Littafan Hausa Novels

Lamarin Gobe Sai Allah Hausa Novel

Lamarin Gobe Sai Allah Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

LAMARIN GOBE....

……sai Allah.

 

_♡ The Love circle._

 

 

Bismillahirrahmanurreem

Dedicated to fatima isah muhammad.

 

FARKO…

G.W.A

 

 

Hadejiya emirates

 

4:pm Thursday evening.

 

 

yelwatattun Bayi da kuyangu ne bila Adadin a kowacce kusurwa ta cikin babbar masarautar, wasu na a tsatsaye suna gadin hanyoyin wucewa nakowace ƙofa ta shige da fice,wasu kuma Da irin kalar hidimar da suka duƙufa sunayi.

 

Dukkaninsu awajen da irin kalar yadin suturar dake jikin sa na danyar Zaren auduga mai duhu da nauyi,mazansu sun saka kalar ja da blue dinkinsu ta sasakken riga da wando mai fadi ta buje.matansu kuma kalar dark blue ne riga da zani Wanda za’a iya kira da shine uniform dinsu duka.

Duhun Zuciya Sarkakiya Hausa Novel Complete

Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana raɓewa gefe tareda sunkuyarda kai ƙasa cikin nuna girmamawa da biyayyarsu gamai kkrin shigowa msmn ma da suka tsinkayo sautin katoton kararrawar bango da ake bugawa domin isarda sakon tahowar mahaifiyar mai martaba sarkin hadejiya wato gimbiya fazilat ma’as sama,tafe take da na hannun damarta wato Babban jakadiyar masarautar mai suna Sayyada Ateeqa wacce kusan kowa ke tsoronta acikin masarautar.

Dan bayan sarki da mahaifyarsa daga gimbiyoyi sai ita awajen zantar da isa da iko acikin wann masarautar.

 

Wanda iya sautin gwalagwalan kafa da na hannu masu balain sheki na danyar zinaren dake hannu da ƙafar uwar gijiyarta Gimbiya fazeelat ma’a sama shi yake sanar da kowa isowarsu tundaga can nesa.

 

Gimbiya fazeelat tsayayyar mace ce wanda tun zamanin mijinta king saiful islam khaleefa ta saba caɓa ado da kwalliya,duk inda take takawa toh sautin sarqar zinari ko gwal,ko wani muhimmin dutsi mai tsada dake sakale a tsintsiyar hannayenta da kafafuwanta shike sanarda isowarta cikin fada har izuwa yanzu da zamanin su ya shude ya zamto zamanin dansu mai martaba Abdlsamad saiful islam khaleefa.

 

Gimbiya fazeelat Ta manyanta sosai Sai dai haryau mulki da kasaita a jininta yake yawo,haka suka wuce ita da jakadiyarta sayyada Ateeqa Cikin bayi da kuyangu ba a samu wanda ya iya kuskuren dagowa kanshi sama ba.

 

Suna ƙarasowa hanyar dazai shigarda ita ɓangaren danta wato mai martaba sarki ABDULSAMAD SAIFUL ISLAM KHALEEFA ta tsaya cak batareda tace uffan ba ta juyo ahankali tadan kalli gefenta na dama inda jakadiyarta take atsaye,saurin matsowa kusa da ita jakadiya tay cikin girmamawa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su hudu, kallo daya sayyada ateeqa tayi musu suka ja nesa can ahankali suka tsatsaya tareda sunkuyarda kansu can kasa.

 

Boyayyar ajiyar zuciya mahaifyar sarki gimbiya fazeelat tasauke tareda shiga kofar da aka jima da wangale matashi jakadiya sayyada ateeka ce kawai tabita abaya snn aka rufe kofar.

 

 

Katafaren Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji Lumtsattsun kujeru na royal chairs golden and red colour. labulaye da chandelliers suma golden colour sai baza qyalli suke snn Duk wani abu daya ƙawata Falon ya zamto shima golden nd red colour dinne da wasu irin royal tabarmai,manya manyan Airmores da incence burners kusan guda shida suna aikin bada Daddan Qamshin turarruka na alfarma da kuma iska mai sanyi wanda already sanyin ma yakama falon takoina sabida wata irin dukiyace ta musamman aka narkashi acikin wnn falon.

 

 

Babu kowa acikin falon tasu ta farko wanda shine zai sadaka da babban falo na biyu wanda ya kasance falon sarauta daganan kuma harzuwa turakar sarki.

 

Ratsa dogon Falon tayi jakadiya sayyada na biye a bayanta ta nufi kofar da zai kaita ainihin falonsa na musamman tana isa dede wajen wanda ke tsaron kofar ya bude matashi,cikin takunta mai sanyi da aji ahankali tashige ciki jakadiya sayyada takoma gefe ta ta tsaya daga nan itama tana jiran fitowar uwar gijiyar tata.

 

Katafaren falone na alfarma an masa kwalliya da royal purple da wani irin cool golden colour,wanda shirun da wajen yay tamkar babu kowa aciki banda qamshi da ƙarar ac dake tashi ahankali.

 

Ajiyar zuciya gimbiya fazeelat ma’as sama ta sauke ayayin data sauƙe ruwan idanuwanta akan ɗan nata.

 

Zaune yake cikin shiga ta alfarma jikinshi killace da golden alkyabba wanda tuni tay bajintar fallasa wata nutsatsiyar siffarsa na kyakkwan namiji mai cikar zati,jarumtacce mai kuma cikar ƙirar halitta da dirarren siffar jiki.

 

Saidai Awajenta haryanzu shi yaro ne dan bazai wuce shekaru 40 a duniya ba saidai sosai Hutu da mulki tareda jinin sarauta ya ratsashi wanda ko kallo daya kay masa bazaka iya kiyasce yawan shekarunsa dede ba.

 

Kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da rikitarwa daya kusan rudata atake tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da ƙarfin hali tanamai sakin masa murmushi mai sanyi.

 

Qarasowa tayi cikin yanayin sanyin jiki da fargaba tanamai lura da yanayin halin tashin hanklin dayake ciki,a hnkli ta rufe idanuwanta dasuka fara canxa kala murya araunane tace

 

Allah yataimakeka ɗana abun alfaharina Darzaza Amalen sarakuna,saƙo daga Asibiti ya iske ni cewa matarka na biyun Ta sauƙa lpya,saidai har yanxu ta farkon bata samu ta sauka ba saima ciwon nakuda dayake tsanantawa.

 

Idanuwansa daya sake watso mata ne yasa taso Daburcewa tayi saurin mikewa tsaye da kyau tareda gyara muryanta cikin nutsuwa ta dauke idanuwanta daga kansa muryanta cike da fargaba.

” tace Doctor suad ne ta bugomin waya tasanar dani cewa matarka na biyu _WATO GIMBIYA SHAKIRA SHEHU (HAJJA SHASHE)_ ta sauka kuma ansamu _ƳA MACE._

 

Tana furta hakan ta Sunkuyar da kanta kasa saboda gudun ganin yanayinsa na ko in kula akan zancen, koda ganin yanda ya dauke wuta tasan babu wani jin dadi ko alamar farin ciki atattare dashi muddin ba labarin uwargidan sa ba ne aka kawo masa ynzu banajin zaiyi wani farinciki.

 

bisa labarin matarsa na biyu wato hajja shashe baice komi ba dan yana hankalce da qudurinsu ita da mahaifyarshi na cutar masa da uwargidansa BAHRIYA AL ABEEDA WANDA AKE KIRA (HAJJA ABEEDA)

 

Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canza kala izuwa kalar tausayin favourite doughter inlawnta hajja shashe wanda take harsashen da wuya yau zataga farincikin mijinta ayau ko ma acikin awannan shekarar sabida Allahne yay ikonsa daya nuna musu iyakarsu tahanyar bata haihuwar ƴa mace ba ɗa namiji ba kamar yadda suka dade sunacin buri akai na cewa itace zata samarwa mijinta da masarautar ɗa namiji magajin sarautan saiful islama.

 

 

Tsawon lokaci kenan tunda ya auri matarsa na farko Bahriyal Abeeda Amma Allah bai taɓa basu haihuwa da ita ba.

 

Gashi suna matsancin son junansu,inda tashine da hakan bazai jawo matsala a rayuwar aurensu ba amma kusan dokace kowani sarki yana buƙatar magajinsa dan haka mahaifiyarsa gimbiya fazeelat wacce ita kadaice ta rage masa a duniya ta dau karan tsana ta jibgashi akan uwargidansa Bahriya al Abeeda sabida bata samu haihuwa ba,hajja Abeeda macece ta kwarai dan sosai tabiyo linzamin mai sunanta wato bahriya Al abeeda the ascertic of basrah,ita mace ce mai tsananin son addini da bautar Allah,takan yawan cewa “duk zuciyar da tay jarumtar yakice mummunan buririka a fadarta to tabbas wann zuciyar zatayi amfani da ilimi wajen bautawa ubangiji..duk tsana da tsangwamar data sha a hannun gimbiya fazeelat dede da rana daya bata taɓa sabawa umarninta ba.

 

Sanadiyar rashin samun haihuwarta akan lokaci yasa aka tursasawa mijinta king abdul samad khaleefa auren yar kawunshi Alhaji shehu fajarudden khaleefa mai suna Shakira shehu fajarruddeni,tun da shakira tazo gidan shikenan duniya tayi ma hajja Abeeda tsauri da zafi sabida makirci da mugunta irinta hajja shashe ya wuce tunanin duk wani mai tunani..

 

Da suka hada kai tare da uwar mijinsu gimbiya fazeelat ma’as sama bakaramin cutar da hajja Abeedan sukayi ba.

 

Duk ƙarfin imaninta da boye rauninta agaban mijinta sai da ta raunana musamman ma da hajja sashe tazo ta samu cikinshi.

 

Tun cikin na wata hudu aka gayayyace Manyan malamai da kwararrun Likitoci suka tabbatar musu da cewa ɗa namiji hajja shashe zata haifa ma sarki.

 

Saidai babu wanda ya tara sani da ikon Allah ashe bahriyal abeeda tana dauke da nata boyayyar cikin wanda itakanta bata san ya shigeta ba sai da cin mutunci da gori yay mata yawa ranar ta yanke jiki ta fadi ta sume aka kaita asibiti nan likitar sarki watoh Doctor maheer sa’eed ya tabbatar musu da cewa hajja abeeda na dauke da juna biyu wanda ratar cikin nata dana hajja shashe baifi wata guda ba.

 

 

Ranar tamkar an wanke zuciyar mai martaba King Abdul samad ne don yay murna irin wanda bai taɓa yi ba..

 

Sanda sakon ya shiga kunnensa atake ya bada umarni ma makama babba aka kira sarkin hatsi ya bude rumbu akayi sadaka da kayan Abinci ma mabukata domin nuna farincikinsa ga ubangijinsa daya cika masa burinsa na bashi haihuwa da macen dayafi kauna a duniya bayan mahaifiyarshi.

 

Farinciki da zumudin daya nuna ya matukar sosa ran hajja shashe wanda ya jawo ita da mahaifyarsa fazeelat suka ci alwashin sai sun ga bayan cikin bahriyal Abeeda.

 

King Abdul samad ya sha mamakin mahaifyarsa sosai dayaga yadda ta nuna bambamci da halin ko inkula da batun samun cikin matarsa na farko wato hajja Abeeda,kuma bawai bata farinciki bane kawai dai a ganinta ai bahriyal Abeeda ba jinin sarauta bace,shakira yar kawunsa ce jinin sarauta,tunda ita jininshi ce dan haka natal haihuwar yafiye mata muhimmaci akan na Abeeda.

 

Haka rayuwarsu ta share watanni acikin rashin samun jituwa da fahimtar juna, tsawon lokutan da hajja Abeeda da kuma hajja Shashe sukeyai rainon cikinsu an fi bayarwa hajja shashe muhimmaci sabida ita jinin sarauta ce kuma an tabbar masu cewa ɗa namiji zata haifa.

 

Babu salo na makirci da mugunta wanda hajja sashe batayishi aboye ba don kawai taga ta kawar da cikin dake jikin hajja Abeeda ba amma Allah bai bata sa’a akan qudirinta ko daya ba.

 

Wani abun mamakin shine mahaifin hajja shashe mutumin kwaraine baima san da cewa yarsa ta shahara wajen bin matsafa ba sabida shi malamin addinine na kwarai da gaske.yaci zamanin sa a lokcin dan uwansa saiful islama khaleefa,shine KAZI na masarautar gaba daya wato chief judge of the kingdom.

 

Haka yarsa shakira zata amshe magani awajen matsafanta ta kawowa uwar mijinsu gimbiya Fazeelat tay mata karyan cewa ruwan rubutu ne da mahaifinta ya aiko akan masu biyu akayi don haka takaiwa hajja Abeeda nata,hakan kuwa gimbiya fazeelat zata amshi ruwan tsafe tsafenta hannu biyu da zumudin cewa shehu fajarudden ne ya bayar ta tursasawa hajja Abeeda ta sha.

 

Burin shakira baifi cikin nan na Abeeda ya ɓare ba amma duk yinta haka Allah ya qaddara zaman cikin har sanda suka kai watannin haihuwarsu.

 

Kafin nan yawan ciwo da zazzabin da Hajja Abeeda takeyi yasaka asirin hajja Shashe ya soma tonuwa Awajen sarki,malaman sa da limaman masarautar sunsha kawo masa bayanin cewa sihiri ake yi akan matarsa daga karshe haryazo shidakansa dan fahimci cewa hajja sashe ce mai aikata wann abun ba wani ba saidai baida cikakken shaidar da zai gaskata harsashen sa akanta.

 

Dama kuma Wata dayane a tsakanin su amma sabida ababen da suke dirka ma Abeeda na sihirce sihirce yasa itama nakudan ya taso mata gadan gadan tun ana saura sati uku ta cika wata tara Naƙuda ya turnukesu lokci guda akayi da su babban asibitin dake hadejiya emirates,ana kaisu ba a wani dade ba hajja sashe ta haifi ƴa mace ,wanda ya jawo saida tay kusan haukacewa data daga ido kalli abun data haifa dayakasnce ya macece ba ɗa namiji ba.

 

Zaucewa da tashin hankli da wani irin bakin duhu shiya rufe hajja shashe da ita da gimbiya fazeelat,tsoro mai yawa ya soma rufeta tafarajin kamar Abeeda ce tayi amfani da tsafi ta maida danta mace don ita ta haifi ɗa namiji, Da kyar aka rarrasheta gimbiya tanamai bata tabbacin babu abunda zai faru har aka samu aka dawo da ita da jaririyarta acikin masarauta.

 

 

Tsawon mintuna ashirin king Abdl samad saiful islam khaleefa yana nan shiru baice ma mahaifyarsa datazo sanar dashi ya samu ƴa mace uffan ba,sanin cewa bazai taba furta komi din ba muddin Abeeda bata samu kanta lpya ba yasata yin niyyar ficewa ta dan barshi.

 

Kanta kasa ahnkli tace

“Nabarka lafiya.

 

Juyawa tayi ta nufi kofar fita tana isa aka bude mata ta fice abunta duk ranta babu dadi

 

Jakadiya tana ganinta ahaka tayi saurin Mara mata baya kanta a sunkuye sbd ganin yanayin uwar gijiyar tata.

 

Suna isa babbar kofa suka fice a sashen sarki kuyanginta su hudu sukai saurin Mara musu baya

Bayi sai zubewa suke a kasa suna sunkuyar dakai yaukan ko kallonsu bata iyayi bare amsa gaisuwarsu dankuwa ranta a matuqar dagule yake da irin shirun da dan nata yayi akan haihuwar hajja shashe.

 

Sashen hajja shashen ta nufa, Tana isa sashen cikin tsananin sauri aka bude mata kofa tashiga ciki kai tsaye hanyar fankacecen bedroom dinta tayi bayan ta wuce babban falonta na musamman inda babu mai shigowa duk fadin masarautar daga ita sai mijinta sai amintacciyar jakadiyarta datake kamar matsayin ƙawa agareta.

 

Duk wani nadaban iyakacinsa falo na farko bedroom dinta kuwa ko jakadiyar bataba shigaba bare wani na daban kuyangarta mai gyara mata kawai ke iya shiga itama ba kasafai ba.

 

Gimbiya fazeelat tana shiga bedroom din taganta a durkushe a jikin lafiyyan gadon dakin tana jera hawaye masu tsananin rauni da zafi

 

Daidaita nutsuwarta da fuskarta tayi tareda sakin gyaran murya batareda takalletaba don sosai tausayinta ya shigeta tun da akace mata ƴa mace ta samu ba da namiji ba

 

Juyowa tayi da sauri tana kallon hajja shashe ayayin tasaki wani irin kuka mai tsumq daya bayyanarda halin bakincikin data tsinci kanta aciki, cikin tsananin taushin murya da tsantsar rarrashi tace,

 

“Ya Allah,shakira Kashe kanki zakiy ne dan baki haifa ɗa namiji ba?

Shin Baki amince da ni uwar da na haifi Abdul samad danace miki ki kwantar da hanklinki ba?

 

Acikin masarautar ne koda akuya kika haifa ba mutym ba toh wallh akuyan nan ne magajin sarki bare ƴa mace mai kwarjinin haske duk duniya.

 

Shakira kikan manta ke wacece,to bari in tunashe ki wallh jini yafi ruwa kauri..ke jinin sarautace ke jininmu ce bazai taba yuwa a dora darajar wata ƴa mace sama dakanki ba.

 

Dan haka yanzu ki kwantar da hanklinki ki share hawayenki ki nitsu kinaji na?

 

Daga mata kai tayi batareda sakin fuskaba kamar yanda suka sababa murya a dashe tace “Allah ya taimake ki uwar gimbiyoyi Abun ne da ciwo..bansan ya zan kare da mijina ba inhar wancan muguwar matarsan ta haifi da namiji ba Already ita kawai yake daukawa mace inta haifa masa ɗa namiji nasan nice zan zamo tamkar wata batacciya acikin rayuwarsa dan ba lallai ya dinga kulawa dani da abunda na haifa ba..

 

Shiyasa dolene hanklina ya tashi,Umma fazila ke kanki kunsan yadda nakeson mai martaba bazan so wani abunda zai rabani dashi ba har abada.

 

Ajiyar zuciya Gimbiya fazilar ta sauke ganin yadda hajja shashe take tambada kuka dagota tay snn ta kalle cikin idanuwanta daya gama canzawa zuwa kalar tausayin kanta.

 

Daidaita nitsuwarta tay snn tace Ki yarda dani shakira..Da na Bazai taba ketare dokoki na ba. Dan haka Nayi miki alkwarin kece mowa agidansa babu wata agabanki saidai bayanki…

 

Yanzu ki tashi ki shirya kanki likitar ki zata zo nan bada jimawa ba domin ta dubaki. Ni zan wuce na barki lpya yata.

 

 

Daga mata kai tay batare da ta dena zubda kwalla ba..

 

Kai tsaye gimbiya fazeelat ta juya tareda ficewa awajen direct ta koma bangarenta tafada private room dinta tana kai kawo cikin zulumin abunda zai biyo baya musmmn in akace Abeeda ta sauka kuma an samu “ƊA NAMIJI”.

08060712446 Inkinason shiga posting grp dinshi den chat up.

LAMARIN GOBE…

…..sai Allah

 

 

_The Love circle._

 

 

02

Har Wajajen ƙarfe shida da rabi na yammacin ranar gimbiya fazeelat bata samu wani wabi cikakkiyar nitsuwa acikin zuciyarta ba.

 

A Cikin sashenta na masarautar daga ita sai amintacciyar kuyangarta datake kamar matsayin yar uwa agareta mai suna wasila wacce akafi sani da umma Ablah sai babban jakadiyarta da kullum ke tare da ita wato sayyada Ateeqa,bayansu yau kowa ma bata amince mai shigowa nan falon ta ba,iyakacinta nan cikin kai kawo da fargaban labarin da zai biyo baya daga can asibiti wajen surukuwanta hajja abeeda da tuntuni take tsammanin jin labarin wani irin jinsin halitta zata haifarwa sarki.

 

Tun ficewarta a sashen hajja shashe hanklinta bai dawo jikintaba,sai dai duk tashin hankli da fargaban datake ji a zcyarta baikai rabin adadin abunda hajja shashen takeji a zuciyarta na bakincikin haifar ma mijinta ƴa mace datayi ba.

Karanta Littafin Jarababben Namiji

Abune wanda haryanxu kwakwalwarta ya kasa dauka zuciyarta kuma ya kasa samun nitsuwa dashi,wani kakkarfan iska mai zafi mai kuma nunnuke da barazanar rasa komi nata take shaƙa a kowani kiftawar lokci na rayuwarta.

 

Tun ficewar gimbiya fazeelat a sashen nata ta saka hannu ta share hawayenta amma bata iya motsawa awajen datake dinba zugum tayi wani irin tsabar bakin cikin dayake mamayarta wanda har ayanxu batajin kafafuwarta ma zasu iya daukarta izuwa sama bisa kan gadonta.

 

Durkushe a tsakiyar lafiyayyen bedroom dinta tay jikinta na wani irin tsuma da hucin takaici, zuciyarta kuwa ta nitse cikin kogon tunani dan tasan kuka ko jimami bazai ficceta ba,kuma shiru bai taba kawo sauki ko magani ba,Kowani giftawar lokaci fargaba ne mai tsanani ke barazanr haukatar da ita,ta riga ta san waye King Abdul samad shidin ƙwankwason jimina ne mai wuyar shafawa,shi namiji ne wanda ba’a iyar mishi cikin dabara,ba a kuma gane gabarsa bare kuma agane bayansa.

tasan ba lallai bane alkwawuran da mahaifiyarsa Gimbiya fazeelaat tay mata ayau yay tasiri akansa musamman ma inhar yau akace uwar gidansa hajja Abeeda ce ta haifar masa magajin masarautarsa.

 

tana da yaqinin in hakan ya faru toh komi ma zai iya faruwa da ita,samun ɗa namiji wajen hajja Abeeda ba zallan bala’i bane daya sauko ma duniyar soyayyarta,

haihuwar tata tamkar babban barazana ce ga rayuwarta mai gaba daya.”toh shin ina mafita?…me zatayi..?

Kuma Ta yaya zata tunkare Abun,lallai bazata sake ta bar rayuwarta ya hallaka a sanadiyar Abeeda ba,bazaitaba yuwa hakan ya faru da ita ba,soyayyar datakyi wa mijinta mai martaba ta mutuwace wanda duk sanda aka raba wnn soyayyr to tabbas tamkar an rabata ne da rayuwarta,batajin zata iya shakar wani kyakwan numfashi awani wajen na daban face a gangan dashi,king abdulsamad shine rayuwarta,yau koda wani zai mutu acikinsu toh saidai ita ko shi amma ba aurensu ba,ba kuma soyayyarta agareshi ba.

 

Ayau tay dana sanin sawa datayi aka raba musu likita mai kula da lafiyarsu duka acikin masauratar,badon hakan ba yau tasan dakomi sai zo mata da sauki wajen kau da abunda Abeeda zata haifa muddin abun ya kasance ɗa namiji ne

 

Tsaki taja tareda kife kai da ƙarfi a kasa sanin ayanzu kam ko Doc maher,wato babban likitar mijinsu king Abdalsamad ya isheta bare ajega Likitar Hajja Abeedar wato doctor surayya mahmud wacce suke takun saƙa da ita.

 

Koda shike taji labarin cewa mijin doc surayyar ya rasu jiya,da wuyane in itace yau akan batun nakudar hajja Abeedar murmushi tay cikin ranta dan hakan awajenta labari mai kyau ne wanda shine zai iya bata isasshiyar dama da kuma lokci akan lamarin Cimma burikanta akan Abeeda cikin sauƙi batare da fargaban komi ba.

 

Dan haka dolene yau din nan ta dauki dukkan wani babban mataki da zai kiyaye faruwar haihuwar Abeeda Domin kuwa tay imani mutuwace kadai yake da ikon da zai rabata da mijinta kuma ya sha abanza amma ba Abeeda ba.Abeeda ko Abunda zata haifa basu isa ba,jikinta da zuciyarta gaba daya bakaramin tsumuwa sukeyi ba,ta dade anan durkushe cikin shirya hanyar da zata amshi saƙon mutuwarta dan tabbas jin labarin samun ɗa namiji wajen hajja Abeeda dede yake da jin sakon malakal maut a cikin kunnuwanta.

 

Wajajen bayan magrib amintacciyar Likitarta wato doc su’ad edress ta shigo cikin masaurautar.

 

Babban filin parking ta ijiye motarta ta fito.

 

sashen hajja shashen ta nufa tana isa sashen aka buɗe mata ƙofa ta shiga ciki kai tsaye kuyangace tay mata nuni da hanyar bedroom dinta wanda a tarihin abotarsu bata taɓa samun iko ko damar shigewa ciki ba

 

Tana shiga bedroom din taganta a tsaye jikin wardrobe din lafiyyan dakin nata ta kammala saka kaya ajikinta kenan ta tsaya daga dan nesa tana jera mata wasu irin rikitattun kallo har ta karaso ciki.

 

Daidaita nutsuwarta tayi tareda yin gyaran murya batareda ta kara kalletaba zuciyarta a dafe tace ”

 

“Doctor Su’ad, ina cikin tsananin halin bakin ciki wanda ke kanki kinsan bazan iya daukarshi a kwakwalta ba.”nayi iya nazari da kuma lissafi kece kawai zaki iya warwaremin wannan lamarin su’ad.

 

Matsowa doc suad tayi cikin sauri tana ganin hajja shashe tasaki wani irin Kimtsatsen saukar numfashi mai zafi da ciwo. Kanta bisa kasa kalar makirci tace.

 

“Allah ya huci zuciyarki gimbiyar sarki uwar masarautar saiful islama,mace daya tamkar dubu,furen kan juji mai taɓaki saiya shirya,gimbiya shakira yar shehu,jinin malamai jinin mahukunta,gaki yar malami,innanki bokanya, kinsha tabara kin sha yaseeen kinkuma sha romon kan shedanu

..kefa majinar bango ce duk wanda ya hauki dolensa ya zame kasa..ke…

 

Hannu kawai ta daga mata alamar dakatar da ita snn ta cigaba da fidda huci,sanda doc suad tay shiru Sann ta dedeta nitsuwarta da zuciyarta snn ta juyo tace

 

“Yaƙi ne mai karfi mai kuma barazanar dauƙe rayuwata yake tunkaroni yau,Ki bani tabbacin cewa zaki iya aikata dukkanin abunda zan umarceki su’ad.

 

Atake ta daga ido sama ta kalleta “Allah ya taimakeki fadi abunda ke cikin ranki nikuna zan cikamiki shi….

 

Lafiyyan murmushin daya bayyanarda da dakewar zuciyata tay cikin tsananin kaushin murya tace “A’a tukuna,

ki tafi kije ki shirya ma wann lokacin kawai,

lokcine mai matukar muhimmaci,..Ina nufin,lokacin da sakon mutuwata zaizo.

Dan banajin akwai bambancin sakon mutuwata da kuma sakon da zan iya riska game da haihuwar Bahriya al Abeeda musamman ma in ta samu Ɗa namiji.

 

Juyowa tay ta zubawa doc suad wasu irin rikitattun idanun da suke rine da wani irin kakkarfan yanayi na rashin imani da tausayi,magana tay kmr ba a cikin hayyacin ta ba tana cewa

 

“Ban damu da duk Abunda zaije ya dawo ba su’ad,ina son Abunda Abeeda zata haifa mace ko namiji ya MUTU yabar duniyar nan yau din nan..bansan taya zaki aikata hakan ba amma koda kowa zai rasa ransa a duniyar nan ne toh ki tabbata Abeeda bata shigo da abunda zata haifa cikin masarautar nan ba…And Whoever fullfilled my wish,awaits him a hefty reward..Nd whoever failed me..

 

Batare data karasa ba

Doc suad ta tsareta cikin sauri tareda tsantsar ladabi tace,”considered ur wishes done ur highness.For it shall be fulfilled no matter what..ur wish is my comand babban gimbiya tozalin sarki..ni zan wuce amma daga gimbiya Abeeda ta haihu zan jira oder daga gareki kfin na aiwatar da yadda kikeso.

 

Daga mata kai tayi batareda sakin fuskaba kamardau yanda suka saba murya a dake tace, “jeki..saina kiraki

 

Kai bisa wuya doc suad ta furta nabarki lpya snn ta bace acikin masaurautar ta nufi hanyar asibitin hadejia emirates.

 

Kasancewarta babban likita mai matsayi kai tsaye ta gudanar da bincikenta ta gano wanda suke akan dakin haihuwar Hajja Abeeda.

 

Doc maheer na offis na lura da duk wani binciken da ungozomomin sukeyi dangane da prolong labour da hajja abeeda take azabtuwa dashi acikin dakin haihuwa.

 

Yanzu hakama doguwar suma tay irinta “temproray shock”din nan,wanda yasaka aka dan bata wasu lokuta na hutawa domin ta farfado dakanta tunda shi shiga shock dib wani abune wanda babu wani masaniya akan faruwar shi a kimiyanci dole sai indakantane zata farfado

 

 

Manyan likitoci mata guda biyu da aka maye gurbin doc surayyar dasu suna can ofiss din Doc maher tare da ungozomin da suke aiki tare dasu Dukannin su a team din karban haihuwar musulmai ne sabida kare martaba da tarihin masarautar.

 

 

Tattaunawa suke a tsakanin su akan lamarin prolong labour da hajja Abeeda keyi dan kuwa wata babban fasihiyar ungozoma mai suna sister susan christiane,

wanda ita bata ma kasance acikin tawagarsu ba amma dai itace akan duty ranar ta basu shawara ,acewarta Daga gimbiya Abeeda ta farfado mafi alheri ayi mata aiki arabata da abunda yake cikinta inba haka ba da yuwar za’a iya rasa daya acikinsu ko ita ko abunda zata haifa.

 

Sun dau lokaci suna tattaunawa akan wnn batun dake ita nurse susan ba musulma bace kuma ma bata cikin authorise officials da suke kan lamarin haihuwar kafin ayi amfani da shawararta dolene sai an tattauna akai ansamu Amincewar Doc maheer tunda shine babban likitar sarki kuma amininshi.

 

Amma mafi yawansu acikin officials din suna ganin kamr shawarar nurse susan zaifiye musu sauki,saidai wasu acikinsu suna tsoron kar abiye na sister susan wani mummunan abu yaje ya faru sarki yay fushi dasu yace bai iyaji ba.

 

 

Tsawon lokcin da suka dauka suna tattaunawar doc suad kuwa harta kammala karade asibitin tayi yan dube dubenta snn ta sanar da mutanen ta datake hulda dasu akan kudirinsu na kashe abunda hajja abeeda zata haifa.

 

Lokacin babu kowa a maternity ward sai dogarai biyu masu tsaron kofar inda hajja abeeda take akwance,sai kuma

Sister susan dake itace akan duty kuma kowa ya shaideta fasihiyar ungoxomace ce.

 

Ita kadai aka barta zaune acikin ward din tana sauraron dawowar tawagar likitoci da ungozomar da suke kula da mai haihuwar.

 

Tsawon awa guda kenan basu leƙo ba tana cikin karanta holy bible dinta taji tsikar jikinta ya wani irin tashi,ahankli ta rufe ta waigo tana juyowa kuwa idonta ya sauka akan windo inda hango inuwar Doc suad edress awaje tareda doctor chukwuemaka okwonko suna famar lekowa ta ciki.

 

Kirjinta taji ya buga ayayin da labbanta ya furta “Blood of jesus” cikin sanyin sauti,a take taji jikinta na labarta mata wani mummunan yanayi atattare dasu.

 

Suna lura da hanklinta a kansu sukayi sauri sukabar wajen daga nan bata karajin motsinsu ba.

Komawa tay ta zauna gamida sauke ajiyar zuciya ta bude bible dinta again tanamai cigaba da abinda takeyi.

 

Lokacin ana neman goma da rabi na dare Doc maheer da sauran tawaga masu kulawa da haihuwar suka yanke hukuncin cewa inhar hajja Abeeda bata farka zuwa nan da awa biyu ba za’a shirya ayi mata aiki domin aceto ransu ita da abunda ke cikinta.

 

Amma kafin nan Doc maher ya shirya tsaf yace xaije yaji ta bakin sarki,dan haka yana tafiya sauran tawagar ma suka dan ja gefe don su huta sabida gajiyar da sukayi tun jiya suna kan abu daya,Still dai nurse susan aka bari a ward din tana xaune tamkar wacce take gadinta ayayin da wayancan tawagar suka kama shirye shiryen abunda zasuyi nan gaba.

 

Bayan ficewarsu baifi da minti goma ba nurse susan ta rufe bible dinta tare da daura dankwalinta akai domin tay adduar bacci dan tasan babu wani aikin da zatay face bayan an kammala da lamarin gimbiya matar sarki.

So take koda na rabn awane ta dan runtsa kafin nan ta bude ido ta cigaba da sauran ayyukan da suke rataye awuyanta

 

Bayan ta killace kanta sosai, Ƙasa ta durkusa gwiwonta zube a kasa idanuwanta a lumshe hannunta bisa sama snn ta fara addua cikin tausashiyar murya

Tace

_”Heavenly father,i come before you today saking for forgiveness of my sins._ _lord,thank you for uve giving me another day to live,my only request this night is to bless my family nd friends,strengthen thy faith oh lord,let them live in contentment nd rejoice in gladness, Baba lord!_

_oh maker, protect them spiritually,mentally,physically nd emotionally.This i pray in then mighy name of jesus. Amen!_

 

Tanakaiwa karshe tay murmushi,Saidai lafiyayyan murmushin da karshen furucin nata ya wanzar a take ya dauke cak ayayin data jiyo kakkarfan karar sautin nishin hajja Abeeda daga kan gadon haihuwarta.

 

Kusan a rikirkice ta miƙe tsaye snn ta karaso da gudu ixuwa gabanta tana mai kallonta kmr zata hadiyeta ganinta kyakkyawar mace na bugawa a jarida

Babu bata lokci tahau dubata ganin haihuwar ne ya taso mata gadan gadan Jiki na ɓari tahau jera mata adduoin tanai mata sannu snn ta juya ta fice cikin mintina kalilan ta aika aka kirawo tawagar dake kulawa da ita,basu wani dauki lokaci akanta ba kuwa tanayin nishi kan yaro ya faɗo,gashi nan zarrrr Ɗa namiji dashi mai masifar kama da siffar ubansa ya fado yanamai callara kuka ayayin da mahaifiyarsa ta rungumeshi tsamm bisa kirjinta tana sauƙe wasu irin kayatattunn murmushi acikin wahalliyar numfashi wanda bayan nan ta koma duniyar sumewar datakeciki.

 

Lkcin Doc maheer na daf da shiga Masauratar saƙon haihuwar ya riskeshi marmaxa ya karaso ciki yaname neman a isar dashi gaban sarki,Anan asibiti kuwa sharp sharp aka kimtsa uwa da yaro snn aka kyaleta domin ta samu karfin farfadowa.

 

 

_Hadejiya emirate 10.50m friday nite_

 

Babban masallaci ne mai ɗauke da ƙayataccun daddumai na sarauta, masallaci ne da dama a ka tanadar na alfarma acikin masauratar wanda mafi akasari sarki da al’umman cikin gidansa sukan sauƙe farillai aciki.

 

Tun ficewar gimbiya fazeelat mai martaba ya fito ya ke zaune shiru anan sallah kaɗai ke iya sawa ya motsa. Shigar sa na dazu ke jikin sa, sai dai ya cire babbar riga da rawani,sumar kan sa kwance lub lub bisa kan sa yana ta Addua ma Al’ummansa,yana kuma rokon Allah ya saukar da matarshi Abeeda lpya.

 

‘Daya daga cikin dogarawa da ke jiran kofa ne ya shigo ya zube daf gaban dogari dake tare dashi kana ya ce

 

‘’ran sarki ya daɗe,

Dakta Maheer ne ya iso yanamai son ganawa dakai cikin gaggawa yace tare dashi da akwai sako mai muhimmacin gameda Gimbiya Bahriya Al Abeeda.

 

Atake ya bada umarni akayima doctor maheer iso izuwa cikin masallacin inda yake zaune bisa red nd golden daddumansu na sarauta.

 

sarki Abdul samad ya tattara nitsuwarsa dan tun daga ƙofa yake kan kallon doc maheer ganin yanayin Jikinshi duk ya kasa samun cikakkiyar nitsuwa sai rawada hannunshi yake fuskarsa kuwa ya kasa boye wanzancer farincikin dake kwaranya akansa.

 

Yana karasowa ciki ya rusuna bisa kasa batare da yaja wata kwakkwarn numfashi ba mai martaba yay saurin datsar kalmomin bakinshi a hankli kuma kasaitance ta hanyar cewa

 

“Fadi labarin Da kazo da shi..

 

Kabbara Doc maheer yay kafin yay masa ikirari masu kaucar da bakinciki da wanxarda nutsuwa.

 

“Ranka shi dade saƙo mai dadi mai kuma daraja ne ya riske ni tun kafin in iso gareka neman wata mafita.

kansa ya dada saddawa ƙasa yana murmushi mai sanyi kafin ya dago kai yace “Allah S.W.A.ya amshi Adduar mu,Allah ya azurta masarautar nan da Magaji, Uwargida gimbiya bahriyal Abeeda ta sauƙa ta samu “ƊA NAMIJI.”..

#Surayyahms 08060712446

#gamji writers asso….

Add Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!