Hausa Novels

Majnoon Complete Hausa Novels

Majnoon Complete Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Majnoon

MASOYANA

 

GABATARWA Bismilahirrahamaniraheem!, da sunan Allah mai Rahama mai jinkai tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S.A.W) da iyalansa da sahabban sa ameen, ya Allah Ina rokon yanda kabani ikon fara littafin nan lafiya ina rokon kabani ikon gama shi lafiya ameen.

 

TSOKACI

_Wannan littafi na rubuta shi don DON FADAKARWA da NISHA D’ANTARWA

Tareda ILIMANTARWA don haka ban rubutashi don cin zarafin wani ko wata ba so duk wanda yaga hali irin nashi to arashi ne nagode.

 

~TUKUICI~

 

Littafin ZAUJEE-MAJNUN gaba dayan sa tukuicine ga daukacin KU MASOYANA, aduk inda kuke afadin duniya Ina fatan alkairin Allah yakai maku, kusani inayin Ku irin babu adadi nan fa ai kundai gane ko lovers? nagode sosai

 

FREE PAGE

 

Bismilahirrahamaniraheem!!!

 

 

Kaduna state

misalin karfe 10:45am na ran monday, da gudu

wasu kyawawan bakak’en motoci ne guda uku suka shiga cikin babban filin jirgi saman nan dake garin kaduna north, ba tareda wani bata lokaci ba sukayi parking alokaci daya cike da kwarewa, wanda hakan yadauki hankali jama’ar dake harabar gurin, gaba daya lanbar motocin irin daya ne kamar yanda naga an rubutu da manya haruffa kamar haka BLUE 1 BLUE 2 BLUE 3,

 

Cikin nutsuwa

aka bud’e kofofin mota biyu alokaci daya wasu manyan mutane suka fito su shidda, kowace mota mutun uku kenan sanye suke da bakak’en suit da bakak’en glass wanda yaboye kwayar idon su, kallo daya zakai masu kagane sudin bodyguards ne wato masu tsaron lafiya mutun jeruwa sukayi tareda kamewa fuskokin nan nasu ba annuri,

 

Dasauri drive daya motar yafito tareda zagayowa ya bude kofa ahankali wani kyakkyawan farin Dattijo ne yafito Wanda akalla zayakai shekara 60 ko fiye da haka sanye yake da blue suit mai asalin kyau da tsada, hannun shi rikeda yar sandan nan da yawanci gogaggun yan boko da masu kudi ke rikewa,

 

sannan wani kyakkyawan bakin Dattijo yafito shima shekaran sa bai wuce na wannan ba, saidai fuskar shi dauke take da zanen bare-bare irin wacce tunda ga goshi har saman karan hancinsa sai guda bibbiyu masu tsawo akan kumatun sa, shima sanye yake da suit din saidai nashi ash color ne shima hannun shi rike da sandar

Kallo daya Zaki masu kagane sudin gogaggun yan Boko ne wa yanda kudi dajin dadi yaratsa jikinsu.

 

Ahankali suka kalli juna tareda sakin murmushi sannan cikin harshen turanci fari yace Barr mukarasa KO?..yace OK Dr gasu” can ma zasu sakko, yace OK sannan suka nufi gurin jirgi da fasinjoji suke fitowa wanda dama tuni yasauka yayinda escorts uku din suka shiga gaba uku suka rufa masu baya.

 

“Wasu kyawawan samari biyu na hango cikin jerin fasinjojin dake sakkowa, wayanda shekarun su zayakai 30 daya fari ne daya baki, farin wanda kyansa yakeda matukar daukan hankali sanye yakeda blue yadi me asalin kyau da tsada anyi masa irin dinkin nan da samarin yanzu sukeyi wanda ake ratsa farin yadi, dinki ya kama jikinshi kad’an inda yafito da asalin cikar zatinsa na cikakkun maza masu jini ajika,

 

kafarsa sanye da blue takalmi me kyau da tsada, shima bakin irin yadin ne ajikinsa harda irin dinki saida nashi yadin ash color ne sannan shima fuskarsa dauke take da zanan bare-bari, suma kallo daya zakai masu kagane Boko da kudi tareda jin dad’i yaratsa jikinsu,

Karanta Littafin Nameer Hausa Novel

sannan ga dukkan alama irin yaran nan yan GATA domin kuwa ko wannan su hannusa daure da agogon gwal da zobba masu asalin kyau yayinda suke ri’e da kyawawan wayoyi tsadaddu guda uku-uku, kunnan su mak’ale da yar Bluetooth din nan ta amsa waya gaskiya guy’s din sun had’u sai kallon su ake cike da burgewa.

 

Fuskokin su dauke da annuri wacce takara bayyanar da kwarjinin su sosai cikin takun kasaita me cike da nutsuwa suke takowa yayinda escorts dinsu hudu ke biye dasu suna ri’e masu da akwatinan su da kuma laptops dinsu

suna gama sakkowa,

 

Sai cak! farin saurayin

ya tsaya tareda yin sauri yadafe kanshi yana yamutsa kyakkawar fuskar shi me cike da lallausan saje, sannan yasaki wayoyin hannu shi suka zube akasa sai yasake dafe kanshi da duka hannunsa biyu tareda lumshe shanyyayun idanun shi sai kuma,yasaki wani irin firgitaccen karan da sautin shi yadauki gaba daya filin jirgi, sannan yafadi kasa tamkar gawa.

Tofa meke faruwa???

 

Cikin wani irin tashin hankali bakin saurayin nan yayi kanshi tareda escorts din shi suka dagoshi yana fadin innalillahi! BLUE meyasa meka?, dai-dai lokacin wayan nan Dattijoji suka karaso gurinsu

cikin tashin hankali farin Dattijo yasaki sandar hannu shi tareda tallabo kyakkyawan saurayin nan, cikin tashin hankali yace Oh! my boy what is wrong with you?..

Gidan Uncle Hausa Novel

sannan yakalli bakin saurayin nan cikin firgici yace BULAMA dama yarona bayada lafiya?.. cike da tsoro yace no Dad wlhy lafiyan “shi qalau muka taho, da sauri bakin dattijon nan yace subhalallahi! to me yasa meshi haka? da sauri yace wlhy papa ban saniba amma nasan tabbas lafiyar sa lau, papa yace yanzu ba wannan ba Dr mu dauke shi zuwa asibiti, cikin sauri escorts din suka dauke shi sukasa amota yayinda Dad shima yashiga yazauna tareda daukan kan Blue yadora akafarsa yana girgiza shi taredaa tura hannun sa cikin lallauwasan suman kanshi yana fadin Oh! my darling boy open u eyes kaji?

 

.yayinda suma su Bulama suka shiga dasauri sannan suma escorts suka shishshiga suka tayar da motocin, cikin sauri suka bar harabar filin jirgin

asibintin shika suka nufa dake cikin garin zariya.

 

Zariya

yau garin na zaria antashi da hazo me dauke da matsananci iska irin me tsananin sanyi nan wacce take ratsa jikin dan adam sosai,

 

kasan cewar lokacin hunturu ne gashi kuma dama lokacin sanyi zariya badama, don haka “kowa kagani sanye yake da rigar sanyi don kare kanshi daga matsanancin sanyi da’ake tsulawa, wanda be hana “mutane fitowa harkokin gaban su yanda suka saba kullum ba,

 

musamman “yan kasuwa sai sauri suke su isa gurin kasuwancin su” yayinda suma masu sana’o’in hannu ba’abarsu abaya ba, suma tuni suka fito gurin harkokin su na yau da kullum kamar dai yanda aka saba,

 

“sukan ma’aikatan gwamnati dama tuni sun dade da tsufa acikin ofishoshin su suna gudanar da aikinsu” kamar yanda, “suma d’alibai tuni sun dade da tsufa acikin makaranta cikin ajujuwa suna daukar darasi.

 

Sabanin wasu” matasan yan’mata da samari dana hango daga d’an nisa kad’an da makaranta Al’azahar academy school dake gadar saye kusa da yellow, suna sanye ne da riga da wando wanda idan bagizo idona ke mun ba kamar kayan makarantar ne,

 

banga fuskokin su ba saidai nayi nasaran k’irgasu wato su biyar ne chif!, maza biyu mata uku, wa yanda suke sanye da farin hijab dogo sosai don har yakawo guiwar kafarsu matan suna ri’e da hannun juna,

 

suma mazan haka suna ri’e da hannun juna ga duk kan alama akwai kauna ta jini tareda shakuwa me tsanani atsakanin su, tafiya suke ahankali tamkar wa yanda kwai yafashe ma aciki.

 

Cike da mamaki na kallin agogon hannuna inda yanuna mun karfe 10:50am wato 11:00am saura minti goma, da sauri na mai da kallona gurin su araina kuwa fadi nake kamata yayi ace yanzu yaran nan suna cikin aji suna daukar darasi kamar sauran dalibai yan’uwan su,

 

amma kuma sai akasamu akasin hakan shin ko me ne dalilin?..

 

banida me bani amsar nan sai wayan nan yara, hakan yasa nadan kara sauri kadan ina cigaba da kallon su tabbas uniform din al’azahar academy school ne ajikinsu, yayinda suka cigaban da tafiya abinsu ahankali ga dukkan alama su basajin wannan sanyin da’ake zabgawa,

 

Nikam gaskiya sun birgeni matuka ganin yanda suke tafiya cikin nutsuwa ba hayaniya balle tada kura irin na sauran wasu dalibai, to dama duk wanda yake al’azahar academy school saika same shi da kamun Kai da nustuwa, domin makaranta ce dake cike da tsantsar tarbiyya kasan cewarta had’e da islamiyya,

 

abin gwanin sha’awa sun sa yar karamar kanwarsu atsakiya suna ta tafiya, sauran kadan nakarasa gurinsu sai naga yar karamar ta tsaya cak! hakan yasa suma duk suka tsaya suna kallon ta, nima tsayawa nayi tareda sakin baki da hanci ina kallon tsantsar kyau da Allah yayi masu gawani irin matsanancin kama dasukai da juna wanda hakan yana nufin sudin y’an AHALI daya ne,

 

Gaskiya “sudin kyawawa ne sosai gasu da tsawo me matukar tsari da sha’awa ba irin me munin nan ba, kallo daya zakai masu kagane cikin biyu sun hada, jini daya KO FULANI ko BUZAYE koma dukka biyun domin kyansu yakai, saidai su” ba farare bane haka zalika kuma su” ba bakake bane saidai fatar su kalace me matukar kyau da tsada, wato chocolate color irin me haske da shaini din nan.

 

Haka zalika kana ganin su zaka fahimci basuda wani tserayya ta haihuwa atsakanin su, domin kuwa wannan nabin wannan waccan nabin wannan haka suke “babbar cikin su wacce ke sanye da wando kore riga da hijab farare shekarun ta zayakai 16, sai me bimata namiji ne shi kuma zayakai shekara 14 shima wando Kore yasa riga fara sai me bimasa mace ce ita kuma shekarun ta zayakai 12,

 

itama riga da hijab farare da wando Kore wato yan sakandiri suke da wannan shirin, sai me bima macen namiji ne shekaran shi zayakai 10 shima wandon sa Kore riga kuma me gida-gida pink colon da ratsin fari wato chak kenan, sai yar karamar su itakam shekaran ta baifi 4 zuwa 5 ba itakam da’alama akwai d’an tazara tsakanin su da wanda takebi, itama wandon Kore ne amma rigarta irin na wanda take bine wato me gida-gida amma hijab dinta fari ne kal wato irin na yan’uwan ta mata sukuma yan primary ne.

 

Gani nayi ‘yar karamar su tasaki hannun dayar takama duka hannuwan babbar tareda daga Kai ta kalle ta sannan ta kwab’e fuska, cike da yarinta tace Aunty BEENA yanju shi kenan ankole mu daga school baza mu qala zuwa ta ba kenan?..

 

shuru tayi tana kallon ta tsawon wani lokacin ba tareda ta bata amsa ba, hakan ne yasa ta turo baki tareda sakin hannuta taje gurin babban namijin ta kama hannun sa duk biyu tace yah BAS shikena daga yau mun daina zuwa school?..shima shuru yayi bai bata amsa ba sai kallon ta da yake,

 

don haka taje gurin dayar macen tace Aunty BANA ki fada mu baza mukara zuwa school ba?..itama shuru tayi tana kallon ta, cikin sanyi jiki ta kalli dayan namijin tareda turo baki tace yah BASH aikai ma nasan bazakai mun magana ba tunda su Aunty Beena basuyi mun ba, ai baruwana daku kuma aina gane saboda bamu biya kudi bane shine aka koremu to ai kafar “Abbun mu tana ciwo baya iya tafiya balle yasamo kudi yabamu, sannan shikuma “kawu Muda yaki ba “Ammun mu kudinta balle tabiya mana shine suka koremu,

 

ta nagama fadin haka sai ta fashe da kuka me ban tausayi, aikam dasauri su kayi kanta yayinda Beena ta tsugunna tayi tsawon dai-dai ita tareda rungume ta ahankali take girgiza mata Kai alamar tayi shuru, shuru tayi sannan tace Aunty Beena sbd bamu kai kudi bane akakore muko?..kai ta gyada mata alama “eh, fuska tasake kwab’ewa tace to ai “Abbu bayada lafiya to aunty Beena wane zaya bamu kudi mukai school?.. cikin tsananin tausayi Kansu tace….

 

Muje zuwa yanzu za’afara

 

So

More

Comments more

typing and pls share

 

Bismilahirrahamaniraheem!!!

 

Sai kuma tayi shuru na kusan tsawon mintin biyu da’alama magana tanayi mata wuya, sannan ta sauke ajiyar zuciya ahankali cikin zazzakar muryar ta me dad’i tace “ALLAH shine zaya bamu don haka karki damu domin yasan halin da muje ciki kinji ko? kai ta gyada alamar to,

 

tace yauwa my Banu to d’anyi mun dariya mana nagani, aikam dasauri tawashe d’an karamin bakinta me dauke da fararan hakora, tace yauwa kokefa to mutafi gida kinga “Abbu da “Ammu suna can sukad’ai ko?..tace to tareda juyawa ta kalli Bass cike da shagwab’a ta mika masa hannu tareda fadin yah Bass dauke ni kaji?,

 

cikin wasa yace nakiya ke da kikace baruwanki damu, so muma baruwan mudake ko my Bash yace eh d’iyar kawu “muda kawai yakarasa fadi tareda yimata gwalo, kafa tafara bugawa cikin shagwaba tace Aunty Beena kingan shi ko?..

 

murmushi tayi wanda kusan tare sukayi da yan’uwan sannan, tace kai yah Bass itakam d’iyar “Abbu da “Ammu ce bata kawu muda ba ko?.. tace eh kawu Muda yace wai haka? kai ta gyad’a almar eh yace to shikenan yar Banu Banu ta yakareshe fadi tareda daukanta yadora akafad’arta,

 

sannan suka cigaba da tafiya abinsu gwanin sha’awa sunayi suna fira me cike da kaunar juna ahaka har suka isa gidan su dake anguwan fadaman sarki alokaci tuni Banuja tayi barci, kasan cewar tsakani anguwar su da school din akwai nisa.

 

Wani gida suka shiga me bakin get wanda kallo daya zakaiwa harabar gidan ka fahimci masu shi suna cikin wani hali, domin kuwa filawoyin dake shuke a harabar gidan duk sun bushe saboda rashin ishenshen abincin su da basa samu,

 

Duk kansu bakinsu dauke da sallama suka shiga wani babban falo wanda yake dauke da wasu tsofaffun kushin din da duk yadinsu ya yayyage,

 

Daku na hudu ke acikin falon don haka direct suka nufi daya daga ciki still bakin su dauke da sallama wanda basu shigaba har saida aka amsa masu tareda basu izinin shiga tukun, sannan suka shiga.

 

Inda suka iske wata kyakkawan mace fara amma ba irin faudin ba tareda wani kyakkawan mutun wankan tarwad’a wanda kallo daya zakai masa kafahimci yanajin jiki matuka kasan cewar yanda yake fitar da numfashi, kwance yake akan wata lotsatsiyar katifa yayinda rabin jikinshi yake rufe da bargo, saidai banda kafafun sa domin kuwa suna saman ciyarta matar tana manmatsa mashi ahankali,

 

Lokaci daya su ka dago kai tareda tsura masu ido, kallo daya zakai masu ka gane su din ne iyayen su saboda tsananin kama, cike da ladabi suka zube agaban su tareda cewa Abbu sunnu da jiki Ammu sunnu da gida,

 

da kai Abbu ya amsa sabani Ammu da tace yauwa sannun ku, amma lafiya naga kun dawo ba lokacin tashi ba? cikin sanyi murya Bana tace Ammu ankoro mune saboda bamu biya kudin makaranta ba, kuma yan school din mu suna tayi mana dariya wai mu duk time sai ankore mu saboda Abbumu baya biya mana kudin school,

 

kuma yau har saida Banu tayi kuka, ko Bash yace eh saida Aunty Beena ta lallashe ta tayi shuru sannan yah Bass yagoya ta har tayi bacci.

 

Da sauri Ammu ta kalli Abbu wanda shi din ma ita yake kallo cikin b’acin rai tace kagani ko kagani ko? haka kakeso mu cigaba da rayuwa cikin kunci? yanzu haka abincin da zamuci yana neman yafi karfin mu ga ciwon ka kullun karuwa yake,

 

Sannan shima karatun so ake ya tsaya masu, gashi kullun nayi magana sai kace nayi hakuri na kyale shi” to kasani wannan karon bazan kyaleshi ba dole naje yaya Muda yabani hakkina kome zaya faru yau saidai yafaru Amma bazan yarda ba, eheee! sannan ta sauke kafafun shi daga saman cinyarta ahankali tamike.

 

Ahankali yabi bayanta da kallo har ta fice daga dakin sannan yamaida hankali kan yaranshi, wayan da tsabar ladabi tunda “Ammun su tafara magana kansu ke duke har tafita.

 

Cikin sanyi murya me dauke da murmushi Abbu yace to yan albarka kuje kucire uniform din bakomai Allah zaya rufamana aciri inshallah kunji ko?, ahankali suka ce to tareda mikewa har da Bass dake goye da Banu suka fita amma banda Beena, shuru yaratsa dakin na wani dan lokaci sannan Abbu yace ya akayi ne ta Abbu maman Ammu?…

 

ahankali tadago kai idanun ta cike da kwalla cikin sanyi murya tace Abbu maganar “Ammu yana nufin zataje abuja gurin kawu Muda kenan ko?… kai ya gyad’a mata alamar “eh ido ta lumshe aikam take hawayen suka zibo cikin muryar kuka tace Abbu meyasa zakabar ta taje?

 

yace saboda tana bukatar zuwa kin kuma sannan bazan hanata ba tunda alkawari na daukarma “lnna ta, duk abinda Ammun ku tabukata nayi mata muddun be sabawa shari’aba to nayi mata, tace amma Abbu kasan kotaje “kawu Muda bazaya bata hakkin taba tunda tunba yau take zuwa ba amma be bata ba,

 

yace haka ne tace to kagani hakan yana nufin baya daninyar bata don inda yanada niyya da yabata, tunda yau shekara hudu kenan tana tafama wahala akan abu daya, yace haka ne amma kinsa halin Ammu ku dakafiya tace to nidai tunda be da niyyar bata hakkin ta don Allah Abbu kace ta kyale “shi aigida biyu ne wanda idan ba duniya akwai lahira,

 

cikin sanyin jiki yace haka ne zan mata magana ki kwantar da hankalin ki kinfan banson kinasa damuwa aranki ko? kaita gyada sannan ta tashi tafita jiki bakwari.

 

Dakin Ammu tashiga bakinta dauke da sallama, tsaye ta isketa hanun rikeda wayar nokia gefe kuma jakace ga kaya zube akasa, tsugunawa tayi tareda daukan kayan tana ninkewa tanasawa cikin jakar bayan tagama tarufe jakar,

 

sannan ta dukar da kai cikin sanyi murya tace don Allah Ammu idan kinje “kawu Muda be baki hakkin ki ba kiyi hakuri ki kyale shi yabaki inda bayada shi kinji? ba tareda ta kalle taba tace to sannan tadauki hijab dinta me ruwankasa dake rataye jiki kofa tasa alamar shirin tafiyar take,

 

Sannan tace to nizan tafi sannan tadauki pos dake ajiye saman gado tareda budewa taciro kudi naira dari biyar ta mikawa Beena, tareda cewa gashi kirike ko zaku siya wani abun ai akwai sauran garin dawa da na rogo ko?

 

kai ta gyada alamar eh tace to don Allah kikula da kanki tareda kannanki wanda nasan kinayi amma kikara, sannan banda yawon banza duk danasan ke bama’a bociyar sa bace, amman ki kula kinji ko?

 

Cikin sanyi murya tace to, Sannan tace yauwa yauwa yau ma zakije gidan “maman “Abdul din

ne gurin sakar?..tace eh to Allah yabada sa’a amaida hankali, sannan adawo dawuri atafi islamiya, sannan ki matsawa babana yaje gurin aikin sutafi tareda Bash idan ”Banu na ta tashi ki kulamun da’ita sosai kinji?

 

tace to Allah tsare hanya tace to Amin Allah yayi maku albarka tashi ki kiramun babana yarakani bakin titi na hau mota zuwa tasha, ahankali ta mike tareda cewa to tafita batare da dadewa ba sai gasu tareda Bass har yacire uniform yana riga da wando nawani fari yadi, ba tareda yace komai ba yadauki jakar suka fita saida tashiga dakin Abbu sannan tafito yatafi raka ta,

 

Yayinda Beena tashiga dakin su cikin sanyi jiki tacire uniform tarage daga ita sai vest iya guiwa batada kiba saidai tanada shave me kyau, gata da dukiyar fulani dasuka cika mata kirji tanada matukar yalwar kashin kai wanda yakeda yawa da tsamo gashi baki sidik tanada ido me matukar kyau infact dai Beena kyakkyawace sosai,

 

ahankali ta zauna akan dan karamin gadon su me dauke da wata lotsatsiyar katifa ahankali ta lumshe ido, tafara tunanin rayuwar su ta baya.

 

ASALIN SU

 

Alh Usaman Dan Sudan shi ne asalin sunan Abbu, karatu ne yakawo shi garin zaria inda yahadu da wani shahararran me kudi me suna Alh sule me dabino wanda yazama ubangida ga Abbun Alh sule me dabino asalin shi mutumin barno ne kuma maraya ne bashida kowa Allah ya azurta shi da dukiya me tarin yawa kasuwanci ne yakawo shi zariya,

 

yanada mata

biyu kuma duk garinsu daya, Haj hajara da Haj Balkisu itama marainiya ce Haj Haraja tanada d’a daya me suna Mudansir, Haj Balkisu tanada y’a daya me suna fatima, gidan Alh sule kullum babu zaman lafiya saboda Haj Haraja masifaffiyar macece gatada kyashi da hassada,

 

wanda har ta koyawa danta Mudassir itakam Haj Balkisu macece me hakuri batada kyashi da hassada kamar mijinta, haka ake rayuwa gida kwasam sai ciwon ajali yakama Haj “Balkisu ba tadade dafara jinya ba tace ga garin nan,

 

Alh sule da Fatima sunyi kuka sosai na rashin Haj Balkisu salihar mace.

 

Bayan rasuwar Haj Balkisu Fatima ta fuskanci matsala sosai agurin Haj Hajara da d’a Alh Muda har da matar sa Safara’u, da Alh sule ya fahimci haka tana gama sakandiri sai ya aurar da ita ga Usman wato Abbu, inda Alh su yaikomai sannan yabashi dankareren gida afadaman sarki Fatima batason Usman ko kad’an,

 

amma batada zabi dole tayi hakurin biyayya ga mahaifinta domin ta fuskanci yanason Usman kasan cewar sa mutumin kirki me amana, bayan auran sai Usman yaje Sudan yadauko mahaifiyar shi domin Fatima taki sauraran shi beyi yin kurin fadawa Alh sule ba domin yana matukar kaunar Fatima bayason facin ranta ko kad’an.

 

Wani abun mamaki Fatima tana ganin Iya mahaifiyar Usman taji duniya babu wacce take kauna irin iya, don haka take bata kulawa sosai tamkar ita ce ta haifeta, wanda hakan bakarin samun kima tayi agurin Usman ba, ahankali Iya ta fahimci Fatima bata kula d’anta don haka sai tafara yimata nasiha cikin hikima don tabi mijinta su zauna lafiya, domin aljannar ta yana karkashin kafar mijinta, kasan cewar Fatima me fahimta ce sai tadauka.

 

Aure da albarka sai ga ciki ranan data haihu tahaifi y’a mace sankowa kin wanda yarasa, ranan zokuga murna gurin Usman da Iya yayinda murnan Alh sule yafi nasu, shiyayi komai ranan suna y’a taci sunan Haj Balkisu wanda ashe Iyama sunanta kenan,

 

don haka sai suna kiranta Beenazeer, bayan Beenazeer ta haifi namiji shine akasa masu sunan Alh sule wato Sulemain shine suke kiran shi Bassam, bayan Bassam ta haifi Banafsha sannan Bashir sannan auta Banuja haka suka taso cikin tarbiyya iyayen su tareda kulawar Alh sule, alokacin lya tadad’e da rasuwa yayinda Alh sule yadauki son duniya yadora masu,

 

komai sukeso yimasu yake musamman Beenazeer, wanda yasa Alh Muda yakeji kamar yakashe Fatima da yayanta kasan cewar shi Allah be ba matarsa haihuwa ba, don haka komai Alh sule yi masu yake da dukiyar sa suna rayuwarsu gwanin dad’i kwatsam ranan wata laraba Alh sule yakira Abbu don yakaishi Abuja kasan cewar dama shike tukashi duk inda zashi,

 

Don haka suna kan haryasu tazuwa abuja sukayi mummuna hatsari

aka kwashesu zuwa asibiti kwanan su biyu acikin asibiti Alh sule yace ga garinku nan, yayinda gaba daya rabin jikin Abbu yadaina aiki Fatima wato Ammu tashiga mummunan tashin hankali itada y’ay’an ta.

 

Ranan sadakan bakwai sai akayi maganar rabon gado inda aka nemi Alh Muda daya fadi abubuwan da Alh sule yabari, budar bakinsa keda wuya sai yace…..

 

Muje zuwa yanzu za’afara

 

 

Bismilahirrahamaniraheem!!!

 

“Ai babu abinda Baba yabari ko kudin dayake kasuwanci dasu duk na mutane ne, kuma tuni yabashi ya mayar masu da abinsu,

 

Cikin tsananin tsoro! Ammu ta kalle shi! haka malaman gurin mamaki yarufe su dajin wannan magana me kamada almara, domin dai ansan “Alh Sule yanada dukiya me tarin yawa,

 

Wanda kuma tabbas tashi ce bata wani ba amma taya d’an sa zayace wai batasa bace to me yake nufi?….yayinda Haj Hajara ta goyi bayan shi domin kuwa da daya daga ciki malaman dazasu raba gadon ya tambaye ta, meye gaskiyar lamarin?..

 

Sai tace ai gaskiyar kenan domin itama kusan kodaya yaushe yanafad’a mata ba dukiyar shi bace, abu kamar wasa yazama gaskiya don haka malaman da suka tsaya akan rabon gadon suka bar gidan,

 

Bayan sun tabbatar ma Alh Muda da mahaifiyar sa cewa muddun sukaci kwayar zarra na hakkin wannan baiwar Allah zasu biyata gobe kiyama, sannan suka fita.

 

Yayinda akabar shi daga shi sai Ammu da Haj Haraja cikin mutuwar jiki Ammu tace yaya Muda kaji tsoron Allah, taya zakace duk dukiyar nan bata “Baba bace?.

 

Dariyar mugunta yayi yace ah! dukiya kam ta duk ta “Baba ce kece dai bazan bawa ko sisin kobo aciki ba, wanda kukaci keda mijinki da y’ay’aki ya’isa haka wannan tawace nida y’ay’ana da zan haifa,

 

tace to don Allah kabada kudin ayiwa Abbun su aiki cikin masifa yace wlh ko sisi bazaya bayar ba aiba kudin ubansa bane, kai su tashi ma subar masa gidan shi,

 

Wasa-wasa Alh Muda yamursashe idonsa yahana ma Ammu gadon ta, kusan kullun taje don yabata tabiya wa yara kudin school, akuma yiwa Abbu aikin kafar sa wanda akace naira miliyan biyar za’ayi Amma Dan talikin nan har yau kusan shekara uku kenan,

 

Amma yaki bata ba tun yana garin kaduna har yakoma Abuja dazama cikin daya daga gidajen Alh sule, kasan cewar dama yanada gidaje a Abuja, aduk lokacin dataje saidai yaimata walakanci idan kuma tacinma yan arzikin yace mata tazo yawan maularta ko?…

 

To shine sai kaga wata rana yabata wasu yan kudi shine zata hau mota sauran suci abinci, idan kuma yanaji tsiya kosisin baya bata saidai Safara’u matarsa tabata kudin motar dawowa, shiyasa komai duk yacab’e masu rayuwa tayi masu zafi hatta da abinci dazasuci yana kokarin yafi karfinsu,

 

School kuwa tun sunayi masu hakuri har sungaji yanzu kusan kullun sai ankoresu, Abbu yasha ce” Ammu tayi hakuri ta kyale “shi tunda yaki bata Amma takiya kasan cewar Ammu akwai kafiya.

 

Ahankali ta sauke ajiyar zuciya sannan tamike cikin nutsuwa tashiga toilet din cikin dakin, Beenazeer kenan tanada matukar nutsuwa da kunya ga ladabi da biyayya musamman ga iyayenta tanada ilimin addini sosai,

 

Domin kuwa ta sauke alqur’an da hadda takuma an wasu littafai addini sosai, yanzu haka tana koyarwa a islamiyar su idan wata yayi abiyata wanda dashi ne suke dan samun abinda sukeci, amakarantar boko kuma tana S S 3 sune ma zasu rubuta jarabawa wannan time din, batada yawan magana domin kuwa miskilace tabugawa ajarida saidai tanada hakuri sosai amma kuma akwai matukar zuciya duk haka kuma tana da tsoro uwa uba ga kafiya wanda da alama Ammu su tabiyo,

 

Sannan tana matukar kaunar iyaye ta da yan’uwanta fiye da yadda take kaunar rayuwarta zata iyayin komai domin sama masu farin ciki, wanda hakan yasa iyayen ta suke kaunarta fiye da tunanin me karatu wanda suka dayai suka san adadisa aransu,

 

Ko bakomai itadin me shiga raice ga duk wanda ya zauna da’ita sai yaji tashiga ransa yaji yana Sonta, hakan nan suma yan’uwan nata suke kaunar ta ko dayake hakan yanada nasaba da yadda iyayen nasu suka koya masu kaunar junan su.

 

Bata dad’e atoile din ba tafito daure da tawul dai-dai lokacin da Banafsha tashigo dakin da sallama, tace Aunty Beena “Ammu ta tafi Abuja gidan “kawu Muda ne?..kai ta gyad’a mata cikin sanyi murya tace Aunty Beena Allah yasa kawu “Muda yaba Ammun mu kudin ta,

 

Ahankali tace ameen my Banaf kicire uniform kisa wasu kayan mutafi gidan maman Abdul tare kinji?..cike da murna tace to.

 

Cikin kankani lokaci Bana tashirya wanda kusan tare suka gama da Beena, sanye suke cikin riga da zani na wata blue atamfa bayan ta murza man kwalacca sai tafeshe jikinta da turaren humra da maman Abdul ta bata sannan su kasa hijab fari sannan suka fita,

 

Dai-dai lokacin da Bassam da Bash suka dawo raka Ammu, Beena tace su shirya su tafi gurin inda suke zuwa koyon dinki sukace to, dinki mata Bassam yakeyi yayinda Bashir yake koyan na maza Bassam tuni ya’iya dinki wanda har dashi suke samun kudin sayen abincin,

 

Sannan su Beena suka shiga dakin Abbu suka sallame shi sannan suka fito suka tafi gidan maman Abdul.

 

Maman Abdul makociyarsu ce, tana zaune da mijinta da yaran su biyu Abdullah da Anisa tanada kekunan saka Wanda take koyawa yammata aciki har da Beena da Banaf, maman Abdul tana matukar kaunar Beena saboda tanada basira sosai gata dasaurin dauka abu wannan kenan.

 

Cigaba

 

ASIBITIN SHIKA

 

“”””*

Koda suka isa cikin sauri aka tarbe su kasan cewar Dad babban Dr ne acikin asibitin don haka akazo da gadon daukar marasa lafiya aka dauki Blue, wanda yaketa faman ihu tareda fisge fisge direct emagency room aka nufa dashi,

 

likitoci sunfi biyar akasa aciki

har da Dad sosai suka dukufa akansa yayinda yaketa fisge fisge tareda wani irin ihu,

 

Likitoci sunyi iya kokarisu akan Blue amma abun yaci tura domin kuwa be daina fisge fisgen da ihun dayake ba, tareda ture duk wanda yai yin kurin rikeshi,

 

Don haka dole suka taru kusan mutum goma aka danne shi sukayi masa alluran barci me matukar karfi, sannan suka fito kowa sai sharan gumi yake yayinda zuciyoyin suke cike da mamakin abinda yasa meshi haka…?

Musamman Dad.

 

Direct wani babban daki suka shiga inda suke tattaunawa especially idan irin haka tafaru, sosai ake tattaunawa akan wannan lalura da tasamu Dan abokin aikinsu, nan Dad yake fadama su yanda abun yafaru, sai daya daga cikin likitoci yace niko sai nake gani kamar aljanu ne suka shafe s….

 

Zumbur Dad yamike cikin bacin rai yace haba Dr lbrahim wannan wace irin magana ce….? D’an nawa ne aljanu suka shafa?…to kasani ni ‘Dana ba buwasu aljanu dasuka shafe “sa, asalima ni mabansan akwai wasu aljanu aduniya ba,

 

Sannan yafita rai bace daga dakin daya daga cikin likitoci yace humm! Dr I b kenan kaima kasan cewa “Dr L U be yarda da duk wani abu daya shafi gargajiya ba,

 

Amma tabbas ciwon “yaron sa yayi kama da shafar aljanu, Dr I b yace “uhumm kaima kafad’a yanzu dai mubari yatashi musake ganin yanayin sa tukun ko?..suka amsa da eh haka za’ayi sannan suka fito kowa yanufi office dinsa zuciyar sa cike da tunani halinda Blue yake ciki.

 

Dad ma koda yafita direct office dinsa yanufa da sauri Barrister tareda Bulama suka bishi, alokaci daya suka zazzauna cikin tashin hankali Bulama yace Dad meye samu my Blue?… Barr ma irin tmbyr yayiwa Dad,

 

Shuru Dad yayi kafin cikin bacin rai yace kai kaji “Dr I b wai aljanu suka shafi my “boy da sauri cikin harshen turanci Bulama yace Dad

meye kuma haka..?wai evil, tsaki yayi yace karya ne Dad me I don’t believe this wooo! Dr yace me to my boy,

 

Shikam Barr shuru yayi yana nazari lamarin can sai yace Dr lamarin fa akwai kamshi gaskiya, da sauri Dad yace haba Barr kamar ya fa?…

 

yace naga yanda yake irin yadda aljan…dasauri Dr yace enough! enough!! enough!!! Barr banaso kana alakanta “boy da wayan nan shirmen da ni kwata-kwata banyi believe dasu ba, yace sorry bawai nace sudin bane amh! to yanzu dai ya jikin nasa”?…

 

Cikin had’e buska Dad yace him in bad condition, yanzu ma saida mukayi masa alluran barci me karfi wanda zata iya kaiwa gobe so idan har yafarka banga wani cigaba ba zanfitar dashi waje, Barr yace to Allah yabashi lfy,

 

Dad yamike tare da cewa Amin mujen ku gida inason nad’anyi wani bincike akan ciwon boy, Barr yace ok Bulama yace Dad ni zan tsaya gurin my Blue murmurshi yayi tare da dafa kafad’ar shi yace karka damu my boy akwai masu kulashi so muje ka huta kaji..?

 

Yace yes Dad, Sannan Dad yafara fita sai Bulama da sauri Barr yakama kunnan shi aikam yasaki yar kara kadan cikin shagwaba yace ahhh! papa akwai zafi fa,

 

Kasa-kasa yayi da murya yanda Dad bazaya jiba, yace l know meyasa bakaji ina rabaka da wannan akida kana ko karin yiko?..yace papa me nayi?..yace gidan ku, cewa fa kayi bakayi believe da aljanu ba, yace gaskiya papa ni ban yarda da wasu aljanu ba, yace to dan ubanka ko ka yarda kokar ka yarda akwai aljanu,

 

Yace to papa ni ban taba ganin su bafa taya zan yarda akwai su?..,da sauri yace Dan ubanka karkayi fatan ganinsu domin ganinsu arayuwa ba alkhairi ba ne,

 

Kai! tsaya ma tukun kanayin addu’a kuwa?..yace papa inayi shimafa my “Blue yanayi sosai har yafini yifa, yace kaidai shashasha ne to wlh gara kadage dayin azkhar domin suna tsare mutum daga bad evil kaji ko?..

 

Yace to dai-dai lokacin da suka karasa gurin mota escorts suka bude masu, suka shiga

kasan cewar tuni Dad yashiga don haka sukaja suka tafi……

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!