Mata a kula Kalar Saurayin da Bazai taba Aurenki ba
BAZAI TABA AUREN KI BA
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da kullum yake burin taba jikinki.
Kafin Kicigaba Da Karantawa Kimin Alkawarin Turawa Yan Uwanki Mata Dan Kwadayin Lada Gareni
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da bashi da zancen daya wuce yaba surar jikinki.
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da baya zuwa kofar gidanku hira saidai ya kira ki xuwa wani waje.
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da yake tsoron haduwa da Babanki.
_Bazai Aure ki ba, wannan saurayin da yake yawan cewa baya so a san kuna yin soyayya wai saboda munafukai.
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da idan yaga yayyenki yake buya kada su ganshi a tare dake.
_Bazai Aure ki ba, wannan saurayin da kullum yazo hira burinsa yaji dumin jikinki.
_Bazai Aure ki ba, wannan saurayin da yake yawan taba wani sashe na jikinki.
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da yake kalallameki kika bishi dakinsa.
_Ba zai Aure ki ba, wannan saurayin da zaiyi miki rantsuwa kamar ya hadiye Qur ani akan idan kin bashi hadin kai ba zai fadawa kowa ba.
_Kisani duk Abinda yafaru a tsakaninku kawai ki kaddara tuni ya fadawa wasu daga cikin Abokansa idan kinzo wucewa suna kallon ki suna yi miki dariya batare da kinsan da cewa ya kwance miki zani a kasuwa ba.
Yar uwa samari suna da tarin hanyoyi kala kala na yaudara, don yace dake inhar baki bashi hadin kai ba zai rabu dake kada kiji tsoron komi ki yarda ku rabun dama can ba masoyinki bane na gaskiya surar jikinki ce ta janyo Hankalinsa zuwa gareki. Kuma koda ace ma kin bashi hadin kan sai ya rabu dake domin bazai auri yarinyar da ta sallamasa jikinta ba tun a waje.
Da ace ya rabu dake bayan ya lalata miki rayuwa gwara ace kun rabu batare daya keta miki haddi ba,
Kadakimanta Alkawarin Dakikaima
Member Leadership Online Auwal Maikasuwa Na Turawa Yan Uwanki Mata
Daga karshe kadaki kuskura kiyi kukan bakinciki don ya rabu dake saidai kiyi kukan murnar yanto zuciyar ki da kikayi daga yin soyayya da kalar mutumin da bai dace dake ba.
ALLAH YA KAREMU DAGA BIN HANYAR SHAIDAN
Leave a Comment