Macijine Shi Hausa Novel Complete
Tag: MACIJINE SHI
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers
Free book
Page 1
Bismillahir rahmanir rahim,Ina godiya ga Allah daya bani damar fara wannan littafi ,bayan kammala littafin soyayyata.Allah kasa yadda na fara lafiya naga bayansa lafiya ameen.
Gargadi banyarda wani ko wata ya juyamin wannnan littafi ta kowace sigar ba.
Wata kyakkyawar yarinya na hango sanye da kaya irin na Fulani ,wato rigar saki dakuma zaninta,duka duka rigar da kadan ta wuce cibiyar ta,saidai kuma ta daura zanin ya rufe mata cikinta ta yadda ba wanda zai ga jikinta awaje.
Farace irin mai sirkin yallow -yellow din nan,tana da doguwar fuska mai kyan tsari dauke da dogon siririn hanci har baka,bakinta dan karami kamar gidan tsutsa,tana da irin manyan idanunnan masu kamar tana jin barci,ga gashin ido zara -zara.
Girarta kuwa ,kamar wacce aka dora Mata ita dan saiti,gaban goshinta wasu yan kananan gashine kwance lub lub kamar na jarirai.
Masha Allah yarinyar ta ko ina ta hadu ,dan doguwace marar jiki saidai fa Allah ya hore mata hips Kai kace wata babbar macece Sannan akwai alamun girma akirjinta , ma’ana dai akwai dukiyar Fulani dasuka fara tasawa akirjin nata.
Duka duka wannan yarinyar bata wuce shekara 15/16 ba ,amma kallo daya zaka yi mata kasan Allah yayi halitta agurin.
Sandace irin ta Fulani ahannunta tana dagawa sama ,da alama tana son hada kan wasu tarin sha’nun dake kiwone wani kayataccen jeji ,dan kuwa ciyawace agurin Kore sharr da ita ,sha’nun suna ta cin abarsu .
Tafiya ta farayi gurin shanun dake dan nesa da ita ,dan ita tana daga jikin wata bishiya ne tana kallon yadda suke kiwo abinsu.
Kanta ta daga ta kalli yadda garin ke hada wani irin hadari baki kirin dashi ,kuma da alama koda yaushe ruwa na iya saukowa.
“Kuzo mu tai gida abokaina kada ruwan nan ya sauko ya taba mu banin son nai mura aradu”
Cikin Yaren fulatanci take musu magana ,tana daga sandarta .aikuwa kamar wanda suke jin me take fadi suka fara yin hanyar gida .
Murmushi tayi tana mai binsu tana kara daga sandarta .
Tafiya suke cikin jajen ita kadai daga ita sai wadannan garken shanun ,sam ba alamun tsoro tattare da ita,yar wakar tama take tana daga sandar sama.
Kusan tafiyar minti biyar sukayi ,sannan na fara hango bukkokinsu dake can gaba kadan .
AHankali naga duk wani annurin dake kan fuskar yarinyar ya dauke ,nan da nan damuwa ta maye gurbin nishadi da take ,sosai naga jikinta yayi sanyi har suka karasa wata bukka dake farkon rigar da alama nan ne gidansu.
Garken shanun ta fara zuwa ta daure su tsaf sannan ta nufi cikin gidan,bakinta dauke da sallama.
Lokacin har anfara yayyafi .
Ba kowa a tsakar gidan nasu ,hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da nufar wata bukka cikin sauri.
Saidai kafin ta karasa kofar bukkar aka daka mata wata uwar tsakar da saida sandar hannunta ta fadi kasa.
Afirgice ta juyi jikinta na rawa sosai kamar dan mazari.da sauri ta karaso gurin matar data daka mata tsawar,
“Gani gwagwgo”ta fada cikin rawar murya. Kallon matar nayi sai na tarar da
matar farace saidai kuma kazanta da rashin kulawa yasa tayi wani irin baki baki fari fari,sannan tana da jiki sosai sam fuskar ta ba alamun rahama a cikinta.
Tana tsaye a kofar bukkar ta tana hararar yarinyar dake durkushe gabanta.
Cikin masifa da bala’i matar ta fara magana da hausarta marar kyau.
“Da kake kokarin shigewa dakin,ubankane zai debi ruwan?
Ko kin ajiye bawanki ne a gidan?matar ta fada cikin zaro ido.
Kan yarinyar akasa jikinta na rawa ta fara magana
“Allah hukkumu hakuri gwagwgo naga ruwa na don sauka ne shiyasa ban deboba”ta fada cikin rawar murya da tsoro.
Wani wawan mari matar ta kai mata cikin rashin imani da tausayi cewar yanzu ta dawo daga kiwo kuma ko abinci bata ci amma take kokarin sake turata rafi.
“Shegen yaro mai bakin hali wllh yanzu koke kidobo min ruwan nan dan ubanki karuwa kawai”matar ta fada tana mai hankade yarinyar .
Faduwa tayi sosai hannunta ya bugu da wani dutse dake ajiye tsakar gidan da alama na zama ne.
Kara ta saka cikin azaba tana mai dafe hannunta dake mata wata irin azabtar zafi.
“Wayyo handi ɗin boni lalashewa gwagwgo hannu na ta ɓalle” ya rinyar ta faɗa cikin azaba.
“Shege wllh dama zai karye danafi kowa jin dadi yarinya kamar aljana,ace kinfi kowa kyau arugarnan? Na tsaneka fatto saina bata wannan shegen fuskan baki.maza ki tashi kona shakeki agurin ki mutu kowa ya huta” cewar matar cikin bala’i da tsantsar nuna tsana ga dattin.
Cikin hanzarin ta mike ta zari wani boket din roba ta fice tana kuka sosai.
Tafiya mai nisa tayi kafin tazo rafin, har zuwa lokacin kuka take hannunta sai zogi yake mata, ruwan ta debo cike da sauri dan kuwa ruwan da ake ya fara karfi.
Saidai me ?tana juyawa tayi arba da wani murtukeken maciji katon gaske ya fasa kai yana huci.
Wani irin mugun tsorone ya kamata nan da nan jikinta ya kama rawa har batasan lokacin da boket ɗin ya fadi kasa ya fashe ba.
Tashin hankali kenan wanda ba’a sa masa rana ,iyakar rushewa da tashin hankali yarinyar nan ta shiga.
Hannu ta ɗora aka tana mai kara ƙarfin kukanta.
“Wayyo ni fattu bukar na mutu na lalashe ya zanyi da rayuwata nashi zai karni wayyo baffana wayyo Allah ,taimaka min”
Ta faɗa tana kallon boket ɗin dake tarwatsa,dama kuma rana ta gama cin ubansa.
Shi kuwa macijin nan ganin yadda ta tsaya tana kallon sa kuma tana kallon fasashshen boket ɗin ta ,sai taga kamar neman makami take ,dan haka afusace yayi kanta
Ihu ta kwalla mai karfin gaske tare da zubewa agurin sumammiya dan ganin yadda macijin nan yayi kanta baki bude.
Masu karatu ya kukaji?
Meye ra’ayinku akan wannan Nobel ɗin?
Ina bukatar comment dinku idan buk din nan yayi muku dadi muci gaba.
Takuce har kullum anty mammy
Msr babi
Page 3/4
________________Cikin tsoro take shafa dogon abun dan jin ko menene,tabbas MACIJINE dan kuwa har kansa ta taɓo.
Aikuwa da hanzari ta janye hannunta cikin kidima ta fara ja baya tare da fasa wani irin gigitaccen ƙara,
“Ahhhhhhhh wayyo Allah baffa maciji!maciji !!maciji!!!”gaba ɗaya ta kidime abinda take iya faɗi kenan jikinta na rawa kamar ɗan mazari.
Allah Sarki baffa dama ba wani barci yake yi ba ,dan yana kula da ɗakin fattu ,kasancewar ɗakin yana gaf da ƙofane,dan haka jin ihunta da yayi ,yasa shi tashi agigice ya nufi ɗakin nata.
Haskawa yayi da tocila can ya hangota jikin bangon ɗakin ta duƙunƙu ne tana ta ihu,da alama batama cikin hayyacinta.
Da sauri ya nufeta yana kiran sunanta”fadimatu !ke fadimatu menene ?ya isa haka gani akusa dake baffanki ne kinji daina ihun “baffa ya faɗa cikin ƙasa ƙasa da murya dan karya ƙara tsorata ta.
Ita kuwa gaba ɗaya ta rikice kawai kira take “baffa maciji zai sareni baffa wayyo Allah na”
Ganin halin da take ciki ne yasa baffa ya fara tofa mata addu’a ,cikin minti biyu kuwa tayi shiru sai rawa da jikinta ke famanyi,ahankali ta daga kanta ta sauƙe kyawawan idanunta akan baffan nata,kawai saita saki kuka tana mai cewa”baffa MACIJINE yake son sarina aradu da idonsa na ganshi anan”ta faɗa tana nuna masa gurin dataga macijin.
Kallon gurin baffa yayi ,shifa ba abinda ya gani agurin ,kawai yana tunanin ko mugun mafarki tayi,dan haka cikin ƙokarin kwantar mata da hankali yace “shike nan fattu ya tafi maza koma ki kwonta kiyi addu’a ba abinda zai sameka kinji”ya faɗa cikin yanayin Hausar su ta Fulani.
Cikin kuka take girgiza masa kai “aradu baffa dawowa zaiyi tun daga rafi suke son cinyeni baffa ,bazan iya kwonshiya Ni kaɗai ba”ta ƙarasa tana mai matsowa kusa da baffan.
Shiru yayi yana tunanin mai ya kamata yayi,dan gaskiya yaga ta tsorata da yawa,dan haka cikin ƙarfin hali yace “tashi muje gurin hansai saiki kwonta shan ko”ya faɗa cikin tausaya wa.
Ai kafin ma ya rufe bakinsa ta kai ƙofa,dan ita kam babban burinta ta bar ɗakin nan,tama manta da gurin wa baffan yace taje.
MACIJINE SHI🪱🪱🪱
Na manya kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers
Free book
Page 5/6
________________Hawa macijin nan yayi kan ruwan cikin fattu ,daidai kan fuskarta ya tsaya tare da fasa kansa ,ya tsaya ƙuri yana kallon fuskar Tata, wacce tuni idanun fattu ke rufe tayi mutuwar kwance ko nunfashi ta kasa shaƙa cikin salama.
Shikuwa macijin nan ganin bata koda motsi saiya sauƙo daga ruwan cikinta ya tsaya saitin fuskar tata tare da fasa kansa yana huci ,.matsowa yayi sosai jikin fuskar tata yana hura mata iska daga bakinsa,sannan ya ɗan ja da baya ya tsaya yana kallon ta.
Ahankali fattu ta ɗan buɗe idanunta dan ganin shin me kuma macijin nan ke shiryawa ?ta yaya yake tsara kasheta itama,saidai tana buɗe idanta suka sauka akan na macijin nan ya ƙureta da idanunsa.
Cike da tsoro da fargaba fattu ta kafe shi da nata idanun,dan tsintar kanta tayi da kasa daina kallonsa,abubuwan mamaki take gani tare da macijin,sam kwayar idanunsa ba irin ta macizai bace,sak!irin ta mutane ce saidai gurin farin yayi wani irin kala kala , blue yellow pink ,Amma asalin kwayar baƙace ƙirin.
Sai kuma taga hawaye na zubowa daga idanun macijin kamar mutum yana kuka.
“Innalillahi wa’inna ilahirin raji’un, Allahumma ajirni fi musibati waaklifni kairan minha,la’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin”shine abinda fattu ta fara karantawa cikin zuciyarta jikinta na wani irin tsuma da karkarwa, tunda take bata taɓa ganin irin wannan macijin ba sai yau,ya maciji zai kasance da idanun mutane? sannan kuma jikinsa akwai banbanci sosai dana macizai,dan shi yana da wani irin jiki mai ban mamaki yadda kalar idanunsa ta kasance haka shima jikinsa yake .sannan kuma bai kai girma irin na macijin jiyan nan ba amma yana da girma shima sosai,kuma dogone na gaske.
Kallon kallo kawai ake tsakanin fattu da macijin nan,inda ahankali ya fara hucewa daga kumbura da fasa kan da yayi ,fattu na kallonsu harya koma normal jikinsa ya daidaita ,sannan ya fara ƙoƙarin barin ɗakin ta wata yar hanya dake jikin katangar karan ,wacce ita fattu sam bama tasan da ita ba sai yau,da alama dai shi yayiwa kansa hanyar.
Saida yaje gab da hanyar tasa saikuma ya juyo da kansa yana kallon fattun,shi bai tafiya ba kuma bai dawo ciki ba.
Sosai jikin fattu ke rawa tana zubda hawaye ,dan yau kam lamarin ya kulle mata kai ,wai wannan wane irin MACIJINE ?shin macijin ne ma kokuma wata halittar?sannan maiyasa yaƙi yi mata komai,sai dai ƙoƙarin ceto ta da yake atsammaninsa na ko bata numfashi?haƙiƙa akwai abin dubawa dan gane da wannan macijin.
“Fattu ! fattu!!kin tashine kinyi sallar lokaci yana ja fa”ta tsinkayo Muryar baffa daga wajen ɗakin yana mata magana .
Jin muryar baffa da fattu tayi sai hankalinta ya ɗan kwanta cikin ɗaga murya tace “baffa kazo ka taimaka min gwogwgo bata motsi”ta faɗa cikin Muryar kuka tana kallon macijin.
Cikin sauri da azama baffa ya shigo ɗakin yana faɗin”subhanallah me kuma ya sami Hansai din?
Cikin kuka fattu ta kalli baffa sannan ta kalli inda macijin nan yake ,har lokacin yana tsaye yana kallon ta,
“Baffa bansani ba kawai ta shigo tana dukana sainaga ta faɗi ƙasa”abinda fattu ta tsinci kanta kenan da faɗa murya na rawa.
Ahankali macijin nan ya juyar da kansa ya bi ta yar ƙofar nan ya fice.
Sai lokacin hankali fattu da nutsuwarta suka dawo jikinta ,cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta tashi zaune ,har lokacin akwai alamun tsoro da firgici akan fuskarta,dan jikinta sai rawa yake.
“Washhhh hannuna”ta faɗa ahankali tana mai runtse ido,dan sosai hannun ke mata mugun ciwo.
Ruwa baffa ya ɗebo mai sanyi wanda ya taru na sama,yana zuwa ya kwarawa gwogwgo ruwan cikin moɗa .aikuwa azabure ta tashi zaune tana ihu”wayyo Allah na maciji zai kasheni malam kawo ɗauki ,fattu tayiminn turen maciji,wayyo wuyana ,wayyo hannuna na shiga uku na lalace”abinda gwogwgo hansai ta farka dashi kenan,maimakon ambaton sunan Allah .
“Kayya hansai ki nutsu ba wani maciji ana fa nine bukar wannan kuma fattu ce ɗiyarki”cewar baffa kenan a ƙoƙarin sa na kwantar mata da hankali.buɗe ido gwogwgo tayi sosai ta kallesu kafin tace “kuturin bala’i Allah ya kiyaye wannan sheɗaniyar ta zama ƴata mayyace fa,wllh ture tayimin yanzun na wani maciji ya kusan hallakani,wllh sainaga bayan yarinyar nan Shegiya may…….wayyo Allah na ya dawo ya dawo”gwogwgo hansai ta faɗa sakamakon hango kan macijin nan da tayi ,ai da gudun gaske ta fice daga ɗakin tana ihu .
Girgiza kai baffa yayi yana Allah wadai da halin matar tasa ,sam baiyi dacen mata ba.kallon Fattu yayi wacce take riƙe da hannunta mai ciwon, hawaye na zuba a idanunta na azaba.
“Ashsha ashsha fattu kiyi haƙuri kinji,komai yayi farko zaiyo ƙarshe ,Allah yana sane da halin da kike ciki in sha Allahu zakiyi dariya anan gaba”baffa ya faɗa cikin sanyin murya da ƙoƙarin kwantar mata da hankali.
Ahankali ta sanya hannu ta share hawaye idanunta ,kafin tace “baffa hannu na ciwo yake min”ta faɗa tana nuna masa hannun dayake mata ciwon.
Kallon hannun yayi yanda ya kumbura yayi suntum dashi ,cikin tausaya wa yace “ayya faɗimatu sannu. Kinji maza daure kiyi sallah saina duba miki hannu kiyi haƙuri, Allah yayi miji albarka”ya faɗa yana mai taimaka mata ta miki tsaye.
“Ameen baffa “ta faɗa tana ficewa daga ɗakin .bayi ta shiga ta kama ruwa sannan tayi alwala cikin dabara kafin ta fito ta koma ɗakin ,Sallah tayi tare da karatun alƙur’ani mai girma ,da ka take karatun dan da ahaka aka koya mata ,bayan ta idar ne baffa ya shigo ɗakin ɗauke da kwarya ahannunsa ,
” Sannu fattu karɓi wannan madarar Kisha kinji,saina duba miki hannun”baffa ya faɗa yana miƙa mata kwaryar.karɓa tayi ahankali tayi Bismillah ta kafa kanta,saida ta shanye kafin ta ajiye kwaryar .
Allah Sarki fattu tasha wahala sosai lokacin da baffa ke gyara mata hannun ,dan yayi tsami sosai ,kuka harda majina,haka baffa ya gyara mata yana mata sannu.bayan ya gama gyara mata ne yace ta kwanta ta huta kafin garin ya gama wayewa.haka ta kwanta tana ajiyar zuciya ,ba jimawa kuwa barci yayi gaba da ita ,abinka da wanda bai sami barci ba dama.
Ficewa baffa yayi daga ɗakin ya nufi nashi cike da tausayin ƴar tashi dayake matuƙar ƙauna.
Ko minti talatin batayi ba tana barcin ta tsinkayo muryar gwogwgo tana kiranta “Ke gantalalliya mayya fito dan ubanki ,ko uwarki ce zata miki aikin?Shegiyar yarinya aljana wllh bakici bulusba yadda kika sa macijin nan ya lagartamin jiki to wllh saina rama ,fito ki ɗebomin ruwa yanzun nan .
Afirgice fattu ta tashi daga barcin ta fito da gudu tazo tana rawar jiki ,Dan bala’in tsoron gwogwgo take kamar ranta.”gwogwgo dame zan ɗebo ruwan “ta faɗa kanta asunkuye.
Da ubanki zaki ɗebo ruwan kinji ?kije ki nemomin kuɗin da zaki biyani bokatina inyaso ki ɗebomin ruwan aciki”gwogwgo ta faɗa tana daga ɗaki,dan taƙi fitowa waje kartaje macijin nan ko ajikin fattun yake.
Masu karatu har zuwa wannan lokacin fa yaran gwogwgo hansai suna kwance aɗaki suna barci.
Amma take ƙoƙarin tura fattu ɗiban ruwa da wannan safiya,alhalin bata da lafiya.dan lokacin da baffa ke gyara mata hannun tana jin ihunta.lokacin tana kwance akan gado tana hucin azabar da macijin nan ya gana mata,”Shegiyar yarinya Gara kemaki ɗandana azabar dana sha ,Allah yasa hannun ya karye ma kowa ya huta.
“Dan Allah gwogwgo kiyi haƙuri wllh bansan inda zan samo kuɗin ba kiyimin rai “fattu ta faɗa cikin kuka.
“Dan kan ubanki tashi ki ɓacemin da gani,wllh kome zakije kiyi bai dameni ba Indai zaki kawomin murtala uku da raina gomata.”ta faɗa tana rarumo wani busasshen kwanon tuwo aɗakin ta cillowa fattu shi.
Allah ne ya kare fattu da tuni kwanon ya sauƙa akanta ,tayi saurin ficewa da gudu daga gidan.
“Shegiya da kin tsaya ai”cewar gwogwgo tana mai kwanciya ba ko sallar safiya.
Koda fattu ta fita daga gidan kuka take sosai ,batasan inda zata nufa ba ,ina zata samo Murtala uku da Naira goma?waye zai bata waɗannan iyayen kuɗin? Kodai gurin jauro zataje tace ya taimaka mata da Murtala uku da Naira goman?kai a’a bazataje ba, dan jauro ba mutumin kirki bane ,ranar nan ma hannunta yake ƙoƙarin kamawa wai yana sonta,kuma baffa yace maiyin hakan ba mutumin kirki bane.
Kusan minti biyar tana saƙa da warwara,kafin ta yanke shawarar kawai ta tafi bakin rafin ta zauna ko Allah zai sa ta sami abun ɗiban ruwan.
Tafiya take ahankali ,wanda kallo ɗaya zaka mata kasan batajin daɗi,hannunta mai ciwon kuwa ta rikeshi da ɗayan hannun.haka ta nufi rafin dake can bayan gari cikin jeji.
“Hai jauro wai kuwa kaga Abinda nake gani”?
Cewar haroji kenan wanda suke zaune akan wata bishiya shida jauro can kusa da rafin da fattu ta nufa.
“Wanda aka kira da jauron ne ya ɗago kanshi dake duƙe yana zuƙar sigari yace “me ka gano mana”?
“Wllh fattu ce kuma ita kaɗai kaganta can ta nufi rafi”ya faɗa cikin ɗoki da zumuɗi.
Da sauri jauro ya kalli gurin da harojin ke nuna masa ,aikuwa fattu ya hango ,cikin hanzari ya fito daga kan bishiyar yace “wayyeee huuhuuu ,yau kam mun fito asa’a dan wllh saimun aikata mata ,wllh saina kusan cinye fattu yau “ya faɗa cikin murna da farin ciki yana mai bin hanyar da fattu ke tafiya,harta kusan ƙarasawa rafin.
Da sauri haroji yabiyo bayansa yana faɗin”ai wllh nima saina ɗana yau ɗinnan inka gama saika birmin siɗi”
Da sauri suke tafiya dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka cimma ta.kawai sai gani tayi sun sata atsakiya.
Kallonsu tayi cikin tsoro da fargaba,tace”meye hakan jauro ku bani hanya in wuce”ta faɗa cikin dakiya da nuna alamun bata tsoro su.
Dariya suka kyalkyale da ita ,kafin jauro yace “wllh fattu yau saina kusan shinyeki gaba ɗayanki Allah ne ya kawo mana ke dan haka maza kwanta “ya faɗa cikin jahilci da rashin imani.
Cikin tsoro da fargaba fattu ta fara ja baya tace”jauro me na maka zaka cinyeni?dan Allah kayi haƙuri wllh bana son mutuwa yanzu ina son ganin innarta”ta faɗa lokacin harta fara zubar da hawaye.
Dariya suka saka sakawa suna tafa hannu kafin haroji yace”jauro kawai kamata da shegen ƙarfi dan bazata kwanta ba ,kuma fa kamar bata san me kake nufi ba ” aikuwa jin haka sai jauro ya cakumo fattu yana faɗin aikuwa yanzu zata san me nake nufi ,yarinya kin cika kin batse amma ba mai amfana dake” nan da nan suka fara kokawa,yana ƙoƙarin Kaita ƙasa ,ita kuma tana Turkewa da ƙoƙarin kwatar kanta. kasancewarsa namiji tuni yaci ƙarfinta dan har ya Kaita ƙasa,ga ciwon hannu.
Daram ya zauna akan ruwan cikinta yana ƙoƙarin cire mata riga.dan tuni shikan ya cire wandonsa daga shi sai wata yar Shara ajikinsa banda wari ba abinda yake yi .haroji kuwa yana tsaye ya juya baya yana gane musu koda me tahowa.
Ihu fattu take cikin tsantsar tsoro da tashin hankali ,tayi mugun razana da ganin abinda jauro ke ƙoƙarin tura mata a bakinta yana fadin”maza Kisha fattu haka ake mana lagus sha maza kiji akwai daɗi”ya faɗa yana ƙoƙarin tura mata jauronsa abakinta wacce ganinta kaɗai ya mugun tsorata fattu.dan bata taɓa ganin wannan ƙaton abun mai numfashi haka ba sai yau.
“Wayyo Allah na shiga uku jauro menene wannan kake ƙoƙarin bani abakina ka bari bana so wayyo hannuna ,wayyo baffa zan mutu” ta faɗa tana wani irin kakkafewa jikinta na wani irin ɓari.
“Wllh yau ko zaki mutu fattu saina kusan cinyeki dan na jima da yunwarki araina, yau kuwa ba mai hanani yin…….wayyo Allah menene wannan haroji maza zoka taimakeni”jauro ya faɗa lokacin da yaji wani gibgegen abu ya fado kansa ya duƙunƙune shi sannan yasa baki ya cafke aliyarsa.
Ihu jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya daɗi can gefe guda……..
Masu karatu,menene wannan ya faɗowa jauro?
Me zai faru nan gaba?ku biyoni next page in Sha Allah,taku anty mammy
Mrs babi
Share and comment
Fisabilillah.
More comment
More typing.
Banda maza Please mata kawai .
By mammy kabeer
MACIJINE SHI 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers
Free book
Page 7/8
________________Ihu jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya faɗi can gefe yana burbura tare da rikan “wayyo haroji jaurota zai cinyemin ka taimakeni zan mutu wayyo maciji “ya ƙarasa faɗa da kyar sakamakon wata danƙa mai ƙarfi da macijin nan yayiwa jauronsa har saida numfashinsa ya ɗauke .
Haroji kuwa ya mugun tsorata ganin halin da jauro ke ciki,ga wannan ƙaton macijin daya kanannadeshi yana ƙoƙarin karya masa ƙasusuwa.
Cikin kiɗima ya rarumo wani ƙaton dutse yayi kan jauro da wannan macijin,yana zuwa baiyi wata wata ba ya ɗaga dutsen ya kwaɗawa macijin nan abayansa.
Aikuwa nan da nan bayan macijin ya fashe jini yayi tsartuwa har kan fuskar haroji,wani ihu haroji ya kwala ,sakamakon sauƙar jinin macijin nan akan fuskarsa ji yayi kamar an watsa masa ruwan batir,nan da nan gurin ya sale kamar wanda ya ƙone sai turiri gurin yake.
Jifa haroji yayi da dutsen hannunsa yana ihu yana faɗin”wayyo Allah idona bana gani wayyo kwayar idona ta zazzage na shiga ukuna “abinda yake daɗi kenan yana ihu da tsalle.
Shikuwa macijin nan silalewa yayi daga jikin jauro ya koma gefe guda tare da kwantar da kansa akasa ,dan kuwa sosai haroji ya kwada masa dutsen nan,kuma da alama ya shige shi .
Gaba ɗayan abinda ke faruwa akan idanun fattu ,tana kwance tana kallon ikon Allah,tabbas zuwa yanzu ta gama yarda cewa macijin nan bashi da biyar cutar da ita ,saima taimakon ta da yake,shin wanene wanan macijin?meye alaƙarta da shi?me yake nema agurinta?anya ma MACIJINE wannan ?kodai aljanine yake zuwa mata asiffar macijin? Wadanna sune tarin tambayoyin da fattu ke yiwa kanta tana daga kwancen wanda bata da amsarsu.
Saidai kuma gaba ɗaya hankalinta ya tashi ganin yadda macijin nan ya kwanta lamo kamar ya mutu.nan da nan tsoro ya mamaye zuciyarta ,cikin dauriya da jarumta ta yunƙura ta miƙe tsaye tana yamutse fuska,hannunta mai ciwon yana riƙe aɗaya mai lafiyar.
Gurin macijin ta nufa gabanta na ci gaba da faɗuwa,dan tsoro take kar ita kuma yayi mata wani abu.tana ƙara sawa ta durƙusa ahankali dai dai inda haroji ya buga masa wannan dutsen ,hannu ta sanya ahankali ,cikin karkarwa jiki ta ɗan shafa gurin ciwon.ai tana ɗora hannunta agurin macijin nan yayi wata irin juyowa tare da fasa kai kamar zai sareta, cikin tsoro da fargaba ta cire hannunta tare da matsawa baya da sauri tana zare ido tana kallon macijin.
Shima yana juyowa yaga fattu ce ,sai ya tsaya yana kallon ta,tare da komawa yadda yake ,wato ya sassauta fusatar da yayi ,kawai ya tsaya yana kallon ta.
Itama kallonsa take cikin tsoro da bugawar zuciya,ahankali macijin ya fara tahowa ,har ya zo gareta ,runtse idanu tayi tana karanta addu’ar Allah ya tsareta.
Ga mamakinta kawai saitaji macijin ya hau kan cinyarta ya kanannaɗe jikinsa ya dora kansa a saman gammon da yayi da jikinsa.
Ahankali ta buɗe idanunta tana kallonsa,shima ita yake kallo saidai idanunsa na zubar da hawaye kuma na jini .
Jikinta kawai rawa yake cike take da tsantsar tsoron abinda zai faru .juyawa tayi tana kallon haroji dake ta faman ihu yana yaɗuwa kasa.sannan ta kalli jauro wanda yake kwance ba alamun numfashi atare dashi,ga jauronsa nan tayi wani irin kumbura na ban mamaki sai jini ke zuba .
Tsorone ya ƙara kamata cikin azama ta yunƙura tare da mikewa tsaye, ture macijin tayi daga jikinta ta kwasa da gudu tayi gida tana kuka .
Koda taje gidan, da sanɗa tayi saurin shiga ɗakinta tana kuka,zama tayi akan tabarmarta tare da kife kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka.damuwace fal cikin ranta,wai meke shirin faruwa ne da rayuwarta?wacece mahaifiyarta?waye wannan macijin da yake ɗaukan hukunci akan duk wanda yayi nufin cutar da ita?tanasan sanin wannan macijin waye shi,kokuma waye ya aikoshi gareta.tana cikin kukanta ne kawai taji abu yana hawa jikinta silililili!!! Afirgice ta ɗago kanta tana kallon macijin daya gama hawa jikin nata. kansa ya ɗora akan wuyanta yana fidda wani irin huci ,shiru tayi tana sauraron yadda macijin ke huci,sanan jikinsa yayi wani irin zafi sosai.duk yadda akayi bashi da lafiya ,kuma dukan da haroji yayi masane solar hakan.
Tausayinsane taji yayi mugun kamata,ahankali cikin tsoro ta miƙa hannunta tare da riƙo saitin wuyansa ahankali ta janyoshi, ko motsi baiyi ba bare ya hanata abinda yake yi ɗin.
Akan tabarmar ta ɗorashi tare da ci gaba da kallonsa,cikin muryar kuka tace “bawan Allah kai waye?meke tafe dakai?waya aikoka zuwa gareni?meyasa kake ƙoƙarin daukar mataki akan duk wanda ya zalumceni?dan Allah karka cutar dani, bani da kowa sai baffana,dan Allah kayi tafiyarki ,idan mutanen garin na suka farga da kai zasu kasheka ,bazan so hakan ba dan Allah na roƙeka ka tafi”ta ƙarasa maganar tana haɗa hannunta cikin kuka.
Shidai macijin nan ko motsi baiyi ba sai huci da yake yi sosai,
Ahankali ta kalli gurin da yaji ciwo dazu sai taga gurin yana turiri kuma yayi wani fari fat.shiru tayi tana kallonshi ,yanzu ya zata yi masa ne?dan da alama fa yana jin jikine, data rasa abinyi kawai saita lulluba zanin sallarta ta fara karatun Alqur’ani mai girma.cikin abinda bai wuce sakwan biyar da fara karatunta ba kawai macijin nan ya fara wata irin murmurɗewa yana sauya kala, da farko yayi jajur dashi,sai kuma yazo yayi baƙiƙirin sosai ,wani irin hayaƙi na fita daga jikinsa .
Duk abinda yake sam fattu bata kulaba ,dan ta ɗaga kanta sama ne tana karatun ,kuma idanunta na zubda kwalla.
Shikuwa macijin nan burburwa ya ci gaba dayi yana murɗewa jikinsa na turiri tare da sauya kala.can kuma ya fara wani irin ƙara mai kama da gurnanin zaki.cikin tsoro fattu ta dawo da kanta ƙasa tana kallon macijin , sakamakon wannan sautin ƙara da taji yanayi.sai lokacin hankalinta ya kai kanshi taga abinda ke faruwa.
Tsorone ya kamata ƙarara “innalillahi wa’inna ilaihir raji’un”shikenan ta tabbata wannan ba maciji bane tabbas aljanine ,ko kuma aljanine ya shiga jiki sa,na shiga uku ni fattu ya zanyi da rayuwata?meke shirin faruwa dani” ta faɗa cikin muryar tsoro da shiga ruɗu.
Shikuwa macijin nan tana daina karatun saiya daina burburwar da wanann gurnanin,ahankali kuma jikinsa ya dawo yadda yake . Ya jima kwance lamo kafin ya fara motsi,kansa ya ɗago tare da fasa kan yana kallon fattu,gaba ɗaya idanunsa sun koma baƙiƙirin dasu sannan wasu irin ƙananan layoyi suka bayyana kusan guda uku aƙasan kanshi, sai wani irin motsi suke kamar ya’yan tsutsa.
Karkarwa jikin fattu keyi kamar an saka mata shokin, lamarin ya matukar bata tsoro ,meye wannan ɗin haka suka bayyana jikin macijin nan? Me yasa daga fara karatun Alqur’ani gaba daya ya sauya kama?tabbas akwai wani boyayyen al’amari game da wannan halittar dake gabanta,kuma zata ci gaba da bibiyar macijin nan sannu kan hankali har saita gano menene tattare dashi.
Tana nan maƙale jikin katangar karanta kamar ƙadangaruwa dan tsabar tsoro da shiga shock ,idanunta ƙuri akan macijin ,wanda shima ita yake kallo ,kusan minti biyar suna haka ,taga macijin ya sulale ya bar ɗakin ta wannan hanyar tashi.
Rarraba idanu ta farayi tana dafe da ƙirjinta ,yau kam tana ganin ikon Allah kala kala ,anya kuwa bata janyowa kanta masifa ba?waima meye alaƙarta da wannan halittar ne?ko dai baffanta zata sanarwa halin da ake ciki ne?kai a’a ba yanzu ba tukunna ,ya kamata ta zama jaruma tayi wanann aikin koba komai zata taimaki rayuwar macijin,dan ta fahimci akwai boyayyen al’amari atareda shi.
Su haroji kuwa gaba ɗaya ya fice daga hayyacinsa sai ihu yake yana faɗuwa ƙasa ,ahaka ya nufi gidan lamiɗon garin ,wanda shine mahaifin jauro ,yana ihu yana tumami, har yaje gaban lamiɗo ya faɗi yana “wayyo idanuna ,wayyo fuskata lamiɗo ka taimaka min.
Ruɗewa lamiɗo yayi wanda yake tsaye jikin wata sanuwa yana bata ciyawa, lamiɗo bashi da imani ,azalumine sosai ,kuma mutanen garin suna matuƙar tsoronsa, dan haka yake mulki na zalumci agarina,ganin halinda haroji yake ciki”kai haroji menene hakan ?ina jauro?me yasameka?sune tambayoyin da lamiɗo ya jerowa haroji
Cikin azabar ciwo da fitar hankali haroji yace “jauro ya mutu maciji ya cinye masa jauronsa yana bakin rafi”
Ai dajin wannan batu hankalin lamiɗo ya tashi ,nan da nan yayi kan haroji yana faɗin wane macijin ?me kake cewa ?jauro ya mutu?ƙaryane badai agarina ba ,ba wanda ya isa ya zo garina ya kashe min ɗana.”lamiɗo na gama faɗin haka ya kira mazan garin ,ya sanar dasu maza aje bakin rafi ataho da jauro.
Aikuwa cikin ƙanƙanin lokaci aka ɗauko shi kamar gawa .
Nan da nan lamiɗo ya nemi haroji ya sanar dasu abinda ya faru .
Nan ya sanar dasu iya abinda idanunsa suka gani,dan shima yana cikin mugun halin mutuwa ko rayuwa dan tuni gurin da jinin nan na macijin ya taɓa ajikinsa yayi wani irin kore shar yana zubar da wani yallow ɗin ruwa .
“Lamiɗo fattu ce ta Turo mana macijin nan ,shine ya kashe jauro”abinda haroji ya faɗa kenan ya sume.
Nan da nan mutanen gurin suka fara maganganu Suna faɗin da “da hansai ta faɗa tace mayyace yarinyar ,tunda har ta fara kashe mutane ba zasu yarda ba sai an hukunta itama.
Ran lamiɗo ya ɓaci sosai ,dan dama yana jin haushi yarinyar da ubanta,ya shirya neman aurenta amma sam taƙi yarda wai karatu take,yanzu kuwa dama tasameshi da zai hukunta su ita da tsohon nata.dan haka cikin bada umarni yace lallai lallai aje ataho da fattu da ubanta .
Nan da nan fusatattun maza suka nufi gidan malam bukar dan aiwatar da ƙudurin lamiɗo……..
Masu karatu meke shirin faruwa ne ?
Wane hukuncin lamiɗo zai zartar akansu fattu?
Mai zai far nan gaba?
Muje zuwa yaki ce dai anty mammy
Mrs babi
Share and comments fisabilillah.
More comments
More typing.
MACIJINE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers
Page 9/10
__________________Nan da nan fusatattun rugar suka nufi gidan malam bukar ,dan aiwatar da ƙudirin lamiɗo.
Allah Sarki fattu kuwa a wanann lokacin tana ɗakinta cikin jimami da tunanin abinda ta gani yau ɗin nan,haka nan ta tsinci kanta da son sanin menene wannan abubuwan dake motsi aƙasan wuyan maciji? wanda tun daɗewa bata taɓa ganinsu ba sai yau,waya sani ma ko wani akayiwa asiri ajikin macijin ?tabbas zatayi iya ƙoƙarin ta dan ganin ta raba macijin nan da wannan abubuwan ,ta yadda koda wani aka yiwa asiri ta hanyar macijin, to asirin zai karye .sannan tana fargabar gwogwgo ta gano cewar tana gidan kuma bata ɗebo ruwan ba.kuma ahalin da ake ciki yanzu bazata iya komawa rafin nan ba ,.dan ta tsorata dasu jauro .
Hayaniyar mutane ce ta cika gidan nasu fattu ,wanda haka yasa gwogwgo hansai fitowa dole badan ta soba, Dan har lokacin nan ita da yaranta ba wanda yayi sallar asuba.
“Kai su waye haka suka zo suka cika mana gida da ihu kamar ana yaƙi?”cewar gwogwgo hansai tana gyara daurin ƙirjinta dake ƙoƙarin kuncewa bayan ta fito daga ɗakin.
“Aa meye hakan arɗo ?lafiya na Ganku da yawanku kun shigo?ta tambaya lokacin da idanunta ya sauka akan mutanen da suka cika gidan,kusan duk mazan garin ne.
Cikin masifa wanda aka kira da arɗo yace “wllh yau saimun ɗauki mataki akan bukar da fattu ,haka kawai yarinya ta fara kashe mutane ,kuma ta rasa ta kan wa zata fara sai ɗan gidan lamiɗo ?wllh yau sai mun kashe Shegiyar yarinyar nan”ya faɗa yana wani zazzaro idanu kamar zararre.
Eh wllh afito mana da ita kawai mukaita gurin lamiɗo ya bamu izini mu kashe mayya.gaba ɗayan mutanen gurin suka faɗi haka cikin nuna fusata da ƙosawa abasu fattun .
Wani irin farin ciki da jin daɗine ya kama gwogwgo hansai ,shikenan zata rabu da alaƙaƙai cikin sauƙi Allah yasa akasheta kowa ya huta ,dama su haɗa da bukar ɗin da yake ɗaurewa fattu gindi ,koba komai shanunsa sun zama nata.gwogwgo hansai ta faɗa cikin ranta.kafin ta kalli arɗo da sauran mutanen tace “aikuwa idan aka kasheta an kyauta ,dan nima nan wllh so take ta cinyeni nida yarana, jiya da kyar mukasha data maƙuremin wuya wai saita cinyeni, ku ɗan jira kaɗan yanzu zaku ganta shegiya gantalalliya,banma san inda ta tafiba, dama haka takeyi kullum inta fice yawon iskanci bata dawowa da wuri,tana can gurin maza”gwogwgo hansai ta ƙarasa maganarta tana mai buga hannu acinya.
“Aikuwa yanzu zamuje mu nemota ko ina ta shiga,wasu sutafi bakin rafin wasu sushiga jeji, mukuma zamu jira ana “cewar arɗo kenan yana kafe sandarsa akasa,sannan ya gyara tsayuwarsa.
Duk wannan abunda ke faruwa akan kunnen fattu, tana jin komai ,saidai tashin hankali,firgici tsoro da kuma ruɗewa sun hanata koda yin kwakwkwaran motsine .
Numfashinta ma da ƙyar yake fita tsabar ruɗewa.
Ta shiga uku !shikenan yanzu kasheta za’ayi?laifin me tayi da za’a kasheta?me baffanta yayi ake nemansa shima? Dama jauron mutuwa yayi ? innalillahi !!!yanzu ya zatayi.
Wani kukane ya kubce mata cikin sauri ta toshe bakinta tana kuka sosai kamar ranta zai fita,ji take dama tana da ikon ɓacewa, tabbas da ba abinda zai hanata ɓacewa ta bar duniyar ma gaba ɗaya.
Ahankali ta miƙe cikin sanɗa ta leƙo da kanta ,ba ƙaramin tsoro tajiba lokacin da taga mutanen da suka zo tafiya da ita.shikena kawai ta mutu,yanzu shikenan bazata cika burinta na ganin innarta ba?wayyo “Allah ka kawomin ɗauki “ta faɗa cikin raunananiyar muryarta mai cike da tsantsar tsoro.
Ahankali ta ƙara leƙo da kanta waje ,cikin rashin Sa’a kuwa sukayi ido huɗu da dan gidan gwogwgo hansai umaru.wanda hayaniyar mutane tasa suma suka farka.
“Laaaah aradu gwogwgo ga fattun can cikin ɗakinta tana leƙowa”ya faɗa yana nuna ɗakin da Fattu ke ciki
.cikin hanzari fattu ta koma cikin ɗakin tana mai runtse idonta ,tare da dafe ƙirjinta.”shikenan sun ganni wayyo Allah na baffa,wayyo MACIJINA kana ina kazo ka taimakeni zasu kasheni wayyo ni fattu”fattu ta faɗa tana mai leƙa hanyar nan da macijin Kebi idan zai bar ɗakin nata inya zo kamar Zariya haka take bankada hanyar macijin da hannunta.
“Munafuka ,mayya dama kina ji ana neman ki shine kika ɓuya nan?to fito yau dubunki ta cika ,mutuwa zakiyi wllh saikin bar duniyar nan yau nima na huta da ganinki ,maza arɗo zoka tafi ta ita gata nan”gwogwgo hansai ke faɗin wannan maganar tana daga bakin ƙofar dakin Fattu,dan tun lokacin nan da tasha matsa agurin maciji bata ƙara shiga ɗakin Fattun ba.
Aikuwa kafin ta rufe baki su arɗo sukayo kan Fattu suna janta.
“Wayyo Allah gwogwgo karki bari su tafi dani zasu kasheni ,wllh ban aikata komai ba wayyo Allah na gwogwgo ki taimaka min”abinda Fattu ke faɗi kenan tana miƙawa gwogwgo hannu cikin kuka mai tsanani.
“Ai wllh dana taimakeki gara hannuna ya karye Shegiyar yarinya ,kutafi da ita can ku kashe banza” gwogwgo ta faɗa tana kaɗa hannu irin yadda ake korar kaji ,cikin farin ciki take maganar.
Ihu Fattu keyi tana kuka,amma haka suke janta kamar akuya aƙasa, suna cikin tafiya ne ,saiga baffa aguje yazo gabansuu ya tsaya riƙe da sanda yana ta haki,dan yana can bayan gari ya sami labarin abinda ke faruwa acikin garin da gidansa,shine ya rugo yazo .
Aikuwa Fattu na ganin baffa ta ƙara fasa ihu tana cewa” wayyo baffana ka taimakeni zasu kasheni” ta faɗa tana miƙa masa hannu,abin tausayi dukta susuce tayi buju buju da jiƙaƙkiyar ƙasa.kallonta baffa yayi
Cikin bacin rai mai tsanani ya ce.
“Sakarmin yarinya arɗo, kona rotsa maka sandar nan akanka” baffa ya faɗa cikin hargowa da ƙaraji,
Kasancewar baffa kowa ya sanshi arugar mutumin kirki ne ,sam ba ruwansa da shiga harkar wani,sanan kuma shine ke ja musu jam’i ,hakan yasa suke ɗan ganin girma da mutuncinsa, dan haka cikin Turo baki da hura hanci arɗo yasaki hannun Fattu wanda ke mata azabar ciwo da raɗaɗi,yana mai cewa”ato lamiɗo ne dai yace mu taho daku,dan haka ya zama dole ayiwa lamiɗo biyayya”ya faɗa yana hararar gefensa, dan yaji haushin sakin wannan hannun na Fattu mai shegen laushi da daɗin taɓawa da baffa yasa yayi.lol
Fattu kuwa yana sakar mata hannu ,da rarrafe ta ƙara so gurin baffa ta rirriƙe shi tana kuka da faɗin”wllh baffa ba abinda na aikata,ban kashe jauro ba ” ta faɗa cikin matsanancin kuka da tsoro, jikin ta sai rawa yake.
Riƙota baffa yayi cikin tausayawa yace “na sani Fattuna,baki kashe jauro ba ,kuma ba wanda zai kasheki, Allah na tare dake kinji”?ya faɗa cikin sigar rarashi,sannan ya kalli arɗo yace”kai arɗo ka kiyayeni ,karka ƙara ƙoƙarin sake aikata irin wannan dabbacin akan ƴata, saboda baka da hankali shine zaka rinƙa janta aƙasa. Kamar wata dabba ?jahilan banza jahilin hofi,muje gurin mai garin zanji idan shiyasaka wannan ɗanyen aikin”baffa ya faɗa cikin mugun bacin rai yana mai riƙe Fattu suka nufi faɗa.
Lamiɗo na hangosu ya fara lasar baki ya kure fattu da idanu kamar maye , yana kissima abubuwa da dama cikin ransa….
Manage please yau ina busy,Dan banyi niyar typing bama yau wllh.
Masu karatu me lamiɗo ke nufine shima?
Hmmmmmm kubiyoni mu hade bayan sallah danjin yadda zata kaya.
Kafin nan ina mana fatan yin salla lafiya,sannan aci Nama ahankali kar azo ana …….
Taku anty mammy
Mrs babi,
MACIJINE 🪱🪱🪱
Na mammy kabeer
(Anty mammy)
Elegant online writers
Free book
Page 11/12
Ta ƙabbalallahu Minna waninkum.
Slm, ƴan uwa masoyan littafin MACIJINE, ina miƙo gaisuwa tare da Barka da Sallah ,Allah ya maimaita mana,yasa munyi karɓaɓɓiyar
Ibada.
________________Kai tsaye su baffa suka nufi gurin lamiɗo,hannunsa riƙe da na fattu ,wacce ke tafiya ahankali cikin azabar raɗaɗin da hannunta keyi,dakuma ciwon jiki.yayinda su arɗo ke mara musu baya burinsu kawai suga wane irin hukunci lamiɗo zai ɗauka akansu fattu ,cikin zuciyarsa arɗo yake fatan inama lamiɗo ya kori su fattu daga rugar ,inyaso su bisu hanya suyiwa fattun fyaɗe,dan su kashe ƙishirwarta dake cin ransu.
Shikuwa mai gari tun daga nesa ya hango su fattu,gaba ɗaya nutsuwarsa ta bar jikinsa,ƙureta yayi da ido guri!!yana haɗiyar yawu da lasar leɓe kamar tsohon maye.
Kallonta yake yana ji kamar yaje ya kamota yayi ɗaka da ita.
haba malam ,yarinya bul-bul da ita kamar nunannen tumatur,lallai yau zai sha shagali.lamiɗo ya faɗa cikin ransa yana mai kallon fattun.
Baffa kuwa suna ƙarasowa gaban mai gari ya nemi guri ya zauna tare da zaunar da fattu kusa dashi,wacce gaba ɗaya arikice take ,tsorone ƙarara shinfiɗe akan fuskarta.tayi luƙus ajikin baffanta jikinta sai rawa yake, ta kasa ɗaga kanta ta kalli kowa ,sai hawaye take sharewa.
Kowa yanemi guri ya zauna ,masu tsayuwa suka tsaya , da ƙyar lamiɗo ya iya saita kansa ya aro nutsuwa ya yaɓa akansa, tare da ɓata ransa ya kalli baffa yace “malam bukar kana sane da irin abinda ƴarka take aikatawa awannan garin ?lamiɗo ya faɗa cikin kakkausar murya .
Ahankali baffa ya gyara zama kafin yace ,naji anata wai wai agari cewar ƴata tayiwa su jauro turen maciji ,amma sam ban yarda da wannan magana ba,dan kuwa ƴata ba mai kashe mutane bace ,sannan ba mayya bace kamar yadda ake faɗa”baffa ya faɗa cikin ɗaure fuska .
Cike da ɓaci rai lamiɗo ya fara magana.
“To wllh malam bukar bazan ɗauki wannan abun agarina ba,yanzu ace abun nata ya wuce kan kowa sai kan ɗana ?sannan kuma kace wai baka
yarda da zancen ba ?kana nufin nayi maka ƙarya ne?to bari kaji dole ne saina ɗauki mataki mai ƙarfi akanka da ƴar taka ,dan ka nuna rashin ɗa’a a gaban fada.bayan kuma kowa yaga abinda ƴarka tayiwa yaranmu,
Dan haka bazan yanke hukunci yanzuba sai zuwa gobe ,idan yaranmu sun sami lafiya,dan haka yanzu za’a shiga da ita cikin gida anan zata zauna cikin wancan bukkar da ake ajiye masu laifi .
Dan haka kowa ya watse sai zuwa gobe da la’asar adawo nan dan jin hukuncin da zan yanke”mai gari yana gama faɗin haka ya jingina da jikin kujerar da yake zaune akai.
gaba ɗayan mutanen dake gurin sunyi na’am da wannan hukuncin nacewar fattu ta zauna a gidan mai gari ,dan karta gudu.
Kuka sosai fattu ta sanya tana riƙe hannun baffa “wayyo Allah na baffa ka taimakeni,dan Allah karka bari akulleni adakin hukunci ,wllh bani nayi musu haka ba ,kuma sunzone da nufin keta min haddi baffa ka kalli Yadda ya famamin targaɗe na wllh ba laifi na bane” fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka kamar zata shiɗe.
Cikin tashin hankali baffa ya riƙe hannun Fattu ,ji yake kamar ya fasa ihu,aduniya ba abinda ya tsana irin yaga Fattu cikin damuwa,”kiyi haƙuri fattu ba abinda zai sameki,in Sha Allahu Allah zai saka mana dan wannan mugunta ce ake son yi mana ,kuma Allah yana bayan mai gaskiya”yana gama faɗin haka ya juya gurin mai gari yace “lamiɗo ina neman alfarmar abarmin fattu mu tafi gida ,zamu dawo da ita zuwa goben,dan bata da lafiya kuma barinta ita kaɗai akwai matsala” ya faɗa cikin damuwa da alhinin wannan rashin adalci da ake ƙoƙarin aiwatar musu.
Cike da mugunta lamiɗo yace “kai bukar ina ganin girmanka karkasa in daina gani ka iya bakinka a faɗa kake,kasan idan na riga yanke hukunci ba mai ja dani ,dan haka ka tashi ka bani guri tun kafin raina ya gama ɓaci kuma yanzu zansa aje anemomin macijin duk inda ya shiga daga nan zuwa safiya ,”lamiɗo ya faɗa yana mai kiran wasu matasa yace su shigar da fattu cikin bukkar.
Kuka fattu keyi tana faɗin”wayyo baffana wayyo Allah ka taimakamin zasu tafi dani wayyo Baffa na karka bari su nemo shi zasu kasheshi. “amma haka suka tura ƙeyarta suka tafi da ita ɗakin hukunci.baffa yana ji yana gani ,hawayene masu zafi suka silalo daga idon bawan Allah ,zuciyarsa kamar ta faso ƙirjinsa yakeji, ashe ma ƙoƙarin keta masa haddin ƴa akayi?amma saboda rashin imani da adalci aka ɗora mata sharri,ba komai Allah zai saka musu.
Juyawa yayi ya nufi gida ransa amatukar jagule,yanzu idan wani abun ya sami yarinyar fa?idan wasu suka ƙara yunƙurin cutar da rayuwarta fa?”ya Allah ka karemin yarinyar nan Allah ka duba matsalolin dake kanta da wanda suke shirin samunta.ya Allah ka sauƙaƙa mata ƙalubalen dake gabanta.haka yayi ta mata addu’a harya ƙarasa gida kwata kwata hankalinsa baya jikinsa.
Yana shiga gidan gwogwgo hansai ta sanya dariya cike da mugunta harda riƙe ciki tana nuna baffa da hannu.”wllh malam Gara ka cire wannan yarinyar daga zuciyarka, inba haka ba kana tsaye zaka yanke jiki ka faɗi ka mutu.ba ruwa na bani da asara, ai wllh banso lamiɗo ya kyaleta wai har sai gobe ba,daya sani yasa anyanke mata kai yau -yau ɗin nan ,da mun huta da nauyinta akanmu” ta faɗa tana turo wani baƙin ɗan kwalinta mai shegen datti zuwa gaban goshinta.
Kallon ta kawai baffa keyi ,cikin zuciyarsa yake kissima iri saɓawa gwogwgo da zaiyi dan yau zai nuna mata matsayin fattu azuciyarsa ,sai dai yana yunƙurowa da nufin maida mata martani,kawai yaji bakinsa yayi nauyi,wani irin shayinta da tsoro ya mamaye zuciyarsa.kai kawai ya girgiza ya wuce ɗakinsa ,wato itama gidan mai garin taje kenan?ba komai akwai Allah.
Fattu kuwa tunda aka turata cikin ɗakin nan banda kuka ba abinda takeyi, ita damuwarta ma yanzu bai wuce na rashin ganin macijinta ba,duk wannan abunda ke faruwa baizo ba.anya kuwa lafiya?kodai wani abu ya sameshi ne?
“Ya Allah ka kare wannan bawan naka ,ka bashi kariya daga sharrin mugayen mutane .
Shikuwa maciji adaidai wannan lokacin yana gidansu fattu yaje nemanta bai ganta ba yayi ta zagaye aɗakinta amma bata nan,tun lokacin datayi masa karatun nan daya fita yaje can jeji ya kwanta ,sam bayajin daɗin jikinsa sosai yake jin ciwo ta ko’ina ajikinsa,sai da lokaci yaja sannan ya nufi gidansu fattu ,ahankali yake tafiya cikin ciyawa da jikin katanga, harya ƙarasa gidansu fattu.
Koda yaje yaga bata nan saiya yi ta zagaye ɗakin yana nemanta ,amma bata nan. Kwanciya yayi akan ɗaurin kayanta yayi lamo kamar ya mutu.saidai hawayene ke zuba cikin idanunsa .
Can kuwa gidan mai gari ,da misalin ƙarfe bakwai na dare sosai hadari ya haɗu agarin, dan haka kowa ya shige cikin gida dan gudun zubowar ruwan,da akowane lokaci yana iya sauƙa.
Daidai wannan lokacin kuma fattu na duƙunƙune cikin ɗakin hukunci sai kuka take zuciyarta tayi mata ƙunci ga yunwa dake addabar ta rabo ta da abinci tun madarar da baffa ya bata da safe.hannunta sai zagi yake mata.
Ahankali taji ana turo kofar ɗakin hukuncin,da alama shigowa za’ayi,ga duhu aɗakin.
Zabura tayi cikin sauri ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa,kar dai ace su jaurone suka dawo ?wayyo Allah na ” ta faɗa tana dafe ƙirjinta ,zuciyarta kamar zata fito dan tsoro da firgici.
Cikin rawar murya tace “wa…w….ayee.”
Ahankali cikin murya mai kama da raɗa,yace “ke kwantar da hankalinki,nine nan lamiɗo”
Ya faɗa yana mai haska tocilan ɗinsa .
Cikin zubar da hawaye tace “dan Allah lamiɗo ka fitar dani daga gurin nan ,wllh ban aikata komai ba,bani na kashe jauro ba”ta faɗa cikin kuka.
“Kinga ki nutsu jauro bai mutu ba yana raye ,kuma idan kika bani haɗin kai muka yi komai cikin sirri ,to zan kyale ki ki tafi gida abinki”lamiɗo ya faɗa yana matsowa gareta.
Ja tayi da baya cikin sauri tace “me kake so nayi maka ?dan Allah ka gyaleni na tafi gida ,an fara ruwa”ta faɗa cikin kuka,dan ta gano manufarsa ,irin tasu jauro ce ,wato fyaɗe yake son yi mata.
Matsowa lamiɗo yayi tare da ruƙo hannunta yana mai cewa”Ayya fattu yarinya mai kyau da kyan jiki ki yarda dani mana duka -duka minti nawa ne ba dayawa zanyi ba kinji ki taimaka min”ya faɗa yana mai janyota jikinsa sosai .
“Wayyo Allah na baffa kazo ka taimakeni,dan Allah lamiɗo kayi haƙuri wllh ba kyau kaji tsoron Allah ka tausaya min na roƙeka”fattu ta faɗa cikin rawar jiki da matsanancin kuka,tana mai tureshi daga jikinta,banda warin tsufa ba abinda yake yi.
“Ke dan ubanki ki tsaya ko saina miki ta ƙarfine?Shegiyar yarinya haka zamu zuba miki ido muna kallonki kin cika kinyi tunjum dake amma ba mai morarki,ki tsaya dan ubanki”lamiɗo ya faɗa yana mai ɗauke fattu da wani gigitaccen mari Wanda saida ji da ganinta suka tsaya na wucin gadi.kusan minti biyu kafin kwakwalwar ta ta dawo aiki,kuka ta sake fashewa dashi mai tsananin gaske lokacin da lamiɗon ya Kaita ƙasa yana ƙoƙarin dage yar ficiciyar rigar dake jikinta ,wacce jiƙaƙƙiyar ƙasar nan ta gama bushewa .
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un wayyo Allah na baffa wayyo mai taimako kana ina?kazo gareni,ina buƙatar taimako ka ahhhhhhhh “fattu ta kwalla wani irin ƙara mai ƙarfi lokacin da lamiɗo yayi………
Tofa masu karatu me lamiɗo yayiwa fattu ne ?
Muje zuwa kuci gaba da bin alƙalamin anty mammy.
Mrs babi
Share and comment fisabilillah
More comment
More typing.
Name: | [MACIJI NE SHI HAUSA NOVEL] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | June, 2022 |

Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe

Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram

Woohh shi in good
WOW
Gaskiya dazun nakeji labarin littafinnan yayi dadi saidai ba’ayin post sosai dan allah akaqara yawansa mungode allah ya qara basira
gaskiya novel din nam zaiyi dadi
Wow
WOW I LIKE THEM
Wow
Thanks
Wow
Wow
Wow
Wow
Allah yqara basira ameen
Thanks
Masha allah dan allah ina son cigaba daga page 35
Wow yayiii dadiii over pls aciii gaba
Allah yakara basira ameen
MAsha Allah
waw fattu
WOW
Wow
Wow tnx
Wow fattu
Nice
Mun gode Allah yakarabasira novel yayi dadi
Dan allah a bani cigaban macijine shi
Dan allah acigaba
A gaskiya yamin dadi sosai
THANKS
Yayi dadi mungode
So sweet
Muna
godiya sosai
Thanks
Mungode sosai dazu naji lbrn sa yayi dadi matuka
Muna godiya acigaba
Masha allah pls acigaba
tnx
Dan allah akarasamana page 2
Allah kara basira yayi dadi acigaba.
dan allah acigaba mungode
Yayi so sai wlh, Allah ya Kara basira da hazaqa,Kuma Dan Allah ya za’ayi na samu wannan book din complete din da,,,,nagode
Gaky yayi dadi daga page nawa aka tsaya yanxu nide nawa 41/42 ne dan Allah atura mana sauran
Thanks
Wow very pretty
Good
Tnx Muna gdy ssae…
It’s so intteresting
Nice book Amman xan iya samin complete dinsa pls
Dan allah a tura mana page 47-48
mmn khairat mungdy na 12_20 dn allah
Tnx dan allah a ci gaba
Dan allah akawo mana 13and14
Wow wllh yy dadi pleass next 12/20
Muna godiya littafi yayi dadi,amma akara yawan posting pls
Mungode sosai
Anty mammy mungode allah yakara basira da ha zaka ina son cigaban macijine shi daga kan na sha biyu zuwa yanda aka tsaya please mun gode
Naji dadin littafin nan
Tnx gsky littafin nan yamin dadi
Thank’s
Gsky yahadu a cigaba
Mungode acigaba
Yayi Allah yabiya
Wow so mashaallah
We need more
Dan allah aciga da posting yayi dadi
Nice novel Don Allah a turomana complete
Mungode sosai Allah yaqara basira
Dan allah turumin da 19 20
Allah littafin yayi dadi sosai dan allah a turamana page 19/30
i like them
Thanks
Thanks
Wlh novel din yayi Dadi. Yaushe za’a sako next page din?
gaskiya littafinnan yai dadi
gaskiya littafinnan yai dadi
Yayi dadi wllh next page pls
Dan Allah ina buqatar complete
Nice
Masha allah
Mungode Allah yakara basira
Tanx
I like this novel pls continues
I like this novel pls continues
Allah yakara basira yakuma kara daukakaki mungode sosai aunty
Allah yakara basira mungode sosai aunty