Mahaifiyata ce sila Hausa Novel

Yan mata

Mahaifiya ta ce sila Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

_*MAHAIFIYATA CE SILA*_

 

 

_By Zahraty_

 

*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*

 

 

 

_*01-02*_

 

…..Kwance take kan bed din ta,birgima take yi kamar wacce zata mutu,wani azababben ciwon mara take ji,gaba daya bata san mai ke mata dadi ba,dagowa tayi daga kifen da take ta juya da kyar,,idanunta sun kada sunyi jajir kamar gauta,da kyar ta mike ta nufi bed side drawer din dake dakin,jawowa tayi ta dakko wani magani a ciki wanda Zuby ta bata,ballan guda daya tayi ta saka a baki sannan ta kora da bottle water din dake kan fridge din,koma saman gadon tayi ko zataji daidai,amma ina kamar ma kara mata wani ciwon ake,a gigice ta mike ta ja drawer din ta balli guda biyu ta watsa a baki ta kora ruwa sannan ta koma ta kwanta.

 

Bata wani jima ba taji ciwon ya dan lafa mata,mikewa tayi ta shiga toilet ta had a ruwan zafi tayi wanka,fitowa tayi ta shirya cikin doguwar Riga baka wanda ya zauna mata das a jikin ta,powder ta shafa, ta saka kwalli kafin ta shafa lip gloss,taje kanta tayi wanda yake baki wuluk,kafin ta kawo ribbon din ta kalan baby pink ta daure gashin ta,hijab ta dauka baby pink da jaka baki sai takalmi baki sannan ta feshe jikinta da wani turare mai sassanyar kamshi,kafin ta sa kai ta fita daga dakin.Tana fitowa ta nufi bedroom din Ammi,kallon Ammi tayi tace”Ammi zanje gidan su Zubaida kinsan nace miki bata da lafiya”,kallon ta Ammi tayi tace “toh kiyi sauri ki dawo,kinsan dai bana son irin sannan yawace yawacen”, shiru tayi sai can kuma tace” bazan dade ba yanzun zan dawo”,gyada kai Ammi tayi tace”na dai fada miki,ai nasan halin ki zama zakije kiyi sai dare ki dawo”,shiru kawai tayi,sai kuma can tace”shikenan bari in wuce sai na dawo”………..

 

Tana fitowa daga gate din gidan ta fara tafiya zuwa bakin titi kafin ta samu Napep,tarewa tayi ta hau ta fada masa inda zata je,tafiyar 15minutes ne ya kaisu gidan su Zuby,tana sauka ta sallami mai napep din sannan ta shiga gidan,a kofar apartment din su zuby tayi knocking, bude mata aka zo akayi,Zuby na ganin ta ta dama tsalle ta rungumeta hade da cewa”yar halas ,kinsan kuwa kina raina,tunanin ki kawai nake yi sai gakk”,dariya tai tare da cewa”ehenn bama zaki bari in gaishe da mummy ba kin wani tareni da zance”,dariya tayi tace”toh bata nan,zo muje dakina”janta tayi suka nufi dakin ta,zama suka yi a bakin bed sannan Zuby ta tashi tayi serving din ta,zama tayi sannan tace”babe what’s wrong,mai ke fruwane na ganki haka”,dukar da kai kawai Eysherh tayi tace”Zuby ina cikin masifa,Zuby ina cikin bala’i,kinsan yanzu har an kai limit din da wannan maganin baya mun aiki gaba daya a jikina,wallahi dazu dada karan kwana da sai dai mkiji mutuwa ta,sai fa danayi over dose sannan na samu relief din wannan abdominal pain din nan”,juyar da kanta Zuby tayi gefe hade da tabe baki tace”wannan kuma ke kika jiyo,in banda abinki ke an fada miki dama zaki dawwama ne da maganin nan yana miki aiki,na fada miki,ki bani chance,their is another way wanda zai fidda ki daga wannan matsalar “.

Karin wasu littafai da zaku so

 

Juyowa Eysherh tai ta kalle ta tace” Zuby na amince yanzun,ki fada mun wallahi ina azabtuwa da yawa,sha’awa tayi mun yawa,bansan ya zanyi ba “,dariya Zuby tayi sannan ta jawo jakar Eysherh dake ajiye a kan gadon,phone din ta ta fito dashi kirar android,kafin ta saki wani munafikin murmushi tace” kinga wannan wayar hannun ta kawo komai da sauki,kinga yanzu haka kawai videos zan tura miki Wanda kallon kawai zakiyi hankalin ki zai kwanta,ba ruwanki da wani magani,ta hanyar nan babe zaki samu sahihin natsuwa”,jinjina kai Esherh tayi tace “shikenan dear,thank you so much”, yanzu ki tura mun da sauri kinsan sai dana mata karyar baki da lafiya”, kwashewa da dariya Zuby tayi tace” au ashe dai kin biyo layi,taya dama zaki zauna kullum kamar wata har gidan gari,ace kwata kwata baki da wani ‘yanci,fitan ma da zakiyi wai sai an baki izini chab”,fuska Eysherh ta marairaice tace “toh ya zanyi ba dole min zauna ba”, tabe baki kawai Zuby tayi tace”chab,kina da aiki babba ace sai dai kawai ka zauna aita juya ka,wai kina ruwa wallahi we are 17yrs fa,we are minors fa har yanzun ,in takaice miki yanzu law bai  hau kanmu ba,so duk abunda muke so zamu iya yi ba wanda ya isa ya kaimu gun hukuma”, jinjina kai Eysherh tayi cike da gamsuwa ga abinda Zuby tace kafin ta gyara zaman ta itama tacve” gaskiya wannan maganar naki tana kan hanya,yanzu ni kinsan su Ammi nada tsanani ne,ga kuma Abban mu kinsan baya tolerating nonsense “,dariya kawai Zuby nta saki sannan tacve” babe abeg bar wannan zancen,with time zaki fahimci mai nake nufi dana ce haka”….mikewa Eysherh tayi tace”nizan wuce,dan ALLAH ki turo mun videos din nan,in samu in dan rage zafi,kinsan in ciwon maran nan ya dawo toh fa ba kanta,kuma kin san bana so Ammi ta fahimta in shiga uku?,tabe baki kawai Zuby tayi tace” tab ALLAH Eysherh kina da aiki,yanzu Ammin kike tsoro,toh ALLAH ya kyauta miki,Ai yanzu an wuce zamanin tsoron iyaye,in har kikace tsoron su shine abunyi Ai kuwa bazaki taba jin dad in rayuwar ki ba”,shiru kawai Esherh ta mata dan bata ma san mai zata ce ba….rakota tayi har bakin junction ta samu Napep ta tafi ita kuma Zuby ta juya ta nufi gida tana cewa”ALLAH ya kiyaye in zauna inajin tsoron wasu iyaye,mutun bazai iya rayuwa yanda yake so ba,hmmmm yarinya ki ma zauna da mana,nasan da sannu zaki gane hanya……

 

……Sai gurin karfe shida Eysherh ta isa gida,tana zuwa ta tadda Ammi a zaune a parlour tana aiki da laptop din ta,sanye take da medical glasses,ta cikin glasses din ta watso ma Eysherh kallon zaki gane kuranki yau,a hankali ta karasa shigowa parlourn,kallon Ammi mtayi cikin rawan jiki tace”Ammi dan ALLAH kiyi hakuri wallahi Mummyn su Zuby ne bata nan shine na  jirata ta dawo muka gaisa”,cikin tsawa Ammi the mata”rufe mun baki mara kunyar yarinya kinje kin gama gantali a gari kin zo kina mun rawan jiki a nan ko?”,tashi tayi ta kamota ta wurga saman kujera,tasa hannunta tana dukanta tana cewa”zaki sani yau,ke ga mara kunya koh”,karfi Eserh tasa ta hankade ta tana cewa”haba Ammi yanzu fa I’m 17yrs old fah,wallahi na wuce duka”,tana fadin haka ta tashi da gudun gaske ta shige dakin ta ta rufe da  key,zama tayi gefen gado tana cewa”haka kawai ina da shekara 17 amma ace har yau ana dukan mutun wai bayi da hankali,mu ba’a zauna an mana tarbiyar da ya kamata ba amma kulun cikin ce mana marasa tarbiyya ake yi haba”….

 

——————————–

 

………..Parking motarta Ummah tayi a bakin gate din school din su Hamrah,tana gama juya kan motar ana kada bell din tashi gida,bata wuce 5mins ba suka fito ita da Saudat wato best friend din ta,tahowa sukayi gurin motar,kallon Ummah Saudat tayi tace”ina wuni Ummah”,cikin sakin fuska ta ansa mata kasancewar ta aminta da tarbiyar yarinya,gashi kallo daya zaka mata ka gane hankalinta da natsuwarta,sannan tace”har yanzu driver din ku bai zo bah”,murmushi ta danyi tace”eh amma ina ganin bazai wani dade ba yanzu zai zoh”sallama sukayi ma juna,Hamrah ta bude passengers seat ta zauna suka tafi,suna tafiya ummahnta kalli Hamrah tace”dear yau dame dame aka muku a makaranta baki fada mun ba”,aiko nan ta fara fada mata duk wani abu daya faru,kasancewar akwai matsananciyar shakuwa tsakanin su da Hamrah yasa ko yaya in tayi mata karya take saurin ganewa,duk da cewa yanzu shekarar ta 20 on service wato tun kafin tayi auren take aikinta amma hakan baisa bayan tayi aure ta haihu ta hofantar da tarbiyar yarinyarta daya wanda take matukar kaunar ba,tayi planning abubuwanta sosai Dan tana da lokacin aikinta tana da kuma na iyalinta,a office takan zauna tayi aikinta amma da ta dawo gida shikenan ta ajiye aikin office sai kuma ta koma tattalin iyalinta,hakan yasa suka shaku da yarinyar sosai.

 

…….kasancewar karfe 3 take tashi daga aiki sai ta jira har uku da rabi a office sannan take ta dakkota,suna zuwa gida abinci kawai zasu ci,zuwa karfehudu kuma Hamrah ta tafi school,bayan ta dawo kuwa gaba daya Ummah bata da wani aabu sai kula da yar ta da kuma mijin ta.

 

Kamar kullum yau ma da daddare suna zaune a dinning table suna dinner, bayan sun kammala Hamrah tayi clearing gurin sannan suka zo suka zauna,kallon ta Abbanta yayi yace”mama na wani course zaki karanta ne”,cike da doki tace”Abba na ni mass com nake so in karanta,ina so in zama Yar jarida”,dariya Abba yayi yace”masha ALLAH kinga kinyi gado,dama ance kyan da ya bani uban shi”,dariya Ummah tayi tace”shikenan tunda ni bazaa gane ni ba na hakura”,dariya Hamrah ta saki tana cewa “kai Ummah ba fa nhaka nace ba,kawai dai ina so in zama yar jarida ce”, daga ta Ummah tayi ntace” kar ki damu babu wata matsala ,duk abunda kike so kuma shi muke so”,cike da jin dadi mtace”that’s my mum”,dariya sukayi dukkan su,mikewa tayi tace”Ummah,Abbah bacci zanyi saij da safe”,ansa mata sukayi da ALLAH ya tashe mu lafiya”sannan ta wuce dakinta,bin ta da kallon dukkan su sukayi cike da kaunar diyar tasu Abbah yace”kingan ta koh,ita daya ta fimun yara Dari da zan samu,tana mun biyayya tana girmamani tana kuma darajani a matsayina na mahaifinta,ya ALLAH ka albarkaci rayuwar wannan baiwa haka,ka bata duk abunda take so duniya da lahira”,cike da jin dadi Ummah ta ansa da”ameen”,sannan suka suka nufi makwancinsu…..

 

 

……Eysherh kwata kwata ranar bata kara fitowa parlour ba,ta kulle dakinta ta hana kowa shiga,ko da su Sumayyah(senior sister din ta)suka dawo daga school bata barsu sun shigo dakin ba,tana zaune tana sakawa tana kwancewa,ayyanawa take kullum sai Ammi tace mata bata da tarbiyya,ai duk koma mai yake faruwa ita ta jawo,taki zama ta lura dasu,kullum aikinta kawai ta saka a gaba,kullum ta dawo daga office ba ruwanta dasu sai dai fada ,ta zauna ma taji damuwar su ma batayi,gashi kuma daddy ba a garin yake aiki ba,amma shi ne kullum kuma ta rinka musu fada,ita fa had ta fara tunanin cewa kawai zata ni shawarar Zuby tayi fito na fito da koma waye,tunda dai yanzu itama ta girma,jin kanta kawai take on top,zata iya taka duk Wanda take so…….

 

More comments…

More typing……….

 

Share pls

 

Zarah

08063304625

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.