Hausa Novels

Mahwish Hausa Novels Complete

MAHWISH HAUSA NOVELS COMPLETE

 

 

 

 

BY HAERMEEBRAERH

Page 1:

 

 

Kunnuwan ta toshe suke da earpiece ta na sauraran shahararren gidan redion nan da ke cikin garin Kano wato Freedom redio, inda aka saka waqar da ta sanya zuciyar ta narkewa tare da tsananin shiga shauki irin na cikakkun masoyan da duk wani motsi ke tuna masu da masoyan su.

A hankali ta bud’e idon ta, domin jikin ta na bata ana kallon ta, ido biyu suka yi da qaramar qanwar ta da ke bi mata wato Zulaihat, dariya sosai Zulaihat ta kece da ita, sannan ta ce,

“Yah Mahwish ki na matuqar bani dariya, yanzu da ki ka kwanta shame-shame ki na kallon sama ido rufe me ki ke tuna wa? Ko ki na hango ki ne tare da Ali Nuhu ku na waqa ne kema?”

Wata sabuwar dariyar Zulaihat ta sanya, sannan ta samu gefen kujerar da wadda aka kira da Mahwish ta zauna, tare da zuba mata idanun ta da ke dauke da tsantsar dariyar tsokana.

Cikin yauqin ta da juya kyakkyawan jikin ta, ta yunqura ta zauna ta na kallon Zulaihat,cikin muryar ta mai cike da amo mai sanya natsuwa da kwanciyar hankali ta ce,

“Hummm Zulaihat kenan, ke fa har yanzu yarinya ce, baki san mene ne so ba,da ace kin san mene ne so, da kin fahimci halin da duk wani masoyi ke shiga in ya ji kida na tashi, ko da ba waqa to kai za ka sama masa waqar da kan ka, kuma….”

“Zulaihat ! Zulaiii !”

Kiran da mahaifiyar su Mahwish ke kwala wa Xulaihah ne ya sanya ta miqewa cikin sauri, da tura baki, ta ce,

“Ke fa Hajiya ke kira, Abba ma na jiran ki tun dazu”

“Amma ai ba ki fad’an ba Zulaiiii zama ki ka yi ki na ta surutu,”

Cikin bata fuska ta kalli Mahwish, dan ta fi kowa sanin ba ta son a kira ta da Zulaii, amma ta ke tsokanar ta,fita daga d’akin na su ta yi ta nufi babban parlourn su, wanda ya ke kewaye da manyan kujeru, waje ne mai matuqar kyau kwarai, kuma madaidaici, zama ta yi a gefen qafar Hajiya ta ce,

“Gata nan zuwa, Hajiya dan Allah ki daina kira na da Zulai, ita Yah Mahwish kun sa mata suna mai dad’i Ni kun sa min Xulaihah kuma ban tsira ba sai an sake b’ata min a dinga kira na da Zulaii?”

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Dariya Mahaifin su Alhaji Farouq Bukar Mai Taya ya yi, sannan ya ce,

“Gaskiya bai kamata ba kam, Hajiyan su ya kamata ki dena b’ata wa autar ki suna”

Wani kallo mai cike da so da qauna, tare da harara irin ta masoya Hajiya ta wurga wa Alhaji Farouq, sannan ta ce,

“Amma dai alhakin saka sunan zulai ya rataya a wuyan ka ne, ni da aka bar ni na sanya sunan Mahwish ba gashi na saka mai dad’i ba,”

“To ya ishe ku, sunan Yaya ta ne dai, takwara na mata,a bar tsokanar Yayata , a dinga cika mata sunan ta daga yau”

“Amma dai Abba Yah Mahwish ce babba me ya sa ba ka saka mata Xulaihah ba sai ni?” In ji Xulaihah da ta bata rai, dan ita sam sam sunan bai mata ba.

Dariyar Mahwish ce ta katse su, nan da nan kuwa Xulaihah ta qara tsuke d’an karamin bakin ta, ta na harare hare, sanin halin ta na saurin kuka ne ya sanya Mahwish gaida iyayen su, ta zauna, ba tare da ta sake magana akan sunan Xulaihah ba.

“Lafiya qlou ‘yar Abban ta, lafiya har na dawo tun 3:40pm ban gan ki ba? Me ya faru?”

Kallon Xulaihah ta yi, ta ga ta na mata dariya, dauke kan ta tayi kawai ta bawa mahaifin ta hakuri, ta ja bakin tata tsuke, su na nan zaune su na hira sama sama, suka ji sallamar yaro, cike da tsuke fuska Mahwish ta tashi ta tari yaron,

“Meye ?”

“Yah Mahwish Yaya Saeed ne ke kiran ki, ya ce sauri yake zai yi tafiya dan Allah ki leqa ku yi sallama”

Kama kunnen yaron ta yi sai da ya saki qara,

“Ibrahim ban sanar da kai kar Saeed ya sake aiko ka ka zo ba? Kai kunnen qashi wai gare ka ko na rodi? Zan ci mutuncin ku da kai da Saeed din, fita ka bar nan ko na dalle ma fuska da mari, wawa mai kama da yayan shi”

Kamar daga sama ta ji an damqi hannun ta, ihu ta sanya ta na qoqarin kwacewa ta gudu, amma ta makara, kunnuwan ta bibbiyu Hajiya ta kama, ta dinga ja kamar ta samu robar balanbalan,

“Kamar yanda bakya jin magana haka Ibrahim ba zai ji maganar ki ba ya qi zuwa aiken wan shi, ke wato a rayuwar ki ba za a iya baki umarni ki bi ba ko? Ba kuma za a iya hana ki ki hanu ba ko? Wuce ki sa hijabi ki je wajen shi kafin na tsinke maki kunnuwan”

Cike da zubar hawaye Masu zafi ta bar wajen, kunnuwan ta jin su take kamar ba a jikin ta ba, saboda tsabar zafi,a gaban madubi ta tsaya, ta janye gashin ta da ya ɗan sauka jikin kunnen ta, ta kalli kunnuwan ta ga yanda suka yi jawur, hawaye ne masu zafin gaske suka sake zubar mata, wayar ta ta dauka, ta danna kira, sannan ta samu waje ta zauna,

“Hello? Dan Allah ka zo yanzun nan in ka na kusa”

Ta na gama fad’in haka ta kashe wayar ta, sannan ta shiga bayin su ta wanke fuskar ta,ta fito, ta tsane ta da towel, sannan ta shafa mai kad’an ta ɗan sanya mata powder, ta sa man lebe tare da zizara kwalli a kyakkyawan idanun ta.

Turare mai sanyin qamshi ta fesa, sannan ta yafa mayafin ta ,ta fita, tsaye ta yi a gaban matashin da zai iya kai shekaru talatin da bakwai, ta juya masa baya, ta na girgiza jikin ta.

Murmushi ya yi kawai, domin in da ana sabawa da wulaqanci to ya ci ace Saeed ya saba da wulaqancin Mahwish a gare shi, bude baki ya yi, ya ce,

“Assalamu alaikum”

Ya tabbata Mahwish za ta amsa sallamar shi ko ba komai ta san mahimmancin hakan, bai tab’a sallama ba tare da ta amsa ba.

A ciki ciki ta amsa shi, sannan ta sake matsawa nesa da shi, yanda ba za a jiyo ta a gida ba, ta ce,

“Wai kai Saeed me ya sa ka ke so sai ka kassara rayuwa ta za ka ji dad’i? An tab’a so dole ne? Saeed ni Mahwish na sanar da kai ba sau d’aya ba, ba sau biyu ba, ba sau uku ba, ba zan tab’a son ka ba, har abada, ina da wanda nake so, kaiii Saeed na sanar da kai a duniya ba wanda na tsani na ga fuskar shi sama da kai,Saeed ko ka had’a dangi da mayu ne banda masaniya?”

Kalaman ta na dukan zuciyar shi, amma Sam sam ba sa zama, kamar wanda ake daukan tsumma a goge su haka suke shiga su na fita.

“Mahwish dan Allah in tambaye ki mana?”

“Tambayoyin ka wanne ne ban amsa ba kaf din su? Kai bari na taqaita maka wahala, kudin ka basu damen ba, in ka ga dama ka fi d’an gote kudi ba zan taba son ka ba, har abada, kyawun ka ba zai taba rud’a ta ba, in ka so ka fi Salman Khan ko larabawan can qasashen da ka ke fita kyau, bai damen ba, ni dai na fad’a maka ba na son ka, ba zan so ka ba, ka je ka nemi wata tun lokaci bai qure maka ba, ilimin ka ba ya gaba na,kaiii Saeed na tsane ka, ba na son ka, ka kuwa gane me na ke nufi da hakan?”

Wani irin abu ne ya tokare masa maqoshi, kalaman ta na tarwatsa duk wani buri nashi akan ta, meye laifin shi? Qarar machine suka ji, cikin sauri Mahwish ta washe baki,ta na murmushin ta mai kara wa kyakkyawar fuskar ta kyau,barin qofar gidan nasu ta fara, ta na takawa cike da yanga ta isa gaban matashin da ke jingine da machine din shi roba roba, nan da nan kuwa fuskar Saeed ta yi jawur sabo da b’acin rai, matashin da ke jikin Machine kuwa kashe masa ido ya yi, sannan ya saki wani murmushin gefen baki, a lokaci d’aya kuma ya kalli sarauniyar da ke mulkin zuciyar shi, ya na bin duk wata gab’a ta jikin ta da kallo.

“Yah Salim barka da zuwa,me ya sa ka jima ba ka iso ba, ka sa na b’ata lokaci na a wajen wannan mayen”

Cikin yanayin bada hakuri wanda aka kira da Salim ya ce,

“I am so sorry baby, har zan fito Ummee ta ban saqo sai da na ajiye sannan na taho, so what’s up, ya ki ke sarauniyar kyawawa, ma’abociyar qamshi da kyau,”

Wani irin dad’i ne ya kama Mahwish, wadannan kalaman na d’aya daga abinda ke sace zuciyar ta, ya ke sanya ta yin nutso a cikin soyayyar Yayan nata Salim.

Sallama Saeed ya musu, ciki ciki suka amsa, sannan suka juya masa baya, cike da qunar zuciya ya ce,

“Mahwish abinda ki ke kina kyautata wa kenan? Ni fa na kira ki, amma ki ka zo wajen wannan yaron da ba zai aure ki ba, duka duka shekarar shi nawa? Da me ya girme ki? Mahwish me zan maki ne ki so ni, dan Allah ki sanar da ni”

Dariya suka sanya a tare ita da Salim, sannan suka kalle shi sama da qasa, cikin dariya ta ce,

“Ka rabu da mu, shi ne abinda za ka min ka burge Ni, wataqila zan san tabbas kai masoyi na ne, tunda ka hakura da farin cikin ka, dan ni na ji dad’i”

Da sauri ya kalle ta, ta na nufin ya sadaukar da soyayyar shi? Ko me take nufi?

“Ko baka gane me take nufi bane? Ai in ka na son mutum za ka so ya yi farin ciki ko? To ka rabu da mu mu yi aure, kai kuma ka je ka samu wata ka aura ka gane?”

“Salim ina tausaya wa rayuwar ka, dan kuwa har yanzu baka san mene ne so ba, dan kuwa ba so ka ke yi ba, ka na dai sha’awar jikin ta ne”

Fada ne ya tashi kaure wa a tsakanin su, cikin qanqanin lokaci Salim ya rikice ya na masifa tare da juya maganar da Saeed ya yi, ya ce ya ce masa mazinaci.

Mahwish kuwa ta goyi bayan Salim dik da ta san ba haka Saeed ya fada ba.

Hayaniyar su ce ta fitar da Abban Mahwish qofar gidan,ganin abinda ke faruwa ne ya sanya shi kiran su ciki baki dayan su ran shi a matuqar bace.

Mahwish kuwa ko a jikin ta, Ita dai koma me zai je ya zo ba za ta auri Saeed ba, ko uban waye ya tsaya masa ba Baffah Sageer ba.

Zaune suke a gaban Alhaji Farouq, ya bi su da kallo d’aya bayan d’aya sannan ya ce,

“Me kenan? Me ye matsalar ku ne ku da in kun hadu kullum sai kun yi fad’a?”

Cikin ladabi Saeed ya duqar da kan shi qasa ya na bada hakuri, Salim kuwa cike da tsiwa da yarinta ya ce,

“Abba ka wa mutumin nan magana, in ba haka ba duk abinda na masa shi ya jawo, wai god’ai god’ai da shi ya ke so ya shiga tsakanin mu Ni da Mahwish, in gaskiya ne ya je ya nemi babbar mace daidai shi mana, mu kuma ya bar mu mu yi auren mu”

Da kallo Abban Mahwish ke bin shi har ya gama maganganun shi da suke fitar da tsantsan yarinta da rashin kunyar shi, sai da ya gama sannan Abban ya kalli Saeed ya ce,

“Saeed ba yau za ka koma Dubai din ba ne? Ko so ka ke ka yi missing Flight din ka kamar last time? ”

“Abba na zo ne mu yi sallama da Mahwish”

“Amma in ban manta ba last time ma akan ta ka yi missing Flight din ka ko?”

Shiru ya yi bai ce komai ba, kan shi a qasa,

“Maza tashi ka tafi, Allah ya bada sa’a ya taimaka, Allah ya yi jagoranci, ya sanya wa kasuwancin ka albarka”

Cike da jin dadi Saeed ya amsa da,

“Ameen Abba, sai na dawo, na gode”

Sallama ya musu ya fita, Saeed yana fita Abba ya kalli Salim ya ce,

“Salim magariba ta yi, maza ka je ka yi alwala mu wuce masallaci, ke kuma ki yi sallah kar na dawo na gan ki zaune ba ki ba, zan sab’a Maki, tunda ke ibada ba ta dame ki ba,”

Cikin tura baki ta bar parlourn ,ta koma dakin ta, ta zauna ta na ta kukan baqin cikin abinda ke shirin faruwa da rayuwar ta……

PAGE 2:

 

 

Har suka je suka dawo kuwa bata yi sallar ba, Hajiya ta yi maganar har ta gaji, babban abinda ya fi wa Mahwish mahimmanci shi ne Abban ta ya dawo ta ji a ina aka kwana.

Shiru, shiru, bai dawo ba, har sai da aka yi isha’i kamar yanda ya saba, ya na shiga ta fita da saurin ta dan ci gaba da tattauna maganar da take ganin ita ce mafita a soyayyar ta da Salim.

Gani ta yi bata ga Salim ba, kuma Abban ta ya rufe gida, tsaye ma yake a tsakar gidan ya na addu’a, (bayan an rufe qofar gida ana karanta ayatul kursiyyu a qofar gidan)da dukkan alamu ya gama fitar yau kenan, wani irin abu mai zafi da d’aci ta ji ya tokare mata wuya.

Wai me mutanen nan suke nufi kenan? Abban nata ma an juyar masa da kai kenan yanzu ba ya goyon bayan ta akan abinda take so? Inaaa dole ne yau Abban ta ya bata amsar abinda ke zuciyar shi game da maganar auren nan, cike da shagwaba da son yin kuka ta ce,

“Abbaaaa ina Salim? Ya na gan ka kai d’aya, Abbaa na zaci ka na baya na ne ashe kai ma ba ka son farin ciki na, Abbaa Salim nake so ni ba na son kowa bayan shi, ba zan auri kowa ba, Abbaa in kuka aura min wani ba Salim ba zan iya rasa rai na,”

Kukan da take danne wa ne ya kwace mata, ai kuwa ta sake shi, ta dinga rera shi kamar wani karatu, Alhaji Farouq kallon ta ya yi cikin tausaya wa, domin kuwa ya san yanda yaran ke son junan su, tun su na qanana, bacci ma ba ya raba su, sai dole, in yau wannan ya kwana a gidan su wannan, gobe wannan zai kwana gidan su wannan, sai da suka fara girma ne aka raba tsakanin su.

Dafa kafad’ar Mahwish Alhaji ya yi, ya ce,

“Mahwish dear, please stop crying, ya isa haka, tun dazu ki ke kuka, ba kya tsoron ciwon kai?”

“Abbaa ban damu da duk wani abu da zai same ni ba, rayuwa ta ba ta da wani amfani ko ma’ana in babu Salim a cikin ta, Abbaa ta yaya zan iya rayuwa da wani ba Salim ba?”

Da kyar Alhaji Farouq ya ja ta suka nufi parlour’n su, ya zaunar da ita, sannan ya kama hannayen ta biyu, ya na kallon kyakkyawar fuskar ta, da ke tsananin zubar da hawaye, ya na jin zafin kukan da take, amma ba shi da yanda zai ya sama mata mafita, ita suka haifa ba ita ta haife su ba, dan haka dole ne ta yi hakuri,ta bi umarnin su.

“Mahwish dear,tunda ki ke da mu a duniya kin taba neman wani abu kin rasa? (Kan ta ta girgiza alamar ahh ahh) wani abun ma Mahwish ba ku san da shi ba za mu yi maku shi, Mahwish ki na zaton ni mahaifin ki da yayu na za mu cutar da ke ? (Sake girgiza kai ta yi alamar ahh ahh) to me zai sa ba za ki iya yi mana biyayya ba akan wannan auren? Tunda kin san ba zamu cutar da ke ba, kuma kin san Saeed mutumin kirki ne, ko so ki ke na yi fad’a da ‘yan uwa na musamman baffan ku? Ki na jin kalaman shi fa, ya ce dole sai kin auri Saeed in dai ba iyaka zan masa da iyali na ba, in nuna masa ni ma na haifa, ki na jin me Goggon ku Xulaihah mahaifiyar Salim din kan ta ta fad’a, ba za ta bari Salim ya aure ki ba, saboda in cancanta ake nema Saeed ya fi Salim cancantar ya aure ki, Mahwish ‘yan uwa na ba da wani mugun nufi suke so ki auri Saeed ba, cancantar shi ce ta sanya aka zabe shi sama da d’an uwan ki na jini, Mahwish kamar yanda Baffan ku ya ce ne, marigayi mahaifin Saeed mutumin kirki ne, kuma Saeed ya yo halayen shi na kwarai, ke yanda Baffan ku da mahaifin shi suka taso ai ko da a wani waje Saeed ya ke neman aure za mu tsaya masa har ya samu, ballantana ya na neman ‘yar mu.

Mahwish na san tsoron ki ba zai wuce akan matar shi ba, matar Saeed kuwa ba ita ce abar dubawar mu ba tunda kowa da gidan ta za ta zauna, ba gida d’aya bane, idan ba ya gidan ki za ki sa a ran ki kamar ya yi tafiya ne, in kuma ya dawo wajen ki shike nan, mahaifiyar shi na tare da matar shi ba a gidan ki za ta zauna ba, na tabbata Saeed duk ya maki wannan bayanin.

Mahwish kar ki ce ban maki qoqarin a baki wanda ki ke so ba, na buga, na raya, kowa ya juyan baya akan wannan maganar,na rasa wanda zai duba lamarin ku ke da salim a gane ku na son junan ku fiye da tunanin kowa, amma duk yanda magana ta kai ta kawo, Saeed kowa ke zab’ar maki, dan Allah ki yi hakuri ki fidda Abban ki kunya, in isa da ke ko sau d’aya ne, kar ki watsan qasa a ido, a zarge ni da rashin baku tarbiyyar da za ku min biyayya”

Ba tare da zato ko tsammani ba Mahwish ta ga hawaye na zuba a idanun Abban ta, abinda bata tab’a gani ba kenan, Abban ta jarumi ne, lallai maganar nan ta wuce duk inda take tunani,yanzu wa za ta kama ya taimaka mata? Ko dai hakura za ta yi ne da Salim din? Ta sharewa Abban ta hawaye ? Cikin kuka mai tsanani, ta bude baki dan yanke hukunci akan rayuwar ta ta gaba, rayuwar da ke cike da sarqaqiya da tashin hankali, rayuwar da ke cike da rud’ani da rikici da firgici.

“Abbaa, na amince da dukkan zabin ku a gare ni, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi,”

Ta na fadin haka ta miqe, ta nufi d’akin su da gudu, a gadon ta madaidaici na katako ta fad’a tare da fashewa da matsanancin kuka, Xulaihah da ta saurari duk abinda suka tattauna akai ce ta zauna gefen ta, tare da qoqarin d’ago ta ta kwantar da ita a jikin ta, Mahwish na jin ta a jikin qanwar ta ta, sai ta sake rungume ta, ta na kuka, ita kan ta Xulaihah din yanzu kukan take, domin ta fi kowa sanin yanda Mahwish da Salim ke son junan su.

“Dan Allah Yah Mahwish ki dena kuka kin ji? Ji kan ki yanda ya dauki zafi, kamar an kara a jikin garwashi, kar ki ja wa kan ki wani ciwon,”

“Ciwo na nawa kuma Xulaihah? Saboda kawai Marigayin mahaifin Saeed na da mutunci Saeed na da mutunci shike nan sai a auran shi kamar banda wanda nake so? Wa zai fahimce Ni ne? Wa zai gane qunci da rad’ad’in da zuciya ta ke ciki? Bana son Saeed, ba na qaunar wanda ya kalle shi da sunan qauna ma, ta ya ki ke tunanin zaman mu zai kasance?”

Hawayen Xulaihah ne suka karu ganin yanda Mahwish ke magana bakin ta na karkarwa, da dukkan alamu, ta kwaso wa kan ta zazzaɓi ne saboda kukan da take ta yi.

Ba tare da sun ji motsi ba, suka ga Hajiya a gaban su, ta zauna a gadon Xulaihah da ke fuskantar na Mahwish, sannan ta ce,

“Mahwish ki sa wa kan ki salama, kinga in ki ka auri Saeed ba ruwan ki da rikicin iyali, daga shi sai mahaifiyar shi, da matar shi d’aya,ko yara ba su da shi,kuma ba gida d’aya za ku zauna da su ba, qanwar shi da yayar shi duk su na d’akin mazan su, amma Salim duk ba za ki samu wata kulawa a wajen shi ba, shi ma kulawa ake da shi, duka duka shekara d’aya da rabi ya baki, yanzu ne ya cika ashirin da d’aya fa, yarinta za ku yi ta yi, Ku zo soyayyar ta koma qiyayya, ga ‘yan uwan shi cike da gida ga mahaifiyar shi, kin dai san masifar goggon ku, Mahwish inshaa Allahu auren nan da saeed alkhairi ne, mu yi ta addu’a ,kin ji? Allah ya maku albarka, ya yi mana zab’in alkhairi”

“Ameeen Hajiya” in ji cewar Xulaihah,wadda ta ke kallon Mahwish ta ji me za ta ce.

Ba abinda ta ce, illa tashi da ta yi ta shiga bayi, a can ma ta jima ta na kuka kafin ta yi alwala, ta koma, bata tadda kowa ba, da alama su na can parlour, ana hira, sallah ta yi kamar caccaken kurciya, ta na idarwa ta dau wayar ta da ke ta ringing ta na ganin sunan Salim sai kukan ta ya dawo sabo.

Shi din ma kukan yake, dan kuwa komawar shi Baffah ya masa tatass daga baya ya masa nasiha, ya nuna masa ko auren aka ce zai yi ba zai iya ba, tunda har yanzu kwanon shi na kitchen dakin shi na gidan, da me zai ciyar da ita? Kuma a ina za su zauna? Makaranta yake yi kuma .

Sai da suka yi kukan su mai isar su sannan suka yi wa junan su alqawurra masu wuyar fahimta, su na nan su na soyayyar su kamar ba su ake qoqarin rabawa ba, ta yi bacci, ya na jin saukar numfashin ta ya kashe wayar, tare da kissing din wayar, ya gyara kwanciyar shi shima sai bacci.

***********************

Shirye shiryen bikin ya kan kama sosai, dan kuwa har lefe da sadaki an kawo ya na gidan su Mahwish.

Saeed kuwa sai ana sati d’aya auren su zai dawo Nigeria, amma duk wani shirye shirye da ya kamata a yi, ana ta yi, kudi kawai yake aiko wa.

A ranar da ya rage sauran sati d’aya auren Saeed da Mahwish, Saeed ya sako kayan shi da ya saro a gaba ya dawo Nigeria.

Mahaifiyar shi ta yi matuqar farin cikin ganin shi, sai da ya gama gaishe ta ya sanar da ita duk wata nasara da ya samu a tafiyar shi, sannan ya mata sallama, ya ce zai shiga wajen iyalin shi ,Hajiya ta masa izinin tafiya.

Ya na isa bakin qofar ya gan ta a rufe, bai kawo komai akan shi ba, dan kuwa ya zaci kawai an rufe ne, saboda sauraye da ke yawo musamman da safe, ya jima a tsaye ya na buga qofar ba alamun za a bude masa, dole ta sa ya kwantar da akwatin shi ya nemo key ya bude gidan ya shiga.

Ya na shiga ya gan ta zaune a parlour alamu sun nuna Tasneem na jin shi, bud’ewa ne ba zata yi ba, kad’a kan shi kawai ya yi, ya shiga d’akin shi da jakar kayan shi, ya na mata addu’ar Allah ya shirya ta, ba dole ya qara aure ba, mace kamar ba mace ba, a mazan ma marasa tausayi bai san ina zai saka ta ba.

Ya na tsaka da b’alle botiran rigar shi ya ji shigar ta d’akin, ta tsaya a bayan shi, ta na fidda wani irin hucin masifa da bala’i.

Kamar wata mahaifiyar shi haka ta fara magana.

“Saeed, (sunan da take kiran shi kenan, ba ko sayawa a matsayin shi na mijin ta) na maka gargad’i akan qara auren nan da ka ke so ka yi, amma ka min kunnen uwar shegu ko? Saeed in ka na son kan ka da arziki ka hakura da wannan auren mu yi zaman mu kamar yanda muke da, in kuma ka dage sai ka yi auren nan, ina tausaya wa rayuwar ku da kai da amaryar taka”

Ta na gama fadin haka ta wuce ta bar masa dakin, ba tare da ya kula ta ba, ko ya nuna mata ya ji me take fadi ya shiga wanka .

Ya na fitowa ya shirya tsaf cikin shadda gezna sai bud’a qamshi yake, ya kafa hular da ta dace da kayan jikin shi, sannan ya nufi inda suke ajiye takalma ya dauki wanda zai shiga da hular shi, ya na gamawa ya dau wayoyin shi, ya bar d’akin.

Tasneem na zaune ta na kallo ta ji fitar shi, qamshin da ke tashi a jikin shi shi ya fi jan hankalin ta, domin kyau da qashin Saeed na daga abinda ya ja ra’ayin ta, bayan dukiyar shi.

Wani irin kishi ne ya tokare mata wuya, kallon shi ta yi tace,

“Sai ina kuma?”

Murmushi ya yi, ya ce,

“Sai gidan Alhaji Farouq wajen amarya Mahwish”

Ji ta yi kamar ya debi ruwan zafi mai tafasa ya watsa mata a jikin ta, amma dake ‘yar duniya ce, sai ta yi yaqe, ta ce,

“Ina zuwa ka bata saqo ka kai mata, zauna bari na zo”

Hanyar kitchen ya ga ta nufa, ya saki murmushi, a zaton shi ko snarks d’in ta mai dad’i za ta bayar a kai wa Mahwish, ya na nan zaune ya ji an kwara masa wani liquid abu, mai dumi kad’an,ga qamshin curry da komai, ya na bude ido kuwa yaji ya shiga, a kid’ime ya miqe ya na laluben hanya, ba tare da ta ce komai ba ta maida tukunyar ta kitchen ta kwanta ta ci gaba da kallon ta, shi kuwa sai kwala mata kira yake, akan ta taimaka masa, yaji ya shiga idon shi.

Da kyar Saeed ya kai kan shi dakin shi, ya wanke idan shi, cire kayan ya yi ya kalle su ya ga yanda miyar ta bata masa kaya wanka ya sake yi, sannan ya tattare kayan ya sa a wajen wanki, ya sauya wasu, idanun nan sun yi jawur sabo da yaji.

Ya na gamawa ya je gaban ta ya ce,

“Tasneem ki guji ranar da raina zai ɓaci akan ki, domin kin san ya akai har auren mu ya qullu da ni da ke, kar ki kai Ni bango Tasneem abun ba zai mana kyau ba”

Key din motar shi ya wuce ya dauka ya bar gidan, gidan su Mahwish ya nufa, ya na kusantar gidan zuciyar shi na zillo da farin cikin ganin masoyiyar shi.

Mahwish kuwa……..

*A gaskiya na ji dad’in comments din ku jiya, sosai da sosai, ba za ku ga lalaci ba kuwa, kun nemi sulhu da yatsu na inshaa Allah

 

 

PAGE 3:

 

Hira suke ta yi da Salim a parlour sun ci abinci sun bar wajen kaca kaca su na ta shan hira, Xulaihah na ta dariyar jokes din da yake basu, wayar Mahwish da ke caji ce ta hau ruri, cikin zargi Salim ya ke bin ta da kallo, ita kuwa fuska a daure ta miqe, dan ta san ba zai wuce mayen nata ba.

Ta na duba wa kuwa ta ga shi ne, bata fuska ta sake yi, sannan ta latse kiran ta yi zaman ta, da ido Salim ke nuna mata alamar ta dau wayar kar ta damu.

Xulaihah kuwa na gefe bata san me suke yi ba, d’aga kafad’a Mahwish ta yi, alamar kiran ya riga ya katse, Xulaihah ce ta ce,

“A gaskiya ban taba zaton Yah Mahwish za ki yi sanyi da wuri haka ba, kin yi bala’in burge ni matuqa, kuma in Allah ya yarda za ki ga da kyau a rayuwar ki, kai kuma Yah Salim Allah ya baka mace ta gari,wadda ta fi Yah Mahwish”

Yaqe suke ta yi daga Salim din har Mahwish, a tare suka amsa mata da

“Ameen”

Qasan zuciyar Mahwish kamar garwashin wuta haka take jin ran ta, Wannan wace irin rayuwa ce, ka na soyayya ba ka da hali da ikon nuna wa? Saeed kuwa ba zai ga da kyau ba Indai ya dage sai auren nan ya tabbata, yanda zuciyar ta take a quntace sai ta shi tafi ta ta quntata.

Mintina uku tsakanin kiran da akai na farko, wani kiran ya sake shiga, sai da ta jima ta na ringing sannan ta amsa, sallamar shi kawai ta amsa, ta yi shiru, miqewa ta yi ta shiga dakin su, mayafi ta yafa ta fita, tsaye ta gan shi jingine da motar shi, tabbas Saeed ya had’u, matuqar had’uwa, amma ita ganin shi take kamar wata halitta daban mai tsananin muni.

Tsaye ta yi a gefen shi ta juyar da kan ta gefe, sannan ta tura d’anlwalin ta gaba, gashin ta da ta dunqule waje d’aya ya zauna dass a dogon wuyan ta, hannayen ta duka biyu zube a qugun ta.

Murmushi ya yi, dan kuwa shi duk yanda za ta yi kyau take qara yi masa, kallon farin wata ya yi, ya ga yanda yake haska kyakkyawar fuskar ta, sakamakon d’auke wutar lantarki da akai, bude baki ya yi ya ce,

“Mahwish ba gaisuwa?”

“Ba a min wanan tarbiyyar ba, sai ka jira sai na koyo sai in maka”

“Allah ya baki hakuri amarya ta, ki na lafiya?”

“Asibiti ka gani akai na da ka ke tambayar lafiya ta? Wai ni Saeed dan Allah me ya sa ba ka da zuciya ne? Anya kuwa akwai zuciya a cikin wanan qirjin naka? Saeed ina mai baka shawara ka gaggauta janye wannan auren tun kafin a daura shi, ina tausaya wa rayuwar ka in ka dage sai ka aure ni, domin kuwa zaka daura aure ne da tashin hankali, da masifa da bala’i, wataqila ma da ajalin ka”

“Subhanallahi, dan Allah Mahwish ki dena irin wannan kalaman, domin basu dace da ‘yar mutunci kamar ki ba, wadda ta fito daga gidan mutunci gidan manya, dan Allah Mahwish ki kalle ni, kuma ki saurare ni, ki sani duk abinda Allah ya hukunta zai faru sai ya faru, ba mu da tsumi ba mu da dabara, in Allah ya nufa ba zan aure ki ba sai ki ga Kafin auren wani abu ya gilma ban aure ki ba, amma…..”

“Allah ya sa mutuwar ka ko mutuwa ta ce za ta gilma a tsakanin wannan qaddararren aure da ake so a qulla a tsakanin mu, Saeed na maka kuka, na maka magiya, na maka bori, na maka wa’azi, ba abinda ban maka ba, dan ka gane yanda na ke qin ka, na ke tsanar ka a rai na, amma ka rufe idon ka,ka toshe zuciyar ka, da kunnuwan ka, to kuwa ba za ka ga da kyau ba Saeed duk randa ka yi gangacin aure na, banza mara zuciya, wanda kare maqasqanci ya cinye wa zuciya, mtswww”

Qoqarin barin wajen take yi Salim ya fita, fuskar nan kamar hadari, ta na ganin shi kuwa ta nufe shi ba tare da bata lokaci ba ta fad’a jikin shi, ta fashe da kuka, kyakkyawar runguma ya mata a jikin shi, cike da tsananin begen ta ya ke shafa bayan ta da sigar lallashi, wani irin abu ne mai duhu ya lullube idanun Saeed, kunnuwan shi suka dauki wata qara, baya ji sosai, jiri na diban shi ya dafa motar shi, hasbunallahu wa ni’imal wakeel kawai yake maimaita wa, matar da zai aura nan da sati ce a jikin wani qaton a gaban shi ya na shafa ta, qirjin ta a na wani gardin, jikin ta na manne da na wani qaton, tunda ya ke da ita ko yatsan ta bai tab’a tab’awa ba, amma Salim ke riqe da ita a haka.

Kamar NEPA sun yi timing komai, Salim na shinshinar wuyan Mahwish aka kawo wuta, ba dan sun saba yin hakan ba, kawai dan su bawa Saeed haushi ko ya yi zargin dama sun saba hakan tare, shi ne dalilin yin hakan.

Saeed bai ce komai ba, da ya samu nutsuwa ta dawo masa, motar shi ya bude ya dauko wata ‘yar jaka da ya zo mata da tsarabar chocolate daga Dubai mai shegen tsada da kud’in da za ta yi hidimar biki, masu yawan gaske ya ajewa Mahwish da ke manne mamat da Salim a dakalin qofar gidan su, ya bud’e baki zai mata sallama ya kasa, wani abu ne qulalle mai d’aci a maqoshin shi, da sauri ya shiga motar shi ya bar wajen, ya na tafiya Mahwish ta fara qoqarin karbar kan ta daga wajen Salim, amma Salim bai san ta na yi ba, domin kuwa da gaske ya fita a hayyacin shi, ya jima ya na neman irin wannan damar da zai ji ta a jikin shi, to gata ya samu, ba zai bari ya yi wasa da damar shi ba.

Wasanni ya hau yi mata, ya ja ta gefe inda ba kowa ne zai gan su ba, tun ta na jurewa ta na jin dad’in abun har ta fuskanci abinda suke ba daidai bane ba fa, da kyar ta banbare jikin ta daga na Salim da ke maida numfashi da sauri da sauri .

Kallon shi ta yi ta ga yanda idanun shi suka koma, jikin shi har wani karkarwa yake ya na so ya sake damqo ta,ja ta yi da baya sannan ta ce,

“Yah Salim ba wannan ne alqawarin mu ba, dan Allah kar ka sa na tsane ka,”

Da sauri ta juya za ta shiga gida, tuntube ta yi da jakar da Saeed ya ajiye mata, kamar ba za ta dauka ba, ta durqusa ta dauka, ta juya ta yi wa Salim sai da safe ta shige gidan.

Salim na nan tsaye ya na jin takaicin rashin nasara akan Mahwish, shigar ta da wasu mintunan ya buga machine din shi ya bar gidan.

Mahwish kuwa na shiga d’akin su ta wuce, ta tarar da Xulaihah na bacci, dab’as ta zauna a gadon ta, ta hau tuna abinda ya faru tsakanin ta da Salim, kuka ta fara yi sosai, a hankali ta ke furta,

“Me ya sa Saeed ka ke so ka shiga tsakani na da masoyi na? Wanda na ke yi wa son da ni kaina ban san kalar shi ko adadin shi ba, Salim kad’ai nake so, na ke so na kasance da shi, tunda nake a duniya ban taba jin son kowanne namiji ba sai shi, ban tab’a son kasancewa da kowa ba sai shi, Saeed me ya sa ba za ka gane kalar tsana da qiyayyar da nake maka ba ne? Za ka yi da ka sanin sani na a rayuwa kuwa, mu zuba mu gani”

Wurgi ta yi da jakar da Saeed ya kawo mata, kudin suka zube a qasa da kwalin chocolates mai kyau a ido, harara ta bankawa kudi’n da kayan ta wuce bathroom, wanka ta yi ta wanke bakin ta,ta gyara gashin ta, ta fesa turaruka, sannan ta yi kwanciyar ta, ba tare da tuna cewar ba ta yi sallar isha’i ba, ba addu’ar bacci ba komai haka ta yi kwanciyar ta.

***********************

Saeed kuwa sai bayan ya bar wajen su ne wasu hawaye Masu zafi ke zubar masa a idanun shi, hotunan Mahwish a jikin Salim ke ta masa yawo a kai,a hankali ya ke furta,

“Mahwish na yarda da ke, na sani kun yi haka ne dan ku ban haushi, to ba zan taba janye wa ba, Allah ne ya jarabce Ni da son ki, kamar yanda ki ka jarabtu da qi na, Allah Mai daidaita lamura ka daidaita mana namu,muna miqa godiya a gare ka akan dukkan jarabawar ka a gare mu”

Tasbihi ya dinga yi ga Allah har ya isa gida.

Tasneem ta ci kuka ta godewa Allah, ta na zaune ta na jiran shi ya shiga gidan zuciyar shi ba dad’i sam, amma bai nuna mata ba a fuska, hasali ma murmushi ya sakar mata kamar ba abinda ya faru a tsakanin su kafin ya fita.

Da kyar ta iya mayar masa da martanin Murmushin shi, saboda ban hakuri da shawarwari da Hajiyan Saeed din ta bata, bayan ta mata waya ta sanar da ita yanda take jin zuciyar ta a game da auren Saeed din da Mahwish, cikin ran ta take furta,

‘Dole ne na bi shawarar Hajiya na hakura for now in dai ina so na cimma buri na’

Ta na gama fad’in haka a ran ta ta miqe ta nufe shi, durqusawa ta yi har qasa, nan da nan kuwa hawaye wani na dukan wani suka fara kwarara daga idanun ta,daga zuciyar ta kukan ke fita, cikin sauri Saeed sarkin tausayi ya duqa a gaban ta, ya kama fuskar ta, hawayen ya dinga share mata, sai da ya ga alamar ba za su tsaya bane ya daure zuciyar shi ya kai bakin shi nata, sun jima a haka, daga baya ya d’aga ta, suka shiga d’akin su, ina nan tsaye a bakin qofa ina tunanin me yake faruwa a ciki ne na ji hyiru? Bayan wasu mintuna masu tsaho na jiyo dariyar Tasneem har da kyakyatawar ta, ta na fad’in.

“Yah Saeed ka bari dan Allah, Sweet zan shid’e fa, ba na numfashi,”

Cikin dariya mai sassanyan sauti Saeed ya ce,

“Kuma ki ke magana? Kin yafe min ko baki yafe min ba?”

A hankali ta furta,

“Na yafe maka, ni ma ka yafe min abinda na maka d’azu inshaa Allahu hakan ba zai sake faru wa ba, ina son ka Yah Saeed, ba zan so na rasa ka ba, na san mene ne a zuciyar ka game da ni, ka ga kuwa dole na ji tsoron rasa ka, in na ji tsoron rasa ka na yi laifi? ”

Rungume ta kawai Saeed ya yi, domin sam sam ba ya so ya tuna baya, an riga an aura masa Tasneem, ba yanda zai yi, to kuwa shi ma dole a bar shi ya auri wadda yake so.

Ni kuwa na ce “ko da ba ta son ka ne Saeed?”……..

 

*Ma biyutiful fiful Dan Allah ku yi min afuwar ji na shiru, abubuwan ne yanzu ba kamar da ba, ba lokaci, inshaa Allahu duk sanda na samu free time za ku ga na sambado maku rubutu mai yawan gaske, Me love U da yawa

 

*BY HAERMEEBRAERH*

 

 

*Assalamu alaikum mutanen kwarai mutanen arziki masu albarka, ina maku barka da Sallah, tare da jimanta mana tafiyar watan Ramadan mai albarka, ina roqon Allah da ya sa mu na daga cikin bayin shi da ya enta a cikin watan Ramadan*

*Masoya karanta novels d’ina da duk wani rubutu nawa ga sabo na kawo maku mai suna MAHWISH wato KYAKKYAWA KAMAR WATA, ina roqon ku kamar kullum ku dinga tara wa saboda in na yi gaba…..*

*Labarin MAHWISH labari ne wanda tushen shi wato jigon shi zan gina shi a bisa labarai na gaskiya, wanda suka faru, na mutane mabanbanta,wanda na ke fatan na rubuta shi a matsayin labarin mutum d’aya*

*Masoya novels d’ina ina fatan za ku min uzuri, domin ba za ku dinga samun post kullum ba, amma inshaa Allahu duk sanda na samu dama zan yi maku posting, ina godiya sosai a bisa soyayyar ku ta tsakani da Allah, Allah ya bar mu tare da imani, ina son ku domin Allah, Allah ya so mu ya lullube mu da rahamar shi….



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Mahwish Hausa Novels Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!