Hausa Novels

Manyan Mata Kalli Hotuna da Video

Manyan Mata Kalli Hotuna da Video

Manyan mata

Manyan mata

 

 

 

 

 

 

[30/09, 10:06 am] +234 906 908 0725: _*🌎RAYUWAR MA’AURATA 🌎*_

 

 

_(Sabon salo)_

 

 

 

 

Hakkin Mallakar

 

 

_*Ikilima Adam (kyauta daga Allah)*_

_Da_

_*Sarat Alk’asum (Maman Nusaiba)*_

 

 

 

 

_JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION_

 

 

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, yadda muka lafiya ya rabbi kasau gama shi lafiya, ina fatan dai my fan’s baku manta Rayuwar Ma’aurata ba, to yau Allah ya nufa mun kawo muku cigabanshi asha karatu lafiya.

 

 

Littafin na kud’i ne akan 300#, kacal zaku sameshi domin k’arin bayani sai ku tuntube wannan number👉🏻 +966599791573 ko kuma wannan 09069080725.

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

 

 

 

_*CIGABAN RAYUWAR MA’AURATA*_

 

 

SHAFI NA DAYA️ 1️⃣

 

 

Cikin matuk’ar razana Zainab take kallon shi saboda tsabar tsoro k’amewa tayi kamar wata Soja,batayi aune ba taji ya dauketa da maruka Har wajen uku.

 

Wani kara ta saki, rike da kuncin ta cike da radadin Azaban da taji ,tace Abban Hussaini me nayi maka ne?

 

Bebi ta kanta ba daukar wayar ta yayi ,yasoma duba wace number ce ,ganin number ansa kawalli ne yasa shi fuskantar ta , cikin bacin rai yace wace ce kawalli?

 

Zainab rike da kuncin ta ,tace wannan kuma ba damuwar ka bane kuma wallahi sai Allah yasaka mun mugu azzalum…

Kafin ta karasa fadin Abunda take niya habawa Abban Hussaini ya soma dukan ta ba kakkautawa Saida tayi laushi bakin ta ya mutu .

 

Wani uban ihu ta kurma tana fashewa da kuka tace ihuu jamaa kuzo Ku taimake ni ze kasheni saboda zeyi sabon aure.

 

Nan da nan Makota sukayi ta shigowa ,ganin ana shigowa gidan cikin tsawa yace nace mukuuuuu Ku fita daga gidan nan ko!..

 

Cike da tsoro kowaccen su tafara juyawa tana girgiza kai .

Ganin sun fita ne yasawa kofar key yadawo cikin gidan tareda zaman kan kujerar yana maida numfashi .

 

Kallonta yake ta Gefen idanu tana Jan jikin ta harta isa kuryan dakin ta .

Gyara zaman sa yayi yasoma fad’in Wallahi Zainab ban miki komai ba, Yanzu muka sa kafar wando daya dake .

 

Wayar ta dake a tarwatse a kasa ya tattara tareda sakawa a Aljihun rigar sa.

 

 

********************

 

Abban Ahmad a kasuwa yaje siyan doya kwaya daya cewar sa komai yayi ,tsada mai na dari ya siya tareda yajin naira hamsin , cikin Isa yace habawa yanda kayan Miya ke tsada ina kai mata ko zakin maggin bazanji ba .

Kokarin wuce wa yake yaci karo da Wata tsalelliyar yarinya kyakyawa Ajin karshe daga ganin ta yar boko ce.

Kasa jurewa yayi hakan yasa yabi bayan ta, sai da ya tsaya ya gyara zaman rigarshi san nan ya karkade wandonshi ya shafa sumar kanshi yana fad’in” Kutmar dumadu gaskiya yarinyar ceb ta had’u. Da hanzari yabi bayanta.

 

Yan mata ! Yan mata !

 

Ji mana , Yarinyar waigowa tayi tana kallon sa , cikin hada rai , yana karasowa gaban ta , ya danna ringtone din wayarshi saiga wayar ya soma kara ji kake ! Wakar hamisu breaker na tashi , bakin sa a washe ya kashe ringtone din , tareda kara wayar a kunnen sa cikin iya taku shi yafara magana yana murmushi yace” haba don Allah banason kuna mun wasa da Aiki rannan na baku Millon uku yau kuma kunce babu kudin nan to me kukayi dasu ne? A’a bazan lamunci cin Amana ba , yanzu ka kira mun Abokin aikin ka Faruk yazo da mota dan na kosa in bar wajen nan akwai Kura da rana yakarashe zancen yana buga uban tsaki. Itakuwa Yarinyar murmushi take tana washe hakora ganin kamar ya gama wayar ne , tace” yi hakuri Yallabai banji me kake fadi dazun ba , wani kallo yake mata kafun daga bisani yace ” Dalla cen ware naga sai magana nake miki kina cin magani , ko bakisan waye ni ba? Yarinyar cikin tsirriyar muryan ta , tace ” afuwan ba kai nakewa kallon banza ba , gyara tsayuwar sa yayi yace ” ni sunana Alhaji Ibrahim mai dala, Babban dan kasuwa ne ni duk fad’in garin nan ba wanda bai sanni ba Babba da Yaro. Murmushi kwance akan Fuskar yarinyar tana fari da idanu tace ” Alhaji kai dan garin nan ne ? Kwarai kuwa anan nake ina da mata mai shegen raini agida da yara , kwabe Fuska tayi tace ” kamarka Alhaji har wace mata , ta rainaka lallai na Lura , batasan darajan aure ba , tsaki yayi yace ” shiyasa nakeson in dankaro mata kishiya , ko zata gyaru tasan hakkokin miji akan matar sa, murmushi yarinyar tayi tace” barta ina shigowa gidan Ido ze raina fata badai takamarta rashin mutunci ba , ka barta zata hadu da wacce tasan darajan aure ,washe hakora yayi yana fadin baby baki fadamun sunan unguwar taku ba ? Cikin fari da idanu tace” ai sunan unguwar tamu gwammaja tagwayen gida da kace a gwada maka gidan Amarya me turare har nan za’a kawo ka, kuma sunana Aysha Muhammad , Mahaifina yana Libya cen yake aiki , zazzare idanu Abban Ahmad yayi yana fadin MashAllah acikin zuciyar sa , afili kuma Yace” MashAllah gimbiya Aysha , kin hadu fa gaki kyakyawar baby ko kinada Alaka da yan shu’arab ne ? kwarai kuwa shine Amsar data bashi tana fari da idanun ta , washe baki yayi yana dariya yana kara kare mata kallo tun daga Sama har kasa , a zuciyar sa yace” chab Zan ja kaya , sai inyita fama da hauwa me bakin rai , jibi yanda yarinyar nan ta hadu ta ko ina , maganar yarinyar ne ya katse masa tunani jin tana fadin , yadai mai dala tunanin me kake? Murmushi yayi yana kame kame yace” kawai ina tunanin motocina dasuke hanya ina Addu’a kada Allah yasa a kama su. Aisha tace” haba Alhaji ka daina damun kanka bazasu kama ba nida nakeson in sun iso in dau daya, ware idanun sa yayi yana sosa kai cikin isa yace ” duk Wanda kike so , ki dauka na baki dama bari dai su iso , yanzu sauri nake zanje gidan mai in dau motata , hannu yasa cikin Aljihun nasa sai gashi ya zaro dubu biyu gajiyyayun kudi , cikin karya harshe yace” my baby amshi wannan ki hau mashin , kinsan bana yawo da canji a hannuna , murmushi dauke a bakin ta , tace” haba Alhaji nasan abune me wahala irin Ku ,su ringa yawo da kudi , kawo wayar ka in baka number ta , ahanzarce ya zaro iPhone din sa , ya mika mata ,itakuwa ganin babban waya tace ” wow Amma fa Alhaji kayi ta ko ina , saka masa number tayi , tareda Miko masa , amsa yayi yafice yana waiwaye sai daga mata hannu yake har ya bace mata da gani .

 

Wani lungu yaje ya rabe yana zazzare idanu , dudu Aljihun sa dubu uku ne , yanzu dubu daya kacal ya rage masa , kai tsaye wajen me kayan Miya yaje yayi siyayyan dari Biyar , tareda tare me mashin din daze kaisa gida yanata waige waige kada Allah yasa Aysha ta ganshi har suka bar unguwar kasuwar.

 

 

Sulaiman , sallama dauke a bakin nasa yashigo gida , hannun sa rike da bakar jaka , da mamaki yake kallon Maryam kwance saman kujera ta daura kafafun ta , daya kan daya eapeace yana kunnenta sai wake wake take , karasa shigowa dakin yayi inda yake kara mata kallo ganin wawar kwanciyar da ita Har ana hangon pad din dake jikin ta , gaban ta ya yatsaya yana magana cikin bacin rai , yace” haba Maryam wai yaushe zakiyi hankali ne , kullum ayita Abu daya saikace karamar yarinya , kallon bakin sa take dan batasan ma me yake fadi ba , hakan yasa ta tashi zaune tareda zare eapeace din daga kunnen ta , tana kallon sa cikin Alamun tambaya lafiya kuwa? Tsuki yaja yace ” ke karki sake kwanciyar iskanci a falo na , bayan kinsan kofa a bude take yana hura hanci , sake da baki take kallon sa tareda soma tattara gashin kanta daya rufe mata fuska , cikin yatsine fuska tace ” to wallahi baka isa ka hanani yin yanda naso agidan nan ba , kafito wajen karuwar ka , wai kai me hankali ko? Kai baka isa kamun fada ba , saboda kai ma kana bukatar hakan takarashe zancen tareda Jan tsuki.

Rike da kugun sa yace ” Maryam ni kike fadawa haka? Kwarai kuwa an fada maka ta mike tsaye tana Galla masa harara , to wallahi zan dauki mugun mataki akan ki cewar Sulaiman kuma daga yau na kara ganin kinyi irin wannan kalan iskanci kwanciyar wlh saina zaneki kuma in tura ki gidan naku kije a baki tarbiyyar iya zama da Miji , maganar karuwa kuma a haka nake son ta , inhar Neman aure ya zama karuwan ci , kenan kema a karuwancin na auroki , ware idanun Ta tayi tana kallon sa tareda buga salati , yo ni kafun ka aure ni kasan na girmi Ajin ka , kaima kasan Masu zuwa Neman aure ne daga yayan sarakuna sai yayan gwamnoni su Minister nabi son zuciyar banza wai shi soyayya na aure ka dan inaganin kamar kai ne din zamufi samu kwamciyar hankali batareda kamun kishiya ba ashe abun ba haka yake ba takarashe zancen tana jijjiga , shikuwa ciza labban sa yayi yace ” ai da sunsan wacece ke koda sadaka aka basu ke wallahi bazasu zo ba , kallanki fa , kyaun da maciji ne, kazantar ki babu me iya dauka a cikin su wanka ma sainace kiyi hakama brush saina sakaki a bandaki sannan kike tuna kiyi , sallah ma saina hada da magiya , babu Da babu jika ke wace irin sakarya ce wacce batasan yanda ake kula da kai da Addini ba ,bare kuma ki kula da damuwar mijin naki, auren kamar nayi nagama wlh saide kiyi duk Abunda zakiyi na miki horn daga yau , kwanciyar banza a falo zesa kije gidan naku kiyi zaman tsawon lokaci ,banza shasha yakarashe zancen tareda barin falon fuuuu kamar ze tashi a iska , aguje tabi bayan sa tana kuka tsare kofar shiga dakin sa tayi tace ” cikin kuka tace ” Sulaiman yanzu da bakin ka ,kace mun kazama innalillahi wa’innalairajun tunda nake ba’a taba Furta min haka ba sai kai ,wawan kallo yake bin ta dashi batareda ya tanka mata ba , yace ” bar wajen nan nace tun kan a haifi da mara idanu , jin yanda sautin muryan sa ya canza babu alamun wasa hakan yasa ta kauce shikuwa a zafafe yashige dakin nasa tareda danna masa key ta ciki , kwanciya yayi kan gadon nasa , yashiga tunani iri iri akan lamarin matar nan tasa, itakuwa Maryam bubbuga kofar take da karfi cikin kuka tace ” Sulaiman ni zaka wulakanta saboda ina karkashin ka , dakyar taja jikin ta , tazo falo ta zauna tana kuka mai tsuma rai , saiga kanwar tashigo daga gidan su, a firgice Yarinyar da bazata wuce 16 yrs ba ,taje gaban yayar tata , cikin damuwa tace” anti Maryam me yake Faruwa ne? Dakyar Maryam ta dago kai tana kallon kanwar ta , tace ” Fauziyya banyi sa’ar mijin aure ba , Sulaiman aure ze kara yanata min wulakanci kala kala daga wannan sai wannan yanzu haryakai matakin da yake fadin inna kuskura ze tura ni gidan namu inyi tsawon lokaci saman in dawo , Subuhannallah Fauziyya ta Furta tace ” kai Kai haba Antin Maryam , Sulaiman din ne ya koma yanda kike fadi kodai wani Abun kika masa , kofa haihuwa bakiyi ba shine ze miki kishiya tun wuri , gaskiya yaci Amanar ki indai haka abun yake , Maryam kara sautin kukan nata tayi tace” ki barshi mu zuba mu gani zanga gidan da ze kawo wata shegiya da sunan mata .

Fauziyya sossai tashiga rarrashin yayar tata , tace ” daman momy ce ta turo ni tace” idan kudin sun taru ki bani inkai mata , sannan ma wai yaushe zaki fara zuwa aikin ki ne? Ware idanun ta Maryam tayi tace ” kiyi kasa da Muryan naki yana ciki fa , Fauziyya zazzare idanu tayi au haba shine baki fadamin ba , kika bari mukayita firan nasa , Allah Yasa be jiyo mu ba , da Ameen suka amsa , Maryam share hawayen nata , tayi tace” aiki sai karshen satin nan InshAllah Zan soma zuwa kinsan hutuna ya kusa karewa , InshAllah Zan huta da bakin cikin zaman gida , sannan kudi kuma ban tara da yawa ba , yanzu yadaina bani kudin cefane saidai yaje yayi siyayya da kansa , shiga dakin nata tayi ta fito tareda bude jakar ta , ta zaro dubu dari Biyu , aciki cikin yin kasa da Murya tace ” Kinga Abunda na samu a Watan nan , yanda yake ban dubu goma arana yanzu ya daina , dubu uku yake ajiye mun , wallahi sauran kudin dubu darin a jakar sa na dauka be sani ba , dan haka ki hada ki kai mata , dani yake zancen harni yake Zagi kazama dan kawai namishi karyan duk samari manya manyan attajirai ne , ware idanu Fauziyya tayi tace” besan shine Attajirin cikin su ba , keko dole ya dau zafi Amma kiyi hakuri InshAllah duk Abunda ake ciki Zan sanarwa mummy daga haka tafice batareda Maryam ta mata rakiya ba.

 

 

Abban Ahmad a afujajan ya shigo gida yana rarraba idanu , sallama yake ta kwadawa tun daga waje sai ihun fadin hauwa ! Hauwa yake? Rigarsa datake wanke wa ne ya ajiye aroban ta taho aguje cikin hanzarin ta , bakin ta na rawa tace” Abban Ahmad lafiya me yake Faruwa dakai ne? Sake kayan cefane yayi kasa yace ” hauwa babu kanta wlh wai akasuwa aka samu Wanda ya yashe mun kudadena har dubu Biyar ya cilla aguje kinsan nace miki har nama Zan siyo , wlh da dubu daya yabarni yakarashe zancen yana sallallami , Hauwa cikin ware idanu tace ” kudaden da ka fita daga gidan nan shine aka samu wani tantitiri ya bika mun shiga uku ni Maman Ahmad tafada tana kokarin dauke ledar kayan miyan , cikin raunin Murya tace ” karka damu haka Allah yaso , kokarin shiga take tana jin zafin Abunda aka masa taji , yana fadin yauwa hauwa bansiye maggi ba da kuma kince kanwa yakare , kisiyo harda gishiri kuma kisai ruwa pompo a sanyaye ta juyo tana kallon sa tace ” Abban Hussaini ai baka bani kudin ba Innalillahi wa’innalairajun yake furtawa cikin surfa ruwan bala’i yace” Anya Hauwa kinason ki gama da duniya lafiya kuwa? koko dai…….

 

 

 

 

 

 

_*Ku kasance da zafafa biyu Masu nishadantar daku Maman Nusaiba tareda Kyauta daga Allah*_

[02/10, 11:07 am] +966 57 767 5904: _*🌎RAYUWAR MA’AURATA 🌎*_

 

 

_(SABON SALO)_

 

 

 

 

 

Hakkin Mallakar

 

_*Ikilima Adam (kyauta daga Allah)*_

Da

_*Sarat Alk’asum (Maman Nusaiba)*_

 

 

_JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION_

 

 

بسم الله الرحمن الرحيم

 

 

_*CIGABAN RAYUWAR MA’AURATA*_

 

 

 

_*SHAFI NA ️BIYU 2️⃣*_

 

Koko wani sabon salon rashin girmama Miji ne kika koyo? Ince miki an yashe min kud’i amma kizo kina wani ban baki kud’in siyan maggi ba, idan fa naga dama Wallahi tsaf zan ki d’aga kafata ki shiga aljanna, ko kin manta aljannar ki na karkashin tafin kafata? Tinda baki san darajar aure ba sai na take abuna. In banda rashin godiyar Allah jiya fa dari biyu na baki kudin cefane kuma na lissafa naga sauran naira ashirin tayi ragowa, to ki sayi maggin da ita mana nifa ba dan iska bane irinki kin gane ko! ki fita idanu na” Ya fad’a yana zare idanu san nan ya nufo kofar shigowa ciki, koda ya iso inda take a tsaye bangaje ta yayi ya wuce yana fad’in” Na kusa maganin ki Mata sai shegen munafurci zaki gane kala ta, kuma kizo ki kawo min abinci in kuma baza ki bani ba sai ki fad’a min.. Hauwa ta rintse idanu jin ta bugu da bango ,a sanyaye ta mik’e tana yarfa hannaye ta iso ciki wajan wankin da takeyi ta nufa ta matse ta shanya tana jin Abban Ahmed yana ta fad’a wai ta kyaleshi. A parlo ta sameshi zaune ya cire hularshi yana watsa mata harara” Kitchen ta nufa ta kawo mishi tuwo da miyar kubewa sai kamshi yake zubawa, a hankali ta durk’usa tace” Abban Aliyu ga abincin nan. Sai da ya watsa mata harara kafin yace” Zuba min a kaina wai ke yaushe zaki gane yadda ake kula da Mijine? Kin wani durk’usa kamar zaki min sujjada fuska ba annuri kina min magana kamar kinga dodo, ke ko irin dan salon nan na kashe mai gida da kalamai baki iya ba? Sai kuma yaja tsaki ya janyo abincin ya soma ci” Sai da yayi kusan loma biyar ya d’ago ya had’e rai cikin b’acin rai yace” Eh lalle ba shakka Hauwa sannu Mandiya Uwar shagalallu, yanzu wannan shine girkin? Gaskiya ina asarar kud’ina a gidan nan” dogon tsaki yaja san nan yaci gaba da cin abincin sai mita yake wai ta cika yaji a miya, idan ya hadiye sai yace ai miyar ba maggi a cikin” Ita kuwa Hauwa tagumi ta rafka tana kallon ikon Allah, cen dai ta tashi tayi taje ta kawo mishi wata takarda ta mika mishi tayi tsaye a kanshi tana had’e rai” Sake da baki yake kallon ta sai kuma yaja tsaki yace” Dukana zakiyi amma ko? Tab’e baki tayi tace” Kaga Abban Ahmed ni ba wannan fad’an bane a gaba na, su Ahmed ne aka korosu daga School ance ba’a biya kud’in da aka ce a kawo ba har kusan wata uku, kuma ji nake da kaina na dauki kudin na baka ka fita ka kai musu ,amma sunce wai ba’a biya ba. Mik’ewa yayi yana zare idanu sai kuma yace” Kundun uban cen ni za’a renawa hankali? Hauwa sune suka kawo sakon ko kuma su Ahmed d’in ne suka kawo? Hauwa tace Su Ahmed dai, yanzu haka da k’yar na rarrashe su sukaci abinci suka kwanta, da nace zan kai su gidan mu su yini sai kuma na tuna ban fad’a ma ba. Kasan Ahmed da son karatu yanzu haka zazzab’i ne a jikinshi da k’yar yayi shuru ni kaina sai da ya bani tausayi.. Abban Ahmed ya jinjina kai yana jin ba dad’i duk da masifar shi yana bala’in son Ahmed fiye da tunanin mai karatu, dan haka yace” Zanje Gobe da kaina su ganni na fad’a musu na kawo kud’in fa. A sanyaye Hauwa tace” To Allah ta kai mu” Da ameen ya amsa san nan ta wuce daki shi kuma ya zauna a parlon…

 

Mufeeda na ta saurin saka hijabin ta da hanzari ta fito parlon tana fad’in” Abban Aliyu kar dai ka fice. Mik’ewa yayi yace” Taya zan tafi na barki bayan nace tare zamu tafi, murmishi tayi tana kallon shi sai kuma ta matso kusan shi ta kai hannu ta gyara mishi hular kanshi tana murmishi tace” Kayi kyau Abban Aliyu d’ina. Dariya yayi har sai da fararen hakoran shi suka bayyana yace” Ai duk kyau na ban kai Matata ba abar alfaharina” Amma fa kar fa na fita wata taga na mata kyau tace tana sona. Murmishi tayi tace Haba wane mutum inji mutuwa ai dama so nake duk wacce ta ganka tasan ana baka kulawa ta musamman a gidan ka, yauwa tsaya ina zuwa minti d’aya please ” Ta fad’a tana shigewa daki. Bata jima ba ta dawo hannun ta dauke da wani kwali, tana isowa ta bud’e ta fito da wani turare mai shegen kamshi ta soma fesa mishi,shi kuma ya lumshe idanu yana shak’ar kamshin. Bud’e idanunshi yayi yakai mata runguma mai kyau yayi kissing din lips d’in ta yace” Allah ya miki albarka Matata” Ameen Mijina muje kar mu makara.. kama hannun ta yayi suka fita har bakin titi, mai Napep suka tare sai da ya fara kai Abban Aliyu School kafin aka sauke Mufeeda a Islamiyar da take koyarwa.. tana zuwa kamar yadda ta saba ta shiga koyawa Yaran karatun Alkur’ani mai girma da sauran litattafai…

 

Sulaiman ne a gaban Mahaifyarshi yana fad’a mata abinda Maryam take mishi, cikin fusata ya d’ago ya kalli Mahaifiyar tashi yace” Gaskiya Mommy bazan iya ba Wallahi sakinta zanyi na huta da wannan cin gubar, haba Don Allah ta mayar min da gida kamar Bola. Har kunya nakeji wani nawa yaje gidana, nidai Mommy kiyi min Azini na saketa kawai..

 

Mommy ta kalleshi cike da tausayawa badan tana tunanin wani abu ba da ta bashi izini ya saki Maryam, saboda ko ita ma ba mutumtata ba take a Matsayin ta na Uwar Mijin ta” numfashi taja tace” Am Sorry my Son kayi hak’uri kaga Y’ar Uwarka ce idan ka sake ta wa zata aura, kayi hakuri wata rana zata gyara take maka biyaya, kuma kasan dai halin Uwarta da anyi haka cewa zatayi ni na saka ka sake ta, zata min abinda ba zan jura ba dan haka kayi hak’uri kaji Allah ya nuna mana lokacin da zaka auri Fatima.. kwafa yaja ya mik’e yana fad’in” Ameen Mommy nifa dama saboda darajar Daddy nake raga mata da kuma ke, amma inba haka ba da tuni wata maganar ake ba wannan ba” Yana gama fad’in haka ya fice waje, rai a b’ace ya shiga motarshi ya nufi Gidan su Fatima..

 

 

Zainab da Maryam ne zaune ko waccen su sanye suke da kayan Doctor’s” Zainab ta girgiza kai tace” Gara dai da muka dawo daga hutun nan bakiji yadda nake jin kewa ba, gashi yanzu Abban Hussain ya koyo wasu sabbin halaye wai saboda tsabar Jaraba ma Nadiya take ko uwar wa ma wai ita yake so ya aura. Waro idanu Maryam tayi ta zabura tace” Kuturu kema abinda yake shirin miki ? Kan bala’i to Alkur’an bamu ga ta zama ba nifa yanzu yama dena bani kud’in cefane,wai da kanshi zaike siyowa Y’ar sarkar gwal d’in da Matan masu hali suke siya ni kinga bani da ita. Shine fa nake zarar kud’i idan ya kawo kafin yakai banki na b’oye, da yazo yace ina kud’i nayi fuska abuna nace ban gani ba” Amma kuwa Sulaiman da Abban Hussain sun cika maciya amana” Ta fad’a tana huci.

 

Zainab ta rafka tagumi cikin jin zafin abinda Abban Hussain ya mata tace” Ai ko zanyi yawo tsirara bazan tab’a bari a kawo min wannan kodaddiyar Yarinyar ba. In banda rashin godiyar Allah irin nasu da mai muka rage su . Maryam tace” Hmmm nifa ranar wai

har Gori ya ringa min wai sai na ga dama nake salla ko ina ruwanshi dani.. wata Nurse ce tazo wucewa taji abinda suke fad’a ta k’araso ta zauna tana murmishi, tace” Namiji kenan ai ko goyashi kikeyi a baya kullum to sai ya ci amanar ki” Ni kaina da kuke gani na da ciwon D’a Namiji a zuciya ta shiyasa yanzu nake shiri da kyau in zan sake aure.. Sake da baki suke kallon ta jin abinda take fad’a? Maryam data zaku taji abinda take shiryawa tace To wani shiri kikeyi wanda har Mijin da zaki aura ya kasa miki kishiya? Taku daya zuwa biyu tayi san nan tace” Idan har kun shirya zan fad’a muku amma ku bari sai gobe yanzu kuzo muje Sir yayi kira.. Jinjina kai sukayi cike da gamsuwa da maganar ta suka tashi sukabi bayanta….

 

Sulaiman nata sharara gudu ranshi a matuk’ar b’ace, Unguwar Jan bulo ya nufa layin gidan su Fatima ya shigo” A bakin kofar gidan yayi parking ya fito waje yana fesar da numfashi, wayarshi ya ciro daga aljihunshi ya dannawa Fatima kira” Assalam alaikum Sahibul Qalbee ka iso ne” Cewar Fatima. Wani k’ayataccen murmishi yayi yana jin b’acin ranshi na raguwa, yace Amin wa’alaikum salam eh my Rurul Qalbee na ke nake jira ina waje” Yana fad’in haka ya katse kiran.. Yana tsaye har ta fito cikin shigarta na kamilar Mace kamar wata wahainiya haka take taku ďai-ďai tana nufo shi. Sai da tayi sallama ya amsa san nan ta mishi izinin shiga ciki” Tana gaba yana binta baya sai binta yake da kallo mai wuyar fassarawa, suna shiga tace” Baba yace yana son ganinka bari na kira shi ko” Murmishi ya sakar mata yana jin kamar ya rungume ta ya binta da kallo har ta fita a parlon. Ajiyar zuciya ya sauke, bata jima ba sai ga Baba ya shigo dakin. Durk’usawa Sulaiman yayi ya gaishe da Baba ,cikin fara’a ya amsa masa san nan ya soma magana cikin kamala, yace Sulaiman dama na cewa Fatima idan kazo inaso na fad’a maka za’a d’aga bikin nan naku zuwa lokacin da Fatima zata zana jarabawa da kuma saukar Alkur’ani mai girma da makarantar su ta shirya yin taron, ina fatan zaka bari har lokacin. Ba haka Sulaiman yaso ba amma ba yadda ya iya haka ya hak’ura ya d’ago a sanyaye yace” Baba ai duk abinda kace haka za’ayi ,idan naje gida zan fad’awa Daddy komai yanzu yaushe ne za’a jarabawar tasu da kuma saukar? Baba ya kalli Sulaiman yadda yayi sanyi sai ya bashi tausayi, yace” sai nan da wata shida ka bani number Daddyn naka sai muyi magana wadda ka bani banyi saving ba na rasa ta. Ciro wayar shi yayi ya amshi ta Baba ya sanya mishi number Daddy” Mik’ewa Baba yayi yace To a gaishe da gida ni zan wuce kasuwa. Sulaiman yace OK Baba Allah ya k’ara girma, Ameen Baba yace san nan ya fita a d’akin.. bayan few minutes sai ga Fatima ta shigo da kayan abinci tana murmishi, ganin Sulaiman a sanyaye tayi saurin aje kayan tana fad’in” Sahibul Qalbee meya faru? Murmishi yayi yace Ba komai kawai dai Baba ne yace sai bayan kin gama jarabawa san nan za’ayi bikin mu” Itama jikinta ne yayi sanyi dan ta k’agara ta ganta a gidan Sulaiman a matsayin Matarshi ta sunna, Ajiyar zuciya ta sauke tace” Ba komai ai wata shida kamar kwana shida ne a wajan Allah.. kallon ta yake bako k’iftawa ganin yadda tasha kwalliya kamar zata wani waje, sunkuyar tayi tana rufe fuska tace” Wai kallon fa? Dariya yayi yace Kawai naga kinyi kyau ne shiyasa. Gyara zama yayi ya soma cin abincin, bayan ya gama ne ya ringa sa mata albarka dan ba k’aramar yunwa yake ji ba . Dariya tayi jin yadda yake santi tace” Wannan santi haka? Jinjina kai yayi yace baza ki gane ba ki tashi muje ki rakani bakin mota” Mik’ewa tayi ta bishi har bakin motar, sai da taga tafiyashi san nan ta koma ciki….

 

Maryam yau cikin jin dad’i ta k’araso gida duk da yamma likis tayi so take yau ta gwada yin abincin da Sabuwar K’awar su ta nuna musu” bakin dauke da Wakar Warr ta shigo cikin parlon tana yi tana gyada kai.. sake da baki Sulaiman yake binta da kallo ganin bata san dashi ba a parlon har ta zauna” Wakar ta tsayar tana maida numfashi taja tsaki tace” Aikin banza aikin wofi Wallahi nidai Maryam banyi sa’ar Miji ba, shi ko irin mai aikin nan ma ya kasa dauka min sai zafin kan tsiya.. Ba komai Wallahi sai nayi rashin mutumci a gidan nan fiye da tunanin shi, ni zai renawa hankali wai kishiya zai kawo gidan” Hmm zai gane wacece Maryam amma dai bari na tashi in daura mishi girki na gani ko zan iya yin biyayar dole.. amma dai n……

 

 

 

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
_*Ku kasance da zafafa biyu Kyauta daga Allah tare da Maman Nusaiba*_

Leave a Comment