Hausa Novels

Makaho ne Hausa Novel Complete

Makaho ne Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Makaho ne

Bismillahirrahmanirrahim

 

Wannan littafin qirqirarran labari ne,

 

Aisha yakubu guree

Iyan auwal

08124285855

 

Marubuciyan

AL’AMIN, YARO NE, ZUCIYA NA, MAKAHO NE,

 

PAGE 1&2

 

 

Wata mata nagani yar kimanin shekaru Arba’in da biyar, hankalinta a tashe,. Sai faman Sharan hawaye takeyi,

Tana zaune a bakin gago,

Wani matashin saurayi dan akimani ashirin da bakwai, kwance akan gadon yayi filo da cinyanta yana bacci, kai daga ganin baccin kasan na wahala ne,

Alhaji musa, yana tsaye da shi da Doctor faisal,

Alhaji yace Dr baccin zaikai kamar awa nawa,

Dr Faisal yace kar kadamu alhaji inya tashi komai zai zama normal,

Nidai abinda zance shine ku gaggauta yi mishi aure,

Alhaji yace Insha Allah Dr cikin satin nan zanmai aure, matan dake zaune tana jin furucin alhaji ta fashe da kuka tare da toshe bakinta gudun kar ya farka,

Alhaji ya kalleta yace inkuka zaki mana tashi kifita,

Dakyar tasamu ta hadiye kukan,

Dr faisal yarubuta maganin da inya tashi za a bashi, yayi musu sallama,

Suka fita tare da alhaji da takardan maganin da zai siyo,

Hajiya hajara sai shafa kan tillon danta takeyi tana addu’an Allah yabashi lafiya, Allah yabasa ikon cin wannan jarabawan,

Kiran sallan magrib ya dawo da ita daga haiyacin ta,

Ahankali tazame jikinta tashiga bayinshi ta dauro alwala , adakinsa tayi sallah, tana zaune tana lazimi har aka kira sallah ishsha’i ta gabatar da sallah,

Baifi da biti sha biyar ba , alhaji tadawo da magunguna daya siya, ta karba ta ijeye akan bed said drow,

Alhaji ya kama hannunta yace zo muje,

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

Sukayi bangaran su, suna shiga yajata suka shiga wanka, agurin wanka duk yanda alhaji yaso tabashi kulawa amman hakan ya gagara, bayan sun kammala shirin, suka daret dakin Adam sukayi, har yanzu bacci yakeyi, suka fito tare da jan qofan,

acikinsu babu wanda yaci wani abun kirki, alhaji yace suje su kwanta tace ita adakin Adam zata kwana,

Alhaji yace a a insan inbakya kusa dani bazan iya bacci ba,

Muje inkin gama dani sai ki koma gurin yaronki,

Badan tasoba haka tabiye wa alhaji,

Bayan sun kammala komai tayi wanka ,

Tadawo dakin Adam,

Alhaji yace iya tashi ta kirashi tace to, misalin shabiyu da rabi Adam yatashi da salati abakinsa,

Masha Allah,

Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan halittan,

Yatashi yazauna alokacin hajiya tayi sallama daga sallah da takeyi,

Ta tashi tazo tana fadin babana,

Wata zazzaqar murya mai hade da sanyi yace my love,

Farine tas dogone mai matsa kaicin tsayi,

Ga idanuwan sa Dara Dara,

Kir incikaku da bayani saidai ince Masha Allah,

Cikin sanyin murya yace my love qarfe nawa yace,

Tace daya saura,

Ya waro idanu yace my love zanshiga toilet bayi sallah ba,

Hajiya tace to babana ta ta taimaka mai yasauka naga yafara lalube , Allahuakbar Ashe duk wannan kyawawan idanun baya Gani,

Hajiya tace muje inrakaka, takama mai hannu suna tafiya taku daya ana biyun yace washiii yare da dafa marar sa, hajiya tace babana cikinne yayi shuru na mintina uku kafin ya daga kansa muje my love , yadan qulleni ne Amman yanzu yasake ni,

Saida takaishi har cikin bayin sannan ta dawo,

Ta dauki waya ta kira alhaji ta sanar mai da tashin Adam , sannan ta gyara mai gado tsaf, ta zauna tana jiran fitowan sa,

Alhaji ne yayi sallama, alokacin Adam yace my love kayan da zan canza,

Alhaji da kansa ya dauki jallabiya da gajeran wando ya miqa masa, inda yazuro hannunsa, ya karba yana fadin Dady shigo kasakamin,

Dama yana tunanin inda zai sa wandon,

Saboda shiyasan yanda cikin ke masa ciwo,

Dady yashigo Adam na tsayi jikin bango daure da towel ya dafa matarsa da hannu daya dayan yana riqe da kayan,

Abba ya karba yasaka masa wando sanna ya ya saka masa riga,

Yakama hannunsa suka fito , yace Dady zanyi sallah , dady yace babana kabari kaci wani abu sai kasha magani kafin kayi sallah,

Adam yace karka damu dadyna zan iya,

Bayan Adam ya idar da sallah , alokacin hajiya ta hadamai coffee mai zafi,

Tabashi balaifi yasha sosai, hajiya tace ka inkawo maka indomi yace my love nagoshi bani maganin,

Tabashi yasha,

Ya kwanta yace my love rufeni, tarufeshi ta taqemai AC , yace my love kuje ku kwanta naji sauqi,

Saida safe yafada yana dada lumshe idanuwansa dady ya kama mata hannu suka fita dare da jamai qofa,

Asuba tagari,

 

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

 

 

 

 

Aisha yakubu guree

Iyan auwal

08124285855

 

 

Marubuciyan, AL’AMIN YARO NE, ZUCIYA NA,

MAKAHO NE,

 

 

PAGE 3&4

 

Alhaji yakama hannun hajiya suka tafi,

bayan sun isa daki cikin damuwa, hajiya tace, alhaji kace cikin satinnan zaka yiwa babana aure ,

Alhaji yace Insha Allah,

Hajiya tace to dawa zaka hadasu,

Nidai a iya sanina babana bai taba yin budurwa ba, akullun inna tunana samun macen da zata zauna dashi tsakani da Allah,

Saboda laluransa,

Alhaji yace hakane,

Amman inna tunanin mu hadasu da yar gidan alhaji Hasan, hajiya tace kana nufin jamila, yace eh,. Hajiya tayi shuru tana tunani irin wannan hadin, yaran gidan basu da kamun kai,

Wata zuciya tace ai gwara wanda kika sani, in aka kawo miki wacce baki sani ba fa, har ga Allah batason hada alaqa da hajiya Karima soboda batan batada tarbiya kuma bata daura yayanta kan hanyan kwarai ba, Amman ya zatayi,

Itada akullun addu’an ta shine Allah yabama tillon danta lafiya,

Alhaji yace hajiya yafada dadan qarfi kafin taji,

Yace tunanin me kikeyi tace bakomai Allah yasanyawa auren albarka,

Amman kana ganin yariyan zata amince,

Alhaji yace mai zai Hana,

Duk inda Ake neman da nakwarai babana yakai,

Inbanda laluran ido me yarasa,

Kuma last week munfara maganan da alhaji Hasan kuma ya amince 💯 to Kinga saidai mu ijiye ranan,

Kuna ni ranar jumma’a nakeso adaura, saboda bama buqatan komai,

Hajiya tace ba damuwa Allah yanuna mana, ya amsa da Amin,

 

Washe gari da misalin garfe tara Adam ne zaune a falon sa, masha Allah, babu abinda bawan Allah nan yarasa saidai idanu, yana waya cikin farin ciki,

Yace my baby ya school,

Daga can ban garen, tace dadyna jiya bakazo ba sai ya’u dreba katuro didai nayi fushi, yace jiya naje wani gurine har lokaci yaqure min,

Cikin sanyin murya yarinyan da bazata wuce shekara goma sha biyu aduniya ba tace, aiyaa Dady na,

Ya’u dreba yace min bakada lafiya ne , ahe qarya yamin,

Adam yace, a a babba baya qarya nine nacemai kaina naciwo,

Tace to dady yanzu yadena ciwon yace eh, tace inna my love yace tana daci, , tace kakai mata wayan,

Cikin sanyin murya Adam yace yau ga yarinya tana aikan dadynta, cikin sauri tace I’m so sorry dadyna ,

Kayafe min natuba,

Tasake mai mai ta kalman kayafemin dady, yace nayafe miki , tace Miss u dady, shima yace miss you too my love,

Ya kashe wayan yana murmushi, Amal kenan, iyayen surutu,

 

Hajiya ce tayi sallama ya amsa da fadin my love, yunwa nakeji,

To aiga coffee dinka nakawo maka,

Cikin jin dadi yace uwa tagari Allah yasaka miki da gidan aljanna,

Tace Amin tare dakai, Allah yamaka albarka Allah yabaka lafiya

Ya amsa da Amin,

Amal na gaisheki cikin jin dadi tace Allah sarki ya makarantan nasu, yace sunanan lafiya,

Hajiya ya kama hannusa ta sakamai cofi yariqe dakyau yafara sha ahankali saida yagama sannan hajiya tace babana yace na’am my love, cikin sanyin murya tace, dady ka yaje nema maka aure,

Ya zaro idanu da fadin aure kuma my love,

Tace eh,

Cikin sanyin murya yace my love wacece zata aure MAKAHO,

my love dukda inna buqatan aure amman laluran ido, yayi mai ciwo hawaye yafara Gan garowa asaman quncinsa,

Hajiya tace babana karka damu Allahn daya daurama shine zai yayye maka, cikin sanyin murya ya laluba hannu hajiya ya riqe yace my love,

Kina ganin zan iya zama da mace a yanayin danake ciki,

Tace zaka iya nidai nasan na haifi jarumi,

Yayi murmushi yace kai naji dadi my love Ashe kin haifi jarumi, takaimai dukan wasa tasan tsokanan ta yakeyi, dan yasanta da kunya, inbai mantaba kamin yasamu laluran nan, bata wani bashi kulawa sosai, bare suyi hira, wai dan yana dan fari,

Samun lalurannan ne tasake duk wani bidi’a ,

Tanaba ma danta kulawan da yadace,

Tace kafara shiri jibi ne daurin auren inji dadynka,

Yace jibi kuma my love, tace eh,

Kuma yarinyan alhaji Hasan, my love kina nufin abban su Haidar tace eh, cikin sanyin murya yace to my love,

Tace bari inje inhada abinci dan dadynka yakusa dawowa,

Cikin sanyin murya yace to,

Tasan abinda yake tunani to ya zasuyi,

Allah yasa hakan ne mafi alkhairi,

Gidan alhaji Hasan shahararran dan kasuwa ne anan garin kaduna a unguwa dosa, dan bokane wanda duk abida kakeso shi zakayi, matarshi daya hajiya Karima, ma aikaciyar gomnati ce, irin matannan ne masu shegen son abun duniya,

Yayanta uku Haidar sai Jamila sai fatima sana kiranta da Zara, Jamila ta kammala karatunta na jami’an , ABU Zaria,

Haider yana costom yana Abuja, inda zara tace secondary School SS2,

Kida dadynta yai mata maganan auren Adam tace Allah ya sauwaqe kamar ita ta dauri makaho,

Dadynta yace yashirya aure babu fashi ,

Yana gama fadar haka yafita,

Tafada jikin momynta tana kuka,momy MAKAHO NE fa,

Momy mai zanyi da makaho,

Hajiya Karima tace ki kwantar da hankalin ki,

Ai ba mutane zamu gaiyata ba,

Babu wanda yasan ma kiyi aure,

Duk wanda yatam bayeki wa kika aura kinuna musu hotonsa,

Kinsa yarinnun yahadu yanada kyau babu wanda zai zainaki, saidai aringa karramaki,

Iyayansa nada kudi,

Kin san shi kadai suka haifa,

kuma naji ranan abbaku na waya dashi yana fadamai duk wani kadarori sa sunan Adam ne,

Mutanenan sun tara dukiya fa,

Jamila kar kimana buqulu,

Ke da kikeson zaga qasashen duniya nima kikaini,

Kudi zaki ringa tatsa masu dauyi,

Ahaka har tashawo kan yar nata,

Jamila ba fara bace amman tsabar blichin yasa tazama fara, duguwace siririya ce , inka qare mata kallon kasan blichin ne yataimake ya, amma batada wani kyau,

 

Abangaren ango babu wani shiri dan alokacin ba’a dade da canja kayan bangaren Adam ba,

Kuma anan zasu zauna,

Dakuna biyu ne , sai falo, aban garan Adam,

 

Ranar jumma’a dubbanin mutane suka sheda daurin auren Adam musa da Jamila Hasan akan sadaki naira dubu dari,Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Makaho ne Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

3 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!