Malama Juwairiyya gyaran nono
Tag: Malama Juwairiyya gyaran nono
GYARAN NONO
idan muka ce gyaran nono akasari ba kowace mace zata
gane me muke nufi ba saboda basu dama da gyarawaba,
alhali kuma rashin gyaran ba karamar illa yake yi masuba
amma su basu sanhakanba, to gaskiya yana da matukar
muhimmanci da tasiri ga mace AMARYA ko UWARGIDA,
BUDURWA KO ZAWARA, da ku gyara nononku, karki bar
nononki hakanan sharaf ba kyan gani, sai kaga mace ta bar
nono a zube, in tana shara mai gida yaga sona ta reto kamar
anratayo agwagi a bayan keke, idan kuka lura sai kuga matan
wadansu yarurrukan wadanda ba hausawa ba (kamar
LARABAWA KO TURAWA) matansu sun tsufa ko sun
manyanta amma martabar nonuwansu nanan daram ta yadda
ko nonuwan wata budurwar a nan baza ka samesu a hakaba,
to hakan zai iya rage maki tasiri wajen maigida, hanyoyin da
zaki bi don kada nononki ya fadi ko kuma idan ya fadi kuma
kina son ya tashi sune zaki samu:
☞ alkama ki rinka yin kunu da ita kina sha safe da rana
☞ ko kisamu garin hulba
☞ da garin tsamiya
☞ da zuma farar saka
☞ da lemun tsami
sai ki hadasu guri 1 ki rinka shafawa a nonon, bayan awa
daya ko ( 30 minutes) sai ki wanke ki shafa man zaitun,
malama zaki sha mamaki.
✎ GYARAN NONO GA BUDURWA ✎
wannan wani hadi ne da akeyi don gyaran nono musamman
ga budurwa, shi wannan hadi kuma kowace macema intana
bukata zata iya amfani dashi saboda tasirinshi, yanda akeyi
shine za a samu.
✧ garin waken soya
✧ garin alkama
✧ garin zogale
✧ garin bawon lemun zaki
✧ kunfan maliya
✧ da zuma
sai kica kudasu guri daya sai ki rinka shafawa a nonon bayan
30mtn ko sama da haka sai ki wanke,sannan kuma ki rinka
shan kunun alkama zaki sha mamaki.
â–“ DON DAWO DA MARTABAR NONO DA GIRMANSA â–“
ga matar da take son ta dawo da martabar nononta ko
girmansa yanda zatayi shine zata samu
✦ ganyen sabara mai kyau
✦ da ‘ya’yan alkama suma masu kyau
sai ki rinka kunu dasu, ko kunun gyada, ko kunun alkama, ko
kunun shinkafa, ko kunun gero, ko ko ko duk dai wanda
yasamu sai ki dafashi da wannan hadin mai albarka.
DON MAGANCE MATSALOLIN MA’AURATA
AMARYA KO UWAR GIDA GA TSARABA
shi wannan hadin yana da banmamaki musamman wajen
karin soyayya tsakaninki da mai gida, da martaba da farin
cikin mai gida da nishadin amarya kuma yanasa maigida yaji
dadin da bai misaltuwa zaki zama gagara gasar masu gasa,
saboda shi wannan hadin manya mata ne
✎ ya’yan kankana
✎ danyar gyada mai kyau
✎ dabino
✎ alkama
✎ garin kumasoriyya
✎ ya’yan zogale
sai ki dakesu suyi laushi sai ki rinka shan karamin cokali da
madara ta ruwa safe da yamma kuma shima mijin zai iya sha.
TSARABA GA MASU NIYYAR AURE
wannan wata irin tsaraba ce mai banmamaki musamman ga
‘yan mata masu niyyar aure, ko amarya, kai harma da
uwargida sarautar mata,
shi wannan hadin yana kara ni’ima da nishadi sannan kuma
yana magance matsalolin da ke rage martabar mace yana
kuma sa juriya yanda akeyi shine:
âž½ karas sai ki yayyankashi kanana-kanana sai ki shanyashi ya
bushe.
âž½ zangarniyar zogale kwara daya1.
âž½ garin jir-jir na asali
âž½ garin dabino
âž½ da rumzali
sai ki hada su guri daya ki dakesu sai sunyi laushi sai ki hada
da mazankwaila sai ki rinka sha karamin cokali da nono dau
daya a rana shima wannan hadin yana da kyau
Wasu littafan Hausa da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels PdfÂ
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng