Hausa Novels

Mahabeer Hausa Novel Complete

Mahabeer Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Mahabeer Hausa Novel Complete
“A garin kaduna a kuma cikin G.R.A.
ta ‘Yan majalissu, Anguwa ce wacce ta tara manya manyan masu hannu da shuni zaune a cikin ta.

‘yan siyasa da masu hali kenan, sannan kuma a koda yaushe cikin unguwar zaka jita tsit babu hayaniya bisaga sauran anguwanni.

Gidan alhaji mu’aazam saraki shine gida mafi d’aukan hankalin mai kallon sa a layin,
Gida ne tsararre na gani a fad’a, duk da gidajen Suma fitattune a tsari da kuma kyau to amman kuma nasa ya d’ara nasu.

In ka shiga cikin Harabar gidan kuwa ba q’aramin girma ne da ita ba.

Daga can gefe kuma tampal tampal ne shaq’e da motoci na yayi sama da nawa a ciki, dan sunfi q’arfin a tsaya q’ilgasu komin sa idon mutum kuwa.

gudan gefen kuma injinan motsa jiki ne kawai sai lambu daga can side d’in Wanda babu kayan marmarin da babu a cikinsa, sannan kuma ga swimming Wanda ke cike da q’ananun kifaye sunata shawagi a cikinsa da fararen ruwa a cikinsu.

Sai d’ayan swimming d’in na wanka shima wani q’aton gaske ne cike da blue d’in ruwa a cikinsa,
daga gefensa ga Wasu kujeru da kuma fararen matakalu na shiga da fitowa a swimming pool d’in, sannan an ajiye wani d’an q’aramin gado da tebur na ajiye kayan buq’atu na Wanda in ka fito wankan zaka iya kwantawa dan hutawa,
ga kuma bukkar dake kewaye da gadon gwanin sha’awa dai abun.

Sam wurin inwa ce zalla babu rana haka wajen yake rayuwar sa.

Hakama q’aton falon gidan inka shigesa komi yayi, Wanda Keda d’akuna Sama da 7 a cikin sa, kowane d’akin babu abinda babu cikinsa najin dad’in rayuwa.

A hnkali ta ke saukowa daga saman benen kaida ganinta kuma zakasan lallai ita d’in matar mnya ce, fara ce tas da ita a q’alla shekarunta bazasu Gaza 37 ba, dayake bafulata na ce ita sosai.
(Hj umaima knn) hannayenta d’auke da wani dogon file ta q’araso ta zauna inda mai gidan nata yake wato Alhj mua’azzam saraki, zaune yk yana aikin duba wasu files files d’in dake gabansa na ofice d’inshi a nutse.

Zama tayi bisa 6arin jikinsa idanunta sunyi rau rau sun cika taf da q’walla, nan danan kuma ta sakar masa kuka mai cin zuciyar mai sauraro.
da sauri mu’azzam saraki ya maido hankalin sa gareta gaba d’aya bayan ya ture aikin da yake yi a lokaci d’aya.

Hannayenta ya ruq’o ya sanya cikin fuskarsa yayi shiru yakasa furta komi bayan duba file d’in hannunta d’in da yayi shima, hankalinsa ba q’aramin tashi yayi ba ganin irin baya nan da file d’in ya q’unsa a cikinsa.

Cikin muryan kuka tace “nuree kaga alamu sun nuna bazan ta6a haihuwa ba a rayuwa ko?!”

 

Mahabeer Hausa Novel Complete
Tun da likitoci sunce wai ita d’in mahaifana bazata iya d’aukan cikin kaba nuree?

 

Nuree mike faruwa ne damu haka?
Allah yayi mana Arziq’in dukiya Amman bai bamu yara ba yau shekara 17 knn da aurenmu nuree Amman na Gaza haifa maka d’a?
wayyo ni Allah na”!

Nan da nan ta sake fashewa da wani matsanancin kuka mai girgiza jiki d’in nan.
Kamota yayi yana shafa bayanta alamun rarrashi shima kukan zucin yk wnda yafi na sarari ciwo.

Ya zasuyi da ikon Allah ne to?

inda dai Allah bai basu ba sai suyi haq’uri, wataq’il ma d’an ba alheri bane a garesu yanzun shiyasa Allan bai basuba sai dai ya azurtasu da arziq’in Wanda har kullum suke temakon bayin Allah dashi.

Sauke ajiyar zuciya yayi ya rufe idanuwa sannan ya sake bud’esu jin tayi shiru da kukan alamun tayi tayi har ta gaji sai sauke ajiyar zuciya da takeyi minti wajen 11 suna a haka sannan ya duba yaga har tayi barci mai tattare da wata irin sabuwar shessheqar ajiyar zuciya sbd wahalar kukan nata data sha.

Girgiza kai yayi na tsananin tausayinta sannan ya gyara mata kwanciya anan wajen sannan ya sumbaci gefen ha6arta ya miq’e kai tsaye ya shiga part d’in mahaifiyarsa wato *Annah*,

Mahabeer Hausa Novel Complete
farar bafillatanar dattijiwa mai Addini da sanin yakamata.

Ganin ta zaune kan carpet sanye da farin hijab tas dashi tana lazumi Wanda hakan ya tabbatar masa da sallar walha ta gama tana lazumi,

 

Izzar So Hausa Novel
Agogon hannunsa ya kalla yaga 11 saura a lokacin, waje yasamu ya zauna kan d’aya daga maka maka grass carpet d’in dake falon Annah d’in, dan jiyayi Sam bazai iya hawan kujeran ba Dan har yanzu zuciyar sa bata samu sukuni ba, bakomi a cikin ta sai tsananin tausayin umaimah dan gane da rashin haihuwar da batayi ba,
Tagumi ya rafka tareda rufe idanunsa zuciyarsa na wani irin d’as d’as.

Mahabeer

 

Jin an janye hannunsa daga tagumin ne yasa yayi saurin kallo wajen.

Annah ce ta zauna gefensa har lokacin hijab d’in na jikinta da cazbahar ta tana ja, dan ita abin ma ya zame mata jiki kullum cikin lazumi take, kokuma taita karanta addu’oe cikin hadith hadith nata.

A hnkali mu’azzam saraki ya sunkuya tareda furta “ina kwana Annah?
An tashi lpia?”

“Alhamdulilla yarona, Amman dai kasan tagumi ba abu ne mai kyau ba ko?
Baice komi ba sai Murmushin da ya d’an kalato da q’yar sannan ya miq’a mata file d’in hannunta yace.

“Annah wannan shine sakamakon da wannan baturen Dr nayz yayi a bincikensa na zuwan da umaimah tayi jia Egypt dan duba lpiar mahaifar nata”!

amsar file d’in tayi sannan ta janyo medical glass d’inta ta sanya mai q’ara q’arfin ido.

sannan ta bud’a file d’in ta fara dubawa itama,
Takusan minti 5 tana q’ara maimaita karanto file d’in itama sannan ta d’ago kai cikin yankewar zuciya ta dubi mua’azzam tace
“yarona?”

D’agowa yayi ya dubeta ya sake maida kansa q’asa yace
“na’am Annah”

Annah taci gaba da cewa “Kuyi haq’uri, insha Allah komi yayi farko zaiyi qarshe, Allah kad’ai yasan nufinsa akan hakan shiyasa bai Baku haihuwan ba, bakomi Allah yasa hakan shi yafi zama mana alheri gaba d’aya”.

​

 

 

 

Name:Name  MAHABEER  HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!