Maimoon Hausa Novel Complete

Compiled By Umar Dalha Funtua
MAIMOON
By
Maman Maama

Bismillahir Rahmanir Rahim

Episode One : The Beginning of the Beginning

Shin ta ina zan fara ne, in fara ta haduwa ta da Ibrahim ne ko kuma ta haduwa ta da Sultan? Ko kuma in fara da baku tarihi na ni kaina?
Sunana Maimuna Muhammad Dikko. An haifeni kuma na tashi garin Abuja, Nigeria. Mahaifina Alhaji Muhammad Dikko bafulatanin garin ‘yalleman ne dake jahar Jigawa. Garin ‘yalleman garin Fulani ne kyawawan gaske wadanda kuma Allah yayi musu arziki sosai har suka watsu a duk fadin Nigeria, musamman garin Lagos da port hercourt tunda yawancin arzikin su na chanjin kudi ne. Mahaifina bai bi family tradition ba saboda shi ya kasance dan boko ne. Yayi primary school dinsa a nan garin ‘yalleman tamkar sauran ‘yan uwansa amma saboda hazakarsa sai head master dinsu ya bawa mahaifinsa Alh Lawan Dikko shawarar in dai da hali gwara a tura shi kasar waje Dan ya fi samun karatu mai kyau.
Da yake kakan mu mai hali ne tun a wancan lokacin, sai ya tattara makuden kudade ya dauko yaro ya tafi dashi Lagos, da taimakon ‘yan uwansu da suke can aka samar wa Muhammad biza zuwa England inda a can ne aka samar masa admission a makarantar Gifted International College inda ya fara karatunsa na secondary school.Duk bayan shekara ake basu hutun session, Muhammad yakan zo Nigeria ya ga iyayensa da ‘yanuwansa ya koma, shi kuma Alh Lawan duk sanda Muhammad zai koma sai ya hada kudade masu yawa ya bashi saboda harkar registration da kuma bukatunsa na yau da kullum. Mahaifiyar Muhammad ma Hajiya Adama ba’a barta a baya ba domin tana iya kacin kokarinta dan har shanun ta na gado take sawa a sayar mata a boye bada sanin mai gidanta ba ta tattara kudi ta bawa Muhammad.
Kwanci tashi har Allah yasa ya gama sec sch dinsa kuma a take ya samu scholarship na karatu a Oxford University inda ya karanci business administration saboda burinsa na ganin ya gama karatu ya dawo gida yana taimakawa mahaifinsa a harkar kasuwancinsa. Daga lokacin ne ya gayawa mahaifansa cewa babu zancen biyan kudin makaranta kuma tunda yanzu he is on scholarship, amma duk da haka Alh Lawan yakan aika masa da kudade dan ya biya bukatunsa. A lokacin da ya gama first degree dinsa ne ya dawo gida da niyyar cika burinsa na karbar garkar business din mahaifinsa amma hakan bai samu ba saboda rigimar data barke a familyn su inda kishiyar mamansa wacce ake kira da Hajja tayi tsalle ta dire tace sam ba zata sabu ba bindiga a ruwa. A cewar ta duk wahalar da aka sha da makudan kudaden da aka kashe akan karatunsa sannan ya dawo kuma yace zai karbi dukiyar gida? Ta kara da cewa” inace cewa a kayi shi mai kwakwalwa ne ba zai yi kasuwanci ba karatu zai yi, sai da aka gama kashe kudi a karatun nasa sannan kuma zai zo yace zai yi kasuwancin to ba’a isa ba wallahi, suma sauran yaran gidan ai ‘ya’yane”.
Da wannan Muhammad ya tattara ya koma England ya dora karatun masters dinsa, yana gamawa ya wuce pH D. Bayan ya gama ne kuma ya karbi aikin lecturing a makarantar. Shekarunsa biyar yana lecturing a Oxford aka bashi award na professorship. A shekarar ne kuma mahaifansa suka dage akan lallai ya dawo Nigeria yayi settling down kaman sauran ‘yan uwansa. Saboda gogewarsa a harkar ilimin kasuwanci da mu’amala da kasashen waje yasa yana dawowa Nigeria government din wancan lokacin ta bashi mukamin ambassador. Kasar da aka fara turashi itace makociyar mu, Niger.

Wannan kenan;
Mahaifiyata Hajiya Fatima wadda ake kira da Bintou, buzuwa ce ta asali, mutuniyar kasar Niger ce. Mahaifinta ya rasu run tana yarinya kuma dama it’s kadai Allah ya bawa mahaifanta. Mahaifiyarta wacce sunanta aka saka min (Maimoon) ita ce ke kula da ita da karatunta har ta kammala sec sch dinta. Anan suka fara chuku chukun turo ta Nigeria dan tayi jamia anan amma saboda rashin hanya da rashin abun hannu sai abun ya gagara. A nan ne Allah ya hada su da mahaifina lokacin yana matsayin ambassador na Nigeria a Niger. Farko tausayinta ya fara ji da sha’awar yadda take da son karatu, daga baya kuma sai soyayya ta fara shiga tsakanin su duk ya cewa ya girme mata sosai. Dama kuma a lokacin Inna (haj. Adama) ta takura masa akan maganar aure dan haka bai samu matsala ba akayi aure ya taho da ita Nigeria ya ajiye ta a gidanmu dake Abuja unguwar Aso drive inda har yau anan muke da zama.

Episode Two: Meet my Family

Gidan mu katon gida ne saboda sanda daddy ya gina shi yayi niyyar dauko iyayensa ya dawo dasu Abuja amma Baffa (Alh Lawan) yace sam shi bazai bar ‘yalleman ba, wannan ya saka daddy ya tsantsara musu gida a can wanda duk da kudin da ‘yan garin suke ji dashi sai da gidan ya zama abin kallo. Sannan ya kawo ma’aikata ya zuba musu tundaga kan masu shara har zuwa kuku. Saboda yace lokaci yayi suma da zasu huta, kuma duk abinda yayi inna sai yayi wa Hajja. Ai kuwa suna hutawar dan babu abinda suke yi illa su ci su koshi su kwanta, kuma duk shekara sai sunje aikin hajji, sannan al’adar daddy ce duk sanda aka turashi wata kasa a matsayin ambassador sai ya debe mu munje munyi wata daya har su Baffa da Inna saboda yana so mu samu wayewa irin ta zamani amma yace ba zamu rayu a can ba saboda tarbiyya.
Mu biyar Allah ya bawa mahaifanmu, uku maza; ya Lawan, ya Habeeb sai Faruk, biyu mata; Hafsat da Ni. Ya Lawan ne babba sai ya Habeeb, sai Hafsat sannan Ni sai dan autan mu Faruk. Da yake mommy kwanika tayi sai ya zama babu tazara sosai a tsakanin mu, dukkan mu a shekaru bakwai ta haifemu sai kuma haihuwar ta tsaya mata, daddy kuma yace mun ishe shi fatan shi Allah yayi mana albarka. Zo gidan mu kaga kyau, saboda mix ne aka samu na Fulani da Buzaye, dan haka in ka ganmu sai ka kasa tantance wanne kabila ne mu, tundaga ma zan mu har matan mu haka muke dan sauda yawa inna takan aiko mana da rubutu tace maganin baki.
Ni maimunatu wadda ake kira da maimoon kamar yadda ake kiran wacce aka saka min sunanta wato maternal grandmother dina, nice ta hudu a gidan mu, nice kuma auta a mata. Fara ce ni tas, fatata mai sheki silkin Fulani da Buzaye, ina da tsaho amma ba sosai ba, fuskata oval shape ce mai dauke da dara-daran idanu kwantattu masu yalwataccen eye lashes, girata kamar an zana ki min ita. Hancina dai-dai misali, lips dina sirara masu kalar pink mai haske, gashin kaina mai cikane kuma mai tsaho, Wanda yazo har kan kafadu na. Ina da dimples a both chicks dina masu lotsawa koda magana nakeyi ballantana kuma ace nayi murmushi.
A gidan mu muna magana da daddy n mu da fulfulde, mommy da buzanci, sannan a tsakanin mu muna magana da English, a school ma English dinne dan haka sai kuma tashi babu Hausa sosai sai dai muji a gurin neighbours ko kuma in munyi ‘yan aiki hausawa.
Duk a cikin ‘yan’uwana na fisu surutu dan ya Walid parrot yake ce min tun ina yarinya, da yake shi ba mai son magana bane, kullum sai yayi ta korata yana cemin parrot, ni kuwa duk abinda na gani sai na tambaya, in ba’a bani amsa bama in yi ta tambayar har sai an bani amsa sai in sake tambayar wani abun daban. Tun sanda na shiga kindergarten daddy ya fahimci duk cikin ‘ya’yansa nafi daukan kwakwalwarsa duk da suma sauran ba baya bane wajen karatu. Tun daga lokacin sai yake biyemin inyi tayi tambayoyi yana amsamin har ya zamanto mun shaku sosai fiye da yadda muka shaku da mommy. Mommy n mu wacce a yanzu lawyer ce takance ko ita zan gada ne in zama lawyer saboda yawan tambayoyi na.
Ina shiga basic school na zama tauraruwa, ga kyau, ga kokari, ga surutu mai shiga rai. Sai ya zama kowa yana ji dani a school din. Bani da fada sam- sam, kuma ina da tsoro, ko juniors dina nayi wa wani abu by mistake sai in basu hakuri saboda ina bala’in lallaba jikina. A basic school na samu nickname din MOON saboda shape din fuskata da bright dimpled smile dina, ga kuma yanayin sunana MAIMOON. Wasa wasa sunana har ya fara bata in ba’a register din makaranta ba. Moon kowa yake kira na dashi.

Kasancewar mommy n mu ita kadai ce a gurin mahaifiyarta (daada) yasa ta dauko ta ta dawo da ita Nigeria cikin gidan mu, akayi mata part dinta a kusa da part din su inna, mu kuma sai ya zamanto bamu da gurin hira sai gurinta tunda Allah bai bata haihuwa da yawa ba sai kuma ya dora mata son mu. Kullum tana cikin kula damu, kunshi da kitso a kan mu ni da Hafsat baya tsufa sai an sake wani, duk da muna da gashi amma kullum kanmu a kitse yake ganin sha’awa.

Episode Three: Loved by All

Shekara daya Hafsat ta bani don haka aji daya ta fini da shi amma ka ganmu sa ka dauka ta bani shekaru da masu yawa saboda ni Allah yayi min karamin jiki, babu tsaho babu kiba sai dan karan surutu, ita kuma Hafsat bata da magana sosai amma akwai sa ido da bin kwakwkwafi, don haka duk abinda nayi tana gani na kuma muna zuwa gida zata gayawa mommy ko daada, inda ita kuma mommy zata hauni da fada, da yake mommy n mu tana da zafi, wannan shi yake kawo yawan sabani a tsakani na da Hafsat. Babban aboki na shine ya Habeeb wanda surutun mu da son karatun mu yazo daya dashi, kullum in mun dawo daga school ina dakinsa, idan an bamu homework shi yake koyamin, shi yake kawomin novels wani lokacin ma in kwanta a cinyarsa yana karanta min. Faruk kuwa dan auta kullum yana gurin daada dan a can ma dakinsa yake in ka ganshi a part din mu to daddy ne yazo gari.
Ina basic 4 Hafsat ta na 5 muka zana common entrance a tare kuma duk mukaci. Babu yadda mommy ba tayi ba akan daddy ya fita damu waje muyi karatu yaki, yace tarbiya tana da wahala a kasashen waje ko da kuwa kasashen larabawa ne, musamman tarbiyyar ‘ya’ya mata. Yayi believing cewa makarantun kasarmu a good enough.
Ba tare da bata lokaci ba aka sakamu a secondary school tare da Hafsat, wannan ba karamin bata ma Hafsat rai yayi ba dan ranar har kuka tayi su daddy na yi mata dariya wai zatayi set daya da kanwarta. Ni kuwa sai na bata hakuri na yi mata alkhawarin idan anzo promotional exam zan ki yin kokari yadda za’ayi mini repeating ita kuma ta wuce. Mommy ba karamin takaicin tafiyar mu tayi ba musamman ma da yake boarding school ce, ana gone zamu tafi na ganta a kitchen tana kuka tana soya mana miyar tankwa, anan na tsareta da tambayoyi taki kulani balle ta bani amsa sai daga bata ta jawoni ta rungume tana ci gaba da kukan ta.
Ranar tafiyar mu kuwa mommy cewa tayi ba zata rakamu ba amma da muna zo tafiya da kyar daddy da daada suka banbare mu daga jikinta dan cewa tayi mun fasa karatun, Daddy kuwa sai dariya yake yi mata, ni kuwa zuciya ta fes ina ta murna abinda. A lokacin shekarata goma amma in ka ganni zakayi tunanin banfi shekara bakwai ba.
Ana kaimu makaranta akayi admitting din mu, Daddy ya roki principal din mu cewa ta bamu daki daya ni da Hafsat saboda yana son Hafsat ta rinka kula dani. Haka kuwa akayi, aka bamu daki daya, gado daya, ni ina sama ita tana kasa, class din mu ma daya, seat dina yana gaban nata. Amma muna zuwa class Hafsat ta chanja seat ta koma can baya wai dan kada a ganmu a tare a gane ni kanwar tace.Amman duk da haka duk teacher din da ya shigo in ya ganni a gaba in yaje bays kuma yaga Hafsat sai ya tambaye ta “is she your sister” ya nuno ni, ita kuwa Hafsat sai bakin ciki ya kamata. Daga baya wai ta tsiri saka nikab tana rufe fuskarta dan kar aga kamannin mu.

A makarantar mu muna da masu yi mana komai tun daga kan shara, wanki, guga, wankin toilet da sauran su. Mu dai bamu kawai shine muyi karatu. Ai kuwa Moon an samu abinyi, nan na zage na kama karatu baji ba gani, kullum ina library sai dai in fito inyi sallah in ci abinci in koma. Da daddare kuma bana karatu sai bacci, saboda ni din gwanar bacci ce, tun inayin sallahr isha’i zan kwanta har sai assuba zan tashi inyi sallah. Daga nan sai mu tafi islamiyya wacce mukeyi daga assuba zuwa 7. Sannan muzo muyi wanka muyi breakfast a dinning hall sai mu wuce class sai 10:30 mu fito break a kawo mana snacks da drinks, wani lokacin kuma farfesu ba kifi ko naman rago da bread mu ci mu koma class. Sai 1:30 muke tashi daga class mu je mosque muyi sallah sai mu shuga dinning hall muyi lunch sannan mu wuce hostel. Daga nan sai inyi wanna in saka evening wears dina in koma class area in shiga library bana fitowa sai 6:00 sannan zan koma hostel in yi magrib, daga nan zan saka Hafsat a gaba da surutu tare da sauran ‘yan dakinmu. Sau da yawa inna dameta sai ta saka ear piece a kunnen ta ta rabu dani, amma haka bazai hana ni yin magana taba. Ban damu ko tana jina ko bata jina ba.
Hafsat duk ta rame saboda ita ‘Yar hutu ce gaskiya. Kuma da gaske tana missing gida, kullum bata con abinci sai race babu dadi, ni kuwa sai in hada da nata da nawa in cinye babu abinda ya dame ni, as long as akwai books a library to bani da matsala.
Duk karshen wata mommy da daddy sai sunzo mana, in ya na gari, ranar visiting day su kawo mana kayan sosai drinks, chocolates, biscuits amma banda kayan abinci kuma banda kudi, haka rule din makarantar yake. Mommy tana damuwa idan taga yadda Hafsat ta rame, in ta tambayeta dalili sai ta saka mata kuka tace ita gida zata tafi, ni kuwa sai inyi ta kallon ta ina mamakin wai ita menene matsalar ta, saboda ni dadi make ji tamkar an saka ni a aljanna. Daddy ya lura da yadda nake jin dadin school kuma ya bani kwarin gwuiwa tare da bani study tips yadda zan fi gane karatu sosai. Sai ya zama na da teacher ya fara mana topic inna shiga library sai na san almost everything da topic din ya kunsa, in na shiga aji kuwa na fara zabgawa teacher tambayoyi har sai yace min ya isa haka. Teachers din mu are very qualified dan haka bana samun matsala dasu, suna encouraging dina most of the times kuma suna jin dadin koyar dani.
Ban dade a school din ba na yi suna, kowa ya san Moon, daga staff har students kuma da yawan su suna sona saboda duk wanda na gani sai na yi masa magana kuma duk ‘yan class din mu kawayena ne banda Hafsat. A class din mu wadda bata iya wani homework ba guri na suke zuwa in koya musu, sam bani da kyashi kuma bani da rowa, wannan shi ya karomin farin jini.
Sai da mukayi hutun first term sannan nasan cewa na yi missing gida, ina shiga gidan da gudu naje na rungume mommy ina hawaye, ina ganin yaya Habeeb na saki mommy na tafi gurinsa da gudu, shima da saurinsa ya tare ni tare da rungume ni a jikinsa kamar zayyi kukan shima. Dama ya Walid shine ya dauko mu. A cikin satin da muka zo gida mommy ta shirya mana tafiya Russia gurin daddy, lokacin yana can, daada kadai muka bari a gidan da masu aiki. Munji dadin holiday n sosai, duk da sanyin kasar amma munyi enjoying kanmu tare da family n mu. Hafsat ta ware dan har ‘Yar kiba tayi abinta.
Bayan hutun mu ya kare ne akasha drama, dan ba Hafsat kadai ba ni kaina cewa na yi bazan koma ba sai dai a mayar damu day school. Mommy kuwa ta goya mana baya. A dole Daddy ya dauko hutu ya taho Nigeria tare damu, sai da ya kai mu har school. Kamar yadda kowa yayi tsammani ni ce na dauki first position, Hafsat kuma second. Daddy yayi murna sosai ya saka mana albarka sannan ya kara karfafa mana guiwa akan karatun mu. A haka muna rabu dashi yana muna hawaye shi kuma yana mana blowing kisses.

 

Episode Four: Moon’s Sister

Kwanci tashi har muka gama J.S 1. Sanda za muyi sessional examination ban manta da alkawarin da nayiwa Hafsat ba, dan haka da akazo exams sai inta amsa questions wrongly, wata kuma sai inyi jagwalgwalo yadda ba zai karantu ba, wata question din ma sai in barta blank inyi submitting. Na daina zuwa library sam -sam sai dai in kwanta inyi ta baccina. Rannan ina bacci da yamma Hafsat ta dawo daga karatu, ta daka min duka a cinya na tashi a zumbur a tsorace, ta hade rai sosai ta kalleni tace ” what is wrong with u?” Na tsura mata ina mamakin nuna caring dinta. Ta taba jikina kamar mai testing temperature dina race “are u sick?” Na girgiza mata kai. “U are behaving strangely this past few days, what is wrong with u? Ta sake tambaya ta tana me tsareni da manyan idanunta, na hadiye yawun tsoro nace mata ” am OK, am just too sleepy these days” race “but u know we have exams tomorrow morning right?” Nave mata “I have already read enough before the exams sister, don’t worry, I will be OK” na yi murmushin tsokana na kuma ce mata ” when did u start caring? This is so unlike u? Tayi murmushi itama tare da bude dan karamin bed side fridge dinmu, ta dauko lemo ta zauna a gefen gadon ta sannan ta kalleni tana yamutsa fuska tace ” gobe ma rana ce and besides, I just asked to know what to tell dad in case something happened. U can do as u wish for all I care” Daga haka ta bude drink dinta ta fara sha.
Babu wanda yasan me make aikatawa a exams hall ba, har sai da mukayi hutu, muna ‘yalleman principal dinmu ta kira dad a waya ta gaya masa cewa something is wrong, malamai sun kawo mata complaint a kaina cewa duk na fadi papers dina kuma daga gani ansan intentionally nayi. Muna zaune a dakin inna, ina kwance a cinyar inna ina zuba mata shagaba ita kuma Hafsat tana kan kujera tana karatun wani novel, sai ga daddy ya shigo. Daga ganinsa nasan cewa something is wrong, nan take cikina ya bada kululu saboda nasan abinda na aikata aschool. Ya zauna a nutse ya gaida inna sannan mu kuma muka gaishe shi duka. Direct ya juyo yana kallona da serious voice yace min” Maimoon mai yasa kika kayar da kanki a exams? ” nan na fara inda inda, nace “am..I ..am sorry daddy, dan Allah kar ka dakeni wallahi bazan karaba?” Hafsat ta ajiye littafin hannunta tana kallon daddy cike da mamaki. Inna ta jawoni jikin ta tana bubbuga bayana a hankali tana tambayar daddy me ya faru cikin harshen fulatanci. Inda shi kuma ya kwashe duk yadda sukayi da principal din mu ya gaya mata, ya kara da cewa ” ni ba dukanta zanyi ba. I just want to know why tayi hakan cos principal dinsu tana suggesting a mayar da ita school ta sake re-writing duk papers dinta. Cikin muryar lallami inna ta kalleni tace” memu? Me yasa kika aikata hakan? Ke meson karatu kuma kikayi haka?” Na juya na kalli Hafsat ina hawaye, ita kuma ta harare ni tare da cewa ” karki kalleni, I did my best inga kinyi karatu kika cemin u have read enough before exams” ta kalli daddy tace masa ” dad kullum bacci take yi bata karatu, innayi mata magana tayi min rashin kunya, God is my witness, I tried my best” tana gama fadin haka ta koma tayi kwanciyar ta. Nan na lura kowa ni take kallo ana jiran amsata. Ni abinda ya bani mamaki shine yadda suka manta da alkawarin da nayiwa Hafsat farkon sakamu a makaranta. Daddy yaga bani da niyyar magana sai ya fara lalllabani da cewa ”
I know u Moon, nasan koda baki yi karatu ba zaki iya cin exams dinki, and your principal said what u did looks intentional. I just want to know why ”
“I did it for Hafsat” nace a hankali, ” I want her to get ahead of me, I promised her zanyi repeating js1, I was just keeping my promise ” shiru dakin yayi kowa yana saurarena, cikin kuka naci gaba da cewa” Hafsat ba ta sona, bata son kasancewarmu a aji daya, she is always sad and lonely saboda duk ajinmu kawayena ne ita kuma bata son ta zama friend dina, I just want her to be happy “.
A lokacin su mommy suka shigo falon ita da yaya Walid da Faruk, kallo ta bimu dashi daya bayan daya sannan ta zauna tana tambayar daddy menene yake faruwa, shiru yayi bai amsa mata ba sai inna ce ta fada mata brief abinda ya faru. A take mommy ta day zafi, daga ni har Hafsat din ta hada ta wanke mu tas. Dama tasan halin Hafsat amma bata dauka har a school bata kulani ba. “She is your only sister, me yasa ba zaki so ta ba? Me yayi miki a rayuwa?” Ta juyo kaina ” and you little mouse, ta yaya zakiyi ki yi asarar shekara guda ta rayuwar ki just saboda kina so ki raba class da ‘Yar uwarki, why didn’t you tell me or your father about what is happening so that we can do something about it, we can put u in separate schools or something. Mommy fada take yi kamar zata ari baki har sai da daddy ya koma shine mai bata hakuri, ita mommy takaicinta shine wai ace “ya’yanta mata su biyu kadai da Allah ya bata kuma ace wai basa jituwa. If we didn’t look after each other, who will look after us?
Sai da kowa yayi shiru sannan daddy ya fara magana:
“tun farko dama nasan basa shiri? Kuma me Hafsat kece fitinanniya. Wannan shine dalilin da yasa na kaiku boarding kuma bace a sakaku a class daya daki daya. Nayi tunanin in sun zauna tare a inda basu da kowa zasu hada kansu, banyi tunanin hakan da nayi zai kara wa Hafsat jin zafin Moon ba. Kuma Ku sani wannan ba zai saka in raba muku school ba. Yanzu abinda za’ayi shine, me Hafsat Ina so ki fada min menene matsalarki da moon?”
Da kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta dago kanta ta share hawayenta fara magana a hankali ” daddy ni bansan me nayi wa mutane ba, kowa yafi son moon, hatta Ku kai da mommy, daada, inna, baffa, yaya habeeb har faruk kowa moon yake so, komai aka tashi yi moon za’ace kuma bayan nice babba. Daddy ko waya kayo sai kace a baka moon kafin kace a baka ni even though I am the eldest” hawaye ne yake zuba a fuskar ta sosai ” a school, teachers dinmu kowa itace tashi haka friends, at school fa ana referring to me as Moon’s Sister as if am her shadow or some supporting actress. I am tired of all this dad, I want to get away from her, i want to start shining on my own, not shining in her light. I never know what she plan, I didn’t even think she can do something like this for me. I didn’t asked her to do it and now u are already blaming me for it. Kuka take yi sodai yanzu, ni kuwa sai na tashi naje na rungume ta muna kukan tare ina kuma rarrashinta. Saboda ni bana so inga mutum tana kuma ballanta ne Hafsat.
Murmushi Daddy yayi yace” duk naji complaints dinki Hafsat, kuma inaso ki sani, daga ni har mom dinku baku da banbanci ke da moon a gurinmu. Abinda baki fahimta ba shine halinku ba daya bane ke da moon, moon ta Fiji son mutane, ke kina da saurin fishi, kullum kina daki to waye zai biki daki ya kulaki. For example, yanzu tunda muka zo garin nan baki fita ba, inajin mom dinku tana yi miki fada dazu, duk kawunnanki da gwaggwanninki babu wanda kika je kika gaisar. Amma moon duk taje, wasu ma twice taje musu. So tell me, why won’t they ask of moon first than u? Duk sanda bans kasar nan Moon kullum sai ta kirani a phone din mom dinku amma ke sai in na nemeki. In kina so mutane su so ki to kema dole ne ki so mutane” nan dai daddy ya yi mana fada sosai. Ni kuma daddy yace min as punishment for what I did, bazan sake exams dina ba, tunda yasan in aka hada first, second and third term scores dina aka day average to bazan yi repeating ba. Inna ma yayi mana fada sosai akan zumunci da kaunar juna kuma da alama fadan ya shige mu Dan tun kafin muyi resuming school na fara ganin chanji daga Hafsat.

See also  Shagalalliya Hausa Novels Complete

 

Episode five: The Strangers

Bayan shekara uku
Haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jindadi da gata. Daddy yana ta samun ci gaba, yana ci gaba da harkar ambassadorship dinsa kuma yana visiting lecturer a Oxford. Ya Walid ya kammala sec sch dinsa inda Daddy ya tura shi Oxford yake karatun degree dinsa a fannin engineering. Ya Habeeb yana ss3, Hafsat dani kuma muna ss2.

Yaune second day of resumption kuma kamar yadda al’adar school din take, yaune ake gabatar da speech and prize giving. Mommy, ya Habeeb, daada da Faruk duk sunzo mana, suna zaune a gurinsu na musamman a side din parents. Ni da Hafsat da babbar kawata Amira munyi kwalliyar mu dai dai misali, muka fito gurin taron. Abinda ya bamu mamaki shine ganin wadansu mutane su biyar da kayan NYSC a jikinsu a zaune a bakin hall din taron. Tsayawa nayi ina kallonsu da mamaki saboda tunda muke a school din ba’a taba daukan coppers sunyi service anan ba, ko teachers din ma ba kowa ake turowa ba, sai very qualified teachers wadanda suka san me sukeyi. A hankali na furta ” this doesn’t look good ” amma ga mamaki na sai naga duk sun juyo suna kallon mu alamar sunji abinda na fada. Kunya ce ta kamani, yayinda Hafsat ta tabe baki tace” I guess there is a first time for everything ” tana fadin haka tayi gaba tare da fizgar hannuna, babu shiri ni da Amira muka bita a baya.
A yanzu kam Hafsat zan iya cewa ta zama budurwa, dan inka ganta ba zaka ce she is just fifteen years ba, ni kuma lokacin ina fourteen amma still bani da girman jiki sai tsaho shima ba sosai ba. Hafsat kuwa masha Allah, dan koni da nake mace wani lokacin tsayawa nakeyi inyi ta kallonta. Fatarta bata kai tawa haske ba amma fa a murje take tana daukan ido, ga laushi. Hancinta yafi nawa tsaho kamar yadda fuskarta ma tafi tawa tsawo. Idanuwanta dara dara farare tas, bakinta mai dan fadi wanda yake dauke da full lips shi kansa abin kallo ne. Kirjinta a chike yake taf haka hips dinta wanda yasa dole mommy ta dinka mata dogayen hijabs saboda in tana tafiya gaba daya jikin ta rawa yake yi. Hafsat mai class ce sosai, ba kowa take yiwa magana ba ballantana kaga dariyarta, amma in tayi dariya wani one sided dimple ne da ita ga kuma jerarrun hakora farare tas abin sha’awa. Ni kuwa mostly English wears nake Takawa saboda nafi feeling comfortable a cikin su. Kuma babu mai yi min magana saboda bani da komai a jiki na sai kyan fuska, wannan kuwa mutane da yawa sukance nafi Hafsat amma ni kam ban yarda ba, a ganina yawan murmushi na ne yasa ake ganin kyau na. Saboda shi murmushi ado ne musamman a gurin mace.
Muna shiga hall din gurin su mommy muka je muka gaishesu sannan muka je muka gaida Maman Amira muka tafi seats dinmu muka zazzauna, saboda an kusa fara taron. Kamar yadda aka saba, bayan bude taro da addu’ah sai aka fara gabatar da jawabai. Hafsat ta dauko novel dinta ta dora akan chinyarta ta fara karantawa ni kuma nayi tagumi da hannu bibbiyu ina sauraren speeches din daki daki. Sai da aka gama sannan aka kirawo passing head girl ta gabatar da farewell speech on behalf of the graduands. Lokacin har kuka nayi saboda tunanin shi kenan bazan sake ganin suba. Hafsat kuwa bama tasan me akeyi ba, sai da taji ina sheshahekar kuka sannan ta dago kanta ta kalleni ta kalli stage sai kuma tayi tsaki ta cigaba da karatun ta. Sai da aka fara rabon gifts sannan ta dago kanta ta rufe littafin da take karantawa ta mayar da hankalinta kan stage. A kayi ta kiran mutane ana basu gifts sannan aka zo kan set din mu. Kamar duk shekara, ni aka bawa overall san nan Hafsat second. Sai da aka gama rabon gifts sannan senior master ya hau kan stage ya fara announcement ” I know all of u notice some strangers wearing strange clothes here” akayi dariya gaba daya, yaci gaba da cewa” they are NYSC members, they are sent here because the are the best in their various fields. The NYSC board wants this school to start participating in the scheme, that is why they sent this coppers to work with us. I hope you students will give them your maximum cooperation ” daga nan sai ya fara kiran su daya bayan daya suna gabatar da kansu tare da fadin subjects din da zasu ke dauka da kuma classes din da zasu dauka. Tunda suka fara naji gabana yana faduwa, haka kawai naji jikina yana bani cewa something not so good is going to happen. Ina cikin haka naji wani daga cikinsu yace” my name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun, from Ibadan. I will be taking SS2 mathematics and geography.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda nayi ta maimaitawa a zuciyata. Ji nayi tamkar an juya min dukkan plans dina na rayuwa ta. Mathematics is my best subject, maths teacher din mu is my best teacher, yaya za’ayi a chanja min teacher a hada ni da inexperienced copper? Ji nayi tamkar inbi su mommy mu koma gida saboda ji nayi gaba daya makarantar ta fita daga kaina. Ban kuma fahimtar me ake ciki ba saiji nayi ana hayaniya alamar an tashi daga taron. Cikin sanyin jiki na dauki gifts dina na tafi gurin mommy na kai mata, haka ma Hafsat. Mommy tana gani na tasan something is wrong, tana tambaya ta kuwa na fara yi mata bayani. Mommy akwai daukan zafi dan haka nan da nan ta jamu sai office din senior master ta fara yi masa bayani akan cewa tun da muna senior class bai kamata a dauki subject as important as mathematics a bawa copper ba, kamata yayi ace an bar coppers a junior classes. Murmushi yayi tare da cewa ” na fahimci complaints dinki Ma, kuma insha Allah in ya fara daukan su in har sunga akwai problem, ina encouraging dinsu su zo su yi complaining. But first they need to give him a chance. We will all need a chance one day in our lives, one way or another”. Da haka muka fito daga office din, mommy tana encouraging din mu akan as soon as muka ga bama gane teaching dinsa mu zo muyi complain. In ba’a dau mataki ba in tazo mana visiting mu gaya mata, in yaso sai tayi wa daddy magana yazo da kansa yayi solving issue din.

 

Episode six: The Challenge

Nidai har ga Allah wannan hukuncin baiyi min dadi ba, saboda haka kawai naji raina baya son copper dinnan, he is too young to teach us a ganina. Hafsat kuwa sai na lura babu abinda ya dame ta. Da nayi mata magana sai cewa tayi “laa ni ban wani damu bafa, musamman akan geography, wancan teacher din ya fiya bayar da note, kin san ni kuma bana son note” (Yar Hutu). Unlucky for me, washe gari muna da geography. Tun safe naji raina ya baci dan ma bashine first period ba,sai munyi biology sannan zamuyi shi. Tom teacher din biology yana gama yi mana sai ya bamu assignment, yana fita sai na dauko assignment dina na fara sai naji hayaniya a class anata leka window. Na tambayi Amira nace “menene wai ake wannan leken” sai tayi dariya tace ” wannan yaron ne ya taho zai koya mana geography” nayi tsaki nace “zai koya musu dai” na ci gaba da zanen da nakeyi na digestive system dan shine assignment din da biology teacher ya bayar. Hafsat naji tace “sabon shiga, ko dan late coming dinnan ma abar mutane su huta baza’ayi ba”. Tana gama fada yana shigowa kuma na tabbatar cewa yaji abinda tace, dariya ce ta kubce min ganin yadda Hafsat ta wani maze kamar ba ita ce tayi maganar ba. Ina kallonsa ta gefen ido na. Ya cire uniform din NYSC ya saka personal shirt da wando amma ya dora p-cap din NYSC din a kansa. Ban wani kalleshi sosai ba na maida hankali na akan zanen da nake yi. Ya jima a tsaye yana kallon mu daya bayan daya sannan a hankali yace “don’t u guys know how to greet? Duk class din muka mike a tare, tare da cewa ” good morning sir” ya jima yana binmu da kallo sannan yace “sit down” inajin Hafsat a hankali tace “finally” Nayi murmushi na zauna tare da ci gaba da zane na. Takowa yayi a hankali yazo gabana ya tsaya yace “why are u laughing?” Na dago kaina na kalle shi ido cikin ido nace ” I am not laughing sir, I was smiling”. “Hmm” shine abinda yace sannan ya kunna board, da yake smart board muke amfani dashi. Ya saka flash drive dinsa na nemo slides din da zai yi mana ranar ya kunna. Ni kuma ina ganin haka na cigaba da zane na. Inajinsa yace “our topic for today is rocks and their origin”. Sannan yayi tambaya “who knows what this is?” Ban dago kaina ba ballantana inga abinda yake tambaya akai saboda ina expecting wani a ajin ya bada amsa, amma ga mamaki na sai naji shiru babu wanda yayi magana. Jikina ne ya bani ana kallona, na daga kai sai na ganshi a tsaye a kaina “miss smiler, we are trying to have a class here” yace min ” can you please, out of the goodness of your heart, tell me what this is?”. Ya fada yana nuna board, araina nace lallai wannan mutumin ya raina min hankali. Ya dan bude ido yace “the picture is displayed on the board, miss smiler, not here” ya sake fada yana nuna kansa. Dariya najiyo kasa-kasa daga bayana sannan na fahinci cewa kallonsa nake tayi. A hankali na janye idona daga kansa. Kallo daya nayi wa hoton black shiny stone din da yayi displaying a board, na dauke kaina. Na mai da dubana kan assignment dina tare da daukan pencil dina na cigaba da zanen da nake yi. A hankali nayi magana nace ” that’s obsidian sir”. Shi kansa da yake kusa dani baiji abinda nace ba, dan haka ya sunkuyo da kansa yace “can you PLEASE, raise your voice a little bit?” Take naji raina na sake baci. “PLEASE” Ya sake cewa da muryar challenge. Dariya na sake ji saga baya na. Ni kuma har lokacin zane na nakeyi. Har ya juya zai koma gurin board sai na daga murya ta nace ” That is Obsidian ” Chak naga ya tsaya sannan a hankali ya dawo inda nake zaune ina zane na yace. “Tell me more” murmushi nayi sannnan na fara kwararo masa bayani tun daga kan yadda earth core take da yadda rocks suke melting su zama lava, yadda mantle da crust suke budewa har lava din ta fito earth surface. Daga nan na koma kan bayanin different types of cooling and solidification na lava din yadda yake producing different kinds of rocks. Sannan na dawo kan shi obsidian din, cooling process din da yake forming dinshi, dalilin da yasa yake black and shiny, composition dinsa, life span dinsa da amfanin sa a gurin mutane. Nafi 30minutes ina magana kuma at the same time ina cigaba da drawing dina. Tunda na fara magana ajin yayi tsit babu wanda yayi magana har na gama. Gamawa ta yayi dai dai da gama drawing dina. Sai da na karewa drawing dina kallo na tabbatar na gama sannan na dago kaina na kalle shi ido cikin ido tare da cewa ” Is there anything more you want to know, SIR?” Na fadi kalmar sir din nima cikin challenge. Sai da wajen 30sec ta wuce sannan ya iya magana yace “wow, that is very correct. No, there is nothing more. U have said it all”.
Kamar hadin baki, yana gama fadin haka aka buga bell din break. Books din mu duk muka rufe muka fice daga class din. Sai da mukayi nisa sannan na juyo na kallo class din mu naga yana nan a tsaye a inda muka barshi ya saka hannayensa cikin aljihun wandon sa yana kallon kasa. “He must be feeling like an idiot” na fada ina murmushi. Amira tace ” Ai kin wanke mana shi tas, I wonder ta yaya zai yi facing din mu tomorrow morning for maths” Hafsat tace “and they said I am the cruel one”. Dariya muka yi muka tafa ni da ita, nace “ai ba cruelty bane, he asked me a question and I answered him. He then asked me to tell him more, so I told him more” wata kawarmu Hasiya tayi joining din mu tace “baki da kirki Moon. You told him more and more. By the way, how do u know so much? Ni dai nasan ba’ayi mana duk wannan a aji ba” Nayi murmushi nace mata a cikin holiday na karanta, nasan za muyi shi a wannan term din. Nayi forming note a kan shi, in kina so kizo ki karba ki copying ” tayi min godiya ta wuce. Amira tace “Tabdi ai ni babu abinda zai saka inyi karatu a cikin hutu, hutu fa akace, we are suppose to huta a cikin hutu”

Episode Seven: The Thin Tall Man

Washe gari first period muke da mathematics. Dan haka tunda na shirya nayi breakfast sai na dauki jotterta, calculator, sannan na duba syllabus naga abinda ya kamata muyi yau sannan na fice sai library. Ina zuwa na tarar librarian din ma zuwanta kenan. Ko gama cleaning library din ba’ayi ba. Na samu guri na jira har suka gama sannan na shiga. Miss Martha, librarian din mu ta tambayeni ya akayi banje class ba, na amsa mata da cewa teacher din mu bayanan kuma inada assignment da nake so in karasa. Ina shiga mathematics section na wuce, na debo textbooks din calculus har uku sannan na samu secluded guri na zauna na fara calculations dina hankalina a kwance. Saboda ina ganin a haka sai nafi ganewa akan ace wannan yaron ne zai koya min. Double period ce damu dan haka a lissafina zaiyi one hour 20min. Ina yi ina duba agogon hannuna har naga one hour ta wuce saura 20mins kenan. Hankali na gaba daya yana kan calculations dina saboda sosai nake jin dadin product rule din da nake yi a lokacin. Ji nayi tamkar ana kallona, da sauri na dago kaina tare da cire earpiece din kunnena. Ido muka hada dashi ga mamaki na sai naga ya sakar min murmushi. Daga dukkan alama ya jima yana kallona. Nayi saurin dauke kaina tare da sunkuyar da ido na kasa ina mamakin ganin shi a nan bayan nasan ya kamata ace yana class dinmu yana koya musu maths. “Mind if I join” ya fada cikin muryarsa mai sanyi. Ba tare da na sake kallonsa ba na ce “no”. Kujerar kusa dani ya ja ya zauna. Ta ke naji na shaki kamshin sa. Na dan matsar da kujera ta kadan saboda kafadan shi da naji yana taba tawa. A hankali ya fara yi min magana wanda na tabbatar da ace da akwai mutun a kusa dani bazai ji me yake cewa ba. ” Why aren’t you in class” “am sorry” na fada a takaice. “Sorry for what” ya fada tare da adjusting kujerar sa yadda zai fuskance ni sosai, na kara jan kujerata baya sannan nace “for not attending your class”. Murmushi mai sauti yayi sannan yace” it is not my class, it is OUR class, we are all suppose to be participating in it”. Yayi shiru sannan ya kara da cewa ” by the way, we miss u in class today. The class was exciting though, but I thought it would have been more exciting if u were there. So I asked of u and was told to check the library. And here u are. So, why are u here?” Ya tambaya yana kallon cikin idona. Na dauke kaina ina inda inda cike da jin kunyar abinda nayi. Ya saka hannunsa ya juyo da fuskata gare shi muke kallon juna, cikin muryar rada ya ce min “you think I am not good enough to teach you, right?” Kunya ce ta kamani, nayi sauri na kwace fuska ta daga hannunsa, nasa hannaye na na rufe idona cikin kunya nace masa “no” da dan karfi. Ga mamakina sai kawai naji ya kama dariya nima bansan sanda na fara dariyar ba. Sai da muka dena dariyar sannan ya dauki jotter din da take gabana tare da cewa ” let’s see what you have been doing for the past one hour” ban ce masa komai ba. Sai da ya gama studying abubuwan da nayi sannan yace ” wow, we were in class tying to solve some few problems while you are here already done with the term. Na zaro ido nace “am not done with the term sir, am not even close” ya rungume hannayensa a kirjinsa, abinda na lura cewa dabi’ar sa ce. Yace ” you are special, do you know that? Nayi sauri nace ” no sir, am not. Kawai dai ina da son karatu ne” na fada ina kokarin kare kaina. Kallona kawai ya tsaya yana yi chike da rashin fahimta. Sai a lokacin na kalleshi sosai. Ba bahaushe bane. Na sunkuyar da kaina. “What tribe are you?” Ya tambaye ni cikin sanyin murya wadda itama by now na fahimci hakan yanayinsa ne. “Fulani” nace ina wasa da ‘yan yatsuna. Yace ” but what you just spoke is Hausa, right?”. Nace “yes” yace ” so u are Hausa Fulani ” na girgiza kaina alamar a’a. Bai sake min wata tambayar ba. Can ya ce ” I am yaroba. I am from Ibadan, Oyo state. My name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun. Will you do me the honor of been my friend? ” ya miko min hannunsa alamar shaking. Na gado kaina na sake kallonsa. Fatarsa ba mai haske nace kamar tawa ba kuma baka bace ( wankan tarwada). Dogo ne sosai sannan siriri ne dan bashi da kiba sam amma kuma straight bayansa yake tsahonsa bai sa ya rankwafa ba. Yana da doguwar fuska da dogon hanci da yalwataccen gashin gira. Bakinsa mai dan fadi ne mai dauke da siraren lips wadanda a yanzu suke dauke da murmushi. Fuskarsa tana zagaye da siririn saje da dan karamin gemu a habarsa. Fararen glasses be sanye a idonsa wadanda suke lumsassu kamar na maijin bacci. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da cewa ” I am Fulani from Jigawa State. My name is Maimoon Muhammad Dikko. Yes, I will like to be your friend and I am sorry for missing OUR class today” ” it is OK friend” ya fada yana sauke hannunsa ganin bani da niyyar shaking dinsa. Agogo hannuna na kalla, ga mamakina sai naga next period har tayi nisa. Da sauri na mike ina harhada takarduna hankalina duk ya tashi. Shima ya mike tare da daukan jotter da nayi calculations yace ‘I will look this calculations over if you don’t mind” “no problem” nace ina sauri duk hankalina yayi class. A bakin kofa ya sameni ina signing out. Ina fita ya biyo baya na, sai a lokacin na sake lura da tsahonsa, dan gabaki daya na a kirjinsa na tsaya. “See u tomorrow” na fada bayan mun fita daga libraryn. “See u in CLASS tomorrow” yace yana jaddada Kalmar class din. Da sauri nayi gaba dan bana so ya cigaba da bata min lokaci tunda already nayi latti a class din English. Ina shiga Aunty grace ta fara tuhumata akan daga ina nake, inda ni kuma na bata amsa da cewa ina library ina assignment ban san cewa har lokaci ya wuce da yawa ba.
Saida aka fita break sannan na tambayi Hafsat ya akayi a lokacin maths. Ta be baki tayi tace “ina ruwanki, ke da kikayi tafiyarki kika barmu da wannan dogon mutumin” nace “sorry tare da langwabar dakai, ta harare ni ta dauke kai alamar har yanzu fushi takeyi. ” is he good? ” na tambayeta. Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace “you will find out tomorrow, we have him double period da safe” ” oh my God Moon, he is so good, ban taba enjoying mathematics irin na yau ba, I really did enjoy it. Wato dalla-dalla yake bin komai kuma sai ya tabbatar kowa ya gane sannan zai yi gaba. Gaskiya Moon kinyi missing ” inji Hasiya wacce ta dawo kusa da desk dina fuskar ta kamar gonar auduga. Na mike tsaye na dubi sauran ‘yan class nace “OK people, tomorrow, I will give the Thin Tall Man a chance” “Thin Tall Man?” suka kusan hada baki. Nace “yes” matter of factly, “baku ga yadda yake bane? I think the name fits him perfectly”. Dariya ajin ya dauka gaba daya, inda ni kuma na bawa Hafsat hannu muka kashe muna kyalkyala dariya. Amira na hango ta gefen idona fuskarta dauke da bacin rai.

See also  Mene Ne Yakesa Nono Su Zama Ƙanana

Episode Eight: The New Imam

Muna hostel da daddare Amira tazo dakin mu ta sameni nayi wanka ina shirin yin bacci, ta zauna a bakin gadona. Da yake yanzu mun zama seniors ba bunks ne damu ba. Still dakin mu daya da Hafsat da wadansu Christians su biyu Naomi da Abigail. Mu hudu ne a dakin mai dauke da gado hudu, lockers hudu da kujerun karatu kowacce da table dinta guda hudu, sai fridge guda biyu. Dakin babu tarkace da yawa da yake Hafsat akwai tsafta kuma duk ta fimu girman jiki hakan yasa ta zama kamar Senior din mu. Babu wanda ya isa yayi kazanta. In kaga Hafsat tana bamu order sai ka dauka ba class din mu daya ba. Muna da toilet din mu guda daya a dakin wanda muke sharing mu hudun, kuma kullum twice cleaners suke zuwa su wanke mana shi duk da ba wani datti yake yi ba. Masifar Hafsat ma ba zata barmu muyi kazantar ba.
Ina tsaye ina kallon fuskata a mudubin jikin locker din Abigail Amira ta shigo dakin sanye da dogon hijab har kasa tare da sallama. Ina ganinta nasan har ta kwanta ta taso. Ta cikin mudubin nake kallonta har ta zauna a kan gadona tace “kai Moon wannan bargon naki da laushi yake, wannan inna kwanta a kansa ai ba zan iya tashi daga bacci ba” na juyo ina fuskantar ta nace ‘ ko kina so in bar miki ne, u can take it if you want. Ina da wani” da sauri tace ” a’a wannan ai sai in kasa tashi sallah asuba” muka yi dariya baki daya. Hafsat dake kwance kan gadonta tana karanta novel tace “Amira wai da gaske yasaiyadin mu ya tafi umrah?” Amira tace “eh wallahi Hafsat, shine ma maganar da nazo muyi. Ya tafi umrah, sai nan da at least a month zai dawo. Na taho na zauna kusa da Amira nace ” to fa, yanzu me ake ciki kenan Amira? Waye zai ke janmu sallah kuma wa zai ke yi mana dori? Amira a lokacin itace mosque prefect dan haka duk wasu bayanai akan harkar addini a gurinta a ke samu. Tace “senior master dai yace they will find a solution. Maybe da assuba in muka je sallah zamu ga new face” na dafe kai nace “oh God, I don’t like these changes da muke samu wallahi” Amira ta gyara zama tace “change is sometimes good Moon. Dama maganar da nazo muyi kenan, karki damu kanki da wadanna changes din har su zo suyi affecting dinki negatively, please Moon, give the change a chance, ki daure, you might even like it. Bana so gobe idan munje masjid kinga new imam ki yi loosing interest akan karatun ki. Kinga kun kusa sauka ke da Hafsat. Kada kizo karatun ki ya koma baya kuma. Muka kalli juna nida Hafsa wacce yayi her usual side looped smile tare da whispering “she likes you” na tashi daga dan kashingidar da nayi nace “I like you too Amira. Kuma insha Allah babu abinda zai samu karatu na, besides, I have u”. Amira tayi sauka tun kafin tazo school din. Shi yasa run muna jss ni da Hafsat muke daukan karatu a gurinta. Tana dariya ta mike tana cewa “ni din bayan in muna karatun wasa kike yi. Da haka ta mike tare da wishing din mu good night, tayi sallama dasu Abigail sannan ta tafi dakinsu
Ajiyar zuciya nayi nayi rigingine ina tunano abubuwan da suka faru a ranar. Na fahimci cewa abinda nayi ban kyauta ba. Ya kamata in bawa Thin Tall Man chance kamar yadda Amira ta fada kafin in ce bana son teaching dinsa. Abinda nayi na kin shiga class dinsa is very wrong, za’a iya furnishing dina akan hakan. Amma duk da haka bai nuna min bacin ransa ba sai ma neman sulhu da yayi dani. Kafin inyi bacci ranar sai da nayi alkawarin insha Allahu gobe zanyi making up for my mistakes.
Washegari kuwa kamar yadda muka yi tsammani hakane ya faru. Mukaji muryar diff liman yana jan sallah. Muka yi joining har aka idar sannan muka tafi class din da ake mana islamiyya. Muna zazzaune muna bitar karatun mu na baya sai gashi ya shigo ajin. Duk da cewa akwai duhun assuba amma class din tar yake da fluorescent light wacce take a kunne. Kallonsa na tsaya yi cikin mamaki. It is the thin tall man. Jallabiya ce a jikin sa ash color sai bakin dogon wando da bakar hula a kansa. Idonsa babu glasses. Ya shigo ya rufe kofar tare da jingina a jikinta, ya ringume hannayensa a kirjisa tamkar mai jin sanyi. Daya bayan daya ya ringa binmu da kallo har idonsa ya kawo kaina, muna hada ido nayi saurin sunkuyar da ido na kasa. Gyaran murya yayi na dago kaina kawai sai naga ya yi min murmushi nima kuma sai na samu kaina da yi masa murmushi. Na sake sunkuyar da kaina kasa a karo na biyu. Ya sake yin gyaran murya tare da cewa “I was asked by the senior master to guide you through your Islamic studies before your mu’allim returns from his pilgrimage” ya tako a hankali ya jingina da jikin board yana facing din mu sannan ya cigaba da cewa “I don’t know how you guys do it, do u have a class monitor or something?” Duk muka amsa masa da “yes” sannan ya bukaci da ta tashi tayi masa bayanin yadda tsarin karatun mu yake. Nan Amira ta tashi cikin nutsuwa ta fara yi masa bayani dalla dalla tare da nuna masa time table din mu. Yana sauraronta attentively yana gyada kai alamar fahimta. Sai da ta gama sannan yace ” with your permission, I will like to make some changes. Instead of group progression I will like it to be individual so that we will carry everyone along. Because of the time factor, we will add night classes to the early morning ones so that we will have enough time. I will discuss this with your Senior master to see if its OK to have the night classes”. Ya zagayo gabana ya dauki alqur’anin da yake bude a gaba na ya duba inda muka tsaya sannan ya mayar ya ajiye yace ” I don’t think we can start today, the time has already run out, we will insha Allah start tomorrow. Maassalam to u all” duk ajin suka amsa masa da “bissalam” banda ni wacce haka kawai naji na zama uncomportable saboda tsayawar da yayi a kusa da seat dina. Duk iskar da zan shaka sai na shaki kamshin jikinsa da scent din after shave dinsa.

 

Episode Nine: Give Me a Chance

Geography lecture din da muka yi was very interesting. Sai yanzu na fahimci abinda Hasiya take nufi lokacin da tace yana bin komai dalla-dalla. He makes sure He carries everybody along. Yana making references da abubuwan da na fada rannan yana kara buda su dayi mana bayani using simple terms wanda ko the most stupidest person zai gane. Anan na kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle, bashi da hayaniya sam.
Toward the end of the class sai ya bamu classwork, kowa ya rubuta abinda ya fahimta a game da topic din yau for 10mins. Kowa ya dauko takarda ya fara rubutu, ni kuma na duba takarduna na rasa fullscap sheet, sai na juyo gurin Hafsat nayi mata alama da hannu akan ta bani paper, take mutuniyar tawa sai ta makale kafada tare da murguda baki. Takaici ya ishe ni gashi time yana tafiya. Sai na juya gurin Amira. Kafin Amira ta fallo min sai naga an ajiye min paper a gaba na, na daga kai na kalleshi na ce “thank you sir” ya amsa da “don’t mention, what are friends for” tare da yi min irin kallon nan na ‘kin tuna’. Nayi murmushi nima na fara rubutu. Ga mamaki na sai na ganshi ya zauna akan desk dina kusa da takardar da nake rubutu a ciki. Lokaci daya wannan special kamshin nasa ya ziyarci hancina, naji wani iri a jiki na tun daga kaina har zuwa yatsun kafata, nan tubutun ya gagareni dan duk ideas dina guduwa sukayi suka barni na kasa hada koda cikakken sentence ne. Na saba jin masculine scent a wajan su ya Walid but it never have this effect on me, nashi is like special, it tells me that he is very much male. Na zama very uncomportable har absentmindedly na fara fidgeting da kasan hijab dina.
A hankali ya sunkuyo da kansa sai tin kunnena, unexpectedly naji yayi min magana a kunne yace “am I making you uncomportable?” Ya fada in a very low whisper. A firgice na dago kaina sai ga idona tsaf cikin nasa with his face few inches from mine. In that instance da muka hada ido dashi, everything froze, me, him, time, the class and even my heartbeat. Ido na ya rufe bana ganin komai, kunne na ya toshe bana jin komai. A cikin wadannan seconds din (or maybe minutes, I don’t know), babu abinda yayi existing a duniya ta sai shi, only him. Fuskarsa kadai nake gani, kamshinsa kadai nake shaka. Apart from him komai ya zama blank. A hankali na fara jin muryar Hafsat tana cewa ” sir, sir, sir” sai muryar kuma ta fara karfi sannan ta zama tamkar kara a kunnena. Nayi blinking once, twice sai a sannan common sense dina ya fara dawo wa, sai a sannan na fahimci abinda ya faru. We have been staring at each other for a while (I don’t know for how long). Take naji tamkar kasa ta tsage in shige ciki, na dauke fuskata da sauri zuwa daya side din. Sannan na lura cewa kusan duk ‘yan class din mu suke kallo. Hafsat naji ta sake cewa “sir” da karfi, daga jin muryar ta nasan cewa she is really angry. Yau na san na shiga uku. What is happening to me? What just happened? Murya can kasa naji yace ” yes, what is it?” “I am through sir” ” through with what?” Ya tambaya har yanzu muryarsa bata dawo dai dai ba kuma clearly kansa ma bai dawo dai dai ba. “Through with the class work sir, you gave us classwork, remember?” Ta fada tamkar mai shirin tashi zama, “ohhh” shine abinda kawai yace yana shafa kansa. Sai kuma ya mike ya kama hanyar fita yana cewa “keep it with u. I will collect it tomorrow” daga haka ya fice ba tare da ya juyo ba, ba kuma tare da ya dauki glasses din sa, handset da papers dinsa da ya ajiye akan podium ba.
Yana fita Hafsat ta zagayo gaba na tare da saka duk hannayenta biyu ta rike kugunta ta na kallona fuskarnan filled with fury ta fara yi min masifa ” were u flirting with the thin tall man ko idona ne yake min karya” na bita da kallo ina mamakin mai take nufi, I still don’t fully understand what happened, ni ina ganin kamar stroke na samu, for all I know I could be sick or something ” answer me” ta sake doka min tsawa. Kafin in bata amsa teacher din mu na physics ya shigo, a dole Hafsat ta zauna tare da zagaya hannun ta a wuyanta alamar I will kill you.
Muka gaishe shi, ya amsa da fara’arsa, ni dai duk jikina a sanyaye. Bayan mun zauna ne ya kalleni yace “Moon, what is wrong with u?” Hafsat nayi sauri tace ” help me ask her oo”. Da yake teacher din mai barkwanci ne Sai yayi dariya yace ” maybe the geography was so boring, worry not my dear, I will cheer you up with physics ” akayi dariya gaba daya. Sai a lokacin ya lura da kayan kan podium, yace ” clearly, the geography was boring to the teacher also, he forget his his things. Do u guys chase him out? ” aka sake dariya gaba daya tare da cewa “no, sir” yace ” OK, to brighten up our Moon, let’s send her on an errand to return this to the runaway teacher ” na sauri nace “I rather not” ina jin Hafsat a bayana tana cewa “good for you” Yace ” why not?” Sai kuma na kasa bashi amsa. Amira ta yi sauri tace “let me take it to him, sir” amma sai ya dage akan lallai ni zanje, a cewar sa it will help clear my head.
Ba yadda zanyi dole na karba na fita, ni yanzu bansan ma inda zan same shiba. Na dau hanyar staffroom. Na shiga naga bayanan, sai naga another copper a zaune yana marking some papers, na gaishe shi tare da tambayar whereabout of Mr Ibrahim, ya dago kansa ya kalleni tun daga kasa har sama with devilish smile on his face tare da cewa ” hello beauty, why are u looking for him? Na hade raina nace “is he around?” Ganin na bata rai sai ya zama serious yace “he is not around, but I can take message for him. My name is victor, Ibrahim and I share the same room” ” OK ” nace ” please give this to him, he left them in our class “Nace tare da ajiye kayan a gabansa.
Na juya na fita, in my mind ina godiya ga Allah da bayanan. Kaina a kasa ina tafiya naji nayi karo da mutum. Nayi sauri na matsa. Bana bukatar in kalli fuskarsa, kamshin da naji ya gamsr dani cewa shine. Cikin in ina nace “I brought your things” ” OK , thanks “ya bani amsa a takaice. Nayi sauri nace” I was asked to do so by our physics teacher ” OK ya sake cewa. Nayi gaba inajin haushin kaina, mai yasa nayi masa magana. Sai kuma naji ya kira sunana” Maimunatu” ban amsa ba kuma ban tsaya ba. Ya biyo ni da sauri yasha gaba na. Ga mamakina sai naga ya kama hannuna, nayi sauri nayi dago kaina na kalleshi, fuskarsa babu murmushin da na saba gani a ciki. Na bude baki na zance ya cika ni sai naji ya saka min wani abu a hannuna yace “this is for u” daga haka ya saki hannuna ya juya ya tafi. Na sauke idona a kan abinda yake hannuna sai naga ashe jotter tace da ya karba a library, a front page kusa da inda na rubuta sunana naga ya rubuta PLEASE, GIVE ME A CHANCE

See also  Mijin Novel Hausa Novel Complete

Episode Ten: I Don’t Know

Har na karasa class ina tunanin mai wadannan kalaman suke nufi. Give me a chance: a chance to do what? A chance to prove what? A take naji kaina ya fara ciwo. Ina shiga class din mu naga teacher din mu zaune akan teacher’s chair ya zabga uban tagumi da hannu bibbiyu sarcastically, na kalli ‘yan ajin naga suma duk sunyi mimicking abinda yayi, bansan lokacin da dariya ta kubce min ba. Yana ganina ya mike taye tare da cewa “ahh she is finally back” nan na fahimci tagumin duk na jira na ne. Ya tambayeni ko na same shi? Sai na samu kaina dayi masa karya cewa ban ganshi ba amma na bawa a mr Victor to give to him, which is partly true. Ina zama ya sake tambayata “are u really Ok? You look pale and not as bright as the moon you are. Make sure you go to the clinic during your break ” na amsa da yes sir. Da yake shi mutum ne mai barkwanci sai ya zamana kafin a fita break har na manta da duk wani abu da ya faru tsakanina da Ibrahim.

Har muka tashi ban kuma tunawa da maganar ba, sai da nazo ina hada books dina zamu tafi hostel sannan naga jotter dina da rubutun sa a front page, nayi saurin sakata a locker dina na rufe na jefa keys din a bag dina. Su Hafsat already dama suna jirana mu tafi. Tunda muka bar class Hafsat take min balbalin fada wai saina gaya mata me ya faru a class, nace mata i don’t know amma taki rabuwa dani. Har muka chi abinci, mukayi sallah, nayi wanka na shirya zan fita library ta sha gabana tace babu inda zanje sai na tsaya nayi mata bayani. Ita Hafsat bata san cewa nafi ta son sanin mai ya faru din ba. Kuma duk tambayoyin ta bani da amsa din su sam sam. Nan dai na koma na zauna nayi folding hannaye na a cinyata nace mata ” what do you want to know ?” Tace “menene tsakaninki da thin tall man?” nace “nothing more than what is between you and him” ” amma menene yasa dazu yake kallonki har ina tayi masa magana bai ji ba? Kuma ya akayi yasan sunan ki bayan bai tambayemu sunayen mu ba? “OK nace mata ina daga mata hannu alamar ya isa haka, sannan na bata labarin encounter din mu a library, na kara da cewa “ina tunanin anan yasan sunana, apart from that, babu wani abu a tsakanin mu.” Tayi frowning face dinta alamar tunani sannan ta girgiza kanta tace ” OK na yarda dake, for now, i just don’t want him looking at you like that” nayi murmushi na ce “my dear sister, ke fa kika taba cemin i can do what ever i want, babu uwanki” ta mike tsaye tana kallona tace ” i am your sister, and i don’t want any relationship between you and him” ta fada with finality.

A ranar da magrib muna zaune a daki na saka Hafsat a gaba da tsokana akan wani neighbor din yazo takanas saboda ya ga Hafsat amma tace ace masa ba zata zo ba. Ina ta tsokanarta tayi min banza sai ga Amira tazo, anan take sanar damu cewa senior master yayi approving night islamic class din mu, zamu fara yau da daddare dan haka mu shirya. Za’a keyi bayan sallar isha’i zuwa 9pm. Sannan ta kalleni da tsokana tace “saura ki sake tsuye mana malami” nayi dariya nace “not a chance, we have made our peace, yanzu ma a matsayin friends muke” Amira tace “so i noticed, friendship dinne ya kawo kallon dazu ko?” Na bata raina nace “don’t start there, kema kinsan in da akwai wani abu you will be the first to know ” tace “to Allah yasa, Just be careful my dear friend”
Amira ta bawa Hafsat shekara daya, ni kuma ta bani biyu. Kuma duk ta fimu hankali da nutsuwa. Tun ganin ta na farko da mommy tayi, tayi approving friendship din mu har ya zamanto ita da maman Amira sun fara kawance. Amira black beauty ce, bahaushiya ce usul, gentle ce kuma komai nata tanayinsa a tsare.
Alokacin da mukaje islamiyya ne nasha mamakin jin irin karatun Ibrahim. Ban taba jin kira’ar da ta yimin dadi irin tasa ba. Cikin sassanyar muryarsa yake kwararo mana karatu wanda nake jin shigarsa tun daga kunnuwana har ‘yan yatsun kafata, naso ace ya cigaba da karatun forever. Yana zuwa inda yake son tsayawa sai ya tsaya. Inajin wata a class din tana furta “masha Allah”. Nima masha Allah din na furta amma a zuciya ta, saboda wannan ba karamar baiwa bace ba daga Allah. Muka biya tare dashi sannan muka fara biya wa kow individually. Ga mamakina da akazo kaina bai nuna wani cewa ya sanni ba koya kira sunana ba. Da aka tashi shi ya fara fita sannan muka hada littattafan mu muka fito. Ni na fara fita a students saboda baccin da nake ji, na saba da baccin wuri. Ina tsaye a bakin kofa ina jiran su Hafsat ina ta faman zabga hamma naji scent din sa a gurin, na juyo amma banga kowa ba duk da jikina ya bani ana kallona. Gyaran murya naji yayi, nayi sauri na kalli side din da sound din ya fito anan naga silhouette n sa a jikin katanga. Gurin da duhu bana ganin fuskarsa amma na gane shine, ya rungume hannayensa a kirjinsa. Na juya kamar zan koma ajin sai yace “are you afraid of me? Do u think i might steal you? ” Na juyo ina kallon gurin da yake amma ban ce komai ba har ya sake cewa ” i just want to say good night to you. I will see you tomorrow morning ” ya juya da niyyar tafiya, nayi sauri nace “Why? ” ya dakata da tafiyar da yake yi ya juyo yana kallona, har yanzu amma yana cikin duhun bai fito cikin haske ba. Yace “why what? ” “why do u feel the need to stay in the shadows, get me alone and say goodnight to me?” Nayi maganar da dan karfi fiye da yadda nayi niyya. A hankali yace min “your friend is here ” nayi sauri na juya sai naga Amira a tsaye a verandah class din mu tana kallona da mamaki a fuskarta tace “moon ke da wa kike fada cikin daren nan” na juya na kalli inda yake, babu shi babu alamar sa, ya gudu. Idan har da gaske friendship yake nema mai yasa zai tsaya a cikin duhu yayi min magana, ya fito cikin haske mana kowa ya ganshi or better still yayi min magana mana a class a gaban kowa.
Muka kama hanyar hostel raina a bace. This guy is trying to play a game with me and i will teach him a lesson. To add peppe to my wound, muna cikin tafiya mukaji wadansu ‘yan ss3 suna hira a gaban mu. Hafsat da son gulma ta rike hannayen mu muke binsu a baya muna jin hirar su. “Gaskiya gayen nan ya hadu” “kema kin gani ashe? Ga kyau ga nutsuwa ga kamala, ga kuma ilmin addini dana boko” “ni muryarsa tafi komai burgeni, kuma daga ganinsa gentleman ne, komai nasa a nutse yake yi” “ke kinga idanunsa kuwa? Wayyo raina. Ai da naje biya karatu wani kallo da yayi min sai naji na manta a wacce surar muke gaba daya” suka kwashe da dariya suka tafa. “To ko dai ya yaba ne? In kuwa hakane mukam sai dai muce sambarka”
I heard enough, na cire hannuna a cikin na Hafsat nakara sauri na wuce su. Ina zuwa daki na cire kayana na shiga wanka. Sai da na fito naga Hafsat ta zage tana bawa su Abigail labarin abinda ya faru suna ta dariya. Wai ashe har plan suka shirya na yadda zasuyi masa magana akan yake yi musu extra lessons ta yadda zasu ja hankalin sa. Ina fitowa Hafsat ta nemi tayi involving dina a conversation din amma naki magana. Nayi adduoi na na kwanta. Bazan iya fasalta me nakeji a raina ba danni kaina bansan menene ba.
Washegari Thursday sam bamu hadu da Ibrahim ba tunda bamu da class dashi kuma ranar babu islamiyya. Ranar Friday na ganshi a assembly hall amma ban yarda mun hada ido ba. Ya saka complete NYSC kakin sa, ina kallonsa naji gabana ya fadi nayi saurin dauke kaina. Ranar ma bamu da class dinsa kuma still babu islamiyya. Muna cikin class da teacher din mu na chemistry sai kawai ga Ibrahim nan ya shigo kamar an jeho shi. Suka gaisa da malamin sannan yace “i want to see one of your students please” teacher din yace masa ba damuwa, but make it quick. Tunda naji yace yana son ganin wata nasan nice, ai kuwa ina dago kaina ya kalleni tare da nodding, ya fita. Bani da option dole na bi bayansa. A kasan wata bishiya ya tsaya nima na karasa kusa dashi na tsaya. Ban gaishe shi ba. Ya jima baiyi magana ba. He seems uncomfortable and out of words. Adam’s apple dinsa ya motsa amma still ya kasa magana. “Why am i here? ” na tambayeshi tare da katse shirun. “I don’t know ” yace yana shafa gashin kansa “OK, look, you asked why I stayed to say goodnight to you that day, and today you asked why I wanted to see you, the answer to both questions is I don’t know. I don’t seem to know anything anymore” na saki baki kawai ina kallonsa. Ya lura da irin kallon da nake masa sai ya hadiye wani mugun yawu yace “I am sorry, I must have sound like an idiot” “nayi sauri nace masa “no, you didn’t sound like an idiot but rather compused” ” yes i am compused, i have never been this compused in my entire life. Please tell me” ya sunkuyo da kansa dai dai fuskata yana kallon kwayar idona “what should I do? “Na kalli cikin idonsa nima, abinda na gani ne yasaka nayi saurin dauke kaina tare da cewa “i don’t know ”

Episode Eleven : The Protector

“You are a smart one, you must know something” kafin in bashi amsa naji Hafsat tama kwalla min kira daga class. Na juya na juya na ganta a kofar ajin ita da teacher din mu. “Good lord” Ibrahim ya fada tare da matsawa daga kusa dani sannan yace “please meet me in the library after school, please come” da haka ya juya ya fara tafiya, sai da yayi nisa sannan ya fahimci hanyar hostel yake tafiya, sannan ya juya kuma ya dau hanyar staff room. Ni kuma na koma class. Ina zuwa kofar class teacher fin mu ya fara tambayata me nayi wa copper din can. Nace masa babu komai. “But he seems agitated, are you sure you are not in trouble with him?” ” i am not sure sir, i have no idea what he was talking about” na amsa masa frankly. Ya jima yana kallona kuma ya fahimci iyakacin gaskiya ta nake fada masa, ya girgiza kanshi a hankali yace “just be careful Moon, if u ever feel like he is crossing the line with you, just report to me or any other senior staff” nace masa tom.

Har aka tashi daga school ban yanke shawarar ko zanje library gurin Ibrahim ba. Saida akayi ringing bell sannan na tuna cewa ban yanke shawara ba. Kamar Hafsat tasan tunanin da nakeyi sai naga ta zauna a kusa dani, na juyo na kalli fuskarta naga babu wasa a cikin ta. In a serious tone tace min “me yace miki dazu? ” na gane maganar da take yi kuma ga mamaki na sai na samu kaina da fada mata gaskiyar yadda mukayi da Ibrahim. Ta girgiza kanta alamar gamsuwa tace “i expect as much. Babu inda zakije, yau a hostel zakiyi karatun ma ko class ba, zaki zo ba ballantana library. Green snake under green grass kawai. Sumi sumi dashi kamar wani na Allah. Ni dama duk ustazan nan bana yadda dasu….. “. Duk da nasan Hafsat tana kokarin protecting dina ne amma sai na samu kaina da jin haushin maganganun da take fada akan Ibrahim. Na dakatar da ita nace “bafa wani abun ba yace min ba Hafsat, he just asked me to meet him in the library. It might be totally different from what you are thinking. Please Hafsat ki bar ni inje inji abinda zai ce” nayi ta lallaba Hafsat amma taki bari na inje. Haka ta tusa keyata har hostel. Ranar haka na wuni jikina da zuciya ta babu dadi. Ina tunanin ban kyauta ba dana barshi yana jira na, kuma deep inside me ina son inje din saboda insan me yake so dani, nima kuma in wanke duk wani kokwanto dake zuciya ta a game dashi. Amma Hafsat ta kasa ta tsare ta hanani sakat.
Washegari da assuba ina tashi gaba na yake ta faduwa saboda nasan yau dai dole zamu hadu da Ibrahim a islamiyya. Hafsat ta hade ranta sosai ta kora min warning akan koya yimin magana kar in kulashi. A haka muka je masallaci mukayi sallah sannnan muka tafi islamiyya. Muna zama sai gashi ya shigo. Na kasa daga kaina in kalleshi har muka gaishe shi duk ya ajin. Kawai sai ganin sa nayi ya zo ya tsaya a gaban seat dina yace “maimunatu” na daga kaina a hankali na kalleshi, bacin ran da na gani a idonsa shi yasa nayi saurin saukar da idona kasa ba tare da na amsa kiran da yayi min ba. “Maimunatu am talking to you ” ya sake cewa cikin tsawa-tsawa. Jikina ya fara karkarwa saboda tsoro, nace “am sorry sir ” “sorry for what? I clearly asked you to meet me after school yesterday but you didn’t. Why? ” kawai sai naji hawaye yana zubo min, sai na fara sheshshekar kuka, ni dama akwai saurin kuka. Tsayawa kawai yayi yana kallona da mamaki sannan yace “why are you crying? For God’s sake I only asked you a question” cikin fada yake min magana. Wani kukan na sake rushewa dashi, ni babu abinda bana so a rayuwata irin a yimin tsawa ko fada. Shi bai san cewa fadan da yake yi min shi ne ya ke sakani kuka ba. Hafsat ce tace masa “she was sick sir, that’s why she didn’t meet you in the library ” duk da kukan da nake yi sai da nayi mamakin yadda Hafsat ta shirga masa karya. Kuma na gane motive din ta, so take yace min in tafi hostel tun da bani da lafiya. Ya sunkuyo dai dai fuskar ta sannan cikin sanyin murya yace min “are u sick? Na girgiza kaina. “Do u want to go back to hostel? ” na sake girgiza kaina alamar a’a. “OK stop crying for God’s sake, or else I will have to send you back to hostel” ya fada da dan karfi wanda hakan yasaka na sake rushewa da wani kukan. Tsaki yayi sannan yace “OK, that’s it, u are going back to hostel” yana fadin haka Hafsat ta mike tare da kamoni kamar wata marar lafiya. Ya dakatar da ita tare da cewa “where are you going to? ” nan ta kama inda inda tana kokarin yi masa bayanin cewa rakani hostel zatayi. Shi kuma ya ce mata tunda nace lfy ta kalau ta barni inyi tafiya ta ni kadai ita kuma tayi karatun ta. Ta koma ta zauna tana zumburar baki, ni kuma na kama hanyar fita. Ina tajin surutan mutane a ajin nidai nayi tafiya ta. Na dan yi nisa da class din kenan naji takun mutun yana bina, ina juyawa na ganshi a kusa dani ya kamo hannuna ya jani da sauri zuwa wani class da babu kowa ya rufe ajin tare da tare bakin kofar. Duk wannan ya faru ne cikin seconds. Wani kukan na sake saka masa ina rokon sa “please let me go, i will never disobey you again, please let me go” kallona kawai yake cikin mamakin yadda nake ta rusa kuka. Ya rungume hannayensa a kirjinsa sannan yace ” do you want me to let you go? ” na gyada masa kai “then stop crying like a baby, for God’s sake I just walk out of my class just to talk to u. Why are you crying? What have I done to u? ” nayi shiru ina sheshshekar kuka, ya sake maimaita tambayarsa ” did i do u anything wrong “. “You are shouting at me” na amsa ina kara sautin kuka na. Dariya ya fara yi kasa kasa yana girgiza kansa ni kuma dariyar ta kara bani haushi, yaya bayan yayi min tsawa ina kuka kuma zai saka ni a gaba yana min dariya? Dan haka sai na rufe fuskata da hannayena biyu na kara rushewa da kuka. Ya tako a hankali ya tsaya agaba na sannan ya sunkuyo kansa dai dai kunne na yadda har inajin saukar munfashinsa a wuya na yace “I am sorry for shouting at you. I promise to never do it again ” na bude fuskata na turo baki ina goge hawayena da bayan hannuna. Ya chiro handkerchief a miko min, nasa hannu na karba na karasa goge fuskata dashi, sannan na daga kaina na kalleshi naga yana kallona yana murmushi. “OK cry cry baby, tell me why didn’t you come to the library yesterday? ” na kalli windon class din naga gari ya fara haske sannan na tuna cewa ya baro students suna jiran sa zai yi musu dori. Na kalle shi naga ni kawai yake kallo yana murmushi daga dukkan alama ya manta da ‘yan class din da suke jiransa. Nace masa “we, will talk about that later, now your students are waiting for u, time is running out ” ya danyi frowning face dinshi alamar tunani sannan yace “good lord! I totally forgot about them.” Ya shafa gashin kanshi sannan yace “just PROMISE that we will talk tomorrow ” na ce “not tomorrow sir, we will talk on Monday ” yace “why not tomorrow? ” Nace “I don’t want to be taking time from our Islamic class time. I will talk to u on Monday if u promise that you will not talk to me during our Islamic class ” yayi shiru yana kallona sannan yace “OK I promise “nayi murmushi nace masa OK. Daganan na bude kofar class din na fita na koma hostel.
Yayi keeping promise dinsa kuwa dan bai kuma yi min magana a islamiyya ba, karatu kawai mukeyi dashi mu tashi. Ranar monday muna da class dinsa kuma nasan dole zai ce min mu hadu a library after school. Yana shigowa bayan mun gaishe shi sai ya dauko wata ‘yar jotter ya rike yace yau discussion za’ayi, zaike mana tambayoyi muna amsawa. Kawai sai ya taho kan desk dina ya zauna kuma ya juyo yana facing dina kuma yana facing sauran ‘yan class din, tunda a front row nake. Nayi sauri na kalleshi sai ya sakar min murmushi, na sunkuyar da kaina kasa duk naji na takura. Yana ta questions dinsa sauran ‘yan class suna amsawa amma ni ban san ma me suke yi ba, saboda yadda yake zaune gab dani kuma duk numfashin dana shaka saina ji kamshinsa. Na rasa inda zan sa kaina. Chan ya ce min “Maimunatu are u OK ” sai da na dan firgita kadan saboda nayi nisa a cikin tunani, na manta ma a ina nake. Nace”yes sir, i am alright ” “are u sure” Hafsat ce tace ” I am sorry sir, but dont you think you are making her uncomfortable? ” gaba daya ajin akayi shiru yace mata “what makes you think I am making her uncomfortable? She is not complaining, is she? ” ta kalle shi ido cikin ido tace “i know she is uncomfortable because she is my little sister ” “ohhh” shine abinda Ibrahim yace sannan ya juyo ya kalleni ya sake komawa ya kalleta kamar mai comparing din mu, yayin da ita kuma ta tsare shi da ido.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top