Kiyon Lafiya

Magance Matsalar Saurin Kawowa

Magance Matsalar Saurin Kawowa

Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa , wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka , don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:

1 A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma karkare ta , sa’annan a dake ta , ayi shayi da ita , bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana. Citta nada sinadari mai zafi na “gingerol” mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.

2 A nemi man na’a-na’a (peppermint oil) mai kyau, musammman ɗan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan) . A wanke gaba da ruwan dumi , a goge lemar sa’annan a shafa man ga zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra). Musamman a shafa idan zakari yana mike, sai jira bayan minti 10 zuwa 15 sa’annan a sadu da iyali. Man na’a-na’a na rage “sensitivity” na zakari , wato rage kaifin ɗanɗano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima’i. Haka kuma za’a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na’a-na’a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.

3 Fita daga gaban mace na ‘yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.

4 Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son ya daɗe bai yi inzali ba to ya tari jima’i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.

5 Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin ɗaya daga cikin wadannan mutanen domin neman ta.

Leave a Comment

error: Content is protected !!