Hausa Novels

Matan Aure Masu Zina

Matan Aure Masu Zina

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Matan Aure kar ku Janyo Bala’i ga Al’umma

 

Wato abin da yake faruwa na jarabawa a rayuwarmu ta yau da mutane suke ta kuka a kai, ya kamata a kullum muna laluben sabubun da suke janyo wadannan bala’o’i da masifu.

Yadda Ake Gane Mace Mai Ni’ima Tun Kafin Aure

Yanzu abin da yake faruwa cikin al’ummarmu na tozarta aure, shi kadai kawai ya kai Allah ya jarabe mu da bala’i, al’umma ta tabarbare.

 

Labaru marasa dadin ji da ake samu nan da can, na yawaitar zinace-zinacen matan aure. Abin takaici sai ka ji -wai- matar aure amma tana fita tana zinace-zinace, ko tana gayyato katti kan gadon mijinta suna lalata da alfasha.

 

Wani abin takaicin shi ne wata kazantar da ake yi, -wai- auren mutu’a da matar aure. Mace tana da miji amma kuma ta yi wani auren da sunan mutu’a.

 

Wannan abin da yake faruwa fa, na tozarta aure, da bata shimfidar miji, da cakuda zurriya da jirkita dangi ba karamin bala’i ba ne fa!

 

Mutane fa suna wasa da wannan lamari, amma Wallahi shi kadai kawai ya kai Allah ya kwashe ma al’ummarmu albarka, a shiga cikin bala’i da masifa, a kasa magance kowace matsala da ta bullo.

 

Haba jama’a, yaushe mutane za su zauna suna rayuwar dabbobi, ya zama ba su da manufa a rayuwa sai ciki da farji da biyan sha’awa kadai?!

 

Wallahi in ba a nisanci alfasha ba, musamman mafiya kazanta a cikinsu, kamar na matan aure masu bata shinfidun mazajensu, ko kuma zinar muharramai (mutum ya yi zina da ‘yar cikinsa, ko ‘yar uwarsa, ya ko kanuwa da makamantansu) to kuwa mun kulla kawance kenan da bala’i da masifa na talauci da rashin tsaro da ta’addanci da annoba da cutuka da rashin tausayi daga shugabanni. Kuma a je Lahira kowa ya girbi abin da ya shuka.

 

La’alla Shaidan ya yi wasa da tunaninka ya ce: to ga can kasashen Turai, ba irin masha’ar da ba sa yi, amma suna zaune lafiya cikin wadata da jin dadi!

 

To ya kamata ka san cewa; ku Musulmai kar ku hada kanku da arna. Shi arne talala Allah yake masa, amma kai kuma tun da ka ce ka yi imani, to dole za ka sha wahala. Allah zai jarabe ka, musamman idan ka butulce ka tsunduma cikin aiyukan sabo.

Leave a Comment

error: Content is protected !!