Hausa Novels

Ladidin Kauye Hausa Novel Complete

Ladidin Kauye Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yarinya ce ƴar kimanin shekara goma sha biyu da aihuwa sanye take da rigar atamfa da wandon yadi.

 

Tafiya takeyi tana waƙa da zabgegiyar bulala a hannun ta me rake ta hango da gudu ta ƙarasa gurinshi yana ganin ta ya washe jajayen haƙoransa kana yace “LADIDI daga ina kika fito haka”¿. Ɗaukar rake ƴan hamsin tayi kana ta ce “daga gida mana”.

 

Ganin LADIDI ta kusa shanye rakeb hannunta tana shirin ɗaukar wani ido ya zare mata kana yace “ke baki da hankali ne kin ɗauki raken hamsin banyi miki magana ba yanzu kuma zaki kuma ɗaukar wani”. LADIDI dake ta shan raken ta yawu nazuba a bakinta tace “wlh ko kabani raken in daɗa ko kuwa yanzu kaci najaki”.

mai raken da aƙalla yayi sa,an baban ta dubanta yayi kana yace “yarinya ki wuce kitafi sabgar ki , LADIDI daketa juya bulala tana dariya tana kallonsa.

 

mai rake ne yace “yarinya ni natafi kiyimun addu,a yau inyi ciniki LADIDI ce tadubi mai rake tace “karka damu”.

 

Mai rake ya juya zeja baron rakenshi yaji saukar bulala dur ƙusawa yayi yana ihu yana sosawa juyawa yayi yaga babu LADIDI babu samatan ta .

 

 

Gudu takeyi har ta isa gidansu , gidane ma dai daici kewaye yake da katangar kara.

YADIKKO na surfen dawa ko sallama batayi ba tashige ɗakin data ke kwana tarufe ƙofa YADIKKO tarasa abinda zatace ta girgiza kai ta ɗaga hanu tana rokon Allah yashir yamata LADIDI.

 

Kayan wasanta ta ɗibo kai tsaye gurin bishiyar kukar data mamayi filin tsakar gidan tanufa YADIKKO tana wanke dawar data surfa ta dubi Ladidi kana tace “bana ce ki dena zuwa gurin bishiyar nan ba¿.

LADIDI ce ta turo baki tana ƙananun maganganu YADIKKO ce ta riƙe haɓa kana tace “to kodai kin kwaso aljanu ne tunda kin nace da zuwa gindin kuka ita dai LADIDI bata kula YADIKKON ba taci gaba da wasanta .

 

 

 

 

 

YADIKKO ce take ta ƙwalawa Ladidi kira tasowa tayi tana bubuga kafa nera goma ta miƙawa LADIDI kana tace “ki ɗauki waccan dawar ki kai ingin Shafi,u kice ya miki yanzu .

 

Ɗauko mayafinta tayi ta ɗaure a kwan kwasonta kana ta ɗora markaɗen a kai .

 

 

Tana cikin tafiya taci karo da me awara ajiye nikan tayi kana ta kirashi tunda yaron ya tabbatar LADIDI ce me kiran har ze kwasa da gudu ta riƙoshi kana tace “ina zaka dan uwarka kasanni kuwa¿”.

 

 

 

Dur ƙusawa yaron yayi kana yace “LADIDI kiyi hakuri talle mai ƙeya tayi kana tace “nawa nawa awaran¿

 

“Biyu biyar yaron yace saboda a tsorace yake Ladidi ce ta haɗa guda huɗu a guri ɗaya tacewa yaron naci biyu ƙara ɗibo huɗu takumayi tace naci na kuɗina saura ala koro nan yaron yadu beta yace “wlh LADIDI goggo na ta hanani LADIDI ce ta buge mai baki ta ɗiibi biyu.

 

Seda yaron yayi nisa sanan yace LADIDI bogaza Allah ya isa LADIDI tayi ƙwafa tasan ko ba komai taci awarar goma a talatin.

 

Nikan ta ɗauka tana zuwa dai dai ingin ɗin Shafi,u tace nakawo niƙa Shafi,u daketa nikan shi be kulata ba magana taƙarayi amma yaƙi kulata ramin cinnaka tagani kusada ƙafar shi ɗaya ta ɗauka tasamai a takalmin ƙafarshi takuma ɗaukar ɗaya tasamai a gefen rigarshi ragowar ɗayan tasa mai gurin da taga ya yage a rigar komawa gefe tayi kana tahau waƙe waƙenta .

 

Shafi,u ne yafara jin cizo ta kafa ze sosa yaji cizo ta kanshi yakai hannu ze Sosa kan yakuma ji ta jikinshi a she cinnaka har cikin wandon shi ya shige da gudu ya fice a ɗakin niƙan yana ihu LADIDI babu abin da takeyi in banda dariya shafi,u ne yayi hanyar gidansu yaje tsallaka murhun girkin gidan yataka tsakiyar murhun a she da wuta kwanciya yayi yana birgima an rasa meke damunshi sedai yasosa nan ya Sosa can LADIDI kuwa tunda Shafi,u yafice take gurin ingin niƙan dama ta iya tana gama niƙan ta daura a kanta tana tafiya tana dariya tana faɗin “dama nakashe goman YADIKKO gashi nasami niƙa a sabill.

 

 

Tana tafiya taci karo da wani me rogo dafaffe tsareshi tayi kana tasauke nikan ta dubeshi tace “mai rogo akwai ala koro¿.” mai rogon nne ya galla mata harara yace “dan uwarki wanne kora dazan baki ala koro LADIDI ce tazaro ido kana tace “uwata fa kazaga mai rogo ne yace me kika isa kiyi jibeki kamar buhun alabo .

 

Be Ankara ba LADIDI ta ɓarar da tiran rogon kasa takwashi wanda zata kwasa tazo guduwa mai rogo ya riƙota faɗawa tayi kanshi tahau ruwan cikin shi tadinga kai mai duka baji ba gan.

 

 

Hakuri yashiga bata ɗagashi tayi kana ta ce “baka ganni yar ƙarama ba shine kakeson cin uwata a banza me rogo ne ya miƙowa LADIDI na ashirin ya zura da gudu .

 

 

Cigaba tayi da tafiyar ta har ta isa gida YADIKKO ce tace “LADIDI baky ajin faɗan da nake yi miki ko ¿.

 

sauke nikan tayi kana tace “YADIKKO zansha ruwa.

 

YADIKKO dake ɓarar gyaɗa tace “wlh ke da yar kishi yace kin shiga uku LADIDI ce kamar an tsikareta ta zabura a guje tafice waje.

 

 

Ƙarar mota ,

taji gurin masu motar tanufa ɗaya daga cikin su ne yadubi Ladidi kana yace “baiwar Allah tambaya muke yi” Murguɗa musu baki tayi kana tace “nifa banason kinin bibi zakayi magana kana wani tsari ɗaya daga cikin motar ne yace kiyi hakuri yammata dama muna neman mallam Adamu ne.

 

ta6e baki tayi kana tace “nasan gidan amma saidai inzaku sani acikin wanan akori kurar.

 

Wani daga cikin motar da tunda ɗayan yafara magana shi beyi ba leƙowa yayi ta cikin motar kana ya ce “ubanwa kika gani a akori kura¿.

 

 

Murguɗa mai baki tayi kana tace “karka ƙara zagina na kusa da shine yace Humaid mu lallaɓata ta raka mu .

 

 

Buɗe mata murfin motar Humaid ɗin yayi shigowarta keda wuya sukaji motar ta game da wari kamar anyi tusa Jalal ne yace “Humaid bakaji wani wari ba dede lokacin da warin ya iso hancin Humaid sun rasa meke wari a motar LADIDI ce ta dube su tace sewani toshe toshen hanci kukeyi sekace wasu malaman.

 

Duban tsafta Humaid ne ya ce wlh ga meyin warin nan hatta bakin ta wari yakeyi LADIDI data tabbatar da ita akeyi ciro alurar ɗinkin hannu tayi kana ta waiga taga Humaid ɗin yadena kallonta murmushi tayi kana tayi gefe da hannun ta sokawa Humaid alurar ihu Humaid yakeyi ba k’a kau tawa Jalal ne yafaka motar kana yazo gurin Humaid ɗin dake faman ihu LADIDI ce ta dubeshi kana tace “meyasa meka ne ɗan gayu¿

 

cikin su babu wanda ya kulata bare su waigo ta Humaid ne yace ja motar Jalal muyi sauri mu isa gidan .

 

 

Sun zo dai dai k’ofar gidan LADIDI tace “to munzo seku fito Humaid dake ɗin gisa ƙafarsa yace “to ai seki koma tun da kin rako mu. Zaro ido waje tayi kana a zuciyarta tace lallai wannan besan ko wacece LADIDI ba .

 

 

Duban ƙafar Humaid ɗin LADIDI tayi kana ta fashe da dariya Humaid da babu halin gudu ya dura mata zagi Jalal ne yace “tunda ta nuna mana ƙofar gidan to muje ka kyale yarinyar nan .

 

 

Hango wata zabge giyar sanda tayi ta ɗauka kana ta gyara bakinta seda tabari Humaid yazo dede saitin shiga gidan ta zula mai a kafar da tayimai allura zubewa yayi a ƙasa yana ihu da gudu ta ƙasa…

 

Malam adamu ne yaj ihu kuma na babban mutum da sauri ya ƙaraso Jalal ne yace “barka malam , malam adamu ne yace a,a wana ke gani kamar yan birni¿

 

Jalal ne yace “malam mune wata yarinya ce tara komu gidanka gashi ta bugawa Humaid sanda a ƙafa ta gudu ,malam yajin jina zancen kana yace “nasan ba wata bace illa LADIDI wannan aikin seita .

 

 

Humaid ne yayi ƙarfin halin magana yace “Jalal kaje kane momin yarin yar nan senaga waye ubananta.

Malam adamu ne yace “wlh gara ka hakura saboda wanan yarinyar ana tunanin tana da aljanu

3 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!