗan uwansa, abokin tagwaitakarsa, Zaid ɗinsa, Zaid ɗin da ya ƙara sunansa a gaban nasa sunan, sai dai kuma idan ya ci gaba da san zurfafa a cikin tunanin LABARINSU na baya zuciyarsa ƙuna take, wani abu ne ke maƙale masa a wuya, shi bai faɗa cikinsa ba shi bai fito daga bakinsa ba.
“Ga abinci ka ci”
Anna ta faɗi a sanda ta gama shafa masa maganin,tana miƙa masa plate ɗin. Yanda yake kaiwa lomar abincin ne kawai ya shaida mata da kalar yunwar da yake ji, bisa ga dukkan alamu ko da aka yi buɗa baki bai ci abinci bw.
Masifar zurfin cikinsa da miskilancinsa da kuma taurin kansa shi ne ke haɗata faɗa da shi, dan da ace bata kawo masa abincin ba, haka zai ƙaraci zamansa a gidan, har ya tashi ya tafi ba tare da ya ce ta bashi abincin ba, alhalin shi ne wanda ya siyo kayan abincin. Kuma bama iyaka kayan abinci ba, komai ma na gidan shi ne ya siya.
“Aliyu!”
Ta kira sunansa a hankali, shi ma kuma sai ya saki spoon ɗin hannunsa ya juyo ya kalleta.
“Dan Allah ka rage yawan fushin nan, ka rage wannan zafin zuciyar taka”
“Anna ba na iya controlling kai na, as far as zan ga ana aikata laifi bana iya hana kaina ɗaukar mataki!……”
A karo na biyu ya yi magana tun bayan zuwasan gidan, tun da ya gaisheta cikin jimla ɗaya bai sake cewa komai ba sai yanzu.
“Haka ne, amma ya kamata a ce kana ragewa, ka riƙa sanyaya zuciyarka, Aliyu babu macen da zata aureka da wannan halin naka”
Ransa ya soma ɓaci, ita Anna ana gabar tana yamma, shi ya faɗa mata cewa zai yi aure ?, shi fa sam babu aure a lissafinsa, bai shirya masa ba, kuma baya jin zai shirya masa ko a nan gaba.
Sai dai ban san abinda Allah ya ƙaddaro ba, bai san ƙaddara da zata kasance ƴan kwanaki ƙalilan ba, ƙaddarar da Allah ya hukunta zata faru a ‘yan kwanaki masu zuwan. Wata iriyar ƙaddara ce da zata tarwatsa komai, sannan ta zama silar shiryiwar wasu lamura.
“Ni na faɗa miki cewar aure nake san yi ?!”
Annan ta yi murmushi, jin muryar tasa na fita a zafafe, ko bai buɗe baki ya faɗa mata ba tasan cewa ransa ne ya ɓaci. Kuma shi da ma haka yake, abu ɗan ƙalilan ne ke ɓata masa rai.
Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama yana ƙoƙarin saita kansa, dan sai bayan muryar tasa ta fito ne ya fuskanci abinda ya yi.
“Sorry Anna, zancen auren ne bana so”
Har a lokacin Anna na iya tsintar sauran fishin da bai gama sauƙe shi ba, kuma da ma shi haka muryar tasa take, kullum cikin darari, ba’a iya maganar arziƙi da shi ta minti goma, kullum idanuwansa a waje kamar me zarewa mutane su.
“Aure shi ne cikar kamala Aliyu, duk wannan muƙamin naka, da dukiyar da ka tara, da wannan shekarun naka, ba zasu baka kimar da aure zai baka ba!….”
Bai ƙara kallonta ba, bare ya amsata, dan ya lura da yau so take suyi faɗa.
TALLAH!