Hausa Novels

Matar Buri Hausa Novel Complete

Matar Buri Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Matar Buri Hausa Novel Complete

*MATAN BURI*

 

*EWF*

 

*BILLY GALADANCHI*

 

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai.

 

01.

 

Kallon juna sukayi a daidai lokacin da Zuly ke ƙoƙarin ganin cewar bata basu kunya ba amma ta kasa, ƙafafuwan nan suntum sun kumbura tamkar an hura balan balan, ga cikin jikinta yayi ƙasa sosai, duk kuwa irin sanyin da ake kwaɗawa ita sam bata jin sanyin banda gumi babu abinda ya ke tsatsafowa daga ilahirin sassan jikinta, walƙiya akayi mai hasken gaske, lokaci ɗaya wani tsawa mai rikitarwa ya biyo bayan walƙiyar abinda ya haddasa wa Zuly tsananin murɗewar ciki takai hannunta ta shafi ƙasan mararta, nan take ruwa ya soma bi ta ƙafarta farare ƙal, sai wani abu mai yauƙi dake zuwa tare da jini ya fara bin ƙafar shima, Rahma jikinta yana ɓari ta ce, “Billy gaba ɗaya banaji  wannan tafiyar zata yiyu a haka, Zuly bazata iyaba ko munaso ko bamaso saimun nemi wurin raɓewa saboda yanayin ta” Numfashi Billy ta sauke mai nauyi sannan ta kalli yanayin wurin, gaba ɗaya zuciyarta bata kwanta da wurin ba itafa aso samune ma ace basu baro gidanba duk a yankasu su huta, ta kuma san Rahma gaskiya ta faɗa, kan wani acikinsu ya yi magana, an kuma zabgo wata razananniya tsawar data haddasawa Zuly zubewa akan gwiwowinta, da sauri sukayi kanta, haka suka kamata su bakwai suka nemi bishiya suka danganata dashi, kafin kace meye wannan ruwan ya kuma ƙwalewa tamkar da bakin ƙwarya!! Sai tagwayen sannu suke jere mata gasunan susu bakwai ko wacce da ciki ajikinta wanda zaikai wata bakwai, biyu daga cikinsu ma watannin cikinsu tara cifcif, Zuly dama tun wancen satin EDD ɗinta ya cika haihuwar ce Allah bai kawo ba sai yanzu. Hafsa cikin takaici ta furta “Ba dubawa ko haihuwar ba ce takaici na, babu hand gloves (Safar hannu), infection zai iya shigar ta, ba kuma haihuwar ba ce tashin hankali na, abinda za’a yanka cibin da shi, kai duk ma ba wannan ba fa ana zuba wannan ruwan ya ya zamuyi da jinjiri idan ya sauka, gaba ɗaya sufa basason sanyi muba suturar arziki ba bare mu sakashi a namu” Nimcy da tun ɗazu batai magana ba cikin kasala ta furta, “Dubawan dai zamuyi still saboda bazamu tabbata muna muhawara ba”  Nisawa Hafsa ta yi sannan ta sunkuya ta fara dubata cikeda ƙarfin hali, cikin jimami ta kallesu acikin hasken dabawai ya wadata bane ba ta ce, “Haihuwar ce wlh, takai kusan 5cm ma, yanzu menene abinyi, tunda ta farko ce zata iya ɗaukar lokaci kafin ta haihu idan zata iya daurewa muyi gaba saimuyi gaba saboda zamanmu anan ba wani alfanu” Gyaran tsayuwa Nimcy ta yi ta shafi cikinta sannan ta ce, “Nida bana ɗauke da komai zan iya goyata ai idan ma ta kasa tafiya, kuma tafiyar ma ai zai taimake ta matuƙa” Haka suka rarrasheta harta daure ta miƙe suka ci gaba da tafiyar da basuda tabbacin inda zata kaisu saboda bawai sunsan inda suke ba ne.”

Tafiyar kusan sa’o’u biyu acikin ruwa mai tsananin ƙarfi zuwa wannan lokacin sun soma karkarwa da ƙoƙarin neman ceto suna rungumar junansu, Zulaiha cikin rawar murya ta riƙo hannun Nimcy sannan cikin hasken daya mamaye sararin samaniya bayan lafawar ruwan saman ta ce, “Ni’ima dan Allah ku taimakeni kashi nakeso nayi” kallon juna sukayi itada hafsa sannan suka kalleta, sai kuma Billy ta kwantar da ita ta buƙaci sudan zagayeta sannan suka fara neman tayaya zasu ga meke ƙasanta alhali ba wadatacciyar haske babu kuma wayar salula ko torchlight a hannunsu! Haka Nimcy ce wannan karon ta duba ta inda ta yi saurin ɗagowa ta kalli Billy tare da cewa “Kaine ke ƙoƙarin fita tana 9cm fa” A hankali ita kuwa ta furta “Innalillahi wa inna ilaihiraji’un, hasbunallahu wa ni’imal wakeel” Sun rasa wane taimakon zasu bata, gaba ɗaya sai tausayinta da suke fama da shi, har zuwa sanda ta soka rirriƙe na kusa da ita daga haka kuma sai kan baby yazo dafe da niyyar fitowa amma hanyar tana neman matse masa, Nimcy duk iya haƙurinta saita soma ƙoƙarin zubda ƙwalla mara misali saboda ita dama tanada rauni, tausayin kansu take gaba ɗaya, sun kasance wasu irin MATAN BURI! Wanda wannan burin ne yake ƙoƙarin hallakar dasu koma ta ce sun halaka, haka sukaita faman dannan saman cikinta ana matsa mararta a hankali hartayi nasarar haifar wani irin ƙaron yaro mai girman ban mamaki mashaa Allah, zuwanshi duniya bai ɓata lokaci ba wurin cancara uwar ƙara saidai uwarsa ta gama galabaita, ko motsi batayi ba suna haka hasken safiya ya fara makayar su, a haka sukayi amfani da atamfa suka yaga zani suka guntule cibiyar suka rabata da uwar, sannan suka nannaɗe jinjirin acikin ɗankwalin uwarsa. Ganinsu a kusada wani da tafkeken kogi  ba ƙaramin tayar da hankalinsu ya yi ba, gashi ya cika ya tumbatsa alamun ya karɓu a wannan daminar bakajin motsin komai sai kukan tsuntsaye, alwala sukayi dukkansu sukayi sallah ɗaya bayan ɗaya aruwan kogin, sannan suka dawo kan me haihuwar, inda suka fara dubata tunda haske ya wadata, Nimcy cikin takaici ta ce, “Wannan yaron ba ƙaramar yaga yayiwa Zulaiha ba, tear ɗinnan har acikin Anus Billy, bamuda yanda zamuyi yanxu saidai mu yi fatan ɓullewa lafiya da kuma wuri, saboda gaskia tana neman taimakon gaggawa” Billy Shiru ta yi suka bata lokaci kusan sa’a biyu ta huta yaron sai ihun neman nono yake, a ruwan kogin suka mai wanka yanata karkarwa alamun sanyi amma ya zasuyi sannan suka ɗauki hanya bayan sun tilastwa uwar ta shayar da shi abinda ba komai a nonuwan nata sai sama sama yasha, kwanansu goma a hanya mangoro kaɗai suke sha, hanyar dabasusan doguwa bace saida sukayi kaukuren dosarta, hanyar dabasusan ƙungurmin jeji bane ba saida buri ya sa sukayi kuskuren dosarta, wannan shine gaba kura baya sayaki!.

Karanta Littafin Ni da Yaya Sadeeq

Jinjirin iskar safiya tana kaɗawa yana ƙanƙame jikinshi wuri ɗaya cikeda nuna alamun jin tsananin sanyi, yama kasa buɗe idonsa, uwar sa dake rungume da shi wasu zafafa. Hawaye suka silalo daga idonta suka kwaranya har suna sauka akan kuncin yaron da kuma cikin bakin sa, rufe ido ta yi na wani lokaci sannan cikin tausayin yaron ta furta, “Zamana acikin matan buri bai janyomun komai ba sai taagwaron dana sani mara misaltuwa, haƙiƙa danasan duniya ta zata juya acikin daƙiƙa kaɗan dana roƙi Allah ya amshi raina kafin zuwan wannan ranar! Da akace kaina kaɗai na saka a wannan fitinar bazanji komai ba akan ɗan tayin jinjirin da baisan komai ba a wannan duniyar mai ruɗarwa! Dafa kafaɗunta Nimcy ta yi cikin tausayawa kansu kafin ta ce, “Zulaiha dan Allah ki sassautawa kanki da waɗannan kalaman marasa amfani, dukda kuskuren da dukkanmu amma babu shakka wannan abin wani yankine daga cikin ƙaddarar mu da duk dabara bazamu taɓa iya kauce mata ba, dan Allah karki janyowa kanki wani ciwon, ga haihuwa a wannan yanayin ga kumburi na tabbar jininki ne ya hau” A raunane ta kalleta, har lokacin muryartaba sarƙe tana rawa ta furta, “Yanzu Ni’ima ta ina zamubi mubar wannan wurin, kwata kwata bana ganin iyakar ruwan nan ta hanyar tsayinsu sai faɗinsu, yaya zamu tsallaka? Ko baya zamu koma, yarona sanyi yakeji Ni’ima, kalli yanda yake karkarwa” Duƙar da kai Nimcy ta yi cikeda jimami hankalin ta ya tashi fiye da tunanin, gaba ɗaya ta kumbura, ga alama sambatu ta ke, ga iyayen yanka ta ko ina a jikinta, gaba ɗaya kana kallon yanayin ta zaka fahimci tsantsar wuyar datake ciki, ga ƙaunar jinjirin da takeda tabbacin idan akaci gaba da tafiya a haka bazai kai labari ba! “Inshaa babu abinda zai sameshi, bara in goyeshi da ɗankwali na kinji” Shiru sukayi na wani lokaci kafin daga bisani su yanke shawarar bin hanyar kaucewa ruwan ko zasu samu mafita.

 

Idan Feezo jajir sanda ya ke kallon wurin, cikin tashin hankali yake magana da Bash, “Yaran nan sun iya rainin hankali da samun wuri, su har sunga wurin guduwa a wannan ƙungurmin jeji? Zanga mai cetonsu duk duniya, bazamuje neman su ba, amma na tabbatar su zasu dawo neman mu, idan suka kai iyakar jejin nan babu shakka zasu nemi mafita da kansu” Bash cikin takaici ya ce, “Feez ga kuma ko waccensu mun kusa cin riba akansu, inaga wannan Ni’imar ce kawai batada ciki a cikinsu, amma ai duk sun tsufa wahalar ciki ma bazata barsu suyi nisa ba amma abina bamu saniba yaushe suka tafi? Yaufa satinmu biyu bama nan” Shiru Feezo ya yi na wani lokaci sannan a hankali ya riƙe wandon sa, “Ita waccen Zulaiha zata kanshe a banza, ban taɓa haɗuwa da mace mai daɗin ta ba, har ina shirin ajiye ta inyita sukuwa a kanta, tafiyarsu batamun zafi ba kamar inda zan sauke nauyin marata, kasan a zaria na hau mata sama da goma kafin mu dawo bamai irin taste ɗinta wlh” Ɗab murmushi Bash ya yi “Feez amma kasan ka ce mun zan hau in ɗana inji ko?” Tsaki ya ja mai sauti, “what ever dai tunda basa nan ai abu ya lalace, amma idan suka dawo saina wulaƙanta su wlh, tunba Zulaiha ba laifi biyu, ina fama da jarabarta kuma yau ya dace ta haihu ko?” Bash yana tsakin shima ya furta, “Yau kuwa ya dace ta haihu, idan sun raba jinjirin da uwarsa magana ta ƙare” Shiru sukayi cikesa baƙin ciki sannan suka juya kawai tare da barin gidan gaba ɗaya!

 

MATAN BURI!! LITTAFI MAI CIKE DA SARƘAƘIYA DA KUMA SABON SALO MAI ƘAYATARWA.

 

MOM NU’AIM.

07084161619.

 

 

 

 

 

1 Comment

Leave a Comment