Hausa Novels

Ma’aikaciya Hausa Novel Complete

Ma’aikaciya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ban ai ka/ki dole ki/ka ranta mun littafi ba, idan yayi ma ki/ka ka karanta idan kuma bai maka ba shikenan, ko ka faɗi Alkhairi ko kai shiru.

 

 

 

 

 

Page 1

 

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

Dija zaune take a falo, tana kallon TV, daman can tun ɗazun ta riga da ta gama duk wasu gyare-gyaren da zatai harda ma abinci, duk da dai ɗazun ɗin data gama abincin tashiga tayi wanka sanan ta fito nan falo tana kallon tv, zuwa can dai Lukman bai kai ga dawowa ba, Dija tana zaune cikin fakon tana kallo ji tayi jikinta ya ƙara yi mata wani iri. Tashi tayi tashiga toilet ɗin da ke cikin falon ta watsa ruwa yadda zataji dama² ajikinta, ko da ta fito nan ta zauna cikin falo, zuwa can ta ƙara samun wani lokaci nan cikin falo tana kallo tashi tayi ta nufa upstairs can bedroom nata, tana shiga ta zauna bakin dressing mirror, kafin kace me cikin ƙanƙanin lokaci har ta gyara jikinta taci,ado tayi taci kwalliya tayi kyau sosai, daman lokacin yamma yayi wanka dare tayi.

 

Ta dawo falo kenan zaman da zatai, bata kai ga zama ba sai ga yayanta Lukman ya dawo daga wurin aiki, bata ƙarisa zaman ba haka tai maza ta nufa inda yayanta Lukman yake, ta amshi jakarshi tana mai sannu da zuwa can ta rungumenshi, hannunshi yasa yana shafa kanta ita ko sai ƙara kwanta tayi akan ƙirjinshi, hanunshi ɗayan kuma yana bayanta. Sanan suka saki junansu, tai maza ta wuce bedroom nashi ta kai mai jakarshi, nan ta barshi cikin falo yana ƙoƙarin shiga wanka. Toilet ɗin dake falo ya shiga nan yayi wanka.

 

Ko da Lukman ya fito daga wanka, taraswa yayi Ƙan warshi har ta fito mai da kayan da zai canza ajikinshi. Fitowar shi kenan ke da wuya Dija ta ƙariso inda yake tsaye daman towel ne daure a jikinsa, nan ta zaunar dashi a kujera dake cikin falon ta sauya mai kayan jikinsa, tagyarashi tsaf yayi kyau sosai ta ɗauko hula ta samai zai tashi kenan ta riƙeshi tana mai nuni da ido, alamun ya tsaya tana zuwa ko da taje ta dawo, mirror ta ɗauko ya diba kanshi kalar kyan da yayi, kamar ta santa abunda shima zai tashi kenan yaje ya diba ta riƙe shi tare da mai nuni da idanu ya tsaya. Lukman amsar mirror yayi a hannunta, sake ƙurama mirror idanunshi yayi, yana ƙara sake kallon kanshi a madubi da kuma kalar kyan da yasha, cikin rashin faɗi yake, “Wow can cuwai ashe haka kika iya kwalliya tsaf mutum yayi kyau sosai Honey ni bansanibah, kike barina ina fita haka ko kyau banyi?”

Dija tace, “No hubby ba haka bane, kawai nima naga maye amfanin na maka kwalliya kayi kyau sosai, kaje ka fita waje kana nuna ma wasu matan awaje suna kallo suna cewa kayi kyau, especially matan da kuke aiki da su acikin Company”

 

“Oh ke kuma kishin da kike kenan, wato bakison kimun kwalliya na fita kenan nayi kyau dan kada wata ta kallah tace nayi kyau koh?”

 

“Emnh ko kaga laifina yayana, amma kayi hakuri naga gwara dai nai ma abuna kwalliya a gida, gani gashi inta kallon abuna ina jin sanyi a raina ko ya ka ce yayana?”

 

“Hakane ƙan wata na ganoki ɗan banzan kishi ne dake wallahi”

 

“Yayana kaji pa, idan banyi kishi akanka ba akan waye zanyi, dole na nuna kishina akanka yayana, maganar gaskiya sam bazan bari wata ta raɓar mun kai ba”

 

“Toh shikenan naji kwantar da hankalinki Honey, ke tawa ce ni kaɗai haka zalika kamar yadda nima nake naki ne mallakine ke kaɗai, zuciyata taki ce, kin zama jinin jikina abokiyar rayuwata ƙan wata bana tunanin akwai wata mace a duniyar nan da nake so bayan ke”

 

“Allah sarki yayana na aminta dakai, nasan nice kaɗai daga ni babu wata, saboda haka tashi muje danitable muje muci abinci, daman na shirya tsaf kamar kullum kaine kawai nake jiran dawowarka kai wanka ka shirya tsaf sai kazo muci abinci tare”

Bismillahi Lukman ya tashi suna riƙe da hannun junansu suka wuce danitable suka zazzauna daman Dija ta riga data haɗa musu komai kawai jiran zuwan yayanta take yazo suci abinci, idan ya gama kintsawa. Dija bata saba da cin abinci ba tare da yayanta Lukman ba, hakan yasa koda yaushe indai yayanta Lukman yana nan bata cin abinci sam har sai lokacin dawowarshi yayi tsawon 3month da sukai da aurensu. Daman already ta zuba masu shi a plate, ta matso da seat nata kusa dashi ta zauna, tare da jawo musu plate ɗaya wanda tana buɗe wa, Wow sai ga delicious jallof rice buɗe wanta ke da wuya ƙamshin abincin ya fara dukan kafofin hancishi, hakan yasashi shaƙar iska yana faɗin, ” wow ƙamshi daɗi”

Haɗa ido sukai suka kalli juna, Murmushi sukai ma junansu Dija tace,

” Allah koh hubbyna, daman wa kai nayishi shiyasa na rufe shi ban yarda ko wanne yaji ƙamshin shi ba sai kai kaɗai nawan”

Nasan da haka gimbiyata nima daga jin ƙamshi na tabbatar da hakan domin wanna girkin na yau ya babbanta da na ko wacce rana.

“Kai pa hubby kana fashemun kai, kaji kah sai kace ba irinshi nake maka kullum bah?”

 

“Uhmm ke dai kawai idan ana sallah ba,a magana amma na yau wallahi special 1 ne ina fada miki Honey”

“Naji amma nidai banga bambancinshi dana ko da yaushe ba”

 

 

“Kawai dai yayana kana faɗe ne”

 

“Ƙan wata kenan karki damu tunda kikaji na faɗa miki haka ki yadda, eh da gaske yayi daɗin” Uhmm uhmmm cikin shagwaɓa take magana, faɗi take, “Nidai wallahi Yaya Lukman ban yarda ba, Bismillah kazo kaci abinci” tunda ta fara shagwaɓa ya bita da idanu yana kallonta, Bismillah da ta cemai ne ya buɗe bakinshi ta saka mai loma daya, ma’ana cokali ɗaya. Lumshe idanu yayi tsabar daɗin girkin da yaji faɗi yake Wow very very nice.

Ita ko Dija ko fara cin abincin ma batai ba data girka, karo na biyu ta sake ɗebo wata loma cikin cokali, ya buɗe bakinshi ta sake sakamai ita ya cinye yana mata santin daɗin girki,haka tai ta bashi abaki yana ci har sai da ta tabbatar yaci ya ƙoshi sannan ta barshi, haka sanan itama ta fara gyara zamanta zataci nata abincin ragowar nashi ne wanda ta gama bashi, ko karawo ba tai bah saboda tana tunanin idan taci wanan ya wadatar, ta ɗauko cokali kenan zata kai shi bakinta Yayanta Lukman yayi wuf yayi sauri ya riƙe hannunta, faɗi yake, “haba, ƙan wata sai kace bana kusa dake ai kamar yadda nima kika gama bani abaki naci kuma naji daɗi sosai har kika ƙosar dani da wannan daddaɗan girkin naki, nima ya zama mun wajibine nima naga na baki shi abaki kamar yadda nima kika ban ƙan wata saboda haka bani cokalin nan”

Kallonshi tayi suka ido Murmushi tayi mai tana cewa, “haba Yaya pls ka bari ni zanci da kai na, kai ma naga kadawo daga wurin aikine, Maybe duk ka gaji sosai to kaga is better ace na hutar dakai na baka shi a bakinka domin kai ma kasamu kahuta,nasan kai kanka kafi samun natsuwa ahakan?”

 

“Ƙwarai da gaske hakane amma, nima indai a kankine inshallah bazan taɓa gajiyawa ba, nidai kawai abunda nake so dake yanzu kawai nidai kibani cokalin, nima na baki abaki hankalina ya kwanta, indai baki bani ba na baki bana tunanin cewa hankalina zai kwantar duk wani hutu da kike magana da farin ciki basu taɓa samu in baki agefena sai dake ƙan wata, miƙo mun kinji pls”

 

Rufe fuskarta tayi tsabar kunyar shi da takeji domin kalamanshi, ta gamsu dasu sosai ɗari bisa ɗari miƙo mai tayi yasa hannunshi ya amsa yana Murmushi sannan itama ta buɗe bakinta ya saka mata loma ɗaya cikin bakinta, mai abu da abunshi kushe abunta ma take a wurinta wai bai daɗi bah.

Dija tana faɗin, “kawai dai yaya kacika zolaya dai haka tace!…”

Haka shima Lukman yayi ta bata abakinta tana ci, har itama ta ƙoshi sanan ya tashi ya buɗe frigde ɗin dake falon ya ɗauko musu ruwa mai sanyi tare da jiuce haka suka sha sukai nak, lukman ya riƙe hannun Dija suka wuce falo nan suka zauna suka cigaba da hira suna kallon tv har magrib ta yi, sanan lukman ya tashi ya shiga toilet yayi tsarki sanna ya ɗaura alwala ya fito ya wuce masallaci nan ya bar Dija itama tana shirin shiga toilet tayi tsarki, tana shiga tayi alwala itama ta fito can bedroom nata ta koma ta ɗauko nadduma ta da iƙama tayi sallah ta idar ta shafa addu’a nan ta zauna kan nadduma tana jiran tsan mani ko zataji dawowan yayanta daganan itama sai ta dawo nan cikin falon.

Shiru² har yanzu Lukman bai dawo gida ba Dija, zaune ta ke nadduma tun ɗazun ko tashi batai ba tana jiran tsan mani, dawowar yayanta Lukman amma shiru bai dawo bah, nan ta ɗauko wayarta tana dadda nawa tsawon lokaci jim kaɗan ke da wuya sai ga ƙarar laspeaker masallaci ana kiran sallah isha’i daman tana da alwalarta wanda tayi sallah magrib Dija ta tashi ta tada iƙama tayi sallah ta idar tana idarwa ta canza kayan dake jikinta tasa kayan bacci transparent, ta koma downstairs nan falo ta kunna Tv tana kallo.

Tana cikin kallonan ta kunna tv, misalin karfe tara dai² 9:00pm sai ga knocked taji ana ƙwanƙwasa ƙofar falon, tai maza ta tashi zumbur da saurin ta buɗe ƙofar ko da bata sani ba, tana jin cewa a ranta yayanta ne Lukman ilai kuwa shi ne, ko da ta buɗe dashi tayi arba tayi kicibis, aiko cikin hanzari tai maza ta rugumeshi tana mai oyoyoyo.

 

Suna riƙe da juna haka suka wuce suka zauna kan kujera nan cikin falon, daga baya Dija ta tashi ta ɗauko dan makulli ta kulle ƙofar falon, sann ta dawo ta zauna. Kusa da yayanta Lukman, kan kace ma uwar shagwaɓa harta fara uhmm uhmm yaya shine katafi karbani nai kewarki ko kadawoma da wuri kasan dai ina nan ina jiranka, budar bakinshi cemata yayi kiyi haƙuri kan wata ina sane dake ban mance dake ba kawai dai wani abu na tsaya jira bayan an gama sallah Isha’i, shine yasa zaki ga na ɗandaɗe pls.

Shikenan yayana tashi muje koh, daman kai kawai nake jira, uhmmm ƙan wata daman nima shirin hakan nake, ya ɗauki remote ya kashen tv suka wuce upstairs bedroom, suna zuwa cikin bedroom ɗin lukman ya fara ƙoƙarin cire kayan dake jikinshi, da sauri Dija tayi maza ta riƙe hannunshi cikin shagwaɓa tana fadin uhmm yaya aikinane pls dan allah ka bari na cire maka, tana gama fadin haka ta sunkuyar da kanta ƙasa, kunyace ta kamata.

 

Shikenan kanwata abunda kike so nima shi nake so, bani da zaɓi sai abunda kika zaɓa,

 

Tsabar murna bata san lokacin da ta fara kissed kumatunshi ba, muah muah muah. Kafin kace me, tasa hannunta duk da tanajin kunya ta cire mai babar riga sanann ta cire mai babban wandonshi, daga shi sai karamin wando da singlet ajikinshi, tana gama cire mai daman hannunshi ƙyarƙyarwa suke suna rawa,bai san sa inda ya janyota jikinshi ba.

 

Ya fara romance nata yana mammatsa jikinta, wani uban ƙara saka mai zata kwace amma ta kasa faɗi take, ” yayana pls dan Allah wallahi zafi nakejin, lumshe idanu ya fara alamun daɗi matsar da yake mata yakeji yana cigaba, dija zafin da takeji batasan lokacin da saki kuka ba, ganin haka da yaya lukman yayi da gaske take zafi takeji hakan yasashi ya saketa daga jikinshi. Komawa tayi gefe ɗaya sai fama rusa kuka take, Lukman zuwa yayi inda take kuka ya durkusa ya lallasheta aan cewar bazai mata komai ba suje su kwanta, hakan yasata tayi shiru ta dena kukan da takeyi, ta bishi suka wuce suka kwanta ya sata aƙirjinsa har bacci ya kwasheta.

 

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

 

 

Washegari da sanyin safiya, Dija da Lukman zaune suke a danitable kan kujera, bayan sun kammala breakfast zaune suke a dani ɗin suna hira.

Zuwa ca Dija tace, “Yayana”

“Na,am kan wata”

“Uhmm yayana nayi maka magana, kamar ka manta”

“Ayyah ƙan wata hakane kuwa kiyi haƙuri, amma yanzu ina jinki faɗa mun?”

“Okay daman maganar ma’aikaciyar da nai maika magana kace zaka nemo mun ne nashiru baka ce mun komai ba, dan Allah yayana”

“Shikenan naji karki damu ki kwantar da hankalinki insha Allah zan sa anemo miki ita shikenan hankalinki ya kwanta, shikenan ni zan fita tashi ki ɗauko mun jakata” cikin hanzari Dija ta tashi taje ta ɗauko ma yayanta Lukman jakarshi sanan ta rataya mai ita, tare da mai sumba agoshinshi, tana mai Allah tsare mun kai sai kadawo yayana, “shima haka ya mata byeee byeeee Ameen ƙan wata”

Dija tashi tayi, tayi aikace aikacen gida wanda hakan ke matuƙar ci mata tuwo a ƙwarya, zuwa can tadawo ɗaki ta kwanta tana hutawa Jim kaɗan sai ga ƙarar laspeaker masallaci ana kiran sallah azahr, Dija ta tashi tashiga toilet tayi tsarki sanna tayi alwala ta fito tazo tayi sallah ta idar nan ta dawo falo tana kwace haka ta ɗan kishin giɗa sai ga Lukman yayanta har ya dawo daga wurin aiki, yau bashi da aikin sosai da wuri ya dawo.

Ta tashi cikin sauri ta mai sannu da xuwa yayana, ta amshi jakar hannunshi ta ajeta gefe ɗaya ya kawo hannunshi kenan zai rungumeta ta matsa ta ja baya Dija. Tambayar data fara fitowa cikin bakinta shine, “yayana ya maganar ma’aikaciyar?”

 

“Please I’m sorry Ƙan wata wallahi sham mantawa nake da maganar nan, amma ki kwantar da hankalinki insha Allah very soon zan kawo miki ma’aikaciya wacce zata rinka tamaki aiki kamar yadda kika buƙata ki aminta da ni Ƙan wata”

 

 

 

 

 

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!