Mallaki Na Ce Complete Hausa Novel
Mallaki na ce hausa novel
TAG: mallakina ce hausa novel
Hohoho! Ina masoya kuma makaranta litattafan hausa novel? Yau ma ga jarumar ta ku ta dawo a cikin sabon littafin ta mai taken *MALLAKINA CE*, *MALLAKINA CE* littafine da ya k’unshi wata irin cakwakiyar soyayya, sark’ak’iya da kuma ban al’ajabi gami da barkwanci, zai fad’akar ya nishad’antar da masu karatu, albarkacin sabuwar shekara da za’a shiga, littafin zai fara zuwa muku *15/01/22*, domin samun na ki da wuri ki/ka hanzarta biya dan karatu cikin salama, ka da ki bari a baki labari maza hanzar ta ki nemi naki akan farashi mai rahusa. Ga mutanenmu na Niger zaku biya katin dala dari Cfa zaku tura akan lamba kamar haka *+227-94-98-56-52*,
Mun gode sai kun zo.
Bismillahir rahamanir rahim
D’AND’ANO
Tag: Mallaki na ce
A nutse kamar yanda ma fi aksarin masu sunan *Abbakar Sadiq* suke kasancewa ya shigo falon da sallama, cikin haiba da k’asaita ya dunfareta, tunda ta ji bai jira an amsa sallamar ba, bai kuma kalli kowa dake falon ba sai ita ya tabbatar mata da wata a k’asa, amma sai ta nutsu tana kallon dogayen k’afafunshi masu d’auke da zara zaren yatsu har saida yayi daf da ita ya rage kad’an yayi saura k’afarshi ta tab’a k’afarta da ke mik’e.
Da wani irin sauri ta tank’washe k’afafunta ta ja baya sannan ta mik’e tare da sakin littafinta dake kan cinyarta tana karatu, rusunawa yayi tare da kai hannu da niyyar cakumar gashinta data bari a waje ba d’an kwali, sai muryar mahaifinshi wanda tun shigowarshi yana shirin amsa sallamarshi amma ya ga ba wannan ne a gabanshi ba sai ya dakata yana kallo ya ga me zai yi.
Mallaki na ce hausa novel
A razane yace “Kai! Lafiyarka k’alau kuwa?”
Da sauri ya janye hannunshi tare da d’agowa ya juya, sam bai yi tsammanin mahaifin na d’akin ba, ashe ba shi kad’ai ba ma har da mahaifiyarshi na zaune da kuma Goggon shi, cikin rashin jin dad’i ya dawo baya ya tsaya kusa da mahaifin na shi dake zaune kan kujera, kakkafeshi da ido Abba yayi yace “Da me ka yi niyyar yi Sadiq?”
Murmushi ya saki ya girgiza kai, tsaf Umma dake kallonshi ta fahimci da matsala, wato murmushin nan ne mai kama da kuka da yake yi idan ranshi ya b’ace, shi kuma gashi miskilin tsiya bai cika nuna damuwarshi ba, mutum ne mai koyi da fad’ar Manzon Allah (S.A.W), yana had’e fushinshi ko da kuwa zai iya d’aukar mataki, Abba kuma da bai fahimta ba d’orawa yayi da “Ban yarda da wannan girgiza kan ba, za ka fad’a min ko kuwa?”
D’aga kanshi yayi ya kalli mahaifin na shi, ba tare daya d’auke murmushin nan a fuskarshi ba yana kallon fuskarshi a ladabce yace “Abba, yarinyar can nake so na koyawa hankali, ina so na ji me ye tsakani na da ita da ke b’ata min suna? Me take nufi da ni da take min haka? Me kuma take nufi da abinda ta fad’a?”
Da sauri Abba ya kalli *Sajeeda* dake tsaye da rigarta t-chirt da zanen atamfa, ta d’auki littafinta ta ri’ke tana kallonsu ita ma sai zare ido take.
Mahaifiyarta da tun da ta ga ta wuntsila ta tashi tasan bata da gaskiya, harara ta cilla mata tace” Me kika masa?”
D’aga hannu tayi sama dake nuni tsakaninta da Allah sannan tace” Wallahi Mama ni ban sani ba, duk wunin yau ma fa ni ban gan shi ba.”
Mallaki na ce hausa novel
Wani kallo ya watso mata, a tausashe kallon yake kuma a nutse, sai dai daga k’wayar idon na shi zaka fahimci kakkausan kallon, yar k’wafa yayi sannan ya maida kallonshi ga Abba dake fad’in” Me tai maka kuma yanzu?”
Cikin sanyin murya yace” Abba har makaranta yarinyar nan ta samu *Zalika* ta fad’a mata wai ni da ita soyayya muke, kuma wai idan bata fita a harkata ba sai ta babbakata da ranta…”
Nunata yayi da hannu yace” Yanzu Abba sai da ita zan yi soyayya? Ta rasa abinda zata had’ani da shi sai da kanta? Abba…Abba, wallahi na rantse da Allah idan yarinyar nan bata fita a shirgi na ba zan sauke mata kafad’a, bana so ta daina daga yau.”
Wata k’wafar ya kuma yi a sanyaye sannan ya mik’e ya fita a d’akin, da kallo duk suka rakashi inda Bintu ta bi Sajeeda da kallo, kallo ne na takaici da jin haushin taurin kan yarinyar, ta sha nuna mata ta fita a harkarshi, amma bata san me yasa bata ji ba?
Umma kam ko kallon Sajeeda ma ba tayi ba sai mik’ewa da tayi ta bi bayan Sadiq, dan ita ta fi kowa sanin halin d’anta.
Mallaki na ce hausa novel
Abba ma juyowa yayi daga kallon daya bi shi da shi na mamakin yanda ya kora gargad’inshi amma a tsanake ba tare da hargagi ba, cikin taushin murya da ruwan sanyi ya aika mata sak’o mai razanarwa.
Auren Lagos Romantic love story
Kallon sauran yaran yayi dake karatunsu amma kunnuwansu da hankalinsu kaf yana ga abinda ke faruwa, inda Khausar sam bata ji dad’i ba, ta yi fatan ina ma Abba bayanan Yaya Sadiq d’in ya shak’i wuyan yarinyar can, tsawar da Abba ya daka musu cewa “Ku tashi ku koma ciki.”
Ita ta dawo da ita daga tunanin da take, da sauri duk suka mik’e suna kwasar litattafansu, saida suka shige Sajeeda ma ta juya zata shiga na ta d’akin yace “Zo nan.”
A hankali ta shiga takowa har ta zo kusa da shi, tsugunawa tayi a raunane kamar za tayi kuka tace “Abba gani.”
Gyara zamanshi yayi sosai ya matsa kusanta yana kallon fuskarta yace “Sajeeda ‘yata, kinsan dai ni mahaifinki ne ko?”
Jinjina kai tayi alamar e tare da amsawa cikin shagwab’ a tace “E Abba.”
Jinjina kai yayi shi ma sannan yace “Ina so ki fad’a min me yasa kika samu budurwar yayanki kika fad’a mata cewa kuna soyayya? Me yasa kika yi haka?”
D’agowa tayi ta kalleshi, sai kuma ta sunkuyar da kanta k’asa ta fashe da kuka marar sauti, dafa kanta yayi yace “Na d’auka ni da ke abokai ne, na d’auka bama b’oyewa juna komai? Yaushe muka fara haka da ke?”
Girgiza kai ta dinga yi amma ba tayi magana ba saboda kukan dake tik’ak’arta, a sanyaye ya sake fad’in “Kinga Sajeeda, ki daure ki fad’a min abinda ya faru, kinga dai bana so ya tab’a lafiyarki a gidan nan, kin san fa bana so hakk’in maraya ya kamani.”
Cikin matsanancin kuka da shashek’a ta k’arasa yin zaune ta fara fad’in “Abba…ka ga dai ban tab’a fad’a ma kowa ba sai kai, bana so ka fad’a ma kowa kai ma, ya zama sirri a tsakaninmu.”
Jinjina kai yayi yace “In shaa Allah babu wanda zai ji, fad’a min ina jinki?”
Saida ta ja majina ta fara fad’in “Abba ni ma bansan me yasa ba, ban san ko yaushe hakan ya fara faruwa dani ba, haka kawai dai na ke jin na tsani Yaya Sadiq ya dinga danganta kansa da wata ‘ya mace, haka kawai nake jin ba dad’i idan yana firar wata ya mace a gabana, raina ya kan b’aci matuk’a idan yana alak’anta kansa da wata mace, wani irin abu nake ji a zuciyata a game da shi, Abba sai na ke ji idan zai nemi aure sai dubu, to zan lalata auren sau dubu saidai ni da shi duk mu zauna a haka ba tare da aure…”
Da sauri Abba yace” Shiiiiiiii!”
Girgiza mata kaibya dinga yi yana fad’in” Ko kusa kar na k’ara jin kin fad’i haka da bakinki, kar ki sake fad’in haka kin ji ko, me yasa kike tunanin zaku mutu babu aure?”
Kallonshi tayi tana share hawaye tace” Saboda baya so na, ya tsane ni Abba, ban san me na masa ba? Ban kuma san hikimar dake cikin abinda nake ji a game da shi ba?”
Kafad’arta ya dinga bubbugawa yace” Daina kuka haka ya isa, share hawayeki kin ji, In Shaa Allah indai Sadiq ne matsalar, to ni nan uban Sadiq *Aminu* na miki alk’awarin d’aura miki aure da shi.”
Sadiq dake ta fafutukar bud’e d’akinshi ya shiga rai b’ace yake fad’in” Na tsaneta, na tsaneki, me yasa ba zaki fahimci haka ba? Mayya kawai aljana bai bak’in hali.”
Umma dake sauraronsa girgiza kai tayi a tausashe tace”…
*Kun ji salon labarin ? Me kuka fahimta game da d’an tsakuren nan?*
*Sai mun had’e yan amana*
Leave a Comment