Hausa Novels

Maktoub Hausa Novel Complete

Maktoub Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

P 1

#Tʜᴇ ᴍᴇssᴀɢᴇ

 

 

K’arar shigowar kiran waya shi ne musababbin da ya sata jan wani irin siriri kuma malalacin tsaki,a yangance kamar ba ta son d’auka ta kai hannu ta bud’e had’ad’d’iyar handbag d’inta made in Gucci company dake rataye jikin shoulder d’inta,yayin da kyakykyawa,kewayayyiyar farar fuskarta mai d’auke da k’aramin baki,dogon hanci had’e da manyan idanunta da suke cikin rainbow sunglasses suka fara bayyanar da damuwa,ta gefe ta d’an saci kallon y’ar uwarta da suke tafiya tare tana d’ane baki kamar za tayi kuka,kyawawa ne dukansu maa sha Allah,but da kyakykyawan kallo guda za kayi saurin gane mai rainbow glasses d’in ta zarta y’ar uwartan dake gefenta nesa ba kusa ba,but duk wanda yayi sa’ar kallonsu tabbas zai so ace ya k’ara,hannayensu rik’e cikin na juna suke tafiya,yanayin yadda suka fito suna hira da dariya gwanin kyau da burgewa,yayin da hakan zai yi saurin bayyana maka irin shak’uwar dake tsakaninsu,dan yanayin da suke ciki ba k’aramin dad’i yake musu ba,tab’e baki ta d’anyi bata bari sister d’intan ta fahimci yanayin b’acin rai da take ciki ba tayi saurin mayar da wayar silent ta tura a jaka,a hankali suka ci gaba da tafiya mai kama da yanga cikin tsakiyar babban compound d’in gidan wanda shuke-shuke suka k’awata,sanye suke da irin gowns d’innan masu zubin babbar riga,komai nasu iri d’aya ne a colour kawai ne aka samu bambanci,likewise their handbags and shoes suma duka haka,daf suna k’arasowa bakin wani brand new toyota landcruiser prado dake parke a carline wani kiran ya sake shigowa,kamar baza ta amsa ba haka ta sake fito da wayar ta zuba mata idanunta da had’ad’d’en sunglasses d’inta ya mamaye,a hankali d’ayar budurwar dake gefenta ta waiwayo a wani mugun yangance ta kalleta kad’an ta cikin glasses dake sanye a fuskarta mai launin pink,colour d’in rigar dake jikinta,fara ce itama sai dai bata kai d’ayar ba,because ita farin nata kamar ya so yayi yawa dan yadda jikinta yake kamar ka tab’a jini ya fito,tana da madaidaitan idanu,hanci da k’aramin bakinta da ya zauna saman fuskarta,a hankali tana ci gaba da kallonta da wani irin sanyayyan murya ta furta “O’ohhh.! Sweetheart why didn’t u pick?” Tab’e baki wacce aka kira sweetheart tayi ba tare da ta kalleta ba tayi k’ayataccen murmushi cikin sanyayye kuma romantic voice d’inta ta furta “Kada ki wani damu habibtiiy,guy d’in da nake baki labarinsa ne,ni na tambayesa inda ya samu number na,wai ya d’auka number ne a wayar..” Sai tayi shiru bata k’arasa ba saboda haushin da taji maganar ya bata,murmushi d’ayar ta sake yi tace “No sweetheart as u know wulak’anci babu kyau,har kina fad’amin hakan all the time nayi,ki d’auka ki ji mene ne zai fad’a.” Fuskarta da damuwa ta d’ago kamar a fusace tana b’ata rai tace “Haba mana na fad’a miki ba na son damuwa ne,shi ya cika takuri yayi ta kiran mutum,bai san lokacin da kake free ba” dariya mai sanye da pink d’in kayan tayi tana sakin hannunta,a hankali ta dawo gabanta ta tsaya tana zare glasses d’in dake sanye fuskarta,daf ta bud’e baki za tayi magana daga can nesa da su suka jiyo wani murya mai cike da kwarjini ya furta *”ISMAT!”* Yanayin da aka yi kiran kamar da fad’a. Saurin runtse idanuwa tayi tana yarfe hannu kamar ta ci chilli powder,a fili k’asa² ta furta “Huh! Ya rabb! When Yaah *BARRAQ* zai daina min titsiye idan zan fita?” Da sauri sai ta zare glasses d’in dake fuskarta ta juyo tana had’iye saliva’s very hardly,fuskarta k’unshe da wani irin munafukin murmushin tsoro tana langab’ar da kai tace “Yes!” Saurayi ne matashi kyakykyawan gaske,wanda ya had’a qualities da duk wata d’iya mace za tayi fatan kasancewa tare da shi,Ilimi,hutu,class,naira,uwa uba kyau,yayin da da kyakykyawan kallo guda za ayi saurin gane tsananin kama ta jini da suke yi da wacce ya kira ISMAT,tun da ya tsaya gurin yayi shiru yana kallonsu na wani lokaci kafin ya rik’e waistband yace “Ina za kuje yanzu da yamma?” In’ina ta fara saboda yadda ya tsare ta da idanu,ganin duk ta rikice ta kasa tsayawa guri d’aya tayi masa bayani da sauri d’ayar ta matso tana rik’e arm d’insa tace “Huh! Ya Barraq ba za mu b’ata ba,za mu dawo yanzun and..” Kallon hannunsa yayi dai² inda ta rik’e ya kalleta yana had’e rai,da sauri ta sake shi tana matsawa side ta d’aga masa hannu tace “Sorry” yace “Uhn!” Bai sake cewa da ita komai ba,ya mayar da hankalinsa kan Ismat dake k’ifi² da ido yana sake had’e rai yace “Tambayarki nake ina za kuje?” Ta d’ago tana matse k’afafu kamar mai jin fitsari tace “Umhn! Dama!” Tsawa ya buga mata yace “Za kiyi magana ko sai na mare ki?” Da sauri cikin firgici ta runtse idanu jikinta yana tsananta rawa ta k’ank’ame d’ayar,k’wafa yayi a fusace yana zare idanunsa yace “Yawon banza za ki koya?” Quickly ta girgiza kai za tayi magana cikin hayaniya yace “Zo ki wuce ciki,idan kika kuskura kika sa k’afar ki wajen gidan nan kuma sai na…” Bai k’arasa ba daga bayansa yaji ance “Za kayi mata me?” Da sauri ya juya ya kalli bayansa jiyo muryar mahaifiyarsa dake tambaya,Ismat dake mak’ale a bayan d’ayar budurwar tana jin maganar mahaifiyarsu hurriedly ta fito ta nufi kyakykyawar matar dake tsaye tana k’arewa Barraq kallo,tana zuwa ta fad’a jikinta ta saki kuka,cikin wani irin takaici Barraq ya bisu da kallo yana fad’in “Mom ban san me yasa ba kya so nayi magana ba,wasu lokutan fa yaran nan baki san ina ne suke zuwa ba,freedom d’in da ake basu idan yayi yawa za’a samu matsala Mom,idan yanzun kina nan babu tabbas ki kai gobe,me yasa Mom? Ina da hak’k’in kulawa da tarbiyyar Ismat because i’m her elder brother besides Daddy ba mazauni bane,but sai kina nuna mata hakan kamar takurata nake yi,idan wani abu ya samu rayuwarta mu duka ya samu,dan Allah Mom ki bari,idan kina bata support za kisa ta raina ni,baza ta tab’a ganin girma na ba,sannan a ko ina ne nayi mata magana za ta iya bad’e min idanu da k’asa tayi min rashin kunya,hakan ba wani abu bane sai don kina nuna mata rashin muhimmancin da nake da shi a cikin rayuwarta,ki sani Mom ba iyaye kad’ai suke da alhakin kulawa da tarbiyyar y’ay’ansu ba,mu da muke y’an uwa muma muna da namu hak’k’in.. Please Mom ya kamata ki ba ni wannan damar a matsayin Yayanta na dunga bincika al’amuranta,idan ya dace suje shi kenan,ba zan hana ba.!” Yadda ya k’are maganar muryansa a k’asa kamar zai fasa kuka idan tace ba haka ba yasa ta kasa cewa komai da farko,Ismat kam da kanta ke jikin Mom lokaci d’aya taji jikinta yayi wani irin sanyi da kalamansa,though a times tana yiwa maganarsa kallon bai² but tabbas a yanzun ta fahimci ya fisu gaskiya har Mom d’in da take mahaifiyarsu,d’ago fuskarta tayi a hankali daga jikin Mom tana sauke ajiyar zuciya,Mom da ta zubawa Barraq idanu ta kasa magana tayi k’wafa a d’an fusace tace “Kai dai Barraq always idanunka na kan yaran nan,da sun fito kace su koma ina dalili? Duka inda kake zuwa na tab’a cewa ina so na sani?” K’asa yayi da kai with elegance yace “But Mom itafa mace ce” a fusace Mom tace “Ko mene ne,thought tarbiyya d’aya muka ba ku,me yasa za ka dunga zargin y’ar uwarka eh?” Yace “Mom ba haka bane ki fahimce ni” za tayi magana Ismat tayi saurin rik’o arm d’inta cikin sanyayyar muryarta tace “No Mom! Na fahimci abunda Yah Barraq yake nufi and ya fimu gaskiya!” Mom tayi saurin kallon Ismat sai dai bata ce komai ba,d’ayar budurwar dake gefe ne tun d’azun tana kallonsu jin abunda Ismat ta fad’a da wuri tayi kicin²,quickly kafin Ismat ta sake yin magana cikin sheshshek’ar kuka tana matso hawaye ta fara fad’in “No Mom! Duk abunda yake faruwa kawai dama Yaah Barraq yana son cewa nice mai laifi,ina son koyawa y’ar uwarsa yawo,da ba haka take ba,ko fita ba ta yi sai yanzun da nake zaune da ita,ni dama ba tun wannan lokacin na fahimci ba ya son zamana a nan ba!” Saurin kallonta Mom tayi tace “Haba *BADRIYAH* waye ya fad’a miki haka?” Barraq dake kallonsu ya tab’e baki because shi ya san abunda ta fad’a haka yake babu k’arya sai dai shi bai fito fili ya yi magana ba,Badriyah cikin sheshshek’ar kuka tace “Tun ba yanzun ba dama na gane nufinsa,kawai yak’i fitowa ne ya fad’a,amman ai Allah yana gani idan na kai Ismat wani wajen da bai dace ba ko nace tayi wani abun da yake inappropriate saboda ta lalata tarbiyyar ta,Allah ya saka muku duka idan na cutar da ita,but kuyi hak’uri yanzun na gane zamana a nan ba shi da wani amfani,Mom ke da Ismat kad’ai kuke so na but Yaah Barraq baya son hakan,kayi hak’uri kaima in Allah ya yarda zan tafi na bar muku gidan ku,nima ba a son raina nake zaune muku a gida ba ai..” Tana gama fad’ar haka bata jira wani yayi magana a cikinsu ba ta juya da gudu² ta wuce cikin babban simplex apartment d’in tana kuka,Mom da duk bata ji dad’in abunda ya faru ba ta waiwaya ta kalli Barraq bata ce masa komai ba sai k’wafa kad’ai da tayi,hurriedly ta juya tana kwala kiran Badriyah then a gurguje suka bi bayanta. Kusan a tare suka shigo cikin parlor ita da Ismat suna kiran Badriyah but har sannan bata amsa ba,dai² lokacin da suke jin sheshshek’ar kukanta da takun takalminta a tare suka kallo direction da sautin yake fita,suna d’aga kai suka hangota tana saukowa daga saman wani irin rantsatstsen staircases da ya bada style mai jan hankali d’auke da trolley sai share hawaye take yi tana k’arawa,jikin Ismat banda tsuma babu abunda yake tayi saurin kallon Mom hawaye suna taruwa a idonta tace “Please Mom kada ki bari ta tafi,kice ta zauna please!” Mom cikin wani irin mutuwar jiki ta kad’a mata kai,a hankali ta fara tafiya wajen staircases tana kallon Badriyah,tana gama sakkowa Mom ta rik’e hannunta,muryarta a k’asa irin na mai rarrashi tace “Haba habibtiiy,yanzun saboda Barraq za ki tafi ki barmu,mu duka ai muna son ki,me zai sa kiyi fushi? Yanzun har akwai abunda zai yi miki ki iya tafiya ki bar sweetheart d’in ki da ni? Kinga kuka take yi itama saboda kince za ki tafi,u know ba za ta ji dad’i ba idan kika barta,please just be patience kada kice za ki tafi a wannan lokacin kin ji?” Kai ta girgiza da sauri tana share hawaye cikin muryar kuka tace “Please Mom allow me to go,ba zan iya ci gaba da zaunawa ba,Yaah BARRAQ yana min wannan kallon” Mom ta kad’a kai tana sake rik’ota tace “No habibtiiy ki zauna kinji zanyi magana da Barraq d’in,ba zai sake ba idan Allah ya so!” A hankali Ismat ta k’araso saboda rashin kuzari tana rik’e trolley d’in hannunta muryarta tana rawa tace “Please habibtiiy don’t go,idan kin tafi binki zan yi bazan zauna ba nima” Badriyah tana girgiza mata kai tace “No sweetheart ki zauna,ai ke gidan ku ne,nima zan koma gida ne,bazan iya zaunawa ba Yaah Barraq yana cewa ina koya miki wasu halin” Ismat ta kad’a kai tana share hawaye tace “Please habibtiiy kada ki tafi,Mom za ta yiwa Yaah Barraq magana zai bari,Mom kice ta bar tafiyan” Mom ta kad’a kai tace “Yeah! Zan yi magana da shi kin ji,ba zai kuma ba habibtiiy” kamar Badriyah ba ta so sai ta rausayar da kai tace “Okay!” Tana fad’an haka Ismat tayi saurin cewa “Za ki zauna d’in?” Ta kad’a mata kai cike da sakarci,Ismat tayi saurin rungume ta tana sakin murmushi tace “Thank u habibtiiy” ta bata wani deep peck a cheek d’inta guda,murmushi suka yi tare Mom dake kallonsu tayi murmushi itama then suka koma sama mayar da kayan tafiyar,Mom kam suna barin gurin ta dawo tsakiyar rantsatstsen parlor ta da yaji alatu,ko ba’a fad’a ba tsarin gidan kansa kad’ai mutum ya kalla daga compound zuwa ginin gidan dole yayi saurin gane lallai mamallakinsa ba k’aramin attajiri bane,wayarta data yasar bisan coach k’irar company’n apple IPhone 11 Pro ta d’auka,in less than two minutes ta kai wayar kunne,cike da bayar da umarni ta furta “Yanzun ka zo ka same ni a parlor” tana fad’a ta katse kiran. Barraq dake kwance saman lafiyayyen royal bed d’insa da yaji white beddings tun bayan da ya shigo yayi shiru yana tunanin kiran da Mom take masa,quickly ya tashi ya fito daga bedroom d’in,a parlor ya sameta ta hakimce,though ba wai tana da irin girman jiki ba,but yanayin zaman da tayi shi zai sa ace hakan,yadda take had’e rai tun kafin ya k’araso da ya kalleta sau d’aya yaji gabansa ya fad’i but haka ya daure ya k’araso yana satar kallonta ya zauna kad’an saman wani kujeran da fad’in “here i’m Mom” waiwayawa tayi ta kallesa tana kad’a kai then ta fara fad’in “yanzun Barraq me yasa za kayi haka? Kana son girma amma kai sam baka san yaya ne za ka same shi ba,shin idan za ka yiwa Ismat fad’an abunda take yi bai dace ba,ya kamata ka dunga nunawa a fili kana zargin da sa hannun Badriyah?” Sunkuyar da kai yayi saboda ya san gaskiya ta fad’a but shi yana yi ne ko Badriyah za taji haushi ta daina jan Ismat yawo mara dalili,silently kamar ba ya son maganar yace “I’m sorry Mom” muryarta a sanyaye tace “Daga yau ba na son haka,idan za ka yiwa Ismat fad’a saboda wani abu da tayi ba dai² ba ka had’a su duka,because Badriyah is ur cousin sis,abunda zai faru da Ismat kaji rashin dad’i itama idan ya faru baza ka ji dad’i ba,please ka bari ka ga bata ji dad’i ba,kuma ko waye aka yiwa haka ba zai ji dad’i ba,ku zauna lafiya dan Allah ba na son rigima,kai ne babba ka kama girmanka please” a hankali ya kad’a kai ya furta “In Allah ya amince Mom ba za’a sake ba” tace “better” ya jima a zaune bai sake cewa komai ba,da aka jima Mom ta kalleshi tace “Tashi kaje Allah kiyaye” yayi ajiyar zuciya yace “Thank u Mom” ta rakashi da idanu har ya shige room d’insa dake nan kusa da staircases. Suna shiga bedroom d’in kai tsaye Ismat ta wuce closet da trolley d’in Badriyah,while ita kuma ta haye saman bed tana kallon Ismat dake k’ok’arin shirya mata kayanta cikin closet kamar yadda na ta suke,tana daga saman bed a zaune ta fara yiwa Ismat maganar fitar da za suyi aka samu matsala,Ismat dake tsaye wajen lafiyayyen reach-in closet d’insu ta tab’e baki,then a hankaki ta waiwayo tana kallonta tace “Habibtiiy na fasa zuwa ni dai” hurriedly Badriyah ta d’ago kai tace “Saboda Yaah Barraq ya yi magana ko kuwa saboda me?” Murmushi Ismat tayi kad’an ta kad’a mata kai,Badriyah ta tab’e baki tace “Okay!” Daga haka bata sake magana ba ta bud’e jakarta da ta yasar gefe ta ciro phone d’inta,tunda tayi shiru ta fara clicking wayar bata sake ko tari ba ta fad’a dandalin sada zumunta. Sanda Ismat ta gama shirya kayan a hankali ta dawo kusa da ita ta zauna,tana kallonta taga fuskarta a had’e da sauri ta rik’o hannunta tana fad’in “Habibtiiy what’s up? What’s happened?” Badriyah data d’ago kyakyawar doguwar fuskarta ta zubawa Ismat idanu,kamar ba za tayi magana ba da farko ta tab’e baki tace “What’s it?” Ismat dake kallonta tace “To wannan had’e fuskar da kike yi fa?” Murmushin yak’e tayi lokaci d’aya ta sake had’e rai tana kautar da fuskarta gefe tayi k’wafa,Ismat tayi ajiyar zuciya ta kwanta tana kallonta ba tare da ta ce komai ba,da aka jima Badriyah ta gaji da kallon da Ismat take mata ta d’ago idanunta tana b’ata fuska tace “Wai me kike kallo?” Murmushi Ismat tayi tace “Kawai ina kallon yadda kika yi ne duk fa wallahi ba kiyi kyau ba,don Allah ki saki fuskar ki” siririn tsaki Badriyah tayi za ta tashi kenan daga gurin ring d’in wayar Ismat ya dakatar da ita,a hankali ta juya ta kalli jakar dake kusa da ita ta sake kallon Ismat tana had’e rai,ganin har lokacin bata daina kallonta ba a fusace tace “Ur phone miss look” tab’e baki Ismat tayi tana juyar da fuskarta zuwa kallon wani gurin tace “Ke rabu da su,idan sun gaji za su daina kira” tab’e baki itama Badriyah tayi daga haka sai bata sake magana ba,sai da taga mai kiran ba shi da niyyar dainawa a hankali ta ajiye nata wayar ta d’auko na Ismat data rufe idanu kamar mai bacci,ta d’an saci kallonta ganin number ne ke kiran babu suna then tayi amswering tana furta “Hello!” Daga can side d’in da aka kira da yake a free tasa wayar,cikin wani irin shak’urarren murya mai cike da sanyi aka amsa “Hi! How are u and how was today?” Saurin bud’e idanu Ismat tayi tayo kan Badriyah with intention of ta kwace phone d’inta,Badriyah tayi saurin janye hannunta tana kallon Ismat ta furta “Alhamdulillah! Da waye nake magana please?” Ismat taga Badriyah ba ta da niyyar bata wayar ta dad’in rai tana had’e rai tace “Habibtiiy ki bani phone d’ina mana,mene haka kin d’auki naki kuma kin rik’e min nawa?” A hankali Badriyah ta zuba mata ido while tana cewa “Na tambaya waye babu amsa” murmushi aka yi mai sauti then yace “Oh! Sorry dear,kina tare da *FAWAD!”* Ta kad’a kai tana lumshe idanu saboda sanyin da muryar mai maganar yake tattare da shi,lokaci d’aya ta ji baza ta iya yi masa rashin kunya ba,a nutse tace “Uhn! Who are u looking for please?” Ya sake yin murmushi yace “mai wayar nake nema,and na kira na bada hak’uri ne please,if na takuraki yanzun my first call was not intentional,i’m just looking for my brother,aka samu matsala nayi missing 1 digit nayi kiran line,please kiyi hak’uri it won’t happen again!” Badriyah tana lumshe idanu tace “Uhn! No problem” yace “But zan iya tambayar wani abu kuma?” Ta kad’a kai kamar tana gabansa tace “What’s it?” Yana sassauta murya yace “Ur name please?” Kai tsaye ba tare da ta yi tunani ba tace *”ISMAT!”* yayi murmushinsa mai kyau yace “Nice name” kafin Badriyah ta sake yin magana da sauri Ismat dake gefe tace “Mene ne haka kuma habibtiiy,why didn’t u tell him ur’s? Kawai sai ki kama ki fad’a masa suna na ni da ban sansa ba?” Badriyah ta kalleta tana matsar da wayar gefe tace “Wayar waye wannan?” Ismat tace “Mine” Badriyah ta harareta tace “Shi ne zan fad’i nawa dan kin rainawa kanki hankali?” Fawad dake sauraren conversion d’insu ta cikin wayar yayi murmushi yace “Ohh! Ki bata hak’uri please,na ga mun yi laifi duka” Badriyah ta harari Ismat tana sake kallon wayar dake hannunta k’iran IPhone 8 Plus tace “Rabu da ita kawai wata irin mai duhun kai ce itan,but ni babu yadda za tayi da ni” Ismat tana kallon Badriyah kamar za ta yi kuka tana nuna kanta tace “Ni kike cewa mai duhun kai?” Badriyah dai bata sake tanka maganar Ismat ba sai sauraron abunda yake fad’a take,Fawad ya sake yin dariya lokacin da Ismat ke fad’in haka yace “I’m really sorry ma’am.” Almost 30 minutes suka d’auka suna magana yana sake bawa Badriyah sak’on ta bawa Ismat d’in hak’uri then suka ajiye wayar lokacin tana kallon Ismat da taji haushi ta rufe idanu kamar mai bacci tace “Idan ba ki da duhun kai me yasa kika bawa Yaah Barraq dama yake hana mu fita a gidan nan? Wai idan bamu samu freedom yanzun ba sai wane lokaci ne? Nifa gaskiya ba na son zaunawa a gida,zama guri d’aya tsautsayi inji kifi,so why bazan fita na sha iska ba tunda i gotta chance?” Ajiyar zuciya Ismat tayi a hankali ta bud’e lumsassun idanunta tana kallon Badriyah ta yada kai gefe ba dai tace komai ba,Badriyah tayi tsaki ganin Ismat ba ta da niyyar yin magana tace “Ko yanzun abunda yasa ni ba zan fita ba raina ne a b’ace da ko baza ki ba ni kam sai na je” still Ismat bata ce komai ba,sai tashi da tayi ta nufi hanyar entrance za ta fita,sai da ta kusa door a hankali tace “Ni kam na je wajen bhai!” Badriyah ta rakata da mugun kallo a masife tace “Allah raka taki gona” murmushi Ismat tayi tana rik’e da handle na bedroom door d’in cikin zolaya tana kallon yadda Badriyah tayi kicin² tace “Ko za kije ne mu tafi tare?” Badriyah ta kyab’e fuska tana yi mata wani kallo tace “Huh! Allah tsare ni da zuwa wajensa,yanzu kam ina zuwa ai ban san me zai yi min ba kuma” saurin fita Ismat tayi tana cewa “kanku ake ji,but ni duk na kasa gane muku always fad’a ba kwa shiri” Badriyah ta tab’e baki tace “Shi dai da bai so a zauna lafiya,mutum kullum fuska kamar wanda ake aikawa sak’on mutuwa.” Ismat da ta fita tayi dariya tana tafiya cikin nutsuwarta,sanda take sakkowa da taga babu kowa a parlor,tana gama tsallako staircases d’in ta wuce hanyar bedroom d’insa,a bakin door d’in ta tsaya ta fara yin knocking,Barraq dake kwance yana operating laptop ya d’ago kansa yana tambaya “Who’s there” Ismat dake tsaye cikin cool maganarta tace “It’s me bhai” tab’e baki yayi yace “come in” a nutse ta murd’a handle d’in ta tura k’ofar,yana adjusting kwanciyarsa daga rub da ciki ta shigo,ya zuba mata tsumammun idanunsa har ta k’araso kusa da shi da sallama a bakinta,yana sake kallonta bayan ya amsa yace “Ya aka yi?” Fuskar damuwa tayi wearing tace “Bhai! Dama zuwa nayi na baka hak’uri,in Allah ya yarda ba zan sake yin abunda za kayi fad’a ba” yana kallon yadda take matse yatsun hannunta yace “Gaskiyar da nake fad’a shi ne nayi miki fad’a kou Ismat?” Saurin kad’a masa kai tayi idanunta suna tara hawaye tace “A’a kawai na fad’a ne,but na sani gaskiya kake fad’a” ya kad’a kai yana tab’e baki yace “Ok then?” Tayi shiru,komawa yayi ya kwanta yace “na ji tafi ki ba ni wajen Allah kiyaye” still tayi ta kasa motsawa,ya d’ago a fusace yace “Tafi mana,tsaiwar me kike yi min a kai kuma?” Ta d’ago kanta tana kallonsa hawaye har sun fara sintiri saman fuskarta tace “Please bhai bazan sake cewa haka ba,kayi hak’uri har abunda Mom tace please!” Idanunsa yayi saurin rufewa because a rayuwarsa ya tsani yaga tana kuka,but abunda yake shirin yi yanzun ya san dole ne ya fara koyan yadda zai jurewa ganin zubar hawayenta,a dak’ile bai yarda ya sake kallonta ba yace “Uhn! Will u get out please my friend?” tana kallonsa tace “Toh” da muryar tausayi,a sanyaye cike da wani irin mutuwar jiki ta juya ta fara tafiya tana share hawaye,ya bita da kallo har ta je bakin k’ofa za ta fita yayi calling sunanta out “Ismat!” Tayi saurin juyowa tana amsawa yace “Ina Badriyah?” Tace “Tana can bedroom” yace “Kice tazo ina nemanta,ku taho tare” amsawa tayi da sauri ta fita,sun jima sosai kafin su zo saboda Badriyah bata yarda Barraq yana kiranta ba,har sai da Ismat d’in tayi mata rantsuwa sannan ta yarda ta biyota suka taho,suna shigowa Ismat tayi sallama,ita kam Badriyah tana had’a rai tace “Ga ni ance kana kira na!” Ya d’ago idanunsa ya zuba mata su saboda jin a yadda tayi maganar da raini,inwardly yayi k’wafa yana saita yanayinsa yace “Yeah! I just want to say sorry kan abunda ya faru d’azun” tayi saurin kallonsa taga ita yake kallo shima sai tayi fuska tace “Uhn! Babu komai” yayi murmushin gefe a ransa yana wani tunani yace “Shi kenan za ku iya tafiya” Ismat da ta ji dad’in abunda yayi da sauri taje ta rungume shi tace “thank u bhai,i love u” yayi murmushi ya shafa kanta,ta juya da sauri ta kalli Badriyah dake shirin fita tace “Habibtiiy why didn’t u say u’re sorry too to bhai?” A fusace Badriyah dake tafiya ta juyo za tayi masifa suna had’a ido da Barraq da ya kafeta da kallo,quickly ta lumshe idanunta tana jin yadda gabanta yake fad’uwa saboda idanunsa ba k’aramin kwarjini suke yi mata ba,duk iskancin da take ji da shi ko fitsara ta shirya yi masa a mafi yawan lokuta da sun had’a ido da shi take jin ta kasa,muryarta tana rawa ta kasa sake kallonsa tace “I’m sorry Yaah Barraq,nima bazan sake cewa komai ba” idanu suka zuba mata jin abunda tace a k’arshe,Ismat ta fashe da wani irin dariya tana satar kallon Barraq daya tab’e baki tace da Badriyah “Ba fa haka ake cewa ba,kice baza ki sake ba” da sauri Badriyah ta kalli Ismat rai a b’ace but ta yi k’ok’arin dannewa,tana aike mata sak’on harara k’asa² tace “Yeah! This is what i want to say ai hausar ne ya gudu” lumshe idanu Barraq yayi ya juya because ya san baza ta tab’a fad’a dai² ba duk da anyi mata gyara,ya riga ya san halayyarta na girman kai ba tun yanzun ba,ba wai iya fad’a ne baza tayi ba kawai bata yi niyya bane,strictly bai yarda ya sake juyowa ba yace “Ya wuce,za ku iya tafiya” daga haka ya ci gaba da aikinsa,suka yi masa sallama Ismat a baya,Badriyah a gaba sai cika take kad’an bata fashe ba suka fito. Suna fitowa za su wuce Mom ta kallesu ganin suna fitowa daga bedroom d’in Barraq ta bisu da idanu da tambayar “Me kuka je yi a room d’in Yayan naku ku kuma?” Ismat cikin farin ciki tace “Shi ne yace mu zo” Mom ta bita da kallon tuhuma tace “Yayi muku mene ne?” Y’ar dariyar jin dad’i tayi tace “Kawai fa Mom ya bawa habibtiiy hak’uri ne kan abunda ya faru” Mom tayi murmushi tana kad’a kai saboda jin dad’in abunda Barraq din yayi tace “Alright! Ya kyauta”,saman armchair Badriyah ta kwanta tana had’e rai saboda ba ta son maganar a hankali tace “ni na baro phone d’ina a bedroom,sweetheart kira wancan yarinyar please ta kawo min” Ismat tayi murmushi tace “No bari na je zan d’auko nawa dama” ta fad’a tana wucewa hanyar staircases,Badriyah ta tab’e baki ta bita da wani kallon takaici tace “ki fad’a mata ta kawo mana,ko dole sai kin je da kanki?” Murmushi Ismat dake tsallake stairs tayi tace “Tana aiki ki jira zan kawo miki” Badriyah ta sake yin tsaki a fusace tace “Ke wallahi *ISMAT* kina da problem,wasu lokutan kina ba ni haushi,idan za kiyi aikin gidan why not ba’a fasa kawo maidservant ba? Kina sane aikinsu ne but sai ki dage kice za kiyi” Mom dake zaune tayi murmushi tana kallon Badriyah but she couldn’t talk har time da Ismat ta dawo rik’e da phone biyu iri d’aya a hannunta,tayi murmushi lokacin tana mik’awa Badriyah da tayi kicin² phone d’inta tace “take please habibtiiy!” A fusace Badriyah ta fizge tana harararta,baiwar Allah duk da hakan bata ji haushi ba ta zauna next to her tana yi mata sanyayyan murmushinta tace “I’m sorry.” Mom dake kallonsu a hankali ta kad’a kai cikin ranta kuwa mamakin halayensu da yayi daban da na juna take yi,even though they’re from one family but d’abi’un su sam babu kama,a nasu side d’in su kam da suke zaune closer to each other,duk da kowa da abunda ke ransa,tunanin kowa kuma daban,but kamar had’in baki a lokaci guda suka bud’e network d’in wayoyinsu,k’arar shigowar sak’onni a jere cikin wayar Ismat lokacin,nan take yaja hankalin Badriyah da sauri ta d’ago kai a yangancen ta kalleta tana sake had’e rai tace…

 

 

 

 

P 2

#Sᴇɪᴢᴇs

 

 

 

Da sauri ta d’ago kai a yangancen ta kalleta tana sake had’e rai tace “please either ki sa wayar ki a silent ko kuma dai ki san yadda za kiyi ya daina damuna!” Murmushi Ismat tayi ta kad’a kai a hankali saboda akwaita da sanyin rai ta sake bawa Badriyah hak’uri,daga hakan bata sake bari wayar yayi k’ara ba ta mayar da shi silent,tana shiga dandalin sada zumunta na whatsapp here ta fara gamo da rututun sak’onni daga number da ake yawan kiranta,tayi shiru tana kallon screen d’in wayar fuskarta d’auke da wani irin mamaki had’e da damuwa,then a hankali ta fara k’ok’arin bud’ewa with intention of ta ga me aka turo da yawa har ya kai 20,sak’on farko sallama ne aka yi sai na bada hak’uri da suke biye da shi wanda yake d’auke da wasu irin tausasan kalamai masu tsayawa a rai bila adadin,deeply tayi ajiyar zuciya jikinta yayi sanyi then ta fara replying masa amsa na sallamar da yayi hannunta har wani shaking yake da ta kasa gane na mene ne? Message d’inta yana yin delivered kafin ta fita taga ya turo mata sak’on godiya,quickly ta kalla taga baya online kuma,sannan bata ga lokacin da yake typing ba,ta ji gabanta yayi wani irin fad’uwa haka kawai da sauri ta fita,kusan mintuna biyu duk sai tunani take yi ta kasa duba wasu messages d’in tana sake kallon number,can tana tunani sai taga sak’o ya sake shigowa daga number dai still,bata yarda ta shiga ciki ba ta tsaya dubawa taga yace “why are u keeping me waiting dear?” Tayi still tana tunani kamar kada ta duba,sai kuma taga dacewar hakan,b’im ta sake ganin wani sakon ya fad’o,tayi shahada ta bud’e tana sauke ajiyar zuciya here taga ya ce “Why za ki barni alone? Alhalin kin san sak’on ki kad’ai ne nake da buk’ata a halin yanzun?” A hankali ta had’iye saliva’s uwa munafiki ya ji tsoron a k’uresa tana satar kallon Badriyah da Mom then ta fara typing masa “Sak’on mene ne?” Ko minti d’aya ba’a yi ba ya amsa “Kawai ina jin son yin hira da ke” strictly tace “Ni ban iya hira ba” emoji ya turo mata yana zare idanu,then yace “Why? Ba ki da abokan fira ne?” Tace “A’a ina da su,kawai bana son magana sosai” yayi murmushi ya tura mata “Ni kuma kinga ina da surutu sosai and idan na zauna guri da wuri ake sani na” tace “Ka ji dad’in ka” yace “Kema haka” murmushi tayi saboda abunda yace daga haka sai bata ce komai ba,da yaji ta yi shiru bata sake magana ba yace “Dear! Kina mene ne yanzun?” Tace “Ni wai?” Yace “Yeah!” Tace “Ina zaune a parlor” yace “Ohh! Kina hutawa kenan?” tace “Mmm!” Yace “but please! Can i ask u something?” Tace “akan mene ne?” Yace “Kawai na ji ina son friendship da ke and idan babu damuwa za ki iya sending min picture d’inki na gani?” tayi murmushi tace “Ba na tura pic a social media” yayi murmushi yace “Sai a ina?” Tace “Babu ko ina” murmushi ya sake yi bai sake cewa komai akan pic ba,sai yace “Ina sister d’inki da muka yi magana fa?” Tace “Ga ta kusa da ni,ko na bata yanzun ma kuyi magana?” Da sauri yace “No! But ki fad’a mata ina gaisheta” tace “Zan fad’a” yace “Yaushe?” Tace “Ko yaushe” yace “Me yasa ba zaki fad’a yanzun ba?” Tace “Mom tana nan” yayi murmushi yace “Kina jin kunyar Mom ne?” Tace “Sosai ma,not a little” ya tura mata emoji na thumbs up,tayi murmushi da sauri tace “Sai an jima” yace “Kina aiki ne za ki gudu ki barni?” Tace “No! Ina son yin karatu ne” yace “Ok! Kina wane school ne?” Tace “BUK!” yace “Mmm! Kice babba ce ke? Ina shiga school d’in sosai wajen uncle d’ina,he’s a Proff and a Chancellor of the school also,kin sanshi ai?” Ta ware ido da sauri tace “Proff Junayd Mutallab right?” Yayi murmushi yace “kin sansa ashe?” Tace “Yeahh! Waye ma bazai sansa ba? Besides kuma he’s my Daddy’s friend ma” daga haka sai bata sake cewa wani abu ba ta b’oye masa sauran maganar,Fawad yayi wani murmushi yace “Woah bravo! Maybe mun san juna ma fa tunda kin san uncle d’ina and matsayinsa na abokin Daddy,maybe ma har gidan ku na sani kou?” ita dai Ismat dariya kad’ai tayi tace “bye for now” yace “Ok! Bye za muyi maganar later,but kafin lokacin ki tanadar min labari mai dad’i please” murmushi tayi tace “Ban iya labari ba” yace “Har ni ma baza ayi min hiran ba kenan?” Ta tura masa emoji da ya rufe ido alamun ta ji kunya,yayi murmushi yace “shi kenan ni zan baki labarin,kina son jin nawa?” Tace “Sure” yace “Ok later” tace “thank u.” Tunda suka gama magana tana ajiye wayar ita kad’anta ta fara blushing tana wani lumshe idanu,Badriyah dake gefenta ta kalleta kad’an bata ce komai ba,a hankali Ismat tayi k’asa da voice tana sakin murmushi tace “Ana gaishe ki” Badriyah data zuba mata ido tana gesturing face tace “Waye yace?” Cikin muryar rad’a tace “Na d’azun da kuka yi magana da shi a phone” ta lumshe ido tace “Na gode” daga haka bata sake magana ba ta mayar da hankali kan phone d’inta,Ismat ta kwantar da kanta a saman shoulder d’inta kad’an tace “U know what habibtiiy?” Badriyah cikin gajiya da magana tace “Sai kin fad’a” tace “He is so kind and nice..” Kafin ta k’arasa Mom ta kallesu tace “K’us² d’in me kuke yi bakwa so naji?” Ismat tayi murmushi tace “Nothing Mom” Mom tace “Idan yayi wari za mu ji ai” Ismat tana sake yin murmushi ta bud’a idanu tace “ba zai yi ba Mom” da wani muryar shagwab’a,Mom tayi murmushi tace “Allah yasa.” Daga haka itama sai bata sake musu magana ba ta ci gaba da aikinta.  Yana kwance da rufaffen ido yana wasa da phone d’insa k’irar company’n apple,iPhone 11 pro gold colour da ya gama chart aka turo k’ofar bedroom d’in da sallama cikin wani irin romantic and husky voice mai tattare da kwarjini,hurriedly ya d’ago daga rub da ciki da yayi,ya sauke madaidaitan idanunsa da a kowane lokaci suke k’ara ma halittar fuskarsa kyau matsayinsa na cikakken namiji mai ji da gayu,k’udi da ilimi uwa uba kyau,akan d’aya guy d’in dake shigowa,ransa a b’ace ya kalleshi cikin yanayin fusata da fad’in *”AADIL!* wane irin iskanci yasa ka barni ina jiranka sama da awanni hud’u? Kawai ka fice ka sa ni zama a d’aki ni ba mace ba?” Kyakykyawan matashin da ya shigo da sauri wanda a shekaru bazai wuce thirty four ba,mai matsaikaicin tsayi,ma’abocin faffad’a kuma murd’ad’d’en jikin da ya bayyana a cikin shirt da ya ainihin kama jikinsa saboda tsaban workout mai launin red wine,da yayi asalin bayyana siffar sa na cikakken namiji,mamallakin doguwar fuska,shanyayyun grey eyes wanda za’a iya kira da “blue” at first glance,but they tend to have flecks of gold and brown,har ma a wasu lokutan they may appear to change color from gray to blue to green depending on clothing,lighting,and mood (which may change the size of the pupil,compressing the colors of the iris),dogon hanci da madaidaicin bakinsa wanda kyakykyawan bread d’insa ya zagaye,ya k’araso rik’e da glasses da yake rufe idanunsa idan zai fita,though a mafi yawan lokaci yana ta’ammali da glasses ne ba don yana so ba,but he just wear saboda idanunsa da ba ya son ana yawan maganarsu ana tankawa,yana shigowa yana unbuttoning wuyan shirt dake jikinsa,kamar ba zai yi magana ba da farkon ya daure bayan ya d’auki lokaci ya furta “Sorry Broah Mami ta tsayar da ni tun d’azun,u know tunda abubuwa suka yi kusa haka ba ni da wani isashshen lokaci yanzun idan ba an gama hidimar nan ba,kamar wani dai ni ne zan yi auren duk an takura ni!” Tab’e baki na kwancen yayi yace “Alright! Ka shirya mu fita” da sauri Aadil ya waiwayo ya kalle shi yace “Ina ne za muje *FAWAD* da wannan lokacin?” Saurin juyowa Fawad yayi a fusace yana jifansa da wani irin kallo yace “Wai kai me yasa idan aka yi maganar fita sai ka tambaya?” AADIL dake wucewa rik’e da shirt da ya cire a hannunsa ya tab’e baki yace “Ka fi kowa sanin ba na son zuwa gurin da ake hayaniya..” Kafin ya k’arasa Fawad ya tashi yana fad’in “Idan ba za kaje bane Malam kawai ka fito kai tsaye ka fad’a,ai ka san bazan ji haushi ba tunda ba yau aka fara ba” tab’e baki Aadil ya sake yi bai yi magana ba kai tsaye ya wuce hanyar bathroom,Fawad dake zaune ganin bai sake magana ba ya harareshi ya koma ya kwanta. Almost 15 mintunes ya fito sanye da white bathrobe jikinsa yana dripping little amount na ruwa,a hanakli yake tafiya cikin nutsuwa fuskarsa nan a had’e kamar gajimare sai k’amshin shower gels da suke binsa duk inda yayi,ya tarar da Fawad kwance yana jiransa,ya kalleshi kad’an ba tare da ya yi magana ba ya wuce,tsaye yayi a gaban magnifying mirror yana duba sumar kansa dake d’igar ruwa silently kamar bai son yin maganar ko ya zama dole sai yayi yace “Mmm! Thought ka tafi ai” Fawad da hankalinsa ke kan phone bai damu da kallon inda Aadil d’in yake ba yace “Saboda me?” Yace “just don’t know,but ko ka yi fushi nake nufi” still Fawad bai kalleshi ba yace “Akan me zan yi fushi?” Aadil dake tsaye gaban mirror yana kallon kansa ya d’an cije lip trying ya gyara sumar kansa ya d’age gira yace “Mmm! Cus i’m not going anywhere” hurriedly Fawad ya d’ago kansa ya zubawa Aadil d’in idanu,saboda takaici bai iya yace da shi komai ba,yayi k’wafa ya tashi a fusace zai fita,Aadil da ya bisa da kallo ta cikin mirror d’in da yake tsaye gabansa har yaje bakin k’ofa,ya saki wani irin makirin murmushin da ya k’awata kyakykyawar fuskarsa,cike da zolaya yace “my friend babu sallama?” Ko kallonsa Fawad bai yi ba ya fice had’e da banging door d’in,tab’e baki yayi a hankali alamun bai damu ba then ya fara shirinsa,as he finished ya fito in a white sleeveless da 3quarter zuwa balcony sai zuba k’amshi yake hannunsa rik’e da iPad na company’n apple da wayoyinsa,tunda ya fito ya zauna saman plastic chair yake game,deeply tunaninsa ya tafi kan ina Fawad zai je a irin wannan lokacin? Ya jima zaune shiru a gurin yana pressing pad d’in,da aka fara kiran sallar maghreb kuma tsam ya mik’e a nutse ya wuce,after ya je masjeed yana dawowa gida lokacin already har anyi salatul isha’a ya kai dubansa kan ion-plated wristwatch na Skmei dake d’aure jikin wrist d’insa here idanunsa suka nuna masa 8:35pm,a hankali ya d’an tab’e baki ya wuce zuwa flat d’insu,wasa² har to 11pm bai ji shogowar Fawad ba,da yaga babu alamun dawowarsa kuma bai kirashi a waya ba ya kashe hasken ya kwanta abunsa. Dai² lokacin suna fitowa daga bedroom kowa ta yi shiru,kafin su sakko k’asa Badriyah ta hango Barraq dake zaune a dining yana cin abinci,ta tab’e baki tana ci gaba da tafiya cikin isa har suka iso wajen,Ismat tayi murmushi tana kallon Yayanta tayi masa sallama then ta zauna next to him tace “good evening bhai” ya kad’a mata kai a hankali yace “kina lafiya?” Tace Alhamdulillah” daga haka bai sake magana ba ya ci gaba da cin abincinsa,Badriyah kam dama ko kallo bai isheta ba saboda tana jin haushinsa,sannan da suka zo bata yi sallama ba,sai tab’e baki da tayi ta koma d’ayan side,opposite da su ta zauna tana latsa wayarta fuskarta har time d’in a had’e,Barraq ya d’ago ya kalleta yaga ba ta da niyyar gaishe shi yana lumshe idanuwa yace “hey my friend! Idan kin zo waje baza ki iya yin sallama ba?” Bata yarda ta d’ago ba saboda ta sani idan tace za tayi masa rashin kunya ma ba iyawa take ba tace “Assalamu alaikum!” Ya d’age eyebrow d’insa guda ya amsa yana harararta k’asa² yace “Ko na yi wani laifin daban kuma?” Tayi shiru bata ce komai ba,sai da aka jima ta ajiye wayar tana d’aukan plate tace “Yaushe nace ka yi wani abun?” Ya d’ago kai because bai yi tunanin za ta sake yi masa magana ba,ya d’an yi jim yana squeezing fuskarsa yace “Na ga har yanzun baki daina fushi ba thought wani abu ya sake faruwa” tace “Ba fushi nake yi ba” yace “Me kike yi kenan?” Tace “nothing” ya kad’a kai yace “Alright!” daga haka basu sake yiwa juna magana ba ya mayar da hankalinsa kan abincinsa ita kuma ta ci gaba da serving plate d’inta.  Tana gama serving kanta ta fara yiwa abincin wani irin cin kamar tana had’iyar medications,Ismat ce ta fara kammalawa bayan tafiyar Barraq,da yake sun saba idan suna cin abinci baza ka ji suna magana ba har su kammala,bayan ta gama sai ta zauna shiru lokaci² tana kallon Badriyah tana jira ta gama su tafi,but duk sanda za ta kalleta sai taga still ci take duk abincin ma kamar ba ta so a haka dai take ci kuma tana yi tana clicking wayarta,tayi shiru bata yi magana ba because ta san yau haushi ne fal ranta idan tace za ta yi magana yanzun sai ta rufe ta da masifa har su kwanta bacci kuma ba zata fasa mita ba,though ta damu ta koma bedroom but haka ta daure ta ci gaba da jiranta,almost 40 minutes da gamawarta sannan Badriyah ta ture plate d’inta gefe,ta tsiyaya drink da ruwa a glass cup ta sha,ba tare da ta damu da kallon side d’in da Ismat take ba ta mik’e tsaye za ta bar wajen,Ismat tayi ajiyar zuciya a hankali ta mik’e ta biyo bayanta suka haura sama tare,as they entered idanun Badriyah suka sauka kan wayar Ismat da take haske,but haka ta wuce bata ce komai ba,Ismat dake biye da ita bata kula ana kiranta ba har kiran ya katse aka sake kira,duk kusan kiran haka suka yi ta shigowa akan idanun Badriyah but haka nan ta kasa cewa Ismat ta duba wayarta ana kira.   Lokacin da Ismat ta gama shirin kwanciya ta d’auki wayar da niyyar tasa a silent here taga rututun miss calls,to her surprise duka kiran daga number Fawad ne,even though har time d’in bata yi saving ba amma ta gane numbersa sosai,ta zaro ido tana kallo da mamaki sosai a fuskarta na lokacin da ya kira bata sani ba,ko da ta nutsu tana dubawa sai taga wayar ya jima a silent,tayi shiru tana tunani,da taga hakan ba shi ne mafita ba,a hankali ta bud’e network d’in wayar,sak’onnin da suka dunga shigowa daga garesa sun yi matuk’ar sake bata mamaki,ta bud’e tana dubawa a hankali,sai taji jikinta duk yayi babu dad’i saboda yadda ya damu da yaji ta shiru,tayi b’oyayyar ajiyar zuciya ta fara masa replying reason da suka hana tayi answering call d’insa,as soon as text d’inta yayi delivered taga ya turo mata answer babu komai dama ya jita shiru ne,shi ne ya kira ya duba lafiyarta,tayi shiru tana mamaki bcos ita ba ta ganin time da yake typing,tayi ajiyar zuciya tace “Please can i ask something?” Sak’onta yana tafiya taga ya turo mata “no problem,u can” tace “Me yasa ba na ganin time da kake typing and ur last seen?” Ya turo mata emoji na smiles kad’ai,ta d’an b’ata rai tace “Baka amsa min ba” yace “I just hid” tace “alright” daga haka sai bata sake cewa komai ba,da aka jima yaji shiru yayi tunanin ko ta sauka here ya fara kiranta,tana kallon kiran ta kasa d’auka because bata san me za tace ba,asali ma ita wani irin kunya take ji tayi magana da shi a wayar saboda bata saba ba besides kiran da yayi ta mata take k’in d’auka,har kiran ya katse tana kallo,ya sake kira for the second time,har ta yi kamar baza ta d’auka ba,ta tuna babu kyau wulak’anci ita da kanta take fad’a a times idan taga Badriyah na yi,lokaci guda ta lumshe idanu tayi answering ta kai wayar kunnenta had’e da yin sallama cikin cool voice d’inta,daga side d’in Fawad yana jin maganarta cikin kunnensa ya lumshe idanu yana gyara kwanciya,kafin ya amsa ta sai da yayi mata murmushi mai tafe da ajiyar zuciya,wanda yasa haka kawai Ismat taji gabanta yayi wani irin mugun bugawa,ta daure tana kulle idanuwanta tace “Good evening” ya sake yi mata murmushi then ya amsa “evening,how are u dear?” Tace “Alhamdulillah” yace “maa sha Allah” daga haka ita dai Ismat tayi shiru,sai shi ya fara tambayarta “Ina kika shiga,ban jiki ba tun d’azun?” Tana lumshe idanu tace “Babu ko ina,na yi karatu ne” daga haka hira sosai yayi ta mata but mafi yawanci tambayarta ya dunga yi akan karatunta,ita dai k’ark’ari ta amsa masa da “Uhmn” ko “A’a’a” duk ta kasa sakin jiki sosai,da aka jima ma bata san lokacin da bacci ya sace ta da wayar a kunne ba,Fawad ya gaji da magana shi kad’ai because time d’in ko amsar “Uhmm,um’um da a’a” da take fad’a bai samu ba,jin shirun yayi yawa yayi murmushi ya furta “Sleep tight cutie”,a side d’in Ismat kamar ta ji me yace lokacin,ta sake gyara kwanciya tana sauke numfashi cikin nutsuwa,ya sake murmusawa jin saukar numfashinta a hankali yayi hanging call d’in. Da safen bayan Ismat ta farka cikin shiri ta fito sanye da women train suite,rigar sleeveless black colour da ratsin yellow,ta kame gashinta a tsakiya da yellow d’in band,k’afafunta sakaye cikin comfortably unisex canvas yellow,a gurguje take haura staircase d’in zuwa fitness room dake next floor,saboda tsoron abunda za ta tarar a wani irin hankali ta tura door d’in wajen,a sad’ad’e ta fara lek’awa ciki cikin tsoro idanunta suka sauka cikin na Barraq dake tsaye rik’e da cup yana juya tea,da sauri tayi k’asa da kai ta shiga da fad’in “good morning bhai” bai kalleta ba yana sanye da black trouser da shirt mai launin kakin sojoji ya amsa fuskarsa babu alamun wasa “morning,sai yanzun ne kike zuwa?” Tayi k’asa da kai tana hard’e k’afafu tace “Bhai ban farka..” Bata k’arasa ba ya d’aga mata hannu da fad’in “kina jira sai na dunga zuwa ina tada ke a bacci?” Ta kad’a kai za tayi magana ya banka mata mugun kallo yace “wuce ki bani waje kafin na mare ki” quickly ta wuce ta fara motsa jikinta bata bari ya sake magana ba. Har to 9am Badriyah bata zo wajen ba,ita dai Ismat tana gamawa lokacin duk ta had’a gumi tana satan kallonsa ta tattare belongings d’inta ta nufi hanyar fita a sad’ad’e,Barraq da ya bita da kallo ya tab’e baki yana rik’e da cup d’in tea yana sipping bai ce mata komai ba,sai ma juyawa da yayi a hankali yana kallon waje ta cikin bright curtain glasses dake zagaye da ginin waje. Da sassarfa ta dunga sakkowa daga saman,tana zuwa second floor suka had’u da Badriyah a corridor dake cikin shirinta za ta sauka dining,fuskar Ismat d’auke da murmushi tana kallonta ta furta “good morning habibtiiy” Badriyah bata kalleta ba dan har lokacin bata daina fushi ba ta amsa “morning how are u?” Tace “Alhamdulillah” daga haka Badriyah ta tab’e baki tayi wucewarta k’asa duk don tana gudun kada Ismat d’in ta sake yi mata magana ko ta tsareta da tambayar dalilin rashin zuwanta gym,while ita a gurin Ismat ma tunda taga tana had’e rai dama ta san halin abarta idan tana fushi ranar baza taje wajen da Barraq yake ba idan ba dole ba har sai sanda ta gaji ta sauko dan kanta,tana ganin ta wuce tayi murmushi tana kad’a kai ta wuce cikin bedroom,tana shiga ta fara cire kayanta ta d’aura towel iya cinya ta wuce bathroom,mintuna k’alilan ta d’auka ta fito kanta nad’e cikin mini towel,ta zauna saman stool ta fara gyara gashinta then ta shafa lotion sai white powder da chapstick da tayi applying a lips d’inta,ta kame gashinta a gefe da black d’in ribbon then ta wuce closet,wasu jumpsuits suspender trousers ta d’auko mai fad’in k’afa wandon black one,rigar ciki peach color sai bak’in suspender da ta zagayo ta saman shoulders d’inta ta mak’ale shi a front na trouser d’inta ta d’aura wristwatch peach color leather one a wrist d’inta ta feshe jikinta da turarukanta masu sanyin kamshi da dad’i,tana kammala shiryawa ta bud’e door ta fito za ta wuce suka had’a ido da Barraq dake tahowa zai yi k’asa,a hankali ta d’an dakata masa ya fara wucewa then ta biyo bayansa,tana sakkowa ta wuce dining kunnenta mak’ale da earpiece bak’i tana sauraren wak’ar DJ AB,here ta iske Badriyah zaune har lokacin bata gama breakfast ba ta k’arasa tana sakin murmushi tana bin wak’ar da take saurare ta zauna next to her,Badriyah kam ko kallon inda take bata yi ba,itama bata yi magana ba tayi serving kanta ma chips da ketchup sai lafiyayyen tea data had’a a cup ta fara ci,Badriyah kam tana gama break d’in ta tashi ta bar mata wajen.  12:00pm Badriyah ta sakko daga sama tana tafiya kamar wahainiya,hannunta rik’e da wani k’aramin purse mai bala’in kyau black one,fuskarta ta ci uban heavy make-up sai walk’iya take yi,lips d’inta ya sha chapstick,Mom dake zaune cikin parlor jin takun tafiya ta d’ago a hankali ta kalli direction d’inta tana sakin murmushi tace “Maa sha Allah! U look beautiful habibtiy” Badriyah ta saki murmushin jin dad’in yabon da Mom tayi mata tace “thanks Mom” Mom dake kallonta har sannan tace “ina ita sweetheart d’in naki take? Ba tare za ku je ba?” Badriyah ta tab’e baki kad’an tana kad’a kai tace “No Mom! Ni kad’ai zanje,ai ba jimawa zan yi ba idan na tafi,da wuri zan dawo” Mom tace “Da kun tafi tare dai,kin santa yanzun idan kika tafi ke kad’ai za tayi ta damunki da waya ki dawo” Badriyah tayi murmushi tana satan kallon Barraq da zai fita cikin k’ananun kaya da suka ainihin amsarsa,ta d’aga murya yadda ta san zai ji tace “Ki barta kawai Mom ta huta tunda ba zan dad’e ba idan na je,ba na son mu fita wani matsalar ya sake arisen” Sarai Barraq ya jiyo ta ya fahimci ma’anar maganar but sai bai bada hankalinsa a wajen ba ya fice yana cewa Mom sai ya dawo,tayi masa fatan dawowa lafiya,hankalin Mom a kan Badriyah tace “Shi kenan habibtiiy Allah ya tsare,ki gaishe min da Hjy *LAYLA* d’in,kice mata in sha Allah zan shigo ko zuwa next week but before then ma dai za muyi waya,ita kuma *JAWAHIR* dama kice kada ta bari mu had’u bata zo gidan nan ba” Badriyah tana dariya ta fara tafiya tace “Tou Mom zan fad’a mata”,tana fitowa ta fara tafiya a hankali taji an fizgota ta baya,a mugun tsorace ta d’aga kai da niyyar ganin waye,idanunta suka sauka kan Barraq fuskarsa babu alamun wasa yana kallonta,rai a b’ace yace…

 

 

 

 

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!