Martabar Yayana Hausa Novel Complete

Martabar Yayana Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Martabar Yayana Hausa Novel Complete

*MARTABAR Y’AY’ANA*

 

By

_Safara’u Dayyib_

 

*HOME OF QUALITY WRITERS ASSO…*

 

 

_Sadaukarwa ga y’ar uwata rabin jikina anty Jimala Allah ya k’ara hada’ kanmu ya kade’ fitina a tsakaninmu ameen_

 

 

*Da sunan Allah mai rahma mai jinkai’*

 

Page1&2

 

_____📖Kuka! ni ke sosai kamar ba gobe ina tunanin da ma a ce jiya zata dawo yau, ama ina duk ranar da ta fito har ta fadi’ baza ta taba’ dawowa ba ko dai-dai da second.

Ina cikin wannan halin naji salamar Yara da hayaniyarsu a take na zabura na mike’ ina gyara fuskata dan bani so su fahimci nayi kuka.

 

“Mama! Mama! Mama! kina ina?”

 

“Ganinan Al’husain miye kake kwalamin kira kamar wani dan farauta uhhm?”

 

“Lafiya lau mama wlh munyi kewarki kuma ma akwai labari mai dadi”.

 

Karin wasu littafai da zaku so

“Allah ya chiryaminkai Al’husain! kana kaganin d’an uwanka da kananka cikin nutsawa suke chigowa gidannan, anma banda kai babban kwabo” na fada’ ina gala mai harara.

 

Al’hasan ya yi murmushi ya ce,”sannu da gida Mama”.

 

“Yawwa babban yaya andawo?”.

 

“Eh! wlh mun dawo Mama”.

 

“Ma sha Allah! to ya karatun ina fatan ba wata matsala?”.

 

“Alhamdulillah Mama”

 

“To mad’Alllah!”.

” Abdul fahad yaya ina fatan de kunyi katatun da kyau”

 

Ya da’ga kai alamun eh.

 

Nace,”to ya yi yan kirki kuyi sauri kuje ku cire tenue, ku watsa ruwa kuci abinci ku dan huta kafin lokacin azhar ya yi”.

 

(حيا يا شبب بسرعة )

(kutafiYA matasa da sauri) gaba d’aya suka shiga d’aki ni kuma na nufi cuisine / madafi dan na masu dubarar abinda zasuci .

 

Nadan jima agwadalar kafin in fito intarda har sun saka kayan shan iska.

“Yawwa ya’ya Mama ku matso muci abinci”, na fada ina kalon Al’husain da har yanzu jikinshi ke asanyaye.

 

Na yi murmushi ina k’ara kalon yanayinshi ganin abin da ke cikin kwanon k’ara b’ata rai yayi sosai kamar zaiyi kuka!

Al’ Hasan ma yayi murmushi shiko tuni idonshi ya kawo ruwa.

 

A take naji tausayinshi ya lulub’eni ya zanyi shike gareni doli ya hakura,

Ahankli muryarshi na rawa, ya ce”mama banson garin kwaki in naci shi bai zaunamin na dunga gudawa Kenan ni de dan Allah in kinada ko k’anzo ne ki bani”.

Ya fada’ yana sakin kukan’da yake rikawa.

 

“Hhhumm” naja dogon numfashi

Na ce,”yi chiru Al’husain kaji da ace akwai wani abin kasani bazan baka kwakin’nan ba kayi hakuri Kaci kaji dana watarana sai labari kude abin da nikeso daku ku maida hankali ga karatunku na islamiya da boko

Ku kasance musu kauda kai ga na sama daku har kulum kuyi dubi da Wanda kuka d’ara Alhamdulillah muna farinciki da abin da Allah ya bamu na halal wani yana can yana nemen abin da zaici koda zaiyi amai da gudawa bai samu ba, ama gamu mu man samu mi zamuyi in bada mu godema Ubangijinmu? Kaci da bismilah in sha Allah bazai ma komi ba inma yasaka zawon to kasani yana cikin abind a Allah ya k’adarama a wanan rana ko lakaci kwakinka”.

 

“Aya bismilah ‘yayan ‘kwarai abin alfaharin mamansu”.

Gaba da’yansu su kayi bismilah sukara cin abinci cikin nutsuwa da farin ciki

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.