MAKWABTAKA
FARKON LABARI
A cikin jerin dogayen gininnikan da suke kan titin
Maharjalele, Kaula Lumpur babban birnim
Malaysia.
Da misalin karfe takwas na safiyar litinin, ga
sanyin safiya, ga sanyi daga gandun dajin da
yake gefen gidajensu yana kadowa. Iskar da ke
kadawa ta yi dai-dai da yanayin garin saboda
zafi-zafin da ake
yi. Nan da nan sai mazauna garin suka sami
nishadi da walwala a wannan safiyar.
Motoci na gani na fada ne suke ta giftawa a
wannan titin, yayin da wasu jama’a da yawa suke
ta wurwucewa da kafafuwansu. Halittar Ubangiji
kala-kala, Allah daya gari bam-bam, kowacce
kasa
da nata yanayin haka da irin kalar halittunta.
Matansu sanye suke da riga da siket na yadi
(material) mai kama da atamfa, sai dan guntun
hijabi iyaka kirji, wasu kuwa riga da wando suke
sakawa (jeans da blause), sai su saka hijabi ko
dankwali babba. *Yan mata *yan gayu kuwa
gajeren wando suke sakawa iya cinyarsu da *yar
shimi. Mazansu kuwa sukan daura zani da riga
ko riga da wando da hula mai kama da Pakistan
launin bakake ko wasu kalolin. *Yan gajeru ne
yawancinsu, farare tas-tas masu
gajeran hanci da luhu luhun idanuwa, suna da
gashi mai tsayi da tsanani laushi da baki. Kusan
gaba dayansu musulmai ne kadan ne suke yin
wani addinin. Amma duk da haka ba sa shari,ar
musulunci, kowa yana holewarsa yadda yake so.
Akwai bakaken indiyawa wadanda asalinsu bayi
ne aka kawo su suma yanzu sun zama *yan
kasar suna addinin Hindu. Sunan kudinsu Riggit,
yana da daraja sosai idan aka hada shi da Naira
dan har ya fi Saudi Riyad daraja.
Umaimah Bello tsaleliyar budurwa matashiya
wacce shekarunta basu wuce ashirin da biyar ba.
Bakar fatace *yar Africa amma tafi wasu fararen
fatar kyau nesa ba kusaba. Fara ce sosai idan ta
shiga cikin fararen ba dukka ba ne zasu nuna
mata fari ba, haka hanci, idanuwa masu kyau,
baki dan madaidaici gani da gashi mai tsawo da
laushi. Kirar jikinta kuwa ba kowacce mace ba ce
ta sami irin wannan kirar. Umaimah doguwa ce
ba tsawo tsololo ba, marar kiba amma ba
bushashshiya ba.
Tsaye take akan barandar gidanta, bene hawa na
goma sha tara, tana kallon kasa tana shakar
daddadan yanayin garin. Daga gani babu
tambaya ta sami nishadi saboda annurin da yake
kwaranya a fuskarta. Matsatstsan lemon zaki ne
ta matse a kofin tangaran (fresh orange juice) a
hannunta.
Idan ta leka ta kalli titi, sai ta kurbi lemon nan
mai sanyi.
Kallon kowannensu take daya bayan daya, ta ga
suna tafe a nutse cikin nishsdi. Sabanin yadda
*yan
kasarta suke Nigeria, kowa yana tafe a zabure kai
ka ce koro shi aka yi, wasu suna tafe suna
lissafin
kudin cefane saboda masifa da suka sha mana
kai.
Sai tausayi ya rufeta har kwalla ta cika mata ido,
musamman da ta tuno danginta na karkara Fulani
masu kiwon shanu.
Ta fada a bayyane, ”Allah Ka kawowa kasata
Nigeria agaji, mu ma mu samu ci gaba kamar
*yan
kasar Malaysia.
Tana daga ido ta kalli ginin gidajen da suke
fuskantar gidanta, sai ta yi arba da mutumin nan
mai nacin kallonta shi ma a tsaye yake a
barandarsa. Daman ta ji ajikinta ana kallonta
kamar yadda ya saba.
Ta galla masa harara, ta ja dogon tsaki ta shige
gida cike da tsananin takaici, musamman yanda
ya ganta daga ita sai *yar yaloluwar rigar bacci
koriya iya gwiwarta, kanta babu dankwali. Ya yi
murmushi yana shirin ya gaishe ta sai ta koma
cikin gida da sauri. Tana shiga falonta sai ta
daga labule ta leka barandar ta ga baya nan,
daga nan ta tabbatar daman don ita yake fitowa
ya tsaya da ta koma shi ma ya bar wajen. Ta
kuduri niyyar shirya masa rashin mutunci muddin
ya ci gaba da takura mata da hana ta sakewa a
farfajiyar gidanta.
Bakar fata ne, amma daga ganinsa ba dan Nigeria
ba ne. Koma dai dan wacce kasa ne yana da
kyau da kyawun sura, dogo ne sosai mai dan
kiba kadan, fari ne sol, mai hanci da gwarza-
gwarzan idanuwa, mai yawan fara,a gami da
fararen hakora a jere reras a cikin bakinsa
madaidaici. Daga
ganinsa yana da tsafta dan dan gayu ne na
karshen zamani. Tun daga gashin kansa zuwa
gemunsa zaka gane tsaftarsa koda yaushe zaka
ga suna sheki, kamshin turarensa kuwa tun daga
benenta take fara jiyowa.
Ta daga ido ta kalli agogo, karfe takwas saura
kwata. Tana da darasi (lecture) karfe tara don
haka sai ta hanzarta fadawa wanka, kan ka ce
kwabo ta gama shiryawa ta fito tsaf sanye da
riga me dogon
hannu launin ruwan hoda (pink blause), wando
(jeans) baki da takalmi (cover shoe pink) sai dan
hijabinta baki iya kirji irin na *yan kasar Malaysia.
*Yar karamar jakar (computer laptop) ta ratayo a
kafadarta ta rufo gidanta, ta fito. Ta hadu da
jama,a da yawa a lift (*yan Malaysia, Chinese,
Indian) da sauransu, amma ba su ishe ta kallo ba
balle ta yi musu murmushi saboda bata sha,awar
ta saba da
MAKWABTANTA. Tana isa kasa ta fito daga lift ta
kama gabanta sannan ta nufo get din fita. Abun
mamaki sai ta ci karo da mutumin na mai nacin
kallonta, wanda gidansa yake saitin gidanta
shima
a hawa na goma sha tara yake, amma gininsu
daban sai dai get dinsu daya saboda duk gida
daya
ne.
Nan danan ta sake tsuke fuska ta kara daga kafa
tana sauri, domin taga ya fara mata wannan
murmushin nasa. Yana da niyyar ya gaisheta, ita
kuma bata bukatar hakan. Saurin da take ya
wuce misali, don haka nan da nan ta bace masa,
sai da ta waiga ta ga ba ta hango shi ba, sannan
ta rage tafiya ta ci gaba da tafiyarta a
nutse. Tana hawan matattakala zata tsallaka
gada zuwa daya hannun kasancewar kasashen da
aka ci gaba ba,a tsallaka titin mota sai dai su bi
ta gada. Hawan matattakala da wuya sai ta ji ta
gaji likis, kasancewar hawan da yawa. Kwatsam
ta ji wata lallausar murya a gefenta cikin harshen
turanci ana yi mata sannu da aiki.
Ta waiga da sauri, sai ta ga mutuminta,
makwabcinta. Ta yi mamaki da ganinsa saboda
ta dade da tsere masa, sai dai idan ta lunguna ya
biyo ba ta titi ba, don ta waiwaya ba ta ga kowa
na biye
da ita ba.
Cikin harshen turanci yake magana, sai da ya jero
mata tambayoyi har guda uku ba ta amsa masa
ko guda daya ba, harya fara tunanin ko ba ta jin
turanci ne?
Sai ya shiga yi mata maganar gwarawa ya fara
kacaccala Turancin yadda ko dan koyo zai gane.
Ya ce, ”Are you from Sudan? Libya? Egypt?
Ethopia? Or Mali?”
Sai ta harare shi ta kawar da kai ta ci gaba da
tafiya. Har yanzu dai yana biye da ita yadda ta ke
sauri
haka shi ma yake yi.
”What is your name?
Yasan dai dole tasan wannan kalmar, sai ya sake
ganin wata sabuwar harara daga gare ta, ta kalle
shi sama da kasa , cikin takaici ta ce, ”MAYE
kawai, sai nacin tsiya !”
Ta yi murmushi ya ce, ”Your name is Maye? Wow
nice name. A zatonsa ta ce sunanta maye. Ya
bita yana ta bayani cukin harshen Turanci, duk
magana daya sai ya ambbaci sunan nan ”MAYE.
Sai takaici ya sake karuwa a zuciyar Umaimah ta
rasa yadda zatayi dashi, kalmar karshe da ya
fada mata ita ce. ”My name is Abdul-Sabur”
Da ya ga da gaske ta kufula sai ya kyale ta, ta
wuce ta nufi hanyar makarantarsu ko tantama
babu a
FTMS GLOBAL COLLEGE ta ke yi, don ya ga ta
nufi hanyar makarantar. Idan kuwa *yar jami,ace
ya za a yi ta ce ba ta jin Turanci? Sai dai idan
idan ba ta da niyyar amsa masa ne, wannan
hujjar mai karbuwace.
Tunda ta sunkuyar da kanta kasa tana tafiya ba
ta kara dagowaba balle ta waiwayo bayanta. Ba
ta
tsaya a ko’ina ba sai a cikin ajinsu, a inda ta
sami kujera ta zauna. Zamanta ke da wuya sai
Malami ya
shigo ajin ya fara yi musu darasi akan abin da ta
ke karantawa, wato soft ware engineering.
****************************** *********
Washe gari misalin karfe goma na safe Umaimah
ta sake fitowa ta nufi makaranta sanye ta ke da
bakar abaya, sauri ta ke saboda tana da test
karfe goma sha daya. Yau ma a bakin get ta ci
karo da mutumin nata Abdul-Sabur, shi ma zai
fita. Sanye yake da wata nakar (suit). Sai da ta
yi da gaske ta gane shi,
don ya sauya taga ya kara kyau.
Ya yi mata murmushi sannan ya yi mata sallama
gami da dorawa da ambaton sunan nan da yake
zaton sunanta ne, wato, ”MAYE”.
Nan da nan ta ji ya bata mata rai, ta harare shi
ta wuce ba tare da ta amsa masa ba. Sai ya
shiga mamakin yadda *yar musulma ta ke da
bakar zuciya haka ko sallama ba ta amsawa. Ba
shi kadai ta ke yiwa haka ba,daga dukkan alamu
harda sauran MAKWABTAN, don ya ga yadda ta
ke tafiya a fusace ba ta ko kallon inda suke.
Tunda yaga Dr, Faduwa ta wuce ba su gaisa ba
ya san tabbas abin ya fi karfin Dr. Faduwa,
watakila ta gwada sau daya ta ga babu riba, dole
ta kyale ta don ba don haka ba ya san yadda ta
ke da matukar son mutane, gata da fara,a ko ka
ganta ko ba ka ganta ba zata yi maka magana.
Ya tsaya suka gaisa da Dr. Faduwa, sannan suka
dunguma su uku suka yi bakin titi. Umaima na
gabansu su biyu suna baya suna ta hirarsu cikin
harshen Nasara (English).
Dr. Faduwa balarabiyar Egypt ce. Allah Ya yi
halittarsa anan saboda ko a larabawan ma kafin
ka sami mai kyauwu irin na Faduwa sai ka
bincika.
Bata da tsayi kuma tana da *yar kiba amma a
dire take, hanci dogo, ga manyan idanuwa, da
lallausan gashi har yana taba cinyarta dan ma
koda yaushe tana cikin yanke shi. Gata *yar
gayun gaske ce tana
shiga suturunta na larabawa a mutunce, kallo
daya zaka yi mata ka tabbatar likita ce dan
sana,ar ta
dace da surarta.
MAKWABTAKA 2
Umaimah ta haye matattakala ta haura gada,
yayin da su biyu suka tsaya a bakin titi suna jiran
tasi, a
inda Abdul-Sabur zai tafi makarantarsa Inti
College da ke unguwar Subang Jaya, ita kuma
tana Sun Way University, don haka mota daya ma
zasu hau, idan aka sauke ta sai a wuce da shi.
Ba jimawa suka sami tasi suka bude suka shiga
gidan baya su dukka biyun. Bayan sun
zaiyyanowa
direba inda suke so ya kai su, sai ya danna meter
ta fara kirga musu kudinsu ba sai anyi dogon
ciniki ba, kana tafe kana ganin kudin da kaci.
Nisan tafiyarka yawan kudinka.
Dr . Faduwa ta dubi Engr. Abdul Sabur ta ce,
”Yarinyar can karama da ita sai fadin rai, ba ta
gaisar da mutane, haka ba ta amsa gaisuwa idan
an
gaishe ta. Na dauka ko don ta ganmu farar fata
ne ya sa bata amsa mana, sai yanzu kai bakar
fata ma dan uwanta ba ta amsawa. Ni kuwa
naga ba gwara
ta dinga gaisawa da mutane ba saboda halin
mutuwa ko ciwo. Ita kadai a gida babu uwa ba
uba ba miji, MAKWABCI ai shi zai fara taimakonka
musamman da yake mu ma musulmai ne *yan
uwanta. Ko ya ya ka gani Abdul?
Ka yi mata yarenku ko zata fahimce ka.”
Ya yi murmushin karfin hali ya ce, ”Wa ya fada
miki tana jin yarena? Ai ba kasarmu daya ba ko
kin zaci duk bakar fata suna jin yaren juna? Ai ba
abin da zan iya yi, sai dai na yi mata addu,a Allah
Ya sa ta gane.
Daga nan suka sauya akalar hirar dan basu saba
da gulma ba irin tamu anan ayi ta cin naman
wanda
baya nan, da aka isa makarantar su Dr. Faduwa,
wato Sun way university ta sauka, zata biya
kudin
mota Abdul-Sabur ya ce ta bari zai hada ya biya
dukka, suka yi sallama tare da yiwa juna fatan
alkhari. Ta shaida masa ba zata dawo gida yau
ba sai gobe, saboda akwai gwaje-gwajen da zasu
yi.
Direba ya fisgi mota ya ci gaba da tafiya bai
tsaya ko’iba sai a Inti Subang Jaya, inda meter
mota ta nuna kudinsa Riggit 35 ne, ya yi dai- dai
da kimanin naira dubu daya da dari bakwai. Ya
zaro ya biya, ya shiga makaranta. A inda ya ke
hada karatunsa na masters.
*Yan Nigeria sun cika kowacce jami,a da ke kasar
Malaysia, musamman jami’o’in kudi, ba kamar ta
gwamnati ba, duk da suma na gwamnatin duk
wacce ka leka zaka gansu burjik.
Wata jami’ar idan ka leka sai ka rantse a Abuja
kake saboda yawan *yan Nigeria. Hausawa da
inyamurai sunfi yawa, ko ba,a fada maka ba ka
san za,ayi rashin ji.
A lokacin da jami’an tsaro wato *yan sanda da
Immagiration suka gane cewar, ba gaba dayansu
ba ne dalibai, sun dai bi hanyar cuwa-cuwa ne
sun sami visa irin ta dalibai amma ba karatun
suke yi ba, sai suka shiga kame ba dare ba rana,
mai gaskiya da marar gaskiya a nufinsu duk
dalibin gaskiyar da suka kama makarantar da
yake zata je ta karbe shi,
wanda kuwa ba ya karatun daman ba,a san shi
ba a makaranta babu mai belinsa.
Don haka zaman gidan kaso (prison) ya kama
shi, har sai ranar da jaki yai kaho. Saboda
Malaysia ba kamar Saudiyya ba ce, wacce idan
aka kama takari za,a sako su ajirgi kyauta a
dawo dasu kasar su,
gobe idan suka hada kudi su koma a sake kamo
su a dawo da su gida kyauta. Su ba sa haka ba
zasu yi
amfani da ko sisinsu wajen kawo ka kasarka ba,
idan na *yan uwanka ba ne suka zo za su tafi da
kai, sai dai ka dauwama a nan.
Yawancinsu ko kuma na ce gaba daya Hausawan
da suke karatu a wannan kasa ba su da wannan
matsala, duk wanda ka gani karatu ne ya kai shi,
iyayensa ko kuma gwamnatin garinsu. An fi
samun matsala a wajen wasu kabilu da ba
Hausawa ba, su ne suke shiga su zauna haka
kawai ba sa karatu.
Aiki ba ya samuwa, haka babu aikin karfin da za
su yi su sami kudi, sukan sami wankin mota, sai
kuma
wannan sana,ar mai hadari, wato safarar miyagun
kwayoyi, wanda idan suka haye sun gama kudi,
idan kuma ta kwabe musu hukuncin kisa ne babu
shamaki.
Wadannan kabilun wadanda ba Hausawa ba sun fi
kowacce kabila zama a club tun daga farkon dare
har zuwa asubah, babu abin da ake sai shan giya
da neman mata, kide-kide da raye-raye. Idan sun
sha sun yi tatul fada sai ya hautsine, sai kaga
ana fasa kwalabe za’ayi cake-cake. Idan ba
jami’an tsaro suka hango ba, ba sa watsewa,
Hukumar Malaysia ta gaji da natsaniyar *yan
Nigeria sai suka shiga kwashe su don su rage
bata
gari. Duk da ba kowa ne ya hadu ya zama daya
ba, akwai dalibai na gari wadan da karatunsu ne
a gabansu.
Cikin dare Immigiration suke kai sumame a irin
gidajen da wadannan bata garin suke cika. Kama
su suke yi kawai babu ji babu gani. Saboda
tsabar razana da guje-guje har wasu sukan
dimauce su diro daga kan dogon bene daga can
kololuwa hawa na biyar ko na bakwai, ko
tantama babu farfashewa kawai suke yi, wasu su
mutu a take,
wasu su karasa asibiti, wasu kuma su jiggata har
abada sun lahanta.
Don haka suke guduwa daga gidajen su idan dare
ya yi, tunda sun fahimci da daddare jami,an tsaro
suke zuwa su kama su, sai su shige wajen ajiyar
motoci ko cikin daji har gari ya waye, sannan su
dawo gidajensu su kwanta suyi barci, daga inda
magaruba ta yi sai su fice sai kuma wata goben
za su dawo gidan. A hanya ma ba su tsira ba ana
kama su da rana, ko da kuwa ka nuna passport
dinka da Visa a jiki ba sa kyale ka, dole sai sun ji
ta bakin hukumar makarantarku. Shin sun sanka
ko ba su sanka ba?
Su na kama ka sai su tamabaye ka sunan
makarantar da kake su tuntubi makarantar. Allah
Ya kyauta, Allah Ya yi mana jagora, Ya ba wa
shuganinmu ikon gyara mana kasarmu, mu huta
zarya kasashen da suka ci gaba mu daina ganin
wulakanci da muzancin da ake mana amin.
*****************************************
Wannan kame bai zo kan su Umaimah ba, sai dai
kullum tana samun labari a makaranta, ta ci sa’a
kuwa a unguwar *yan kasar ta ke zaune, duk
rukunin gidajen ita da Abdul-Sabur ne kadai
bakake, ita ce kuma kadai *yar Nigeria.
Sai taji takaici ya rufo mata, kishin kasarta ya
kama ta, ta ji kamar ta bar karatun ta koma
kasarta talaucin ya kashe ta. Ta sake jin ta tsani
duk wata farar fata, musamman ma *yan kasar
Malaysia. *Yan Malaysia ma ta fi tsanar jami,an
tsaro da suke takurawa *yan kasarta. A wani
bangaren kuma sai ta ga ai ba laifin *yan
Malaysia ba ne, laifin
shugabannin kasarta ne Nigeria da suka ruguza
mu, suka handame mana dunbin arzikin da
kasarmu ta ke da shi.
Ita kadai dai a cikin gidanta tana ta wasi-wasi a
zuciyarta. Ta zunbura baki kai kace fada ta ke yi
da wani, tsaki kuwa da kwafa ta yi fiye da sau
dari a cikin awa guda. Tana zaune akan dinning
table din da yake falonta,
karatu ta ke da laptop dinta, amma ba ta
fahimtar komai, daga dukkan alamu rayuwa ta
tsananta a gare ta, tabbas ba karamar matsala
ba ce ta koro ta daga kasarsu ta yiwo hijira zuwa
wannan kasa mai
tsananin nisa. Daga gani ba ta jin dadin
rayuwarta musamman da ake nunawa *yan
kasarta kabilanci
ana yi musu kora da hali. Hakika badon guguwar
da ta korota daga can ba ta fi wannan kura da ta
hakura da karatun ta koma gida.
Ta fada a bayyane, ”Ya ya zanyi da rayuwata?
Ina zan saka raina? Ba ni da kowa, bana kaunar
kowa babu mai kaunata”
Sai ta dafe kai ta surnano da wani zazzafan
hawaye mai radadi.
Ta fada a zuciyarta, ”Daga dukkan alamu wata
rana za,a zo a dauki gawata a cikin gidan nan,
saboda
bakin cikin da nake ciki. Ta yi zumbur ta mike da
sauri kai ka ce zungurarta aka yi. Ta nufi cikin
dakinta da sauri ba ta tsaya a
ko’ina ba sai cikin bandakinta a in da ta dauro
alwala don ana ta kiraye-kirayen sallar
magaruba.
A gaban gadonta taa shimfida abin sallarta, cikin
nutsuwa take gabatar da sallolinta. Bayan ta idar
da farilla sai ta dinga jero nafilfili, addu,a ta ke
Allah Ya yaye mata masifun da suka addabi
rayuwarta, tana neman Allah Ya koro mata farin
ciki a cikin zuciyarta, saboda ta kasance tana
cikin kunci tamkar zuciyarta zata buga.
Ta ci sa,a kuwa ruwan sama ake ta tafkawa
kamar da bakin kwarya, ya yi dai-dai da lokacin
da Allah Ya ke karbar addu’ar bayinSa.
****************************************
Kwanci tashi Umaimah Bello ta yi watanni uku a
Malaysia haka sun yi nisa da fara karatu saboda
a farkon September suka fara, ga December ta
kusa karewa. Duk inda ka juya babu abin da kake
gani sai jama,a musamman Turawa sun shigo sun
yi bikin kirsimeti.
Ana saura kwana uku kirismeti Umaimah ta
shirya da yamma ta fito ta yiwo sayayyar kayan
abinci,
duk abincinta ya kare, saboda tasan idan aka
shiga bikin kirsimeti manyan super market da
malls za su cika da jama,a.
Sanye ta ke da riga da siket *yan kanti (purple
color), sai dan karamin gyale baki da ta yane
kanta,
tana sanye da takalmi baki a kafarta mai tsini
kadan, ta ratayo jakarta baka. Iska mai sanyi ce
ta ke kadawa saboda anyi ruwa an dauke, ba ta
tsaya a ko’ina ba sai a tashar jirgin kasa da yake
tafiya a sama (Mono rail). Shi wannan
jirgin kasan a sama yake tafiya anyi masa
hanyarsa *yar siririya a sama, wadanda ke cikin
jirgin suna
hango mutane da titinan motoci a kasa. Jirgin
yana dauke da kujeru da yawa, amma akasarin
wajen tsayuwa ne ya fi yawa fiye da
kujerun zama, don an yi karafunan rikewa da
wasu igiyoyi a ake rikewa. Jirgin ba shi da direba
computer ce kawai ta ke tukawa, haka ba ya
ribas gaba kawai yake yi. ***************
*************************
da fatan littafin ya muku,
am gaskia ya kamata kowa ya bada contribution
na comment dinsa . Dan ina son post twins a
rana ammana sai ana samun ishashen commnt
ne shine zai bada daman yin hakan..
MAKWABTAKA 3
Manyan ledoji biyu ta cika makil da kaya, don
haka ta fara tunanin hawa tasi wacce zata kai ta
har
kofar gida zai fi yi mata sauki don idan ta ce zata
bi jirgi zata sha wuyar hawa da sauka benaye.
Don haka saita tsaya a titi ta tsayar da tasi ba
tare da bata lokaci ba, ta shige ita da kayanta
dukka. Ta
sanar masa inda zata je, ya danna meter suka
nausa. Da suka isa unguwar sai ta dinga nuna
masa
hanya har bakin get din gidan su. Ta biyashi
Riggit 10 ne cif-cif, sannan ta jido ledojinta ta
fito mai tasi yaja motarsa ya tafi abinsa.
Kamar daga sama ta ji wata murya wacce ta ke
kokarin gusar mata da farin cikin da ta kunso
daga BB Plaza.
Kalmar ”MAYE” ta ji ya ambata, Ta waiwayo a
fusace Abdul-Sabur ne ya nufo ta da farin cikin
sa. Ta ji kamar ta kifa masa mari, sai tayi tsaki
ta juya da sauri yayin da nauyin ledojin hannunta
suke rinjayarta.
Cikin harshen Turanci ya ce, ”Maye, taimakonki
da leda daya, saboda naga kayan sun yi miki
nauyi.
Ba ta amsa masa ba, sai ta ci gaba da tafiya, ya
kai hannu zai karba ta daka masa tsawa.
Cikin harshen Hausa yau ma ta yi masa magana.
Kai ! Ka kyale ni, dole ne?
Duk da ba ya jin yarenta ya ga alamar fushi a
fuskarta, ya san fada take yi masa. Don haka sai
ya
sakar mata ledarta ya tsaya cak yana kallonta
har ta haye branda, ta ci gaba da jan Ledojinta
sannan ta shige lift ta haye sama.
Masu suna daga zaune suna kallonsa daga
dukkan alamu suna tausaya masa saboda
kacaccalawar da ta yi masa. Ya wuce gidansa
ransa ba dadi, babu
abin da bai saka ba a ransa game da Umaimah,
ya kudira har karshen rayuwarsa ya daina kula
ta.
Tunda Umaimah ta shiga gida ta rufe dukkan
wundunanta da kofofinta ta kashe fitulun dakunan
falo da korido, kicin dinta ne kawai da fitila. Ac
da talabijin ce kawai a kukkunne. Wanka, Salla,
cin abinci, karatu bacci da kallo kawai ta ke yi
acikin gidannan ita kadai, sai da ta shafe sati
guda cur ba ta leka wundo ba ma balle ta fito
baranda ko ta fito waje.
Tana ta kallon yanda ake ta bukukuwan kirsimeti
a talabijin, ba ta damu ta ga kowa ba kamar
yadda ba ta so itama aganta. Dama a ce ba sai
ta fita makaranta ba za,a dinga turo mata
darasin da za a koya mata ta computer, ba dan
dole ba ba zata sake lekowa waje ba, don ita
wannan rayuwar ta ita kadai ta fiye mata dadi.
A ranar ne da daddare misalin karfe goma na
dare, ta ji ana buga mata kofa. Mamaki marar
misaltuwa ne ya rufo mata, don tunda ta ke a
gidan nan ba ta taba yin baki ba, ba ta da kowa
a kasar nan. *Yar karamar shimi ce a jikinta da
gajeran wando nan
danan ta yayimi zubulelen hijabinta ta saka tana
sanda ta zo ta leka ta hudar da ke jikin kofa. Sai
ta ga wata mace duk da batasan sunanta ba,
tasan MAKWABCIYARTA ce, sun sha haduwa a lift
ko a bakin get amma basa magana. Kawar Abdul-
Sabur ce, don tana yawan ganin su tare, wato
Dr.Faduwa.
Sai taki budewa, kuma har yanzu Dr. Faduwa ba
ta daina buga kofar ba gami da danna kararrawa
ba kakkautawa.
Umaimah tana jikin kofar tana kallonta ta ki ta
bude, fiye da mintina goma. Daga karshe Dr.
Faduwa ta zaro wayarta ta kira Abdul-Sabur cikin
harshen turanci ta ke shaida masa tana ta
bugawa
ba,a bude ba, da alama dai babu kowa a gidan.
Ba ta ji amsar da ya bata ba, sai taga ta kashe
wayar ta
ci gaba da kai-kawo a koridon. Ba jimawa sai ga
Abdul-Sabur ya bayyana, sanye yake da doguwar
riga jallabiyya fara da carbi a hannunsa, daga
dukkan alamudai daga masallaci ya ke.
Ya hau bugun kofa da karfi, yana danna
kararrawa shi ma kamar yadda Dr. Faduwa ta yi
ta gaji ta bari.
Umaimah na labe tana kallonsu ko kwakwkwaran
numfashi ba ta yi balle ta yi tari. Banda haushin
su
ba abin da ta ke ji, ta rasa dalilin shishshigin da
suke yi mata, sun takurawa rayuwarta. Saboda
takura ta baro kasarta ta zo inda ba,a taba
saninta ba. To saboda me za su saka mata ido,
dole ne a yi mutuncin?
Ta ci gaba da saka yadda zata bullowa Abdul-
Sabur ya kyale ta, ta yi rayuwarta ita kadai,
yadda ta tsarawa kanta.
Nan dai ta ga su Abdul Sabur suna tsaye suna
shawarar yadda za su yi. Sun yi shawara kala-
kala, sun yi shawarar kiran jami,an su zo su balla
kofar su gani, ko suje makaranta su fada, ko
kuma su
sanarwa masu gadin gidan (security).
Shawarar da suka tsaya mafi sauki, ita ce su fara
sanarwa masu gadi. Nan da nan taga sun juya
sun nufi lift ta tabbatar bakin get suka tafi. Ta
ruga daki da gudu ta je ta saka kayanta, wata
doguwar rigar leshi ce (gown) ta saka da dan
karamin hijabi ta dawo bakin kofar ta tsaya tana
jiran wanda Allah Zai kawo.
Ba jimawa sai ga security guda biyu a bakin
kofarta, hannayensu cike da makullai suna kokarin
soka makulli a jikin kofar gidanta, sai ta yi wuf ta
bude ta bayyana a gabansu cike da mamaki a
fuskarta.
Cikin harshen Turanci ta tambaye su, ”Lafiya me
yake faruwa ne? Sai suka yi cirko-cirko suna
kallonta amsa daya ta gagare su. Da kyar dayan
ya bude baki ya ce.
”Makwabtanki ne suka lura sati guda ba sa jin
motsinki, kuma ba,aga fitarki ba, sun buga ba ki
bude ba, shine suka sanar mana za mu bude
gidan mu ba ko lafiya? Ta hade rai tare da
yamutsa fuska, ta ce, ”Ina nan, lafiyata kalau. Sai
dai inaso ku jawa wadannan makwabtan nawa
biyu kunne, mace da namiji su fita daga harkata,
musamman namijin yana
takurawa rayuwata. Ku fada masa ba shi ba ni,
ya rabu da ni tunda ba zamansa nake yi ba. Suka
amsa mata da, ”To zamu sanar musu…
Basu rufe bakinsu ba, sai ga Abdul-Sabur da Dr.
Faduwa sun taho da sauri hankalinsu a tashe
suka nufo su. Kafin su karaso Umaimah ta ce da
ma’aikatan ”Good night.
Ta shige gida ta banko kofa ta datse ta ci gaba
da lekensu ta jikin hudar kofar. Dr. Faduwa ta
tambaya a dimauce, ”Kun bude
gidan, tana nan lafiya?
Sai suka shaida musu duk abin da ya faru, kuma
suka dora da sanar da su sakon da ta bayar a
fada musu. Dr. Faduwa ta dubi Abdul-Sabur
shima ya dube ta, sai ya sunkuyar da kai kasa
cikin jin kunya ya rasa abin da zai ce.
Ma’aikatan suka wuce suka barsu a nan a tsaye
suna ta kallon kofar gidan Umaima.
Can Dr. Faduwa ta nisa cikin kufula. ta ce,
”Abdul tsayuwar me muke yi anan? Mu koma
gidajen mu mana, ai maganinmu kenan da shiga
shirgin da babu ruwanmu. Kai duk ka jawomin
harna fara baccina mai dadi ka ishe ni da waya in
zo in duba ta. Ashe duk bugun nan da
muke tana jinmu don tsabar rainin hankali ta
kyalemu saboda tsabar tsana. To ma ye ya yi
zafi zamu zauna muna wulakanta kanmu, muna
yar da girman mu akan *yar yarinya karama
kamar wannan? Allah Ya gani mun fita hakkin
MAKWABTAKA.
Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce, ”Kin fadi
gaskiya Faduwa, ki yi hakuri da na jawo miki,
insha Allah bazan kara jawo miki irin wannan ba.
Sai suka juya suka tafi, yayin da Umaimah ta
jingina ajikin kofar ta dade a tsaye, ita kanta ta
rasa dalilin da yasa ta ji aranta ba dadi. Ta san
tabbas bata kyauta musu ba, ai wanda ya kulaka
ya damu da hakin da kake ciki mai kaunarka ne.
Amma ba laifin ta ba ne, zuciyarta ne batason
makwabtaka. Ba ta so adinga bada hakkin
KAKWABTAKAR.
****************************************
Gaba dayansu jarabawa suke yi, don haka
kowannensu ba ya zama a gida, gari na wayewa
sai su fice makaranta, sai da magaruba kuma.
Wasu lokutan Umaima tana rigasu dawowa, tana
daga kan barandarta ta ke hango dawowar su,
sai tayi sauri ta koma cikin gida, don kada ma
Abdul-Sabur ya hau sama ya bude barandarsa ko
wundo ya ganta.
Shi ma ya sha hangenta tana tafiya, ko tana
dawowa daga makaranta, amma bai sake
marmarin saukowa su hadu ba. Ya cika da
mamakin dalilin da yasa ta ke wannan muguwar
zuciya kamar ba musulma ba, harya fara tunanin
kilama ba musulma ba ce, hijabin dai kawai take
sakawa don ta saje da *yan kasar kamar yadda
wasu baragurbi ke yi idan suna son su cimma
wasu manufofi nasu.
A haka suka ci gaba da zama har suka gama
jarrabawar semester, aka rufe makarantu. Da
yawa daga dalibai suna ta shirin tafiya gida hutu,
saboda yana da yawa yayin da wasu irin su
Umaimah suka
mike kafa ba in da za su je.
Abdul-Sabur ya yanki tikitin jirgin sama na
komawa kasarsu Ghana don yin dogon hutun nan.
Haka Dr. Faduwa ita ma a satin zata tafi kasarsu
Egypt. Don ta shekara ba ta je ba.
Ranar da Abdul-Sabur xai tafi harya saka
kayansa a tasi sai ya garzaya gidan Umaima ya
sakale wata
farar takarda a jikin kofarta, ya juya da sauri ya
tafi.
Jirginsa na dare ne dan haka kwana da yini suka
yi a hanya ya isa Accra babban birnin Ghana. Sai
bayan tafiyar Abdul-Sabur da kwana uku Umaima
ta fito zata je Bukit bin tang za ta yi cefane,
sai ta razana da ganin doguwar wasika a jikin
kofarta, alhali bata da kowa, kuma ba ta san
kowa
ba a kasar.
Ta dade tana tofa addu’o’i kafin ta taba takardar,
sannan ta dangwala hannu a kikin takardar, ta yi
sauri ta cire hannunta alamun tsoro, kai ka ce
wuta ce ta done ta. Ta sake mika hannu a karo
na uku kamar mai tsantsani, kamar wacce zata
taba kashi ta zaro takardar ta bude a tsorace.
Marbass Dan Aunty…
MAKWABTAKA 4
Ba komai ba ne a cikinta illa zankadeden rubutu
cikin wani kayataccen turanci. Ta fara karanta
saman, sallama ce cikakkiya aka yi mata.
Ko waye mai wasikar nan cikakken musulmi ne,
don haka ta sami kanta da kosawa ta karanta
abin da ya ke cikin takardar. Cikin nutsuwa ta
hanzarta karanta cikakken sunan marubucin
wasikar
Abdul-Sabur Abdul-Rashsid, wannan ne ya sa ta
yi kokwanton ko ba ita aka yi wa takardar ba,
kuskure ne aka samu don ba ta jin ta taba cin
karo da mai irin wannan sunan. Ta manta a
lokacin da mutumin nata mai kiranta da MAYE ya
fada mata sunansa.
Ko da ta fara karanta layi na biyu daga cikin
wasikar sai ta ga kalmar ‘MAYE’ ta bayyana, don
haka ta tabbatar ta tabbatar wasikar ta ta ce,
daga makwabcinta ta ke. Sai ta ji ranta ya baci,
ta yi kwafa ta gyada kai saboda takaici. Ta
yamutse fuska ta fara karantawa a shelake.
Ta gyara tsayuwarta, ta gyara gilashin idonta
sosai ta ci gaba da karantawa, nan da nan taji
kafarta
kamar ba zata iya daukarta ba, saboda sagewa
hade da tashin hankali. Sai ta ji ba zata iya fita
ba kuma, ta koma cikin gida ta zauna a gefen
gadonta tana karantawa. Ta na sake maimaitawa,
yayin da
taji kanta ya yi mata nauyi, zuciyarta tana ta
bugawa kamar zata fashe. Ta jji ta shiga damuwa
marar adadi, ta ji kamar an zare mata lakka. Wai
shin me yake faruwa? Me Abdul-Sabur ya rubuta
mata ne da ya ta ba zuciyarta haka Oho?
Allah Shi Ya barwa kanSa sani.
Har ta kwanta cikin dare ta ji maganarsa tana yi
mata yawo a kwakwalwarta, sai ta laleba fitilar
da ke gefen idonta ta kunna ta sake jawo wasikar
a karkashin filonta ta karanta, ta sake
maimaitawa.
Hakika maganganun gaskiya ne, amma tana
ganin ba zata iya bin gaskiyar nan ba, don zata
takura.
Daman masu magana suna cewa, gaskiya daci ne
da ita.
Abin da ya rubuta kuwa ba wani abu ba ne illa
aya ce guda ya dauko sukutum don ya
wa,azantar da ita, don yana tunanin jahilci ne
yake damunta.
Da Turanci ne amma ga fassarar kamar haka:-
Assalamu alaikum warahamatullahi wa
barkatuhu.
Ya *yar uwata musulma ‘MAYE’ ina matukar jin
ciwon halayenki a matsayinki na musulma. Shin
ko kin san MAKWABCI a musulunci?
A’a ba ki sani ba,
don da kin sani da kin dinga amsa sallamar
MAKWABTANKI. Idan ni namiji ne kina zargin zan
cutar da ke. Dr. Faduwa fa?
Ki yi tunani ki gyara halayenki. A cikin arba,una
hadis, hadisi na goma sha biyar Manzon Allah
(S.A.W) ya ce, ”Duk wanda ya zama
ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira, to ya
kyautatawa makwabcinsa.
Ki sani makwabci ba karamin hakki gare shi akan
makwabcinsa ba. Daga karshe ina yi miki sallama
na tafi kasata Ghana. Allah ya kaddara
saduwarmu, amin.
Daga Abdul-Sabur Abdul-Rashid.
****************************************
Dr. Faduwa ma ta tafi kasarta Egypt, bayan
tafiyar Abdul-Sabur da kwanaki uku. Sun tafi sun
barwa
Umaima gidan sai ta yi ta leke-lekenta ita kadai
babu mai kulata bare ya takura mata. Tama
yawan
tsayawa baranda ta yi ta kallon titi, idan ta gaji
da tsayuwa akan baranda, sai ta jawo doguwar
kujera (stool) ta zauna, idan ta fara gyangyadi
sannan ta tashi ta shiga cikin gida, ta kwanta
akan doguwar kujerar falonta, ko kuma ta wuce
daki kan gadonta. Ba ta cika yin girki ba, sai dai
tayi ta shan
shayi da biskit, ko lemo (juice) da biskit abincinta
ke nan.
Sai jifa-jifa take dafa abinci, shima ba wani
kayatacce ba ne, shinkafa da wake da mai da yaji
ne saboda ba ta da walwalar da zata nutsu ta
shiryawa kanta abinci mai dadi.
Tana sallah ta yi addu,a sosai, haka kuma ta ke
ware lokacin da take shirgar kuka, kusan kullum
sai tayi wannan kukan saboda tuna baya. Tabbas
kawai rayuwa ta ke amma ba ta jin dadin
rayuwarta, tana iya kwana biyar bata furta kalma
daya ba, banda karatun sallah bata magana.
To idan ta yi maganar ma da wa za ta yi?
Daman da tana da waya ne ta amsa waya ta kira
ko a kira ta,
to ba ta da waya don bata bukatar asan tana
raye. Anya kuwa rayuwa zata yiwu a haka?
Ace mutum shi kadai zaiyi rayuwa a duniya, babu
dangim babu MAKWABTA, babu abokai? Kai abin
da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, inji
masu iya magana.
Umaimah dai haka ta zabarwa kanta, sai ta dade
tana kallon barandar Abdul-Sabur, ta ga kamar
zata ganshi amma sai taga wayam! Idan iska ta
kada wundon kabule ya kada, sai ta bude ido
tana
kallo, sai ta zaci motsinsa ne sannan taga ba shi
ba ne. Ashe dai ko ya ya mutum yake dadi ne
dashi?
Tabbas tana jin ba dadi da ta zamo babu wanda
ya san da ita. Ga shi anyi hutun makarantu balle
ta je makaranta duk da ba hira ta ke da kawaye
da abokai ba,
amma dai tana dan jin sanyi a ranta, kuma tana
rage lokaci akan dogon zaman da ta ke yi da ta
ke
yi agida ita kadai.
Dare ya ki yi da wuri, idan da daddare ne ta ga
gari ya ki wayewa da wuri. Dogon hutu ne aka
basu na tsawon watanni uku, gashi ko wata daya
ba ta cika ba, zaman duk ya gallabe ta. Tana ta
sassaka abubuwa aranta. Ta yi shawarar ko ta
tafi Negeria, amma garin da ba a taba saninta ba
ta je ta gama hutunta ta dawo? Ko
kuma ta tafi dubai ta shakata ko zata ga
abubuwan da za su nishadantar da ita, ta ga
jama,u kala-kala daga kasashe daban-daban?
Amma tana fatan kada Allah Ya sa ta hadu da
*yan kasarta *yan garinsu wadanda suka taba
saninta a rayuwa. Domim dubai ta zama
matattara, kuma cibiyar cinikayya mutane daga
kowacce kasa a duniya zuwa suke. Sai ta ga da
taje Dubai me zai hana ta tafi Saudia don tayi
umara ta fadawa Allah bukatunta duk da tasan
duk inda bawa yake ya yi addu,a Allah Yana
ganinsa, kuma Mai amsawa ne.
Yadda rayuwa ta kuntata a gare ta ina ita ina
maganar nishadi? Ai gara ta je Saudia, ta kaura
Ka,aba da Shabbaki, tunda ita a ranta ta fi
kaunar mutuwa da ace ta ci gaba da rayuwa a
haka.
Sai ta surno da hawaye zafafa a lokacin da take
binciko Passport dinta, tana tunanin yadda
rayuwa
ta cunkushe ta cakude mata cikin dan kankanin
lokaci tana karamarta. Ta fada a bayyane yayin
da ta saka gefen hannunta ta sharce hawaye.
”Alhamdu lillah alah kulli halin”. Ta fada a
bayyane.
Yadda taga dare haka ta ga rana, tana ta sake-
sake iri-iri a ranta. Kafin gari ya waye zuciyarta
ta tsayar mata da shawarar gwara ta tafi Saudia.
Gari na wayewa laraba ce, misalin karfe goma sha
daya na safe Umaima ta fito a shirye tsaf cikin
kyakykyawar shigarta, dogon hijabi ne har kasa.
Babu abin da ake iya gani a fuskarta sai tafukan
hannayenta. Ta ratayo jakarta mai dauke da
Passport dinta da kudi masu yawa. Sannan ta
hado da ATM Card dinta, don idan kudi bai isa ba
ta fitar da wani.
Tana fitowa titi, sai ta tsayar da tasi tana zama
ta ce ya kai ta, ‘JALAN AMPANG’ unguwar da
ofisoshin Embassy suke. Ta shaida masa
Embassy Saudi Arabia ta ke so ta je. Ba tare da
bata lokaci ba suka tafi, Riggit goma sha tara ne
dai-dai, ta bashi ashirin ta wuce ba tare da ta
karbi canjin ba.
Shigarta ke da wuya sai ta ga ma’aikata na
girmamata, sun karbeta cike da fara,a saboda
shigarta da ta burge su. Ta koro musu bayanin
cewar Visa ta ke nema zuwa Saudiyya har
tsawon
wata guda saboda tana so taga likita a can. Nan
danan aka yi ta dogon Turanci da cike-ciken
takardu aka ce ta dawo bayan kwana biyu, bayan
sun karbi Passport dinta Sai ta tsinci kanta tana
mai farin ciki tun bata tabbatar za su ba ta ko ba
zasu ba ta ba. Tana komawa gida ta kama
harhada kayan tafiya ta zuba a akwati. Kirga
awanni kawai ta ke yi don ta kagu kwana biyu ta
cika taje ta karbo Visa, tikiti kawai zata yanka ta
hau jirgi ta isa kasa mai tsarki. SAUDI ARABIA
Haka kuwa aka yi, kafin sati ya zagayo Umaimah
har ta hada komai ta isa gari mai albarka,
Madina.
Satinta biyu a Madina ta kaura kacokan
Shabbaku, bacci ne kawai ya ke dawowa da ita
dakinta na Hotel. Addu’a kawai ta ke akan
dimbun bukatunta da kuma fatan cikawa da
imani. Sannan ta dawo Makka a inda ta ci gaba
da gudanar da ibadunta. Kwana take a harami
tana dawafi, da nafilfili. Addu’a ta ke, amma fa
kuka ta ke da hawaye tana fadawa mai kowa mai
komai
abin da yake addabarta.
Takan saki nikaf dinta ta rufe fuskarta idan ta
hangi *yan uwanta bakar fata, musamman idan
ta ga *yan Nigeria ne Hausa/Fulani, saboda ba ta
so dai-dai da rana daya ta hadu da fuskar da ta
sani.
A ranar da ta cika wata guda cur a ranar kuma
zata koma gida Malaysia, da daddare misalin
karfe tara tana cikin dawafin bankwana sai ta yi
kicibus da wani abu daya firgita ta, ya ba ta
mamaki, ga shi cikin rashin sa,a ba ta saka
nikafinta ba. Fuskarta a bude take tarr ! A fili ga
hasken lantarki tamkar da rana.
Kamar yadda ta hadu da mummunan faduwar
gaba mai dauke da dimbin mamaki a bayyane a
fuskarta haka ta ga ya faru da su su ma. Ta
tsaya cak tana kallonsu yayin da suma suka
kame suna dogon kallonta.
Abdul-Sabur Abdul-Rashid na hannunsa na
sakale a kafadar wata mata daga dukkan alamu
dai matarsa ce, wacce yake matukar so da
kulawa. Sai Matar ta yi mamaki da razanar da
Umaimah da Abdul-Sabur suka yi da suka ga
junansu. Nan aka hau kallon-kallo tsakaninsu su
dukka ukun ba tare
da wani daga cikinsu ya iya furta kalma daya ba.
Umaimah ce ta fara gaggauta barin wajen, ta
kutsa cikin jama,a tun suna hango ta har ta bace
musu.
MAKWABTAKA 5
Umaimah ta sauka a kasarta Malaysia a cikin
gidanta. Tabbas addu,a ba ta faduwa kasa, Allah
Ya
na amsa addu’ar bayinSa a duk sanda suka
rokeShi. Ta riki Allah Ya yaye mata kunci da
damuwa nan da ta addabi zuciyarta. Haka kuwa
ta sami saukin damuwar nan da ta dankare mata
a zuciya. Ita kaidai agidanta amma tana ta
nishadi. Wannan muguwar faduwar gaba da
mugayen tunani na tuna abubuwan da suka faru
da ita a baya duk suka ragu. Haka Allah Ya amsa
addu’arta Ya rage mata tunanin matattun da ta
rasa a cikin danginta,
ta sami tawakkali a ranta cewar sun tafi ba zasu
dawo ba. Ta yi tawakkali da *yan uwanta jinin
jikinta, masoyanta na hakika da ta rabu da su
karfi da yaji. Ta tattara tunaninta, rayuwarta da
lamuranta ga mahaliccinta. Shi kadai ne gatanta,
kuma Shi ne mai
taimakonta.
Ta sami nutsuwa nan ta jawo takardun karatunta
ta yi ta karatun abin da za su yi nan gaba tun
ma kafin a koya musu. Don haka daga dukkan
alamu zata fi *yan ajinsu ganewa. Karatu ne ake
yinsa cikin sauki babu neman wani biro da littafi
ana dogon rubutu (note), a computer (internet)
za ka yi ta dubawa, kowa yana da printer sai dai
ka yi ta fitarwa a cikin takardu kana karantawa.
Bayan nan ta mallaki manyan littafan karatu (text
books) wadanda suke bayani filla-filla game da
abin da ta ke karanta, su ma suna taimaka mata
wajen ganewa sosai da sosai.
Da hutu ya kare sai ta ci gaba da zuwa
makaranta tana daukar darasi. Kullum ba ta fashi
asabar da
lahadi ne kawai take zama a gida ta yini tana
bacci safe da rana, da yamma kuma ta tsaya
akan baranda tana kallon titi. Idan dare ya yi sai
tayi karatun boko ko kur’ani, sai ta yi dan kallo
ta tashi
ta fara salloli (kiyamullaili), abubuwan da take
gudanarwa a rayuwarta kenan a kasar nan.
Har yanzu Dr. Faduwa da Engr. Abdul-Sabur ba
su dawo ba, ba wai ta damu su dawo ba, amma
koda yaushe suna fado mata a rai. Har ma ta fi
kaunar kada su dawo balle su fara shiga
rayuwarta. Ba ta ki ace da suka tafin nan ba sun
tafi ke nan har abada, zai fiye mata sauki don ba
ta son a dinga gaisawa kamar yadda suka bukaci
haka daga gare ta. Tasan sun fi ta gaskiya, kuma
ba ta kyauta musu ba.
Maimakon ta yi ta rashin kyautawar ai gara ace
ba sa nan, ba ta gansu ba, basa ganta ba. Don
ba zata iya yi musu abin da suke bukata daga
gare ta ba wannan alkawari ne ta yiwa zuciyarta
babu ita babu wani MAKWABCINTA har abada.
****************************************
A yammacin ranar lahadi misalin karfe biyar na
yamma, Umaimah na zaune a babban wajen
shakatawa na sun way Lagoom tana bangaren da
aka killace namun daji (zoo). Tana zaune a gefen
wani dutse wanda ke bulbulowa da ruwa, tana
hango namun daji da dandazon Turawan da suke
ta layin kallo da daukar hotuna. Iska mai sanyi
ce ta ke ta kadawa har cikin kanta ta ke jiyo
sanyin iskar duk da dan karamin hijabin da ta
saka. Riga da siket ne a jikinta *yan kanti masu
launin fari da baki, sannan ta saka takalmi fari
mai tsananin tsini da jakarsa fara.
Turawa biyu ne mace da namiji daban-daban
sukazo suka roke ta ta yarda su dauki hoto da ita
saboda ta yi kyau sosai. Sai ta tsinci kanta tana
duban jama,a tana murmushi ita ma kamar yadda
suke yi mata murmushi da zarar sun hada ido da
ita.
”Assalamu alaikum”.
Kalmar da ta jito kenan cikin kamilalliyar murya a
saitin kunnenta na dama. Nan da nan ta wurga
ido ta dubi inda muryar ta fito. Kafin ta gama
waiwayowa kamshin turarensa ya daki hudojin
hancinta, ko ba a fada mata ba tasan kanshin
wannan disigner ne (Dolce Gabbana) ya fesa.
Ta daga ido da sauri ta dubi kyakykyawar surar
jikinsa, har zuwa zukekiyar fuskarsa. Yayin da
idanuwanta suka tsaya cak tana kallon wasu
fararen hakoransa yana yi mata dariya. Ta yi
matukar mamaki da ganinsa a wannan waje
kuma a dai dai wannan lokaci. Ba ta amsa masa
ba, sai ta
dukar da kanta kasa.
Abdul-Sabur ya sake matsowa gare ta cikin
harshen Nassara ya ce, ”Kin yi min izinin na
zauna tare da ke?
Ta girgiza kai alamar a’a
Sai ya yi murmushin karfin hali ya ce, ”Ni ne
Abdul-Sabur makwabcinki, yau satina guda da
dawowa.
Wannan kalmar ta makwabci ita ta sake saka
mata tsanar ya kasance a kusa da ita, don haka
tun bai rufe bakinsa ba, ta yi cimak ta mike tsaye
da sauri ko waiwayowa shi ba ta yi ba, ta nufi
get din fita.
Kira ya ke, ”Maye! Maye!!
Ta ki waiwayowa a inda kalmar ‘maye ta sake
hassalata. Ba ta yi wata-wata ba ta tsayar da
tasi ta shige ta tafi gida. Ta nemi nishadin
zuciyarta ta rasa, sai takaici da ya taru ya yi
mata dankar. Ta yi da na sanin zama a gidan nan
saboda takurawar da
Abdul-Sabur yake yi mata. Tabbas dole ta tashi
daga gidannan da zarar kudin hayarta na shekara
ya kare gara ta nemi inda babu bakar fata ko
daya balle ya yi tunanin yi mata magana. Tana
fitowa daga tasi ta ci karo da Dr. Faduwa ita da
kawayenta sun fito daga cikin get daga dukkan
alamu rako su tayi za su shiga tasi su tafi gida.
Don haka ta yi saurin tsayar da ya kawo
Umaimah, ta yi ta kallon Umaimah tana so su
hada ido ta yi mata magana, yayin da Umaima ta
ki kallon inda suke balle su gaisa. Ta zaro kudin
mota ta biya ta saba jakarta, ta kawar da kanta
gefe ta kara gaba.
Dr. Faduwa ta bi ta da kallo kawai tana girgiza
kai da alama tana mamakin hali irin na Umainah.
****************************************
Jiki da jini, dare daya Allah Ya ke sauke ciwo
sauki kuwa sai ahankali. Kwana daya da yini
guda cur ta yi tana ciwon ciki mai tsanani, tun
tana kan gado tana murkususu har ciwo ya
tsananta ta fado kasa.
Juyi kawai ta ke a tsakar daki babu abin da ta ke
ambato sai, ”Wayyo Allah, wayyo Allah cikina,
Allah
Ka taimake ni. Idan ciwon ya dan lafa kadan sai
ta rufe ido ta fara
dan bacci, can sai ciwo ya dawo ya turniketa, ta
sake kwalla kiran sunan Allah, tana neman
agajinSa.
Allahu Akbar, Shi kadai ne mai yaye ciwo a duk
sanda Ya so. Addu’a ta ke, kuka ta ke,
murkususu ta ke yi ita kadai, amma ciwon bai
dauke ba ga shi ta kasa tashi zaune ma balle ta
tashi tsaye tayi tafiya.
Tun cikin dare Abdul-Sabur yake ta kasa kunne
yana sake saurarawa shi dai kamar daga dakin
yarinyar nan yana jin ihu ana kiran Allah-Allah.
Don haka a zaune ya kwana, idan aka jima sai ya
tashi ya bude wundo ya yi ta leken gidanta bai ga
kowa ba, kuma bai daina jiyo karar ba. Ya bude
baramda ya fito ya tsaya yana ta sauraro, tabbas
ihun mace ne, kuma daga saitin dakin yake
fitowa. Tabbas yau ba lafiya akwai matsala!
To amma ya za’a yi ya sani? Ta ina zai iya
taimakonta?
Abin da ya kwana ya yini ke nan yana zulumi. Ya
saukko ya hau benensu kofar gidanta ya tsaya.
Ya
tabbatar ta ciki aka datse. Ihun take yi kuma
sosai yana jiyo ta, sai yai kamar zai buga mata
kofa sai ya
tuno sakon jan kunnen da ta bayar a bashi, don
haka sai ya fasa.
Ya juya zai koma gida sai ya ji ba zai iyaba, ya
sauko gidan Dr. Faduwa da yake kasan na
Umaimah a hawa na goma sha takwas ta ke. Ya
ci sa,a ma kofarta a bude don ita mace ce mai
jama,a ta yi baki, wasu mata ne guda biyu *yan
Indiya suna ta hira.
A yadda ta gan shi ta san ba ta jin dadi, saboda
ba ya walwala, sai ta shiga tambayarsa ko
lafiya?
Ya yi murmushin karfin hali ya gaishe ta da
kawayenta, sai ya roki Dr. Faduwa ta fito waje
suyi magana. Ta biyo shi a gigice, yayin da
zuciyarta ta ke ta kadawa don fargabar abin da
zai fada mata.
Cikin zumudi ta ke tambayarsa, ”Lafiya?”
Ya girgiza kai, magana ya ke cikin marairaciyar
murya.
Ya ce, ”Faduwa, ki yi hakuri, ki taimaka min ki
taimakawa addininki, ki yi don bin sunnar Manzon
Allah (S.A.W) ki yi don hakkin MAKWABTAKA”
Sai ta dafe kiriji ta fara hawaye nan da nan ta
rikice daman rikirkitacciyar ce, ma,ana tana da
saurin gigicewa.
Nan da nan Larabci ya hautsine bakinta ta manta
ma Abdul-Sabur ba ya jin larabci.
Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Abdul-Sabur
ishfi?
Ya girgiza kai ya fada cikin harshen Turanci, ”Ki
yi mini turanci don na fahimce ki. Ki kwantar da
hankalinki, ba wani abu bane illa matsala ce ta
faru ga makociyarmu. Waccan yarinyar ta hawa
goma sha tara. Ina ga kwana ta yi a kwance ba
ta da lafiya, ina jin ta kasa ta shi ta bude kofa.
Ina tsoron ka da ta mutu a cikin gida ita kadai
don ba ta da lafiya sosai.
Dr. Faduwa ta murtike fuska, tare da aika masa
harara, ta tabe baki yayin da ta yi saurin goge
hawayen da ya cika mata ido. Ta murje idanuwan
radau ta dube shi.
Ta ce, ”Tunda nake a rayuwata ban taba ganin
mutum mai laushi da rashin zuciya irinka ba.
Haka tunda nake ban taba ganin mutum mai
taurin da bakar zuciya ba irin na wancan yarinyar,
fitsararriya ce marar kunya, wacce ba ta son
mutane, mai bakar aniya. Ko a cikin satin nan na
hadu da ita a bakin get ta harare ni da *yan
uwana ta wuce. To ni kuwa me zan yi da ita?
Shawara ta karshe da zan ba ka Abdul-Sabur
shine, ka koma gidanka ka shige ka rufe, abin da
babu ruwanka dadin kallo gare shi. Idan ta mutu
tarube ta yi wari masu gadi za su gaji da warin
su
balla gidan su dauke ta su binne. Idan da *yan
uwanta anan a sanar musu, ballantana ma ba ta
da *yan uwa ko kawa, balle saurayi saboda bakin
halinta. Ni dai kaga shiga ta gida, ina da abun yi,
ba zan kare a wannan yarinyar ba.
Ta juya a fusace zata shige.
MAKWABTAKA 6
Ya yi sauri ya tari gabanta yana magiya cikin
wata marainiyar murya mai tafe da tsananin
damuwa, magiya da tausasa lafazai.
Ya ce, ”Faduwa, ki yi taimako don Allah ba don
niba, ba don ita ba, ba don halinta ba. Ki yi don
cika hakkin MAKWABTAKA, kina da ilimi, kin san
yadda Ubangiji Allah (S.W.A) Ya yi magana a
alkur’ani mai girma akan hakkin makwabci akan
makwabcinsa.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, a lokacin da
Mala’ika Jibrilu ya ke isar masa da wahayi akan
hakkin makwabci akan makwabcinsa ya ce, ya
zaci za’a ce makwabci zai iya gadar
makwabcinsa.
Abdul-Sabur ya surnano da hawaye mai yawa. Ya
ce, ”Allah Shi ne Sabur, ma,ana Mahakurci, na
kasance Abdul-Sabur bawan Allah mai yawan
hakuri. Bana rama tsiya da tsiya, sai da alkhairi.
Haka bana fushi sabida darajar sunana.
Faduwa yarinyar nan tana da hakki a kanmu a
matsayinta na musulma, kuma makwabciyarmu.
Mu cika hakkin daya rataya a kanmu ko da ita ta
ki, zai yuwu jahilci ne ke damunta, rashin sani ko
kuma wani dalili nata na daban saboda shirmen
yarinta da yake damunta. Tana cikin halin wuya,
ciwo mai tsanani tun cikin dare ba ta runtsa ba,
ina jiyo rakinta.
Dr. Faduwa ta yi kasake tana dubansa, domin ya
daure ta da jijiyoyin jikinta.
Ya fada cikin sassanyar murya, ta ce, ”Kana so
na taimake ta ko? To ta ya ya zan iya taimakon
yarinyar da ta kulle gidanta, kuma ta ce a ja
mana kunne kada mu sake shiga harkarta?
Abdul-Sabur ya marairaice, ya ce, ”Wajen masu
gadi za mu je, mu sanar musu su debo mukullai
su bude ta ta baya a ga halin da ta ke ciki.
Sannan a matsayinki na likita kije da akwatinki na
taimakon gaggawa (first aid box) ki taimaka mata
kafin a kaita asibiti.
Dr. Faduwa ta ce, ”Kaje ka sanar musu idan an
bude gidan an tabbatar ba ta da lafiyar da gaske,
kuma ta amince na zo sai ka kirani a waya na
taho da akwatina.
Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya yi godiya
ya hanzarta sauka kasa wajen masu gadi, don ya
sanar musu.
Yayin da Dr. Faduwa ta shiga gida ta fara korowa
kawayenta labarin abin da ya ke wakana
tsakaninsu da Umaimah. Sun fusata dajin haka
suna masu roko, magiya da ba wa Dr. Faduwa
shawarar cewa ko Umaimah zata mutu kada ta
taimaka mata. Ya yin da haushin Abdul-Sabur ya
rufe su, suka yi ta Allah wadai da irin wannan
rashin zuciya tasa. Bayan mintuna goma wayar
Faduwa tayi kara, ta na dubawa ta ga sunan
Abdul-Sabur ne, sai ta dubi kawayenta ta yi
murmushi.
Ta ce, ”Ga shi nan inajin zancen zai yi min.
Suka ce ”Kada ki amsa, ki kyale su can su
karata.
Faduwa ta ki amsawa, sai kira yake yana sake
maimaitawa amma ta ki dagawa.
Kwatsam suka gan shi a gabansu, yayin da ya
dubi Faduwa ya dubi wayar da ke kan cinyarta
tana ruri,
ma’ana amsawa ne kawai ba zata yi ba.
Ya girgiza kai cikin rashin jin dadi, ya ce, ”Ashe
Faduwa ba ki aminta da ayar da na kawo miki ba,
game da hakkin makwabci akan makwabcinsa? A
cikin suratul Nisa’i Aya ta 36 Allah Ya yi magana
akan makwabta.
”Kuma ku bautawa Allah, kada ku tara shi da
kowanne abu.Ga mahaifa a kyautata musu kuma
ga ma,abocin zumunci da marayu da matalauta
da makwabci ma,abocin kusanci da makwabci
manisanci da abokin gefe da hanya da
abubuwanda hannuwanku na dama suka mallaka.
Lallaine Allah baya son wanda ya kasance mai
takama mai yawan alfahari. Sadakallahul azim.
Faduwa ta dubi kawayenta, ta ce, ”Kunji yadda
yake daure ni da jijoyoyin jikina ko? Ai dole na je
na duba yarinyar nan.
Kawayenta suka hautsine da hayaniya suna cewa,
kada ta je.
Abdul-Sabur ya dube su a nazarce, ya sake
tabbatarwa ba musulmai ba ne, kana ganinsu
zuryan ka ga Hindu.
Ya juya ya dubi Faduwa cike da takaici, ya ce,
”Har zaki tsaya kina sauraron Ahlul-kitabi,
wadanda ba
musulmai ba, ana miki maganar Allah da Manzon
Sa, maganarsu har tafi maganar mahaliccinki?
Haba
Faduwa kada fa ki bata a sanadiyyar wannan abu
ki rasa imaninki. Abu kalilan sai ya kai bawa
aljanna, haka abu kankani sai yakai mutum wuta.
A sanadiyyar taimakon yarinyar nan da zaki yi, ki
ceto ranta za ki iya samun rahamar Ubangiji…”
Bai rufe bakinsa ba Faduwa ta yi cimak ta mike
tsaye ta shiga daki ta dauko akwatinta, suka fice
yayin da kawayenta suka bisu da harara babu
abinda suke ji sai haushin Abdul-Sabur da ita da
Faduwar da ta biye masa.
Lallai Umaimah ta galabaita, bakinta ya bushe ko
makwarwar ruwa babu a makoshinta. Ta tuje
gashin kanta, haka rigar barcin da ke jikinta duk
ta kanannade saboda burgima. A karkashin gado
ma aka zakulota saboda burgima,, ta wahala har
karfinta ya kare, don haka ko yatsanta bata iya
dagawa balle ta bude ido ta kalli wanda ke kanta.
Daga ta bude ido sai ta rufe luuu kamar
sumammiya. Nan da nan tausayinta ya lullube
zuciyoyin duk
bil’adaman da yake gurin, scurity uku, Faduwa da
Abdul-Sabur.
A gigice Faduwa ta bude akwatinta ta dauko
allurai da magunguna ta fara aiwatar da ayyuka
irin na kwararriyar likita. Abdul-Sabur ya ruga
kicin ya bude firij ya dauko ruwan sanyi ya kawo
ya mikawa Dr. Faduwa. Ta ce, ”A,a kada a ba ta
ruwan sanyi sai dai abu mai dumi kanar shayi ko
Coka oat.
Don haka Abdul-Sabur ya sake garzayawa kicin
ya jona ruwan zafi a butar lantarki (kettle), ya
bude
lokokin kicin din sai ga komai a jere reras wajen
kayan abinci daban, kayan shayi daban
kwanuka,kofuna,cokula. Kicin dinta a tsare ya ke
ga tsafta ko ina.
Ya dauko kofi da cokali ya sake daurayewa
sannan ya zuba sukari kadan, milo da madara,
sannan ya
zuga tafasasshen ruwan zafi akai, ya jujjuya ya
dauko ya kawo.
Dr. Faduwa ta karbi kofin ta dago kan Umaimah
akan cinyarta ta dinga tarfa mata da cokali, sai
sha
take sabida tsananin yunwa da kishirwar da ta ke
addabarta.
Dr. Faduwa ta dubi security ta ce, ”tana bukatar
karin ruwa da gwaje-gwaje a gano kan ciwon,
dole a kaita asibiti.
Sai suka gaggauta kiran wayar asibiti suka
bukaci da su turo da motarsu (ambulance) za,a
dauki mara lafiya.
Abdul-Sabur ya bude durowar kayanta yana
dubawa, ba tare da ya san wanda zai daukar
mata ba. Kaya ne a goge a linke sanka-sanka,
sai kamshi suke yi, daga baya ya riguna da
bangarensu, siket, abayoyi, mayafai da dai
sauransu.
Ya jawo wata doguwar riga ja (abaya) da dan
kwalin ya hada ya mikawa Faduwa, ya ce ta saka
mata. Ya roki masu gadi da su fita falo su bari
mace ta shityata.
A falo ne ya isa kan teburin cin abinci a in da ta
dora laptop dinta da takardunta, ya shiga
babbankadawa, a nan ne ya ke ganin sunanta
ajikin takardun, ta rubuta UMAIMA BELLO, a she
ba sunanta MAYE ba? To me kalmar MAYE take
nufi?
Ya karanta a baiyane, ya sake maimaitawa, sai
yau yasan sunanta. Ya ci gaba da bankada
durorwoyinta da suke falon, takardu ne kala-kala
duk na makaranta. A jikin durowar Talabijin stand
ya ga wata *yar karamar jaka ya bude ya ga
himilin
hotunanta ne. Ya fara budewa cikin sauri yana
dubawa, ya ganta ita da danginta mata da maza,
yara da manya, da kuma tsofaffi. Wato iyayenta
da kakanninta.
Ya cika da mamaki da ya ga wasu hotunan, gashi
babu wanda zai iya tambaya a yi masa bayani.
Bai gama kallo ba ya ji jiniyar mota (zmbulance),
kan kace kwabo sun hayo da gadonsu, suka shiga
dakinta cikin gaggawa, suka dorata akan gadon
mai taya suka turota a shassheme kamar gawa
sai numfashi ta ke yi sama-sama.
Abdul-Sabur ya shiga dakinta da sauri ya bude
jakarta ya fara bincikawa yana neman I,D card
dinta bai gani ba, sai dai yaga passport dinta. Ya
yi sauri ya bude ya duba, ya ga hotonta da
sunanta
radau, sai yau yasan kasarta ashe yar Nigeria ce?
Ya zakulo *yar karamar jaka (wallet). A cikin
jakar ya bude anan ne ya ga I.D card dinta na
makaranta wato FTMS, da wasu kuma na wasu
makarantunta
na can Nigeria. Ya hada ya mikawa malaman
asibitin.
Shi da masu gadin gidan ne suka kukkulle mata
ko ina a gidan, sannan suka watse. Dr. Faduwa
ta koma gidanta, security suna rike da makullin
gidan suka koma dan dakinsu a bakin get, yayin
da Abdul-Sabur ya koma gidansa.
Umaima kuwa na can akan gadon asibitin ana
ceto rayuwarta don ta galabaita, bata ciki
hayyacinta.
Daga asibitin aka yi wa makarantarta waya suka
tura malamai mata guda biyu, su ne za su dinga
zama da ita.
Ya kasa zaune, ya kasa tsaye, balle ya kwanta,
babu ma maganar cin abinci a wajen Abdul-
Sabur, ya shiga damuwa sosai, saboda tausayin
rai.
Babban abun tausayin ma shine rashin hakikan
*yan uwanta a kusa ga babu waya balle a buga a
sanar musu. Ko saboda hakin mutuwa.
Addu,a yake, Allah Ya sa ta rayu kada ta mutu,
ba ya son ta mutu duk da ta tsane shi, ba ta ki
ta ga ba
ya doron kasa ba. A daddafe ya bari gari ya
waye,
da sassafe ya shirya ya fito wajen masu gadi, da
suka gaisa sai ya tambaye su adireshin asibitin
da aka kai Umainah.
A rubuce suka bashi kamar haka:- Sime Darby
Medical Center Subang Jaya Jalan SS12/1A
47500 Selangor Darul Ehsan, Malaysia.
Babu wata matsala yasan ma asibitin, ba shi da
nisa da makarantarsu. Sai ya yi musu godiya ya
nufi asibitin. Yana hanya yana fargaba guda biyu.
Na farko yana fargabar yadda zaiga jikinta, sauki
ko tsanani. Sannan na biyu yana fargabar yadda
za ta yi idan ta ganshi, farin ciki ko takaici?
MAKWABTAKA 7
Ko ba a fada masa ba, yasan ta tsane shi, ba
mamaki idan ta ganshi ta disga shi. Shi dai koma
mai zai faru ya ji ya gani sai ya je ya saka a
ransa duk abin da yake yi yana yi ne saboda
Allah, kuma a wajenSa yake neman sakayya.
Ya isa asibiti a reception, ya yi musu bayanin
suna da yanayin ciwonta, na da nan suka fada
masa
hawa na uku ta ke, da lambar dakin da ta ke. Ya
yi godiya ya nufi dakin, yayin da fargabar da yake
ciki
ta sake tsananta. Yana ta addu’a dai har ya isa
kofar dakin, ya kwankwasa a nutse gami da yin
sallama,
sai yaji muryar wasu mata sun amsa masa
sannan ya tura kofar ya shiga.
Aka hau kallon-kallo tsakaninsa da matan biyu,
daya *yar Malaysia ce, daya kuwa India ce. Yayin
da Umaimah ta ke sheme akan gado ana mata
karin ruwa, idanuwanta a rufe alama dai baccci ta
ke yi.
Ya karaso jikin gadon ya gaishe su, sannan ya
gabatar da kansa cewar shi makocinta ne,
sannan suka saki ransu don da sun yi masa
kallon rashin fahimta. Ya tambayesu yaya me
jikim? Suka yi ta koro masa bayanin abubuwan
da suka faru da ita a jiya, cewar ciwon cikin ya
tsananta, amma yau da safe ta sami sauki sosai,
har ta sami bacci.
A cikin bayanansu ya gane cewar ma,aikatan
makarantarta ne, sai ya ji hankalinsa ya kwanta
tun
da ga masu kula da ita Allah Ya kawo. Ya je
kanta ya tsaya ya yi ta tofa mata addu,o,i na
neman sauki, afuwa, rangwame daga Rabbul-
Samawati.
Ya ce da su, ”Idan ta tashi a ce Abdul-Sabur
yana yi mata sannu.
Ya yi musu sallama ya tafi sai yanzu yaji
hankalinsa ya kwanta, da ya ga jikin da sauki. Da
yammacin ranar Dr. Faduwa zata tafi unguwa ta
biyo ta gidansa ta iske shi a zaune a falo ya yi
tagumi. Kallo daya ta yi masa ta san bayajin
dadin rayuwarsa. Ta sami kujera ta zauna ta
gaishe shi, sannan ta tambaye shi. Shin yana da
labarin halin da marar lafiyar nan ta ke?
Ya amsa mata da, ”eh ta sami sauki sosai, na je
na duba ta ma dazu.
Sai ta yi kasake tana kallonsa, da alama tana so
ta ji yadda suka karke.
Ta tambaya da sauri ”Ta ganka? Kun gaisa?
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ”gaskiya bata
ma san na je ba, saboda tana bacci. Dr. Faduwa
ta yi ajiyar zuciya ta ce, ”Barkanka, na
taya ka murna da ba ka sameta idon ta biyu ba.
Ya yi mamaki dajin kalamanta, sai ya tambaya,
”Me yasa kika ce haka?”
Ta tabe baki ta ce, ”Da ba zata amsa maka ba,
saboda yadda nasan tsanar da ta yi mana. Ya
kyalkyale da dariya, ya ce, ”Kai Faduwa, ai abun
bai kai haka ba. Ni dai uzirin da nake bata shine,
na san tana da wani dalilinta na daban, aka
bibiya laifin wasu ne ya shafemu. Ina yi mata
addu’a Allah Ya sa ta gane.
Faduwa ta ce, ”Ai ba don kai ba yarinyar nan ko
zata mutu ba zanje kanta ba. Kai ne dai da naci
ka
kasa rabuwa da ita, na rasa dalili. Koda yake na
fahimce ka, kana son yarinyar nan sosai, kuma
har cikin zuciyarka.
Abdul-Sabur ya gyra zama ya zazzare ido don
mamaki, sai ya girgiza kai. Ya ce, ”Babu ko daya,
da za ki yarda da ni yi miki rantsuwa, wallahi
babu maganar so a tsakanina da wannan
yarinyar. Haba Faduwa kamar ba ki san
halina ba, shekararmu biyu da ke agidan nan, ya
kamata ki fahimce ni ki kuma fahimci irin macen
da
take burge ni. Na daya, kin sanni da son macen
da ta mallaki hankalinta, ta san rayuwar duniya
sosai, ba *yan matan nan da suke rawar kai ba,
wai su *yan boko. Umaimah yarinya ce karama
ba sa,ar soyayyata ba ce.
Na biyu halayenta kwata-kwata ba su yi min ba
don ba ta da tarbiyya, fitsararriya ce, ba ta burge
ni ba don ina son mace mai kunya da sanin
darajar na gaba da ita.
Na uku, musulma ce amma ba ta da ilimin
aiwatar da addinin don ba ta bin abin da Allah ya
ce, ba ta
kyautatawa makwabtanta ba, bata bayar da
hakkin MAKWABTAKA. Inajin tausayinta ne kawai
kasancewarta mace,
kuma yarinya karama a kasar da babu iyayenta,
ba dangi ba kawayenta. Ina so na nusantar da ita
tasan hakkin makwabci akan makwabcinsa, ko
don gaba ma tasan yadda zata zauna da
makwabtanta ko bayan ta yi aure. Na dauketa
kamar karamar kanwata mai neman shawarata.
Yanzu da na biye mata shirmen nan da ta ke na
babu ruwanta da mu, da ta yaya za,a yi a san
tana
cikin gidan nan a kwance babu lafiya? Ai ko
mutuwa ta yi ba za,a sani ba, sai dai idan ta
mutun
ta kwana uku ta rube wari ya ishi jama,ar gidan a
balla kofa a ganta. Ina amfanin irin wannan
alhalin
mu dukka musulmai ne?
Faduwa, ina tausayin mace, musamman wacce ba
ta gaban iyayenta, ko hannun mijinta. Duk inda
na ga matashiyar mace sai na ji ina sonta,
saboda ina da kanwa wacce na fi sonta a duniya
fiye da kowa da kuma komai da na mallaka.
Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce. ”Nasan da
haka Abdul amma fa yarinyar can ba *yar mutunci
ba ce.
Duk inda ka kai ga nuna mata hanyar Allah ba
zata saurare ka ba.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ”Wanda yake
abu saboda Allah baya cewa ya gaji kuma baya
fushi ya ce ya daina. Ina yi mata addu’ar Allah
Ya ganar da ita, yanzu a matsayinki na likita idan
kika duba
yarinyar nan (psychologycally) za ki ga tana da
matsala a rayuwarta. Zai yiwu an guma mata
wani
abu ne na takaici ta yi hijira ta dawo nan, amma
ya za,ayi ace mace ita kadai ko kawa ba ta yi,
balle saurayi ko miji, kuma ko wayar hannu ba ta
da ita (handset). Wannan fa abin dubawa ne
Faduwa.
Dr. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ”Na lura tana
cikin damuwa, amma duk damuwarta ai ba ta fi ni
ba,
amma na ke daurewa na ke shiga jama,a na ke
gaisawa da kowa lafiya.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ”Ka ji ta, wai
ba ta kai ki ba ni me yiwuwa duk na fi ku
damuwa,
amma nake daurewa. Kowanne mutum da kika
gani a duniyar nan yana da tasa matsalar, kuma
tasa kadai ya sani, sai ya yi ta ganin kamar ya fi
kowa matsala.
Dr. Faduwa ta ce, ”Haka ne, Allah Ya yaye mana.
Zo ka raka ni ‘KL Sentral zan je na ga wata
kawata ta haihu.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ”yi hakuri
wallahi bazan iya zuwa ba. Bana jin dadi saboda
bana iya cin abinci, ba na bacci kwana biyu ke
nan.
Dr. Faduwa ta mike tsaye ta yi dariya, ta ce,
”Lallai kai kafi kowa ma tausayi, akan ciwon
yarinyar ne
ka kasa bacci da cin abinci? Ai kuwa gara ma ka
cire ciwon nan a ranka, kaci gaba da harkokinka
idan dai wannan ce ina nan da kai tana warkewa
zata ce ba ta san mu ba.
Abdul ya yi dariya ya ce, ”Ke ma na ga alama kin
kasa fahimta ta, amma ina fatan ki fahimce ni
nan
gana.
Faduwa ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba,
ta bar Abdul-Sabur a nan a zaune yana tunani.
Bayan kwanaki hudu, sannan aka sallamo
Umaimah daga asibiti, sai da matan nan biyu
suka raka ta har cikin falonta. Bayan sun roke ta
ta dawo gidansu ta zauna har jikinta ya yi kwari
saboda ba dadi zaman ita kadai ta ki amincewa,
ta ce su barta zata iya zama ita kadai. Suka ba
ta magunguna suka fita suka tafi a motar da
suka zo. Fitarsu da kamar mintina goma,
Umaimah na zaune har yanzu akan kujera tana
tunanin tashi ta rufe kofa sannan ta shiga ta yi
wanka, sai taji ana danna kararrawa a bakin
kofar gidanta. Ta yi mamaki marar misaltuwa, ta
taso da sauri ta daga labule don kofar a bude ta
ke.
Abdul-Sabur ta gani cikin kyakykyawar shigarsa
ta wando baki (jeans) da riga fara (Shirt).
Kamshin nan nasa na turaren (Dolce Gabbana)
shi ne ya daki
hancinta, kamshin nan ba karamin tuno mata
baya ya yi ba. Ta yi mamak da jin yau ya ambaci
sunanta
‘Umaimah’ maimakon ‘Maye’ da yake kiranta a
baya.
Sai ta ji saukin tsanar da tayi masa a baya. Ba ta
amsa masa ba, ta ci gaba da sauraron abin da
zai ce
don ta matsu ya fada ya wuce, ba ta kaunar ya
dade a bakin kofarta.
Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ”Ya ya jikinki? Ina
fatan kin sami sauki sosai? Allah Ya baki lafiya.
Ta saki labulen ta labe ba tare da ta amsa masa
ba.
Ya ci gaba da jiran amsar da zata ba shi, ya ji ta
yi shuru. Sai ya gyara tsayuwa. Ya ce, ”Umaima,
ba na binki da wata manufa illa alkhairi. Manzon
Allah (S.A.W) ya ce, kada ka
kwana ka koshi makocinka ya kwanta da yunwa.
Haka ka dubashi idan bashi da lafiya. Idan har
makwabci bai amince da makwabcinsa ba yana
gudun zai cuce shi ta hanyar fada masa bakar
magana, zagi ko duka, ko kuma neman halaka
shi, to wannan makwabci ba shi da rabo a lahira.
A kwai kissar wata mata da ta rasu bayan kuma
an shaide ta da yawan sallah, azumi, kyauta
sadaka.
Amma aka ganta a wuta. Da Annabi (S.A.W) Ya
binciki abubuwan da ta aikata a rayuwarta ta
duniya sai aka shaide ta ta cika komai banda abu
daya, shine ba ta kyautatawa makwabtanta. Tana
musguna musu, ba ta zauna lafiya da su ba,
wannan dalili shi kadai ne ya kaita wuta
(Wa’iyazubillah).
Don haka ya ke kanwata Umaimah ki yi hakuri ki
zauna da MAKWABTANKI lafiya, ki ba ni ba ko
don nan gaba. Na barki lafiya, duba ki na zo yi
ina fatan Allah Ya baki lafiya, bissalam.
Ya juya ya tafi gidansa.
Sai ya wuce ya bar ta a nane da jikin labule ta
kasa motsawa, daga dukkan alamu wa’azin fa ya
shige ta, dan ta tsorata, tabbas ta san gaskiya ya
fada mata tsagwaronta. Amma ba ta jin zata iya
aiwatar
da nasihohinsa, saboda dalilinta da yawa akan
cuta da musgunawar da MAKWABTANTA suka
dade suna yi mata a doron kasa.
Ta girgiza kai ta fada a bayyane, ”Zam iya
amincewa da kowa a duniya, amma ban da
makwabtana, saboda sun zalunce ni.”
UHM to ai da sauki tunda ni ba makwabci bane,
da fatan zaki aminta dani Umaimah…
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 8
Ta jawo kofarta a fusace ta datse, yayin da ta
hau faman huci, ranta ya duguzuma ya baci. Ta
tabbatar
muddin ba ta bi nasihar Abdul-Sabur ba tana
cikin halaka. Duk abin da ya fada gaskiya ya fada
mata, amma kuma ya tuno mata da kasurgumin
bacin ran da ya faru da ita a baya tsakaninta da
MAKWABTA.
Ta dade a zaune a falo tana tunanin yadda aka yi
MAKWABTANTA suka san ba ta da lafiya, sai ta
shiga mamakin yadda ma aka shigo gidan akasan
bata da lafiya alhali kofarta a kulle. Ta tashi a
hankali ta shiga dakin, ta tsaya tana kallon inda
ta kwanta, ta shiga dauki ba dadi da
kwakwalwarta tana kokarin tuno abubuwan da
suka faru da ita kafin ta fara ciwon ciki.
Abin da zata iya tunawa shi ne, ta saka rigar
bacci ta kwanta akan gado, yayin da ta fara jin
ciwon ciki mai tsanani ya turnike ta. Tun tana
juyi harta fado kasa abin da zata iya tunawa
kenan.
Ta tsuguna kasa a hankali ta dauko rigarta a
tsakar daki ta dudduba, sai ta shiga dogon
tunanin yadda
aka yi aka sauya mata rigar jikinta. To yaya ma
aka yi aka san bata da lafiya? Shine abin da yake
damunta. Tabbas ishara ce Allah Ya nuna mata,
saboda mutum dadi ne da shi. Duk in da ka kai
da kin mutane ka kwanta kai ka dai a cikin gida
ka
mutu dole mutane za su bude su dauke gawar,
su bunneka, don haka dole mutum ya yi
mu’amala da mutane. Ta dade a zaune tana
tunani, har da koke-koke, dom ita ma ba haka ta
so ta kasance tare da jama,aba, dole ce ta saka
ta ko ta fito da niyyar gaisawa da jama,a tana
ganinsu sai ranta ya baci ta fasa.
Ta jima a zaune a gefen gado tana kuka, sannan
ta tashi ta shiga wanka. Bayan ta yi wanka ta yi
sallah,
sannan ta lallaba ta shiga kicin don dafa abin da
zata ci, saboda yunwar da ta ke addabarta.
Ciwo ne yake samun mutum a lokaci guda, sauki
kuwa sai a hankali. Babu ciwon cikin dai a yanzu
amma ba ta jin karfin jikinta da dadin bakinta.
Tana kuma shan magungunanta, don haka gaba
daya satin Umaimah ta kasance a gida ba ta fita
makaranta ba. Sai da ta tabbatar ta warware
sosai,
sannan ta shirya ta fito zuwa makaranta, ranar
litinin da safe da misalin karfe tara kenan.
A cikin lift Umaima ta hadu da Dr.Faduwa, mai
hali ba ya fasa halinsa, ba ta yarda ta hada ido
da Dr.Faduwa ba, balle ta yi mata sallama.
Kasancewar su takwas ne a cikin lift din, sai ta
sami lungu ta labe daga bayan Faduwa har suka
iso kasa inda kowa ya firfito.
Jefa kafarsu ke da wuya akan baranda suka yi
kicibus da Abdul-Sabur daga dukkan alamu
Faduwa yake jira. Daga yadda ya ga Umaimah ta
zabura ya san ta yi mamakin ganinsa dai-dai
wannan lokacin, kuma a wannan waje.
”Zo ki wuce”. Inji Abdul-Sabur ya ce da
Umaimah gami da matsawa ya bata hanya. Ta
sunkuyar da kanta kasa ta wuce abinta ba tare
da ta gaishe shi ba kamar yadda ya ke sa ran
samun gaisuwarta ko don wa,azin da yayi mata.
Faduwa ta dube shi ta juya ta dubi Umaimah, ta
girgiza kai ta ce da shi.
”Ka ga abin da nake fada maka ko? Ai mai hali
ba ya fasa halinsa.
Tafiya suke zuwa get din fita, yayin da Umaimah
ke gabansu, sauri kawai ta ke yi, don kada ma ta
jera
da su. Amma duk da haka takan jiwo wasu
abubuwan da suke fada a kanta.
Faduwa fada ta ke yi da karfi kan rashin tarbiyyar
Umaimah, yayin da Abdul-Sabur yake nemar
mata uziri cewar, akwai dalilinta na yin haka kada
tayi saurin yanke mata hukunci.
Umaimah ta tabe baki ta ce a ranta, ”Koma dai
me zaku ce matsalarku ce, ku ta shafa dan ba
kwa gabana, da zaku rabu da ni, da na fi jin dadi.
Ta kara daga kafa tana sauri, ta haye saman
bene a
inda zata haye gada zuwa makarantarta. Daga
nan ba ta waiwayo su ba, bata san inda suka
bulle ba kuma. Tana kyautata zaton tasi suka
tsayar suka shiga.
****************************************
Zangon karatu na karshen 2nd semester ya zo
karshe, har an fara jarabawa a wasu makarantun,
yayin da makarantar su Umaimah har sun yi nisa
da farawa.
Ta yi karatu cikin dare, ta yi da safe, ta yi da
maraice, yayin da ta ji kwakwalwarta ta yi kamar
zata buga don takura. Harta daina fahimtar abin
da ta ke karantawa don haka sai ta harhada ta
rufe. Ta
fito baranda ta tsaya tana kallon titi, motoci da
mutanen da suke giftawa. Iska mai sanyi ta
yamma
ce ta ke fifitawa, ta sake gyra tsayuwarta tana
kallonsu, sai ta ji ta fara washewa daga damuwa
da gajiyar karatu.
Sallama ta ji an yi mata babu bata lokaci ta kalli
inda muryar ta fito, ko ba a fada mata ba ta san
Abdul-
Sabur ne dan daga saitin gidansa muryar ta fito.
Ta dube shi ta ga yana tsaye a barandarsa yana
yi
mata murmushi. Ya yi matukar mamaki da ya ji
ta amsa da ”Wa’alaikassalam.
”Ya ya karatu? Ya yi karfin halin tambayarta.
Wannan karon dai bashi da amsa, don haka ya ja
fatar bakin ya kame, bai sake yi mata magana ba.
A
zatonsa zata koma cikin gida kamar yadda ta
saba idan ta ganshi, sai ya ga ba ta tafi ba,
amma ba ta sake daga ta dube shi ba. Ya dade a
tsaye yana kallonta, sai ya koma ciki ya rabu da
ita. Sai da ta ji ana kiran sallar magaruba ta
koma cikin gida daga nan bai sake ganinta ba, sai
da yammar washegari tana dawowa daga
makaranta da alama dai jarabawa ta je ta zana
ta dawo.
****************************************
A lokacin da gaba daya makarantun jami’o’in
suka gama jarabawa suka yi hutu, dalibai suka
fara yayewa, yayin da Umaimah ta ji a ranta,
daman zata iya tafiya kasarta hutu itama don ta
gaji da zaman kadaici, sai dai kash! Ba zata iya
tafiya ba don ba ta so a san tana raye.
Jifa-jifa ta ke hango Faduwa da Abdul-Sabur da
alama su ma wannan hutun ba zasu tafi gida ba.
Suna nan, don haka sai ta dan ji sanyi a ranata,
ta ji ashe ba ita kadai ba ce wacce zata zauna.
Duk da ba ta tunanin za su dauke mata kewar
komai.
Idan taji kamar zuciyarta zata fashe don tunani,
sai ta shirya ta fita wuraren shan iska, inda zata
ga
jama’a daban-daban da abubuwa masu ban
sha,awa.
Malaysia kasa ce wacce babu abinda suka saka a
gaba irin shakatawa musamman daga yamma
zuwa dare. Idan ka shiga cikin KL inda tulin malls
suke babu abin da zaka dinga jiyowa sai sautin
kida. A gefen tituna kuwa jama,a ne da’ira-da’ira
sun zage abubuwan kallo kamar masu wasa da
maciji, masu kada giraya (giter), masu rufa ido.
Kida kuwa duk kusurwar da ka zo giftawa da irin
sautinsa, kasancewar baki musamman Turawa
suna shigowa sosai don shakatawa.
A yau Umaimah yawon nata ne ya motsa don ba
ta san takamaimai inda zata nufa ba, zaman
gidan ne
ya ishe ta niyyarta tunda yamma idan ta fita sai
dayan dare zata shigo gida. Don kwanaki biyu ta
yi
tana bacci ta gaji da kwanciya. Da ta je sayan
tikitin jirgin kasa sai ta tamabayesu, ina ne tasha
ta karshe
idan aka tafi daga nan? Matar mai sayr da tikiti
ta zayyano mata cewar.
”Yanzu jirgi zai zo daga KL Centaral, ya shigo ta
‘Tunsamban Than’ ya zo nan ‘Maharjalela’, sai
ku tafi ‘Hangtuah’, sai ‘Imbi’ sannan ‘Bukit bin
tang,
Umaimah ta ce, ”Idan ya wuce Bukit bin tang, sai
ya tafi ina?
Matar ta ce, ”Zai tafi ‘Raja Chuland’, ‘Bukit
nenas’ ‘Dang Wangi’, ‘Medantuanku’, ‘Chow kit’
sai ya tsaya a ‘Titi Wangsa’ sannan ya juyo…”
Umaimah ta yi murmushi, saboda ta ji yawon da
akalla zata kai sha biyun dare a hanya. Sai ta
tambaya nawa ne kudinta daga Maharjalela zuwa
Titi wangsa?
Matar ta ce, ”Riggit goma sha uku”. Ta zaro ta
biya ta wuce, zuciyarta cike da annuri.
Ana ta turmutsitsin shiga jirgi mutumin da ke
gabanta ya yi sa’ar samun kujera ya zauna. Ita
kuwa a tsaye ta ke ta rike karfe. Bayan ya zauna
ya juto ya dubi mutanen da suke tsaye a kansa.
Abdul-Sabur ne sai yayi ido hudu da Umaimah
itama sai yanzu taga fuskarsa, sai ya yi zuruf ya
mike tsaye kai ka ce bawa ne ya ga ubangidansa.
Yayin da ita kuma take kokarin kawar da kai gefe
har da matsawa da da hanya ma cikin mutane
zata
kutsa ta bace masa.
Cikin harshen Turanci yake magana, don haka duk
jama’a na jin abin da yake fada kuma sun zuba
musu ido.
Ya ce, ”Zo ki zauna, ki zauna ga kujera.
Umaimah zo ki zauna.
Har sau uku, don babu yadda zata yi ido ya yi
mata yawa ta lallabo ta zauna cikin sanda kanta
a sunkuye a kasa. Ranta a bace don bata so
hadu da wanda ta sani a yammacin nan, saboda
ta fito da niyyar yawatawa ta ga gari, gari ya
ganta. Ba ta son wani mahaluki ya dame ta
kuma.
Jirgi dai sai tafiya yake yana tsayawa a tasoshisa
daban-daban, ya sauke wasu ya kwashi wasu.
Sai ta ga Abdul-Sabur ba shi da niyyar sauka ta
dago ta dube shi, shima ya dube ta sai ya yi
mata murmushi,
Ya ce, ”Ai ba’a zo Bukit bin tang ba na san a nan
za ki sauka, ni ma haka can zan je.
Ta tabe baki ta sunkuyar da kai kasa cikin rashin
kulawa da zancensa. Ba jimawa aka sanar, ‘Bukit
bin tang’, ya juyo ya kalle ta, sai ta rataya
jakarta ta yunkura ta tashi, ta bi bayansa su da
dandazon jama,a. Yayin da ta tabbatar ya wuce
gaba, sai ta
noke ta ki fita ta kutsa lungu cikin mutane ta
sami kujera ta yi zamanta a wani bangaren. Ba ta
dago da kanta ba sai da ta tabbatar an rufe jirgi
yadda bazai iya dawowa ba. Ai kuwa ta hango
shi yana ta waiwaye-waiwaye yana nemanta, har
ya so ya ba
ta tausayi, amma kuma taji sakayau kamar an
cire mata kaya da ya sauka.
MAKWABTAKA 9
Duk ta karaci yawonta da bata lokacinta a karfe
goma ta hawo jirgi ta juyo gida. Da suka zo
tashar
‘Bukit bin tang’ sai suka sauke fasinjoji suka dibi
wasu. Kwatsam sai ta ga Abdul-Sabur ya nufo ta
kai tsaye,
idanuwansa a kanta suke.
A ranta ta ce, ”Ga mayen nan, kamar aljani, duk
inda na sa kafata sai na ganshi ko da kuwa kasar
na
bari. Anya kuwa wannan mutum ne?
Ta hada girar sama da kasaa, don tasan ta yi
masa laifi kada ma ya ga fuskar tambayarta wani
abu.
Sai ta cika da mamaki a lokacin da ta ga
fara,arsa yadda ka san ba ta taba saba masa ba.
Ya yi mata
sallama gami da yi mata sannu da dawowa.
Ta gyada kai kawai ba ta amsa masa ba, suka ci
gaba da tafiya babu abin da yake yi illa kakkare
ta da yake, don kada a matseta a lungu saboda
karatan da suka cunkushe cikin jirgin. Jirgi ya
cika
makil saboda kowa ya na so ya koma gida, don
dare ya yi. Har yanzu su duk a tsaitsaye suke sun
rike igiya babu kujerar zama. Motsi kadan ta yi
sai ya juyo ya kalle ta cikin tattausar murya yake
yi mata sannu. Sai ta ji kamar ta kurma ihu don
takaicin ya shiga harkarta. A haka dai har suka
karasa ‘Maharjalela’. Babu yadda ta iya, dole ta
fito dan niyyarta ta ki fita a wuce da ita wata
unguwar,
sannan ta dawo idan ya tafi. Kamar yasan haka
ta ke nufi, sai da ya tabbatar ya saka ta a gaba
suka fito tare.
Tafiya kawai take kanta a sunkuye a kasa,
tambaya kala-kala da labaru ya ke rero mata,
wadanda basu shafe ta ba, ba su shafi tsarin
rayuwarta ba. ‘Yes ko ‘No kawai ta ke jero masa.
Har suka sauko daga
tashar jirgin suka nufo gida. Tambayrta yake, ya
ya kwarin jikinta, cikin ya daina ciwo ko?
Ta dago kai ta dube shi a fusace ta galla masa
harara ta girgiza kai don takaici gami da dorawa
da dan siririn tsaki.
Cikin harshen turanci suke magana ta ce, ”Kai….
Kai Abdul-Sabaur, bazan boye maka ba, a
gaskiya kana takurawa rayuwata da yawa. Ka
sani na baro garinmu, kasarmu na zo kasar da ba
a taba sanina
ba, ni ma bansan kowa ba, saboda gudun takura.
Me yasa zaka nemi saika sanni dole? Bana son
damuwa, don Allah ka yi hakuri ka daina shigar
min harka, na fi jin dadin rayuwata ni kadai.
Murmushi ya yi mata, ya ce, ”Allah Sarki yarinta.
Umaimah ki yi hakuri, ki kara hakuri, ko ba ki
fada min da baki ba, na san kin takura a
yanayinki da
nake gani, na san na dame ki. Amma ita rayuwar
duniya da kike gani kowa hakuri yake da ita,
kuma
kowa yana da matsala, wata matsalar ma har ta
fi ta ki. A matsayinki na musulma ai ba wannan
hukuncin za ki yanke ba na tahowa inda ba
asanki ba, kuma ki ki yarda ki saba da kowa idan
kika yi haka kamar kinyi fushi ne da kaddarar da
Allah Ya dora miki. Musulmi na gari yana fara,a
yana
mai godiya ga Allah a lokacin da yake cikin
tsanani. Ba ki taba jin kissar nan ta wani mutum
ba? Wanda bakin cikin duniya ya dame shi, ya je
Ka’aba yana dawafi, yana cikin damuwa, yana ta
addu’a. Sai ya hadu da wata mata, wacce suke
zagaye tare. Fara’a matar ta ke ti fuskarta cike
da annuri, gata
kyakyktawar gaske. Sai ta burge shi ta bashi
sha’awa ya ji dama shine ya sami irin farin cikin
da take ciki. Tun yana fada aransa, har ya fito ya
tambayeta.
Ya ce, ‘Yah ke wannan mata, ke kuwa wanne irin
farin ciki kike yi haka ne? Daga ganinki ba ki da
matsala a duniya. Sai matar ta sake yin
murmushi, ta ce, ‘bawan Allah ni ce kuwa nake
da damuwa, saboda mai gidana ne ya tafi kiwo
tunda safe bai dawoba har dare ya
yi, ashe mutuwa ya yi a can, sai na aika babban
dana ya je ya nemo shi daya tafi shima maciji ya
sare shi ya mutu, ma kaji shiru na fita neman su
na bar karamin jariri kafin in dawo gida na zo na
tarar
kura ta cinye shi. Na dawo bani da kowa yanzu a
duniya Allah Ya karbe abunSa. Godiyar Allah ce
kawai da wadatar zuci yasa kaga ina dariya.
Tun daga wannan lokaci mutumin ya daina
damuwa da matsalarsa ya ji ashe shi tashi
matsalar shafar mai ce. To haka akeso musulmi
na gari ya kasance.
Umaimah ta dubeshi yayin da jikinta ya yi sanyi,
ba ta kara magana ba har suka shiga bakin get.
Ta kama hanyar gidanta shima ya nufi
bangarensa.
Kalmar karshe da ya furta a gare ta, ita ce,
”Bissalam. Ta amsa da ”Ma’assalam.
Ta wuce gida yana mai tsananin mamaki da irin
kwakwalwa da dadadan kalamai masu tausasawa
irin na Abdul-Sabur. Mutum ko shaidan ne sai
jikinsa ya yi sanyi idan ya fara yi maka nasiha.
Tabbas Abdul-Sabur mutum ne mai rikon addini
da iya xama da jama. Amma ita duk da haka bata
tunanin taci gaba da zama a gidan nan, don ta ga
sannu a hankali Abdul-Sabur zai sa ta saba da
MAKWABTA, ita kuwa ba ta son su saba sam.
Sai yau Abdul-Sabur ya fara jin sanyi a ransa a
game da Umaimah, yau ce rana ta farko da ta
fara bude bakinta ta yi masa doguwar magana,
har da ya yi tunanin ko batajin turanci ne sosai
shi yasa ba
ta son magana. Sai ya ji ta iya Turanci sosai, sai
ka ce a kasar Turawa ta yi karatun tubalinta
(Primary da secondary). Daga dukkan alamu zaici
galaba a kanta, ya fara rusa mata bakar akidar
nan da ta saka a ranta, ta kin gaisawa da
makwabtanta.
Asuba ta gari Abdumaimah !!!