Lubnah Yar Aiki Hausa Novel Complete
Tag: Lubnah Yar Aiki LUBNARH ‘YAR A’IKI
Part one 1
MALLAKIN NUSAIBA USAMA WATO NUSEEY YAR AMANA.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM .
Shara take a tsakar gidan tana wake waken ta can taji motsin fitowar boss din nata yana waya ta baya lallabawa tayi dan tafiya tajiwa kunnen ta abinji labewa tayi tana jinsa yadda yake wayar
“”I really miss you alot my happess to be sensely speaking ina son ganin ki yau din nan””( nayi kewar ki sosai farin cikina magamar gsky ina son ganin ki yau din nan””
Daga dayar bangaren naji tayi murmushi tanacewa
“”Haba ruhina yaushe yaushe na tafi da zakace kana son ganina nafa kusa dawowa nan da kwana biyune fa kada kaji kawani damu”” dan bata rai yayi
Karanta Gidan Uncle Hausa Novel
“”Owk daman ai baki damu daniba shiyasa kike yimin wannan maganar to shikenan babu damuwa ai shikenan sai anjima””
“”Haba mana ruhina wasa nake amman dan Allah kabari sai jibi na dawo har yanzun ban kammala aikin da nakeyi bane kuma kaga har yanzu jikin mummy babu dadi sosai bata gama farfadewa ba amman zanyi kokari nadawo nan da jibin insha Allah””
Murmushi yayi “”owk babu damuwa farin cikina Allah ubangiji yadawo min dake lafiya””
“”Amin summa Amin farin cikina kokai fa banji dariyar kaba yau”” murmushi yayi sosai harsai da taji murmushin nasa ta waya sannan sukayi bankwana suka aje wayar
Tabe baki lubnarh tayi tana wani yatsina fuska tace “”mumafuki kamar da gaske bayan nan….. Maganar natane yasarke jin yafara wata wayar ta kara labewa danji ,,
“”Hello muradina ya kike””
“”Owk babu damuwa sai kinzo ina jiranki fa yanzu kinji muradi”” owk byeee see you”” daga haka yakatse kirar kwalawa lubnarh kira yafara yi da gudu tabar gun sannan tafara amsawa ta iso da saurin ta ta tsugun na
“”Gani yallabai”” kallon ta yayi “”kifara gyaran gidan da kyau sabida hajara tana hanya jibi insha Allah””
Murmushi tayi sannan tace “”to yallabai insha Allah zangyara dan Allah ina son naje gida naga su mama nima yau amman yau zan dawo””
“”To ba damuwa zaki iya tafiya””
“”To nagode”” kinyashi tayi kallon ta yayi yace “”uhmmm da wani abune kuma nace zaki iya tafiya ko bakiji bane ba “”
“Ahhhh naji yallabai daman dan Allah so nake kaban kudi sabida natafi ma su mama dashi sabida basu da kudi a hannu su”” kallonta yayi yasa hannu ya dauki kudin aljuhun sa yamika mata kallon sa tayi ta marairaice fuska
“””Gaskiya yallabai wannan kudin mai zaice musu “” bata rai yayi yace
“”Uban me kike nufi da wannan kudin mai zaice musu so kike na baki gaba dayakudin da na mallaka ko me””?
Bata rai tayi “”haba yallabai kaima kan kanka kasan wannan dubu goman bazaice musu komai ba ai””
“”Lubnarh ni kike gayawa haka””
“”Nashiga uku yallabai daga fadin gaskiya kasan yadda nake kokarin buye abinda ke faruwa agidan nan amman duk baka gani shikenan yallabai babu damuwa ko wancan dawowar auntyn saida takusan ganewa amman nayi iyakar yina nabasar da abun narufe shi””
Tsaki yayi yakara cilla mata yayi tafiyar sa batare da yajira abinda zata kuma cewa ba tabe baki tayi sannan ta tattara abinta da duba dubu biyar yakara mata tayi murmushi tace “”zaka sanine wallahi bakaga komai ba mahakinci kawai”” sannan tayi dariya tacigaba da sharar ta..
“”Wallahi bazaki gane bane surprise nakeson nayi masa yau din nan shiyasa banfada masa zandawo yau ba saidai kawai yaganni kamar saukar aradu””tacigaba da hada kayanta tana wani farin ciki zataje taga rabin rainta tabe baki kausar tayi tace ”””ke kuwa aunty da kin bari gobe dan Allah kinga sainima nabiki mutafi tare kinji”” tsayawa tayi da gyara kayan tace
“”Ai daman kintashi kinshirya ne mutafi yanzu kausar dan Allah bazaki gane yadda nake son ganin mijina ba kwata kwata nayi missing nashi da yawa””
“‘a’a wallahi yadda kike son ganin naki nima haka nake son ganin nawa bugun zucuyar dan kwarama ke kuna tare safe rana har dare amman nifa nazo goben idan nashirya ko jibi”” a haka suka gama ta rakata tashiga motar ta tayi gaba sai kd
Tana kwance saman kirjin sa tana dariya kamar wacce tasamu aikin hajji
Lubnarh kamm taje gidan su suna zaune suna fira taba mama kudin da jabir yabata zare idanu mama tayi tana rike baki
“”Eyyyyeeee lubabatu duk wadannan kudin shiyabaki kin tabbata anya lubabatu”” bata rai lubnarh tayi
“”Haba mama kawai sai na daukar masa kudi Allah shiyaban fa””
“”Ni bance haka tashi kije kigaida innan ku kidawo”” batarai ta kumayi tana turu baki ita bazataje ba sanin idan zata kwana tanayi mama ba kallon ta zatayi ba ballantana tace ci kanki yasa tamike tanufi dakin inna asabe tana shiga ta taddata zaune tayi uban tagumi tana kallon silin sallama tayi kallo daya ta mata takawar da kai batare da ta amsa mata sallamar ba bata damuba saima tabe baki da tayi tace “”ina yini inna””” harara ta cillah mata tare da cewa
“”Daban yini ba zaki ganni nace da ban yiniba zaki ganni munafukar banza munafukan hufi dagake har uwar taki ina sane da duk wata munafuncin da kukeyi kuma zakuyi dana sanine matsiyata kawai karuwar banza da hofi kawai tashi ni kiban gu anan”” kwallane taciko mata bata bari yafito ba ta kakalo murmushin karfin hali ta kalle ta batare da ta tanka tayi gaba tafita tayiwa mama sallama tafita zata koma gida harta kai kufar gida ta dawo tace “”mama har zan tafi banga yayaba har yanzu bata dawo ba””
Shafa kanta tayi “”zan fada mata kinzo kinji Allah yayi muku albarka kije kada anemeki agida kinji”” gyada mata kai tayi sannan ta share kwallar dake gangaro mata tarungumi mama tana shafa bayanta sannan suka rabo tayi na gida ta tari motar yakaita gida,,
Tana shiga gidan taga motar azeezah saida gaban ta yafadi haka ta daure tashiga gidan mai gadine yace mata sannu lubnarh da dawowa kallonsa tayi tace “”yauwa yayana ya aikin” murmushi yayi yace “”alhmdllh”” sannan tashige bata shiga bangaren ba tashiga nata dakin ta dauki littafin ta tafita gerden ta zauna tana karatu littafin koyon turancine take karan tawa tana kuma dan tsintar wasu abubuwan kasancewar tayi primary kuma tanada kwakwalwa sosai tana saurin gane abu da wuri tana cikin karatunne taji an finciki littafin gada hannun ta dagowa tayi tasan mai wannan aiki ko ba afada ba azeezah ce durkusawa tayi tana gaidata yamutsa fuska tayi
“”Ke dan uwarki sai yanzu kikaga daman dawowa daga tsinannen gidan naku ko yar banza mai kama da aljannu kawai””
Muje zuwa littafi na gaba danjin yadda zata kasance a littafin lubnarh Yar aiki taku nuseey yar Amana.
Leave a Comment