Hausa Novels

Matar Gurgu Hausa Novel Complete

Matar Gurgu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

page 1-5

 

Zaune take abakin gadonta tana shan shisha tana lunshe idonta yayinda kunnuwanta ke jiye mata zafafan kalaman soyayya ta cikin wayar data kanga akunnenta wanda masoyinta Anwar ke feso mata cikin kunnan nata.

 

“my humy kin fiye min kowa ackn family na samun irinki sai ansha wahala,ko acikin mata babu mace mai dadinki da Ni’imarki babu macen data iya ihu ayayin jin dadin kwanciya dan Allah kidawo Abuja mu mori junanmu kinga sanyi akeji kyanta ace kullum muna tare a cikin bargo in dare yayi.

 

Humaira taja ajiyar zuciya kana tace”bazaka gane ba Anwar walh inason tahowa Abuja nima nayi kewarka amma babu wannan damar tunda kawu yaje takanas ya kamoni acan aka dawo dani gida akasamin takunkumi ko unguwa sai an hadani da kanwata ta rakani walh yayana daya dawo daga lagos tsananin tsaro yake min kawu yasa yakula da duk wani motsina ko kasan ma Aure suke so suyi min…. “Aure fa kikace humy??innalillahi yanzun kina nufin kin kusa zama matar wani,? walh bazan iya jure rashinki na har Abada ba kiyi gaggawar sama mana mafita inba haka ba zansha poising na mutu….” karka fara Anwar dan walh inhar kayimin asarar kanka bakayimin Adalci ba domin ina mugun sonka.

 

Anwar yayi tsaki daga can inda yake kana yace “to walh inhar baki samo mana mafita ba saina aikata gara ki rasani aduniyar duka.

 

Humaira ta gyara zama bayan tasake jan hayaqin shishar kana tace “kana ji ko Anwar so nake Ana daurawa idan na tare agidansa Ince masa zanje bikin kawata Abuja inyaso sai inzo gunka ka gurji angwancin nasa tunda shi miskini ne.

 

Anwar yayi dariya yace “kaji yar gari shiyasa nake mugun sonki humaira,to Amma meyesa zasu Aura miki miskini fatan ba kuturu bane ba ko makaho.

 

tayi dariya tace “ai inda makaho ne da sauqi zanta guduwa ne batare dana tambayeshi fita ba,to Amma wannan babban Miskini ne wato *GURGU*…

 

yayi saurin tarar numfashinta dacewa “Gurgu kuma humaira? ke ko me kikai musu zasu Aura miki gurgu Alhalin kyanki da ajinki yakai ki Auri shugaban kasa ko gwamna.

 

tace “hhuumm wai nan horo ne zasuyi min kuma kyauta aka bashi ni sati biyu kawai aka tsaida na bikin yanzu ma haka saura sati daya dayake dan uwa ne shiyasa akai masa wannan gatan.

 

dariya Anwar yayi yace “lallai kuwa an masa gata ke kuma Anmiki mugunta,to Allah yasa dai ba ‘yar jagora zaki zame masa ba wajen fita bara….

 

 

humaira tace “kai wannan gurgun me aji ne da abin hannunsa kuma yana da kyau gashi… “yi min shiru waye baida kyau da zaki ringa yabon wani dan iskan can da ban…wato kin ma fara son shi da har kike koɗashi inaji ina gani…

 

itama tayi saurin tararsa da fadin “sorry my Anwar walh banyi dan in sosa maka rai ba,ai duk kyansa duk arzikinsa walh bai kaika ba ko kusa ko alama,bare kuma aje ga kakan Dadi wato iya sex kafi duk maza Cakwala dadi fa ka manta sunan da nake kiranka da shine..?

 

Anwar ya murmusa saida tajiyo sautin murmushinc tasan takan faranta masa ne inhar tayi masa hakan

 

dan hakan saitahau masa kirarin data saba masa na iya shege “Cakwala dadi na kogin zuma,Runbun dadi na rijiyar Ruwan dadi, kaci dadi kasha dadi babu me hanaka na Gidana.

 

yayi dariya kana yace “hhmmm to godiya nake my humy zan kiraki anjima bari na daga wayar Dady naga kiransa yashigo.

 

sukai sallama ta kashe ta ajiye wayar agefe ta shiga tunanin yanda zata kashe Auren idan aka daura dan bazata iya zama da Gurgu ba Alhalin tana dirarriyar mace me azababben kyau kuma ita ba Nakasasshiya amma iyaye zasui mata haka.

 

gashi ta saba da Anwar tun zuwanta gidan Galar Abuja dashi ta saba bata jin dadin kowane namiji inba shi ba to ita kuwa me zatayi da wani Gurgu.

 

*****

Da Safe Humaira ta gama shirinta Tsaf Ta fito daga cikin Dakinta ta rufe dakin tasaka masa key ta fito a tsakar gidan matan gidanne ke mata kallon banza wata kuma na mata kallon Allah ya shiryaki

 

wasu kuwa kallon Tausayawa Rayuwarta suke na ganin yanda takeyin Rayuwa mara ‘yanci

 

Ta tsaya atsakar gidan kusa dasu takallesu Fuska a hade ba alamun ma tasaki tace musu “Ina Tsoffin gidan? (Tana nufin mazan gidan Kawun nan ta da suke Control nata)

 

babu wacce tace mata kanzil acknsu saima da suka fara tashi daya bayan daya suna barin gurin dansu cusa mata takaici kowacce nayin sashinta

 

su biyar ne dama saiya rage mace guda agun wacce tadan fisu sakar mata kenan Mama Rabi

 

Humaira taja tsaki kana tace “Aikin banza ai bansan antsane ni ba sai naji anhadarmin anmin Duka tukun na.

 

Mama Rabi tace “To amma Humaira dawa kike acikinmu?wa kikaji yace miki Uffan?ke meyesa akida kunya ne.?

 

Humaira tace “To amma ai tambaya nayi sbd Antsaneni babu wacce tabani amsa cikinku ko? wai me na kashe muku ne…. ‘” Uwarki da Ubanki kika kashe… Nace uwarki da ubanki kika kashe ko baki jini ba.?

 

Muryar Kawu Bala taji abayanta yana magana da kakkausar Murya.

 

saida cikinta yayi qugi tsabar tsorata da dajin muryarsa da tayi.

 

Kawu bala yace mata “rashin kunyar da kika saba kikaxo kiyi musu ne.

 

ta kalleshi kamar tayi magana kuma saitayi shiru.

 

ya nunata da Yatsa yana fadin “kishiga hankalinki walh dan yanxun jikinki zaiyi tsami,wato Bakin cikinki yakashe mahaifanki shine muma kikeso ki kashe mana mataye ko,?

 

kanta akasa amma ta zoɓaro baki

 

 

kawun yaci gaba da fadin “Ina zakije ma ?kuma wa kika tambaya zaki fita?

 

Humaira tace “Gidansu kawata zanje Ummi zata rakani karbo dinkunan da zansaka da biki.

 

“Da izinin wa?

 

Tace”yanxun nake da niyyar zuwa gareku na tambaya ai.

 

kawu bala ya gyada kansa yace “to nabaki awa guda inbaki dawo akan lokaci ba sainayi maganinki.

 

 

Ta gyada kai kawai yayinda saida tabari yashige sashin matarsa kana ta fita da sauri.

 

A gidansu Kawarta Ummi kuwa bayan sun kebe ummin ke cewa “Ke wai da gaske kin yarda da lamarin Aurennan kin hakura zaki zauna ?

 

Humaira tace “to kawata inban yarda ba ya zanyi dasu,kinaga na dade ina yin bariki amma basu barniba,Auren farko ma yimin sukai na biyu ne suka bari nakawo to ga wannan ma…..Ummi ta dafe kirji “Nashigesu kina nufin kintaba yin Aure dama?

 

Humaira ta murmusa tace “kwarrai ma kuwa har 2 ga na uku za’aimin da Gurgu…

 

Ummi tace “wai da gaske Gurgu ne? nifa nazaci wasa kikemin.

 

humaira tace “Sam ba wasa nake miki ba Gurgune,Gurgun ma fitinanne wanda yafi me kafa lalata da iya shege domin har Koken yake saidawa yana safarar kayan maye sosai.

 

Ummi tace”walh kinyi wauta ni rashin wayonki ma nagani dahar kika dawo gida zasui mk wanann danyen Aikin na Auren GURGU tab ai walh idan nice bazan ma dawo gidan ba gaba zan kara bare har aganni ayimin wannan gagarumar Cutar.

 

Humaira tace “kinsan nayi fitina arayuwa sannan bana musu biyayya kawun nan nawa mutum guda nafi shayi shine Kawu bala sai ɗansa da aka taba bashi Aurena yaki karba yaya badamasi shima wutane bashida mutumci shima ina shayinsa shine ma yanemo inda nake agidan galar ta mu yataho dani har hakan ta kasance akaina,ashe shirinsu kenan su Aura min Gurgu dan suyi magani na,nikuma walh kwanton Bauna zan musu gaba zan felle idan nai masa dole yasakeni dan bazan zauna dashi ba yanzun ma ganin na dade ina bariki shiyasa zan dan huta na wasu watannin….Ummi tace “wai saikiy ta cewa kin dade wane irin dadewa bacin sau daya jal akai miki Ajo,ai kyan dadewarka ayi maka ajo biyar ko fi ke fa ko shekara uku bakiy ackn harkar ba,nifa Ata biyar nake kuma Ajo dai me sunan Ajo na Takama da samun nera anyiminshi yayi biyar walh yanzun ma dan dai ina son Faruk ne yasa nadawo gida zaman istibra,i da babu abinda zai dawo dani to amma faruk da Auren yake so na shiyasa nabiye masa dan ma yanada abin hannunsa.

 

Humaira tace “hakan yafi ai ka Auri me hali,kuma nima ai Wanda zan Aura din yana da hali sosai wataqila ma yafi faruk dinki kudi…

 

ummi tace “Karfa ki manta faruk fa yana simogalin na shige da ficen kayan abinci ɗanye sannan yana da Club nashi na kanshi.

 

dariya humaira tayi kana tace”lallai yahada arziki,tsakaninsu dai Allah ne masani Amma nikam Ummi da inyi Rayuwar baya data gudana aguna gara min in Auri GURGU…

 

Ummi tace “kama yaya kina nufin Rayuwarki da Anwar a can gidan gala?

 

humaira tace “wannan nake nufi ba,ai rayuwata da Anwar me dadi ce kowa yasanmu muna gudanar da soyayyarmu gwanin sha,awa ne kawai Rayuwa baya danayi ackn Gidanmu Rayuwar qunci da Takaici da kuma Dana sani.

 

Ummi tace”wai kamar yaya ,kina nufin kinsha wahala ackn gidanku? iyayanki ne suka wahalar da ke ko suwa,?

 

Humaira ta girgiza kanta tace”sam basu ba ne,Ai mahaifiyata bata da magana ma sannan tana da hakuri matuqa ga kara da kawaici gara ma mahaifina Amma yanada fushi saidai yanada hkrn shima su 6 ne ackn gidan duk maza suna zaune da matayensu kowa a sashinsa kannensu mata 4 suna gidan mazajensu walh ummi nasha wahala da iyayena suka rasu agidannan karshe ma sai suke cewa A dalilina iyayena suka mutu,,,haka kuma naje nayi zaman Gidan yari akan kashe mijina na fari danai…. dafe kirji ummi tayi ta zaro ido tace “ke humaira da gaske,?

 

Humaira ta gyada kanta tace “walh da gaske kawata kinsan ai nace miki mijina na farko auren dolene su suka zabamin shi bana sonshi haka Suka Auraminshi to walh nasha wahala a rayuwata dashi har mutuwarsa na gwammaci ma ina ma yana duniyar.

 

ke intakaice miki ummi adalilin takurawar da ‘Yan uwan mahaifin nawa sukaimin yasa nabar gida nashiga duniya..

 

Ummi tace”Tabdijan dama sune sanadi amma suke nuna damuwarsu akai to aiko zanso naji labarinki humaira.

 

humaira ta gyara zama tace “To zanbaki kadan daga cikin Labarina amma atakaice sbd lokaci kar yaja injanyowa kaina Duka agun Kawu bala don ya bani lokacin komawa yanzun ma karya na shirga masa kan cewar zanzo gunki muje mu karbo dinkunan da zansaka a bikin shiyasa yabarni na fito…

 

Ummi ta gyara zama ta zaqu taji yanda Humaira tayi rayuwar qunci da gwagwarmayar zama da kawun nanta da kuma abinda yasa aka kaita kurkuku.

 

 

 

Leave a Comment