Hausa Novels

Littattafan Hausa Novel Complete Download

Littattafan Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Littattafan hausa novel complete

Domin samun littafan Hausa Novel Complete se ku danna wannan link din domin sauke manhajar Hausa Novel.

Littafin a tsakanin Soyayya

Free page*
_Laguna Beach, California._
Babban Beach ne mai girman gaske dayaci sunan shi, Beach ne daya sami World recognition wanda har duniya tabashi World Best Beach a shekaran 2018, atsanake fishing vassel (boat) ke tafiya akan blue ruwan, wani dogon farin saurayi ne tsaye ata gaban jirgin yanada dan jiki kadan dan cikakke ne yana thick body irin jikin maza masu sunan maza, yana sanye dawani brown shirt da dan gajeren short na maza wanda da kadan ya wuce bombom dinshi,

Littattafan Hausa Novel Complete

kafafun shi sanye dawani white bathroom slippers mai kyan gaske dayadan yima kafarshi tsawo, kanshi sanye da wata jan pcap, kunenshi daya makale da dankunne dake walkiya yana tsaye yana kallan blue ruwan da kifaye ke tsalle suna fitowa suna komawa,

 

yakai kusan minti biyu a tsaye ahaka kafin ya fuzar da iska mai dumi ya mika hannunshi yadau fishing rod dake gefenshi jingine da karfen baki bakin jirgin, dauka yayi ahankali ya rike ya warware igiyan kafin yazura fishing rod din cikin ruwan, dan murmushi yasaki for the first time kana gani kasan he loves wat he’s doing,

 

jawo fishing rod din yayi waje tunawa da yay mantuwa yasake kallon gefenshi wani dan sachet din ledane da akai zanen kifaye ajiki an rubuta fish food ajikin ledan ya dauka, bude ledan yayi yasa white hand dinshi ciki yaciro abincin kifi guda daya dake kama da cheese balls saidai yafi cheese balls tauri yakama hook din fishing rod din ya makala abincin hook din ya bame abincin bam hakan yasa ya maida fishing rod din cikin ruwan yana jujjuyawa sanin yanzun nan he’s about to catch a fish,

 

almost 30sec kafin yay wani irin murmushi cikin wata murya chan kasa mara kara sosai yace “gatchuu” dasauri yay wining spring din igiyan ya shiga dawowa baya, ringing wayarshi dake cikin aljihun short dinshi ya shiga yi dan lumshe ido yayi ya bude daidai lokacin igiyan dake rike da hook din yafito rike da wata katuwar kifi mai rai sai kici kicin kubutar da kanta daga hook din take amma takasa janyo fishing rod din yayi yana murmushi yana kallon kifin ya sauka kasa ya karasa yana tafiya yana kallon fish din yakai gaban wani dan basket mai zurfi all this while wayarshi na ringing amma bai damuba ya jefa fish din cikin basket din sanan ya ijiye fishing rod din akasa yasa hannu ahankali yaciro hadadden wayarshi daga aljihu ya kalli screen din dan yatsine fuska yayi kaman wanda bayason daukan wayar ya danna yakai wayar kunenshi ashgwabe yace “Dadddddd” yawani ja sunan kaman mai shirin kuka,

 

daga tachan bangaren wani muryan wanda yadan manyantane yace “don’t Dad me anan, kasan abinda kayi, you know Aliyu, ina bodyguards dinka?” mutumin yafada cike da masifa, yamutse fuska yayi cikin murya chan kasa kaman wanda baison yay magana yace “nasan u already know, why are you asking again?” “kaci gidanku Aliyu, kaniyarka nace, nikake ma magana haka? Ai dama nasan inda suke dasu nafara communicating inji lafiyan d’ana kafin nakiraka, and maza maza ka juya jirgin nan ka koma chan bakin Beach inda ka barsu,

idan kanason kai fishing carry them along with you kaje kai fishing dinka since is your hubby, while you are fishing su suna gadin ka, I hired them just to protect you for me, kasan how much nake spending for your security iyye?” sosai shima cikin fushi kaman zai hadiye zuciya yace “ai bance ma inaso ba,

 

Littattafan Hausa Novel Complete

Powered by: www.mynovels.com.ng

I don’t need them am old enough to protect my self Dad, and besides Allah is the protector of all mankind, kuma ni stop treating me like a toddler am not that baby you use to feed Cerelac and gaber rice, am 29years 7months am an Adult and ni bansan security ko bodyguards ne whatever their name is, free me Dad please” daga tachan bangaren mutumin yace “sannu Mr Aliyu Adult, yaushe ka girman dududu? Katashi kataho fishing bakasaka sweater ba am sure anjiman nan, anjima kadan zaka fara sneezing up and down, ka juya jirgin nan kawuce katafi wlh kona sassaba maka, zan sassaba maka Gadanga kanajina ko, kawuce katafi kuma next week zaka dawo Nigeria you will be under my watch ko hankalina ya kwanta nima nagaji da kiran security ka every single minute ina tambayan su kai, gwara kadawo gabana ina ganinka kullum hankalina akwance, ka juya jirgin nan katafi and find something to cover yourself am I clear?” shiru yayi yaki magana ya daure fuska sosai batare daya zare wayan daga kunenshi ba cikeda masifa mutumin yace “am I clear Aliyu?” murya chan chan kasa yana turo baki yace “eh” ya katse wayan duk ranshi a dagule ya maida wayar aljihun wandonshi ya kalli fish din daya kamon dahar yamutu yatashi ahankali yay wajen injin din jirgin ya kunna yazo ya tuka jirgin yafara gudu ya juya, yayi gudu na almost 12min sanan yakai bakin beach din idanunshi akan bodyguards dinshi guda biyu dake nan bakin beach din a tsaye inda ya barsu suna sanye da bakaken suit daya yarike babban bargo dayan kuma bai rike komiba, karasawa sukayi bakin ruwan tun kafin yay parking, parking yayi yafito batare daya kallesu ba yafara tafiya, wanda ke rike da bargon ne ya mikamai. “Sir ur Dad asked us to give you blanket to cover yourbody” cikin fushi batare daya kalli bargon ba yace “I don’t want it” yay gaba abinshi suka juya da sauri suna binshi agaban wani babban jeep yabude ya shiga baya ya zauna atishawa yayi da sauri guard din daya iso wajen ya mikamai yace “Sir please take it u are catching cold already” wani mugun kallo ya watsamai yace “get in the car and drive me home or I leave the car for you Mr” da sauri duk suka shiga, tada motar yayi sukaja suka fita daga wurin lumshe ido yayi, sosai yaji yanajin sanyi kuma baiso yace sukashe AC motan kaman Dad yay winning kenan ai dayace sanyi zai shigeshi he was so happy earlier but Dad ruin everything ga wanan mayun security dake tare dashi, wani dan wahalallen tsaki yaja ya gyara zama ya rungume hannayenshi, wajen 20min drive sukayi sukai parking agaban wani hadadden gida, da sauri suka fita kafin ma subude mai kofa ya bude da kanshi ya watsa musu harara ya wuce yay cikin gida yabude door yashiga Littattafan Hausa Novel Complete.

Babu kowa a hadadden palor stairs yahau da sauri yana atishawa ya bude wani hadadden daki da komi na ciki yakenan sky blue color, zama yayi kan Royal bed yanajin sanyi har cikin kashin shi hannu shi ya mika zaidau remote din AC dake kan pillow dake kan gadon wayarshi ya shiga ringing daukan remote din yayi ya kashe AC kafin yaciro wayan daga aljihu daure fuska yayi ganin sunan Dad, kaman wanda akace dole yay picking call din ganin wayar na neman katsewa ya kai kunnen shi yay shiru batare dayace komiba cikin kwantar da murya mutumin yace “yanzu fushi kake da Dadyn ka ko Gadanga na?” shiru yayi baice komi ba ahankali mutumin yace “haba Ali Gadanka gusar yaki,

yaron baban shi tashi kadau rigan sanyi kasaka kaji Mr Aliyu Adult” dan murmushi yayi dan yasan cikeda tsokana Abban shi yafadi haka. “yauwa tashi to kasaka kaji” “uhm” yafadi yana sauka daga kan gadon yakarasa gaban wani mirror wardrobe dake bangon dakin yana kallon kanshi har hancinshi yay jajir sabida sanyi wani boturi ya danna kofar wardrobe din yabude ya ijiye wayan kan stool din wajen yaciro wata dark sweater mai kyau yasaka tamai mugun kyau yakara fito da hasken fatarshi,

 

daukan wayar yayi yamaida kunenshi Daddy yace “kasaka sweater?” gyadamai kai yayi yace “eh” “yauwa ko kaifa kaga yanzu sanyin zai ragu, stop acting stubborn kaji Aliyu na, I know you sama d kowa, I know how fragile you are bakason iska dayawa, abu kadan mura mura, you need to take care of yourself okay saisa ma nace zakadawo Nigeria kawai ko hankalina ya kwanta” kaman zaiyi kuka yace “Dadddd” “common don’t Daddy me my friend” cikin muryanshi mai bala’in dadi da taushi yace “Nigeria weather is super harsh Dad,

I don’t wanna come back please nika kyaleni” cikin Dan kakkausar murya Dady yace “nakiya, anki a kyaleka din” saikuma yay shiru kafin yadan sassautar da murya yace “haba Gadanga na, eh babana, mai sunan Abba, kafa gama project dinka kagama komi, I’ve missed you badly, kadawo gida lemme arrange everything idan akwai any available flight gobe kabiyo kadawo gida inda cibiyarka take, kana dawowa kaga saimu nema maka mata kai aure abinka ka ijiye iyali ko Son?” kwanciya yayi akan gadon yaja bargo ya lulluba tareda lumshe ido ya gyara wayan akan kunenshi yace “nikadena min maganan aure Littattafan Hausa Novel Complete.

idan shizakamin bazan ma dawoba, women are so lousy I don’t think I can ever live with one” da sauri Dad yace “no, no bashi zanma ba, muma bar maganan, please kadawo kaji” ahankali yace “alright but not tomorrow akwai abunda zanyi saidai next tomorrow or rather on Friday kawai” “har Friday, yaufa Tuesday Aliyu, kana nufin nan da kwana uku, please on Thursday kadawo kaji Gadanga na” shiru yadanyi saikuma ya nisa yace “ok Dad” murmushi sosai baban nashi yayi har hakan yasa shima ya murmusa jin mahaifinshi na murna sabida ya yarda zai dawo. “kaci pancake yau kuwa?” yatsine fuska yayi yace “naay” “why? Maiya hanaka cin fav dinka?” kaman zaiyi kuka yace “bakai kabatamin raiba you ruin my day Dad” cikin dan tashin hankali yace “nizaka ma shairi Gadanga?” dan murmushi yayi batare dayace komiba. “karka damu idan kadawo akwai wani pastry shop dat makes d best pancakes,

 

I can testify to that dan ranan danaci pancakes dinsu
saida tastbud din yay rawa zan aika a sayoma harda Valvet cake ma zakaci kaci har sai kaci kature yafi na California ku dadi I promise Nigeria yanzu mun cigaba muma” dan murmushi yayi yana lumshe ido, murya chan kasa agajiye yace “okay Dady” “you are sleepy ko wanan danaji muryanka chan kasa” gyadamai kai yayi yace “yeah” “alright Son, sleep kaji please allow your bodyguards to do their job kaji Son, am paying them just to take care of you, you are too fragile so kadena hanasu kula dakai, now sleep nima am about to enter Chamber, I love you” murya chan ciki yana kara nitsewa cikin gado cikeda gajiya kaman wanda yay dako yace “love you too Dad” katse wayar baban nashi yayi tsabagen gajiyan dayayi yakasa janye wayar daga kunenshi ya juya ya kara narkewa cikin bargo bacci mai shegen dadi yay awon gaba dashi.

 

 

 

 

_Suleja, Nigeria._

Dan babban falone dake shimfide da ledan daki brown mai gida gida, ga saitin kujeru na daidai rufin asiri masha Allah dakin sai kamshin turaren wuta yake ko ina tsaf tsaf babu ko digon datti, wata matace a tsakar dakin dake kan dadduma tana salla, kana ganinta kasan tadan kwan biyu a duniya tanada jiki sosai, sallame sallan tayi cikeda natsuwa sanan ta daga kai ta kalli agogon bangon dakin tana istigifari, karfe 9:08AM, karfe tara harda minti takwas na safe, tashi tayi daga kan dadduman tadau charbinta tarike tafara tafiya ta doshi kofan fita daga dakin, yaye labule tayi ta leko tsakar gidan da maganganu kasa kasa ketashi wata matace zaune kan tabarma a tsakar gidan babu hijabi a jikinta, kafafun ta da aka zana mata bakin lalle irin na amare dayay mugun kyau ta daura kafafun kan wata yar pillow datai bakin kirin wacce kana ganinta kasan na lalle ne, ta mikar da kafafun anja skirt dinta sama har zuwa wajen gwuiwanta sabida lallen, sai kuma hannu ta na haggu da shima ta mikar dan yasha iska shima ba’a gama da zana mata shiba dan baima soma shirin bushewaba, sai kuma dayan hanunta da ke hannun mai zanen lallen tana zana mata. “Aneesah” da sauri yarinya data dukufa tana zanama matan lalle ta dago kanta da sauri ta waigo, bakar yarinya ce full definition of melanin skin, wani irin glowing dark skin take dashi dake shining bana wasaba, giranta a cike da gashin gira har giran na neman hadewa dan in between space din two giran ma gashine sai dan tawadiyan Allah a tsakiyansu dayay ma fuskarta kyau bana wasaba, tanada dogon hanci sosai kaman karas, kwayan idanunta farare fat kaman madara sabida hasken su, gashin idanunta bakake dogaye wara wara dasu, sai dan lips dinta dakenan pink sosai dayakara haska fuskarta, gefen fuskarta dogayen sajene lub lub a kwance, kanta sanye da bakin hula, kunenta babu dan kunne sai gashin keyanta dakenan a kwance lub lub wasu sunyi coils, kana ganin yarinyar kasan she’s so hairy, tana sanye da wata bakar rigan atampa. “Aneesah” Mahaifiyar tata takara kiranta akaro na biyu tana fitowa daga dakin gabaki daya rike da charbin hanunta ta tsaya agaban dakin, da sauri ta ware manyan fararen idanunta ta kalli Maman nata tace “na’am Ammi” “bakigama lallen ba kinsan karfe nawa kuwa tara harda yan kai” zaro ido tayi dan batasan lokaci yaja hakaba adan rude tace “innalillahi Ammi nayi latti, Madam yau zatamin fada, yanzun nan zan gama mata” tai maganan tana gyara xaman lallen a hanunta tacigaba da zanama matar lalle agurguje, ganin yanda take sauri yasa Ammi tace “ki kwantar da hankalinki kimata atsanake kar ayi shirme” gyadama mahaifiyar nata kai tayi tacigaba dayi anatse, komawa daki Ammi tayi dan xigaba da zikirinta.
Ko 5min bata karaba tagama yimata lallen tai murmushi tana kallon hannun tace “ki zauna anan yanzun nan zai bushe, zan jamiki ruwan dazaki wanke dashi inya bushe, ni yanzu wanka zanyi natafi wurin aiki” murmushi matar tayi tana kara kallon lallen nata dayay mata kyau bana wasaba mussamman ma tasan idan Baban Aisha yadawo daga lagos yau saiya yaba lallen shima dan yanason lalle shi arayuwanshi, tashi tayi a gurguje tai wajen rijiya ta kwalama Mamanta kira Littattafan Hausa Novel Complete.

 

“Ammi nagama zanja ruwa nai wanke wanken sainai wanka natafi” Ammi dake kan dadduma tana jan charbi tace “kibar wanke wanken zanyi, ja ruwa kawai kitafi wajen aikin ki kinyi latti dayawa” guga tadauka tazura a rijiyan tace “tom Ammi” a gurguje taja ruwan tacika botikin takai gefe ta ijiye ta kalli matar datama lallen tace “ga ruwan ki nan” ruwan data ijiye mata agefe matar ta kalla tai murmushi tace “nagode Aneesa” murmushi tayi daya kara mata kyau tadau ruwan wankanta data jawo takai gaban kitchen dinsu ta ijiye kitchen dinsu ta shiga tadau tsumman cire abu awuta tadauko tukunyar dake kan rushi tafito ta juye ruwan zafin a cikin botikin ta ijiye tukunyar tadau ruwan tai bayi. Bata wani jimaba tafito da sauri tana sharce ruwan fuskarta fatarta sai shining take sabida wankan datayi, dakinsu ta shiga har lokacin Ammi nakan dadduma hakan yasa ta wuce ta shiga wani daki wanda yakenan dan karamin gado ne adakin sai wani tsohon sip, sip din ta bude ta ciro doguwan rigan atampa da wani farin gogaggen hijabi, shiryawa tayi tsaf tasaka kayan bayan ta shafa mai, wani irin cool kyau kayan sukamata doguwan rigan saiya kara fito da tsayinta sosai dan dagowa ce, hijabin ta warware ta saka batare data tsaya su shafe shafeba dantai latti, hijabin yay ma fusjarta kyau, hulan ya zauna akanta sosai tadau yar karaman crossing bag dinta ta rataya tafito ta kalli Ammi tace “Ammi natafi” “adawo lafiya, ki kula dakanki kinji” murmushi tayi tana daukan kofin kokon dake saman TV stand ta kurba ta ijiye hakan yasa Ammi dake binta da kallo tunda tafito tace “ki zauna kisha mana, kin tsaya kina kurban koko a tsaye” girgiza mata kai tayi tace “Ammi nai latti madam zatamin fada wlh, banama jin yunwan sosai, natafi Ammi kimana girki me dadi kinji” tai maganan tana fita daga dakin tana leken fuskan Ammin dantaji mezatace, binta Ammi tai da kallo batare datace komiba, tsakar gida tafita matar datama lallen tace “harkin fito, ga kudin lallen” ta mika mata yan dubu daidai guda biyu karasawa wajen tai akunyace ta mika hannu ta karba ganin dubu biyu ne yasa ta zari daya ta mika mata dayan tace “dubu dayane kudinki” kin karba matan tayi tace “wanan hadadden lallen kona amarya albarka shine zakice dubu daya, a’a nidai kirike to nabaki” murmushi tayi akunyace tace “nagode” “yauwa Aneesa mai lalle nima nagode adawo lpy” juyawa tayi takoma daki tai sallama ta shiga kudin tamikama Ammi tace “Ammi ga kudin lallen, natafi” ta juya harda dan gudunta harda dan gudunta tafita ta kalli matar tace “sai anjima” “adawo lpy Aneesa” fita tayi daga gidan, da sauri sauri take tafiya harta fita anguwan su ta tare keke napep abakin titi ta shiga d sauri tace ” _Modest bakery & dessert home_ zaka kaini malam” tada keken yayi yace “naira dari zaki bada Hajiya” “muje” tacemai tana duba jakan ta dari taciro kudin tarike tana kalle kallen hanya, kusan tafiyan minti ashirin yakaisu wajen, Babban bakery ne sosai dakenan abakin express road, sauka tayi daga kan keken tamikamai kudin tajuya da sauri tai cikin wajen security bakin kofan ne yabude mata kofa yana kallon fuskarta kaman zai hadiyeta shidai arayuwan shi yana mugun son Aneesa yarinyar na burgeshi over amma haryau yakasa gaya mata, tun ranan da tafara zuwa wajen nan baya manta ranan itada mamanta sukazo tana sanye da wani pink hijabi har kasa tanata kalle kallen wurin, tun ranan yaji yarinyar ta shiga ranshi. Kawar da tunanin yayi daga ranshi yasakin mata murmushi mai kyau yace “ya akayi kikai latti haka Aneesa? Kije Madam na office dinta tace dazaran kinzo nace kisameta asama nasan fada zatamiki ki lauyance mata kice bakida lafiyane saisa kikai latti na tsani naga tanamiki fada” yay maganan yana kallon fuskarta cikeda damuwa, gyadamai kai tayi asanyaye tama kasa magana tsabagen yanda gaban ta ke faduwa, shiga ciki tayi tana kallon koina, few people ne zaune akan chairs da table dake zagaye a wurin some nacin cakes da drinks wasu kuma ice cream, karasawa gaban kanta tayi tabude ta shiga daidai lokacin wata ma’aikaciyar wajen mai suna Fatima tadauko two cup of ice creams data tsiyayo daga machine ganin Aneesa tsaye yasa tace “yauma kinyi latti ko, tun safe sai sintirin zuwa neman pancake dasu cakes ake barinma valvet amma bakizo da wuri kinyi ba, anyway kije Madam na kiranki yau ta sakko kasa tana duba kokinzo yafi sau hamsin” tai maganan tana daura ice cream cups din akan tray ta dauki tray din tafito dantaje takaima wayanda saukai order ice cream abinsu, sosai gabanta kefaduwa amma ta daure ta doshi stairs harta kai gaban office din madam din da aka rubuta CEO’s Office hanunta har rawa yake taciro daga hijabi ta kwankwasa kofan kaman wacce ke shirin guduwa, daga tacikin office din akace “yes, who is there?” bakinta har rawa rawa yake tace “i….is me, A.. Aneesa Ma” shiru akayi kafin chan ace “come inside” ahabkali ta murda handle din kofan ta shiga hadadden office ne da akai fentinshi fari sai uban haddadun office furnitures, wata matace da akalla zatai 45 zaune akan kujeran mai office, taci suit baki kanta dauke da attachment alamun ba musulma bace, sai wata mata da alamun bakuwarta ce zaune akan kujera duk suka zuba mata idanu kaman zasu hadiyeta da duka, kasa jure kallon dasuke mata tayi ta saukar da kanta tasa hannu ta goge zufan daya feso mata a goshi tace “good morning Ma” tadanyi shiru tana sauke ajiyan zuciya kafin ahankali cikin irin muryan mara gaskiyan nan tace “am sorry Ma, bazan kara zuwa latti ba daga yau, am sorry please” tai maganan ahankali kaman zatai kuka, biro Madam din tadauka ta shiga rubuce rubuce abinta ita bata bata izinin fita ba kuma batace mata kalaba, saida tai kusan minti biyar sanan ta dago ta kalleta tana tauna kan bironta saikuma ta janye byron daga bakinta tace “Aneesh” haka take kiran sunanta dan bata iyaba, adan tsorace tadago kanta ta kalleta tace “na’am” cikin fushi Madam tace “bazan jure wanan lazyness dinan nakiba do you know what it means a business customer yayta zuwa neman abu zai saya ana cemai babu?” tadanyi shiru tana kallon Aneesa data sunnar da kanta kasa tace “8 ne time dinki na zuwa aiki, come and make cake, meat pie, chicken pie, valvet and pancakes wanan shine aikin ki kawai a wurin nan amma baxaki zo da wuriba when you know most people have pancakes as breakfast, wat sort of unprofessional act is this? Coming late to work am not gonna take it, kunyan maman ki nakeji da tuni nakoreki, ga professional pastry chiefs nan all over Nigeria but because I want to help you, inajin tausayin mamanki I stick to you you this quack chief, and daga yanzu duk idan kika kara latti am going to deduct money from your salary stupid girl, get out my office kiwuce bakery and do your work, fita!” ta daka mata tsawa kaman tana koran kare, da sauri Aneesa ta juya tafita fararen idanunta har sunyi ja.

 

 

Tsaki Madam taja cikeda bacin rai ta buga table dan sabida haushin asaran datasaka tayi this morning hakan yasa kawar tata dake zaune tace “why are you getting angry over this? Ki koreta mana since she’s not serious” tsaki Madam din takaraja tace “I wish is as easy as u say, I just wish” takarajan tsaki sanan tace “kinga yarinyar nan haka she’s the reason behind all this huge customers din dakikaga ina dashi, many people rather come here susai cakes than suje other bakeries damukedashi, wasu ma all the way from cikin Abuja suke zuwa nan susai all this dessert, Friend this girl Aneesh hands are blessed, don’t worry this is ur first time in my store all this while dana bude kina Lagos bari tagama baking zansa akawo miki wlh u will ask for more, Allah yabata ne kawai, I try so many times manya manyan bakers na dauko just to try them out suyi min bakin but nasu baya taba matching nata, hers is just perfect, ta iya fluffy cakes in fact the fluffiest cake dabaki tabacin irinshi ba.

DOWNLOAD COMPLETE A TSAKANIN SOYAYYA

Mun gode da ziyarar shafin mu na My Novels

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!