Hausa Novels

Matana Hausa Novel Complete

Matana Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: MATANA

 

*Mallakar*

AUTAR MAMA

 

*FREE BOOK*

 

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

 

*Whatsapp group female only*

 

 

 

 

*Wannan labarin ƙirƙirarre ne, banyi shi ɗan cin zarafin wani ko wata ba! Sannan idan yayi shige da labarinka/labarinki coincidence ne Yawwa*

 

*Comments share and vote dinku yana da matukar mahimmanci idan yayi karanci zan maida abuna ba kudi*

 

I just published “Chapter one” of my story “MATANA”. https://www.wattpad.com/1244491068?utm_source=android&utm_medium=com.fmwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=o9%2BQEkOO%2B%2BgWQIC5cTMHCzbXTwqhZlePSAfDhNhMIWOLZJlr4JeKlheUBO3S1xGgWe3pkj0STqiT1nlqZkweW%2FUmn6tof7nTk91OpomwLHuO3cwRy7Exdpf9h3z%2BHkgq

 

 

*001*

 

*KANO NIGERIA*

 

Karin wasu littafai da zaku so

“Zara’u! Zara’u!! Wai uwarki kike yi a daki da har yanzu bazaki fito ki dauraye kayan nan ba kinsa gari na damuna yanzu-yanzu hadari zai hado ruwa ya sakko? Matar da ke gaban murhu ta fada tana tada jijiyoyin wuya.

 

A kasalance ta tashi daga kan katifa tana jin kanta na mugun sarawa gaba ɗaya daren jiya bata iya wani baccin kirki ba, ta kasa sawa zuciyarta salama a kan wannan lamarin, a duk lokacin da zata tuna toh zuciyarta na dawowa danye ne, amma Allah yasan me ya tanadar ma ta maybe abinda ta ke so din ba alkhairi bane..

ajiyar zuciya ta sauke tana gyara dan kwalin dake kanta, kayakkyace irin kyan Hausa fulani bata da haske fatarta chocolate color ce, kuma tsayinta ba chan sosai ba.. fitowa tayi daga dakin tana kallon Inna da ke janyo ruwa a rijiya…

“Munafuka sai yanzu kika ga damar fitowa saboda ba kayanki bane ko? Sauke idanunta tayi daga kan Inna tana saka slippers dinta ta nufi bakin rigiyar ta ce ” Kawo na janyo! Sakar ma ta gugar Inna tayi tana kare ma ta kallo ta ce ” Baki daina kukan ba kenan ko Zara’u? Wai ke wace iriyar mayyar zuciya gareki ne? Baki da zuciya ne a rayuwarki? Ina ce har gidan nan Uwar yaron nan tazo ta ci mutuncina da naki? Saboda mayyar zuciyarki bazaki cire sonsa a ranki ba? Ni wallahi ban taba ganin me mayyar zuciya irin ta ki ba ai ko dan sarki ne inda ni ce wallahi na barshi har abada, shashanci kawai! Kuka Zara’u ta fashe dashi dan dama abinda yake cinta kenan..

baki sake Inna ke kallonta kafin ta fara tafa hannu ta ce ” Na shigesu ni Aminatu! Kuka? Godai² dake kike kuka saboda na fada Miki gaskiya? Ai kuwa kina tare da wahala wallahi, yaron yana chan zai amarce da matarsa kina nan kina asarar hawayenki, ke ba manema kika rasa ba gasu nan rututu ni da ace Saude ta ce ma take da manema haka ai wallahi da tuni an wuce wajen, ke baga karatun ba kuma baga auren ba, shi wanda kika nacewa gashi chan da amaryarsa wani satin daurin aure sai kiyi tayi ai” Daga haka Inna ta nufi daki.. Goge idanunta tayi ta cigaba da janyo ruwan zuciyarta na zafi da ciwo, bata taɓa sanin tana ƙaunar Ammar haka ba! Bata taɓa tunanin zafin rabuwa da masoyi ya kai haka ba, amma tasan Allah na sane da ita kuma zai share ma ta hawayenta insha Allah, Allah yana tare da mai haƙuri” Tana kammala janyo ruwan ta hada ruwan kumfa sannan ta fara wankewa Saude da Inna kayansu..

Inna ce ta fito daga daki tana barar gyada ta ce ” Wannan gyada dana saro bata da dadi Alquran, wata ma babu a ciki.. ita dai Zara’u bata ce komai sai wankinta ta ke yi.. zama Inna tayi a kusa da tukunyar girkinta tana kallon Zara’u ta ce ” Bakiji me nace ba? “Inna naji me kuma kike so nace? Kai Inna ta gyada tana fad’in ” Dama babu abinda zakice, da ace zancen Ammar ne nan kika fi kauri ai” Zara’u bata ce komai ba sai aikinta ta ke yi.. tana cikin shanya kayan wata matashiya ta shigo gidan sanye da uniform na islamiyya, bazata wuce 15yrs tana matukar kama da Inna sai dai ita din fara ce sol…

Bakinta ɗauke da sallama ta ƙaraso cikin gidan tana kallon Zara’u ta ce ” Laa Aunty Zara’u wankin kike? Sai da na cewa Inna ta barni idan na dawo zanyi naga baki da lafiya” murmushi kawai Zara’u tayi ta cigaba da shanyarta dan already ta gama wankin. “Cire kayanki kizo ki tuka tuwan nan” cewar Inna kallon budurwa.. “Aunty ya jikin naki? “Naji sauki Saude! Cewar Zara’u tana ma ta murmushi.. daki Saude tawuce Inna ta Kwabe baki tana kallon Zara’u ta ce ” Ni dai gaskiya zan fada miki rayuwar nan komai hakuri ake yi, ki cire komai a zuciyarki Allah yayi dama ba mijinki bane, kina zaune zaki ga Allah ya kawo miki wani wannan damuwar ta ki bazata canza komai ba Zara’u, addu’a ita ce makamin mumuni” “Toh Inna! Zara’u ta amsa idanunta na cikowa da hawaye.. Saude ce ta fito daga daki sanye da doguwar riga yar kanti, bakin murhu ta nufa.. Zara’u na gama shanya ta koma daki, a kan katifa ta kwanta tana takurewa waje ɗaya zuciyarta na ma ta wani irin zugi.. wayarta ƙirar Infinix note8 ce ta fara vibrating, dubawa tayi ganin me kiran AMMAR shine sunan da ke nunawa a screen din.. runtsa idanunta tayi kaɗan tana jin wasu zafafan hawaye na zubo ma ta.. har ta katse bata dauka ba, wani kiran ne ya kara shigowa, nan ma bata dauka ba dan sam bata so ko muryarsa ne taji hakan ba karamin kara ma ta damuwa ya ke ba.. 3missed calls daga baya sai ta saka wayar a Flight mode…

Kife kanta tayi ta fara rera kuka zuciyarta na zafi sosai..

Bayan sallar magriba tana zaune tana karatun Alkur’ani Saude ta shigo rike da kwanan tuwo da miya ta ajiye a gabanta tana fad’in ” Aunty muci abinci” Sai data kai kan simini sannan ta rufe Alqur’anin ta ajiye..

tare suka ci abincin duk da cewa bawai dadin abincin ta ke ji ba amma rabonta da saka wani a cikinta tun safe shima ruwan shayi kawai tasha. Ita ta fito da kwanon waje tana wanke hannunta a bakin rariya yaro ya shigo yana fad’in ” Wai ance Zara’u taje inji Ammar! Bai jira anbashi amsa ba ya fita.. Inna ce ta fito daga daki kallon Zara’u tayi ta ce ” Babu inda zakije, uwarsa zai miki? Ko bakinciki ya ke son kara miki saboda ba shi ya haifeki ba? “Dan Allah Inna ki barni inje” “iyeeeee! Shikenan laifi nane kije! Daga haka Inna ta koma ɗaki. Itama Zara’u daki ta koma tana kallon Saude ta ce ” dauko min hijabi a sip.. tashi Saude tayi ta fice a dakin.. bata dade ba ta dawo rike da well ironed hijab ta mikawa Zara’u.. sakawata tayi tana fita daga dakin… A tsaye ta hangoshi gaban gidansu kadan ya jingina jikin motarsa hannayensa rungume a kirjinsa, dogone fair in complexion, kwantaccen saje a fuskarsa wanda ya karawa farar fatar fuskarsa kyau da tsari. Tabbas za’a sashi jerin kyawawa.. tun kafin ta ƙaraso wajen idanunta sun ciko taf da hawaye tunawa da sati iyanzu yare da matarsa kuma wata daban ba ita ba.. tsayawa tayi daga inda take wani ƙululun bakin ciki ya tokare ma ta zuciya.. daga inda ya ke yana hango siraran hawayen da ke zuba a kuncinta kasancewar layin akwai wutar nepa. Ganin taki ƙarasowa ya sashi karasawa inda ta ke, ƙasa tayi da kanta tana jin yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi gaba daya ma yanzu haushinsa ta ke ji.. matsawa baya tayi ganin yazo daf da ita.. cikin cool voice ya ce “Zarah! Ɗago da narkakkun idanunta tayi ta saka cikin nashi, lallausan hannunsa ta ji cikin nata, kasa kwancewa tayi sai hawaye masu zafi da suka zubo kan kuncinta tana jin zuciyarta na wani irin kunci, zafi da ciwo duk lokaci ɗaya. “Zarah kiyi hakuri, i know it’s hot alot amma ki dinga mana addu’a kinji ko? Zame hannunta tayi cikin nashi tana goge hawayenta batare da tace komai ba. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana kallon ta ya ce ” Kinaso Nima na tafi gida da damuwa? Shuru tayi ba tare da tace dashi komai ba. “bakya son magana dani kuma? Ya kara fada yana kallonta. Da kyar ta iya faɗin ” Zan koma ciki sai da safe” Bata jira cewarsa ba ta wuce ciki tana jin hawaye masu zafi na biyowa bisa kuncinta.

 

*Banyi alkawarin typing kullum b saboda school Allah y bamu Sa’a*

 

*08142904255*

 

 

 

 

Autarmama ce

 Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Matana Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!