Maltina Da Peak Milk Basa Kara Jini A Jikin Dan Adam
mutum yana karancin jini, ko tana dauke da juna biyu ko ta
Haihu ta zubar da jini diyawa sai kaji ance a bashi malti na da
peak milk, a fahimtar mutanen mu zai kara jini.
Gaskiyar magana babu alaka sakanin karin jini da Maltina da
Peak milk, sabida wake kwara daya yafi Maltina da Peak milk
wajen samar da sinadaran kara jini.
Idan kun duba jikin gwamgwanin peak milk za kuga babu
sidaran karin jini a ciki ( not rich in iron) Haka Maltina ma
Babu sinadaran kara jini a ciki.
Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk yazama
maganin karin jini ?
Amsa: wannan kawai al’adace ta mutanen mu ba tareda sanin
abun ba.
Maltina na dauke da sinadaran:
– Calories
– Carbohydrates
– Fat
– Vitamin
– No Iron
Peak milk na dauke da sinadaran:
– Fat
– Carbohydrates
– Protein
– Salt
– Vitamin A and D
– No Iron
Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana
bukatar sinadaran iron daga abincin da muke amfani.
Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashe
wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani
da su wajen siyan abinci masu dauke da iron kamar :
– Wake
– kifi
– Nama
– kwai
– Kaza
– Fara
– zogole
– Cashew
– cavage
– salat
– Spinach
– da sauran su.
Allah ya kara mana lafiya gabaki daya.
Tayimin kankanta complete hausa novel