Sirrin Rike Miji

Littafin Hasken Ma’aurata na Auwal Azare

Littafin Hasken Ma’aurata na Auwal Azare

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Hasken Ma’aurata

GABATARWA

da sunan Allah mai rahma mai jinkai tsira da aminci su kara tabbata ga manzon tsira muhammadu rasulullahi (saw) ina farin cikin gabatarda wannan littafin kai tsaye ga yan uwa da abokan arziki musamman wadanda zasu amfana da alherin cikinsa

 

DALILIN WALLAFA

kusan kowanne littafin ma aurata idan ka duba yana bayanine akan wani bangare na matsaloli tareda kawo hanyoyin gyarawa bazaka samu littafinda ya hada duk wata matsala ta jikin mace da namiji tareda hanyoyin gamsarda junansuba ganin haka yasa nayi tunanin duba ingantattun magunguna na mace da namiji na tattarosu waje daya na rubuta shine littafin ya zama sunansa HASKEN MA AURATA

 

TSARE TSARENMU

mun tsara duk Wanda ya mallaki wannan littafin ta hanyar download to zai zama daya daga cikin members dinmu na group saboda haka Ku kasance damu a network domin sanin sirrikan ma aurata

 

ga number mu

08133484236

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

KARIN NI IMA

 

wannan hadin shine ake cewa kankanr jaraba wanda suka iyata ba a kwace musu miji

kema ki koya kiga yanda zaki tara ni ima

 

kawai ki samu kankana (water milon) me kyau saiki fere samanta da wuka ma ana kiyi mata kofa a sama saiki samu kanum fari (Clave) ki dakashi ki zuba acikin kankanar sai kuma ki samu dabino shima ki nikashi ki zuba a cikin

kankanar sai kuma Kwakwa (coconut) kwallo daya ki fasa

ki zuba ruwan a cikin kankanar sannan itama kwakwar ki gurzata ta zama gari ki zuba aciki kankanar shikenan kin hada saiki ajiyeta a waje me tsafta kamar firig bayan sa o i goma sha biyar (15 hours) saiki fara sha harya kare wannan yana aiki sosai….

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

BUSHEWAR GABA KUMA DOMIN MAGANCE MATSALAR.

 

ki kasance me yawan shan kayan karin ruwa (fruit) sannan ki koyi tsumi kala kala don idan wani beyi mikiba wani zaiyi miki

Sannan zaki iya bin hanyoyi biyu

 

1 kisamu madarar shanu ki hadashi da chukui da zuma ki damasu waje daya kinasha cokali3 safe da yamma

 

Yana saka mace ta zama me ni ima da saurin jikewa lokacinda sha awarta ta tashi

 

2 sai kuma na biyu zaki iya fasa kwai guda 1,ki buga ya kadu sosai

sai ki zuba ruwan ugu rabin cup a ciki

kisa zuma cokali3 ki kuma kadawa sosai

ki zuba madarar gari 2 spoon ki kuma kadawa

sai kisa lemon tsami kadan don ki rage karni ki kuma kadashi

sai ki shanye idan kikayi kwana 3 kinayi a jere zakisha kyauta a wajen me gida….

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

(YANDA AKE DAFA KAZAR AMARYA)

 

ki samu ridi danye ki dakashi ya zama gari saiki samu harzar kabewa ki zuba mata ruwan zafi ki barta ta jiku sai ki tace ruwan saiki zuba wannan garin ridin sannan Ki daka minannas ki zuba garinsa aciki to wannan ruwan shine zaki dafa kazar aciki amma kisamu budurwar kaza bayan kin gyarata kin cire kayan hadin saiki zuba idan da hali ki samu farin gadali ki daka ki zuba aciki zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso ki dafata ta dafu sosai sannan ki sauke ki cinyeta gaba daya har miyar wannan itace kazar amare kuma kowacce mace zata iya kuma zatayi idan saura kwana hudu a sadu da ita

 

yana saka mace ta zama me ni ima da dandanon jima i

 

 

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

 

TSUMIN MATA

 

 

 

na farko zaki iya samun dabino bayan kin cire kwallon saiki jikashi ya jiku ki zuba masa kanumfari da minanas ki markadasu sai ki tace ki saka mazarkwaila bayan ta narke aciki shikenan kin gama saiki ajiyeshi kinasha…

 

 

ko kuma zaki iya samun ruwan kwakwa da madara peak da zuma sai garin ridi ki hadasu guri daya ki gaurayashi sosai saiki ajiyeshi kinasha

wannan ga ni ima ga karawa mace yawan sha awar namiji

 

 

 

 

KO KUMA KI JARRABA WANNAN KISHA MAMAKI

 

KIYI TSUMIN ZOGALE

 

ki sami ganyen zogale ki wanke ki tabbatar babu datti saiki cocumber (gurji) ki fereshi ki yanyanka ki hada da ganyen Zogalen ki markade da blander saiki tace ruwan ,sai ki zuba madara da zuma aciki idan kinaso yayi sanyi ki saka a firij

yayi sanyi lokacin shan ruwa kisha…

 

KO KIYI TSUMIN BAURE

 

Ki samu sassaken baure ki zuba masa ruwa ki dora akan wuta idan ya tafasa zakiga ruwan ya canja kala saiki sauke sannan ki tace ruwan dama kin daka kanun fari saiki zuba garin sannan ki zuba zuma kadan saiki saka bazar kwaila sannan ki mayar dashi kan wuta idan ya tafasa zakiji yana kamshi saiki saukeshi sannan ki ajiyeshi kina shansa sau2 a rana…

 

 

KO KUMA KIYI TSUMIN RAKE…

 

ki yanka rake kanana kanana kamar alawar yara sai ki saka a tukunya da ruwa ki jefa kanumfari bada yawa ba fa da yar cittar ki itama ba mai yawa ba sannan ki bare dabinon ki cire kwallon ki jefar kwallon saiki dakashi ya zama gari saiki zuba aciki sai ki dora kan wuta ya dahu sosai sai ki sauke ki matse rake ki cire sannan ki tace ruwan sai kuma ki maida kan wuta ki saka mazalkwaila a ciki sai ta narke sai ki sauke kisa a fridge yayi sanyi kisha

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

SAI KUMA ABINDA YASHAFI FARJIN MACE

 

BUDURCIN

 

Wannan kalmar bata barin yan mata hankalinsu ya kwanta koda kuwa Mace tanada tabbacin bata taba aikata wani abu Wanda zai rabata da budurcintaba

Yan mata an dade ana tsoratasu da wannan kalmar harma wasu suna ganin raina musu hankali akeyi domin kowa da irin bayaninda zaiyi akan yanda budurcin mace yake

 

Shidai budurci ajikin mace masana ilimin jima i sun kasashi gida hudu

 

(1) kashi na farko sunce fatarda take tsakiyar farjin mace wacce ta toshe kofar farjin itace take fashewa kuma tana fashewane ta hanyoyi da yawa musamman kamar saduwa da namiji ko bude kafa ko hawa wani abu ko gudu da dai sauransu amma kuma dolene idan ta fashe aga jini

 

(2) wasu kuma sukace budurcin mace wani ruwane me kamada na ni ima kuma kowacce mace tana dashi yana zuwane alokacinda ta fara saduwa da namiji kuma namiji zaiji wani irin dadi saboda duk jikin mace wannan ruwan yafi komai dadi amma ita kuma zafi takeji lokacinda yake fita kuma ruwan farine amma akwai alamar jini ajikinsa to wannan shine ruwan budurci kuma kowacce mace sau daya yake fita to ta wannan hanyar ake ganewa mace ta taba saduwa da wani

 

(3) wadannan kuma sukace budurcin mace yar wata karamar tsokace a saman farji Wanda kuma don an saka yatsa ko azzakarin namiji baya fashewa saidai idan haifuwa tayi abinda suke nufi anan duk abinda shiga yayi ba fitaba baya fasashi duk dadewar mace tana saduwa da namiji matukar bata haifuba to yana nan amma daga ta haifu zai fashe kofar ta bude dole sai anyi yan dabaru zai koma

 

(4) na hudu kuma cewa sukayi sun yarda budurcin mace yar.fatace a tsakiyar farji amma saduwa da ita baya fasa matashi saboda shi kansa saduwa da mace kala ukune

(1)Akwai Wanda za a sadu da ita tana budurwa ta balaga kuma tanaso to wannan budurcinta baya fashewa saboda sha awarta ta motsa kuma idan mace Sha awarta ta motsa ruwa yana taruwa a farjinta kuma yana budewa sannan fatar budurcin tana dagawa

(2)Akwai kuma Wanda za ayi bataso ma ana da karfi za ayi mata to wannan shi zai iya fasa budurcin saboda Sha awarta bata motsaba

(3) sai kuma Wanda za ayi mace tana karama wannan bata balagaba shima budurcin yana fashewa koda kuwa tanaso akayi ko bataso..

 

YAYA MACE ZATAYI MATSI IDAN TA RASA BUDURCINTA?

 

ga yanda zakiyi Ki daka Garin zogale ki tankadeshi

 

Kisamu man kadanya (ana samu awajen masu islamic medicine)

 

Kisamu man zogale (ana samu awajen masu Islamic cemest)

 

Kisamu Qwaro shine Wanda ake tawada dashin kuma ana wanke hula dashi (ana samunsa awajen masu kayan bakar koli)

 

Kisamu man shanu (ana samunsa awajen masu sayarda nono)

 

Duk ki hadasu waje daya ki kwabasu suyi kamar sa o i5 wato 5hours zakiga sun hade sai kiyi matsi dashi kuma zaki iya rabashi kashi3 wato kiyi matsi dashi sau uku acikin sati biyu

 

To abin tambaya anan tayaya budurwa zata gane ta rasa budurcinta kuma tanada tabbacin bata taba saduwa da namijiba?

 

1 Lokcinda kika tsuguna toilet ko mummunan zama zakiji iska tana shigarki

2 Zaki saka yatsarki daya ko biyu su shige

wadannan sune manyan hanyoyin ganewa akwai kananan hanyoyi masu yawa wanda babu hikimar fadarsu

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

HADIN MANYAN MATA…

 

 

kisamu totuwar rake me tsafta ba bawonsaba Wanda kikasha ki busar da ita saiki hada da miski fari da kanunfari saiki hadasu waje daya ki dakasu ki samu garwashin wuta kina zuba garin kadan aciki kina tsuguno kibar hayakin ya ratsa gabanki sosai kisamu kamar 3minutes

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

MAGUNGUNA

 

 

ZUBAR RUWA A GABAN MACE.

YAYA ZA A MAGANCESHI?

 

Zaki iya samun garin hulba da ganyen magarya ki tafasa ruwan kirinka dunduma wajen wato kina zama aciki

sannan kina shafa man zaitun

Insha allahu za kiga amfanin maganin

 

Kokuma ki samu zuma da garin tafarnuwa da garin zogale da garin habbatussauda ki cakuda ki rinka sha sau3 akowace rana shima wannan yana aiki

 

 

Kuma zaki iya dafa ruwan gishiri kina zama aciki ko kuma kina shan hulba da ruwa duk zasu iya miki amfani

 

 

 

Sannan zaki iya daka tafarnuwa kina zuba garin a abinci kinaci

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

CIWON CIKI DA CIWON MARA LOKACIN AL’ADA

 

budurwa ko matar aure me fama da wannan matsalar

kisamu wadannan magungunan

1 garin hulba

2 garin habbatussauda

3 garin kiswatul Hindi

saiki hadasu waje daya ki zuba ruwa da Zuma aciki sannan ki dafasu idan ya dafu saiki ajiye wannam ruwan da safe ki debi karamin kofi kisha kafin kici komai anaso ki dafa Wanda zai miki sati daya kafin ya kare kin huta da wannan matsalar insha allahu

 

 

WARIN GABA

 

Ga Kadan daga cikin Abubuwan dakesa gaban mace yana wari.

1. Tafiya babu wando.

2. Rashin sanya takalmi, koda kuwa acikin gidane.

3. Dadewa akan masai (toilet).

4. Rashin canza pant da wuri.

5. Yawaita cin danyar albasa.

6. Istimna’i (Masturbation) wato mace ta

biyawa kanta buqata ta hanyar wasa da gabanta.

7. Tsarki da ruwan sanyi.

8. Rashin aske gaba, dadai sauransu.

 

 

TO TAYAYA ZA A MAGANCE MATSALAR?

 

 

1.ki dinga tsarki da ruwan dumi.

2. Kidinga yawan canza wando a kullum kamar sau 2

ko 3.

3. Ki rage cin danyar Albasa.

4. Aduk lokacin da kika kama al ada ki dinga wanke

gabanki da ganyen magarya da farin almiski.

5. Sannan ki daina tsugunawa akan masai (toilet) kina daukar

tsawon lokaci.

6. Ki yawaita aske gabanta duk sati 1 ko 2.

7. Sannan kada ki rinka saka pant da jikar ruwa ajiki bayan kinyi tsarki ki goge kafin ki sashi

8. Kada kirinka barin iska tana shiga farjinki musamman matan Aure wasu suna kwanciya babu wando kuma panka ko easy sunayi ki sani iska ko sanyi da wuri suke jawowa Mace illah a gabanta…

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

BAN GAREN MAZA

 

KANKANCEWAR GABA

 

kankancewar azzakarin namiji ya kasu kashi uku kuma kowanne yanada nasa matsalar saidai wani yafi wani

 

(1) na farko akwai wanda azzakarinsa yake kankancewa ya koma kamar na karamin yaro musamman a lokacin sanyi to amma lokacinda yaji sha awa yana iya mikewa ya girma ta yanda zai iya jima i amma bayan yayi inzali azzakarinsa yana kara kankancewa hakika wannan bashida wata matsala babba saidai idan hakan tana faruwa dakai zan baka shawara ka kasance me tsarki da ruwan dumi amma ba wanda yakeda zafi sosaiba kuma yanada kyau ya zama iyalinka zata iya tayar maka sha awa bayan inzali

 

(2) akwai wanda lokacinda baya sha awa gabansa be kankanceba amma koda yaji sha awa baya kara girma ma ana saidai kawai ya kumbura ya mike babu abinda yake karuwa to wannan shima babu matsala sosai saidai ya kamata ka rage cin zaki da maiko.

 

(3) wani kuma azzakarinsa yana kankancewa lokacinda bayajin sha awa amma kuma koda yaji sha a wa baya karuwa sosa duk irin sha awar dayaji baya wuce tsayin 3-inc ko 8-cm wannan irinsa shine ya dace ya nemi magani domin bincike ya nuna namijinda yake gamsarda mace sosai shine wanda azzakarinsa yakai 5-inc ko kuma 10.3-cm kaurin kuma ya kai 3-cm lokacinda yake cikin sha awa

 

TAMBAYA ME AKAFI BUKATA TSAYI KO KAURI?

 

babu sahihin bayani akan wanda yafi gamsarda mace domin kowacce mace da abinda takeso saidai wanda farjinta yake bude tafi bukatar namiji me kaurin azzakari ita kuma wanda take matse take bukatar me tsayi a takaice kowanne yanada matukar muhimmanci a wajen namiji kuma bazaka gane hakanba saika rasa daya daga ciki

 

TAMBAYA MEYE MAGANINSA?

 

wannan shine karo na 8da nake bayanin kuma insha allahu zanyi bayanin maganin sau 15 yanzu kana iya jarraba samun yayan gabaruwar hausa ka dakasu sannnan ka tankade ka samu garin habbatussauda ka hadasu kana zuba cokali daya acikin shayi marar madara amma kana iya zuba lifton da zuma..

allah ya temakemu……

 

 

akwai mazakutar bujimi (sa) amma wanda ba a dandakeba ana dafa azzakarinsa amma lokacinda za a dafa baza asaka kafi zabo da maggi da gishiriba domin zasu iya hana maganin aiki bayan ya dafu sai aci kuma zaka iya dafawa sau biyu a wata daya…

 

sannan azzakarin ayu shi kuma dama bushashe ake samu a jikashi ya kwana sai namiji yasha ruwan sannan ya wanke gabansa da ruwan shima za ayi sau biyu a wata daya….

 

wadannan bayanan sun inganta idan namiji azzakarinsa bashida tsayi da kauri yanda zai gamsarda mace to zai iya jarraba daya daga ciki

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

MAGANIN BASIR

 

kanemi sassaken dinya da saiwar tsada da saiwar sabara

Amma yakamata sassaken dinyar yafi yawa sosai dukkansu ka dakasu saika gauraya.

Kullum karinka dibar cokali daya ka dafa da ruwa kofi daya sannan ka tache kasha har zuwa mako daya (1week)

idan kuma basir din yana tsirowa to Sassaken dinyar zaka samu ka dafashi tun yana danyensa Sannan ka surka ruwan daidai misalin yadda bazaka chutu dashi ba.

Sannan ka juye acikin bahon

wankanka, saika rinka zama aciki

 

 

 

to a bangaren maganin islamic kuma kasamu Garin Habbatus Sauda kamar cokali 3 saika hada da Garin sassaken Dinyar shi kuma cokali 1 ka saka garin citta cokali.1 saika samu zuma kamar copy karami ka zuba ka gauraya karinka shan cokali2 safe da rana da yamma wato sau uku a rana

idan tsirowa basir din yakeyi zaka iya samun garin Hulba da bagaruwa da kuma garin sassaken dinya ka rinka dafawa kana zama acikin ruwan zafin kuma ba sai namiji kadaiba koda mace idan tana fama da basir zata iyayi…

 

 

wadannan magungunan dukkansu sun inganta maza da mata suna amfanin dasu

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

KARFIN AZZAKARI DA MATSALAR SAURIN KAWOWA MANIYI

 

 

(1) shafa man ayu akan azzakari ko kuma jika gaban ayu a rinka wanke gaba da ruwan yana tsayarda jijiyoyin azzakari saidai bazai hana maniyi saurin zuwaba amma koda maniyi yazo da wuri sha awa bata tafiya zaka cigaba harka gamsarda uwargida

 

(2) ana iya hada furen dabino da hanno da tsintsiyar maza da sauyar hankufa a dakasu arinka shansa da shayi me lefton yana kara karfi da tsayi

 

(3) na uku nayi bayaninsa abaya kuma yafi kowanne aiki wato azzakari yayi karfi lokacin sha awa maniyi baya tahowa da wuri garin sauyar gaude

garin hulba

garin Habba

gadalin ma aurata

garin mai bauna

sassaken dandan

ganyen zurma

duk zaka dakasu waje daya kasha da zuma koda shayi wanda babu madara sai lefton.

 

(4) amfanida sexy copy a ruwan shayi shima yana temakawa namiji wajen jure jima i ba tareda azzakarinsa yayi sanyiba wato zaka zuba garin a ruwan shayi wanda babu madara ka shanye..

allah yasa adace

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

MAGANIN BATURE

 

 

wasu daga cikin magungunan bature da yanda ake sarrafasu

 

1 (man-xl) wani grem ne wanda idan namiji yashafa akan azzakarinsa yana kara tsayi da kauri lokacin sha awa

 

lokacinda kake amfani dashi ka yawaita shan kayan fruit wato kayan yayan itatuwa yana temakawa wajen kara kuzari

 

2 sai kuma (samu oil) mayine wanda ake shafawa akan azzakari kafin afara jima i yana saka namiji ya dade be gajiba domin yana dakatarda fitar maniyi na lokaci me tsawo saidai yanada dan zafi

 

ana bukatar idan ka saka shafa karinka gogewa domin barin wannan mayin ajikin azzari yana saka tsagewar sa

 

 

3 (sex panther) turarene shima da ake fesawa akan azzakari kafin jima i yana saka namiji sha awa kuma yana saka namiji ya dade beyi riless ba

 

shikuma wannan anaso afesa 1hour kafin jima i kuma kadan ake fesawa

 

 

4 sannan akwai (developpe sex) Wanda shima grem ne ana shafawa a kan azzakari domin yana saka azzakari yayi karfi sosai har sai namiji ya gamsarda matarsa

 

saidai yana saka ciwon kunkumi (kugu) sannan idan aka shafa da yawa zaisa gaban namiji ya dade be kwantaba kadan ake shafawa kuma anaso ya zama namiji yana yawan jima i

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

TO GYARAN NONO YAYA SIRIN GYARAN NONO YAKE?

 

 

1na farko AKwai nono mai mango Shape (Shine wanda nipples dinsa yaKe Kallon sama) irin wannan nonon baya zubewa da wuri irn wannan batashan wahalar gyara

 

2- sai kuma Pointed breast (shine zakuga yana kallon gaba wato (straight) gasKiya irin wannan nonon yana saurin faduwa.kuma me wannan tarinka shan kunun alkama kona na albasa musamman idan sun fara kwanciya

3- Akwai nono mai Kallon gefe zakuga aKwai nisa (gap) sosai a tsaKanin nonuwa biyun Kuma nonon har ya Kusa shiga hammata irin Wannan nonon ma yaKan dan Kwana biyu bai zube ba. Mai irin wannan nonon dole ta rinKa amfani da rigarsa (brzya) wanda Keda distance tsakanin biyu curves na (brazy) amma sauran shaps guda biyu na farko zasu iya amfani da rigar nono Wanda kawai zatayi musu (normal straight brezy) amma: Ba’a son mace ta rinKa saka riga Ko rigar nono (brazy) wanda ya matse mata nono saboda zai riKa danne ginshikin nononta kuma daga yayi laushi mako daya (1WeaK) to dolene nononta ya fadi, Ku rinKa sayan (brazy) mai fadin hannu da baya Saboda yafi bada temako (SuPPort) fiyeda mai siraran hannu da bashida fadi

 

Wannan kadan daga cikine domin bayani akan nono yanada yawa sosai

 

Yanzu ga wani hadi wanda tuntuni matan birane dana kauye suke amfani dashi wannan hadin zakiyine idan kinga nononki ya zama kankani kinaso ya ciko kamar balambalam to ki gwada wannan

 

zaki shanya aya ta bushe saiki hadata da garin alkama da farar shinkafa da aya da gyada duk ki jikakasu ki markada saiki tace ruwan sannan ki sake dorawa akan wuta saiki saka sauran kayan hadin wato zuma da madara peak data gari saboda yayi kauri kina juyawa akan wuta daga yayi dan kauri kadan saiki juye kina shansa kullum sau2 a rana budurwa zatayi matar aure wanda bata shayarwa zatayi

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

 

KARA GIRMAN NONO

 

 

garin farar shinkafa da garin alkama da garin habatussauda da garin plantain da aya da gyada mai zabo (mai bargo)ki markadesu sai ki ajiyesu kina damashi kamar kunu ko kuma koko lokacinda kikazo shansa memakon sugar zaki iya zuba zuma idan da hali ki saka garin madara…

wannan hadin budurwa zatayi haka matar aure wacce ta gama shayarwa zatayi

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

GYARAN NONO

 

akwai garin gyara nono wanda ake sayar dashi cikin karamar roba me sanye da tambarin masu hadashi to saidai mata da dama sun kasa fahimtar tayaya suma zasu koyi hadawa da kansu domin idan suka rasa na sayarwa?

 

zaki samu garin hulba sai garin waken suya da garin farar shinkafa wanda akeyin tuwo da ita duk wadannan zaki hadasu waje daya ki ajiyesu kinasha da zuma idan bakyashan zuma saiki kisha da madara peak ko kuma nonon saniya kuma anaso kullum kisha kiyi kamar sati daya

 

wadanda ya kamata suyi amfani dashi sune kamar budurwa wanda nononta kananane sosai ko kuma matar aure wanda ta gama shayarwa nononta ya kankance wannan zaisa nononta ya ciko ya kara girma

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

GYARAN NONO

 

kowanne nonon mace cikinsa akwai ginshiki da yake sakawa yayi tauri wanda daga yayi laushi nonon zai fara kwantawa idan kuma wannan ginshikin ya zama baya girma to zakaga nono ya zama karami kamar babu komai akirjin mace

to irin wannan tarinka dafa furen zogale bayan an tace ruwan sai a zuba zuma a gauraya anasha zaisa nonon yarinka girma kuma kara tashi sannan koda mace me shayarwa zata iya saboda zai kara yawan ruwan nonon

 

shidai wannan ginshikin yanayin laushine sakamakon kwanciya akan nono ko kuma saka matsatsiyar rigar nono to idan kin fahimci hakan da wuri saiki rinka hada garin aya da garin gero da garin alkama kinayin kununsu kinasha yana saka nono ya ciko kuma yayi tauri

 

to saidai idan har shi wannan ginshikin yayi kasa da yawa yayi laushi sosai wannan akwai baban aiki kafin ya dawo domin mata da yawa baya gyaruwa saidai kamar irinsu kunun albasa dana alkama

 

 

 

 

KUNUN ALKAMA

 

yin kunun alkama bashida banbanci da yanda akeyin kowanne irin kunun saidai akwai gagarumin babanci wajen ciko nonon mace domin shi wannan kunun koda mace tana shayarwa zata iya shansa saboda zai temaka mata koda ta gama shayarwa nononta bazasu kankance su zama kananaba amma ba aso mace me cikin tarinka shansa…

 

yanda zakiyi alkamar zaki samu ki hadata da farar shinkafar tuwo da aya danya saiki jikasu zaki iya saka gyada danya saiki kayi markadensu idan an markada saiki tace kiyi kunu dashi kamar dai yanda kika saba dama kunu ko koko zaki iya saka kayan hadi don yayi miki kamshi kuma wadansu suna zuba madara aciki lokacinda za asha adadin yawansa kuma duk yanda kikeso zakiyi…

 

 

 

 

 

 

YANDA AKE KUNUN ALBASA

 

 

ga yanda zakiyi

ki samu albasa ki yankata sannan ki dafata da zallan ruwa

har sai ruwan yayi baki sai ki sauke ki tace albasar ki zubar saiki xuba xuma acikin ruwan sannan ki zuba garin gero ko kamu da garin alkama sannan ki xuba madara paek ko.nono ko kuma ki saka garin madara luna

ki mayarshi kan wuta kina juyawa idan kin tabbatar ya zama.kunu saiki saukar dashi ki rinka sha da duminsa kuma kadan zakiyi yanda zaki iyasha gaba daya idan ya kwana zai iya baci kuma zakiyi bayan kwana daya saiki sake sannan akalla ana bukatar kiyi kamar sau goma

 

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

(RAGE GIRMAN NONO)

 

 

to Abinda zaki fara lura dashi shine ya yanayin jikinki yake? sannan yaya nononki yake?

Idan kinada kiba sannan nononki irin Wanda yakeda tsayine to gaskiya akwai wahala ace maganin rage nono yayi miki aiki

Amma nononda yakeda girma koda bashida tsayi amma be kwantaba shi wannan yana iya raguwa da wuri kuma hakan yana kara masa kyau..

 

Kisamu Ganyen lemun

zaki sai garin Buhuru sudaniya.Ki hada ki dakasu ki dinga shafawa a nonon zai ragu amma ki rage shan madara da kunun aya da yougut Ki dinga soya hanta da kitsen akuya kina ci zasu ragu kuma bazasuyi bacci ba

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

(HANYOYIN GYARAN JIKI)

 

Idan ana Saura wata daya bikinki to ki rage shiga rana idan da halima kidena shiga rana koda yake zaki iya amfanida nikaf domin kiyaye fuskarki idan kuma saura mako biyi (2wek) saiki samu

kurkum,

madara

kwai

dilka

xuma

lemon tsami

da kuma turaren gaf gaff

Ki hada Kurkum da madara da kwai ki shafe duk jikinki dashi ki barshi yayi sa oi hudu (2hours) sai ki samu kyalle me kyau ki samu ruwa ki goge face dinki ahankali saiki shiga wanka da ruwan dumi ba soso ba sabulu, in kin fito saiki hada dilka da lemon tsami da xuma da ruwan zafi ya narke ki shafe duk jikinki da shi sai kiyi turaren gafgaf xuwa mintuna talatin (30minutus) ki shiga wanka da sabulu ba soso, haka xaki dinga yi kullum har sati daya

Wannan shine gyaran jiki na musamman

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

GYARAN JIKI

 

narkanwa ko (stretch marks) kusan kowacce mace data fara haifuwa tasan yanda take bata mata ciki musamman farar mace wata har sauran jikinta yana canjawa musamman mace me kiba

 

zaki iya hada man kadanya

da Man zaitun

saiki matsa lemon tsami aciki kina shafawa

 

ko kuma man hulba da man zaitun ana hadasu waje daya arinka shafawa yana saka wajen yarinka bacewa ahankali.

 

sannan akwai grem na cemest da ake sai dasu kamarsu (mustela) ko (mederma) da kuma (coaca butter) da dai sauransu zaku iya jarrabawa Allah yasa adace

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

KARIN HIPS (DUWAWU)

 

(1) Kisamu dankali na hausa ko na turawa ki dafashi saiki yanyankashi sannan ki dakashi ki zuba acikin nono ko madara peak sannan ki zuba zuma ki gaurayashi sosai kisha zaki iyayinsa sau3 Akowanne sati tabbas wannan hadin har ni ima yana karawa mace

 

(2) ko kuma ki samu kankana ki yanyankata da gwanda itama ki fereta sai kabewa itama ki yankata kokumba (gurji) shima haka da tumatur ki yanyankashi ki wankeshi duk kiyi markadensu waje daya ki tace ruwan kinasha sau2 a rana

Shima wannan yana kara hips sannan yana karawa mace ni ima…

 

 

 

 

KARIN HIPS (DUWAWU)

 

 

budurwa ko matar aure kike zaki iya jarraba wannan hadin wato Abarba da Ayaba, da Gwanda da Kankana ki markadasu ki tace ruwan sannan ki zuba Zuma da Madara peak ki ajiyeshi inda bazai baciba ki wuni kinasha kuma kowane lokaci zaki iyasha babu adadi amma anaso kisha da safe kafin kici komai

 

 

Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe,

ki hada da ganyen Alayahu, ki

zuba Tumatiri da Albasa, ki yi

kwadonsu da kuli ki rika ci shima wanan yana karawa mace hips …

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

GYARAN GASHI

 

abunda ya shafi gyaran gashi kasancewar anasamun mayika masu gyarawa mace gashi shiyasa bamu cika kawowa na Islamic ba amma kasancewar wasu suna bukatar na Islamic insha allahu zamu rinkayi koda atakaicene

 

hulba da man kwakwa babu abinda ya kaisu gyaran gashi kusan duk wani sinadarin gyaran gashi idan kayi bincike zaka samu akwai daya daga ciki idan kika samu garin hulba kika hadashi da man kwakwa zaki iya hadawa da man ridi saiki shafa agashinki bayan kamar sa.a daya (1hour) saiki wankeshi anaso kiyi sau biyu ko uku a sati daya kuma kiyi har zuwa wata daya

wannan zai gyara miki gashi kuma yayi laushi musamman masu fama da karyewar gashi

 

shikuma man zaitun ana dafashi bayan anyi wanka ana shafawa akayi yana saka gashi yayi baki yayi sheki…

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

(RAGE KIBA)

 

dama Kiba ko tumbi awajen mace idan tayi yawa tana hanata wadansu abubuwa da yakamata tayi don burge mijinta

 

dole idan kinason rabuwa da kiba saikin kasance me yawan motsa jikinki

Ki rage yawan hutu da zama a waje daya

Kitafasa gamji da jar kanwa da sabara kitace ruwan kimatse lemon tsami ki zuba zuma kidinga sha da duminsa

In Sha allahu zakiga canji ko kuma kinashan ruwan khal tuffah da lemon tsami wato idan kika hadasu waje daya saikina sha kullum kafi kici abinci

 

 

 

 

SABULUN GABA

 

 

 

ga yanda zakiyi ki shanya ganyen magarya ya bushe sannan ki dakashi ki tankade saiki zuba masa man hulba kadan ta yanda bazai tsinkeba saiki samu sabulun zaitun zakiga sunansa (zaitun zaplan) saiki yankashi acikin wannan garin magaryar amma kamar matar aure zata iya hadawa harda bagaruwa (gabaruwa) saiki samu turmi ki dakasu su hade saiki samu karamar roba ki ajiye duk lokacinda kikayi wanka saiki wanke gabanki dashi …

 

sannan akwai wadanda basu gane yaya ake wanke gaba da sabulu ba domin wasu sabulun kawai suke sawa a farjinsu shine zaisa yake musu kaikayi bayan sun gama wankewa ba aso kumfar sabulu tana wucewa budurcinki (vargina) sama saman kawai zaki wanke da hannunki…

 

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

SAI AMFANIN WASU DAGA CIKIN MAGUNGUNA

 

 

 

SIRRIN KUKA

 

garin kuka da ake miya dashi tuntuni mata suke amfani dashi ajikinsu wajen sauko musu da ruwan ni ima tareda dandanon jima i

 

idan ni ima kikeso kisamu garin kuka ki hada da madarar gari ko peak ko nonon saniya ki gauraya ki zuba zuma kadan kisha da safe sannan kisha da yamma wannan babu tantama akansa ki jarraba kiga ruwan ni ima

 

idan kuma gabanki yana wari ko kuma kinso kiyi dandanon jima i kisamu garin kuka ki hadashi da garin miski kina tsuguno yana matsi kuma yana hana gaban mace yayi wari

 

 

MATSI DA LALLE

 

idan kinsamu lalle kiyi kokarin ajiyeshi domin zaki iya tafasa garinsa ko kuma ganyen da saiwarsa amma zaki saka tafarnuwa sai Ki juye shi a wani mazubi Ki zauna akai tururin yana shigarki ta kasa idan yayi sanyi daidai shiga sai ki tsiyaye ruwan Ki zauna aciki har ya huce insha allahu idan kikayi wannan zaki matse sosai kuma babu ke babu infection

 

sannan zaki iya samun garin lalle me kyau ki hadashi da farar zuma kiyi matsi dashi bayan kamar sa o i uku (3hours) saiki wanke sannan ki shafa man zaitun a wajen shima wannan ya inganta kuma tuntuni mata suke aiki dashi yana saka mace tayi dandano sosai…

 

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

SIRRIN COCUMBER

 

namiji me matsalar saurin kawowa maniyi lokacin jima i zai iya samun gurji ya markadashi ya tace ruwan sannan ya zuba zuma ya gauraya yanasha kullum har kwana biyar anaso daga ranarda ka fara shan wannan maganin ka yawaita jima i sosai insha allahu za aga canji sosai

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

SIRRIN GANYEN GASAYA

 

 

bayan kin wankeshi saiki dakashi sannan ki debo kamar cokali biyu ki hada da zuma me kyau cokali daya

 

 

sannan saiki zuba akan farin kyalle me tsafta ki zuba akayi

 

 

saiki nadeshi kamar yanda ake nade laya

 

to ana bukatar kisamu wando (pant) me tsafta ki saka aciki amma idan kin lura da photon anaso wajenda yake naso ya zama shine a gabanki

 

 

bayan kin saka wandon anaso yakai kamar sa o i goma ko fiyeda haka to saiki cire ki wanke wajen da ruwan dumi shikenan kin gama saiki jira haduwa da oga kiga sumbatu ranar dandanonki daban yake wannan saikin gwada kinji

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

 

MATSI DA GANYEN ALOVERA

 

idan kinaso ki matse gabanki ciki da waje ta yanda mijinki zaijiki kamar budurwa to ki rike wannan ganyen ki sarrafashi kamar haka

 

1 .Ki sami aloevera da karo da kanumfari saiki zuba ruwa ki tafasa bayan kin tace anso ki ajiyeshi har yayi sanyi kina tsarki dashi

 

2 .sannan idan kika samu ganyen aloevera ki matse ruwan saiki dauko man zaitun ki gauraya kiyi matsi dashi bayan kin wanke da ruwan dumi saiki sake sakawa har zuwa dare wannan sirrin duk wanda tayi zatayi mamakinsa shine ake cewa gyaran bazawa

 

kuma wannan sirrin banda budurwa

 

 

 

HASKEN MA AURATA

littafin auwal azare

 

KADAN DAGA CIKIN AMFANIN ALBASA guda6

 

1. Albasa tana tacewa jinin jikin ‘Dan Adam. Duk mutumin da yake fama da matsalar karancin jini, ya yawaita cin

albasa. insha Allahu jininsa zai

yawaita.

 

Wanda yake fama da ciwon SICKLE

(CELL ANEMIA) ya rika yanka albasa tare da Ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu wannan ciwon Sickler din zai

yi sauki.

 

2. MAGANIN TARI sannan Wanda yake fama

da tari ko mura mai tsanani ga ciwon kirji ya nemi Man Albasa kamar cokali 9, zuma

cokali 9.ya gauraya arika shan cokali uku

bayan kowanne cin abinci. Insha

Allahu Ciwon Qirjin zai warke, Kuma

tarin ma za’a dena.

 

3. RASHIN YIN BAWALI : Wanda yake shan wahala wajen yin fitsari ko

bahaya, Ka nemi Man albasa ka

gauraya da zuma da lemon tsami. ka

rika sha safe da yamma. kuma ya rika shafa man albasa ajikin Mararsa shima insha Allahu zaka samu waraka cikin

lokaci kankani.

 

4. CIWON SUGAR : Duk mai fama da yawan fitar fitsari saboda diabetes

(Ciwon Sugar) ya nemi albasa mai kyau ya rika yankawa kullum yana ci.Insha Allah sugansa zai sauka, kuma

zai dena yawan fita fitsarin

 

5. ZUBEWAR GASHI : duk matar da

take fama da zubewar gashi, ko

kwarkwata, ko amosani, ta samu

Ruwan albasa da Man Simsim, da kuma garin Baqadunas. ta rika shafawa a matsirar gashinta kullum kafin ta

kwanta barci. idan ta farka sai ta

wanke da ruwan zafi. ta ci gaba da yin haka har tsawon kwana bakwai.

 

6. BASIRI : ana yanyanka albasa a dafata sannan ayi kwadonta da kuli (karago) arinka ci kullum insha allahu za ayi mamaki

 

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

alhamdu lillahi wannan littafin yazo karshe saiku saurari fitowar cigabansa

 

 

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!