Madubina Hausa Novel Complete

Madubina Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Madubina

*Page 1&3*

 

 

Zaune suke a saman wata kujerar ƙarfe irin wadda ake a jiyewa acikin jami’oi, domin zaman ɗalibai irin wace mutun huɗu 4 zuwa uku 3 zasu iya zaunawa.

 

 

Suna zaunane awani kayatacen place publique,(wajan zamane da aka tanadar domin mutane), wajene daya ƙayatu da shuke shuke irin na zamani, ga iska mai daɗi yana kaɗawa abun gunin b’urgewa.

 

 

Sai hira suke suke a tsakanin su, sunata dariya idan ka kalesu zaka fahimci tsantsar soyayyar dake a tsakanin waƴannan jinsi guda b’iyu.

 

 

Dukansu kyawawane farare wanda farin nasu bai haska sosai ɗinnan ba, dai² misaline suturar dake a jikinsu kuwa kamar bata bahaushe ba domin sunyi kama da ɗiyan turawa yanayin suturar dake ajikinsu.

 

 

Kallonta ya yi na wani ɗan lokaci tare da murmushi a fuskarsa, kafin ya sauka asaman kujerar ya durƙusa agabanta ya kama hannun ɗaya yace,

 

 

“Babu shaka Fadeela kece farin cikina kece nutsuwata sannan kece duk wani jindaɗi nawa, basan ta yadda zan kwatamta miki yadda soyayyarki ta ratsa jini da duk wani sashe na jikina ba ta samu wajan zama a zuciyata ba”

 

 

Ya numfasa akaro na biyu ya sake kai dubansa agareta cewarshi, “bana tunanin akwai ranar da zata zo na tsinci kai na ba’a cikin soyayyarki ba, domin ke ɗin kin zamarmin Madubi agareni wadda idan na rasaki bansan halin dazan tsinci k’aina ba, Fadeela ki taima ki karɓi soyayyata please kada kice a’a rashinki agareni baban haɗarine a rayuwata, ina sonki Fadeela bazan iya rayuwa idan babu keba!…”

 

 

Kallonsa take da murmushi a fuskarta tare da gasgata kalamansa, tabbas maganarsa gaskiyace domin duk abunda yake faɗa yana fitowa ne daga zuciyarsa ba daga laɓan bakin saba.

 

 

Ɗayan hannunta da bai riƙeba ta kai hannunta ta riƙe ɗayan hannunsa ta murmusa ta buɗe bakinta tace….,

 

 

“Fadeela Fadeela wato ba zaki tashi daga bacinnan bako so kike sai kin makara kamar jiya kinata shegen bacci”

 

 

Wannan maganar ita ce tayi sanadiyar farkawarta daga baccin da take, ita da masoyinta habibinta kuma Madubi agareta.

 

 

Tashi tayi ta sauka daga kan ƙaton gadonta wanda zai iya d’auka mutum uku 3 tana bubbuga kafafuwanta akasa tana faɗin,

 

 

“Ohhhh Mama meyasa zaki tasheni ina cikin mafarkina mai daɗi, gashi yanzu kin dakatar dani daga faɗa masa abunda na jima inasan faɗa masa” Tana magana tare da ƙarisawa wajan Mamanta da take ta faman gyara ɗakin Autartata da duk yabi ya hargitse.

 

 

 

Tana karasawa ta kama ka fadar Mafaifiyarta ta ta kwanta akai taci gaba da shagwaɓa.

 

 

“Wato ke dai har yanzu ba zaki dai na maganar wannan banzan yaron ba, wanda shi kwatakwatama bai san ma kina wannan shirman naki ba, wadda ko kullaki baya yi amma ke kin nace masa sai kace chewgum, wai shi ɗaya ne a duniy’ar nan? ga samari masu sanki “ya“yan manya duk kinƙisu saboda wanda be masan kina yi ba!…..”

 

 

Ɗayar ka fadar tata takama tare da juyo da ita gabanta tace,

 

 

“Haba Mama meyasa ba zaki bani shawara ba, yadda zan jawo hankalinsa izuwa gareni amma saiki dinga kashe mun ƙwarin giuwa, kin sani bayin kai na bane faɗawa soyayya da shi ba, Allah ne ya halitamin ita acikin zuciyata, ni kai na dazan iya da tuni na fitar dashi a cikin zuciyata” ta saki Mamanta ta koma bakin gado ta zauna, Aje abunda ke a hannunta Mama tayi ta zauna a kusa da ɗiyartata tabbas tasan bayin kanta bane Allah ne ya ƙaddara mata wannan a matsayin kaddararta wannan itace tata kaddarar.

 

 

Kamota tayi tace “ba ina sarar da ke bane ɗiyata inason ki samu wanda zai soki ne, na tabbata idan ya gano da irin soyayyar da kike masa zai iya amfani da wannan damar wajan ƙuntata miki”

 

 

“Mama ki daina saka wannan tunanin aranki, insha Allah hakan bazai zama gaskiya ba”

 

 

“Ni kai na ina fatan hakan amma komai wuya komai runtsi ka da ki taɓa furta masa kalmar soyayya da bakinki, idan ba shine ya fara furta miki ba”

 

 

Akaro na b’iyu ta sake kama kafaɗun mamar tata tace, “haba Mama sai kace dai kin manta wacece Fadeelanki”

 

Littafan Hausa Novels

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
Shafa gefan fuskanta tayi tare da kwantar da ita a saman ka fad’arta tace, “nasani ɗiyata amma yadda kike nuna damuwarki akansane ni ke ga kamar ba zaki iyaba”

 

 

“Mama ina mai tabbatar miki koda son sa zai kasheni , bazan taɓa furta masa kalmar so ba ki yadda dani”

 

 

“Shikenan yanzu dai ki tashi kije ki shirya kinga yauma kin makara, ki tashi na haɗa miki ruwa aban ɗaki tun dazu ”

 

 

Tashi tayi daga jikin Mamanta ta miƙe tsaye sai yanzu na kare mata kallo har kasa farace kuma farin nata dai_dai ba sosai ba doguwace amma bacen ba ba tada jiki sosai kuma baza’a sakata jerin marasa jiki ba jikinta d’an dai_daine tanada dogon hanci da d’an karamin b’akinta ga idanunta masu d’an girma gashinta har bayanta shiba b’aki ba kuma shi ba jaba.

 

 

Sanye take da riga da wando ƙananan kayan na bacci ɗan wandon iyakarsa cinyoyinta sai rigarma itama ƙaramace me siraran hannuwa.

 

 

Ta kali Mamanta tare da shaguɓe fuska, ta ɗan buga ƙafarta akasa tace, “Uhn uhm ni dai yau ke zakimin wanka”

 

 

Filo Mama ta ɗauka ta jefeta da shi da gudu ta tsere ta shiga ban ɗaki, ta janyo ƙofar tana mai cigaba da dariya itama Mama tashi tayi tana dariya taci gaba da aikinta tana faɗin “Allah ka shiryamin Fadeela Ameen”

 

 

Kusan ta ɗauki lokaci kafin ta fito daga toilet ɗin. A inda tafito taga ɗakin nata an gyarasa sosai sai ƙanshi yake ga katon bed inta yasha shimfiɗar sabuwar bed ship komai na ɗakin kallar blue ne da glod kama daga labulaye da kujeru sai painting ɗakin da yake blue da fari.

 

 

Faɗin irin tsaruwar da ɗakin ya yi ɓata lokacine, iya wannan zai tabbatar maka da cewa ba ɗiyar tallaka bace suna da rufin asirinsu.

 

Hatta kayan da zata saka Mamarta ta riga data fitar mata, suna aje asaman bed murmushi tayi aranta kuma tana ƙara jinjina ƙauna irin wace iyayanta da yayunta suke nuna mata a filli ta furta “ina kaunarku nima”

 

 

Ba wani ɓata lokaci ta shirya acikin kayan da aka tanadar mata, doguwar rigace black sai mayafin rigar daga samanta ta ɗan kame sai kasanta daya buɗe ba ƙaramin kyau rigar tayi mata ba, ta ɗauki ribon black shima ta kame lalausan gashin kanta daya sauko mata har a b’ayanta ta, ƙarasa bakin dressing mirror ta ɗan shafama fuskanta powder da man baki data shafa a bakinta daya ke pink colour ne gwanin sha’awa.

 

 

Masha Allah duk da cewa ba wani kwalliya tayi ba, shigar da tayi ba ƙaramin fito da ainihin kyawunta ya yi ba. Gyalen kayan ta ɗauka tayi rollen katan dashi ta, koma ɓangaran takalminta ta ɗauki wani baƙi (black colour) mai tsini ta saka, ta ɗauki jakarta itama black colour ɗin ce, ata ƙaice dai komai nata black colour ne na yau tayi dressing, wayoyinta ta ƙarasa a inda ta sakasu charge ta ɗauka kirar Iphone13 sai ƙaramar da take Infinix hot8 ta sakasu a jakanta, maganar turare kuma zan iya cewa ɓarinsa tayi a jikinta domin babu ta inda ƙanshi baya tashi a jikinta.

 

Bayanta kamala komai ta fito daga ɗakin nata, duk family suna zaune ne a dinning area suna jiran fitowar kanwar tasu mace ɗaya tilo da Allah ya basu. Hira kawai suke a tsakaninsu a yanayin da suke hakan zai tabbatar maka shaƙuwa da irin tsoyayar da take a tsakanin Wannan familly.

 

 

Ƙarar takalminta kawai sukeji, yayin da take saukowa daga saman step sai kanshin turaranta daya mamaye dukannin fallon yayin daya haɗe ƙanshin da fallon ya keyi ya bada wani ƙanshi mai daɗi.

 

Yayanta wanda dagashi sai ita shiya tashi daga kujerar daaya ke akai zaune, ya karaso wajanta yana mai faɗin,

 

“Kai little irin wannan kyau haka, ai saiki saka duk mu suma anan ga wani ƙanshi sai kace kantin shagon sayar da turare ya fashe a gidannan”

 

Dukansu dariya suka saka ita kuwa ɓata rai tayi irin na shagwabarnan ta ƙarasa kusa da baban yayansu ta tsaya kusa da kujerar daya ke kai a zaune tana bubbuga ƙafa tace

 

“Baby(sunan da take kiransa dashi) ka gansa ko wai nice little wai duka ma shekara nawa ce yaban? da zai cemin little nidai ka faɗa masa bana so!…” Tayi maganan cike da shagwaɓa

 

“Kinga ki ƙyalesa ai kowa yasan anan keba little bace”

 

“Oho ni dai nasan na girmi wata hadda shekara 3” ya saka dariya

 

Da gudu tabi bayansa suka kama zagayan fallon, ta gagara kamasa. Su kuwa ba abunda suke idan ba dariya ba idan da sabo sun saba da halin Fadeel da Fadeela.

 

Dadyne yayi magana yana murmushi yace, “kinga Daughter zoki zauna ki ƙyalesa zanyi maganinsa”

 

Tana haki ta ƙarasa kusa da Dadynta taja kujera kusa dashi ta kwantar da kanta asaman ka faɗarsa tace “yauwa Dady motar da kace zaka saya masa kadda ka siya”

 

“Ki kyalesa bazan siya masa ba domin dama naga yana wasa da karatunsa yanzu”

 

Fadeel ɓata fuska ya yi, ya dawo kan kujerarsa ya zauna yana hararar Fadeela, ita kuwa gwaliyo tayi masa tana mai ƙara yi masa dariya shi kuwa kyaci yai mata irin na zaki sani nan.

 

Sai ayanzu Fadeela ta samu damar gaisar da iyaye da yayun nata “wai. Dady ina yaya Jafar ne” tai maganan tana kara gyara zamanta asaman kujera yay’in da Mama ta tashi zatai serven insu kafin Dady yakai gayin magana sai jinsa sukai yana saukowa shima daga kan step yasha fararan kaya sai zuba ƙanshi yake idan ka kalesa zakaga santsar kamarsu da Fadeela sai dai shi ya fita dogan hanci kuma b’akinsa yafi nata ƙaranta.

 

Tashi tayi daga inda take tayi aguje wajan yayanta ta rungumesa tana faɗin”Good morning tween brother”

 

“Morning to Angel fatan kin tashi lfy” yai magana yana kokarin rabata da jikinta yaja hannunta suka ƙarasa suka zauna suma.

 

Ya mekama kowa hannu sukai musabaha ya gai da mama yay’in ta Fadeela tabbar kusa da Dadynta ta dawo kusa da Tween bros ɗinta dama idan kaga Fadeela kusa da Dady to Yayanta bayananne.

 

Haka wannan familyn suka ci abinci cike da raha, lokacin da suka ida kuwa kowa ya fita aiki ya yi, da Dady shida baban yayansu wato Fauzan suka fita idan ya ajesa shi saiya huce wajan aiki. Fadeel kuma motarasa ya shiga ya wuce Company yaya Fauzan kasan cewar yau bayada lecture a makaranta sai Fadeela wace yayanta kuma tween ɗinta wato Jafar ze sauketa a makaranta shima ya yi Company,

Mama ita ka ɗai ce a gida yau itama idan ta kamala aikinta zata wuce gidan aminiyarta da take biki a yau……..

 

 

Sai muce adawo lafiya love familly.

 

 

Nima anan zan dasa aya sai mun sake haduwa a wani sabon shafin.

 

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.