Madubin Gobe Hausa Novel Complete

Madubin Gobe Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: MADUBIN GOBE

 

Page 1

Na Pharty BB

Free Book

 

“Nuratu! Nuratu?” Hajiya Sadiya da take zaune bakin katifar Æ´arta tana Æ™iran sunanta, lokaci É—aya tare da yaye abin da ta rufe jikinta dashi.

Motsi tayi har lokacin bata buÉ—e ido ba.

“Mami da sauran lokacin shan maganin, don Allah ki bar ni inyi bacci kaÉ—an, yanzu zan farka.”

“Ki tashi kisha ko in É“ata miki rai, tun É—azu nake faman tashinki kin Æ™i ji.”

Yaye abin da ta rufe jikinta Nuratu ta yi, ta tashi ta zauna, tana mutsetstseke ido ta ce.

“Yanzu Mami bazan taÉ“a kwana na wuni ban sha magani ba, shikenan rayuwata haka za ta Æ™are.”

Sauyin yanayi da ta gani a fuskar mahaifiyarta ya sakata yin shuru, ta karɓi maganin hannunta da ruwa.

“Komai zai wuce Nuratu. Ƙaddarar mu gaba É—aya kenan ba ke É—aya ba. In sha Allah watarana za ki kwana ki wuni ba ki sha magani ba da yardar Allah. Ko kin manta me Dr Awwab ya faÉ—a.”

Girgiza kai Nuratu ta yi lokacin da ta saka ruwa a bakinta don kora maganin. Haka kullum ake faɗa mata cewa komai zai wuce amma ba ta taɓa kwana ta wuni abun da ya wuce bai faɗo mata a rai ba.

“To kina tuna hakan. Maza ki tashi ki shirya makaranta, ke wasu in sun kusa fara final exam basa bacci basa zama amma ke banda bacci baki da aiki.”

“Ba ni da lecture ne ai, duk anyi closing, test ake yi.”

Tashi Mami tayi ganin tasha maganin ta fice ta barta. Ganin haka ya saka Nuratu komawa ta kwanta. Tunanin rayuwarta ta shiga yi, ganin abun zai ɓata mata rai don har kanta ya fara ɗaukar zafi ta miƙe da sauri tana shiga bathroom.

Wanka tayi ta fito ta saka riga da skirt na lace É—inta tare da mayafinta babba, za ka rantse matar aurece don yadda ta rufe jikinta ruf da shi. Ba tayi wani kwalliya ba ta É—auki wayarta da jakarta na makaranta ta fita.

A falo ta samu mahaifiyarta zaune tana kallon huÉ—ubar Jumma’ah, gefenta yarinya dake taimaka mata tana gugan kayanta.

“Mami zan leÆ™a makaranta, daga nan zan biya gidan Aunti Rahma?”

“To kar ki jima dai, banda shiga hayaniya. Ki gaisheta.”

“Za taji.”

Nuratu tace tana É—aukar mukullin motar Mami ta fice dashi da sauri.

“Ki dawo min da mukullin nan.”

Mami tace da karfi, jin ba zata dawo ba ya sa ta cewa.

“Kiyi tuÆ™i a hankali.”

Murmushi kawai Nuratu tayi da tsakanin Mami da Æ´an uwanta take yi, sai wanda ta basu muhimmanci a rayuwarta suke ganin murmushinta, shekarun baya har ta mance menene murmushi balle dariya.

Makaranta taje ta sama an manna time table, ganin babu wani abun ya sata fita ta nufi gidan yayarta Aunti Rahma. A waje tayi parking É—in motar ta shiga.

Sallama tayi kofar falonta kafin ta shiga, Rahma dake cikin ɗaki tana hutawa bayan sallamar ƴaƴan ta sun wuce makarantar taji muryar ƙanwarta da sauri ta fito tana murmushi.

“Ashe dagaske za kizo.”

“Kin san dai bana Æ™arya.”

Nuratu tace yayin da take zama saman kujera. Zama ita ma Rahma tayi suka gaisa tana tambayarta Mami ita kuma tana tambayarta sauran Yayunta da É—anta Khair da yayunsa.

See also  Karuwar Miji Na Complete Hausa Novel

Ruwa ta kawo mata da abinci, Nuratu ta girgiza kai.

“Nayi breakfast tun 7, Mami bata yarda ta barni da yunwa.”

“Hakane autar Mami. Amma kuwa sai kinci abincin gidana”

Rahma tace tana haɗa rai ganin haka ya saka Nuratu cin kaɗan ta bari. Suka hau hira dan sun kwana biyu basu haɗu ba. Su biyun in ka cire Aunti Hasiya mai bin Aunti Rahma da Rukayya wacce Nuratu take bi sun fi shiri, ko dan ta kasance ita ce babba ita ƙarama.

Sai wajen ƙarfe ɗaya Nuratu ta fara shirin tafiya bayan ta taimaka Aunti Rahma da abincin rana ta mata sallama.

Gida ta nufa ta samu Mami bata falon cikin sanɗa zata wuce ɗakinta taji Mami ta ƙirata.

Juyawa tayi tana sosa ƙeyarta.

“Sorry Mami.”

“Kinsan dai lokacin shan maganin ki ya kusa wucewa amma ki kayi zamanki. Na Æ™iraku dukkan ku ke da yayarkin ba wanda ya É—auka.”

“Kiyi hakuri Mami. Muna aikine ba mu ji ba. Magani kuma yanzu zan sha.”

“Lafiyar ki nake nema miki Nuratu, kin fini buÆ™atar hakan sanin kan ki ne.”

Shuru Nuratu tayi cikin sanyin jiki. Gaskiyar Mami, ta fita buÆ™atar lafiya duba da abubuwan da suka faru a rayuwarta. ƘoÆ™arin ta kullum ta ganta tana walwala da farin ciki tamkar sauran al’umma. Wani lokaci ko tasha maganin in ta fara tunanin abin da ya wuce, ko yazo mata kanta, ko tayi tozali da makamancin shi zata wuni tamkar bata sha magani ba domin ciwon zai nuna alamu zai tashi, sai dai Mami tana bakin Æ™oÆ™arinta ganin ta kawar mata shi a ranta walwalarta ya dawo.

“Kiyi hakuri Mami.”

Nuratu tace ganin Mami ta nufi É—akinta.

“Ya wuce.”

Ta bata amsa dashi ta shige É—aki ta barta.

Tana son ƴartan duk cikin ƴaƴanta. Su biyar ta haifa amma duk ciki tafi sabo da ita sun fi shaƙuwa. Ko dan a gabanta ta taso ita ɗin. Abubuwan da suka faru a rayuwarta ita da Nuratu Ƙaddarar suce da Allah ya rubutu musu ba daman kaucewa. Ita ƙaddara rubutacciyar shafine a rayuwar ko wani bawa da baya tsallakewa.

Tare suka sha wahalar su duk da sauran yaran sun tausaya musu halin da suka shiga a shekarun baya haka ma mahaifinsu da ba tayi tsammanin haka daga gare shi ba. Amma daga baya komai ya ƙara lalacewa yaci gaba da tafiya kamar da.

Tana son Nuratu tana tausayin ta kuma tana bata taimako dai-dai gwargwado da zata iya bata a matsayin ta na mahaifiyar ta.

Karin wasu littafai da zaku so

11/03/1996.

DAMATURU, YOBE STATE.

Sallamar da mai gidanta yake kwalawa shi ya sata fitowa da sauri a É—akinta. Zaune ta same shi a falo ya kurawa talabijin idanu.

“Sannu da zuwa.”

Sadiya tace yayin da take zama kusa dashi sai lokacin ya farga daga tunanin da yake ya kalleta bai ce komai ba.

“Lafiya Abban Rahma?”

Shine tambayar data mishi ya kawar da idanuwanshi daga kanta yana girgiza kansa.

“Ba lafiya, amma komai allahamdulillahi.”

“Ba lafiya? Ko dai bamu samu matsayin da muke nema bane?”

Ta faÉ—i hakan dan son sanin abinda ke faruwa.

“Ban samu ba Sadiya, sai dai fatan muyi addu’a Allah bamu Sa’a wani shekaran.”

See also  Kuruciya Hausa Novel Complete

Cikin sanyin jiki tace.

“Ameen.’

Dan tasan yadda mijinta yaci burin samun babban matsayi a wajen aikinsa.

Maganar mijinta Alhaji Mamman Bashir shi ya sata dubanshi.

“Mai aka ce miki a asibitin?”

Murmushi tayi kamar mai jin kunya tace.

“Juna biyu ne kamar yadda kake zargi.”

Murmushi yayi dan yana son Æ´aÆ´a. Jin ciki jikin matarshi ya ji damuwarshi ta kau yace.

“Allahamdulillahi Allah raba lafiya. Amma zaki yaye Rukayya ko?”

“A’a, da na sanar dasu in nayi yaye in na samu ciki yaran suna jinya sai suka ce this time kar nayi yayen sai na kusa haihuwa.”

“To hakan yayi. Allah kaimu lokacin.”

Ameen! Ta amsa dashi suka taɓa hira wajen sha biyu yace zai leƙa wajen kasuwancin shi ba zai jima ba zai dawo.

Alhaji Mamman Bashir.

Ɗa na ƙarshe wajen iyayen shi. Su shida suka haifa mata huɗu maza huɗu, maza biyu sun rasu saura su huɗu. Mahaifinsu ya jima da rasuwa amma da wayonsu sai mahaifiyar su da itama bata fi wata da rasuwa ba. Duk sunyi aure da ƴaƴansu. Ɗan asalin fulanin Gombe mazauna Gombe. Sunyi karatun boko da islama ba laifi.

Alhaji Mamman Bashir ya karanci harkar kasuwanci in da ya kammala karatun shi bai samu aiki ba kuÉ—in gadonshi ya fara sana’a dashi Allah ya sawa kasuwan albarka ya fara bunÆ™asa Allah yayi zamansa a garin Damaturu jihar Yobe, anan yaci gaba da kasuwanci shi har lokacin yana neman aiki. Shiga da fita da yake yi tsakanin garuruwa a wata tafiyarshi Æ™asar Nijar ya haÉ—u da Halimatul Sadiya Æ´ar asalin fulanin Nijar.

 

Auren soyayya su kayi bayan soyayya da su kayi na shekara É—aya ta tare gidan mijinta dake cikin garin Damaturu jihar Yobe.

Halimatul Sadiya marainiya data taso gaban kakarta. Iyayenta sun rasu a hatsarin mota sun barta da yayunta maza uku, biyu sunyi aure a ƙasar Libya ɗaya yana aure a Doso jumhuriyar Nijar.

Tsakanin miji da matar ba laifi suna zaman lafiya dan Alhaji Mamman Bashir ba abinda ya rageta dashi yana bata kulata kuma yana son matar shi. Arziki ya ƙaru kasuwanci ya zauna masa a lokacin ya samu aiki a Company shiga da fita na kayan abinci. Samun aikin shi ya sashi neman yaron shago dan kula mishi da aikin kasuwancin, shi kuma ya fara kula da ofishin sa sai lokaci zuwa lokaci yake duba shagunan sa.

Shekara uku da auren Alhaji Mamman Bashir da Halimatul Sadiya kafin Allah ya bata haihuwar Æ´a mace suka saka mata suna Rahma.

Daga nan haihuwar ya buÉ—e dan ranar da Rahma ta cika shekaru biyu ta haifi Æ´a mace Hasiya, shekaran Hasiya É—aya ta samu cikin Muhsin shima yana cika shekara uku ta haifi Rukayya da yanzu watanta goma ta samu cikin wata É—aya.

Duk saurin haihuwarta Alhaji Mamman bai taÉ“a gajiya ba dan yana son ya’yansa. Arziki ya linku ya zama wani Alhaji. Ya kai su Hajj sun sauÆ™e farilla shi da matar shi.

Wannan cikin ma tun sati ɗaya da ya wuce yake roƙarta taje asibiti shi fa bai yarda da ita ba. A jikinta taji cikine da ita amma bata son zuwa. Ganin ya damu da hakan yasa taje ta tabbatar da hakan.

A yau kuma yake saka ran samun cigaban wani matsayi a gurin aikin shi da Allah bai nufa zai samu ba.

….

Hayaniyar Rahma da Hasiya sun dawo daga makaranta ya sata barin kitchen É—in Muhsin yana bin bayanta.

Yaran ta samu cikin falon suna ta surutu ga Rukayya gefensu tana bacci.

See also  Kanwata (My Sister) 1 to End

“Kai za ku tayar min ita, maza ku wuce É—akin ku ina zuwa zan cire muku kaya.”

To yaran suka amsa dashi suka kwashi jakansu da takalma su a hannu suka wuce ɗakinsu ta koma kitchen ɗin ta sauƙe miyarta ta wuce ɗakin yaran. Kayansu ta canza musu zuwa na gida kafin su fito.

“Mami abinci zanci, yunwa.”

FaÉ—in Hasiya tana tsalle saman kujera.

“Haka dai kullum kina cikin ci sai Æ™iba kike Æ™arawa.”

Mami tace ta wuce kitchen ta zuba musu a babban tray ta kawo falon ta ajiye a tsakiya.

“SauÆ™o Rahma, Muhsin kai ma ka haÉ—u dasu kuci.”

Mami tace ta komawa kitchen ta kawo musu ruwan sha dana wanke hannu.

Gaba É—aya suka wanke hannunsu suka zauna suka fara ci.

Kitchen Mami ta wuce ta haÉ—a na mijinta a food flask mai kyau da plate da spoon kafin ta fito ta wuce É—akinta dan wanka.

Bayan ta gama ta yi sallar azahar da har lokaci ya É—an gota, ta fito falon ta samu sun gama cin abincin Rahma tana share gurin. Gefe kuma Alhaji Mamman Bashir yana jijjiga Rukayya da surutunsu ya farkar da itatana kuka.

“Mun leÆ™a kina wanka.”

Cewar Alhaji Mamman yana miƙa mata Rukayya.

Hannu tasa ta karɓeta yayin da take zama tace.

“Wallahi Abban su bayan na gama aikin zafi ya dame ni, ga zirga zirga na asibiti duk na gaji shine na watsa ruwa.”

Zama yayi gefenta yayin da take shayar da Rukayya take tambayar shi ya kasuwa.

“Babu daÉ—i, ashe kayanmu duk sunyi expire yaron nan bai sanar dani ba. Fitana sai da na cire miliyin É—aya da rabi na bashi ya Æ™ara da sauran cinikin da yayi ya sari wasu kayan.”

“Bai kyauta ba, irin haka sai ya sanar da kai tun wuri kafin lokacin.”

Hajiya Sadiya tace cike da jimamin abinda ya faru.

“Ai na mishi faÉ—a sosai shi da sauran yaran, wai dama akan zai sanar dani jiya ne kuma ya mance.”

“Allah mayar da alheri.”

Hajiya Sadiya tace tana zare Rukayya daga abincinta ganin ta ƙoshi ta miƙa Abban ta ya karɓeta yana amsawa da ameen.

“Bari in kawo maka abinci.”

Kai ya É—aga mata yana ma Rukayya wasa yasa ta wuce kitchen. ÆŠaukowa tayi a babban tray har da ruwan zobo data haÉ—a masa ta kawo mishi falon.

Tare su kaci kasancewar ita ma bata ci abincin rana ba. Bayan sun gama ta tattare gurin.

Washegari ranar Alhamis da asuba ta samu ɗan saƙon ya sanar mata ƙiran da ake mata daga garinsu.

Bayan ta sanar da mijinta yace ta shirya taje ta ji lafiya sai tayi kwana biyu.

“Ji nake kamar ba lafiya ba Abban su.”

“InshaAllah lafiya lau.”

Girgiza kai tayi tana cewa.

“A jikina nake jin ba lafiya. Zan tafi dasu Rahma.”

“Makarantar su fa da islamiyya.”

“Yau da gobe suyi hakuri, asabar sai mu dawo su samu zuwa islamiyya Lahadi.”

“To shikenan Allah kiyaye hanya.”

Yace ya É—auki dubu hamsin ya ajiye mata.

“Ga wannan ki riÆ™e a hannunki. Ilyas ya kai ku zan bashi kuÉ—i yayi full tank.”

“Nagode. Nagode sosai Abban su.”

Hajiya Sadiya tace tana murmushi amma cikin zuciyarta haka kawai take jin yana bugawa.

Fita tayi ta shirya yaranta ta haÉ—a kayansu ta haÉ—a nata suka fita lokacin Ilyas ya dawo daga shan mai.

Sai da Abba yaga tafiyarsu yana ma Æ´aÆ´an shi bye bye kafin ya koma gidan shima ya shirya ya wuce aiki.

….

ÆŠANÆŠANO.

Vote.

Comments.

Share

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top