Kannywood News

Maryam Yahaya Ba Tada Lafiya Ga Hirar Ta Tare Da Mahaifin Ta

Maryam Yahaya Ba Tada Lafiya Ga Hirar Ta Tare Da Mahaifin Ta

 

 

 

 

 

 

 

FITACCIYAR jarumar Kannywood Maryam Yahaya da iyayen ta sun ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai an yi mata makaru ne wanda ya sa ta ke fama da rashin lafiya a yanzu.

Sun bayyana haka ne a wata ganawa ta musamman da su ka yi da mujallar Fim a daren yau.

Tun da aka wayi gari a yau dai aka dinga yaɗa labarin cewa jarumar ta na fama da tsananin rashin lafiya, musamman ma a soshiyal midiya inda kowa ke ta faɗin abin da ya ga dama a kan lamarin, har wasu na cewa jarumar ta mutu.

To sai dai jarumar ta ce ba haka labarin ya ke ba.

Maryam Yahaya Ba Tada Lafiya Ga Hirar Ta Tare Da Mahaifin Ta

 

A lokacin da wakilin mu ya kai ziyarar gani da ido a gidan iyayen Maryam a Kano domin gano gaskiyar surutan da ake bazawa a faɗin ƙasar nan game da ita, mahaifiyar jarumar ta yi masa iso zuwa wurin jarumar.

Wakilin namu ya yi kaciɓus da jarumar da ‘yan’uwa da abokan arziki su na ta hira, sun sa Maryam a tsakiya, wanda hakan alama ce ta ta na samun sauƙi.

A tattaunawar ta da mujallar Fim, Maryam Yahaya ta bayyana mamaki kan yadda ake ta surutu a kan abin da ba a tabbatar ba ko aka je aka gani ba.

Jarumar ta ce, “Kamar kowane ɗan’adam Allah ya na jarabtar sa da cututtuka, ni ma ya jarabce ni a wannan lokaci. Amma ni na san cewa komai ya na da lokaci, sai dai masu yin yamaɗiɗi.”

Da mujallar Fim ta tambaye ta ainihin abin da ya ke damun ta, sai ta ce, “Kawai dai cuta ce daga Allah.”

Maryam Yahaya

A kan ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai wasu daga cikin abokan sana’ar ta ne su ka yi mata asiri, Maryam ta ƙaryata batun da cewa, “Ni na san Allah ne ya ɗoro min, kuma ba na zargin kowa a cikin wannan masana’anta.

“Hasali ma dai, mu na zaune da kowa lafiya domin jarumai sun zo duba ni da dama; wasu na sani, wasu ma ban sani ba ina kwance. Ba abin da zan ce da Allah sai godiya bisa ni’imar sa.”

Da mujallar Fim ta tambayi jarumar ko ta na samun tallafi daga abokan sana’ar ta ‘yan fim, sai ta amsa da cewa, “Ina samu, sosai ma, domin duk wanda ya zo za ka ga ya kawo mani wani abu, da sauran su. Su na hidima da ni sosai.”

Ta kuma miƙa saƙo ga masoyan ta da cewa, “Ina samun sauƙi kuma ban mutu ba kamar yadda wasu ke yaɗawa, sai dai kawai yanzu ba na jin ƙarfin jiki na; kun san dai marasa lafiya kan ya dawo daidai.”

Bayan tattaunawa ta Maryam, wakilin mu ya ji ta bakin mahaifin ta, Malam Yahaya Yusuf, wanda ya bayyana cewa sun ɗauki kwanaki wajen 40 su na ɗawainiya da rashin lafiyar jarumar.

Karanta kuma Sai da aka biya N5m kafin ‘yan bindiga su sako ni – furodusa Ali Bulala Gusa

Ya ƙara da cewa kowa Allah ya kan iya jarabtar sa a kan komai.

A kan raɗe-raɗin da ake yi, malamin ya ce, “Ba ma alaƙanta wannan abu da sa hannun wani. Allah ne ya kawo, kuma shi zai yaye. Na gode.”

A lokacin wannan ziyara, wakilin mu ya lura da cewa Maryam ta rame sosai, domin kuwa duk wanda ya san ta a baya to yanzu idan ya ga ramewar da ta yi dole ya tausaya mata.

Rashin lafiyar nata ya kai ga har ba kowa ake bari ya shiga inda ta ke ba don ya duba ta.

Da fatan Allah ya tashi kafaɗun ta, amin.

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!