Macen Sirri Hausa Novel Complete
Bismillahir rahmanir rahim
Acan ƙasan anguwar akwai wani jeji daya kasance yana ɗauke da fulani ,wasu basa jin hausa wasu ko sbda suna tallan nono suna jin hausa. Rugar Ruwaji ta kasance tana ɗauke da shanaye masu yawan gaske ,kasancewar Ruwaji mutum ne mai arziƙin , ƴa ƴansa uku da Modibbo da Usmanu ,
da Ramatu ,Modibbo shine babba sai Usmanu ke binsa Jamila ce autarsu tana da shekaru 15 , yayan nata ko ya doshi talatin da biyu Usmanu shekarasa ashirin , sun yi karatun islamiya dana boko mai zurfi duk da karatun da sukayi basu yi yunƙurin barin jejin ba ,sbda ji sukeyi rayuwar nan tafi musu daɗi .
Matarsa wacce Æ´aÆ´an suke kira da Dada tsohuwar kirki ga son mutane ita dai a burinta idan da Ruwaji ya yarje mata da tuni bata jejin nan ,koda yaushe tayi magana sai yace “mata ai komai da lokaci.
Ranar Juma’a ,ranace da Jamila take cin ado sosai kuma bata tallar nono ko É—aya kuma babu wanda yake matsa mata sbda sun san irin Æ™oÆ™arinta , bayan tayi wanka ta fito É—aure da zanin atamfa ta nufi É—akinsu ,
kasancewar sun so zama a gurin harda gini sukayi kuma filin nasu ne , man shafawa ta É—auko ta zauna bakin gado tare da lakato man ta shafe jikinta tare da taÉ“a Dada dake kwance tace “wane kaya zansa ?”Dada da bacci ya fara kamata tace “haba Jamila kullum nine mai zaÉ“a miki kaya kisa duk wanda kikaga yayi miki man “Jamila na murna ta janyo jakar kayanta ta ciro riga da zani iri É—aya da É—ankwali zanin babu kalmasa ta É—aura ,
ta juya tasa riga wai kar Dada taga Æ™irgrn dangin ta , tana gama sawa ta fice tasa takalminta na roba wanda ba kullum take sanyashi ba sai zata yawon juma’a ko kuma anguwa , ficewa tayi ta nufi É—akin Matar Usmanu mai suna Harira ta zauna tare da cewa “ina yayana ?”Harira irin matan nan ne da bata Æ™aunar taga danginsa sun raÉ“esa tayi tayi akan subar rugar nan su koma wani gurin Usmanu yaÆ™i ,
yace “inhar ba babansa bane yabar ruga shima ya bari gara ma ta dena wanan zancen “Harira ta taÉ“e baki tace “kin bani ajiyarsa ne da zaki tambayeni ?Jamila ba baya ba gurin rashin kunya tace “to idan ba’a tambayeki ba wa za’a tambaya ta fice da gudu tana murguÉ—awa Harira baki “zan kamaki “Harira tace “tana Æ™wafa ,
Jamila na fita taci karo da yayan nata suna shirin shigowa gida shi da abokinsa ,cafkota Usmanu yayi yace “ina zaki ne Jamila naga kinci kwaliya ?”Jamila na dariya tace “yaya yaufa juma’a “Usmanu na dariya yace “au ai na mance ga abokina yazo gurinki “durÆ™usawa Jamila tayi ta gaida abokin yayan nata ya amsa yayan ya basu guri abokin ya riÆ™e hannun Jamila suka É—an fara tafiya ,sai da sukayi nisa sanan ya tsaya yace
“Jamila ba tun yanzu ba ina É—awainiya da soyayyarki a zuciyata ina fatan zaki amince in fito a matsayin mijinki “rufe fuska Jamila tayi kana tace “ni nacewa “baba bazanyi aure da wuri ba karatu zanyi kuma ya amince min “murmishi abokin yayi kana yace “naji ban katse ki ba idan munyi aure nayi miki alÆ™awarin barinki kici gaba da karatu kinji
“kasancewarta mai wa wayon gaske tace “Laminu kayi haÆ™uri ni karatu zanyi bazanyi aure yanzu ba “ta juya ta dawo gida ,da gudu ta faÉ—a É—akin nasu tare da sakin kuka a jikin Dada ,cikin firgici Dada ta miÆ™e tace “mai ya faru ne Jamila am”Jamila dake share hawaye taba wa Dada labarin kaf hirar da sukayi da Laminu bata rage komai ba ,
Dada tace “Jamila am ba haka akeyi ba kinsan Laminu yana da zuciya kuma abin da tunaninsa yazo masa shi yake baya duba abin da zai biyo baya ina ganin ki bashi haÆ™uri ku rabu lafiya shine mafita.
Jamila dake kuka tace “nifa karatu nake sonyi Dada “uhm Dada tace “tare da miÆ™ewa ta fice sbda fitinar Jamila .
Sai da Laminu ya daÉ—e zaune a gurin da Jamila ta barshi yayi dariyar mugunta tare da cewa “yaro man kaza in tasan wani batasan wani ba “ya miÆ™e yabar gurin , kai tsaye gidansu ya wuce ya sami mamansa wacce yake ce mata Fulani tana zaune tana gyara masara ,
ya zauna kusa da ita cikin shagwaÉ“e fuska yace “Fulani nace ina son yarinyar Ruwaji tace “bata sona wlh duk abin da ya biyo baya suyi kuka da kansu “gaban Fulani ne ya faÉ—i har da zata haushi da faÉ—a dai kuma ta sassauta murya kasancewarsa auta kuma shine É—anta tilo bayanshi ko É“ari bata taÉ“a yiba a hanlin yanzu yana da shekaru ashirin da bakwai a duniya ,
tace “Laminu na kabi a hankali ni da kaina zanje gidan in samesu inyi musu magana akan kana son Æ´arsu “turo baki Laminu yayi kana yace “ai tace “ba yanzu zatayi aure ba kuma ta zageni ma “waro ido Fulani tayi kana tace “ikon Allah har Jamila takai matakin da zata dinga yiwa na gaba da ita rashin kunya to ai yayi ka barni dasu kawai “ba tare da Laminu ya kula Fulani ba ya wuce ya barta zaune a gurin ,
dandalin da suke zama shida abokansa ya nufa ,yana zuwa suka fara É—ago masa hannu yawancin su tsummokara ne a hannunsu na shaye-shaye , da alamun damuwa Laminu ya zauna a cikinsu yace “kai ku dakata wlh ina cikin wani hali ,wai kamar ni Jamila tace “bata sona ,kuma naga Æ™iyayyata a cikin idonta ina wlhi da sake “abokan ne suka tuntsire da dariya É—aya daga cikinsu yace “ai bakasan abin da zakayi ba ,
kawai ka bari ta fito da nono ka hura mata hodar nan da muke siyarwa “tafawa sukayi Laminu yace “gaskiya nagode da shawara ,kwata-kwata ban kawo wanan tunanin ba ashe gara danazo gareku tabbas nagode “abokan sukace kai dalla ware tsakaninmu har da wata godiya ne “cikin muryar su data kasance babu daÉ—in saurara ,
Æ™arÉ“ar nasa yayi shima yabi sahu ,suna zaune a gurin har yamma tayi sbda ba sana’a suke ba sana’arsu itace siyarda hodar ibilis , sun bugu sosai basa tantance fari da baÆ™i Lamin yace “mu haÉ—u gobe ni nayi gida “amsa masa sukayi da a huta lpy “ya tafi yana tangaÉ—i .
Kai tsaye ɗakinsa dake ƙofar gida ya nufa tare da buɗe kwaɗon jiki ya shige ,ya faɗi jugub kan katifarsa yana surutai ,sallah kam babu magana sai dai muce Allah ya bamu alheri.
Washe gari tun safe Jamila ta fito wanka ,bayan ta shirya aka haÉ—a mata nono a robar fenti da fura da dambu da suga ,Dada ta É—orata har zata fita Dada tace “bakici komai ba Jamila ?”waro ido Jamila tayi kana tace “ai na mance amma idan naje can zansha nono “to Dada tace “tayi mata Allah ya bada sa’a “amin Jamila tace “ta wuce , tana cikin tafiya ta haÉ—u da babanta tace “baba sai na dawo “yace “Jamila Allah ya dawo dake lafiya tace “amin ya wuce ,
tana tafiya tana waÆ™a har ta iso Æ™ofar gidan su Laminu ,tsayawa tayi ta gaishe da Fulani mahaifiyar Laminu ,amsawa Fulani tayi babu yabo babu fallasa tace “ya maman naki ?”lafiya Jamila tace “ta wuce tana ci gaba da waÆ™arta , tayi nisa sosai tana shirin gyara hijab É—inta daya rufe mata fuska taji an cafki boobs É—inta ,a razane ta fara kiciniyar buÉ—e fuskarta hannunta É—aya na riÆ™e da robar dake kanta cikin muryarta siririya tace “dan Allah waye bana son islanci “Laminu daya rikice jin taurin boobs É—inta ya É“arar da nonon tare da É—agata cak still fuskarta a rufe yake yana tafiya da ita yana waige É—aya daga cikin abokinsa yazo da mashin suka haye ,
tafiya suke sosai babu ko sararawa sai da suka iso wani katafaren gurin mai kama da store, dan É—aki ne na ajiyar abinci , mashin É—in ya tsayar , Laminu yace “yawwa ArÉ—o barmu anan kaje ka sanya ihu kace kaga wani ya gudu da Jamila “Jamila dake cukuwaikuye da hijab tace “….!
Ina masoya littafin NIDA YARINYA a fito a nunamin love ta hanyar siyan zazzafan littafina mai É—auke da tsantsar soyayya wacce ta wuce na littafin NIDA YARINYA kardai in cimaku da surutu siyan nagari..
https://mynovels.com.ng/kafin-aure-hausa-novel-complete/
https://mynovels.com.ng/bakar-fata-hausa-novel-complete/
Comments and share