Hausa Novels

Maraicina Hausa Novels Complete

Maraicina Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Yarinya ce da bazata wuce shekaru goma sha biyar ba a Duniya, d’auke da farantin da kwanika a kanta tafe ta ke tana kuka har ta iso k’ofar wani gida ginin k’asa ,shiga ta yi d’auke da sallama a bakinta tana kuma ci gaba da kuka, Matar dake cikin wani d’aki ce tafito da sauri tana ” Fad’in to munafuka yau ma kinyo min kwantai ne? To Wallahi bari kiji sai kin cinye shi kin biyani.cikin kuka ” Ta ke fad’in kiyi hak’uri Baba ba kwantai nayi ba wasu ne sukaci abincin sukak’i biya. Wani kukan kura Baba tayi ta damk’e ta tana dukan ta hak’uri take bata amma tak’i hakura, “Fad’in take muguwa haka kawai ki b’atarmin da kud’i to a jikin ki zan fanshe su bak’ar munafuka, nasan duk wannan bakin halin naki na Uwarki ne ki ka d’auko, haka kawai bani da haihuwa ba anbarni da wahala.tun tana iya bada hak’uri har ta kasa sai da Baba ta tabbatar da ta daku sannan tabar ta tare da ” Fad’in kuma ki tashi ki had’amin kwanuka ki wanke, tana gama fad’ar haka ta shige d’aki.

 

 

Tashi tayi da k’yar ta had’a kwanukan tana wankewa bata k’arasa ba Baba tafito da tulin wanki watsamata ta yi tare da “Fad’in gashinan ki wanke su tsaf..

 

 

Bayan ta gama wanke_wanken ta fara wanki sai da ta gama wankin tsaf, ko da ta gama duk jikinta ciwo yake gajiya da yunwa sun taru sun mata yawa. Wani k’aramin d’aki tashiga koda nak’arewa d’akin kallo k’arami ne sosai sai tabarmar dake shimfid’e da “Yar bagen kayanta a gefe zama tayi tareda yin tagumi tana tunanin rayuwarta tun tashin ta a cikin wannan halin take, hawaye ne masu zafi kebin kuncinta batayi aune ba taji an fincikota waje. “Toh munafuka zaman me kikemin a nan wakika ajiye da zaiyi shara da d’aura sanwa ke dai anyi “Yar banzar Yarinya duk cutata da kike bakya gani..

 

 

 

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Tashi tayi ta share gidan sannan ta had’a icce zama tayi tana fifita wutar amma tak’i takama sai hayak’i duk idonta ya yi ja tsabar wahala, ba ita tagama abincin ba sai bayan magriba. D’akin Baba tashiga ta sanar da ita tagama. fitowa tayi ta kwashe abincin sai k’ank’are kawai tarage mata tanagama kwashewa ta shige d’aki.

 

 

D’aukar abincin tayi tafara ci harta cinye bàdan takoshi ba tasha ruwa ta tayi sallah san nan ta kwanta….

 

Saukar ruwan da Baba ta watsa mata ne ya tasheta da safe, a kid’ime ta tashi cikin tsoro take murza idonta batayi aune ba taji saukar duka. Kuka take ta na rok’on Baba ta yi hak’uri gajiyar da ta yi jiya ne yasa ta makara bata saurara mata sai da tagaji dan kanta. Tafito zata shiga band’aki ne Baba ta dakamata tsawa cikin fad’a take “fad’in ajiyemin buta kuma karki kuskara ki d’ebarmin ruwa, ai kin san lokacin d’auko ruwa yayi amma saboda tsabar mugunta kikayi kwanciyar ki ban san bawan da kika ajiye ba da zai ciyar dake a banza, ba zaki wuce ki d’ebomin ruwan ko saina sauya miki kamanni..

 

 

Bokiti ta d’auka ta fita wurin d’aukar ruwan taje ba kowa sai ita kad’ai haka take ta d’ibar ruwan har sai da tagama cika komai na gidan sannan tayi Sallah, tana gama sallar tafito ta had’a murhu ta d’aura ruwa, tana nan zaune sai da yatafasa ta dama koko san nan taje takai wa Baba, aiken tayi ta siyomata kosai da sugar tana dawowa tafara sharar gidan san nan ta had’a kwanikan da suka b’ata ta wanke, sai bayan tagama ne Baba ta mik’o mata kokon a d’an k’aramin kofi ko sugar babu amsa tayi ta shanye ta wanke kofin, d’akin Baba tashiga ta gyara ta share tana gamawa taje cefanen kayan abincin siyarwar da suke…

 

Bayan tadawo haka tasake had’a wuta ta d’aura sanwar sai da tagama san nan “Ta kira Baba ta zuzzuba a kwanika, sai da Baba taci ta koshi san nan ta k’ank’are mata sauran k’anzon ta bata, cinye wa tayi san nan ta d’auke farantin tallar duk da haka “Sai da Baba tai mata kashedin kar tai mata kwantai Kuma kar ta b’atar mata da kud’i….

 

Leave a Comment